+2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria

Download and read free hausa novels

SADAUKI UBAN SADAUKAI part 1A

SADAUKI UBAN SADAUKAI !!


littafina daya 1


littafin shuraih usman


part 1A


Kimanin Shekaru Dubu Daya Da Suka gabata


A Nahiyar Sudan Anyi Wata Birni Mai Suna Yemen


Birnin Yemen Babbar Birni Ce Don Duk Nahiyar Sudan Babu Wata Birni Data Kaita Girma tattalin Arziki Da Kuma Yawan Dakarun Yaki


Birnin Yemen Na Karkashin Jagorancin Wani Adalin Sarkine Ma'aboci Addinin Musulunci


Sannan Kuma Dukkan Jama'an Wannan Birni Addini Daya Suke Bi itace Islama


Sarki Ayyub Yakasance Yana Matan Aure Guda Hudu Sannan Kuma Yana Da Ilmin Addini Daidai Gwargwado,sannan Yana Kamanta Adalci A Tsakanin Matayensa Bil Haqq


Wayannan Mataye Nasa Kyawawane Na Gaban Kwatance Dukkanninsu Sun Fito Ne Daga Manyan Gida


In Kadauke Amaryarsa Mai Suna Taufidatu Itace Takasance Ya Ga Wani talakan Masinci


Bil Haqq Taufidatu Ta Dare Dukkan Kishoyinta Kyau Nesa Ba Kusa Ba


Hakan Ce Ma Ta Sanya Hassada Gami Da Kishi Suka Daru A Zuciyoyin Wayannan Kishiyoyin Nata


Sarki Sam Ya Tsani Zalunci Da Azzalumai Wannan Shiyasa Talakawa Ke Jin Dadin Mulkinsa

BABBAN GORO part 1D

BABBAN GORO
-------------------------
Littafina daya
.
Part 1D
.
With shuraih 99%
Typing by :- http://facebook.com/shuraih.usman

.
Al'amarin kifyan sarkin aljanu kuwa wanda gidansa yake cikin karkashin kasa , a tsakiyar ruwa, rabon daya fito tun lokacin daya bayar da tsaron bishmalu dan sarki kan'anu na misra
.
A halin yanzu bishmalu ya zama saurayi dan shekara sahirin da biyar. Kuma a iya tunaninsa bai da wani uba wanda ya fi kifyan , amma bai taba ganinsa ba a zahiri sai acikin madubin tsafi
.
Fitowar sarki kifyan keda wuya aka lullubeshi masu gaisuwa nayi, masu bambadanci nayi shikuma sai ya hau kankaragarsa ta mulki ya zauna , sannan yace aje a zo masa da dansa , nan take aka zo da bishmalu , bishmalu ya durkusa yayi gaisuwa.
.
Kifyan yace" na fito ne domin ganinka , dakuma son gabatar da wani muhimmin zance a gareka , wanda baka san dashi ba , yanzu ne lokacin da zan yi maka bayani ka fahimta tunda ka mallaki hankalin kanka .ya kai bishmalu ka dubi kowa dake cikin fadar nan ka dubi kanka ,zaka ga cewa ba irin kirar halittar ka bane , domin mu aljanune kai kuma bil'adama ne, to kasani kai ba dana bane . iyayenka bil'adama ne kamar kai , ni sato ka nayi tun kana jariri sakamakon laifin da mahaifinka yai mini, ya auri matar dana ke so"
.
Nan take kifyan yai nuni da hannunsa izuwa wani madubin tsafi ! Sai ga hoton sarki kan'anu kwance bisa gado a turakarsa yana jinya.
.
"Wannan shine mahai finka, daga nan zuwa inda mahaifinnan naka yake tafiyar wata da watannice . Kasani ya kai bishmalu son dana kewa mahaifiyarka shine ya dawo kanka a yanzu.
.
Kifyan ya sake nuni da hannunsa izuwa wani madubin tsafi sai ga hoton ashwar bisa doki a dokar daji yana tafiya.
.
"Wannan wani jarumine da ake kira ashwar , wanda ya taho da niyyar fitar dakai daga cikin gidannan ya mai da kai hannun babanka, amma bai san cewa yayi babban kuskure ba , har duniya ta tashi ba wani mahalukin bil'adama daya isa ya shigo cikin fadata"
.
Kifyan na gama wannan jawabi ya tuntsure da mahaukaciyar dariya wadda tasa gidan ya kama girgiza , har sai da ya rufe bakinsa sannan gidan ya tsaya daidai.
.
Bishmalu ya dubi sarki kifyan yace " ya kai sarkin sarakai badan kada ranka ya baci ba da nace kasa akaini wajen mahaifina mu gana "
.
Cikin fushi sarki kifyan ya mangare bishmalu da iskan bakinsa sannan yace" a kul nakara jin kace na kaika wajen babanka"
.
'Da nine inba sai ankaini wajena babana ba ko ata masifa 99% ke magana
.
.
"To kasani daga yau duk kimarka ta zube a idanuna gwarama ka kasheni na huta da takaicin abin daka yiwa mahaifina"
.
Kifyan ya sake bushewa da dariya , sannan yadubi fadawansa yace" ku na son wannan yaron ko kuwa na kasheshi yanzunnan?"
.
Gaba daya suka rude da cewa " muna sonsa ya sarkin duniya"
.
Wannan hayaniya ta fadawan kifyan tasa bishmalu ya firgice ya fadi kasa sumamme,
Nan take sarki yasa akayi wani turare na hayaki , aka fesawa bishmalu ya farfado, sarki ya sake dubansa yace
" Yanzu wakake so mu ko iyayenka"
.
Bishmalu yace" ku nake so, don ku ne kuka reneni , ban san wadan can ba"
.
Koda jin haka sai fada ta rude da shewa , nan take akayiwa bishmalu wanka ya zama dan sarki kifyan, aka yi biki da gagarumat walima , bayan an kare, sarki kifyan ya zagaya da bishmalu cikin fadodinsa guda ashirin da bakwai da ke cikin wannan gida na sarauta, ya nuna masa sirrikansa gaba daya banda sirrin inda ruhinsa yake.
.
Wannan shine abin daya faru tsakanin sarki kifyan da bishmalu dan kan'anu na misra, wanda ke can kwance cikin jinyar rashin lafiya tsawon shekaru ashirin da biyar.
.
.
Shuraih 99% ke ce daku
.
Ashwar na can cikin jeji ya kutsa kai , bai san ma inda yake nufa ba . Kwanci tashi yaje wani gari , yasamu wasu mutane a bakin kofar shiga ashwar ya sauka daga kan ganjarma yayi wa mutanen sallama , sai yaga basu kalleshi ba , ya kuma matsawa yai sallama , kawai sai suk zabura wajen su goma shahudu suka kewayeshi, wani daga cikinsu yace
"Kai yaro mene ne ya biyo dakai ta wannan kofar? Baka sani ba cewa garinnan yana da kofofi hudu amma wannan ta zama mallakinmu? Ba a wucewa ta nan sai anbiya harajinka dana dokinka"
.
Ashwar ya dubesu a wulakance yace" menene kuma haraji?"
.
Wannan batu ya harzuka gudansu, don haka sai ya zagaya bayan ashwar da nufin ya sharara masa mari, caraf sai ga hannunsa a hannun ashwar, ya zaci abin na wasa ne , sai yaji ana rumurmutse masa hannu kamar gyale , mtumin ya ringa ihu da sauran suka ga haka sai suka debi sanduna suka rufe ashwar da duka titim! Titim!! Suna bugunsa sandunan na karairayewa , tamkar akan dutse suke bugawa . Gaba dayansu suka firgita da ganin wannan al'amari, sai suka arce
.
Ashwar ya kada linzamin dokinsa ya shiga cikin gari . Yana cikin tafiya yaga wasu 'yan mata su shida kyawawan larabawa , sun debo ruwa a tulu daga rafi . Ashwar ya dubi wadda tafi sauran kyawu yace " 'yan mata dan Allah taimaka mini da ruwannan mana na sha"
.
Batare da jin kai ko wulakanci ba ta miko masa tulunta, Ashwar ya karba ya kafa kai ya zuke fiye da rabinsa, sannan ya miko mata, sannan yayi godiya .
Sauran 'yanmatan suka dubeta suka kyalkyale da dariya , wata cikinsu tace
.
"Yanzu ke Asma'u don wahala bata isheki ba shine zaki bayar da kyautar ruwan da kika debo acan nesa da gari , aikuwa mu baza mu koma da baya ba don raka ki debo wani"
.
Nan take suka wucu su kai gaba , ita kuma Asma'un sai ta dora tulunta aka ta juya da baya dan komawa rafi. Koda ganin haka sai ashwar ya sauka daga kan dokinsa yace ta hau , shikuma ya ruke mata tulun , batare da musu ba Asma'u ta hau kan ganjarma Ashwar ya ruke mata linzamin , su kai gaba suna tafe suna hira kai da kagansu sai ka dauka bawa ne da uwargijiyarsa, kasancewar ashwar bakin fata ita kuma balarabiya.
.
Shuraih 99% nake ce daku"Kai kuna tare dani kuwa "
.
"Baiwar Allah shin anan garin kuwa akwai musulmi mabiya Addinin musulunci?"
Ashwar ya tambaya
.
"Kwarai kuwa , fiyr da rabin mutanen garinnan duk musulmine sai de , saidai sarakunanmu azzalumaine , kuma mai karfi shi ke da ikon yin abinda yaga dama , yanzu haka da akwai wasu azzalumai 'yan fashi da suka addabe mu, shi yasa da zarar magariba tayi kowa sai ya shige gidansa ya rufe kofa , komai zafi ba a isa ayi kwanciyar waje ba , in kuwa mtum ya kwanta a waje saidai da safe a ga gawarsa "
.
Koda ashwar yaji haka sai ya cika da mamaki yace " Ni kuwa da yardar Allah zanyi muku maganinsu daga yau sun dai na yin fashin"
.
"Haba dan samari wane kai , ai BABBAN GORO SAI MAGOGIN KArFE. Mutanan da sun fi mayakan garin nan ma karfin tsafi da sihiri , ya za kai da su"
.
"To shikenan tunda kina shakka ina so ki amince mini kwana a kofar gidanku"
.
"Wannan mai saukine amma fa duk abin daya sameka kada ka zargi kowa ka zargi kanka"
,
99% ke magana kuna biye dani kuwa
.
Haka dai ashwar da Asma'u suka ci gabada hira har suka je rafi suka debo ruwa suka dawo.
Asma'u takai ashwar gidansu ta gabatar dashi a gaban iyayenta , tare dayi musu bayanin tarar aradu daka wadda yace zaiyi cikin mamaki mahaifin Asma'u ya dubi ashwar da kyau yace
.
"Kai yaro shin rayuwar duniyace ta ishe ka haka ko kuwa wani abin bakin ciki ne yasa kazabi mutuwa akan rayuwa?"
.
Ashwar yayi murmushi yace " baba babu ko daya amma dai ni nakasance mai son yin fada da karya da kuma azzalumai, na tsani kafirci da zalunci , burina Addinin musulunci ya rinjayi kafirci a doron kasa, bana dogoro ko takama da karfi ko tsafi,face taimakon ubangijina wanda shine masanin dukkan abinda ke fili da boye "
.
Wannan batu yasa jikin mahaifin asm'u yai sanyi yayi shiru daga bisani yace
"To masu magana sunce ba'a kwacewa yaro garma amma wannan garmar da kake shirin dauka tafi ka nauyi sai dai muce Allah yaba sa'a"
.
Haka dai ashwar ya cigaba da hirarsa da Asma'u da iyayenta har rana ta fadi.aka kawo abinci sukaci tare gabadaya , magariba nayi suka yi sallama da shi suka shiga cikin gida suka rufe kofa .shi kuwa gogan sai yai alwala yai sallah a kofar gidan , har ya idar da sallar yayi yan Addu'oinsa baiga wani yazo gare sa ba ,
Ashwar ya debi ruwa arijiya ya baiwa ganjarma sannan yai shimfida. Agefe gida yayi kwanciyarsa tamkar yana cikin dakin matarsa.
.
'Yan fashinnan da suka saba shigowa sai gasu sun dira akan ashwar kimanin su arba'in ashe Asma'u a soro ta kwanta koda taji magan ganunsu sai ta kwalla ihu take ashwar ya farka , alokacin har daya daga cikinsu ya hau kan ganjarma yana cewa
" Ni kam yau na fito a sa'a na samu lafiyayyen doki"
.
Ashwar ya mike zumbur ya dube su yace " ku azzaluman bayi me ke tafe daku"
.
Gaba dayansu suka bushe da dariya , dayansu yace
"Yau kuma bakon marar kunya aka samu a garinnan ? Kai yaro yau karar kwana ta kawo ka makasa "
.
Wannan batu ya fusata ashwar nan take ya hausu da duka, gashi babu ko allura agareshi amma su da manyan makamai a hannunsu ya zame musu ala kakai, duk wanda yakai masa sara ko suka sai ya goce cikin zafin nama ya kama hannunsa ya murde ko ya karya. Cikin kankanin lokaci ya zubar da mutum goma kasa sumammu da 'yan fashinnan suka ga haka sai suka fara jarraba tsafe tsafensu da sihirce sihirce, amma duk suka zama a banza don basuyi tasiri ba akan ashwar , sakamakon Addu'ar daya ke ta karantawa a zuciyarsa , nan fa wuri ya dada ya mutsewa , ihu da kuwwar 'yan fashin tasa duk jama'ar garin suka bubbude gidajensu suka fito, don ba'a taba jin irn wannan tashin hankali ba a garin . Yayin da jama'a suka taru sai aka iske ashwar tsaye shi kadai a kofar gidansu Asma'u .
'Yanfashinnan gaba dayansu su arba'in suna kwance cikin jini, wasu a sume , wasu akarairaye. Nan take gari ya dauka da shewa don farin ciki aka yi ta al'ajabin jarumtakar ashwar.
.
Koni nan nafishi jarumta 99% ke magana
.
Ita kuwa Asma'u saita ruga da gudu ta rungume Ashwar tana cewa ta samu mijin aure Mutanen gari sukayi ta kawowa ashwar kyautar dukiya, amma ko daya bai karba ba .
Anan ya sanar dasu labarinsa da dalilin fitowarsa daga garinsu, ya bukaci o akwai wanda yasan inda birnin duma yake .
Gaba daya akayi shiru sai daga can wani dattijo tsoho tukuf wanda duk garin babu mai tsufansa ya dogaro da sanda ya karaso inda ashwar ke tsaye ya dafa shi ya ce
.
"Yaro nasan inda birnin duma yake"
.
Koda jin haka sai farin ciki ya kama ashwar , ya rungume tsohon yana mai matukar farin ciki, daga nan yabi tsohon zuwa gidansa.
.
Daga nan zuwa birnin duma tafiyar shekaru ukune.
Birnin duma garine na aljanu zalla inda sarki kifyan ke mulki" dattijo yafadi tare da ajiye numfashi.
.
Cikin tsananin damuwa Ashwar yayi ajiyar zuciya yace " hakika duk abin da aka fadi haka yake , amma ni yanzu guiwata tayi sanyi , burina ya yanke ,domin babu yadda za'ai naje birnin duma a cikin kwanankin da aka diba mani wa'adi"
.
Bisa mamaki tsohon ya dubi ashwar yace "ban gane bayanin ka ba "
.
Shuraih ke cewa daku
.
Nan take ashwar yai masa cikakken bayani kan sharadin da sarki Abul dinar ya shimfida masa , kafin ya amince ya aura masa gimbiya mabaruka . Tsoho yayi shiru yana tunani har izuwa wani dan dogon lokaci , sannan yace
"Ya kai wannan jarumi ina da wani dan'uwa wanda zai iya taimakonka a bisa wannan al'amari sunansa raslanu , bawan Allah ne wanda ya kaura daga cikin gari ya koma can jejin surgam yaci gaba da bautar ubangiji, don kada wani abun duniya ya rude shi daga nan zuwa jejin surgam tafiyar kwana goma sha biyuce, amma ka sani akwai ababan hadari a wannan jeji, fiye da shekaru sittin a tarihi babu wani mutum wanda ya keta ta cikin surgam batare da ya zama gawa ba, face wannan dan'uwa nawa wato ruslanu. Shi ma hakan ta farune sabida Allah ya hore masa baiwa mai dumbin yawa . Idan har ka sami nasarar ganinsa , tamkar ka sami nasarar shiga fadar sarki kifyan ne"
.
Ashwar yayi shiru yana nazarin wannan bayani sannan yace " ya kai wannan dattijo mai albarka , ina tabbatar maka da cewa ko zan rasa raina sai naje jejin surgam na sadu da wannan dan'uwa naka Ruslanu, kuma gobe goben nan zan yi shiri na tafi
.
Ashwar na rufe baki suka jiyo tambura sun cika gari , cikin sauri suka fito daga cikin gidan, kawai sai su kai arba da mutane jingim akasa , sun rako wani doki guda daya izuwa ga ashwar , ba kowa bane akan dokin face Asma'u ta sha kwalliya da ado irin na amare, cikin mamaki ashwar ya tambaya
"Me ke faruwane"
.
"Ai an daura aurenka ne da Asma'u , yanzu haka amaryarka muka kawo maka"
Mahaifin Asma'u ne da kansa tabada wannan amsar
.
.
Laifin dadi karewa
Abdulziz sani m/ gini ke ce daku
Kash! Mai karatu anan zan dakata sai mu hadu a BABBAN GORO KaSHI NA BIYU don mu ji yadda zata wakana
.
SHIN JARUMI ASHWAR ZAI YADDA DA WANNAN AURE DA AKA YI MASA BATARE DA NEMAN AMINCEWARSA BA?
.
ME ZAI FARU YAYIN TAFIYARSA ZUWA JEJIN SURGAM?
.
A CIKIN WANI HALI GIMBIYA MABARUKA TAKE AYANZU?
.
SHIN ALJANIN BOKA GULMANU KUTUNTUMA NA BIYE DA JARUMI ASHWAR KUWA?
.
TA YAYA ASHWAR ZAI SHIGA BIRNIN DUMA HAR YA SHIGA FADAR SARKI KIFYAN YA DAUKO BISHMALU?
.
Toh Alhamdulillah dama tun kafin nafara na sanar daku cewa book 1 ne kadai akasa
.
Sai kun jini a sabon littafi
$ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
,
Tweets:- https://mobile.twitter.com/Shuraih_Usman?p=s

.
.

.νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

BABBAN GORO part 1C

BABBAN GORO
.
Littafina day (1)
.
Part 1C
With shuraih 99%
.
Typing :- http://facebook.com/shuraih.usman

.
Ashwar ya kwance wannan dattijo , sai ya hangi wasu dakarun sun bullo da kwari a hannayensu. Ashwa ya yunkura yai alkafira izuwa inda dokinsa yake , ya ciro mashinsa ya rike a hannu daya yana majajjawa da shi . Dattijo ya koma bayansa ya buya . Dakarun nan suka sako ruwan kibau , ashwar yai ta kadewa da mashin hannunsa , har kibiyoyin nasu suka kare , sai suka zare takubba suka yiwo kansa anan nefa ashwar yayi tunanin yazama wajibi yayi amfani da makami.
Don haka sai ya matsa jikin dokinsa ya dau takobin nan nasa zabbau , nan fa wuri ya yamutse, barade na kai masa sara da suka yana karewa , shi ma yana kai musu , sai da aka sami sa'a guda ana wannan fafatawa sannan ya karar da su.
.
Koda ya waiga bayansa sai yaga dattijannan akwance jini na zuba ta gefen cikinsa . Ashwar ya ruga gareshi ya sunkuya ya dauke shi . Faruwar hakan keda wuya ya hango wata bataliyar ta irin wadannan dakarun da yayi fada dasu , wadannan dakarun yawansu ya ninka na baya sau uku. Badan tsoro ba sai don ya ceci yaruwar wannan dattijon
Ashwar yayi sauri ya haye dokinsa rungume da dattijon yayi cikin jeji a sukwane , dakarun suka bi bayansa amma cikin kankanin lokaci ya basu rata mai yawa , har ya bace musu ,
Dole suka hakura suka koma da baya.
.
Yayin da ashwar ya fuskanci sun tsera wa wadannan makiya , sai ya tsaya a karkashin inuwar wata bishiyar , ya sauko da dattijon nan yayi masa shimfida ya kwanta , sannan ya dauko wani dogon rawani daga cikin jakarsa ta daure cikin dattijon don tsaida jinin dake zuba .
.
Ashwar ya dubi dattijon a yayin dayake kakarin mutuwa yace "yakai babana sanar dani inda zan kaika kusa ayi maka magani"
.
Dattijon ya yunkura cikin karfin hali tare da taimakon ashwar ya hada bayansa da jikin bishiya ya zauna , numfashinsa na fita sama-sama yace
"Yaro kada ka wahalar da kanka ,ni tawa ta kare , kasani daga nan zuwa garinmu tafiyar wata guda ce , nafito daga birnin Nurul islam ne , garine na ma'abota Addinin musulunci , abin dayasa kaga wadannan mutane sun kamani suna tayi mani azaba , saboda sun ga ina bautar ubangijin musulunci ne ina sallah"
.
Koda da jin wannan batu sai ahwar ya tuno da labarin da tsoho makabul ya bashi dangane da maganar boka akan daukakar da zai samu aduniya , nan take ashwar ya sake tallafe tsohon nan akirjinsa yace
"Tuni ina da labarin wannan Addini naka , kuma nayi imani dashi a zuciyata shigar dani cikinsa"
.
Dattijon yayi wani irin tari mai ban tsoro idanunsa suka kakkafe kamar ya mutu , amma sai numfashinsa ya sake dawowa yace a cikin karamar murya "yakai wannan saurayi ka saurari abin da zan fadi yanzu ka maimaita shi, idan kayi haka ka zama musulmi.
.
Nan take dattijon yai kalmar shahada , daa ashwar yakasa kunnensa da kyau dai dai dattijon na gama fadin kalmar ransa ya fita ,
Shi kuma ashwar sai ya maimaita kalmar shahada, sannan ya mike ya haka rami ya binne dattijon yasa alama a kabarinsa , sannan ya hau dokinsa da nufin tunkarar birnin Nurul islam
.
Kwanci tashi ashwar nata tafiya a cikin jeji kwana da kwanaki bai sake gamuwa da komai ba face namun jeji, wasu sai yayi kallon kallo da su , wasu kuma ya fafata da su ko su tsere da kansu don ganin wuya ko kuma ya hallaka su , shi kansa ashwar sai da ya dunga mamakin irin wannan baiwa daya keda ita ta sadukantaka da jarumta da kuma rashin tsoro, ya tuno da cewa tun baifi shekara goma sha ba , mahaifinsa ke tafiya da shi farauta jeji, da hanunsa ya sha kama 'ya'yan kura da damisa ya murde mudu wuya su mutu.
.
Tafiya dai taci gaba har ya sami kwana talatin cif , duk tsawon iyakar kwanakin nan ashwar yayi a lissafe suke a kwalkwalwarsa , kuma arubuce jikin kefen takobinsa , ba dan komai ba yayi haka ba , sai don kada ya wuce wa'adin da sarki abul dinar ya diba masa ba komawa gida , sau tari idan ashwar ya tuno da gimbiya mabaruka sai yayi ta yan wake wakensa ta soyayya shikadai cikin tsakiyar dokar daji,
In banda tsuntsaye da suke tayashi da sautin kukansu, ba ya samun mai tayashi debe kewa
.
Kwatsam ya hangi karamin gari a gabansa , kai tsaye ya tasamma garin har ya isa , da zuw a ya iske gaba dayan mutanen garin sanye suke cikin kamilar sutura mazansu da matansu, musamman ma matan ko'ina a jikinsu a rufe yake , kwayar idanunsu kacal ale gani Abin da ya fara riska shine wani gini wanda ya iske mutane a kofarsa suna ta shiga, wasu kuma sun tsuguna suna wanke gabban jikunsu da ruwa. Daga can kuma sai yaga wani daga cikinsu ya hau bisa wani tudu dake jikin wannan gini yana wasu maganganu masu kama da karatu, aciki karatun ne ya ji ya ambaci kalmar nan ta shiga musulunci wadda marigayi dattijo ya biya masa .
Koda jin haja sai farin ciki ya lullube Ashwar. Ya gane cewa wannan gari shine Nurul islam
.
Shuraih 99% nake ce daku
.
Ashwar ya sami wuri ya tsaya , ya sauka daga kan dokinsa ya tsaya cak yana kallon mutane suna kallonsa. Jim kadan sai yaga kowa ya shiga cikiN dakin nan, mutum daya ya wuce gaba saura suka tsaya bayansa aka fara wani aiki mai kama da bauta . Ashwar na tsaye yana lekensu da mamakin abun da sukeyi har dai suka kammala , suka firfito wannan mutum wanda ya shugabanci aikin bautar ya nufo inda ashwar ke tsaye
.
Balarabe ne fari , kuma dogo kyakkyawa, shekarunsa zasu kai hamsin da doriya, kamar yadda yake balar
Abe haka dukkanin sauran mutanen garin suke
.
Da zuwa ya kalli ashwar yace" yakai wannan bako daga ina kuma me ya kawoka birninmu"
.
Da ashwar yaji wannan tambaya acikin yaren daya sani ne wato larabci sai murna ta kama shi, nan take ya kwashe labarinsa tun daga farko har karshe ya zaiyana masa . Duk wannan abu dake faruwa sauran jama'ar gari na tsaitsaye a gefe suna kallo.
.
Ashwar na gama bada labari ,sai wannan mutumi ya rungumeshi yace "ai ka zama dan'uwanmu tunda ka shiga Addinin Musulunci, wannan daki daka gani mun shiga masallacine ne inda muke sallah, wannan dattijo daka gamu dashi a wancan gari na baya daga cikinmu yake, kuma yaje ne isar da sakon Allah ga wadannan makafirta , shi yasa suka tsareshi suka yi tayi masa azaba . Kashe shi da sukayi kuwa sun taima ka mashine, don yasamu shahada babban rabo a wajen ubangijin musulunci"
.
Balaraben ya kara da cewa "Ni sunana Imamu Hamid , ni ne shugaba a wannan gari yanzu tunda Allah ya kawo ka garemu sai ka zauna awannan gari don kasab yadda ake bautar Allah kuma ka fahimci Addini , tabbas ubangijin musulunci mai taimako ga bayinsa ne , wadanda suka dogara dashi , tabbas zaka nasara a bisa abin daka fito nema . Izan har baka kaucewa dokokin Allah ba"
.
.
Nan take Imamu Hamid ya rukke hannun ashwar ya tafi da shi izuwa gidansa. Gaba daya garin kuwa ya cika da labarin zuwan jarumi ashwar , da kuma ababan al'ajabin da ke tattare da shi
.
Ashar ya zauna a garin Nurul islam har tsawon sati uku inda ya koyi ibada har da karatun alkur'ani daya ke Allah yabasi kaifin basira cikin 'yan kwanakinnan ya samu ilmi mai yawa, kuma ya karbi littatafai na sauran fannonin ilimin Addinin kamar tauhidi da dae sauransu, ya kudurce a ransa zai ci gaba da neman ilmin addini a duk sa'add ya sadu da masana.
.
Ranar da ashwar ya cika kwana ashirin da uku a wannan gari na Nurul islam, a rannan yai sallama da su Imamu Hamid aka kawo guzuri mai kyau aka bashi , ya yi godiya sannan yai bankwana dasu , yatafi yana mai bakin cikin cikin rabuwa dasu, suma suna yi, sakamakon shakuwa da albarkar HASKEN MUSULUNCI(next book insha Allah)
.
LoKacin da ashwar yayi dan nisa da gari , sai rubuta adadin kwanakin da yayi ajikin kufe na takobinsa, ya lissafa dana baya sai yaga a halin yanzu ya cimma wata uku saura kadan, ya zamana kenan baifi saura wata guda da 'yan kwanaki ba wa'adin da aka dibar masa ya cika , wannan yasa hankalinsa yayi mummunan tashi , domin ko abirnin inda Nurul islam bai samu wanda ya taba jin labarin inda birnin duma yake ba.
.
"Yanzu yaushe nasan inda wannan gari yake har naje na dauko bishmalu ,sannan na koma garinmu duk a cikin wadannan kwanaki?"
.
Tambaya ce wadda ashwar yayi wa a zuciyarsa , kuma shi kansa baisan amsarta ba .
.
Bayan kamar rabin sa'a yana tafiya , sai hadari ya hado , nan take ruwa ya kece kamar da bakin kwarya ,dan haka sai ashwar ya ruga karkashin wani dutse ya fake , ya daure dokinsa a jikin kafarsa sannan ya kishingida , cikin yan dakiku kadan bacci ya saceshi.
.
Yana cikin wannan baccine dokinsa yayi haniniya yaja kafarsa , ashwar ya tashi ya duba bai ga komai ba ,
Kawai sai ya koma baccinsa. Dokin ya kara haniniya a karo na biyu . Ashwar ya farka a fusace ya mike ya dada dubawa ko'ina bai ga komai ba , sai yayi tsammanin dokin nasane yake bukatar yayi kiwo, don haka sai ya kwance shi ya koma baccinsa .yin hakan keda wuya , kawai sai yaji saukar wani abu ajikinsa , yana bude ido yaga raga ta rufe shi, wasu dakaru kimanin su arba'in na ruke da ragar da makamai sun kewaye shi
.
"Tashi mu tafi " daya daga cikin baraden ya fadi.
.
Kada ku manta kuna tare ne da shuraih 99%
.
Ashwar ya dubeshi ya dubi sauran, ya tabbatar babu imani a fuskokinsu, da farko yayi niyyar ya ganar dasu kuransu, amma sai yace a ransa
.
"Bari dai naga gudun ruwarsu"
.
Batare da gardama ba ya bisu izuwa wani gida aka sa shi cikin wani daki aka kulle har magariba ta kawo jiki.
Wannan tsarewa da aka masa batazo masa da illa ba sai dai rashin sallah da kuma dokinsa da yake tunanin ya bace a jeji, gashi duk makamansa na fada na jikin dokin .
Ashwar yadaga hannunsa sama ya roki Allah yasa wannan tsarewa ta zame masa alheri
.
Washe gari wannan tawaga data kamo ashwar suka taru acikin gidan , gaban ubangidansu, inda dayansu da ke bayanin cewa basu samo koda tsuntsu ba sai wani yaro da suka samo yana ajiye a cikin daki.
.
"To yaushe zaku cinyeshi? Ko kuwa kun fison ku gama da tsofaffin da ku ka kamo tukunna"
.
Gaba daya sukace ai sunfi son yaron, saidai yayi musu kadan, dan wani ma bazai samu koda rabon kunne daya ba , nan take ubangidan wadannan mutane yayi musu sulhu, akan a fito da naman gaba daya a cinye don kar ayi fada.
Wannan zance gabadaya a kunnen ashwar akayi shi.
Don haka sai ya cika da mamaki daya ji ana maganar a cinye dan adam kamar yadda ake cin naman dabba.
.
"Ni kuwa naga ta yadda za a cinyeni ina ji ina gani"ashwar ya fadi cikin zuciyarsa.
.
Dankari makari,lallai yau akeyinta inji 99% ke magana'
.
Jim kadan aka bude dakin da ashwar ke ciki, abinci ne aka kawo, wani gajeren mutum ne kato ya shigo da shi cikin wata karamar tasa ko sallama babu ya ajiye , ya juya ya fita aka garkame kofa, ashwar ya dubi abincin na yaga bai san irin saba gashi yana jin yunwa amma sai yafara wasi wasi ko yaci ko ya bari.
Tabbas yasan dae mutanenan kafiraine baisan ma koda me sukayi abincin ba. Kawai sai ya yanke shawarar yayi baccinsa na jiya da baikarisa ba , nan take ya bingire yai ta sharara barci kamar wadda yake cikin gidansa
.
Kwatsam yaji wata murya a sama ance " tashi mu tafi"
.
Yana bude idanunsa yaga wasu kartine suk uku.
Ashwar ya tashi bako musu suka sa shi agaba sai wajen babbansu , wani katone mai tumbi, ya saki ciki sai kace garwa. Cikin tsawa ya dubi kattin yace
.
"Ku ajiye shi anan ! Ku fito da tsofaffin"
.
Ashwar ya zauna yana kallon ikon Allah sai yaga an fito da mutane sun fi dari, nan dai yaga anjera su gaba daya alayi kamar masu shirin tada sahun sallah,
Hardashi ahwar din
Mai katon cikinnan ya tashi da kyar ya fara zagaya su ashwar, bai dafa kowa ba sai wani tsoho wanda ko kyaleshi akayi ya kalli kisan da za'aiwa sauran zai iya mutuwa don tsananin firgita , don ko ayanzu ma baisan cewa yana fitsari a wando ba , jikinsa na kyarma tamkar mai mugun zazzabi , nan take karti suka kama wannan tsoho suka jefa shi cikin wata katuwar tukunya wadda ke karkashin wata murhun wuta na dafuwa, ruwan ya cikinta sai zabalbala yake ,
Ai kamar hadiyar kwayar gero haka tsohonnan ya lume cikin tukunyar , ko tarinsa ba'a jiyo ba.
Wasu karti su biyu da suke rike da ludayin tukunyar suka hada hannayensu hudu suka tura ludayin zuwa karkashin tukunyar suka tsamo.
Sai ga gangar jikin tsohonnan ta motse kamar curin nakiya, gaba daya fatar jikinsa ta sutale duka akansa kuwa babu silin gashi koda daya , atakaice dai ya dahu yai lugub . Ja daya za aiwa tsokar namansa ta rabu da uwar jiki.
.
Koda ganin wannan al'amari sai ashwar yai salati yace" Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
.
Kafin a ankara ya suri kato guda ya mai dashi bulala , yai ta dukan sauran kattin , nan da nan gida ya rikice da ihu da kuwwa , katon nan da ke zaune a kujera kamar kula sai kujerar ta karye ya fado ji kake tim! Bama kafiran azzaluman mutanen ba wadanda ma aka kamo don acinye saida suka gigice.
Tsoffin cikinsu suka shiga wani hali don wasunsu ma sun fado sun ture abincin . Azzaliman kuwa duk sun firgice sun dimauce , wasu su kayi waje da gudu wasu suka yiyo kan ashwar wato masu karfin halin kenan , shi kuwa yaci gabada da rugurguzarsu suna zubewa kamar mai kada karmami. Musulman da aka kamo suka hau salati.
.
Bayan da ashwar ya sumar dana sumarwa ya kashe na kashewa , masu gudu kuwa suka tsere ya rage saura shugaban masu cin naman mutanen nan kadai, kwance akas ya kasa tashi bare ya gudu, sai nishi yake da kyar , nan take ashwar ya kaimasa wawura ya sunkuce shi sama duk girmansa ya zama na banza , don tamkar ashwar ya daga buhun audiga ne, tsundum ya jefashi cikin wannan tukunya mai zabalbala , jama'a gaba daya suka rugo wajen ashwar suna yi masa godiya da sa albarja ashwar ya fice ya bar su suna ta murna da wake-wake .
Wani abin mamaki yana fitowa daga cikin gidan sai ya iske dokinsa tsaye kamar dama yasan da fitowarsa yanzu,
Ashwar ya kalli dokin yayi murmushi sannan yace
"Daga yau nasa maka suna ganjarma"
,
Kai masu karatu nafara gajiya fa 99% ke magana
,
Ashwar yayi tsalle ya haye kan ganjarma , ya sukwane shi zuwa cikin jeji.
Wannan shine abin daya faru ga jarumi ashwar, bayan ya baro garin Nurul islam
.
.
Naga kamar bakwason littafinnan
Anya kuna son inci gaba kuwa
.
.
Littafin abdulaziz sani/m gini(kings of adventure stories)
.
Typing:- Shuraih Usman
Tel' 08133209890
.
.
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

BABBAN GORO part 1B


BABBAR GORO

.
Littafina daya (1)

Part 1B

.
With shuraih 99%
Typing by :- http://facebook.com/shuraih.usman

.
Sarki abul dinar ya mike tsaye da kansa ya daka tsawa , nan take akayi tsit.
.
Sarki ya dubi ashwar cikin murmushi yace" ya kai ashwar kaji jarabawar dake gabanka shin zaka iya ?"
.
Gaba daya idanun jama'a suka zubo kan ashwar.
Ashwar yayi shiru yana kallon jama'a har idanunsa suka kai kan gimbiya, inda ta mike zumbur tana mai kokarin tace ya amsa, amma sai ya da kansa ya dubi tsho makabul, nan take makabul yayi masa inkiya ya amsa.
.
"Ran sarki ya dade na amince da wannan jarabawa , kuma nayi alkawarin zan zo da bishmalu dan sarkin misra cikin wannan fada taka"
.
Cikin tsananin farin ciki ta daka tsalle sama sannan ta rugo da gudu ta rungume ashwar agaban jama'a , nan take fada ta sake rudewa da hayaniya ,
Sarki da 'yan majalisarsa suka mike suka shiga cikin gidan sarauta ,
Ita kuma gimbiya sai ta tafi da ashwar izuwa gidanta .
Surutai iri iri daga bakin jama'ar gari suka yawaita. Wasu suce hakika ashwar mahaukacine, wasu kuwa suce yarinta ce ta dibeshi yayi wauta, wasu ma har zuwa sukai suna yiwa tsoho makabul ta'aziya suna cewa"dan ka ya zama gawa"
.
Shi kuma sai dai yayi murmushi kawai agaresu su tafi suna gulmarsa.
.
Farin ciki wajen gimbiya mabaruka a wannan rana yafi karfin misaltuwa .
Nan take tasa aka shiryawa ashwar walima ta musamman , inda kuyanginta suka shiga hidimar girke girke .
.
Cikin kankanin lokaci aka samar da abinci iri iri da ababan sha kala kala .wannan walima an yi tane awani daki ta musamman cikin gidan gimbiya mabaruka ,
Kuma ba'a gaiyaci kowa ba face ashwar shi kadai, sai kuma abar begensa wato gimbiya , ma'ana su biyu kadai.
Suka zauna karkashin wani dogon tebur mai dauke da kujeru hamsin, akan wannan tebur aka shirya dukkanin wannan abincin da ababan sha bisa farantai , akan kowane faranti akwai kuyanga tsaye rike da cokali , da zarar gimbiya ta bukaci abincin sai kuyangar ta garzayo ta kawo, ta zuba a cikin wani babban faranti dake gabansu ita da ashwar anan fa mabaruka ta nuna tsantsar soyayyarta ga ashwar domin da hannunta ta dunga bashi abincin yana ci , ganin haka shima sai ya dunga ciyar da ita da hannunsa, har suka ci suka koshi.
.
Nan take mabaruka ta kama hannun ashwar ta kaishi cikin falonta inda take saukar manyan baki suka zauna. Dayake ashwar bai sa ba da ko'ina ba in ba gidan gona ba ,sai ya zama dan kauye yayi ta kalle kalle a cikin falon
.
Mabaruka ta bushe da dariya tace"haba masoyina ya zaka dunga kalle-kalle kamar wanda ya fito daga kauye.
.
Wannan batu yasa ashwar yayi murmushi yace "ranki ya dade dolene ki ga kauyanci a tare dani domin tunda aka haifeni a cikin gidan gona na ke rayuwata , ban taba shigowa cikin gari ba sai ranar dana hadu da ke , hatta sa'adda aka kaini dakin tuhuma hankalina ya gushe ban taba shiga wajen ba sai a ranar. Hakika kece sanadin shigowata cikin Al,umma , tun tasowata ban san komai ba face bauta da biyayya ga sarki abin dana ga iyayena nayi , ban san sanya sutura mai kyau ba irin wadda nake gani yanzu ajikin su, bansan kwanciya ba akan shimfida sai ciyawa da harawar doki.tabbas kin sauya komai na rayuwata bazan taba mancewa dake ba "
.
Yayin da ashwar yazo nan a zancensa sai ya ga idanun gimbiya mabaruka ya ciko da kwalla , nan da nan hawaye ya fara zuba bisa kuma tunta .
Wannan yasa hankalin ashwar ya tashi, yadan matsa kusa da ita ya durkusa bisa guiwowinsa cikin kaskantar da kai yace
.$
"Ya shugabata ki yimin gafara idan na saba miki a cikin maganganun dana fadamiki"
.
Bisa mamaki sai yaga fuskarta ta fadada da murmushi , sannan ta rike kafafunsa suka mike tsaye tare, ta dubeshi da kyau tace
.
"Ya masoyina na rantse da wata ko kadan baka bata mini rai ba, kawai na tausayawa rayuwarka ne . Hakika sai yanzu na tabbatar da cewa mahaifina yana mulkin zalunci, domin an tauye hakkinka dana iyyenka , A matsayinku na bil'adama da ba dabbobiba, bai kamata ace baku da sutura ba face walki, tabbas inda nasan cewa akwai irinku a garinnan da tuni na kai muku "
.
Shuraih ke magana
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yaji duk tsigar jikinsa ta tashi, jikinsa yayi sanyi, ya kura mata idanu kuma ya kasa cewa komai . Mabaruka na ganin sauyin........
.
Kash kuyi hakuri makaranta fallen littafin ya lalace akalla dai fallen daya lalace yakai goma sha daya. Amma zanyi kokari na dan bayyana muku abubuwan fallen ke kunshe da shi cikin gaggawa
.
Shuraih kemagana
Boka gulmanu yazo ya samu sarki abul dinar ya sanar dashi cewa" lallai wannan yaro kar ya wuce kwana uku bai yi wannan tafiya ba kuma a sanar dashi cikin wata uku kacal akeson ya dawo tare da bishmalu"
.
Sarki abul dinar ya dubeshi cikin mamaki yace " yakai sarkin matsafa shin meyesa kace haka "
.
"Aljanina ne ya sanar dani haka kuma ya tabbatar min muddin bai bar garinnan cikin kwana uku ba toh tabbas zaiyi nasarar shiga birnin duma kuma ya dauko bishmalu"
.
Sarki abul dinar najin haka yai umarni ga wani bardensa. Dayaje ya sanar da jarumi ashwar cewa cikin ya tabbata cikin kwana uku ya fita daga garinnan ya nufi birnin duma , sannan wata uku gareshi muddin wata uku ta gota koda da kwana dayace to ko yazo da bishmalu wannan gari to tabbas ya fadi
.
Wannan shine abin daya afku a fadar sarki abul dinar
.
Shidai mahaifin bishmalu wato sarkin Misra ya auri wata kyakkywar mata , ita wannan matar duk wanda ya aureta mutuwa yake sakamakon sarkin aljanu kifyan dayake matukar sonta koda sarkin misra ya aureta sai aka ringa tsorota da shi ana mai kashedin ya rabu da ita ,
Wata rana ya fita farauta shida baradensa suna cikin jeji sai sukaji wata murya ta barke da dariya sannan akace da su "ya kai wannan sarki mai taurin kai lallai ka rabu da wannan mata taka don ita mata ta ce ni kadai"
.
Sarkin misra na jin wannan batu yace karyarka tasha karya baka isa karabani da mata ta ba ......
.
Wata sarka yagani ta shake wuyansa nan take ya ringa makyarkyata .
Can sai yafadi wata kalma sai wannan sarka ta tsinke ,
,
Baraden suka juya tare da sarkin misra suka dawo cikin gari
.
Toh fa tun daga wannan rana ne wani ciwon kai mai tsanani ya addabi sarkin misra.
Wannan ciwo ta hana shi sakat domin idan ta tashi mai tamkar zai mutu haka yake .
.
Koda matarsa taga wannan ciwo taki ci taki karewa sai ta tafi wajen boka ta sanar dashi wannan ciwon na sarki take bokan ya bata wata laya yace ta dauara layan awuyan sarki.
.
Tazo ta daura layan , aiko tana daurawa sarki ya ji shi garau tamkar wata ciwon kai bata taba samun saba a duniya.
.
Ana nan ana nan rannan sai matar sarkin misra ta samu ciki ,
Sarkin misra yai murna kwarai , bayan cikin ya cika wata tara sai ta haife santalelen yaro wanda tsabar kyaunsa ma ana zaton aljani ne
.
Sarkin misra yayi murna kwarai amma mai hade da bakinciki sakamakon mutuwar matarsa yayin haihuwa ,
.
Aka saka ma yaron suna bishmalu ,
Wata rana da daddare sarkin misra yai mafarki da wani garjejen aljani yana rike da dansa yace mai" tun da ka kashe mata ta toh na dauki danka daga yau yazma dana baza ka sake yin arba da shiba.
Har ka mutu
.
Washe gari sarkin misra ya farka baiga bishmalu ba yai neman duniya amma bai ganshi ba daga bisani yaje wajen boka toh ananne boka ya tabbatar mai da cewa dansa yana nan a raye wani hatsabibin sarkin aljanu ne ya sace shi ya kaishi birnin duma sunan wannan aljani kifyan
.
Sarkin misra ya tura sadaukai , jarumai da dama amma duka ba labarinsu
.
Daga karshe ya hakura ya sadakar
Amma sabi da bakin ciki kullum cikin kuka yake yanzu haka yana fama da wata irin cuta , wannan cuta anyi magani anyi magani amma ina taki warkewa ,
Amma bokansa ya fadami duk randa yai arba da dansa bishmalu toh zai warke daga wannan cuta .
.
Wannan shine takaitaccen tarihin bishmalu daga bakin shuraih 99%
.
.
Koda ashwar ya sami sanarwar sarki abul dinar kan cewa ya gaggauta barin garin kafin kwana uku
.
Sai yayi shiri
Tsoho makabul ya iso gareshio dauke da wasu makamai , mashine da takobi sai kuma kibiya
.
Tsoho makabul ya mika mai yace " amshi wayannan makamai kasani wannan bokan daya fadamana cewa zakayi gagarumar shahara a duniya shine ya bamu wayannan makamai yace duk sa'adda ka girma in damka ta a hannunka.to yanzu lokaci yayi "
.
Ashwar ya amsa yana mai godiya ga tsoho makabul
Zuwa asuba ashwar yagama shirin shi sannan yarubuta wasika ya bawa tsoho makabul kan cewa in gimbiya mabaruka tazo ya bata sannan ya sanar da ita shi yatafi .
.
.
Bayan fitarsa daga birnin sarwaliya ya yanki daji yaci gaba da tafiya
Sudai wayannan makamai da tsoho makabul ya bashi sihirtattun makamaine
1.acikin makaman akwai wata mashi wadda duk abin da aka soka da ita to fa saide wani bashiba ita wannan bashi har dutse fasashi take ta tarwatsa shi sannan ta wuce
2sai wata kwari da baka wanda shi wannan kwarin I zan har ka harbata toh zataje ta cake duk wadda kake bukata ta cakeshi sannan ta dawo cikin gwafanta itama wannan kwari tana huda dutse sannan ta tarwatsa shi
.
(Har yanzu dai ni shuraih hakuri nake baku sakamakon lallacewar sauran fejin kuma ni kaina nasan bazan baku labarinnan yadda take ba amma zan dan kokarta)
.
3sannan kuma akwai wata sihirtacciyar takobi wadda take da kaifin tsiya koda bishiya aka sara da wannan takobi toh anan take zai bushe sannan ganyayyen bisansa su bushe yafadi kasa.
Shi wannan takobi idan dare yai sai kaga yayi haske inda zai haskaka ma marikinshi hanya
.
.
Wata rana ashwar ya kwanta yana barci saiyayi mafarki a cikin mafarkin nasane aka sanar da shi cewa akwai wata gari agabansa izan ya shiga garin kada yaci komai ko ruwa ne kada ya yadda yasha
,
Koda ya farka daga barcin ne sai yaga mai ai safiya tayi sannan rana ma ta fito .
Tafiya kadan yayi sai ya hangi wani gari agabansa batare da shakkar komai ba ta dumfari wannan garin yana shiga cikin wannan gari sai yaga wani tsoho yana noma koda tsohon ya gansa sai ya kariso gabashi suka gaisa bayan sun gaisa ne tsohon ya dauko wasu dabino ya mika ma aswar.
.
Har ya kai hannu zai karba sai kawai ya tuna da mafarkin da yayi jiya da daddare .
Sai yafasa amasar wannan dabino.
Tsohonnan yayi yayi da ashwar ya ci dabinon amma ashwar yaki sai wannan tsohon ya tashi mai haikan yana so ya kasheshi koda ashwar yaga haka sai ya zaro takobinsa ya fille kan wannan tsohon sannan ya ci gaba da tafiyarsa izuwa cikin garin
.
Shidai wannan gari sarkinsu ya kasance mugune kuma azzalumi , yana bautar wani dodone kuma wannan dodo kullum sai an yakama sa bil'adama yasha jininsa , kullum barade sukan fita zuwa farautar mutane, sukuma mutanen garin yayin da baki suka shigo gari sai su yan yamesu da abubuwan makulashe wanda aka zuba amaganin bacci aciki kana ci shikenan naka yaja
.
Yayin da dakarun sarki masu farautar mutane suka fita farauta izan har basu sami mutum ba sai sudawo izuwa birnin su a cikin mutanen gari sai ayi kuri'a duk wadda tafada kansa toh shine za'a yanka wa dodon da sarkin ke bautawa ya shi jininsa.
.
.
Ashwar na zuwa kasuwar wannan gari sai jama'a suka yanyameshi dakayan ciye ciye shikuma duka ya basar yace musu bayaci
Koda sukaga alamar cewa ashwar bazaici kayan ciye ciyen ba sai suka hasala suka haiko masa da nufin su kamashi
Koda ashwar yaga haka ai saiya ciro takobinsa yaringi saransu yayin dasuka ga ashwar yayi musu muguwar barna sai suka rabu dashi
.
Can sai gawasu dakaru nan sun kama wani mutumi ma'abocin fararen kaya sun yiwa wannan mutumi jina jina suna tafaman jansa akasa
.
Koda suka kariso gaban sadauki ashwar sai shugabansu yace dashi kai wa ne ne kai da harzaka shigo cikin birninmu sannan kayi mana irin wannan ta'adi
.
Ashwar yace dashi ni bakone
.
Shugabar wannan dakaru ya zaburo domin yakama ashwar aisai aswar yai wa shugabar dakarun karo afuska,
Sai gashi ya baje akas ko shurawa baiyiba da jama'a suka suka ga haka sai gudu, sauran dakarun da suke tsaye suka ce da wa Allah ya hadasu in ba ashwar ba? Ashwar baiyi tunanin amfani da makami ba a wannan fada, don haka hannu da kafarsa ne makamansa cikin kankanin lokaciya tarwatsasu.
.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kuyi hakuri in kunji nayi kuskure ku gyara min
.
Muhadu a part 1C
,
Littafin Amdulaziz sani/m gini(kings of adventure stories)
.
Domin sada zumunci mu hadu a page dina na face book. Shuraih 99%
.

ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч Shuraih usman

BABBAN GORO part 1A


BABBAN GORO
-------------------------
Littafina daya
.
Part 1A
.
With shuraih 99%
Typing by :- Shuraih Usman

.
Zaku sha karatu har ku gaji
.in naga bakwa respond toh zan ajiye littafina agefe
.
.
Awani zamani can baya anyi wani attajirin sarki wai shi abul dinar ,wanda matsafa da masu harsashe suka tabbatarda cewa babu attajiri kamarsa a duniya ,saboda tarin dukiyar da Allah yabashi wannan sarki yana da matan aure guda goma sha shida kuma yana da kuyangai tamanin gabaday wayannan mata nasa babu wadda ta raba haihuwa sai guda daya ,
Wata mace da ake kira hauziya
Duk acikin matan abul dinar hauziyace yar talakawa ,domin duk sauran daga yayan sarakuna sai yayan mayan attajirai na duniya
.
A ranar da aka fuskanci hauziya ta sami ciki ,sai sauran kishiyoyinta suka cika da bakin ciki .
Batare da da bata lokaci ba suka shiga bin hanyoyin da zasu tabbatar da cewa cikin ya zube ,masu tsafi nayi ,masu surkulle nayi, kai wasu ma kiri kiri a fili sukka ringa yin abubuwan da zasu sa cikin ya zube amma ubangijin musulunci shine mai yin yadda yaso ,sai ya kare hauziya daga sharrin kishiyoyinta .
Shikuwa sarki abul dinar koda yaji cewar hauziya ta sami ciki , sai yadauki son duniya ya kwallafa a akanta . Domin zata share masa hawaye a bisa bakin cikin daya addabi rayuwarsa ta duniya ,wato rashin magaji ,
Dayake ya tabbatar da cewa sauran kishiyoyinta bazasu kyaleta ba, sai ya dauketa ya kaita wani gidansa dake bayan gari .
Ya ajiyeta ita kadai ,
Daga ita sai bayi masu yi mata hidima .
Gidan ya zama ba'ashiga da fita ,in ba shi kansa ba .sarki abul dinar ya tare wajen hauziya , tare suke ta rainon cikin har wata takwas .
A ranar da cikin ya cika wata takwas da kwana shirin da biyar .
Ciwon nakuda ya kama hauziya .
Cikin yan dakiku kadan ta haifi sankaceciyar 'ya,
Wadda atun tana jinjiniyar aka tsorata daganin kyawunta.
.
Sannu sannu akayi ta rainon yarinyar wadda aka sawa suna Mabaruka ,har ta girma .
Ta zama cikakkiyar budurwa ,
Wadda saboda tsananin kyau labarinta ya cika duniya . Jarumai da matsafa da dama sun hallaka junansu a kan soyayyarta
.
.
Wata rana gimbiya Mubaruka ta fita rangadi , don shakatawa cikin wata babbar gona ta mahaifinta ,kuyangi da barade na take mata baya.
.
Kwatsam sai ga wata katuwar macijiya mai girman gaske , ta bayyana a gabansu .
.
Koda ganinta sai barade da kuyangi suka kwalla ihu, suka ruga baya da gudu ,
.
Baraden nan suka yi ta rige rigen gudu ,sun mance da aikinsu na tsare lafiyar 'yar sarki .
Ita kuwa mabaruka sai ta tsaya kyam ta kasa gudu , don tsananin razana , hawayen bankwana da duniya suka tsiyayo daga idanuwanta .
.
Katuwar macijiyar ta wangame baki zata hadiyeta , kawai sai mabaruka taga wani bakin bawa yai tsalle ya rungumi wuyan macijiyar
.
Nan fa suka kama kokawa shi da macijiyar su fadi can su tashi can.(Ni kaina shuraih sai dana kusan....basai na karisa ba)
.
Shi yana kokarin ya turmusheta ya rarumi wani icce dake waje guda ya soketa ita kuma tana kokarin kannannadeshi ta karairaya kasusuwan jikinsa . Haka dai suka yi ta dauki ba dadi har tsawon rabin sa'a , macijiyar nan tai masa fata-fata , duk jikinsa ya rune da jinin raunuka
Amma hakan bata sa ya saketa ba ,
A hakan dai Allah ya bashi iko , hannunsa ya kai kan wannan icen cikin zafin nama ya dauki icen ya caka abakin macijiyar , ya bullo ta tsakiyar kanta .
.
Nan take macijiyar ta sulale ta fadi kasa matacciya,
Shi kuma bawan yafadi kasa a sume .
.
Koda ganin haka sai gimbiya mabaruka ta ruga gareshi ta rungumeshi tana kuka ,
Gaba daya jikinta ya baci da jininsa .
Ahaka sarki abul dinar da dakarunsa suka zo suka sameta .
.
Nan da nan aka ban bareta daga jikin bakin bawan , aka tafi da ita shi kuma aka yayyafa masa ruwa ya farfado daya ke shi bawa ne marar gata ,
Sai aka tuhumeshi da laifin rungumar 'yar sarki ,
Ba'ama duba sai da ran dayayi ba, dan ceton 'yar sarkin.
.
Saboda haka aka kaishi dakin tuhuma ,aka dauddaureshi da sarkoki aka yita gana masa azaba iri iri.
.
A iya tunanin Mabaruka wannan bawa ya mutu wannan dalili shi yasa tai ta kuka har hankalinta ya gushe ta suma bayan ta farfado ta mike zaune daga kan gadon data ke kwance ,
Inda tai arba da mahaifiyarta hauziya zaune a gefen gadon idanunta cike da hwaye .
Koda ganin mikewar mabaruka sai farin ciki ya kama hauziya.
.
"Mama ina gawar bawan daya ceci rayuwata?"
Mabaruka ta tambaya fuskarta cike da alamun bege
.
"Waya ce miki ya mutu? Ai dogon suma yayi kum, kuma anzuba masa ruwa ya farfado ,yanzu haka yana can daure a dakin tuhuma"
.
"Me yayi za'a kaishi dakin tuhuma?"
.
Batare da mabaruka ta saurari karin bayani ba ta mike tayi waje da gudu ,
Mahaifiyarta tana kira amma taki dawowa , bata tsaya ako ina ba sai a kofar dakin tuhuma,
Da zuwa ta dakawa masu gadin tsawa tace "su bude mata kofa kofar "
.
Jikinsu na rawa suka bude kofar ta shiga , inda ta iske shi kwance magashiyyan cikin jini .
Nan take tasa aka kwance sarkar dake jikinsa , tasa aka kaisa gidanta inda taimasa wanka ta sama magani a raunukan jikinsa sannan tasa aka kawo masa abincin sarauta , ya cika tumbinsa ! Daga nan aka kaishi wani dakin hutu ya kwanta yai barci, har sai da rana ta fadi sannan ta shiga dakin ta tashe shi , duk su biyun suka kurawa juna ido
.
"Yakai wannan jarumi menene sunanka"
.
Bawa yayi murmushi yace "ni sunana Ashwar "
.
"Ya akai kana matsayin bawa a gidanmu na sarauta amma ban taba ganin kaba ?"
.
Ashwar yasake yin murmushi yace "yake gimbiya kisani babu yadda za'a yi ki taba ganina , domin tun da aka haifeni ban taba fitowa ba daga cikin lambun sarki na can bayan gari sai ayau .
Mahaifina shine bawan dake kula da wancan lambu na sarki , tun yana saurayi yake wannan bauta harya tsufa ya mutu , nikuma na gajeshi
Mahaifiyata ma acikin wannan lambu ta rasu yanzu haka kabarinta na cikin lambun
A yaune sarki ya aika mini naje daya lambun nasa nayi aiki wanda shine kika ziyarta don rangadi
To ina cikin aikine na hango shigowarku keda kuyangi da barade .
Kuma sai naga wannan katuwar micijiya ta tarwatsa kuyanginki da baraden
Duk sun gudu sun barki shi yasa na sai da raina don ceto rayuwarki".(Ni 99% nace lallai kacika sadauki)
.
.
Koda jin haka mabaruka tai ajiyar zuciya hawayen tausayi kauna suka zubo mata tace "ya kai Ashwar kasani daga yau bawani namiji da zan aura in ba kaiba
.
Cikin razana Ashwar yaja da baya ya takure jikinsa ga bango yace" ranki ya dade ki rufa min asiri , ki tuna fa ni bawane , bawan ma bakin fata ,ke kuwa gaki balarabiya 'yar sarki,ina ni ina aurenki"
.$
Mabaruka tayi murmushi tace "ai babu ruwan so da matsayin jinsi ko launi ,idan duk duniya zata taru banga wanda ya isa ya raba ni dakai ba , abu daya nake so na ji daga bakinka kawai , kana sona ko baka sona?"
.
"Haba gimbiya ai babu wani namiji da zai ganki yace baya so , amma ai wutsiyar rakumi tai nesa da kasa kuma BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE"
.
"Kwarai kuwa"wata murya ta amsa daga bayan su.
.
Mabaruka da ashwar suka dubi bakin kofa a tsorace , sukayi arba da sarki Abul dinar fuskarsa a murtuke wasu kartin barade shida na tsatsaye a bayansa suna muzurai tamakar saci babu.
.
Cikin fushi ya dubi mabaruka yace "haba gimbiya shin kin mance da martabar gidannanne ?kin manta da matsayinki na 'yar sarki ne?har zaki wulakanta kanki ki dauko bakin bawa ki shigo dashi har cikin gidanki mai Albarka.
.
Maimakon mabaruka ta nutsu kota firgita da wannan tambaya sai ta kyalkyale da dariya sannan tace "haba Abba ka runa fa mahaifiyata ta fito daga dangin talakawa ,me yasa ka aurota har kuka haifeni? Shin baka tsammanin zubar martabar sarautarka ne? Hakika sone yasa idanunka suka rufe , tunaninka ya gushe ka manta da matsayinta......"
.
Cikin hanzari abul dinar ya tari numfashin mabaruka yace" yata kada ki yi la'akari da wannan , domin inki kai tunani akwai alaka ta jinsi da jini tsakanina da mahaifiyarki amma tsakaninki da wannan bakin bawan babu alakar komai"
.
"Abba ni dai Ashwar nakeso"
(Shuraih 99% ke magana)
.
Wannan bayani ba karamin girgiza Abul dinar yayi ba , don tsabar takaici sai da yaji kwalla ta zo masa amma sai ya juya baya yayi shiru yana tunani , daga can ya juyo ya dubi mabaruka yace" na amince da niyyarki amma bisa sharadi "
.
Cikin mamaki mabaruka tace "wane irin sharadi ne?"
.
"Zakiji sharadin gobe da a fada gaban dukkanin jama'a.
.
Nan take sarki ya juya ya fice daga dakin ,barade suka take masa baya.
.
Ashwar da mabaruka suka dubi juna cikin tsananin damuwa
.
"Ai daman na san wannan al'amari bazai taba yiwuba , nagaya miki cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE"
.
Mabaruka tayi murmushi tace "ashwar ina so ka kalli cikin kwayar idanuna kaga ya mini abinda ka gani aciki "
.
Ashwar ya kura mata ido har tsawon 'yan dakiku kadan sannan ya kawar da kai
"Me kagani acikin idanuna?"
"Banga komai ba face digon baki da zagayen fari"
.
"To wannan zagayen farin daka gani ba komai bane face fadar zuciyata , wannan digon bakin kuwa daka gani guda daya tilo ba komai bane face kai Ashwar Kai kadai nake so bazan so wani ba yan kai ,idan kuwa aka aura mini wani ba kai ba saidai ya zauna da gawata"
.
Haka dai Ashwar da mabaruka sukaci gaba mahawara yana ta kokarin nuna mata matsala har zuwa gabannin magariba ,sannan ya tafi gidan gona ita kuma taci gaba da tunanin hanyar dazata bi ta shawo kan al'amarin .
Wannan shine abin daya faru tsakanin jarumi ashwar da gimbiya mabaruka .
.
Shuraih ke magana
.
Al'amarin sarki abul dinar kuwa lokacin daya bar gidan 'yarsa mabaruka sai hankalinsa ya dada dugunzuma ya rasa abinda yake masa dadi aduniya , har ya isa turakarsa yana cikin wannan hali , ya kasa zauni ko tsaye sai da dukkanin barorinsa da fadawansa suka fahinci lallai akwai abin da yake damunsa .
Bayan yayi dogon tunani sai ya tura aka kirawo masa yan majalisarsa cikin turakarsa daga cikin yan majalisarsa sarki Abul dinar akwai waziri, galadima ,wambai da Gulmanu sarkin matsafa na garin.
.
Bayan dukkaninsu sun zauna , sai sarki Abul dinar ya basu labarin abinda ke faruwa tsakanin 'yarsa mabaruka da kuma jarumi Ashwar, sannan yace
"Kunsani cewa abin kunya ne ace 'yarmu ta auri bakin bawa ,tabbas idan akai martabar masarautarmu ta zube , sauran kasashe ma dake makwataka damu sai sunzage mu sun raina mu ku sani idan muka sanar da mabaruja kuru-kuru cewa ba zamu amince ta auri ashwar ba , tabbas zata iya hallaka kanta, nidai nace da ita zan bata shi amma bisa sharadi ,sharadin kuma nace sai gobe da safe zan tara jama'ar gari na fadi a gabansu .
.
Toh ku sani sharadin nan fa ni kaina ban san shi ba , wannan shine dalilin dayasa na tara ku anan, inaso muyi tunani mai zurfi mu kafawa ashwar sharadin nemo wani abu mai tsananin wuyar samu a duniyar nan, wanda a sakamakon neman sa ma zai hallaka in yaso kun ga dole mabaruka ta rungumi kaddara"
.
Yayin da 'yan majalisa suka ji wannan bayani na sarki abul dinar sai duk suakayi shiru suka shiga tunani aka rasa wanda zaice kala , har ya zuwa wani lokaci daga can sai gulmanu sarkin matsafa ya mike yace
.
"Ya sarkin sarajkai hakika ni ina da mafita akan wannan al'amari kuma na rantse da wata sharadin da zan dora Ashwar akai bai is ya haye shi ba ina so ku yi hakurin jin wannan sharadi har zuwa gobe da safe "
.
Koda abul dinar yaji wannan batu sai fuskarsa ta fadada da murmushi yace na yarda dakai sarkin matsafan duniya gulmanu , shikenan na sallameku, kowa ya tafi gida sai gobe da safe mu hadu a kofar fada
.
Nan take 'yan majalisa suka watse batare da wani daga cikinsu yace kala ba aka bar sarki acikin dumbin farinciki
.
Birnin sarwaliya babbar garine mai tsohon tarihi ,wanda a halinm yanzu sarki abul dinar yake sarauta a cikinsa gaba daya al'ummar farin ma'abota Addinin bautar wata ne , duk sa'adda wata ya cikja kwana goma sha biyu gaba dayansu maza da mata yara da manya sukan fito tsakar dare , suyi sujjada ga watan suna masu fadin bukatunsu da rokon gafarar kurakuransu, wannan abu ne wanda ya yi matukar tasiri zukatunsu
.
Bayan sarki yagama shawara da yan majalisarsa sai yasa akayita shela da yekuwa aka sanar da jama'ar gari cewar gobe da safe ana gaiyatar kowa a fada ba ayafewa ko da yara ba . Masu shela basu daina sanarwa ba har sai da dare yayi , sannan suka je suka kwanta.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kashe gari jama'a sukayi ta tururuwa suna zuwa fada kungiya kungiya ,ayari ayari ,har daga kauyuka,kai wasu ma saga makotan kasashe sai da suka zo don son ganin kwakwaf,saboda labari ya bazu cewa akan maganar 'yar sarki ne da bakin bawan data nace tanaso.
A cikin wadanda suka halicci wannan taron akwai wasu jarumai kimanin su shida masoya mabaruka , wadanda suma ashirye suke dasu salwantar da rayuwars son ganin sun sami aurenta.
.
Bayan sarki abul dinar da'yan majalisarsa sun hallara , sai aka tura wani bafade yaje yakira ashwar daga gidan gona . A sannan ne gimbiya mabaruka ta iso tare da kuyanginta da baradenta , nan take taje ta zauna bisa kujerar dake daf da karagar sarki ,
Sarki ya dubeta yai murmushi .
Hakan keda wuya kuma sai ga ashwar tare da da bafajen da aka aika ya kirawo shi sun iso, da zuwa aswar ya fito tsakiyar filin fada , ya fadi yayi gaisuwa ga sarki , bayan an amsa gaisuwar ne aka yi masa izinin mikewa tsaye , yana mikewa ne yayi ido biyu da abar begensa tana mai yi masa wani irni murmushi mai tona asirin zuciya .
Cikin karfin hali ashwar ya yiwa mabaruka murmushi , sannan ya kau da kai ga barin kallonta don tsoron kada tsananin kyawunta ya rinjayi zuciyarsa ya kamu da sonta .
Tun daga ranar da ashwar ya fahimci cewa gimbiya mabaruka na sonsa , tsoro da damuwa suka cika zuciyarsa .
Badon komai ba sai don ya tabbatar mahaifinta ba zai maraba dashi ba , wannan dalili yasa ya danne sha'awar bege da so a zuciyarshi ,har a halin yanzu ashwar bai yadda son mabaruka ya shige shi ba , kai in ba don ma bin umarnin sarki ba da tabbas ba zaizo wannan kira da akayi masa ba.
.
.
A cikin wannan gona ta sarki wadda ashwar ki aiki , akwai wani dattijo abokin aikinsa wanda ake kira makabul. Makabul tsohone sosai , domin shekarunsa sun kai kimanin tamanin da doriya . Makabul aminin baban ashwar ne , don asali ma tare aka siyo su a matsayin bayi daga nahiyar kasar bakaken fata,
Tun suna samari yan shekara sha tara.
Tun ashwar na yaro karami ya taso yake ganin abotar da ke tsakanin mahaifinsa da makabul, don haka bayan rasuwar mahaifinsa sai ya rike makabul tamkar mahaifinsa komai zaiyi sai ya shawarce shi . Yanzu hakama makabul dinne yabashi shawarar yazo fada don amsa kiran sarki kuma yace dashi kome aka bukaci da yayi akan mabaruka kada yaji tsoron komai ya amsa cewar zaiyi, komai wahalar al'amarin. Koda ashwar ya tambayi makabul dalilin da yasa yace ya sai da ransa.
.
Sai yace dashi" tun mahaifinka nada rai mun taba zuwa wajen wani boka wanda yayi bincike akan ka , bokan ya sanar damu cewa zaka shahara a duniya , kuma zaka auri 'yar sarki, amma sai ka karbi Addinin musulunci
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yayi shiru yana tunani daga can yace" kai baba makabul yanzu a ina zan sami ma'abocin wannnan addinin daka fadi? Kasani cewa babu masanan sa anan garin dakuma kasa shen kewayenmu"
.
Makabul yayi murmushi yace "kada ka damu akwai tafiya da zakayi tabbas zaka hadu da ma'abota Addinin musulunci,da zarar kun hadu ka karbi Addinin, in da rabon mu ma zaka dawo gida ka sanar damu wannan Addini mu karbe shi, don tabbas shine Addinin gaskiya , amma kiri kiri sarakunanmu sun ki shi don kwadayin duniya , da son mulkinsu na kama karya "
.
,
Duk wannan hira ta wakana ne adaren jiya tsakanin ashwar da makabul.
.
Yayin da ashwar ya karbi umarnin mikewa tsaye gaban sarki a tsakiyar fada, sai sarki Abul dinar da sarkin matsafa gulmanu suka dubi juna , nan take gulmanu ya mike tsaye , yayi gaisuwa ga jama'ar gari sannan yace
.
"Yaku al'ummar sarwaliya kun sani cewa sarkinmu ya dade da rashin samun haihuwa sai bayan shekara da shekaru ya sami mabaruka,
Yau gashi Allah ya yarata takai mun zalin aure, ku sani cewa 'ya'yan sarakuna jarumai, da mtsafa sunzo da yawa ba adadi sun nemi aurenta , amma basu samu ba saboda tace bata sonsu .
To yau an wayi gari gimbiya mabaruka ta budi baki ta fadi wanda takeso ,kuma bawani bane face bakin bawannan dake tsaye agabanku wato ashwar"
.
Nan fada ta rude da hayaniya sai da aka yi tsawa sannan kowa ya yi shiru.
.
Boka gulmanu yaci gaba da cewa " to mu muna da ka'idoji a wannan masaruta ta mu muna kafin mu aurar da yar mu duk wanda zai auri 'yar sarauta dolene ya kasance daya cikin uku, abu na farko shine sai ya kasance. Mashahurin mai arziki , abu na biyu dole ne ya kasance dan sarauta , abu na uku dolene ya zama jarumin da yayi mashahuriyar jarumtaka a duniya . Kun sani cewa wannan saurayi ashwar dake tsaye a gabanku bai kasance cikin daya daga cikin wadannan ka'idoji dana lissafa ba saboda haka yanzu dama daya gareshi dole ne yaci jarabawar da zamu yi masa akan jarumta , indai yaci wannan jarabawar to zamu amince mu aura masa gimbiya mabaruka"
.
.
Ehem shuraih 99% ke magana muje zuwa
.
Koda jama'a sukaji wannan batu sai akayi shiru kai kace mutuwa ce ta gifta ,
Kowa ya kasa kunne don yaji wace irin jarabawa ce za'ayi wa jarimi ashwar.
.
Boka gulmanu yayi shiru zuwa 'yan dakiku kadan sannan ya nisa yace"Abin da muke so ashwar yayi don mu tabbatar da jarumtakarsa shine , munasa kaje birnin Duma ka shiga fadar sarkin Aljanu kifyan, ka dauko mana Bishmalu dan sarkin Misra wanda tun yana jariri sarki sarki Kifyan ya sace shi, ahalin yanzu Bishmalu ya cika shekara ashirin da biyar. A duniya .
Kasani indai kayi nasarar dauko Bishmalu , sarkin Misra yayi alkawarin zai raba kasarsa biyu yabaka Rabi , mu kuma take zamu aura maka gimbiya mabaruka , kaga ka jefi tsuntsu biyu da dutse guda kenan wato ga sarauta ga auren 'yarsarki
.
Boka gulmanu na gama wannan jawabi fada ta sake rudewa da hayaniya, kowa na cewa wannan aikora da haline , dan tabbas an san cewa babu wani mahaluki daya isa yaje birnin Duma don gari ne na Aljanu zalla , Aljanun ma bakake mazalunta kuma kafirai, sarkinsu kifyan shine ubangijinsu don shi suke bautawa.
.
Ragowar jaruman nan guda shida , wadanda suka zo da niyyar sallama rayuwarsu son aurar Gimbiya mabaruka sai duk suka zare jikkunansu suka boye a cikin jama'a don sun tabbatar da cewa ba zasu iya cin wannan jarabawa ba, dominn labari ya bazu ko'ina a duniya cikin wannan zamani cewar sakin Aljanu kifyan ya zama gagara badau, ya Addabi dukkan aljanu da bil'adama dake doron kasa.
.
Littafin :- king of Adventure stories(Abdulaziz sani madakin gini)
.
.
WANE NE BISHMALU
.
YA AKAI SArKIN ALJANU KiFYAN YA SACESHI
.
SHIN AShWAR ZAI YADDA YA AMINCE DA WANNAN JARABAWAR
.
IN MA YA AMINCE SHIN ZAI SaMU NASARAR DAUKO BiSHMALU DAGA FADAN SARKI KIFYAN
.
.
Domin jin wayannan amsoshi sai ku tareni a babbar goro part 1 B
.
.

TASKU part 9


Upload : 25 Jul 2017 - 19:12
Size : 155 kb _______________________________________
--- TASKU
--------------------------------------------------------------
__kirkirarren labari_____________________
----daga Shuraih 99%------------------------------
Part 9
.
.
Ina zaune bisa wani kujera, na yi zurfi cikin tunani
.
"Assalamu'alaikum" naji muryar Abbana
.
Umma ta ce ta amsa mai sallamar , ko kallon inda nake baiyi ba ya wuce izuwa dakinsa
.
Ina ganin haka nace a zuciyata yau dea zanje na ba Malam hakuri, inma wani laifin na mai a iya sanina ni dai nasan babu laifin dana aikata masa,
.
Na tashi na nufi cikin dakin nasa, sallama nayi na shiga na iske shi a zaune bisa kushin a tsakiyar falonsa,
Ya amsa sallamar amma kansa aduke yana danna waya,
.
Na durkusa bisa guiwowina a gabansa nace " Malam kayi hakuri, bisa abin dana aikata, duk da bansan abin dana aikatan ba, tunda na taso a gidan nan baka taba fushi da ni ba sai wannan karon
Sannan kuma fushin iyaye masifa ce ga yayansu, don Allah malam ka yafeni, kaine komaina a rayuwa kamin komai"
.
Sai asannan ne yadago kai ya dubeni "ni baka batamin rai ba, illa dai kawai abu daya , malam shuraihu (sunan da babana ke kirana da shi kenan) shin me ya hadaka da wannan yarinya sannan kuma a cikin tsohon dare,
Ta yaya zaka nemi ka bata sunan wannan gida namu , dukkan mutanen wannan angwan suna ganina da kima da mutunci, "
Yadanyi ajiyar zuciya ,
Sai a sannan ne na fahimci inda maganan Malam ya nufa,
Yaci gaba da cewa" shin yaushe ka watsar da tarbiyar dana baka , shin yaushe rudin duniya ta fara debarka, kodai MUGAYEN ABOKAI ke maka hudubar shaidan, sam sam bazan yadda ka batamin suna a wajen mutane ba" yafada cikin bacin rai
.
Na dubeshi sannan nace"Malam ba abin da kake tunani bane , babu wani wanda ya'isa ya gurbata wannan tarbiyar daka bani sai Allah, dayar dar Allah bazan taba jawo maka zagi wajen mutane ba,
"
Nan na fede wa babana biri har wutsiya, sannan na kara da fadi mashi cewa ni ina Sonta da aure ne bawai da wani nufin ba
.
"Alhamdulillah Alhamdulillah dama mu abin da muke so kenan , tuntuntuni nake ta yi dakai akan kayi Aure amma sam kaki toh yau kam babu wanda ya kaini farin ciki bisa wannan zance daka sanar dani, yar gidan wacece"
Nan na dan susa keya " bansan sunan mahaifinta ba amma zan....."
Sallamar da mukaji ne ya dakatar da zancena,
Mahaifiyata ce ta shigo dauke da farantin abinci ta ajiye farantin mai dauke da kuloli biyu da kuma cokula a saman wani dan karamin gilashi mai kirar teburi, wanda akayi dama don hakan ,"
.
******** *********** ******
Ina tafe bisa mota ta kirar 406, wani sauti na saka , sai tashi yake yadda kasan wani club ,
,
Pakawa nayi a gefen titi sannan na kira wayan mjd,
.
Bayan ya dauka ne na sanar dashi yanzu haka ina kofar gidansu ina jiransa,
,
Baifi minti biyar ba da ajiye wayata, sai gashi nan ya fito, yana zuwa ya shige gidan baya ya zauna. Na duve shi" malam kasan ni ba direban kabane koh"
.
Murmushi yayi sannan yace" ok zaka basu labari badai ni ba ,muje zuwa..."
Ya fito ya dawo gidan gaba kusa dani, nan na tashi motar muka hau hanya,
,
"Ya baba ina muka nufa" yafada dai dai lokacin dana sharo wata kwana ta wani babban gareji,
"Ba saidaka zan ba,kaji don haka ka kwantar da hankalinka" na fada yayin da hankalina ke wajen tuki
.
Har muka iso gidan bai ce dani ufFan ba mun karisa ciki sannan na kira wayarta,
,
Bugu daya Tadauka anan na sanar da ita ina gidansu, inajin lokacin da ta sa shewa, sai kuma tace dani na kariso dama mahaifinta yana so yai magana dani,
,
******* ********** *******
Rantsatstsen falone wanda ya amsa sunansa , mahaifinta yana wani babbar kushin maicin mutane akalla goma , sai kuma ita Rufaidan tana gefensa
,
Nida mjd zaune bisa wani sofa mai cin mutum uku zuwa hudu, mun fuskanci juna da mahaifinta,
,
"Yaro tabbas ka ceto yata daga shiga wani hali na rayuwa, sannan ka ceto martabar wannan gida,ni nama rasa da wata kalma zan yi amfani da ita wajen yi maka godiya,na gode yaro, shuraihu kake ko shuraiha" mahaifinta yafada yayin daya ke dubana,
.
"Shuraih ne sunan baba, sannan basai kayi mini godiya,ai wannan ba wani abu bane tamkar kanwata haka take ,ka dai gode ma Allah mai kowa mai komai,"
,
Wayarsa ce tayi kara nan danan ya daga magana sukayi daganan yace damu shi zai tafi izuwa wani taro da aka kirashi na gaggawa,
.
Bayan tafiyarsa ne na dubi Rufaida wani zunzurutun sonta ne ke kara shiga cikin zuciyata,
,
Toh anan ne na tambayeta ya akayi har wayannan karti suka kawota cikin wannan kwarin da kuma dalili
.
Nayi mata wannan tambayar ne don kawai naji sautin muryarta wanda ya kasance mai zakine tamkar zuma,
,
Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dubemu ni da mjd tafara bada labarin kamar haka
"Mahaifina........
Ku biyoni a part 10
Its Shuraih 99%
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч @Shuraih Usman

TASKU part 8


_______________________________________
--- TASKU
--------------------------------------------------------------
__kirkirarren labari_____________________
----daga Shuraih 99%------------------------------
Part 8
.
.
Daga nan bansan kome ya faru dani ba
,
Idanuwa na ne suka fara budewa, na dan fara gani dishi dishi,
.
Toh a sannan ne idanuna suka washe na fara gani da kyau,
.
Kwance nake bisa wani katifa mai dan karen laushi, a gefena ga mahaifiyata! Da mahaifina,
Gefen haguna kuwa, Mjd nagani shida Anas ,
.
Na dan mike da kyar na jingina da bangon wAjen wanda nake tunanin asibiti ne,
.
"Sannu, koma ka kwanta," mahaifiyata ta fada, a lokacin data ke dubana
.
Sai a sannan ne na lura da kafata na hagu , wani dogon karfe ne a gefen gadon a sakale ajikin karfen wani farin bandeji ne wanda ya taimaka wajen tallafo kafata, izuwa sama,
Wajenda wannan karen ya dan kara min cizo, an dabaibayeshi da bandejii
.
Sai a wannan lokacinne a bubuwan da suka faru dani suka fara zarya a cikin kwalkwalwata
.
Na tuna lokacin dana bingire kasa, abin da kunnuwana suka jiye min na karshe shine*n sautin kukan rufaidah,
.
Na dubi mahaifiyata nace mata "umma ya akayi na zo wajennan,"
.
"Abokinka ne ya dauko ka, kaida wata yarinya, a can wani angwa," ta ce dani tana duban mjd
.
Mjd najin haka ya matso kusa dani sannan ya dafa kafaduna," Nazo gidankune nemanka shine aka sanar dani baka nan, dana tambayi umma shine tace min tun da mukayinnan ne haryanzu ba ka da wo ba"
Yadan sauke ajiyar zuciya sannan yaci gaba"toh a lokacinne nakira wayarka, bayan an dauka ne naji sautin mace kuma da alamu kuka take, anan ta sanar dani halin da kake ciki, tai mani kwatancen, wajen da kuke ,
Ina zuwa kuwa na iske baka cikin hayyacinka, nan na daukoku izuwa wannan a sibitin yanzu haka ita tana wancen bangaren, amma abin dana keso dakai, ka kwantar da hankalinka babu abinda ya sameta, kawai, dai dan kurkurjewan da tayine ake yi mata treatment nashi"
.
Na mayar da dubana wajen mahaifina , wanda ya hada rai tamkar an turo masa da sakon mutuwa, "baba....."
Yada katar dani ta hanyar daqa mani hannu alamar baya bukatar wani zance.
.
********* *********** ******
Zaune nake a tsakar gidanmu, a gefe ga ummata, tana gyaran shinkafa,
,
Yau kwana daya kenan da sallamata daga asibiti,
Tun alokacin na fahimci mahaifina yana daddaure mani,
Koda na gaishesa sai dai ya amsa a cikin daure fuska, sabanin daa
.
.
Gidan mu gidan mutuncine sannan mahaifina malamine, Sunansa, Mu'azu toh sabida malumtarsa sai ake kiransa da Malam Mu'azu,
Ummana itace kadai matarsa, sunanta, Maryam, ana mata lakabi da mairo, ni kuma umma nake kiranta,

kuma nine kadai dan da suka haifa a duniya,
.
Bakaramin ji dani mahaifina yake ba, dun ya nunamani gata, tun ina karamin yaro, har nafara girma, toh a sannan ne yasaka ni awata makaranta ,SOKOGA,private ce nayi nursery da primary acan daga baya kuma na koma KDF acan ne nayi secondry school dina
,
Dana idar sai na sami admission a NSUK, ina karanta fannin Engineir,
,
Shekaruna biyu kenan da fara aiki da wata kamfani na kera kayan motoci da na mashina, a Abuja,
.
A ka'ida ta duk ranar jumu'a, ina zuwa gida nayi hutun mako tare da mahaifana,
.
Wannan makonma hutun nazo
dana san abin da zai faru dani kenan tabbas da na hakura da wannan hutun,
,
Muna namu Allah na nashi,
Wannan shine takaitaccen tarihina
.
Kubiyoni a part 9
.
Its Shuraih 99%
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч @Shuraih Usman
search.txt
Upload : 01 Jan 1970 - 07:00
Size : b

TASKU part 7


_______________________________________
--- TASKU
--------------------------------------------------------------
__kirkirarren labari_____________________
----daga Shuraih 99%------------------------------
Part 7
.
.

Wasu murdamurdan karnukane su biyu, jikinsu sur gashi, girman kowani dayansu yakai girman kosashshen rago, baki bude suka nufo mu suna haushi,
,
Sam sam karka dauka wai ina jin tsoron karnuka ,
Toh ni da anguwarmu ma cike yake da karnuka
.
Toh amma da nai arba da wayannan kosasssun karnukan sai da hantata ta kada , domin ban saba ganinsu ba
.
A dai fina-finan indiya da america ina ganinsu, toh amma a zahiri dai yaune mukayi kicibis dasu
.
Koda wayannan karnuka suka fara kusanto mu
Sai rufaida ta rude ta tsuguna a kasa ta rufe fuskarta,
.
Haryanzu wukar dana cire a kugun katonnan yana hannuna ,
Nan na kara damkeshi da kyau tamau,
.
Karnukan suka daka tsalle a lokaci daya suka fado jikina , a sannan ne suka mangareni na fadi akasa,
.
Rufaida na ganin hakan sai ta taso daga tsugunen data ke ta dauki wani shirgimemen dutse,
Tayi nasarar jefar kare guda da wannan dutsen sai dai , dutsen bai jimata rauni ba,
.
Karnukan dukkansu suka juya izuwa kanta, na tabbata izan har suka, isa gareta , lamari ya baci
.
Cikin sauri na yi gudu na wawuri kare daya na yafa da kasa sannan na caka mai wuka a kafarsa daya, nan ya kwanta sai shureshure yake, dayan karen na ganin haka, sai ya dubeni sannan ya nufo ni cikin gudu
.
Koda ya rage baifi zira'I kadan muhadu ba sai ya daka tsalle ya fado jikina yasanya gaba daya farcensa a gefen wuyana bakinsa kuwa wadda take wangame tana saitin maqokwarona, nufinsa ya fasa makoshina da fikarsa
.
Koda na fahimci manufarsa, sai na yunkura don na yi cilli dashi amma naji na kasa sakamakon dannenin da wannan karen yayi,
.
Karfin tsiyane da shi, da kyar na tureshi daga jikina,
.
Sannan na bishi na kama bakinsa na caka mai wukar a tsakiyar ka har sai da ta fito ta cikin bakinsa nan take yafadi kasa matacce,
,
Na nufi wajen rufaida wacce tagama tsorata da wayannan karnukan
.
Nakama hannunta muka tashi tsaye,
Toh a daidae wannan lokacin ne al'amarin ya faru,
Wani radadine ya ziyarce kafata, na'zata ko zarto ne aka sa za'a yanke kafar, sai a sannanne idona yai arba da dayan karennan ya damfara wa kafata cizo,
.
Na janye kafata daga bakinsa, na dan rarrafa, ina cikin rarrafen ne naji hannuna ya taba wani abu ,
.
Bakomai bane illa guntun bulo, ji nayi saukar karennan a ruwan cikina,
.
Ai ban tsaya wata bata lokaci ba na rarumi wannan bulo din na maka masa aka,
Nan yayi gefe, ya bingire a kasa koda naga haka sai na tashi, na hau ruwam cikinsa, nai ta maka masa wannan bulo din aka har sai da bulo din ya juya izuwa gari,
,
Sai a sannan ne hankalina ya dawo jikina na yunkura na mike tsaye ,
,
******** *********** ********
,
Munyi tafiya mai nisa a cikin wannan daren,
Har muka iso daidai wajen wani gada wanda a akasar wannan gada ba komai bane illa wani katon kogi, shi wannan kogin ana mai lakani da mahannu,
.
Muna zuwa daidai gadan na turje sakamakon kafata data ke yimin wani mugun ra dadi,
.
Na dubi rufaida na ce da ita, "duk da mun kasance muna cikin halin tashin hankali, toh wannan bazai sa na gagari furta miki sakon zuciyata ba"
.
Ta dubeni cikin alamun rashin fahimtar inda zance na ya nufa
"Tun lokacin dana fara ganinki, lokacin da idanuwa sukai arba da wannan kyakyawar fuskar taki, tun a sannan wani mashi mai dauke da dafin sonki ya ca keni a kahon zuciyata,
Kece kawai maganin wannan dafin sam sam wannan lalurar dake jikina bai dameni ba,
Don muddin akan kine zan iya, sadaukar da rayuwata,
Kisani Rufaida I NA SONKI,
Bawai so na fatan baki ba sannan bawai so irin na mayaudara ba , ke wata ginshikice na a cikin rayuwata"
Ina gama fadin wannan kalmar na bingire kasa sumamme.
Daga nan bansan kome ya faru dani ba
,
.
Ku biyo ni a part 8 .
.
Its Shuraih 99%
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч @Shuraih Usman

TASKU part 6


_____________________________________
--- TASKU
----------------------------------------------------kirkirarren labari________________
----NA Shuraih 99%-----------------------
Part 6
.
.

Koda wayannan karti hudun suka ga abinda nayi wa dan'uwansu sai suka zaburomani tamkar zasu cinyeni danye
,
Zobe suka yi mani sannan muka fara kallon kallo tsakanina dasu,
,
Yadda kasan giwaye ne suka sa cinnaka a tsakiya haka sukaimani, wani garjejen kato daga cikinsu ya rarumeni yadaga sama sannan ya tika da kasa,
,
Ai nan naji tyamkar, kashin bayana ya karye, na kwala ihu ,
Koda ganin hakan sai daya daga cikin kartin ya dubi wanda ya kwada ni da kasa yace
"Yanzu sisini maza je ka duba lafiyar Gogo, "
Wanda aka kira da sisinin najin haka ya nufi wajen katon dana barar dazu da dutse
,
Ya dagashi daga kwancen dayake, sannan ya zaunar dashi,
.
Sukuwa cikon ukun sai suka fara dumfaro inda nake kwance , koda na farga da su sai na cika hannuwana da kasa,
Daidai wani kato ya kawomani naushi sai na tsuguna ya naushi iska, kafin yakai ga juyowa na watsa mai wannan kasar dana diba cikin hannuwana acikin idanunshi,
,
Nan ya tsaya turmus sai karkade idanu yake,
.
Nan take kuma idanuwana suka kai ga mararsa inda ya soke wata wuka irin na yan daban nan kafin yan'uwansa suyi wani yunkuri, tuni har na zare wukar a mararsa ,
A samam makoshinsa na sanya wukar sannan nayiwa yan'uwarsa barazanar, cewa in suka kariso gareni toh tabbas zan yan kashi,
.
Koda suka ga haka sai dukkansu suka fara ja da baya ,
.
Nima ina ganin hakan na dubi wannan budurwar da haryanzu take kwance gashin kanta a barbaje, sannan bakinta na fidda jini
,
Nace mata" tashi mu tafi"
.
Nan ta mike ko dankwalinta bata tsaya daurawa ta nufo bayana
.
"Kana jefa kanka a cikin matsanancin tashin hankali, lallai kasani muddin ka aikata, abin da kake yunkurin aikatawa toh lallai, sai kayi dana sani , alokacin da dana sanin bazai yi maka amfani ba
.
Murmushin karfin hali nayi sannan nai duba ga budurwarnan na ce mata ta fice daga cikin kogon
.
Shi kuwa katon dana sanya mai wuka a makoshinsa ko kwakkwarar motsi ba yayi , a tunaninsa a kowani loka ci zan iya danna hannuna wukar ya lume cikin maqokwaronsa,
.
Jansa nakeyi muna tafiya har muka kawo bakin kogon a sannan ne na juya na dubi yan'uwansa, "Lallai kada kuyi gangancin fitowa daga cikin wannan kogon , domin muddin kuka fito kuwa wannan dan'uwankun sai de wani ba shi ba"
Na fada cikin gargadi garesu.
.
Nan suka dakata sai muzurai suke,
,
Maimakon mu haura saman kwarin ta inda na gangaro wato ta bakin titi, sai muka haura ta dayan gefen inda zai bulla dani gidajen mutane,
,
Duk wannan tafiyar da mukayi ban yadda ko da wasa na kauce da hannuna daga saman makoshin wannan katon ba.
.
Muna haurowa saman kwarin sai na bankaje katon , nan take ya fada cikin kwarin da mirgine,
.
Ban tsaya wani bata lokaci ba na kama hannun wannan budurwar wacce bana iya , ganin fuskarta, muka ci gaba da gudu,
.
Gudu muke wanda ko waiga bayanmu ma ba mayi, nan wannan budurwar ta yi tuntube da wani gwangwani ta fadi,
.
Sai a sannan ne na tsaya na lura da wajen da muke, muna wani faffadan filine , wanda ciyayi suka dan tsiro kadan kadan a gefen mu na dama wani babban gidane na kece raini
.
Gaba daya jikin bangon wannan gida a lillike take da kwayakwayai lantarki, wayanda suka haske kofar gidan,
.
Hasken kofar gidan ne ma ya dan haska wannan faffadan filin da muke ciki,
.
Nan na duba a gogon wayata, 2:25,
Tun danake ban taba ganin musifa irin wadda naganta a yau ba ,
.
Danai duba izuwa wannan budurwar sai naga ita ma ta mike ,
.
Hasken nan ya haska mani fuskarta, Turus kawai nayi yayin da kaina ya kusa juyewa,
.
Na dan muntsili hannuna wai ko mafarki nake, tabbas a zahiri ne
.
Kamar ko yaushe fuskarta sai sheki yake a yayin da wasu siraren hawaye ke gangarowa ta saman kumatunta,
Sirara kebbanta sun rine da jan baki,
.
Ba wata bace face RUFAIDAH
Yarinyar dana Zuzuce akanta
,
Ita ma na fuskanci ta ganeni sabida yanayin da fuskarta ta nuna,
,
Hau hau hau hau
Naji daga gefena ina juyowa nai arba da su,
,
Wasu murdamurdan karnukane su biyu, jikinsu sur gashi, girman kowani dayansu yakai girman kosashshen rago, baki bude suka nufo mu suna haushi,
,
Tir kashi anyi gudun gara an.........
Inji hausawa
,
Wai karya ta kare bori taci boka
Tobe continue
,
Its Shuraih 99%
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч @Shuraih Usman

TASKU part 5_____________________________________
--- TASKU
----------------------------------------------------kirkirarren labari________________
----NA Shuraih 99%-----------------------
Part 5
.
.
Wannan shine tambayar dana yiwa zuciyata.
,
Toh ma mezai dameni koma dai wanene ke wannan kuka babu abinda ya shafeni
.
"Tai mako jama'a! Babu wani bane yazo ya taimakeni!" Naji wata murya na fadi, ta cikin surkukin kwarin dake gefena,
Tabbas wannan muryar mace ce , sannan kuma duk yadda akayi tana cikin wani haline
.
Ban tsaya wani dogon tunani ba na fada cikin kwarin ina fadawa na cigaba da gangarawa,
.
Nan na isa cikin wani surkukin ciyayi , toh anan ne Mafarin shigata cikin TASKU ya samo asali
.
Tabbas da nasan ko menene ke shirin faruwa da ni toh da banyi gangancin kara shiga cikin surkukin ba
.
Ina wuce ciyayin nan, na iske wani dan kogo,
batare da wata fargaba ko tsoro ba na danna kai cikin wannan kogon,
.
Na kunna tocila na wayana yayin dana kutsa kai cikin kogon ,
Wannan kogon dai irin ramukannan ne da ake tonawa don neman arziki ,
Babu komai acikin kogon in banda duwatsu da kuma rairayin ciyayi,
,
Ina kara gaba na ja tunga nayi turus sakamakon abinda idanuwana suka gane mani
.
Bakomai nagani ba face wata kyakkyawar budurwa, kwance a kasa, sannan wasu karti, su biyar sun zagayeta,
.
Biyu daga cikin kartin nan sun rike ma wannan yarinya hannu, yayin da wasu karti biyu suka rirrike mata kafafu , a sannan ne wani kato ke kokarin yi mata fyade ,
,
Ita ko babu abinda take illa ihu da karaji da neman taimako,
,
Sudai wayannan karti zasu kai shekaru talatin dukkansu, sannan gaba dayansu sun sanya bakaken kayane, jaket ce baka ajikinta anyi mata Ado da wasu duwatsu na karfe ,

.
Yayin da wayannan karti suka ganni cikin wannan kogon ,
Sai guda daga cikinsu wanda yake kokarin haike ma wannan yarinya ya dubeni sama da kasa sannan yace dani cikin wata murya mai kama dana jaki
"Kai dan tsako ,Ka kama gabanka tun kana numfashi "
.
Koda naji wannan zace nashi sai na juya da niyyar na fice daga cikin wannan kogo ,
Har na fara tafiya sai naji muryar budurwar tana cemani" Malam dan Allah ka taimaka mani, ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka"
.
Najuyo sannan nayi magana yadda zasu iya jina " kiyi hakuri yar'uwa "
.
"Yanzu da kanwarka ko wata yar'uwarka kaga za aketa mata mutuncinta ,haka zaka juya ka tafi"
Tafada yayin da akarshen maganar tata ta kare da kuka
,
Ban iya mai da mata da amsa ba sakamakon yadda maganar ya shiga cikin zuciyata
.
Kawai sai najuya na fice daga cikin kogon
,
Ina ji tana kirana amma ya zanyi dole ce tasa , domin gaskiya ni ba jarumi bane kuma bana da kirar sadaukantaka a jikina,
.
Toh koma dae menene ai hausawa nacewa sarkin yawa yafi sarkin karfi
,
Ayayin danake wannan tunanin ne naji zuciyata ta fara tafasa, ni kaina bansan lokacin dana juya na koma cikin kogon nan ba
.
Ina zuwa naga wannan katon na kokarin cire mata kaya hakan ne yakara tunzura ni
,
Nan na nemi wani katon dutse na dauka ina zuwa na sami daidai saitin gadon bayansa , na mai dundu, da wannan dutsen, nan ya kife, ,
,
Koda wayannan karti hudun suka ga abinda nayi wa dan'uwansu sai suka zaburomani tamkar zasu cinyeni danye
,
Zobe suka yi mani sannann......

TASKU part 4_______________________________________

--- TASKU

--------------------------------------------------------------

__kirkirarren labari_____________________

----daga Shuraih 99%------------------------------

Part 4

.

.

Ai bansan lokacin dana saki baki Galala ina kallonta ba
.

Koda ta kariso gabanmu saita tsuguna ta gaishemu sannan ta fara magana yayin datake dubana
"Kuyi hakuri da abun da nai maku jiya"
Bakina na rawa na ce"ai babu komai ,"
.

"Wallahi jiyannan na rudene sosai shi yasa,kuma na zata Abba zai min fadane shi yasa" ta fadi cikin wata irin murya tamkar bata son fadin maganar,

.

Ta kara dubanmu tace"Sunana Rufaida "

."Sunana shuraih, wannan koh m...."

Mjd ya katseni yayin daya ke fadin "malam barni na sanar da'ita sunana, "

Dariya kawai mukayi yayin daya cigaba"wai nine zai min lamuni,toh Allah yasa ina da baki "

Nanma murmushi kawai tayi,
"Mujahid ko kice mjd sunan kenan"

.

Na dan harereshi nace"sai kuma akace ka fadamana nickname ko"
.

*******************

Bayan mun yi musayar nombobi nida ita sabida zumunci, daga nan muka rankaya zuwa gidanmu ,sabida cikinmu dake kiran ciroma.

.

Zaune muke muna cin abinci nida mjd anan ne yake sanar dani wani wajen bikin Sallah da zamuje da la'asar wai shi minki,

.

***************

Muna isa bakin get din muka nausa kai ciki sakamakon get din dake bude, anan muka sami wajen parking muka paka motan

.

Samarine da 'yan mata ke ta zirga zirga a cikin wajen ,yayin da wasu yanmata wayanda suke tare da samarinsu, zaka gansu tare suna hira.

.

Yaune zuwana na farko wannan waje ,dun haka sai na nufi bayan wani bishiya domin na dan huta ,

Wani makeken bencine dakure akusa da jikin bishiyar, saman bencin na dane,

Mjd kuwa muna shigowa cikin wajen naga ya nufi wajen wata yarinya daga nan suka ci gaba da tadin su,

.

Daga wajen danake zaune ina hangen samari da yanmata dake zirzirga a wajen ,wasu gungun samarine da yanmata naga sunyi da'ira a wani kebabban waje, daga inda nake zaune ina iya sauraron sautin gular dake tashi,

.

Na tashi daga inda nake zaune na nufi wajen, koda na isa sai naga ashema yan'mata ne da samari keta gwargwazon rawarsu, sai tika rawa ake, ayayin da Dj ya saki kidan Ado gwanja na asha ruwa
.

****************

Kwata-kwata. Wajen ya gundureni ,zaman wajen ya fita min arai,

Nan naje wajen dana bar mjd tare da budurwarsa suna zance,

Koda na isa wajen ban samesu ba na duba sama da kasa gaba daya cikin minki ban samesu ba.

.
Dana kira wayarsa ne yake sanarmani shi yanzu haka fa babansa ya kirasa, kuma ya nemeni mu tafi bai ganni ba,
.
karfe 11:24pm agogon wayana ya nuna mini, nan take na fito bakin titi ina neman acaba, duk da nasan da wuya na samu acaba saboda dare da yayi,
.
Nafi minti talatin ina tsaye a bakin titin amma ko alamar acaba ban gani ba,duk da wani sa'in mashina da motoci sukan wuce jefi jefi,
.
Nan na yanke shawarar na taka saiyadata har Allah yasa na sami dan acaba,
,
Nayi tafiya mai nisa sosai har na fara gajiya, a sannan ne na iso angwan lambu,daidai gaban gidan rediyon N B S
,na sami wani dakali na dan zauna don in huta daga nan na cigaba da tafiya,

Baccin na hutane na cigaba da tafiya, har na iso wani waje dana duba agogon wayata 1:54 Am

Na danyi tafiya kadan kenan sai naji hayaniyar mutane, sama sama dana dan kara gaba ne na fahimci kamar shishshikar kuka ne ke fitowa ta cikin wani sunkuru,

Karkaji nace sunkuru ka dauka ko acikin dokar daji nake, a bakin titi nake wani wawakeken kwari ne dogo tamkar kwalbet, shimfide a gefen titin
Shi wannan kwari hanyar ruwane idan ana ruwan sama ta ciki yake bi yai wuce warsa, kwarin din cike yake da ciyayi, sannan a saman kwarin gidajene da kuma gidan giya,
Dana dan lura da kyau na kasa kunne sai naji shishshikar kukan na fitowane ta wani restaurant, restaurant din yana saman kwarin ne,
.
Shishshikar kukan ya cigaba da kara hauhawa, nan da nan na fahimci muryar mace ce,
.
Toh shin wacece ke kuka acikin wannan tsohon daren
.
Kubiyoni a part 5
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

TASKU part 3

_______________________________________

--- TASKU

--------------------------------------------------------------

__kirkirarren labari_____________________

----daga Shuraih 99%------------------------------

Part 3

.

.

"Amma Fa daga ninta kaga yar babban gida, " cewar mjd

.

"Ba yar babbar gida ba koma meye sai , amininmu ya shawo kanta" anas yafada yana kallona , yana dariya

.

Na dubesu a tsanake nace "koma dai menene gobe zamu ga gidansu ai"
.

**************

Kwance nake bisa kan katifata , idanuwana radau suna kallon katakon silif(batre)

A sannan ne A gogon bangon dake rataye a jikin bangon dakina ya nuna karfe 1:00AM, na dare,

.

Wannan ne ya tunasar dani daga nannauyan tunanin dana fada,

.

Yanzu haka wajen awanni biyu kenan da tafiyan su mjd da Anas

Tun daga lokacin nake ta Allah Allah barci ya daukeni Amma ina dana runtse idanuwana sai fuskarta ta bayyana yayin da siraran lebbanta ke furta kalamai tamkar bazasu furta ba

.

Naso ace na baiyana mata sakon zuciyata ,

Naso ace Na san sunanta

Naso ace nasan gidansu

.

Duk wayannan ban damu dasu sosai ba saboda nasan gobe duka zan sansu amma ,abin dana damu da shi sosai shine, shin zata karbi kokon barana,

Shin zata amince dani a matsayin masoyinta

Shin zata yadda nazama abokin rayuwarta

.

Da irin wayannan tunanin ne har karfe biyu yayi a sannan ne wani nannauyan barci ya ziyarci idanuwana .

***************

Bani da farkawa ba sai wajejen 7 bakwai na safe,

A sannan ne na tashi na nayi wanka sannan nayi kalaci(break) da shike yau Take RANAR SALLAH

.

Wata shadda tace fara mai daukar idanu
Na sanya sannan na sanya hula zanna bukar fara sol amma tuntunta bakine sidik.

.

Sai kiran nomban mjd nake amma taki shiga ,

.

Dadai na gaji da kirar sai na fito daga gida , nan na tare dan acaba, nai mai kwatancen wajenda zai kaini,

.

Saukana keda wuya na nufi wajen bakaniken ,

Ina zuwa na tarar dashi yana gyara wata mota, nai mai sallama, sannan nace mai
"Dafatan ka idar da gyaran"

.

"Sai oga an idar ko tuntuni"

"Da kyau ai hakan yayi"

Daga nan na shiga cikin motar na tashe ta sannan na hau kwalta,

.

Daidai lokacin dana faka a kofar gidansu mjd , daidai lokacin shi kuma ya fito
Yana sanye da shadda shima farace amma bai sanya hula ba,

Sai wata kalar aski daya yi mai taken dakalin shedan(punk)

.

Yana ganina yazo muka tafa sannan yace dani" baba ai nasan sai ka rigeni isa wajen bakaninkennan "

'

"A'a nai ta kiran wayarka amma ban sameka ba shiyasa kawai naje na dauko"

.

"Oh shit wayan tana hannun kanwana wallahi, amma no problem, muje kawai"

Ya bude gidan gaba na mai zaman banza ya shige,

"Ina muka nufa" nafada yayin da nima nake kokarin shigowa cikin motar,

"Masallaci mana"

"Ok" kawai na fada sannan na tashi motar muka nausa

*************

Hon na rangada a bakin get din gidan sannan wani tsakurarren mai gadi ya fito hannunsa rike da kulki , sai da yazo daf da motar ya kare mata kallo sannan ya je ya bude get din

.

Awan mu biyu kenan da tashi daga masallacin idi,

A sannan ne muka rankayo izuwa adress din data bamu,

.

Tabbas gidan ya hadu ba laifi muka nufi wajen parking

.

Bayan mun parking motar mun fito mun tsaya,

.

"Toh sai mu shiga koh yallabai" mjd ya fada yayin daya fara tafiya yana dumfarar kofar da zata sada shi cikin gidan,

Nan nima na mara mishi baya

.

Maigadin ne yai mana iso cikin rantsastsen falon maigidan,


Muna zama shima ya fito ya dubemu sannan muka gaisa,

Bayan mun gaisa ne yake tambayarmu " ko kune rufaida tace mani zaku kawo mani mota"


.

"Kwarai kuwa mune nan baba"
Mjd yabashi amsa
"Kuyi hakuri da abin daya faru jiya"

.

"Babu komai baba ai komai mukaddarine daga Allah,"

.

"Ni kaina saida nayi mata fada akan irin abun datai maku da tace sai kun gyara motar"

.

"Samsam,karka damu da wannan ai komai ya riga ya wuce"
Sai hira suke shida anas
Ni ko sainaji wata sanyi acikin raina sakamakon jin sunanta danayi RUFAIDA na sake maimaita sunan a cikin zuciyata,

Nan na shiga rarraba idanuwa ko zanga ci sa'a na ganta, domin so nake na sake ganin kyakyawar fuskarnan tata,

.

Har muka idar da magana da mahaifinta wanda bai sanar damu sunansa ba

Muka fito daga cikin falon sannan muka durfafi kofan da zata sadamu da farfajiyar gidan

.

.

"Sannunku da zuwa" naji i muryar da bazan taba manceta ba acikin rayuwata, tana fadi ta bayana

Juyowar da mukayi ne mukai arba da,ita kamar kullum yauma tana cikin wani dogon rigane harkasa sannan ta yafa wani gyale wanda yai matukar dacewa da kalan rigan jikintan,

.

Ai bansan lokacin dana saki baki Galala ina kallonta ba
.
Tobe conti
.
Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]

TASKU part 2


_______________________________________

--- TASKU

--------------------------------------------------------------

__kirkirarren labari_____________________

----daga Shuraih 99%------------------------------

Part 2

.

.

Nan ta fara magana tamkar bazata yi ba, ni kuwa babu abin danake sai kallon siraran lebbanta wayanda suka rinu da janbaki,

Wanda hakan ba karamin kyau ya kara masu ba ,

.

Chochulate color ce, doguwa wanda har taso ma ta fini tsayi, duk dana kasance ina da tsayi tamkar bishiyar kwakwa

.

Fuskarta faffadane , idanuwanta dara dara madaidaita, wayanda suka kara fitar da siffar kyauwun fuskar tata,

.

Ma tsakaicin karan hancinta wanda ya taimaka wajen fidda siraran lebbanta,

.
kai mai karatu duk yadda naso na baiyana maka ita saidai na fada amma tafi haka

.

Tana sanye ne da doguwar riga mai hade dankwali yayin data yafa gyalenta, a kafada ,

.

"Kai malam kaduba irin asarar da ka jamini kuma wannan motar batawa bace ta abbata ce , sai magana na ke tayi da kai amma kai sam hankalinka baya tare gareni" na tsinkayi daddadan sautin muryarta cikin kunnena ,

.

.

"Ehhhm ehhm, maganar ma ta gagareni furtawa sai in ina na ke"

.

Na dube ta dakyau sai naga wasu siraran hawaye suna zarya akan kyakyawar fuskannan tata,

.

"Kiyi hakuri , wannan duk laifina ne " na ji muryar mjd na fadin haka dana duba sai na ganshi a gefena ashe ma ya kariso ni bansaniba

.

"Ni babu abin daya shafeni ko laifin wanene cikinku nidai damuwata a gyaran motata ,"

.

Ta fada cikin murya mai ban tausayi, ai tunima na manta da wani abu waishi yunwa.

muryarta kadai inzan ringa saurara toh ya isa ya gusar min da dukkan wani bacin raina ,

.

"Ok toh indai wannan ne baki da damuwa , yanzu ki shiga cikin motar mu je gun bakanikai na tabbata yanzu dai basu tashi ba"
Inji mjd yayin daya ke dubana

"Kwarai kuwa "nace dashi amma fuskana na duban fuskarta ita kuma tunda tai mani kallo daya ta kau da kanta , ga barin kallona

.

¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤. ¤¤¤¤¤¤¤. ¤

Cikin wasu mintuna kalilan muka isa wajen bakaniken wanda yake zama a hayin waziri,

Nan dai ya ca jemu wasu kudade, mjd ya ciro ya biya ita kuma ta wuce gida , amma kafin ta wuce ta bamu Address din gidansu akan idan angyara mukai mata motar.

.

Hakan ba karamin dadi yai mini ba ,

Muna isa angwa nida mjd na fito na shige gida zuciyata cike da tunane tunane

**********************

Ina kwance a cikin daki fuskata yana kallon saman silif, zaka rantse da Allah cewa slif din nake kallo, toh Amma hankalina ya tafine ga tunano, wannan sirirriyar sautin muryar wadda da kuma wannan fuskar da bazata taba goguwa cikin idanuwana ba

.

"Shuraih! Shuraih!! Shuraih!!!"
Naji mruyar anas tsulum, nan na mike ina mai dubansa ,cikin mamaki

.

Bawai mamakin ganinsa nake ba a'a yadda akayi har ya shigo cikin dakin bansani ba alhalin ba bacci nakeba.

"Nayi sallama yafi baki goma amma kaki ka amsa mini" na tsinci muryarsa na mai fada mani,

"Kayi hakuri wallahi wani tunanine nake"

.

"Tunanin me"

.

"Tunaninta kake koh" naji muryar mjd , wai ashema tare suke da anas ,

Sam ban farga cewa yana cikin dakin ba sai daya fadi haka tukun

"Wacece ita" anas ya fada yayin daya ke duban mjd,

"Wata beuty ce muka ja mata asara, yau "

Nan ya labarta masa yadda mukai da ita

.

Ni dai sai jinsu kawai nake

Mjd yadan dukeni sannan yace"amma fa 99% kayi dace dun gaskiya yarinyar she is pretty,sai dai zakayi fama da'ita"

.

"Wani fama kuma zan da ita"

Na tambayeshi

.

"Zakayi fama da kuka mayena,dun yarinyar saurin kuka gareta sai kace wata ....."

.bai karisa maganar ba na kaimai dukan wasa,

Nan muka dara


.

.

Wannan labari Goron Sallah ne ga
dukkan Masoyana gaba ki daya

Hop kunyi Sallah lfy

Toh Allah ya maimaita mana

.

Ku biyoni zuwa par 3

Ban hana ayi copy co share din wannan labari ba Amma duk wanda ya cire sunana toh Allah ya isa
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
@[100013101818311:0]
νįά● @[296485144050085:0]
Fðя мðяє

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]

ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
ℓįкє : @[296485144050085:0]
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter