=2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria.

chat or inquires any novels with us

Saturday, 29 December 2018

AISHA cigaban AJALI na shafi'u Dauda Giwa page 1

AISHA
Cigaban AJALI
Shafi'U Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Page 1
.
BABI NA BIYAR
kakkarfan kwan lantarkin da ke kwararar da wadataccen haske a saman falwayar da ke a cikin asibitin ya haske kusan ko'ina a harabar dakunan jinya uku da kuma wani bangare na ofishin ganawa da marasa lafiyar wadanda ke a kulle .
.
Babu kowa a harabar asibitin idan aka dauke `yan tsirarun mutanen da ke fitowa daidai yin fitsari da kuma wadanda ke zuwa famfo su dibo ruwa a cikin daren. Duk da yake kusan ko'ina a cikin asibitin a wadace yake da hasken kwayayen wuta manya da kanana, hakan bai kwantar da
hankalin Kallamu mai gadin mutuware ba,
.
wanda yake a makure ya lullube jikin shi da tsohon bargo.
Yana rike da cocilar shi wanda a koda yaushe ko ba a dauke wuta ba, ba yasan rabuwa da ita.
.
Kallamu ba boyayye ba ne a asibitin, akalla ya kai shekaru goma sha shida yana wannan gadi na mutuware. Ba a cikin asibitin kadai ba, hatta a cikin garin an san wannan tsoho dan kimanin shekaru sittin a duniya.
.
Mutane da dama sun san shi ne saboda jarumtakar shi da ake gani. domin kuwa ba karamin jarumi zai kwashe shekaru goma sha shida yana kwana tare da gawarwaki a mutuware ba.
.
Kallamu mai gadi tsoho ne da ake so a zo a zauna tare da shi ana yi mashi tambayoyi a kan wannan aiki nashi. Mutane suna so ya rika ba su labarin abubuwan da aka ce ana gani a mutuware idan dare ya yi.
.
Kallamu mai gadi ya sha tabbatarwa da mutane cewar in dai a fannin zama tare da gawa ne to shi fa sai dai a ba shi lambar yabo idan za a ba shi, amma babu wata gawa da za ta tsorata shi a wannan duniyar, ko daga ina aka kawo ta. Tsohon ya taba cewa an taba yin wani kazamin hadarin mota wanda aka rasa mutane Ashirin nan take.
.
Kwaso su aka yi akazo da su mutuware, wadansu ma ba a ga hannuwansu da kafafuwansu ba. Kallamu mai gadi ya ce a daren da wannan al`amari ya faru yana zaune a kan kujerar shi sai yaji motsin tafiya a cikin mutuwaren. Ba zato ba tsammani sai ya ga daya daga cikin gawarwakin mutanen wanda kafadarshi daya
ta cire, ya taso yana dingishi, yana dafa bango
yana tunkaro shi, kai tsaye ya nufo inda yake.
.
Mutanen da ke sauraron tsohon suka tambaye shi a tsorace.
"Sai ka yi yaya, Baba?"
Tsohon ya yi dariya ya ce.
"Af! Zancen banza kenan. To ni irin wannan tsunburkan na gawa ai na sha ganin shi idan dare ya yi. Kuna tsammani gudawa zan yi? Tsayawa na yi har ya karaso inda nake zaune ya tsaya a kaina muka hada ido, kanshi fa a rabe yake duk ya farfashe a wajen hadarin kuma hannushi dayan ma ya guntule saura rabi."
.
Mutunen suka yi tsuru-tsuru a zaune suna jimamin wannan labari mai ban tsoro na Kallamu mai gadi, a karshe sai yace da su "Sai na tambaye shi me ya fito yi waje? sai ya ce da ni ya fito ne yana jin yunwa zai sha kunu. Na fada muku na saba da ganin irin wadannan 'yayyakun da waibuwar ta gawarwaki a wannan mutuwaren. .

.
Na dauko ragowar furata na mika ma shi na ce ya zauna ya sha. Ya zauna ya shanye furar nan dukanta. Da ya gama na ce da shi, ya tashi ya koma inda ya fito. Ya tashi yana dingishi, ya koma cikin mutuwaren ya kwanta, inda ya fito."
.
Wani wanda ya fi kowa tsoro a cikin mutanen da ke sauraron labarin tsohon ya ce.
"Tsakani da Allah Baba, idan ni ne na ga haka, ko miliyan dari za a ba ni daga ranar na gama gadin mutuware har abada." Tsohon ya bushe
da dariya a wancan lokacin ya ce.
.
"Ka bar mutum da aikinshi kawai......... ai aikin wani wani sai kallo da ma." Jin wadannan labarai da Kallamu maigadi yake bayarwa suna matukar birge mutane, domin kuwa koda a ce karya ne ansani kowa ne cewar tsohon yana yin namijin kokari.
.
Domin kuwa shi kadai yake kwana a mutuwaren, wacce aka kebe ta a can karshen asibitin a cikin wasu dogayen shuke-shuke. Koda rana ba kowa yake so ya tunkarar wajen ba, to ballantana kuma a ce da daddare, mutum daya ya kwana shi kadai a wajen. Idan ba a cewa Kallamu maigadin mutuware jarumin tsoho ba to me ya dace kuwa a kira
shi?
....
Ai ko yaci sunansa
In Allah ya yarda anfara kenan
Its Shuraih 99%

Friday, 28 December 2018

ABOKAI littafi na biyu 2 part 2

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 2
.
"Kikkirrkirrrrkirr......"
Sautin karar bude kofan dakin ya katse masa tunani, lokaci daya ya mike ya dubi kofan dakin yana mai tu'ajjibi
.
"Waye wannan" Aliyu ya fadi cikin siririyar muryarsa
"Ubankane" Audu ya bashi Amsa yayin da suka shigo cikin dakin
A rude Aliyu ya dubesu duk da baya iya ganin fuskokinsu da abubuwan dake hannunsu amma yaaji ajikinsa ba mutanen kwarai bane
Tunani ya fara akan yadda akai har suka shigo dakin shi da kansa ya kulle kofan dakin ta waje sa'annan ya shigo ta taga, itama tagar ya garkameta
.
"Ya akayi kuka shigo mana daki" Aliyu ya tambaya cikin kakkausar murya
Silli yayi yar karamar dariya yace "fasa kwadon mukai"
"To in fasa kwadon kukai me yasa banji kara ba yayin dakuke kokarin fasawa" Aliyu ya sake tambaya
"Mun sanyawa bindigunmu salansa ce ta yadda ko kai muka harbe ba za'aji karan sauti ba, da hakane muka bazge kwadon" Audu ya fadi yana hasko bindigar dake hannunsa da tocila
.
Lokaci daya Aliyu ya razana sakamakon ganin abunda bai saba gani ba,
"Me mukai maku dun Allah kada ku cutar da mu"
"Ba ku mana komai ba,hakanan muddin kuka bi umarnin mu to zamu rabu lafiya, in kuma aka samu akasin haka, Alburusan bindigata a shirye suke da kasa tsere"Audu ya fadi yana jujjuya bindigarsa
Ya dago kai ya dubi siririn razanannen saurayin dake gabansa a hankali ya tako izuwa gaban saurayin, ya yunkura da nufin ya wuce gaba don ya iski gadon da su haidar ke kwance, kwatsam Aliyu ya sha gabansa yace "dun Allah kada ku cutar da su,domin kuwa sune rayuwata"
.
Audu ya dago kai ya dubi Aliyu ransa a bace yace "dan samari ka gaggauta cire hannunka daga jikina sannan ka matsa min a hanya kafin hushina ya tabbata akanka,"
Silli ya matso kusa da Audu yace "Audu inajin mu kyalesa kawai muyi aikin dake gabanmu domin kuwa lokaci yana dada karatowa"
.
Audu ya dubi silli kana ya dubi Aliyu yace "ok" yana gama fadi ya yunkura da nufin ya wuce amma sai Aliyu yaki matsa masa daga hanya, hakanne ya harzuka dan ta'adda Audu cikin fushi ya daki Aliyu da kotar bindigarsa a tsakiyan ka
.
Kakkarfan Ihu mai kara Aliyu ya saki gami da dafe kansa sannan ya fadi a kasa ko kwakkwaran motsi bai yi
.
Ansakuwwar karar ihun Aliyune ya farkar da dukkan daliban dakin daga barci,
A firgice Jibrin,haidar,hasan da mansir suka farka daga daddadan barcin da su ke, cikin razana suka dubi gabansu,
Anan sukai arba da abun da ya yi matukar tayar masu da hankali, Aliyu suka hango a kwance magashiyan kansa na bulbulo da jini,
"Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'uun" haidar ya fadi lokacin da ya sauko daga kan gadon da suke kwance
"Aliyu me ya sameka" jibrin ya fadi cikin muryan kuka lokaci guda abokan suka ruga don su isa inda Abokin nasu ke kwance, tsananin tashin hankalin da suka tsinci kansu a ciki shine ya makantar da su ga ganin shedanun yan ta'addan dake tsaye a gefen Aliyu,
.
Suna isa inda Aliyu yake kwance suka zube a kas jibrin yayi sauri ya tallafo kan Aliyu dake bulbulo da jini, yana kuka yace "haba Aboki ka tashi mana kada ka tafi ka barmu"
.
Cikin zafin nama haidar ya yanki wani gefe na rigar dake jikinsa ya nade kan Aliyu da shi,
Kalubale na farko kenan da Abokan suka taba tsintar kansu ciki, zuciyoyinsu na dukan tara-tara, hankulansu inyai dubu ya tashi,idanuwansu babu abunda suke sai bulbulo da kwalla,
Babu abunda ya kara tayar masu da hankali sai daukewar numfashin Aliyu, mansir ya kasa kunnensa a hancin Aliyu don jin ko yana numfashi, koda ya tabbatar baya numfashi sai ya dago kansa idanuwansa na zubda hawaye yana cewa "kada kai mana haka Aboki, dun girman Allah ka tashi,ya kake son muyi aboki" yana gama fadin hakan ya kifa kansa a tumbin Aliyu
.
Haidar,hassan da jibrin suka runga sumbatu suna kiran sunan Abokin nasu koda zai tashi,,,,
"Ai bazai taba tashi ba, domin kuwa yayi doguwan bacci wanda bazai taba farkawa, dama kun dena bawa kanku wahala kun mike mun wuce"
Kwatsam Abokan suka tsinkayi wata murya mara dadin saurare tana fadin haka,
Lokaci guda Abokan suka kai dubansu ga wurin da muryan ta fito inda sukai arba da yan ta'addan biyu, suna rike da dogayen bindigu
******========******
"Boys! Boys!! Boys!!! wake up, chidinma! Samson!! Abubakar!!! Habib!!! Steven!ismail,fahad, abeg wake up"
Tsorataccen matashin saurayin ya fadi yana duban daliban dake kwance cikin dakin,
A wurin daliban kuwa ko su san yanayi, sai ma gyara kwanciya da wasu daga cikinsu sukayi
Jagwa ya dubi aba yawo yace "Aba yawo kaga yan iskan yara harda gyara kwanciya, inaga sai mun aiwatar wa dayansu tukun"
"A'a jagwa kada ka fara in baso kake asirinmu ya tonu ba, " aba yawo ya fada yana kusantar wurin da daliban ke kwance yana zuwa wurin ya sa tafkeken hannunsa ya shararawa daya daga cikin daliban tafi a baya,
.
A razane dalibin ya farka yana mai kurma ihu sakamakon zafin daya ziyarci bayansa,
A haka aba yawo ya runga bin daliban yana tashinsu ta hanyar sharara masu tafi,,,,
,,,,,,,
Dalibai ne da yawansu bazai wuce goma ba a tsastsaye sun takure kansu a wuri guda, yawancinsu suna sanye ne da guntayen wanduna da fararen singileti, kallo daya zakaiwa daliban ka tsinci tsoro karara shimfide akan fuskokinsu,
.
Yan ta'addan biyu Jagwa da Aba yawo suna tsaye a gaban daliban, bakin bindigoginsu na fuskantar daliban,
"Ku wuce mu tafi" jagwa ya fada yana yatsina fuska
Cikin tsoro daliban suka fara matsawa suna nufar kofan dakin aba yawo ya daka masu tsawa yace "kai kui sauri mana, kada ku bata mana lokac....."
Karar ihun da ya ziyarci kunnuwan dan ta'addan ne ya katse Maganar tasa,
.
"Ihun me waye haka" Aba yawo ya fadi yana kallon jagwa
Jagwa ya yatsina fuska yace "inajin ko wani ne yayi taurin kai su kuma su Audu suka harbesa, kai ka san halin Audu baya da hakuri"
"To ai kuwa ya bata mana aiki dun karar ihunnan babu inda bai ansa ba a makarantar nan "
"Kai dan ubanku baza kui sauri ku fice daga dakin nan ba" jagwa ya fada yana dumfarar kofan dakin
.
Agurguje daliban suka karisa fita daga dakin,
Zancigaba

Monday, 24 December 2018

ABOKAI littafi na biyu 2 part 1

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 1
.
Dare ne mai dauke da sassanyar iska, dake busowa ta jikin bishiyoyin da suka mamaye Dajin, Dajin yayi tsit baka jin motsin kowa sai hargowan iska da kukan tsuntsaye , gamida kukan kananun kwari
.
Doguwar mota trela mai tayoyi goma [ten tyre], ta faka a cikin kungurmin dajin mai yanayin ban tsoro,
.
Direban motar ya fito daga cikin motar yana sanye da bakar rigar sanyi, ya kifa hula hana salla a kansa,
Bayan yan dube-duben da direban yayi sai ya koma cikin motar,
.
Bayan shudewan lokuta kalilan sai mutane hudu suka diddirgo daga cikin motan, direban shine a karshe
daya daga cikin mutanen yace "kai silli futo mana da kayan aiki,"
Wanda aka kira da silli ya koma cikin motar,
Izan ka dubi mutanennan zaka ga ba wasu bane illa, JAGWA,AUDU da ABA YAWO sai kuma direban motar,
Silli ya sauko daga kan motar hannunsa rike da jibgegiyar akwatin karfe, ya damfare akwatin da kasa, yace "ga kayan na kawo audu"
Audu yayi murmushi wacce tafi kama da kuka, ya sunkuyo ya kama murufin akwatin ya budeta
.
Dogayen bindigogine kirar AK 47 maqire a cikin akwatin, Audu yakai hannu yana shafa bindigogin, ya karkata bakinsa sannan ya bushe da dariyar mugunta sautin dariyar ta amsa a cikin dajin tamkar a ansakuwwa
.
Jagwa ya sunkuyo ya debi bindigu uku, ya mika wa Aba yawo daya, dayan kuma ya mikawa Silli, ya dubi audu yace "muje"
Audu ya dau bindiga daya ya tokare bakinta a sama, yace "dafatan kun dau hanyar da kyau yadda yanzu ba za mu manta taba"
"Haba Audu Sati daya fa muka dauka muna yin shirinnan ai babu inda muka manta don gaba daya Taswirar hanyar da ta makarantar gamida ta eriyar a kaina suke" Silli ya fadi yana kokarin rataya bindigar a kafadarsa
.
Gajeruwan tafiya ce ta kaisu ga riskan katangar makarantar Government College keffi, suka kariso jikin katangar da bata wuce kamu goma ba, sukai cirko cirko silli ya fiddo wata takarda daga cikin Aljihunsa, ya ajjiye a kasa sannan ya haska takardan da yar karaman tocila mai karamin haske, yace "wannan shine taswirar makarantar gaba daya, zamu shiga makarantar ta katangannan" ya nuna wani gefe a jikin taswirar sannan ya cigaba "hostel din makarantar guda Shida ne, dukkan su suna wurare daban daban, a tsarin da mukai hostel biyune zamu kama, dun haka muna shiga makarantar ta nan zamu fara cin karo da hostel din Gongola house, ta kanta zamu fara , bayan mun kame dukka daliban hostel din jagwa da aba yawo zasu iza keyarsu wurin da motarmu take, ni da kai " ya nuna audu "sai mu wuce Benue house mu kama daliban hostel din duka, sai mu hadu a wurin da muka faka motarmu,,,"
Silli ya karashe bayanin yana duban fuskan Audu sannan ya dau taswirar ya jefeta cikin aljihu,
.
"Kace babu masu gadi a makarantar" jagwa ya tambayi Silli
Silli yayi wata fatalwar murmushi wacce ta kara fidda munin fuskarsa yace "babu masu gadi a makarantar, imma da su ai saimu kawar da yayan banza, jikokin fir'auna"
.
Yan ta'addan su hudu suka haura katangar makarantar inda suka fada cikin surkukin daji mai duhu a cikin dajin sukai ta tafiya har suka iso gaban Hostel din Gongola house
.
Fasalin Ginin da a kaiwa hostel din fasalin ginin zamanin da ne, an shafe bangon hostel din shudin fenti, hasken farin wata ya haskaka hostel din ,
.
Damar da yan ta'addan suka samu kenan wurin karewa hostel din kallo,lokaci daya yan ta'addan hudu suka tallafo bindigoginsu suka daidaita su a hannuwansu cikin sanda suka nufi dakunan kwanan daliban,
Jagwa da Aba yawo suka durfafi shashin dama yayin da Silli da Audu suka nufi shashin Hagu
"Yana ga dakunan a garkame da manyan kwaduna" Audu ya fadi yana duban dakunan hostel din dake garkame da manyan kwaduna Silli ya fiddo da salansan bindiga daga aljihunsa yace "ai daliban ne suke kulle kansu"
.
"Dole sai de mu balla kwadunan " Audu ya fadi yana kokarin daura salansan bindiga a bakin bindigarsa,
Silli ya saita bakin bindigarsa a kan jibgegen kwadon dake sakale a jikin kofan dake gabansu,
Sannan ya saki ma kwadon wuta,
.
Ba shiri jibgegen kwadon ya balle, silli ya sanya bushasshen hannunsa dake boye cikin safa ya cire kwadon daga jikin kofar yai wurgi da shi gefe daya,
Ya kama marikin kofan ya bude dakin, sannan ya kutsa kai ciki,
.....
Jagwa da Aba yawo suka iso bakin wani daki, se dai wannan dakin babu kwado a jikinsa, jagwa ya kama marikin kofan dakin yaja da zummar ya bude amma sai kofan taki buduwa hakan ya tabbatar masu ta ciki aka kulle dakin
.
Cikin takaici aba yawo ya dubi jagwa yace "yanzu ya kenan zamuyi tunda yan iskan daliban nan sun kulle kofan ta ciki"
Jagwa ya danyi guntun nazari kafin yace "matsa min na jarraba wata dabara"
.
Aba yawo ya matsa daga bakin kofan dakin jagwa ya matso kusa, ya fara dukan kofan da hannu, kofan ta fara bada wani sauti sakamakon dukan da jagwa keyi mata,
.
"Who is that" wata murya ta fadi daga cikin dakin
Maimakon jagwa yayi magana sai ya cigaba da bubbuga kofan, "a'a who is that na, person dey sleep you come de distrurb him" aka sake fadi karo na biyu daga cikin dakin
Jagwa ya wage wawakeken bakinsa yace "kai open this door, you come dey sleep you no know weting dey happen "
.
"Cai what, ok but who are you" na cikin dakin ya tambaya
"Eh see this guy u dey ask me who I be, if you no open dis door toh you na go die there" jagwa ya bashi amsa
..
"Ok lemme open" aka fadi daga cikin dakin, kofan dakin ya fara motsi alamar ana kokarin budewa
.
Kofan dakinne ya bude wanwar, jagwa da aba yawo sukai arba da matashin saurayin daya bude kofan yana tsaye a bakin kofan babu komai a jikinsa face gajeruwan wandon kwallo, saurayin da bai kula da abubuwan dake hannun yan ta'addan ba yayi hamma gami da mika yace "ya bros wetin dey happen" ya fada cikin magagin bacci
.
Lokaci daya fuskan saurayin ya canja daga yanayin magagin bacci zuwa tsananin firgici, idanuwansa A bubbude ya daga hannunsa sama, bakin sa na kakkarwa jikinsa na bari tamkar mazari, "abeg bros don't kill me" matashin saurayin ya fadi lokacin da tsinin bakin bindigar jagwa ya kusanci Tumbinsa,
.
Aba yawo yayi masa alamar yai shiru, a razane saurayin ya dora hannunsa daya akan bakinsa ya tsuguna a kas
Jagwa yayi masa inkiya da bakin bindigar akan su koma cikin dakin,
Matashin saurayin da yan ta'addan suka shige cikin dakin
.......
Yana kwance kan katifarsu ga sauran abokannasa a gefe suna sharar barci, fuskarsa na kallon silin dakin din yana murmushi a zahiri in ka gansa zakai tsammanin Silin dakin yake kallo amma abun bahaka yake ba a wurin Aliyu SARKIN DARIYA,
Tunanin Abar kaunarsa yake, yana mai zumudin gobe tayi, a yadda ya kudirta a ransa ba zai taba runtsawa ba har safiyar gobe, tun da Aliyu yake A rayuwarsa bai taba tsintar kansa a lambun farin ciki, mai cike da kayan Annashwa.....
"Kikkirrkirrrrkirr......"
Sautin karar bude kofan dakin ya katse masa tunani, lokaci daya ya mike ya dubi kofan dakin....
.....
Zan cigaba

Tuesday, 18 December 2018

ABOKAI littafi na daya 1 part 12

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 12
.
"Ok na fahimce ka sai yanzu na gano abin da ka hango maganarka dutse daka ce hankulan mutanen Nijeriya sai ya tashi, to amma izan na dauko maganarka ta farko kace Gobe, kana nufin yau da dare kenan zamu fita aikin ko kaka"
Jagwa ya fada yana kokarin sake zaro wata sigarin
.
Audu ya mike tsaye ya zaro karamar bindigarsa wacce ako wanne lokaci take soke a kugunsa, ya kafa bakin bindigar a lebbansa sannan ya juya akalar bindigar ta kalli bakin kofar dakin,
"Al'umman Nijeriya,Gwamnatin Nijeriya bala'I bisa kanku, Masifa bisa kanku babu mahalukin da zai kareku daga wannan masifar da ta tunkaro ku," Audu na gama fadin hakan ya fice daga dakin
****** ****
Masoya suka ce Soyayya ruwan zumace kauna ruwan rakece, hakika maganarsu ta tabbata akan Aliyu da zara'u,
Zara'u ta tsinci kanta cikin wawakeken kogin soyayya, inda ta runga ninkaya cikin Annashwa,
Tun daga ranar da zara'u ta furta wa Aliyu kalmar Kauna, suka fara gina soyayyarsu bisa koyarwan Addini, suna kula da junansu sosai, ya kasance kusan kullum Aliyu,haidar,mansir,jibrin da hasan a benue market suke wuni ,
.
Zara'u ta yi farin ciki ainun da samun masoyi mai matukar kaunarta, hade da manyan yayu hudu masu kula da ita,
Tana jin dadin kasancewa cikin su, sabida akowanne lokaci cikin fara'a suke, sukegusar mata da bakin cikinta su maye gurbinsa da farin ciki, suke share mata hawayenta a duk sa'ilin da bukatar hakan ta taso, sun dauketa tamkar yar'uwarsu ta jini, a da can suna kiran kansu da Abokai biyar, amma yanzu kiran kansu suke da YAN UWA shida,
,
A dan kankanin zaman da zara'u tayi da abokan ta fahimci cewa igiyar abotarsu mai karfice, sannan ta san halayen kowa daga cikinsu, gami da tarihinsu,
Kaman kullum yau ma Abokan ne tare da zara'u a tsaye a bakim gate din makarantar, haidar ya tare acaba guda biyu, ya juyo ya dubi zara'u wacce ta kafe Aliyu da idanu, shima Aliyu idanunsa akan ta suke baya kiftawa,
"Kanwarmu zo ki hau ku tafi, ki bar mayen soyayyar nan,"
Haidar ya fada
Zara'u tayi murmushi ta juyo ta dubi manyan yayyunata tace da su, "nagode sosai yan'uwana, sai gobe izan Allah ya kaimu"
Tana gama fadin hakan ta juya ta nufi wurin da babur din yake har ta kai wurin sai ta tsaya ta, ko ba'a fada mata ba tasan idanuwan Aliyu akanta suke
Zara'u ta juyo ta fara takawa a hankali har ta karisa wurin abokan mansir ne yace "me ya faru kuma kika da wo ko kinyi mantuwane a benue market naje na dauko maki"
"Magana zan da sahibina"
Zara'u ta fadi tana kallon Aliyu
Cikim zumudi Aliyu ya kariso gabanta murmushi dauke akan fuskarsa,
"Dama so nake na fadamaka, gobe zan yi maka babbar kyauta, wacce baka taba tsammani ba,"
Zara'u ta fadi tana wasa da yatsunta , Aliyu yayi murmushi har fararen hakwaransa suka bayyana yace "kice gobe nayi kyakkyawar tanaji kenan,"
Ta gyada masa kai , jibrin ya kariso wajen yace "to sarkin masoya ai kabarta ta tafi gida ko, ko so kake ai wa kanwarmu fada a gida"
"To zara'u sai goben in Allah ya kaimu" aliyu ya fada,
Jibrin,haidar,hasan da mansir suka hada baki lokaci daya suka ce "to Allah ya kiyaye hanya yar karamar kanwarmu,"
"Ameeen" ta fadi daga nan ta hau babur din . Mai babur din daya gaji da tsayuwa ya tayar sannan ya bashi wuta, shi ma dayan mai babur din daya lodi, kulunan abincin ya bisu a baya.
*********
Irin zunzurutun Zumudin zuwan gobe da Aliyu yake bata faduwa, ya gagara sukuni Allah Allah yake gobe tayi don yaga irin kyautar da masoyiyar tasa zata bashi,
.
Babu mutumin da zai arba da Aliyu a wannan rana bai fahimci cewa yana cikin farin ciki ba, A ranar rawa ya runga yi gami da tsalle,
Ya addabi sauran abokan nasa da surutu yana fadin "kai soyayya da dadi abokai ya kamata kuma ku fara ko don ku dandani irin dadin dake cikinta wanda ya dare Zuma dadi"
" duk wanda baya soyayya bakaramin kwaransa akai ba"
"Masoyiyata ina jiranki, ina fa sonki, jinin jikina nakine masoyiyata, jinin jikinki nawane masoyiyata, sonki yai mani kamu a zuciyata, ya ratsa cikin jini da bargon jikina,"
.
"Ka ga Aliyu don Allah kai mana shiru muyi barci mana, ka duba agogo ka gani yanzu karfe Goman dare ne fa, amma duk kabi ka damemu da waka, in da gaske begen masoyiyarkan kake me yasa baka bita gidansu ba" Jibrin ya fadi yana gyara kwanciyarsa
"To naji nayi shiru, amma fa ni bazan iya barci ba," Aliyu ya bashi amsa
Jibrin yayi tsaki ya dubi haidar,mansir da hasan wayanda sukai nisa cikin bacci yace
"Can ta matse maka mudai kam munyi Zaria"
........
Abokai da yan uwa ku gafarceni, littafi na daya ya kare a nan,
Shin yan ta'addan zasu sami nasarar cika kudirinsu
.
Yaya alakar Abokan zai kasance daga karshe,
Wani kyauta zara'u ke kokarin baiwa Aliyu
*
Ni Marubucin littafin SHURAIH USMAN nace sai mu tara a littafi na biyu don jin cigaban wanga labari a wani loton
.

ABOKAI littafi na daya 1 part 11

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 11
.
******
Labarin kama dan ta'adda Sidi kashe babba kashe yaro ya karade gaba daya Ilahirin Garin Nigeria da kewayenta, inda gidajen watsa labarai da jaridu gami da kafar sadarwa sukai ta yayata labarin,
.
Dogon dakine da ya tsaru iya tsaruwa , a tsakiyar dakin an girke wani dogon teburi na gilashi daya kusan mamaye dakin,
An zagaye teburin gilashin da wasu kyawawan kujeru masu matukar laushi,
.
Kwamishinan yan sanda Abdullahi makeri ne sanye cikin kayan Gida yana zaune akan daya daga cikin kujerun da sukai wa teburin kawanya fuskarsa na duban wani mutum dake zaune a gefensa
.
Mutumin daya kasance fari yana da kiba ga katuwar tumbi nan daya ajje tamkar mai ciki, yana sanye da fararen kaya zariya ya yafa babbar riga akanta,
,
Lokaci daya farin mutumin da shekarunsa baza su wuce hamsin da wani abu ba ya juya da dubansa ga karshen dogon dakin, cikin sauri shima kwamishinan yan sanda Abdullahi makeri yai duba izuwa karshen dogon dakin inda wani makeken talabijin ke kafe a jikin bangon dakin,
.
Wata kyakkyawar matace cikin shigan hausawa aka nuno cikin talabijin din tana cewa
"A jiya ne talata yan sandan garin kano bisa jagorancin mataimakin kwamishina kamalu suka kai harin sumame ga yan ta'addan nan da suka addabi Nijeriya a wani hotel mai suna city hotel dake karamar hukumar warawa inda sukayi mummunan artabo da yan ta'addan, daga karshe yan sanda sukai nasarar harbin dan ta'adda daya, suka kuma kame shugaban yan ta'addan mai suna SIDI kashe babba kashe yaro,
A tattaunawar da muka yi da Acp kamalu shugaban rundunar da suka kai sumamen ya shaida mana cewa daya daga cikin yan leken asirin da suka barbaza a cikin garin kano ne ya sanar da su maboyar yan ta'addan, basuyi kasa a guiwa ba ya demi jami'ai suka nufi hotel din , Acp kamalu ya kara da cewa jami'I daya ne yaji Rauni a kafadarsa yayin artabonsu da yan ta'addan kuma iyanzu yana nan ana kula da shi a asibiti,
Shi kuma shugaban yan ta'addan yana nan a tsare a wajen yan sanda duka duka dai anan muka kawo maku karshen labaran namu na yau...."
.
Farin mutumin yayi gyaran murya kana ya dubi kwamishina yace "gaisheku jami'an mu, kunyi aiki mai kyau muna alfahari daku"
"Mun gode yallabai" kwamishina ya fadi yana murmushi
"Wani asibiti kuka kai Jami'in da aka harbesa a kafada ,"farin mutumin da aka kira da yallabai ya bukata
"General hospital sir"
.
"Ok, bazan......."
Maganar tasa ta katse a sakamakon karar ansakuwwar wayarsa data karade dakin,
Farin mutumin ya saka hannu cikin burmemiyar babbar rigarsa ya ciro wayar , kai tsaye ya kara wayar a kunnensa daga can bangaren aka ce
"Assalamu'alaika you're excellency Abubakar Bappa the governor of kano state "
"Wa'alaikassalam you're excellency Umar bahaje the President of Nigeria"
Farin mutumin da sai yanzu na fahimci shine Gwamnan kano ya fadi yana murmushi
"Na samu labarin artabun da jami'an mu sukai da yan ta'addan nan , dafatan kun baiwa jami'in da yaji raunin kyakkywan kulawa"
Aka fadi daga can bangaren
"Eh yallabai yanzu haka ma yana cikin koshin lafiya" gwamna Abubakar bappa ya fadi
"Nan da yan wasu kwanaki zan shigo Nijeriya, sannan ina son dan ta'addan da aka kame din nan kulawarsa ta koma hannun Sojoji, saboda gudun mishkila"
.
"Yallabai me zai sa ba zamu barshi a wajen yan sanda ba tunda yanzu haka yana nan suna gana masa azaba iri iri, don ya fadi wani ta'addanci ne suke shirin aiwatarwa nan gaba, sannan su waye ke taimaka masu"
"Ok kuyi duk abun da kuke ganin yafi dacewa, sai anjima ABOKI na"
"Yauwa bahaje sai anjima"
Gwamna Abubakar bappa ya fadi kana ya mayar da wayar cikin aljihunsa fuskarsa cike da murmushi
Ya dubi kwamishina yace "ku cigaba da tsare dan ta'addan, zan neme ka zuwa wani lokacin, menene sunan dan sandan da yaji raunin ma"
"Mudassir," kwamishina ya basa amsa
Lokaci guda gwamna ya mike tsaye ya gyara burgujejiyar babbar rigarsa "a bashi dubu hamsin hade da hutun tsawon lokaci har sai ya warke"
Ya fada yayin da ya soma tafiya yana dumfarar kofar fita daga dogon dakin
"Ok sir"
*****=========*******
Garin Kaduna,
"Audu yanzu me ya kamata muyi,duk yaran da oga ya bukata na kawo su amma kuma Oga yanzu yana can hannun yan sanda"
Jagwa ya fadi yana kallon Audu wanda Ransa ke matukar bace,
Audu yayi ihu gamida karaji ya daga hannunsa sama ya doki karamin teburin gilashin dake gabansa wanda akai musamman don ajje abinci da abun sha,
.
Karar tarwatsewar teburin gilashin gami da ihun da Audu yayi ne ya sanya mutanen dake Harabar Gidan suka durfafo dakin da su Audu suke cikin Gudu,tafiyar kankanin lokaci ce ta sadasu da dakin gaba dayansu suka zazzaro kananun bindigogi daga kugunsu suka afka cikin dakin,
.
Rundunan Mutanen da akalla sun kai Goma sukai kasake da bindigun a hannunsu sai kalle kalle suke, daya daga cikin mutanen ne yace "yallabai ca muke ko wani abunne ya faru da muka ji ihu da kuma karar fashewar gilashi "
.
"Babu komai ku koma kan bakin aikinku" jagwa ya fadi yana kokarin ciro wani abu cikin aljihunsa
Fakitin sigari ya ciro ya zare kara daya ya kafeta a labbansa, kana ya ciro kyastu ya ya kunna ma sigarin wuta,
"Yanzu me ya kamata muyi don ganin oga ya fito" jagwa ya fadi yana feso hayaki ta hanci ta baki
.
"Abun da nake tunani kenan don kunsan in babu oga to babu ta yadda aikinmu zai yiwu" Aba yawo dake can kuryan bango ya fadi
Audu yayi murmushin kuna sannan yace "tabbas yan sandan Nijeriya sun tsokano wa kansu tsuliyan dodo, sun taro babbar masifar da bata da karshe tun da har suka kama mana shugaba sa'annan suka kashe dan'uwanmu, gobe goben nan mutanen Nijeriya zasu fara yi wa gwamnati bore, domin kuwa a gobe ne mutane zasu farka da mummunan labari wacce zata tayar da hankulansu"
.
"Ban fa fahimci maganar kannan ba, shin me zamu aikata da har zai tayar da hankulan mutanen Nijeriya"
Aba yawo ya fadi yana kokarin matsowa kusa da Audu,
Audu ya fashe da dariyar kyeta yana duban jagwa da aba yawo yace "mummunan Tuggu na shirya wacce zatai silar abubuwa da dama ciki kuwa har da asarar rayuka"
"Wacce iriyar Tuggu kuma" jagwa ya bukata
"GARKUWA, (kidnapping)" audu ya bashi amsa
"Wa zamu yi garkuwa da shi, mr president ko wa," jagwa ya sake tambayar audu yana zukan guntun sigarin dake hannunsa
"Government College Keffi, daliban makarantan gaba dayansu zamu sace, "
.
"To babban magana, lallai kuwa da babban aiki gabanmu amma kuma kake cewa gobe kasan akalla sai mun shafe sati muna shirya yadda zamuyi mu shiga makarantar"
Aba yawo ya fada
Jagwa yayi murmushi ya yadda guntun ragowar sigarin dake hannunsa akan Tiles din dakin yace "duk bama wannan ba, dakwai makarantu bila'adadin a Nijeriya me yasa ka zabi Government College keffi a cikinsu"
.
Audu ya sake barkewa da dariya wacce tafi kama da kukan jaki a karo na biyu kana yace "gaba daya jihohin Nijeriya talatin da shida , ta hadu ne a makarantar, domin kuwa kowacce jiha tana da dalibi a makarantar"
"Kayi mani gwari gwari kasan ban cika gane hausan nan taka ba" jagwa ya bukata
Audu yayi murmushi sannan yace "ina nufin bawai mutanen jihar nasarawa ne kadai a makarantar ba, akwai dalibai daga sassan nijeriya, wayanda karatu ne ya kawosu garin, kasan makarantar kwana ce"
.
"Ok na fahimce ka sai yanzu na gano abin da ka hango maganarka dutse daka ce hankulan mutanen Nijeriya sai ya tashi, to amma izan na dauko maganarka ta farko kace Gobe, kana nufin yau da dare kenan zamu fita aikin ko kaka"
Jagwa ya fada yana kokarin sake zaro wata sigarin
.

Sunday, 9 December 2018

ABOKAI littafi na Daya 1 na Shuraih Usman part 10

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 10
.
"Anya Aliyu zai zo kuwa ga shi har Hudu tayi "
Zara'u ce ke fadin hakan cikin zuciyarta, Tun dazu ta idar da Saida Abincinta a iya saninta karfe Hudu, bai taba yi mata a makarantar ba, uku da wani abu take barin makarantar,
Cikin kasala ta mike tsaye ta isa wurin kulolin abin cin ta fara harhada kayayyakin ta, har ta gama har hadawa zuciyanta na muradin ganin Aliyu bata taba jin tana zumudin ganin sa ba irin yau don yau ya kasaance tamkar babbar ranace gareta.
.
Ranar da zata bayyana masa abun da ke kunshe cikin zuciyarta wanda da can kunya ya hanata fadi,
"Ke zara'u me zai hana ki dan tsaya kiyi jiransa zuwa hudu da rabi indai bai zo bane sai ki tafi gobe kwa hadu"
Wani sashi daga cikin zuciyarta ya sanar da ita, lokaci guda tayi na'am da shawarar da barin zuciyartar ta bata, bayan ta gama kikkimtsa kayanta waje guda sai ta koma ta zauna akan dogon bencin dake bayan ta
.....
Kamar daga sama sai zara'u ta jiyo muryan Haidar yana doka ma mutanen wurin sallama cikin barkwanci,
Wata jibgegiyar tsohuwa mai nanannen hanci ne ta amsa sallamar kana tace "a'a abokai yau kam kun makara dan tuni munci kasuwa yanzu haka shirin rufe kasuwar muke"
.
"Ayya yar tsohowa ai muma yau ba Kasuwar mukazo ci ba, wacce muka saba zuwa wajenta tun da can yanzuma wurinta muka zo" Mansir ya fadi cikin barkwanci yana kallon yar tsohuwar
.
Wata bakar mata mai Jiki bazata wuce shekaru talatin ba dake gefe tana Suyan doya ta juyo ta kallesu tace "tab to kun makaro don tuni wacce kuka zo wurintar ta wuce Gida"
"Kenan har yanzu doya bai kare ba, to ma ta ya za'ai ya kare alhalin mai doyar tana ehm ehem ehmmm"
Jibrin yafadi yana murmushi,
"Kai kunga banason shekiyanci dun Allah ku wuce wajenta ga zara'un can tana shirin Tashi"
Bakar matar ta fadi
Dukkansu sukayi dariya suka nufi wurin da zara'u take, inda sabo sun saba a duk lokacin da suka zo benue market sai sunyi barkwanci da matan dake wajen, musamman ma maman Ladi,
.
Wani irin farin ciki take ji mara misaltuwa lokaci daya ta tsinci kanta tana mai murmushi
Su janet dake gefe suna kula da yanayinta suka dan matso kusa da ita janet ta dafa kafadarta tace
"Ga su Aliyun sunzo don nasan su kike jira inba haka ba da tun dazu kin wuce Gida"
.
"Assalamu'alaiki hasken Idaniyata" Aliyu ne ya rangada sallama cikin murya mai sanyi,dadi hade kwantarwa masoyi rai,
Cikin fara'a ta dago kai ta dubesu su Biyar ne kamar yadda ta sansu
Ta amsa sallamar Cikin daddadan murya wadda har tafi na Aliyu dadi,
Janet ce ta mike zumbur ta dubi Aliyu tace
"Ai gwamma da kazo Tun dazu take jiranka, "
"Da gaske kike " Abokan biyar suka bukata cikin hade baki,
"Hmm. To in ba Aliyu take jira ba wa take jira ita da take tashi karfe uku amma gashi yau har hudu da rabi , to me take jira"
Dayan budurwar tafadi tana kallon zara'u wacce ta ke kallon kasa
Janet tace "barta kawai blessing, aliyu zara'u tana sonka fa kawai dai kunya ce ta hanata........."
.
"Ke yi mana shiru da Allah" zara'u ta katseta da fadin hakan,
Ta mike tsaye ta dubi Aliyu shi da Abokansa tace "Aliyu"
Cikin wata iriyar murya ta kira sunan nasa
"Na'am zara'u"
Ya amsa cikin farinciki da doki na jin abun da zata fadamasa, yasan dai yau dolenta ta kauda kunya gefe guda ta fadi masa abun da ke ranta game da shi
.
Zara'u ta jinjina kai, ta daga kwayar idanunta ta kalli idanun Aliyu wanda yake kafe a kanta
"Aliyu ayau zan kauda kunya na fada maka matsayinka a zuciyata, Aliyu nasan cewa kana matukar sona, kana matukar kishina, ka na Zumudin Ganina,to kasani nima ina Sonka, babu mutumin dana ke zumudin gani sama da kai, a duk lokacin da zan rabu da kai na kanji ba dadi, na kanji dama nayi shekaru dakai kana fada mani dadadan kalamanka, I NA SON KA aliyu"
.
Tsalle Aliyu yayi cikin murna suma abokan nasa suka mara masa baya suka runga ayayyaku wanda suka kirashi da MURNA ko celebration,
Tsirarun dalibai da mata masu saida abinci a benue market sai dariya suke don in da sabo to sun saba da ganin abokan a irin wannan yanayi a duk lokacin da suke farin ciki,,
.
"Maman jona wai me ya samu yarannan haka suke ta tsalle tsalle suna yi wa mutane ihu" mama ladi ta tambayi wata mata kirista dake gefenta tana saida fanke,
"Ba zai wuci akan yarinyar can bace" maman jona ta fadi,
Tsaki maman ladi tayi kana tace "aiko anyi yan iskan yara"
...
zara'u taji wani sanyi ya ziyarci ranta nan take wani dausayin cakudadden dusar kankara ya tarwatse a zuciyarta sanyi mai ni'ima ya mamaye zuciyar gaba daya,
.
Bayan Abokan sun gama murna da jin furucin daya fito daga bakin zara'u sai suka matso gabanta, suka dubeta mansir ya yi murmushi yace
.
"a gaskiya mun yi farin ciki sosai zara da kika aminta da abokinmu kika dauke shi a matsayin saurayinki da yardar Allah wannan soyayya taku sai ta kaiku ga aure "
.
"Ameen mansir, ki sani cewa dukkan wani damuwa na Aliyu damuwar muce,bakin cikinsa bakin cikin mu ne, hakanan farin cikinsa farin cikin mu ne, daga yanzu kema kin zama wata sashe a cikinmu"
Jibrin ne yafada yana kallon zara'
.
Hassan ya matso kusa yana murmushi ya dubi zara'u yace "zara' ga Amanar Abokin mu kuma jigon farin cikinmu mai sakamu nishadi a kowanne irin yanayi, Dan Allah ki kula mana da shi kada ki sanya shi kuka, domin izan yayi kuka to muma duka sai munyi kuka"
.
Zara Wacce kanta ke duke yana kallon kasa, tun sa'in da abokan suka fara bayanin ta sadda kanta kas tana jin zantukansu
Ta dago kai a hankali tace "in Allah ya yarda ba zan taba baku kunya ba"
.
Haidar ya dubi sauran abokan nasa yace "sai muyi sauri mu kwashi kulolin nan mu wuce ..."
Batare da sun jira ya idar da maganarsa ba suka fara kwashe kuloli da sauran kayan abincin,
.
Zara'u ta mike da sauri tace dasu "da kun barsu don yanzu mai kwashewa zai zo"
.
Haidar yayi murmushi sannan yace "ki dauke mu a matsayin yayunki zara, yayu har hudu baza su iya barin karamar kanwarsu ta kashe kudinta wurin daukan wayannan kananun kayan ba"
Yana gama fadin hakan ya ciccibi wata murgujejiyar kula ya aza a kansa
.
Hasan wanda ya dora yar karamar kula akansa hannunsa na dama na rike da farin roban penti, ya juyo ya dubi zara'u yace "kamar yadda aboki haidar ya fadi, daga yau kin zamo kanwarmu, agabanmu dai ba zaki sake wani aikin wahala ba,"
.
"Naji dadi gami da farin ciki da samun yan uwa hudu, da Masoyi masu jajirtacciyar zuciya ,masu burin su kauda wa kanwarsu da dukkan bakin cikin ta, ina ma da Allah ya halicceni a matsayin kanwa daga cikin dayanku" zara ta fadi cikin murya mai kashe jiki,
Dukkansu jikinsu yayi sanyi, lokaci daya suka fahimci halin da Zara take ciki,
Siraran hawayene suka fara zarya akan kyakkyawar fuskarta ta sanya hannu cikin sauri ta share,
Aliyu ya dubeta yace "Masoyiya meye kuma na kuka ai yanzu duk mun zama daya"
Yafadi cikin sigar wasa,
Mansir ya matso kusa da ita yana kokarin ture Aliyu yace "da Allah ban wuri, tun ba aje ko'ina ba har ka fara sanya mani yar kankanuwar kanwa kuka, yi shiru yar kankanuwar kanwata,ga Alawa nan na kawo maki" ya ciro chaculeti yana mika mata,
Ta mika hannu ta karba tana mai murmushi
"Amma fa kada ki baiwa wannan dan kwadayin dun nasan sai ya nemi ya sha" haidar ya fadi yana kallon Aliyu,
Lokaci na farko da Aliyu ya fara kame dariya amma duk da haka sai da ya murmusa wadda hakwaransa suka baiyana,
"Masoyiya zaki shanye kuwa ki hanani" Aliyu ya fada yana kallonta da murmushi akan fuskarsa
,
Noke hannu tayi alamun ta hana sannan tace "ai yayana yace kar na baka" cikin muryan yara tayi maganar, hakan ya sanya su duka suka kwashe da dariya har sauran matan benue market masu saida abinci dake gefe suna kallonsu wayanda abun yayi matukar basu sha'awa
Inna mai doya ta bude faffadan bakinta mai kama da kofan gari tace "ja'irar yarinya, ashe itama son Aliyun take"
.
Abokai biyar da budurwa zara suka durfafi gidan su zara' a haka sukaita hira cikin Annashwa nishadi gamida farin ciki,
Farin ciki a xuciyar zara baya faduwa, ta samu kanta cikin wani irin yanayi na farin ciki irin wadda bata taba tsintar kanta ciki ba,
*****

ABOKAI littafi na Daya 1 na Shuraih Usman part 9

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 09
.
***
Karamin wajene mai dauke da manyan bishiyu guda hudu bishiyoyin sune suka taimaka sosai wajen yiwa wurin rumfa da rassansu, na daga cikin abun dake kara wa wajen ni'ima shine daddadan iskan dake futowa ta cikin bishiyoyin da suke wurin
.
Tsirarun mutane ne a wajen suke kasuwancinsu yawancinsu matane masu saida Abunci da kayan kwalama, daga gaban wajen da dalibai suke kira da beneu market dogon bencine a girke saman kututturin itace a gaban bencin da kadan wani teburin katako ne mai dauke da manyan kuloli na abinci sai Robobin zuba abinci dake gefe cikin karamin roban penti
.
Tana zaune akan dogon bencin tayi tagumi, lokaci lokaci takan mike tsaye tayi waige waige da alama dai wani abun take nema,
Kamar ko wani lokaci yanzuma ta mike tsaye ta kai dubanta hanyar dakin kwanan dalibai tana waige waige ko idanunta zasu ci karo da Abunda take nema
!!
Wasu yan mata biyu wayanda kallo daya zakai masu ka gane ba Musulmai bane suna zaune a gefenta sun kula sosai da yanayinta hakan yasa suka dan matso kusa da ita,
"Zara, me kike lekawa ne haka tun dazu kin kasa samun sukuni sai leke leke kike"
Daga cikin matan daya ta fadi cikin gurbatacciyar hausa,
Zara tayi ajiyar zuciya ta juyo da kyakkyawar fuskarta ta dubi yan matan wayanda suke sanye da kananan riguna da fingilallun Siket tace
"Ba komai Janet"
Bakar budurwan da aka kira da jenet tace "ko dai Aliyu kike lekene"
"A'a aliyu kuma me zai sa na riga lekensa"
Zara ta fadi
"So mana," janet ta bata amsa tana duban budurwar dake gefenta
Cikin halin ko'in kula zara tace "So kuma haba waya fada maki cewa ni ina sonsa,"
Dayar budurwar tayi murmushi tace "zara kenan kina so kina kaiwa kasuwa, in bakiyi sauri kin amshi soyayyarsa ba kina ji kina gani wata zatai maki kwace"
.
Zara tayi shiru taki cewa komai ta sadda kanta kas tana Tunani a hakikanin gaskiya tana matukar Son Aliyu to amma tana jin kunyar fadamasa,
.
Tun Aliyu yana SS2 zangon karshe ya hadu da zara a benue market,
Wata rana suna dawowa daga Aji zasu wuce zuwa hostel ,
Suna tafiya suna hira cikin wasa da dariya Aliyu sai dariya yake kyakyatawa, kamar ance ya kai dubansa benue market, ya na kai dubansa benue marker yayi arba da ita tana kokarin, zuba shinkafa a roba,
yana ganinta yaji zuciyarsa ta harba, cikin kankanin lokaci wani kifiya mai dauke da dafin sonta ya soke shi a zuci,
.
Lokaci daya ya tsayar da dariyar da yake, ya tsaya cak yana kallonta,
Tana da matsakaicin tsayi gami da matsakaicin Jiki,farace amma ba sosai ba ta mallaki doguwar fuska mai dauke da kananun idanuwa hade da dogon karan hanci gami da tsukakken baki mai siraran labba wayanda ta rinesu da jan baki,
.
Tana sanye cikin doguwar riga har kasa, ta suturce jikinta da shudin hijabi har kasa,
Zuciyar Aliyu ta tafi ga zara, ya saki baki galala yana kallonta, tun da yake a rayuwarsa babu macen daya taba gani yaji kwatankwacin abun daya ji akan zara kanta, yasha arba da kyawawan mata wayanda suka dare zara kyawu kira da komai amma ko kadan basu taba burgesa ba bare har takai ga yaji yana sonsu,
Lokaci na fari da ya fara jin wani abu akan mata, lokaci na farko daya fada cikin Kogin Soyayya,
Babu abun da ya kara rikitashi sai da lebbanta suka fara motsawa, lokacin datake kokarin mikawa wani yaro canjinsa,
.
Kai tsaye ya nufi wurinta fuskarsa na kallonta idanuwansa kafe a kanta,
"Sarki ina zaka je"
Haidar ya tambaya yana kokarin bin bayansa
Aliyu wanda hankalinsa yayi gaba bai ji abunda haidar ya fada ba ya cigaba da tafiyarsa,
Da gudu haidar ya karisa wurinsa tun kafin ya isa benue market ya kama kafadarsa yace "haba Aliyu na yi maka magana yafi baki uku amma kayi biris dani"
"Yi hakuri aboki wallahi hankalina ne yayi gaba" aliyu ya fadi yana duban haidar
,
Mansir,jibrin da hasan suka kariso wajensu
"Haba malamai muna cikin tafiya kun zo kun tsaya anan alhalin kun san halin da nake ciki"
Mansir ya fada yana kallon Aliyu
Hasan ya kara da fadin "kun fa san dukkanmu yunwa ce ke hajijiya damu, kai aliyu ba dazu kai ta kukan ba'a tashi daga aji wuri ba, to gashi an tashin kuma kunzo kun tsayar damu"
Jibrin kam shiru yayi, fuskarsa babu yabo ba fallasa , ya dafe cikinsa da hannunsa na dama
Haidar ne ya yace da su "kuyi hakuri abokai Aliyu ne yayi kamu shine ya biyo kamun ni kuma na rakosa"
Jibrin yadan yamutsa fuska yace "wani irin kamu kuma"
Haidar yayi murmushi yace "Suruka ya samo mana"
Dukkansu suka zazzare idanuwa suka hada baki wajen cewa "da gaske, wacece"
Shi kansa Aliyu bai san yadda akayi har haidar ya gano sa ba to amma abun da bai sani ba shine alokacin da ya saki baki yake kallonta, haidar na kula da shi, har sanda ya nufi benue market shi yasa haidar ya bishi a baya,
.
Cikin zumudi da rawar jiki jibrin ya matso kusa da Aliyu kai kace ba shi bane dazu yayi lamo dafe da ciki, yace "aboki wace ce ne"
Aliyu yayi murmushi yana mai kallon inda zara'u take Zaune,
Dukkansu suka juya da dubansu izuwa kanta,
"Kai tubarkallah" mansir ya fadi
"Amma kayi dace Aboki" jibrin ya dora
"Shin ka sanar da ita kuwa" Hasan ya fadi
"Ya kamata muje yanzu ka sanar da ita" haidar ya fadi yana kokarin janyo Aliyu, a hankali aliyu ya zame hannunsa daga na haidar yace da su "daga ganinta bakuwa ce don ni ban taba ganin ta a nan ba to amma hakan ba shi zaisa na gagara sanar da ita Ina Son ta ba, amma ba yanzu ba ku bari sai mun zauna mun yi shiri"
.
Tun daga wannan Rana sai ya kasance a kullum Abokan biyar sai sun kaiwa benue market ziyara kuma kai tsaye wajen Zara'u suke tafiya, Aliyu yayi ta cikata da surutai, tun yanayi bata kulashi har dai ta fara Kulashi, tun bata damuwa da shi har takai ta fara damuwa da shi, ganin cewa ta saki jiki sosai da shi sai suka hadu shi da abokansa suka fada mata kudurinsa, sai dai har yau shiru kakeji , babu amsa amma Aliyu ya riga yasan cewa tana sonsa , kunya ne ya hanata furta masa
.
Aranar yau ne Zara'u ta kudurce a ranta zata sanar da Aliyu Amsar tambayarsa, ta kudurce zata kauda kunya ta fadamasa cewa ita ma tana sonsa, a iya saninta duk lokacin da aka tashi daga Aji abokan basa taba wucewa zuwa hostel har sai sun yada zango a beneu market, sun dubata
.
To amma yau sabanin kowanne rana Awa biyu kenan da tashi daga Aji amma bataji duriyan abokan ba, hakan yasa sa'I sa'I take mikewa tsaye tana leke ko zata hangosu don tana da tabbacin zuwansu
,,


ABOKAI littafi na Daya 1 na Shuraih Usman part 8

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 08
.
Karar fitar harsashi daga bakin bindiga gami da ihun da Oga sadi ya saki shine abun daya Razana sauran yan ta'addan,
.
Cikin zafin nama yan ta'addan suka zare bindigoginsu suka fara yiwa yan sandan dake waje ruwan harsashai,
.
Jami'an yan sandan suka cigaba da sakin wuta ya zamana cewa suna musayar harsashi tsakaninsu da yan ta'addan
.
Shakka babu yan ta'addan sunyi mamaki kan yadda akayi har aka gano suna boye cikin hotel din, cikin bacin ran an harbi shugabansu a kafa, yan ta'addan suka ta sakin wuta ba sararawa
.
A cikin musayar wutar da ake ne wani jibgegen dan sanda ya kwalla ihu ya fadi kasa kafadarsa na hagu na bulbulo da jini
.
Da wuri yan sanda biyu suka kinkimi katon dan sandan da aka harba a gefen kafada su kai waje da shi
Da yan Ta'addan suka tabbatar cewa muddin aka cigaba da wannan gumurzu to nan bada dadewa ba Alburusan bindigoginsu zasu kare a samu nasarar kamasu sabida haka sai jagwa ya zo gindin tagar dakin ya doketa da hannu take gilashin da ke jikin tagar ya tarwatse
.
Ya juya yawa Balbali inkiya da hannu kan cewa su zo su fara fita shi zai ji da yan sandan
Batare da bata lokaci ba Balbali ya nufi tagan dakin wanda ke can kuryar dakin , jagwa ya dawo bakin kofa ya cigaba da sakin harsashai daya harba harsashi daya sai ya dakata yaji ko harsashin tayi nasarar aikata abun da ake bukata
.
Sabanin yaji ihun jami'an tsaron sai de ya sake jin wata karar fitar harsashi ta durfafo dakin hakan tasa yake boyewa a jikin bangon dakin
,
Jagwa,aba yawo da Audu suka durfafi tagar dakin bakin bindigunsu na fuskantar kofar dakin da yake a bude , jira kawai suke wani mai kararrar kwana ya leko,
Kimanin dakiku talatin kenan da lafawar musayar wutar, bakajin karar komai cikin dakin in ka dauke nishin da oga sadi yake,
Yana kwance a kasa ya rakube da jigin bango hannunsa na rike da bindigarsa ya saita bindigar a daidai saitin kofar dakin, kafarsa ta hagu kuwa sai bulbulo da jini take tamkar an yanka Kaza
.
Cikin kankanin lokaci jagwa da Aba yawo suka fice daga dakin ta taga, Audu yai wa balbali inkiya da hannu kan cewar su dau Oga sidi su tafi da shi
.
Audu da balbali suka ciccibi oga sidi sukai sama da shi suka dumfari tagar dakin da zummar su fice da shi toh a lokacinne Al'amarin ya faru, Al'amarin daya yi matukar fusata dan ta'adda Audu, Al'amarin da ya kusan Zauta dan ta'adda Audu,
.
Mataimakin kwamishina kamalu ya jinjina bindigarsa da yadubi wasu yan sanda biyu dake gefen hagunsa yai masu inkiya da hannu
.
Lokaci daya yayi Gungure ya wuce ta gaban kofar dakin fuskarsa da bakin bindigarsa na kallon cikin dakin
.
Abun daya ga yan ta'addan na kokarin yi shi ya sanya cikin sauri ya harba harsashin bindigarsa
,
Audu na na wajen dakin ta taga Balbali yana ta ciki yana kokarin daga Oga sidi Sama ya tsallake tagar , Audu kuma kokari yake ya tallabo kafafuwan Oga sidi ta yadda da zarar ya haure tagar to a hannunsa zai fado
Balbali ya baiwa kofan dakin baya bindigarsa na ajjiye a gefen Tagar , kokarinsa shine oga Sidi ya far ficewa,
,
Karar da Balbali ya kwala gami da karar fitar harsashi shine abun da yayi matukar Razana Audu, balbali ya fadi a kasa Rikica kai kace giwa ce ta fadi, ko shurawa bai yi ba yace ga garin ku nan
.
Audu da oga Sidi sun yi matukar Razana da harbin Balbali da akayi nan take audu ya fara kokarin janyo oga sidi daga cikin dakin
.
Jami'an Yan sandan gaba daya suka kunno kai cikin dakin suna masu sakin wuta,
.
Ganin jami'an tsaro sun kunno kai cikin dakin kuma ya tabbata in har suka shigo dakin zasu iya hallaka sa
"Audu ka sakko mu tafi"
.
"Me kake jirane Audu ka sakko mu tafi"
"Kassako man audu"
"Zasu iya kashe ka muddin sukai arba da kai"
"Ka sakko mu tafi"
Audu ya tsinkayi muryan yan 'uwansa Jagwa,Aba yawo da Taku,
Ya kai dubansa izuwa kasan hotel din ta inda yake jiwo sautin muryoyinsu
.
Ya hango su akan Rufin wani gida, kasan Hotel din kuwa mutane masu yawa suka mamaye suna kallon abun da ke faruwa
.
Bakin bindigar wani dan sanda ne ya leko cikin dakin, ganin haka sai audu ya daga bindigarsa yana kokarin sakin wuta amma sai bindigar tayi Turjiya , ta na kukan rashin Alburusai,
.
Audu yai harbi da bindigar ta bakin kofar dakin lokaci guda yayi tsalle ya rabu da jikin Hotel din yana mai kallon oga Sidi wanda ya tabbata ba makawa zai jami'an tsaro sun kamashi
.
.....
Babban kurskuren da yan sandan suka yi shine da suka dunguma baki dayansu suka afka ma yan ta'addan , izan da sun bar wasu a wajen harabar hotel din da babu makawa sai sun yi Nasarar Kame yan ta'addan
.
Koda Dan ta'adda Audu ya dirgo saman Rufin wani Gida, bai tsaya wata wata ba ya Ruga da gudu ta wani sashe mai karancin mutane
.
********
Hasan,Aliyu,Mansir,Jibrin da haidar suna sanye cikin riga riga mai launin ja da fari dogon hannu da Jar doguwar wando
.
Tafe suke cikin Annashwa da farin ciki
"Sarkin dariya yanzu dai sai ayi kokari a kame dariyar ko" mansir yafadi cikin murmushi yana kallon Aliyu
.
Aliyu wanda ya natsu sosai yadda kasan frofesa za shi wajen wani muhimmin taro yayi murmushi gami da gyara kwalan rigarsa ya sake tsuke zanzaron da yayi sannan yace "in Allah ya yarda"
.
Dukansu suka kyalkyale da dariya,
Kai tsaye suka nufi Kasuwar makarantan wurin da ake saida Abinci da sauran Abubuwan kwalama, dalibai suna kiran wurin da BENUE MARKET,
Kasancewar kasuwar yana kusa da BENUE HOUSE shi yasa aka lakaba masa wannan suna
.
"Aboki kafa yi dacen budurwa sai de..."
Haidar ya fadi yana murmushin tsokana
Mansir ya ce "sai de mai"
Jibrin yayi murmushi yace "sai de ita zahra'un batayi dacen saurayi ba, haba mutun kullin baki a bude wannan wata rana ai sai ka cije ta" ya karisa maganar yana dariya
,
Dukkansu suka dara in ka dauke Aliyu daya sha kunu ya bata rai, hasan ya matso kusa da Aliyu ya dora hannunsa akan kafadar Aliyu yace "Aboki ka rabu da zancensu na soki burutsu nasan ita kanta Zahra'u tana sonka domin kaidin ba karamin kyakkyawa bane, gaka da haiba da cika Ido, "
Aliyu yayi murmushi yace "nagode aboki kai kadaine ke goya ma soyayyata baya kuma da yardan Allah nan da yan lokaci kalilan zata sanar dani cewa tana sona a gabanku yan kushe"
Yafadi yana kallon su haidar
Dariya sosai jibrin yayi kafin yace "tab kace ma kai kake kidinka kuma ka ke rawar ka "
.
"Ai ya sanar da ita sai de har yau shiru kake ji babu amsa" mansir ya fadi yana duban jibrin
"Toh Allah yasa dai ba son maso wani kake ba wanda hausawa suka ce koshin Wahala"
Haidar ya fada
.
Haidar,jibrin da Mansir sukai shewa sai dai ganin Abokan nasu biyu sun bata rai
Yasa jibrin ya dan matso kusa da hasan yace "haba aboki sarkin dariya kada kayi Fushi ni nasan yarinyar tana matukar sonka, kawai dai tsiyace muke maka"
Haidar ya kara da fadin "shin kai baka lura da irin kallon data ke maka bane aduk lokacin daka je Benue market,izan da wata rana zaka lura da irin kallon to tabbas da ka tsinkayi zuzzurfan So na gaskiya Makare a cikin kwayar idanunta"
.
"Irin murmushinn data ke yi ma ya isa hujja domin murmushine dake dauke da sakon Zuciya,aboki muna tare dakai yau sai ta sanar damu matsayinka a Zuciyarta"
Mansir ya fada yana kokarin tallafo habar aliyu wanda ya saki fuska , har zuciya Aliyu yaji dadin maganganun Abokan nasa,
.
Lokaci guda yaji wani kwarin gwiwa ya shigeshi cikin dakewa yace "maganarku Gaskiya abokai ayau ya kamata nasan matsayina a wurin ta don haka mu je mu same ta"

Tuesday, 4 December 2018

AJALI na Shafi'u Dauda Giwa page 12

Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke dai je ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya shigo."
.
A'isha ta mike cikin farin cikin tana rangwada ta nufi kofar gidan.
Hakika sun yi dace ita da angonta Nazifi, Allah ya hada ta da mai sonta kuma ita ma take kaunarsa. Ya raba ta da wannan wahalallen da a da ya nace mata, A'isha ta ce a zuciyarta tana murmushin farin ciki.
.
Ta kama kofar gidan da hannayenta biyu, ba tare da wani fargaba ko zullumi ba TA BUDE MASA kOFAR!
****====******
Dankareren kayataccen gidan ne da ya kai matuka wajen tsaruwa. Jama'a da dama kan dakata don yiwa kyakkyawan gidan kallon tsaf! saboda ginuwarsa.
Mutane da dama kan tuna da kayataccen gidan saurauniyar ingila
dake "BUCKINGHAM PALACE" a duk lokacin da suka dubi tsararren gidan. Wani dadin abin da ke matukar jan hankalin jama'a ga hadadden gidan shi ne daddadan kamshin furanni dake gewaye da gidan.
dan tsamurmurin dattijon maigadin da ke zaune akan bencin a gefen katotuwar kullalliyar kofar gidan mai fasalin fuka-fukan dawisu, ya dan yamutsa fuska gami da gyara rikon jaridar da ke hannusa tamkar mai tsammanin shekowar wani a guje ya wafce ta, cikin zakuwa ya soma bude shafukan cikin ta, a shafi na biyar ya yi ido hudu da labarin da yayi matukar jan hankalinsa mai taken KADDARA KO FANSA!
.
A hanzarce ya muskuta gami da gyara zama, kana ya sake kafa kwala- kwalan idanunsa akan hotunan gawarwakin wasu mutane biyu mace da namiji da ke gefen rubutun, cikin zakuwa ya soma karantawa.
.
A safiyar jiya ne yan sanda suka tsinci gawar
wani saurayi Nazifi tare da masoyiyarsa A'isha.
.
An tsinci gawarwakin ne yashe a cikin wani sabon gida bayan an harbe su da bindiga har lahira.
Tuni jami'an tsaro sun cafke wanda ake zargi da aiwatar da kisan gillar wanda ya kasance wani matashin soja wanda shima yake kaunar budurwar, wanda kuma har an sa ranar bikin su da ita amma kuma ita ba ta kaunarsa.
.
Mahaifin yarinyar mai suna Alhaji Dage ya yi
nadamar afkuwar mummunan al'amarin sannan kuma ya tabbatarwa da wakilinmu cewar dukkan wannan al'amari da ya afku laifinsa ne sakamakon tilastawa diyar tasa da ya yi a kan sai ta auri wanda ita ba shi take so ba. A karshe ya yi kira ga iyaye a kan su dinga mayar da hankali a kan dukkan abin da `ya`yansu ke bukata matsawar dai hakan bai sabawa addini ba.
.
Sannan kuma ya yi doguwar addu'a gami da bayyana matukar alhininsa ga mamatan
.
Don jin yadda zata kaya mu hadu a cigaban littafin nan mai suna A’ISHA don
jin karshen sarkakiyar sarkakakken labarin.
Na gode, naku Shafi’u Dauda Giwa.
.........................
Anan kuma ayau muka kawo karashen littafin AJALI amma da yardar Allah daga nan zuwa wani lokaci zan saka maku cigabansa
.
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing Shuraih Usman 99%
....
JINJINA GA
Shafukan
Shuraih 99%
Zauran labarai
Home of Littatafan yaki and Hausa novels
.
Ina mika sakon gaisuwata ga ahalin kungiyar
TSANGAYAR MARUBUTA
TASKAR GIDAN LITTAFI
.....
Nine naku a kullum da ko yaushe Shuraih Usman
99%
Ku tareni a littafin A'ISHA

TASKU littafina daya 1 part 11

Tasku 11

Daga cikin wayannan mutane wasu gardawa suka nufoni da zummar su kamani, cikin sauri sai na rufe dakin sannan na garkame kofan, ban tsaya wata wata ba na nufi kofan fita daga gidan ina zuwa kuwa naga gate din a kulle babu ta yadda banyi ba dun na bude anma abu ya gagara
.
Gaba daya na birkice jikina sai bari yakeyi, na runga tunanin abun daya kamata na yi cikin sauri na dumfari katangar gidan domin kuwa na kware wajen haura katanga, don tun lokacin da muke makarantan kwana izan muna son mu shiga gari toh katanga muke haurawa,
.
Ban tsaya wani tsaibi ba na kama katangar wanda ma sam bashida tsayi nayi kokari na haura kan katangar daide zan dirga a waje kenan sai naji hannu ya rike mani kafa daya na saki ihu ina kokarin fisge kafata, dakyar dai na samu na kwaci kafata daga hannun wanda ya rikeni din cikin sauri na dirgo a wajen gidan sai de me
.
Anan hankalina ya kusan fita daga jikina, numfashina ya nemi ya dauke don kuwa abunda na gani ya tabbatarmin da lallai na fada a cikin TASKU babba, a dokar daji na tsinci kaina babu gida agaba babu gida abaya,
.
Karar gate din gidan danaji ne ya katsemin tunanina na tabbata sune suke fitowa ban tsaya duba hanya ba na yanki daji na runga falfala gudu wanda sam bansan ma ina zan nufa ba, ni dai kawai gudun ceton raina na keyi, nayi gudu mai nisa har na iso bakin titi, toh a nan ne na runga neman abun hawa amma ban samu ba domin kuwa lokacin dare yayi, masu abun hawa daddaya ne suke wucewa suma kuma ko na daga masu hannu alamar su tsaya basa tsayawa
.
Babu abunda nake sai kuka inajin mugun tsanar sabeer a cikin zuciyata , da dai naga na dade a bakin hanyan ban samu abun hawa ba sai na cigaba da taka sayyada ta, ina tafiya sauri-sauri gudu-gudu har na fara isowa wajen jama'a toh a nan ne hankalina ya soma kwantawa
.
Dai dai nazo wajen wani kwari sai naga wata bakar jeep kirar range rover, na daga mata hannu alamar ta tsaya, nayi mamaki da naga ta tsaya don kuwa ni sam ban yi tsammanin zata iya tsayawa ba,
Tsayawar motar keda wuya sai wasu katti su uku suna sanye da bakaken kaya , suka fito daga cikin motar batare da bata wani lokaci ba suka iso inda nake suka rufe mani baki sannan suka jani cikin motar suka ja,
.
Direban ya ciro waya daga aljihunsa ya buga sannan ya kara a kunnensa can sai yace Oga S.B mun kama yarinyar , yanzu haka tana hannunmu, mu kasheta ne ko mu kawo maka ita
Ban san abun da aka cemai daga wancan bangaren ba sai ji nai yace Ok oga angama
.
Mun danyi tafiya kadan sai kuma ya faka motar a gefen hanya sannan ya dubeni da kyau sai naga ya lashe baki da harshensa, ya maida dubansa wajen daya daga cikinsu yace mai " ABA YAWO wai kaji fa oga da wani wawan zance "
Wanda aka kirawo da aba yawo yace "me yace ma"
"Wai cemin yayi na kaimai ita yanzu yanzu"
"Toh kai nufinka ina zamuje da ita inba wajen oga ba"
"Damuwana dakai kenan abayawo baka da ganewa, haba ka dubi zukekiyar yarinyarnan kace wai haka zamu kai wa oga ita, kuma kaima kasan ko mun kaita yanzu kasheta zasuyi su ba wa shegen dodon sun nan jininta yasha"
Ai inajiin haka sai cikina ya kada , numfashina ya kusan tsayawa sai a sannan na tuna da Addu'a na somayi a zuciyata
Direban yaci gaba "dun haka muma zamu dan faka mu yagi namu rabon kafin mu kaimai ita,ko ya kuka gani"
Ya idda maganarsa yana duban sauran yan uwansa
Suka gyada kai alamar sun amince direban ya bude kofa ya fito suma duka suka fito nima suka fito da ni suka daukeni suka kaini cikin kogon nan daka tarar damu suna kokarin suy mani fyade sai Allah ya kawo ka kace ceni,...."
Rufaida ta karashe labarinta tana mai shisshikar kuka,
Daga ni har mujahid mun firgita da jin labarin da rufaida ta bamu,
"Inna lillahi wa inna ilaihirra ji'un "
Shine kadai kalman da bakina ya iya fadi,
.
Na dubi rufaida da razananniyar fuskata nace "shin kin fadawa mahaifinki?"
"A'a ban fada masa ba"
"Amma mai yasa baki fada masa ba kina da sanin cewa lamarinnan na iya sanadin rasa rayuwarki"
"Eh na sani amma sam bana son mahaifina ya sani, saboda muddin ya sani sai ya kusan Kasheni" rufaida ta fada tana share hawayen da ke kwaranyowa daga idanunta
.
"Amma rufaida yana da kyau ace kin fadawa mahaifinki saboda a dauki kwakkwaran mataki akan lamarinnan tun kafin Mugayen mutanen nan su sami nasarar kamaki," mujahid wanda yake a firgice ya fada yana kallon Rufaida
.
"Don Allah ina rokon ku da kada ku fadawa mahaifina don muddin ya sani yana iya Kasheni"
Rufaida ta fada
.
Babu irin yadda ba muyi da rufaida ba akan ta sanar wa mahaifinta da lamarinnan , amma ta ki daga karshe ta runga yi mana magiya tana bamu hakuri akan kada mu sanar da shi,
A ce warta wai akwai lokacin da ya kusan kasheta da duka don ya ganta tana magana da wani dan unguwar,
.
Duk da haka sai dana nuna mata illar rashin sanar da shi din da kuma abun da hakan zai iya jawo wa
.
**********
Muna tafe ni da mujahid kan hanyarnu na komawa gida,
Fuskokin mu na duban kasa
Dukkanmu da tunanin da yake yawo cikin zuciyoyinmu,
.
"Shuraih ni dai in kabita shawarata ku kai maganar nan wajen hukuma don kuwa wannan ba karamar magana bace, ni nafi jiyewa ita Rufaida saboda taga Sirrinsu a kowani yanayi zasu nemi hanyar da zasu kasheta don kada ta tona masu Asiri" mujahid yafadi lokacin da yake duban fuskata
.
Nayi murmushi amma na tsoro " ni kaina tunanin da nake kenan,don lamarinnan ba karami bane ya kamata a sanya hukuma ciki amma dai kaji yadda mukayi da rufaida, babu yadda banyi ba akan mukai maganar nan wurin Hukuma taki ace warta wai bata son mahaifinta ya sani,"
.
"Karabu da ita shuraihu ita yarinyace har yanzu da yarinta akanta kazo yanzu mu wuce barikin yan sanda, "
Nayi shiru ina nazarin maganar mujahid Ni kaina nasan maganar mujahid gaskiyace don ya dace mukai maganar nan gaban yan sanda to amman gudun abunda zai biyo baya nake, na kai dubana izuwa sararin samaniya inda idanuwana sukai arba da hazo hazo na gajimare,
,
Na fada sabon kogin tunanin mafita akan wannan lamari, don kuwa in har mukai sake toh rayuwarmu ni da Abokina Mujahid gami da Abar kaunata Rufaida yana cikin hadari don akowanne lokaci zamu iya fuskantar barazana wacce zata iya kaiwa ga mutuwarmu
.

Tasku 12
.
Na fada sabon kogin tunanin mafita akan wannan lamari, don kuwa in har mukai sake toh rayuwarmu ni da Abokina Mujahid gami da Abar kaunata Rufaida yana cikin hadari don akowanne lokaci zamu iya fuskantar barazana wacce zata iya kaiwa ga rasa rayukanmu
.
Mafita daya ce mu sanar da mahaifin Rufaida abun dake faruwa, na aiyana hakan a zuciyata gaba daya a rikice nake, dun nayi matukar tsorata da labarin da Rufaida ta sanar dani,
Yanzu da ace banzo ba da shikenan Rufaida ta rasa Rayuwarta kenan,
.
Alokacin da na tuna haka sai naji zuciyata ta buga da karfi , gabana ya yi mummunan faduwa, Addu'a na fara yi azuciyata kan Allah ya karemun abar kauna daga sharrin yan mafiya, dama dukkan mutane gami da Aljanu
.
Alokaci daya na dubi mujahid wanda ya sadda kai kasa ko ba'a fada min ba nasan shima labarin da rufaida ta bamu ne yayi matukar Tsorata shi,
Nasan Ayau kam dukkan wani katabus na shi ya kare,
"Mujahid " na kira sunansa
Ya dago kai ya dubeni da tsoratacciyar fuskarsa wacce ta fara tsastsafo gumi yace "na'am"
"Me zai hana yanzu mu je mu samu mahaifin rufaida mu sanar da shi abin dake faruwa, kaga sai ya dau mataki"
.
"Yanzu kayi magana, mu juya muje mu sameshi yanzu ba sai anjima ba" mujahid yafada yana mai juyawa
.
"To ai damuwar daya ce"
"Me ce ce Damuwar"
.
"Yanzu ko munje gidan bayanan "
"Baya nan kamar yaya"
"Ka manta a gabanmu ya fice da zu "
Na fada lokacin da hankalina ya tafi ga wata bakar Mota kirar Jeep data tunkaro mu gadan gadan na kurawa motar ido bana ko kiftawa, gabana ya cigaba da faduwa
.
Mujahid ma ya lura da motar cikin tashin hankali ya ke bin motar da kallo,
Daidaikun mutanen dake wucewa ta hanyar da wayanda suke sabgoginsu suka kurawa motar ido don ganin ba karamin Gudu motar keyi ba, kuma cikin angwa
.
Sai da ya kasance tazarar da ke tsakaninmu da motar bai da nisa sannan hankalina ya tashi na tabbatar cewa ba lafiya ba ganin yadda motar ta dumfaro kanmu
.
Motar tayi burki a daidai gabanmu kadan ya rage ta yi waiji da mu, ni da mujahid mun riga da mun sadakar motar tabi ta kanmu amma cikin mamaki sai mukaji karar birkin motar a gabanmu
.
Yan angwa da mutanen dake wucewa suka tsastsaya daga nisa suna kallon irin gangancin da mamallakin bakar motar yaso yi suna tir da shi, wasu daga cikinsu kuwa gani suke tamkar Shifci ce
.
Mujahid ya dubeni cikin tsoro yace "shuraihu wai me ke faruwa ne, me ne ne gamin mu da bakar motar nan"
,
"Ni kaaina ban taba ganin motar ba sai......."
Maganata ta katse Daidai lokacin da kofar gaba na motar ta bude wani bakin mutum mai suffar mutanen Farko ya fito daga ciki,yana sanye da bakaken kaya gamida bakar takalmi sau ciki
Kallo daya na mai na ganeshi, yana daya daga cikin mutanen da na kwaci rufaida daga hannunsu ,
.
Dogon mutumin mai kirar samudawa yayi wata fatalwar murmushi wacce kan iya tsorata mutum, na tabbata izan yayiwa yara kanana wannan murmushin to zasu iya sumewa
.
Hannunsa na hagu tana cikin wando yayin da hannun damansa take kugunsa abunda idona ya hango mani a kugun nasa shine abun daya kusan sanya ni sakin fitsari a wando
.
A mafarki, da fina finai kadai nake ganin ta ban taba tsammanin zanganta a zahiri ba , Bindiga ce kirar pistol take soke a kugunsa
Mutumin ya nufoni ba karamin razana nayi ba da zuwan mutumin ya rungumeni yana cewa "ya kake ne mutumina, kwana biyu"
.
Na samu kaina da furta mai lafiya
Ya je ya rungume mujahid suka gaisa kafin daga bisani ya ce damu "abokai ammafa kun debo tafiya mai zai hana kuzo na rage maku hanya"
Yana maganar hannun damansa tana shafa karamar bindigar dake soke a mararsa
.
Mutanen da suka tsura mana ido da suka ga yazo ya rungume mu sai dukkansu suka cigaba da Al'amuransu suna masu tir da irin wannan dabi'a ta Shifci
.
Naso nace mai mungode amma sai naga yana kada mani dan yatsansa akan kada na yadda nace A'a
Haka ina ji ina gani muka nufi motar tasa ni da mujahid Gidan baya muka bude da zummar shiga , turus mukai sakamakon ganin Rufaida a cikin Motar an daure mata hannuwa da kafafu hakanan an rufe mata baki da wani irin Salaten wanda ban taba ganin iirinsa ba sai a fina finai
.
Nayi mamaki sosai da ganin rufaida, kai kace ba itace mu kabarta dazu a gidansu ba,
"Uwar me kuke jirane har yanzu da baku shigo ba"
Wani Kato dake kujeran gaba ya fadi na lura shine ke tukin motar
.
Da saurina na shige cikin motar na zauna kusa da masoyiyata rufaida, mujahid ma ya biyo bayana,
Direban ya tashi motar ya bata wuta
..............
Anan na kawo karshen Littafi na daya
Sai ku biyoni cikin TASKU littafi na Biyu 2 domin jin yadda zata kasance
.
Wannan labari kirkirarrene daga Shuraih Usman
Shekarar rubutawa 2016
Gyara 2018
Marubuci Shuraih Usman
Hakkin Mallaka (m) Shuraih Usman
Copyright (m) Shuraih Usman 2016
.


TASKU littafina daya 1 part 10

Tasku part 10
Littafi na daya 1
"Wata rana na fita zanje siyayya na nufi wani Mall da shigana wajen na shige wani shagon sai da kayan mata , toh a nan ne na hadu da shi..."
.
Nan na katse ta ina mai tambayar da wa kika hadu ,
Nan da nan fuskarta ta canja ta cigaba "wasu Abaya na mata na dauka naje wajen biyan kudi domin na biya,
.
Tunda na shigo cikin wannan shagon na lura da wani kyakkyawan saurayi yana ta kallona, shi wannan saurayin yana sanye cikin bakar suite, da bakaken takalmi, ya ci bakar tabarau
.
Koda nazo biyan kudin sai mai shagon yake sanar dani ai wancan mutumin ya riga daya biya min ko, na juya wajen da naga mai shagon ya nuna min da hannu banyi mamakin ganin wannan mutumin ba
.
Karisowa wajen da nake yayi sannan yayi mani sallama
"Assalamu'alaiki yake wannan kyakkyawar gimbiya"
.
"Wa'alaikassalam" na fada cikin sakin fuska
Kallo daya na mai na gane me ya kawoshi wajena
"Da farko dai suna na sabeer anma anfi kirana da S.B gaskiya tunda nake a rayuwata ban taba cin karo da macen da naji na kamu da tsananin kaunarta a zuciyata ba duk da dai ban san sunan ki ba amma ina so ki sani cewa I NA SONKI"
.
Kwata yana yinsa bai min ba hakan tasa na ce dashi " malam sabeer kayi hakuri don kuwa dakwai wanda nake kauna so kuma na aure" ina fada mai hakan na wuce nai tafiyata, sannan na bar mai kayayyakin a wajen
.
Ban san ya akayi ko ta yaya sabeer ya samu nombana ba, wata rana da daddare kawai ina kwance a cikin dakina sai wayana ta dau kara, koda na duba fuskar wayar sai naga bakuwar nomba ce , hakan yasa na fita harkar kiran ban daga ba
.
Sai da aka kira kusan sau goma sannan na dauki wayar na daga
"Assalamu'alaiki ma'abociyar kyawu, " naji muryan da inaji na gane mai muryan,
Na amsa mai da "wa'alaikassalam"
"Rufaidah kisani cewa nayi bincike akanki na gano cewaa bakyada wani saurayi,
Ina sonki rufaidah ki taimaka ki amshi tayin soyayyata ko zuciyata ta dan rage zogin data ke yimin , ina sonki rufaidah"
.
Nan dai yai ta damuna da surutansa nai shiru dai kawai ina jinsa,
Ba'a dade ba naji nafara sonsa, har takai ga yakan kirani a waya muyi dogon hira,
.
Wani lokacin kuma zuwa yake muje shakatawa da sauran wuraren da masoya ke tafiya
.
Yadda nake jin soyayyarsa araina a lokacin, bazan taba rabuwa da shi ba
,
Wata rana bayan sallar isha'I sabeer yazo wajena domin ya saba zuwa kuma koda yazo toh baya karasowa kofan gidanmu, sai dai ya tsaya a bakin angwanmu ya kirani a waya ni kuma nazo na sameshi, ko Abbana bai san cewa ina da masoyi ba nima kuma sabeer ya kwabeni akan kada na fada mai,
Koda na tambayeshi dalili sai yace min wai baison dukkan wani abun da zai kawo cikas ma soyayyarmu, wai ya fiso kawai abbana yaganshi a lokacin da zai turo magabatanshi irin wayannan zantukan nasa dayake fadamin sune suka hanani sanarwa wa abbana cewa ina da saurayi
,
Alokacin da sabeer ya kariso angwanmu sai ya bugo mani waya ya sanar dani, toh dama na riga dana fadawa Abbana cewa zankai wa kawata ziyara in anjima shi yasa ban samu wata matsala ba wajen fitowata daga gida
.
A inda ya saba tsayuwa a wajen na sameshi , na bude murfin motar na shiga gaba,
Yana sanye da kana nan kaya jajjaye sun dame jikinshi da kyau yayi mugun kyau, idanuwansa suna boye cikin bakar tabarau din daya saka ,
Yana ganina ya fadada fuskansa da murmushi sa'annan yace beuty kinga yadda kikayi kyau kuwa tunda nake ban taba ganin kinyi kyau irin na yau ba, nayi murmushi nace mai, ai kaima yau kayi mun mugun kyau musamamman ma wayannan kayan daka saka sun dace da jikinka"
Dariya yayi sannan yace beuty so nake ki rakani mududduba wani Gida na ke son na siya domin kuwa a cikin gidan zamu zauna,
Cemai nayi muje don kuwa ni ban kawo komai a raina ba
.
***********
Motarmu ce ta faka a gaban wani tangamemen gida muka bude kofa muka fita, sabeer ya ciro wata na'ura daga aljhunsa mai kamar waya, ya daddana sai naga gate din gidan ya bude da kansa,
Jinjina kai nayi nace a raina tabbas sabeer ba karamin mai arziki bane, amma kuma bansan sana'arsa ba, akullum na tambayeshi aikinsa sai ya cemani kasuwanci yakeyi, hakan kawai yasa nake basarwa bana son tambayansa don gudun kada ransa ya baci
.
Muka shiga cikin gidan da sabeer ya faka motarsa agun da ake ajjiye motoci, shiganmu gidan keda wuya sai na samu kaina cikin faduwar gaba , gabana sai faduwa yake amma sai na dake , sabeer ya riko hannuna yaja ni cikin falon, babban falone wanda ya aka kawata shi da kayan ado tako ina, bamu tsaya anan ba sai sabeer yace mani mu fara zazzagaya gidan
Mun zazzagaya gidan gaba daya babu dakin da bamu shiga ba,
Bayan mun dawo rantsastsen falon gidan mun zauna muna huta gajiyan tafiyar da mukayi, sai sabeer yace mani" beauty bari na dan kawo maki lemu ko"
Gyada mai kai nayi alamar na amince
Ya tashi ya shiga wani daki wanda shine kadai dakin da bamu shiga ba acikin gidan, akalla ya dau mintoci biyar bai fito ba hakan yasa na bi bayansa cikin dakin ina bude kofan dakin anan naga abun daya tayar mani da hankali, jikina sai bari yake ,kwakkwalwata sai da kusan tsayawa
.
Mutane ne wajen su ashirin suna jere a cikin layi bibbiyu dukkansu suna sanye ne da jajayen jallabiya sannan sun dora wani jan kyalle a goshinsu,
A gaban wayannan mutane wani tsohon mutumne tukuf da shi gashin gemunsa fari fat, mutumin yana sanye da bante sai wani jan tawul daya rataya a kafadarsa,a durkushe a gaban wannan tsohon sabeer ne shima ya daura jan kyalle a goshinsa, yana rike da wata kwarya a hannunsa ,
.
Dukkansu suka juyo da kallonsu gareni yayinda sabeer ya mike tsaye yazo tsakiyar mutanen nan yace "wannan itace kyautata ga dodo barnumu, "
Yana gama fadin hakan sai ya kafa kwaryar dake hannunsa a cikin bakinsa, yana cire kwaryar ne naga wani dison ja a gefen bakinsa
.
Daga cikin wayannan mutane wasu gardawa suka nufoni da zummar su kamani, cikin sauri sai na rufe dakin sannan na garkame kofan, ban tsaya wata wata ba na nufi kofan fita daga gidan ina zuwa kuwa naga gate din a kulle babu ta yadda banyi ba dun na bude anma abu ya gagara

TASKU littafina daya 1 part 9

TASKU
kirkirarren labari
daga Shuraih 99%
Part 9
. . Ina zaune bisa wani kujera, na yi zurfi cikin tunani . "Assalamu'alaikum" naji muryar Abbana . Umma ta ce ta amsa mai sallamar , ko kallon inda nake baiyi ba ya wuce izuwa dakinsa . Ina ganin haka nace a zuciyata yau dea zanje na ba Malam hakuri, inma wani laifin na mai a iya sanina ni dai nasan babu laifin dana aikata masa, . Na tashi na nufi cikin dakin nasa, sallama nayi na shiga na iske shi a zaune bisa kushin a tsakiyar falonsa, Ya amsa sallamar amma kansa aduke yana danna waya, . Na durkusa bisa guiwowina a gabansa nace " Malam kayi hakuri, bisa abin dana aikata, duk da bansan abin dana aikatan ba, tunda na taso a gidan nan baka taba fushi da ni ba sai wannan karon Sannan kuma fushin iyaye masifa ce ga yayansu, don Allah malam ka yafeni, kaine komaina a rayuwa kamin komai" . Sai asannan ne yadago kai ya dubeni "ni baka batamin rai ba, illa dai kawai abu daya , malam shuraihu (sunan da babana ke kirana da shi kenan) shin me ya hadaka da wannan yarinya sannan kuma a cikin tsohon dare, Ta yaya zaka nemi ka bata sunan wannan gida namu , dukkan mutanen wannan angwan suna ganina da kima da mutunci, " Yadanyi ajiyar zuciya , Sai a sannan ne na fahimci inda maganan Malam ya nufa, Yaci gaba da cewa" shin yaushe ka watsar da tarbiyar dana baka , shin yaushe rudin duniya ta fara debarka, kodai MUGAYEN ABOKAI ke maka hudubar shaidan, sam sam bazan yadda ka batamin suna a wajen mutane ba" yafada cikin bacin rai . Na dubeshi sannan nace"Malam ba abin da kake tunani bane , babu wani wanda ya'isa ya gurbata wannan tarbiyar daka bani sai Allah, dayar dar Allah bazan taba jawo maka zagi wajen mutane ba, " Nan na fede wa babana biri har wutsiya, sannan na kara da fadi mashi cewa ni ina Sonta da aure ne bawai da wani nufin ba . "Alhamdulillah Alhamdulillah dama mu abin da muke so kenan , tuntuntuni nake ta yi dakai akan kayi Aure amma sam kaki toh yau kam babu wanda ya kaini farin ciki bisa wannan zance daka sanar dani, yar gidan wacece" Nan na dan susa keya " bansan sunan mahaifinta ba amma zan....." Sallamar da mukaji ne ya dakatar da zancena, Mahaifiyata ce ta shigo dauke da farantin abinci ta ajiye farantin mai dauke da kuloli biyu da kuma cokula a saman wani dan karamin gilashi mai kirar teburi, wanda akayi dama don hakan ," . ******** *********** ****** Ina tafe bisa mota ta kirar 406, wani sauti na saka , sai tashi yake yadda kasan wani club , , Pakawa nayi a gefen titi sannan na kira wayan mjd, . Bayan ya dauka ne na sanar dashi yanzu haka ina kofar gidansu ina jiransa, , Baifi minti biyar ba da ajiye wayata, sai gashi nan ya fito, yana zuwa ya shige gidan baya ya zauna. Na duve shi" malam kasan ni ba direban kabane koh" . Murmushi yayi sannan yace" ok zaka basu labari badai ni ba ,muje zuwa..." Ya fito ya dawo gidan gaba kusa dani, nan na tashi motar muka hau hanya, , "Ya baba ina muka nufa" yafada dai dai lokacin dana sharo wata kwana ta wani babban gareji, "Ba saidaka zan ba,kaji don haka ka kwantar da hankalinka" na fada yayin da hankalina ke wajen tuki . Har muka iso gidan bai ce dani ufFan ba mun karisa ciki sannan na kira wayarta, , Bugu daya Tadauka anan na sanar da ita ina gidansu, inajin lokacin da ta sa shewa, sai kuma tace dani na kariso dama mahaifinta yana so yai magana dani, , ******* ********** ******* Rantsatstsen falone wanda ya amsa sunansa , mahaifinta yana wani babbar kushin maicin mutane akalla goma , sai kuma ita Rufaidan tana gefensa , Nida mjd zaune bisa wani sofa mai cin mutum uku zuwa hudu, mun fuskanci juna da mahaifinta, , "Yaro tabbas ka ceto yata daga shiga wani hali na rayuwa, sannan ka ceto martabar wannan gida,ni nama rasa da wata kalma zan yi amfani da ita wajen yi maka godiya,na gode yaro, shuraihu kake ko shuraiha" mahaifinta yafada yayin daya ke dubana, . "Shuraih ne sunan baba, sannan basai kayi mini godiya,ai wannan ba wani abu bane tamkar kanwata haka take ,ka dai gode ma Allah mai kowa mai komai," , Wayarsa ce tayi kara nan danan ya daga magana sukayi daganan yace damu shi zai tafi izuwa wani taro da aka kirashi na gaggawa, . Bayan tafiyarsa ne na dubi Rufaida wani zunzurutun sonta ne ke kara shiga cikin zuciyata, , Toh anan ne na tambayeta ya akayi har wayannan karti suka kawota cikin wannan kwarin da kuma dalili . Nayi mata wannan tambayar ne don kawai naji sautin muryarta wanda ya kasance mai zakine tamkar zuma, , Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dubemu ni da mjd tafara bada labarin kamar haka
.
Ku biyoni a part 10 Its Shuraih 99%

TASKU littafina daya 1 part 8

TASKU
kirkirarren labari
daga Shuraih 99%
Littafi na daya 1
Part 8
.
. Daga nan bansan kome ya faru dani ba , Idanuwa na ne suka fara budewa, na dan fara gani dishi dishi, . Toh a sannan ne idanuna suka washe na fara gani da kyau, . Kwance nake bisa wani katifa mai dan karen laushi, a gefena ga mahaifiyata! Da mahaifina, Gefen haguna kuwa, Mjd nagani shida Anas , . Na dan mike da kyar na jingina da bangon wAjen wanda nake tunanin asibiti ne, . "Sannu, koma ka kwanta," mahaifiyata ta fada, a lokacin data ke dubana . Sai a sannan ne na lura da kafata na hagu , wani dogon karfe ne a gefen gadon a sakale ajikin karfen wani farin bandeji ne wanda ya taimaka wajen tallafo kafata, izuwa sama, Wajenda wannan karen ya dan kara min cizo, an dabaibayeshi da bandejii . Sai a wannan lokacinne a bubuwan da suka faru dani suka fara zarya a cikin kwalkwalwata . Na tuna lokacin dana bingire kasa, abin da kunnuwana suka jiye min na karshe shine*n sautin kukan rufaidah, . Na dubi mahaifiyata nace mata "umma ya akayi na zo wajennan," . "Abokinka ne ya dauko ka, kaida wata yarinya, a can wani angwa," ta ce dani tana duban mjd . Mjd najin haka ya matso kusa dani sannan ya dafa kafaduna," Nazo gidankune nemanka shine aka sanar dani baka nan, dana tambayi umma shine tace min tun da mukayinnan ne haryanzu ba ka da wo ba" Yadan sauke ajiyar zuciya sannan yaci gaba"toh a lokacinne nakira wayarka, bayan an dauka ne naji sautin mace kuma da alamu kuka take, anan ta sanar dani halin da kake ciki, tai mani kwatancen, wajen da kuke , Ina zuwa kuwa na iske baka cikin hayyacinka, nan na daukoku izuwa wannan a sibitin yanzu haka ita tana wancen bangaren, amma abin dana keso dakai, ka kwantar da hankalinka babu abinda ya sameta, kawai, dai dan kurkurjewan da tayine ake yi mata treatment nashi" . Na mayar da dubana wajen mahaifina , wanda ya hada rai tamkar an turo masa da sakon mutuwa, "baba....." Yada katar dani ta hanyar daqa mani hannu alamar baya bukatar wani zance. . ********* *********** ****** Zaune nake a tsakar gidanmu, a gefe ga ummata, tana gyaran shinkafa, , Yau kwana daya kenan da sallamata daga asibiti, Tun alokacin na fahimci mahaifina yana daddaure mani, Koda na gaishesa sai dai ya amsa a cikin daure fuska, sabanin daa . . Gidan mu gidan mutuncine sannan mahaifina malamine, Sunansa, Mu'azu toh sabida malumtarsa sai ake kiransa da Malam Mu'azu, Ummana itace kadai matarsa, sunanta, Maryam, ana mata lakabi da mairo, ni kuma umma nake kiranta, kuma nine kadai dan da suka haifa a duniya, . Bakaramin ji dani mahaifina yake ba, dun ya nunamani gata, tun ina karamin yaro, har nafara girma, toh a sannan ne yasaka ni awata makaranta ,SOKOGA,private ce nayi nursery da primary acan daga baya kuma na koma KDF acan ne nayi secondry school dina , Dana idar sai na sami admission a NSUK, ina karanta fannin Engineir, , Shekaruna biyu kenan da fara aiki da wata kamfani na kera kayan motoci da na mashina, a Abuja, . A ka'ida ta duk ranar jumu'a, ina zuwa gida nayi hutun mako tare da mahaifana, . Wannan makonma hutun nazo dana san abin da zai faru dani kenan tabbas da na hakura da wannan hutun, , Muna namu Allah na nashi, Wannan shine takaitaccen tarihina . Kubiyoni a part 9 . Its Shuraih 99%

TASKU littafina daya 1 part 7

TASKU
kirkirarren labari
daga Shuraih 99%
Littafi na Daya 1
Part 7
.
. Wasu murdamurdan karnukane su biyu, jikinsu sur gashi, girman kowani dayansu yakai girman kosashshen rago, baki bude suka nufo mu suna haushi, , Sam sam karka dauka wai ina jin tsoron karnuka , Toh ni da anguwarmu ma cike yake da karnuka . Toh amma da nai arba da wayannan kosasssun karnukan sai da hantata ta kada , domin ban saba ganinsu ba . A dai fina-finan indiya da america ina ganinsu, toh amma a zahiri dai yaune mukayi kicibis dasu . Koda wayannan karnuka suka fara kusanto mu Sai rufaida ta rude ta tsuguna a kasa ta rufe fuskarta, . Haryanzu wukar dana cire a kugun katonnan yana hannuna , Nan na kara damkeshi da kyau tamau, . Karnukan suka daka tsalle a lokaci daya suka fado jikina , a sannan ne suka mangareni na fadi akasa, . Rufaida na ganin hakan sai ta taso daga tsugunen data ke ta dauki wani shirgimemen dutse, Tayi nasarar jefar kare guda da wannan dutsen sai dai , dutsen bai jimata rauni ba, . Karnukan dukkansu suka juya izuwa kanta, na tabbata izan har suka, isa gareta , lamari ya baci . Cikin sauri na yi gudu na wawuri kare daya na yafa da kasa sannan na caka mai wuka a kafarsa daya, nan ya kwanta sai shureshure yake, dayan karen na ganin haka, sai ya dubeni sannan ya nufo ni cikin gudu . Koda ya rage baifi zira'I kadan muhadu ba sai ya daka tsalle ya fado jikina yasanya gaba daya farcensa a gefen wuyana bakinsa kuwa wadda take wangame tana saitin maqokwarona, nufinsa ya fasa makoshina da fikarsa . Koda na fahimci manufarsa, sai na yunkura don na yi cilli dashi amma naji na kasa sakamakon dannenin da wannan karen yayi, . Karfin tsiyane da shi, da kyar na tureshi daga jikina, . Sannan na bishi na kama bakinsa na caka mai wukar a tsakiyar ka har sai da ta fito ta cikin bakinsa nan take yafadi kasa matacce, , Na nufi wajen rufaida wacce tagama tsorata da wayannan karnukan . Nakama hannunta muka tashi tsaye, Toh a daidae wannan lokacin ne al'amarin ya faru, Wani radadine ya ziyarce kafata, na'zata ko zarto ne aka sa za'a yanke kafar, sai a sannanne idona yai arba da dayan karennan ya damfara wa kafata cizo, . Na janye kafata daga bakinsa, na dan rarrafa, ina cikin rarrafen ne naji hannuna ya taba wani abu , . Bakomai bane illa guntun bulo, ji nayi saukar karennan a ruwan cikina, . Ai ban tsaya wata bata lokaci ba na rarumi wannan bulo din na maka masa aka, Nan yayi gefe, ya bingire a kasa koda naga haka sai na tashi, na hau ruwam cikinsa, nai ta maka masa wannan bulo din aka har sai da bulo din ya juya izuwa gari, , Sai a sannan ne hankalina ya dawo jikina na yunkura na mike tsaye , , ******** *********** ******** , Munyi tafiya mai nisa a cikin wannan daren, Har muka iso daidai wajen wani gada wanda a akasar wannan gada ba komai bane illa wani katon kogi, shi wannan kogin ana mai lakani da mahannu, . Muna zuwa daidai gadan na turje sakamakon kafata data ke yimin wani mugun ra dadi, . Na dubi rufaida na ce da ita, "duk da mun kasance muna cikin halin tashin hankali, toh wannan bazai sa na gagari furta miki sakon zuciyata ba" . Ta dubeni cikin alamun rashin fahimtar inda zance na ya nufa "Tun lokacin dana fara ganinki, lokacin da idanuwa sukai arba da wannan kyakyawar fuskar taki, tun a sannan wani mashi mai dauke da dafin sonki ya ca keni a kahon zuciyata, Kece kawai maganin wannan dafin sam sam wannan lalurar dake jikina bai dameni ba, Don muddin akan kine zan iya, sadaukar da rayuwata, Kisani Rufaida I NA SONKI, Bawai so na fatan baki ba sannan bawai so irin na mayaudara ba , ke wata ginshikice na a cikin rayuwata" Ina gama fadin wannan kalmar na bingire kasa sumamme. Daga nan bansan kome ya faru dani ba , . Ku biyo ni a part 8

TASKU littafina daya 1 part 6


TASKU
kirkirarren labari
NA Shuraih 99%
Littafi na daya 1
Part 6
.
.
Koda wayannan karti hudun suka ga abinda nayi wa dan'uwansu sai suka zaburomani tamkar zasu cinyeni danye , Zobe suka yi mani sannan muka fara kallon kallo tsakanina dasu, , Yadda kasan giwaye ne suka sa cinnaka a tsakiya haka sukaimani, wani garjejen kato daga cikinsu ya rarumeni yadaga sama sannan ya tika da kasa, , Ai nan naji tyamkar, kashin bayana ya karye, na kwala ihu , Koda ganin hakan sai daya daga cikin kartin ya dubi wanda ya kwada ni da kasa yace "Yanzu sisini maza je ka duba lafiyar Gogo, " Wanda aka kira da sisinin najin haka ya nufi wajen katon dana barar dazu da dutse , Ya dagashi daga kwancen dayake, sannan ya zaunar dashi, . Sukuwa cikon ukun sai suka fara dumfaro inda nake kwance , koda na farga da su sai na cika hannuwana da kasa, Daidai wani kato ya kawomani naushi sai na tsuguna ya naushi iska, kafin yakai ga juyowa na watsa mai wannan kasar dana diba cikin hannuwana acikin idanunshi, , Nan ya tsaya turmus sai karkade idanu yake, . Nan take kuma idanuwana suka kai ga mararsa inda ya soke wata wuka irin na yan daban nan kafin yan'uwansa suyi wani yunkuri, tuni har na zare wukar a mararsa , A samam makoshinsa na sanya wukar sannan nayiwa yan'uwarsa barazanar, cewa in suka kariso gareni toh tabbas zan yan kashi, . Koda suka ga haka sai dukkansu suka fara ja da baya , . Nima ina ganin hakan na dubi wannan budurwar da haryanzu take kwance gashin kanta a barbaje, sannan bakinta na fidda jini , Nace mata" tashi mu tafi" . Nan ta mike ko dankwalinta bata tsaya daurawa ta nufo bayana . "Kana jefa kanka a cikin matsanancin tashin hankali, lallai kasani muddin ka aikata, abin da kake yunkurin aikatawa toh lallai, sai kayi dana sani , alokacin da dana sanin bazai yi maka amfani ba . Murmushin karfin hali nayi sannan nai duba ga budurwarnan na ce mata ta fice daga cikin kogon . Shi kuwa katon dana sanya mai wuka a makoshinsa ko kwakkwarar motsi ba yayi , a tunaninsa a kowani loka ci zan iya danna hannuna wukar ya lume cikin maqokwaronsa, . Jansa nakeyi muna tafiya har muka kawo bakin kogon a sannan ne na juya na dubi yan'uwansa, "Lallai kada kuyi gangancin fitowa daga cikin wannan kogon , domin muddin kuka fito kuwa wannan dan'uwankun sai de wani ba shi ba" Na fada cikin gargadi garesu. . Nan suka dakata sai muzurai suke, , Maimakon mu haura saman kwarin ta inda na gangaro wato ta bakin titi, sai muka haura ta dayan gefen inda zai bulla dani gidajen mutane, , Duk wannan tafiyar da mukayi ban yadda ko da wasa na kauce da hannuna daga saman makoshin wannan katon ba. . Muna haurowa saman kwarin sai na bankaje katon , nan take ya fada cikin kwarin da mirgine, . Ban tsaya wani bata lokaci ba na kama hannun wannan budurwar wacce bana iya , ganin fuskarta, muka ci gaba da gudu, . Gudu muke wanda ko waiga bayanmu ma ba mayi, nan wannan budurwar ta yi tuntube da wani gwangwani ta fadi, . Sai a sannan ne na tsaya na lura da wajen da muke, muna wani faffadan filine , wanda ciyayi suka dan tsiro kadan kadan a gefen mu na dama wani babban gidane na kece raini . Gaba daya jikin bangon wannan gida a lillike take da kwayakwayai lantarki, wayanda suka haske kofar gidan, . Hasken kofar gidan ne ma ya dan haska wannan faffadan filin da muke ciki, . Nan na duba a gogon wayata, 2:25, Tun danake ban taba ganin musifa irin wadda naganta a yau ba , . Danai duba izuwa wannan budurwar sai naga ita ma ta mike , . Hasken nan ya haska mani fuskarta, Turus kawai nayi yayin da kaina ya kusa juyewa, . Na dan muntsili hannuna wai ko mafarki nake, tabbas a zahiri ne . Kamar ko yaushe fuskarta sai sheki yake a yayin da wasu siraren hawaye ke gangarowa ta saman kumatunta, Sirara kebbanta sun rine da jan baki, . Ba wata bace face RUFAIDAH Yarinyar dana Zuzuce akanta , Ita ma na fuskanci ta ganeni sabida yanayin da fuskarta ta nuna, , Hau hau hau hau Naji daga gefena ina juyowa nai arba da su, , Wasu murdamurdan karnukane su biyu, jikinsu sur gashi, girman kowani dayansu yakai girman kosashshen rago, baki bude suka nufo mu suna haushi, , Tir kashi anyi gudun gara an......... Inji hausawa , Wai karya ta kare bori taci boka Tobe continue , Its Shuraih 99%

TASKU littafina daya 1 part 5

TASKU
kirkirarren labari
NA Shuraih 99%
Littafi na Daya 1
Part 5
.
.
Wannan shine tambayar dana yiwa zuciyata. , Toh ma mezai dameni koma dai wanene ke wannan kuka babu abinda ya shafeni . "Tai mako jama'a! Babu wani bane yazo ya taimakeni!" Naji wata murya na fadi, ta cikin surkukin kwarin dake gefena, Tabbas wannan muryar mace ce , sannan kuma duk yadda akayi tana cikin wani haline . Ban tsaya wani dogon tunani ba na fada cikin kwarin ina fadawa na cigaba da gangarawa, . Nan na isa cikin wani surkukin ciyayi , toh anan ne Mafarin shigata cikin TASKU ya samo asali . Tabbas da nasan ko menene ke shirin faruwa da ni toh da banyi gangancin kara shiga cikin surkukin ba . Ina wuce ciyayin nan, na iske wani dan kogo, batare da wata fargaba ko tsoro ba na danna kai cikin wannan kogon, . Na kunna tocila na wayana yayin dana kutsa kai cikin kogon , Wannan kogon dai irin ramukannan ne da ake tonawa don neman arziki , Babu komai acikin kogon in banda duwatsu da kuma rairayin ciyayi, , Ina kara gaba na ja tunga nayi turus sakamakon abinda idanuwana suka gane mani . Bakomai nagani ba face wata kyakkyawar budurwa, kwance a kasa, sannan wasu karti, su biyar sun zagayeta, . Biyu daga cikin kartin nan sun rike ma wannan yarinya hannu, yayin da wasu karti biyu suka rirrike mata kafafu , a sannan ne wani kato ke kokarin yi mata fyade , , Ita ko babu abinda take illa ihu da karaji da neman taimako, , Sudai wayannan karti zasu kai shekaru talatin dukkansu, sannan gaba dayansu sun sanya bakaken kayane, jaket ce baka ajikinta anyi mata Ado da wasu duwatsu na karfe , . Yayin da wayannan karti suka ganni cikin wannan kogon , Sai guda daga cikinsu wanda yake kokarin haike ma wannan yarinya ya dubeni sama da kasa sannan yace dani cikin wata murya mai kama dana jaki "Kai dan tsako ,Ka kama gabanka tun kana numfashi " . Koda naji wannan zace nashi sai na juya da niyyar na fice daga cikin wannan kogo , Har na fara tafiya sai naji muryar budurwar tana cemani" Malam dan Allah ka taimaka mani, ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka" . Najuyo sannan nayi magana yadda zasu iya jina " kiyi hakuri yar'uwa " . "Yanzu da kanwarka ko wata yar'uwarka kaga za aketa mata mutuncinta ,haka zaka juya ka tafi" Tafada yayin da akarshen maganar tata ta kare da kuka , Ban iya mai da mata da amsa ba sakamakon yadda maganar ya shiga cikin zuciyata . Kawai sai najuya na fice daga cikin kogon , Ina ji tana kirana amma ya zanyi dole ce tasa , domin gaskiya ni ba jarumi bane kuma bana da kirar sadaukantaka a jikina, . Toh koma dae menene ai hausawa nacewa sarkin yawa yafi sarkin karfi , Ayayin danake wannan tunanin ne naji zuciyata ta fara tafasa, ni kaina bansan lokacin dana juya na koma cikin kogon nan ba . Ina zuwa naga wannan katon na kokarin cire mata kaya hakan ne yakara tunzura ni , Nan na nemi wani katon dutse na dauka ina zuwa na sami daidai saitin gadon bayansa , na mai dundu, da wannan dutsen, nan ya kife, , , Koda wayannan karti hudun suka ga abinda nayi wa dan'uwansu sai suka zaburomani tamkar zasu cinyeni danye , Zobe suka yi mani sannann

TASKU littafi na daya 1 part 4

TASKU
kirkirarren labari
daga Shuraih 99%
Littafi na daya 1
Part 4
.
.
Ai bansan lokacin dana saki baki Galala ina kallonta ba .
Koda ta kariso gabanmu saita tsuguna ta gaishemu sannan ta fara magana yayin datake dubana "Kuyi hakuri da abun da nai maku jiya" Bakina na rawa na ce"ai babu komai ," .
"Wallahi jiyannan na rudene sosai shi yasa,kuma na zata Abba zai min fadane shi yasa" ta fadi cikin wata irin murya tamkar bata son fadin maganar,
.
Ta kara dubanmu tace"Sunana Rufaida "
."Sunana shuraih, wannan koh m...."
Mjd ya katseni yayin daya ke fadin "malam barni na sanar da'ita sunana, "
Dariya kawai mukayi yayin daya cigaba"wai nine zai min lamuni,toh Allah yasa ina da baki "
Nanma murmushi kawai tayi, "Mujahid ko kice mjd sunan kenan"
.
Na dan harereshi nace"sai kuma akace ka fadamana nickname ko" .
*******************
Bayan mun yi musayar nombobi nida ita sabida zumunci, daga nan muka rankaya zuwa gidanmu ,sabida cikinmu dake kiran ciroma.
.
Zaune muke muna cin abinci nida mjd anan ne yake sanar dani wani wajen bikin Sallah da zamuje da la'asar wai shi minki,
.
***************
Muna isa bakin get din muka nausa kai ciki sakamakon get din dake bude, anan muka sami wajen parking muka paka motan
.
Samarine da 'yan mata ke ta zirga zirga a cikin wajen ,yayin da wasu yanmata wayanda suke tare da samarinsu, zaka gansu tare suna hira.
.
Yaune zuwana na farko wannan waje ,dun haka sai na nufi bayan wani bishiya domin na dan huta ,
Wani makeken bencine dakure akusa da jikin bishiyar, saman bencin na dane,
Mjd kuwa muna shigowa cikin wajen naga ya nufi wajen wata yarinya daga nan suka ci gaba da tadin su,
.
Daga wajen danake zaune ina hangen samari da yanmata dake zirzirga a wajen ,wasu gungun samarine da yanmata naga sunyi da'ira a wani kebabban waje, daga inda nake zaune ina iya sauraron sautin gular dake tashi,
.
Na tashi daga inda nake zaune na nufi wajen, koda na isa sai naga ashema yan'mata ne da samari keta gwargwazon rawarsu, sai tika rawa ake, ayayin da Dj ya saki kidan Ado gwanja na asha ruwa .
****************
Kwata-kwata. Wajen ya gundureni ,zaman wajen ya fita min arai,
Nan naje wajen dana bar mjd tare da budurwarsa suna zance,
Koda na isa wajen ban samesu ba na duba sama da kasa gaba daya cikin minki ban samesu ba.
. Dana kira wayarsa ne yake sanarmani shi yanzu haka fa babansa ya kirasa, kuma ya nemeni mu tafi bai ganni ba, . karfe 11:24pm agogon wayana ya nuna mini, nan take na fito bakin titi ina neman acaba, duk da nasan da wuya na samu acaba saboda dare da yayi, . Nafi minti talatin ina tsaye a bakin titin amma ko alamar acaba ban gani ba,duk da wani sa'in mashina da motoci sukan wuce jefi jefi, . Nan na yanke shawarar na taka saiyadata har Allah yasa na sami dan acaba, , Nayi tafiya mai nisa sosai har na fara gajiya, a sannan ne na iso angwan lambu,daidai gaban gidan rediyon N B S ,na sami wani dakali na dan zauna don in huta daga nan na cigaba da tafiya, Baccin na hutane na cigaba da tafiya, har na iso wani waje dana duba agogon wayata 1:54 Am Na danyi tafiya kadan kenan sai naji hayaniyar mutane, sama sama dana dan kara gaba ne na fahimci kamar shishshikar kuka ne ke fitowa ta cikin wani sunkuru, Karkaji nace sunkuru ka dauka ko acikin dokar daji nake, a bakin titi nake wani wawakeken kwari ne dogo tamkar kwalbet, shimfide a gefen titin Shi wannan kwari hanyar ruwane idan ana ruwan sama ta ciki yake bi yai wuce warsa, kwarin din cike yake da ciyayi, sannan a saman kwarin gidajene da kuma gidan giya, Dana dan lura da kyau na kasa kunne sai naji shishshikar kukan na fitowane ta wani restaurant, restaurant din yana saman kwarin ne, . Shishshikar kukan ya cigaba da kara hauhawa, nan da nan na fahimci muryar mace ce, . Toh shin wacece ke kuka acikin wannan tsohon daren . Kubiyoni a part 5

TASKU littafi na daya 1 part 3

TASKU
kirkirarren labari
daga Shuraih 99%
Littafi na Daya 1
Part 3
.
.
"Amma Fa daga ninta kaga yar babban gida, " cewar mjd
.
"Ba yar babbar gida ba koma meye sai , amininmu ya shawo kanta" anas yafada yana kallona , yana dariya
.
Na dubesu a tsanake nace "koma dai menene gobe zamu ga gidansu ai" .
**************
Ina Kwance nake bisa kan katifata , idanuwana radau suna kallon katakon silif(batre)
A sannan ne A gogon bangon dake rataye a jikin bangon dakina ya nuna karfe 1:00AM, na dare,
.
Wannan ne ya tunasar dani daga nannauyan tunanin dana fada,
.
Yanzu haka wajen awanni biyu kenan da tafiyan su mjd da Anas
Tun daga lokacin nake ta Allah Allah barci ya daukeni Amma ina dana runtse idanuwana sai fuskarta ta bayyana yayin da siraran lebbanta ke furta kalamai tamkar bazasu furta ba
.
Naso ace na baiyana mata sakon zuciyata ,
Naso ace Na san sunanta
Naso ace nasan gidansu
.
Duk wayannan ban damu dasu sosai ba saboda nasan gobe duka zan sansu amma ,abin dana damu da shi sosai shine, shin zata karbi kokon barana,
Shin zata amince dani a matsayin masoyinta
Shin zata yadda nazama abokin rayuwarta
.
Da irin wayannan tunanin ne har karfe biyu yayi a sannan ne wani nannauyan barci ya ziyarci idanuwana .
***************
Bani da farkawa ba sai wajejen 7 bakwai na safe,
A sannan ne na tashi na nayi wanka sannan nayi kalaci(break) da shike yau Take RANAR SALLAH
.
Wata shadda tace fara mai daukar idanu Na sanya sannan na sanya hula zanna bukar fara sol amma tuntunta bakine sidik.
.
Sai kiran nomban mjd nake amma taki shiga ,
.
Dadai na gaji da kirar sai na fito daga gida , nan na tare dan acaba, nai mai kwatancen wajenda zai kaini,
.
Saukana keda wuya na nufi wajen bakaniken ,
Ina zuwa na tarar dashi yana gyara wata mota, nai mai sallama, sannan nace mai "Dafatan ka idar da gyaran"
.
"Sai oga an idar ko tuntuni"
"Da kyau ai hakan yayi"
Daga nan na shiga cikin motar na tashe ta sannan na hau kwalta,
.
Daidai lokacin dana faka a kofar gidansu mjd , daidai lokacin shi kuma ya fito Yana sanye da shadda shima farace amma bai sanya hula ba,
Sai wata kalar aski daya yi mai taken dakalin shedan(punk)
.
Yana ganina yazo muka tafa sannan yace dani" baba ai nasan sai ka rigeni isa wajen bakaninkennan "
'
"A'a nai ta kiran wayarka amma ban sameka ba shiyasa kawai naje na dauko"
.
"Oh shit wayan tana hannun kanwata wallahi, amma no problem, muje kawai"
Ya bude gidan gaba na mai zaman banza ya shige,
"Ina muka nufa" nafada yayin da nima nake kokarin shigowa cikin motar,
"Masallaci mana"
"Ok" kawai na fada sannan na tashi motar muka nausa
*************
Hon na rangada a bakin get din gidan sannan wani tsakurarren mai gadi ya fito hannunsa rike da kulki , sai da yazo daf da motar ya kare mata kallo sannan ya je ya bude get din
.
Awan mu biyu kenan da tashi daga masallacin idi,
A sannan ne muka rankayo izuwa adress din data bamu,
.
Tabbas gidan ya hadu ba laifi muka nufi wajen parking
.
Bayan mun parking motar mun fito mun tsaya,
.
"Toh sai mu shiga koh yallabai" mjd ya fada yayin daya fara tafiya yana dumfarar kofar da zata sada shi cikin gidan,
Nan nima na mara mishi baya
.
Maigadin ne yai mana iso cikin rantsastsen falon maigidan,
Muna zama shima ya fito ya dubemu sannan muka gaisa,
Bayan mun gaisa ne yake tambayarmu " ko kune rufaida tace mani zaku kawo mani mota"
.
"Kwarai kuwa mune nan baba" Mjd yabashi amsa "Kuyi hakuri da abin daya faru jiya"
.
"Babu komai baba ai komai mukaddarine daga Allah,"
.
"Ni kaina saida nayi mata fada akan irin abun datai maku da tace sai kun gyara motar"
.
"Samsam,karka damu da wannan ai komai ya riga ya wuce" Sai hira suke shida anas Ni ko sainaji wata sanyi acikin raina sakamakon jin sunanta danayi RUFAIDA na sake maimaita sunan a cikin zuciyata,
Nan na shiga rarraba idanuwa ko zanga ci sa'a na ganta, domin so nake na sake ganin kyakyawar fuskarnan tata,
.
Har muka idar da magana da mahaifinta wanda bai sanar damu sunansa ba
Muka fito daga cikin falon sannan muka durfafi kofan da zata sadamu da farfajiyar gidan
.
.
"Sannunku da zuwa" naji i muryar da bazan taba manceta ba acikin rayuwata, tana fadi ta bayana
Juyowar da mukayi ne mukai arba da,ita kamar kullum yauma tana cikin wani dogon rigane harkasa sannan ta yafa wani gyale wanda yai matukar dacewa da kalan rigan jikintan,
.
Ai bansan lokacin dana saki baki Galala ina kallonta ba . Tobe conti
shin ku na son ku riga samun littatafanmu da zarar mun dora to kuyi sauri ku subscribing namu
Join Our Newsletter