+2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria

Download and read free hausa novels

TARAR ARADU littafina daya 1 page 14

Tarar Aradu
Littafi na daya 1
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 14
.
.
Toh jama'a sakamakon rashin sauran fallayen littafin
hakan yasa, dole da kaina zan karasa maku wannan labari
sai ayi hakuri da kura kuran da za'ai arangama da su
.
Ahalin yanzu nida tsuntsun da'ake kiwonsa akeji duk
daya
muke ,
Domin kuwa bana fita ko'ina daga shago sai shago,
Sai idan angama abinci a miko min ta kofa mai shiga
cikin
gida ,izan kaga na fita to da daddarene ko da asubah
idan
zamuje sallah nida yayana
.
Wata rana da asubah na fita sallar asubah nida yayana
toh dama ni idan na fita salla nida yayana bama dawowa
gida sai safiya domin kuwa tsayawa muke a masallacin
muita karatu har sai gari ya waye, kaman kullum yau
hakan ta faru,
Mun fito muka nufi gida ina zuwa kofan gidan gabana ya
buga sakamakon ganin kfan dakina danayi a bude,alhalin
kafin na tafi masallaci sai dana sanya dan makulli na kulle
dakin gaba daya
.
Na dai daure na doshi dakin ina bude dakin na saki wani
salati sakamakon abunda nagani acikin dakin,
Wata mata daga ita sai shimi iya cibiya da wani dingilallen
wando iya cinya tana kwance kan katifar barcina,
Ina bude dakin matar ta tashi tayi mika, sannan tadan
mummustsuka idanuwanta ta dubeni tace yauwa malam
kai nake jira dama tun dazu nake son na tafi,
.
Na dubeta baki bude cikin mamaki nace mata wacece ke
sannan meya kawoki cikin dakina,
Tayi tsaki tace kaji rainin hankali kadauko ni kuma kana
tambayata ko waye ni lallaima, malam ka bani kudina
yanzu ina son zan tafi
.
Ke dan ubanki wani kudin zan baki, yi maza ki fice daga
cikin daki yar iskan karya, na fada cikin fusata,
Ai nan matannan tai tsalle ta cakumemin gaban riga
muka fito daga waje tana cewa wallahi sai ka biyani kudin
kwana na, tayaya za'a yi ka dauko ni ka kwana dani
sannan kace baza kaa biya ba ai wallahi sai ka biya,
.
Ba'a bata wani lokaci ba har matannan ta tara min jama'a
nan raina ya baci na tsinka mata mari ai ba shiri ta sakeni,
na cigaba da jibgarta da kyar mutanen angwa suka
kwaceta a hannuna amma duk da haka matannan sai ihu
take ita sai na biyata kudinta, a haka yayana yazo ya
samemu
.
Yayi bakinciki sosai kuka ne kawai baiyi ba ya tambayeta
nawane kudin bakunya bare tsoron Allah matannan tace
dari uku ne, cikin kunan rai yayana ya ciro kudin ya bata,
matar ta wuce dakina ta kwashe kayanta tazo wucewa ta
dubeni tace Assha, ai wallahi daga yau baka dauko ni
dakinka, sai de mu ringayi acan yadda muka saba,tunda
kai kace tsiyane aranka,, ko kallonta banyiba donni abun
har mamamki nake ni daban taba ganinta ba,
.
Na dafa yayana nace wallahi yaya....ya katseni ta hanyar
daga mani hannu yace umar da na zata abun naka zai
tsaya kan sace sace ne toh tunda takai ga sai ka bata bin
suna ka kawo karuwa cikin gidana toh ka kwashe naka ya
naka ka kara gaba kasan inda dare ya maka daga yau
kabar gidannan kenan
.
Iya tashin hankali yau na gani, kuka ne kawai banyi ba,
Cikin kankanin lokaci na shiga shagona na dauki wata
tsohuwar jakar kayana, na dauki hanya wacce bansan ina
na nufa ba
Tafiya kawai nake zuciyata sai radadi take yimin A lokacin
da hotunan abubuwan da suka faru dani suke yawo a
kwalkwata tamkar a majigi,
Duk da ya kasance wunin ranan bansa ka komai a cikina
ba, amma hakan bai sa naji yunwa ba
Na isa wata angwa na samu gindin wani waje na zauna na
kifa kaina a cikin guiwowina, ayayin da tunani iri iri keta
zarya a kwakkwana, ji nake tamkar na kashe kaina na
huta
.
******
Na tashi na nufi wani masallaci domin yin sallar Isha'I
domin kuwa yanzu na tabbata mutane ko sun gani ba
zasu shaidani ba, bayan na gama sallar ne sai kwanta a
masallacin da nufin na kwana a masallacin in yaso gobe
da safe sai in wuce kauyenmu wajen iyayena,
Mutane daddaiku ne sukayi saura a cikin masallacin har
barci ya fara dibana sai naji ana tashi na na dago da kai
domin naga waye wannan
"Malam tashi koh zamu rufe masallacin ne "
Su biyune suna sanye da manyan kaya
Kallo daya nai masu na ayyana araina kodai limaman
masallacin ko kuma wasu malamai na daban
na tashi cikin rashin jindadi na fita daga masallacin na
samu wani dan kewaye a jikin masallacin na kwanta,
Bayan sun kulle masallacin ne zasu tafi sai naji dayan
yace "malam ladan kaga wannan yaro ya koma can ya
kwanta kuma, da alama matafiyine don ga shi dauke da
Jaka"
Wanda aka kira da ladan yace"malam liman kenan ai
wannan yaro daka ke gani kasurgumin barawo ne, sau
uku ana kamashi a kasuwar kwari, yanzuma daka ganshi
anan inaga koh ya lababo ne ya sace mana mita,ko kuma
mic"
Liman najin haka sai ya rike baki yace "assha "
Sai ya daga murya da alama wasu yakewa magana yace
"kai samari kuzo ku jibgi wannan mara kunyar barawon,
tun kafin ya kassaramu"
.
Ina jin haka ban san lokacin dana zabura a guje ba na
tsallake, dan karamin katangar daya katange gewayin
dana ke kwance na ranta ana kare, inajin ihu da
kururwan mutane suna cewa atare barawone atare haka
na ringa cin uban gudu har na fice daga angwar gaba
daya, ina shawarar na tsaya kenan sai naji wani Abu mai
nauyi ya bugi kaina daga nan kuma sai ji nayi na kife akan
wani ruwa ruwa mai wari, daga jin wannan wari na gane
warin giyane ko na aman giya,
Idanuna dishi dishi suke gani, wani katon mutum nagani
ya tsaya akaina yana rike da wata katako 2 by 2, mutumin
ya sunkuyo da kansa daidai kunne na yace
"Umar dan wasa daga yau wasanka ya kare , dun kuwa
yanzu zan aika ka kiyama, dama sakamakon irinku kenan
masu taurin kan tsiya"
Ya daga wannan katakon sama da nufin ya buga mini
aka.........
.
Masu karatu anan muka kawo karshen littafin TARAR
ARADU na daya 1
Kaman yadda kamin mufara wannan littafi na fada maku
cewa 1 and 3 kadai nake da su bani da 2, dun haka gobe
zan fara post na TARAR ARADU littafi na uku 3 Allah ya
kaimu da rai da lafiya
$
TARAR ARADU
(m) Umar Lawan Abdul
Littafi na daya 1
Typing Shuraih Usman
.
.
Domin download na wannan littafi dama wasu sauran
littatafan sai ku shiga shafinmu anan kuyi like
Like:- www.facebook.com/hausaebooks

TARAR ARADU littafina daya 1 page 13

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 13
aranar unguwarmu sai da daddare nashiga........
********* ************ ********
Ahalin yanzu nida tsuntsun da'ake kiwonsa akeji duk daya
muke ,
Domin kuwa bana fita ko'ina daga shago sai shago,
Sai idan angama abinci a miko min ta kofa mai shiga cikin
gida ,izan kaga na fita to da daddarene ko da asubah idan
zamuje sallah nida yayana.
Shi kansa rashin jituwa mai karfi ta shiga tsakaninmu.
Abisa abunda yakira cimasa mutunci.
Nayi masa rantsuwa da Allah akan duk abubuwanbani da
hannu aciki yaki yarda.
Sai yanzu na fuskanci ashe irin wasan da mutuminnan
yake nufi kenan.
Hakikanin gaskiya wasan nasa bantaba ganin wanda
yakaishi muni ba, sai dai duk wannan bana zaton zan bar
farida,domin kuwa kaunarta ta rigaya tabi jikina.
Yau iatace rana ta farko dana shirya zanje wajenta tun
bayan da'aka yimin sharri.
Bakomaine yasa na daga kafa illa tsabar bakin cikin dake
damuna.
Ahalin yanzu kuka awajena babu wuya domin kuwa da
zarar na tuna bana control na kaina abinci ma kadan
nake ci.
Na isa goron dutse da kimanin karfe tara na dare .
Badon komai ysa nayi dare hakaba sai don gudun kada
wani wanda yake kasuwar kwari yaganni ya tona min
asiri.
Tuni su farida rufe gida, nasani abune mai wuya ace wai
bacci take kasancewarta mai matukar kwazo, na
kwankwasa kofa.
Bada jimawaba naji takun kafa
"Waye"
Aka tambaya muryar farida ce
"Umar ne"
Na bada amsa tuni ta gama shaida muryata nan da nan ta
zare sakata takuma bude kofa kawai naga ta fashe da
kuka.
Nayi mamakin abinda yasa haka , kodai dun na dade
banzo bane?
Muka dunguma cikin gida kukantane yafoto da hajiya yau
maimakon gaisuwa kuramin ido kawai tayi,ta kuma rike
baki
"Ashe zaka sake dawowa gidanmu umar, na dauka bazaka
kara takowa ba"
"Me zai hanani zuwa mummy?"
Itama sai naga tafara kwalla
"Kai kuma umar hanyar da za'abi da kai kenen"
Sai nagane ashe labarin abin dayafaru tuni ya iso
garesu.banyi mamaki ba domin kuwa goron dutse
unguwace data kushi yan kwari da dama.
Nida farida muka zarce daki alokacin datake ta faman cin
kuka.
"Umar nafadamaka muddin kana tare dani bazaka sami
kwanciyar hankali ba amma ka ke keshe kasa kaki yarda
to yanzu daka gani da idonka ai ka hakura"
Tacigaba da kuka
"Dakata farida"
Nace da ita
"Shin wai kin daina kaunatane ko yaya"
Ta tsuguna agabana
"Umar bazan daina kaunar kaba har abada"
Nayi murmushi
"To indai hakane farida banga wani abin dazai sani in
janye ba,kisani na dora tubalin soyayyarmune akan gini
biyu,imma dai nasami cikar burina imma a kirgani a
mutum na hudu daya rasa ransa, kisani ahalin yanzu
cigaba da kaunarki ya fiyemin sauki,domin kuwa mutuwa
afagen dagar neman aurenki yafiyemin mutuwa
asakamakon hauhawar jini"
Na sunkuyo gareta
"Farida izan narasaki bazankai labaraiba"
Kuramin ido kawai tayi tana kallona , unkai tsawon minti
daya mun zurawa juna idanu, daga bisani fuskarta ta
yaye izuwa murmushi.
"Oh! Umar Allah yabar mu tare har abada"
Na mayar da murmushinta sa'arda bakina yake motsawa
a kokari na lalubo kalmar amin .
Tamike tsaye akuma loakci guda da tazauna akan hannun
kujerata ta dubeni fuska da fuska
"Da ka gujeni umar da mutuwa zanyi, bazan iya rayuwa
babu kai ba "
Na girgiza kai
"Bazan gujekiba farida har abada koda kuwa za'rika
yankan naman jikina
(Kaji soyayyar gaskiay kenan
Its shuraih 99%)
******* *********** ********

TARAR ARADU littafina daya 1 page 12

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 12
Nayi mamakin irin wannan sammako da alhaji ya bugo a
yau mu dukkaninmu ya rigamu zuwa.
Hatta ibrahim wanda shi yake tafiya da makullai.........
Naga saukar ibrahim daga mota kafin mu karaso to
menene ya fito dashi?
Kodai irin abinnane domin yakama mai kin fitowa da
wuri.
Na durkusa na gaidashi jamilu ne kawai bai iso ba.
Ba 'afi minti biyar ba shima ya'iso akafara hada hada
"Kuzo inji alhaji"
Ibrahim yafada yana raba mana idanu
Muka nufi wajensa cikin rashin sanin abin da kiran ya
kunsa.
"Ku zauna "
Yace damu lokacin daya ke nuna mana benci.muka zauna
daura da juna
"Bawani abune yasa na kirakuba illa wani abu daya afku
wanda banji dadin saba.ya nunani nida jamilu jiya ku na
aika cikin motata , to amma dana isa gida sai natarar da
abin da baiyimin dadi ba, wanda banga amfanin abar min
kes ba alhali an dauke agogon.
Wand yin hakan babbar rainin hankaline da bazan juraba
.
Abin dana keso nasani shin jamilu kaine ka zare agogon
ka kai kedin kawai ko kuma umar kaine ka dauki agogon.
Kuna iya bani amsa anan izan bahaka ba kuwa kuna iya
shaida ma yansan da"
Uka kalli juna nida jamilu akuma lokaci guda muka fara
rantsuwa ,wallahi mu bamu dauka ba.
Alhaji yayi murmushi
"To shikenan kuzauna anan "
Yazare sailula bisa ga dukkan alamu yana ma yansanda
wayane. Bada jimawaba sai gasu sun iso su hudu
"Gasunan ku tafi dasu gida jensu ku bincikomin agogona
"
Aka tasamu agaba .
Nidai babban abin daya dameni aga nazo da yansanda
gida a matsayin ana zargina da sata.to amma badan
hakaba to da ina iyayin komai ma
Musamman tunda nasan bandauki agogoba.
"Ku hau nan"
Yansandan sukace damu lokacin da muka iso gindin
motarsu.
Bayan mun zauna kan bencinne aka fara tambayar inda
za'a nufa .
"Ana iya zuwa ko'ina ma "
Nabada amsa cikin halin yarda da kaina .
"Wanene umar"
Daya daga cikin yansandan ya tambaya.
Na dora yatsana a kirji lokacin da nake nuna kaina
"Gidan ku za'anufa"
Dansandan yacigaba da fada.
"Dama kana da kyasa kyasan sata harbiyu abaya"
Nazare idanu sakamakon jin kazafin da bazai yiwu na
musa shi ba.aka sanar da direban inda za shi.
Bai gushe yana tuki ba saida muka iso kofar gida.
Bakom al'amarin ya sanya tulin yara taruwa, cikin
kyarma nasa kuba na bude dakin , tare da yansanda
muka shiga.
Suka shiga laluben kowanne lyngu da kowanne kusurwa.
Badon bakin cikin daya ke cina ba da babu abinda zai
hanani dariya.
Sakamakon dagewar da yansandan sukayi neman agogo.
Wanda hakan tamkar leka tundin kulline domin gano
rakuminka daya bata.
Tuni sun gama birkita ko'ina amma haryanzu ba'a ga
agogo ba.
"Muje a duba cikin gida"
Daya daga yansandan yafada.
"Dakata tukunna"
Inji wani dayake kokarin daga katifata.kyalkyalin daya
bayyana a karkashin katifar shi yasanar dani akwai wata
ajiyar da bansan da'ita ba,
Ba komai bane illa kyakkyawan agogo yana walkiya,
daukewar numfashina yazo daidai da lokacin dawani
radadi ya ratsa kuncina.
Sakamakon wani bahagon mari da daya daga cikin
yansandan ya kwadamin.
"Kace bakai kasata ba"
Nan danan bakina yafara fadin abin dani kaina nasan
baza a yarda da shi ba.
"Wallahi yallabai sharri akayimin"
"Barawon banza barawon wofi dama tun sa'arda kazo
kake yimana sace sace kaboye kudin alhaji, kaci sailula ,
yau luma gashi ka saci agogo"
Jamilu kenan ya hauni da bambami sa'arda muka fito
waje!
"Barawo! Barawo!! Mai kasata? Agogo ya sunan ka? Umar"
Wata kwarya kwaryan waka kenan da yara suka kirkirota
bayan da'aka watsani mota akafara tafiya.
Aguje sukabi motan suna raira waka , basu rabu da muba
saida muka hau titi.
Nasha zagi kala kala da kuma mari dabam dabam kafin
mu karasa.
Ahaka muka iso har kasuwar kwari daya da ga yansandan
na cumuimiye da kuquna . Ya kwadamin mari sa'arda
yake kokarin dankwafar dani agaban alhaji
"Alhaji yaron tsinannen barawone daya kamata a
ladabtar dashi"
Yamika ma alhaji agogon kafin kace meye tuni mutani
sun cika wajen.
Kama daga kwastomomi zuwa masu kanti.
"Allah wadaranka"
"Allah tsinema"
"Allah watsa ka"
Sune mabambantan lafuzzan dake fita daga bakin
mutane.
Wadansu har basa samun daman ganina sabida
cunkosan mutane.
Zazzafan radadi yarinka bin jikina, ba radadine na zafin
duka ba 'a'A radadine na mamakin sharrin da'aka yimin
da babu daman na musa shi, babban abinda yafi damuna
shine sunana daya riga yabaci akasuwa da
unguwarmu,toni yanzu da wacce fuskar zan ringa kallon
mutane.
"Wayyo Allah umar kacuceni kaci mutuncina"
Muryar yayanace lokacin daya iso yana kuka, ya nufo
kaina da gudu yansanda suka rirrikeshi.
"Ku kyaleni na kasheshi tunda bashi da sauran amfani"
Da kyar yansanda suka janyeshi baya
"To shikenan daga yau umar na sallameka kar ka kara
fitowa indai akwai mutumin da bama shiri dashi bai wuce
barawo ba"
Alhaji kenan loakci na farko dayayi magana tun bayan
isowar mu.
Ya sallami yansanda, da sunso abarsu su tafi dani alhaji
ya hana 'aka barni anan .
Har saida jama'a suka watse sannan na. Tashi, aranar
unguwarmu sai da daddare nashiga........
AYYA JIKI MAGAYI
DAMA DUK WANDA YACE ZAI TARI ARADU DAKA TO
LALLAI SHIMA YASAN SAKAMAKON
(Maudu'I)
Izan da kaine umar zaka cigaba da soyayya da farida ko
ko zakayi hankali
Waitin for sharhi
Zanci gaba
Its shuraih 99%

TARAR ARADU littafina daya 1 page 11

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 11
Bayan dana karya kumallo sai najawo wata bakar jaketna
na dora sakamakon sanyi da akatashi da shi.
Sai kawai na nufi kasuwa muka ci gaba da hulda kamar
yadda muka saba ........
Da rana ta raba sai kuma zafi ya kori sanyi,
Wannan yasanya kowa cire rigar daya kara .
Muka rarrataye.
Da alamun yau alhaji agajiye yake ,domin kuwa tunda
yazo ya dare kujera yake ta gyangyadi abinsa.
Sailularsa kashe alarm din yayi domin kar adameshi.
Kawai ya dorata ahannun kujera .
Bai farkaba sai bayan la'asar shima sai da muka yo sallah
sannan na tasheshi
Yayi mika da hamma sannan yafara lalube-lalube ba
musan kome yake nema ba sai bayan daya rasa sannan
ya dubemu
"Wai ina sailulata take?"
"Ina kuka sanya min sailulata"
Duk muka yi shiru,kawai sai muka fara rantse-rantse
kowa yana fadin bai gantaba.alhaji yafara salati
"Da batan sailular nan gwara batan kudin da'aka
sayeta,manya manyan abokan mu'amalata ta taurai suna
tuntubatane ta wannan layin,akwai kuma nombobi da
dama wanda a sailular kawai na shigar dasu,ciki kuwa
harda wani mutumin danakeso na tuntuba in anjima don
Allah duk wanda yasan inda take yafada zan bashi dubu
hamsin"
Babu wanda yayi magana acikinmu.
Ahaka alahaji yafita akaba da cigiyar sailular duk
kasuwa.amma shiru kakeji.
Duk yanda akayi de wanine ya lababo ya saceta.
Bayan alhaji yadawo daga sallah sai ya zauna akan
kucjera.
Ko magana ma bayayi saboda tsabar takaici yananan
zaune har kusan sallar magriba.
Dif nepa suka dauke wuta ba'aganin komai agurin sai dai
in ka kura ido sosai zaka hango irin kwaronnan
"makyallu"
Koriyar wuta nata fita daga bindinsa
Yayi kememe abinsa ajikin bango.
Jamilu ya tabo ibrahim "dubi hikimar Allah"
Wai duk wannan haske daga bindin kwaro yake
Ya jinjina kai
"Kadan kenan daga hikimarsa"
Alhaji ma ya waiwaya wajen domin yagane ma idanunsa ,
Jamilu kuwa yace sai ya daukoshi.
Adai dai lokacin haske yagama kantin sakamakon
generator da'aka tayar,
To amma kwaron ya shige cikin kaya wutar kawai ake
gani.
Dana kura ido sanaga ashe ma rigata ya shiga.
Jamilu ya laluba ,sai naga ya hada. Gami da fadin "kai"
Ya kuma ja dabaya
"Menene?"
Ibrahim ya tambaya
"Ba kwaro bace ashe sailulace"
"Wace irin sailula"
kuma na tambaya fuska a yakune
"Sailula nawa kasani"
Jamil yafada loakcin dayake dauko rigar,
Akazo da ita gabanmu aka sanya hannu aikuwa sailular
alhajice, wai ashe kyallin danjar sabis muke hangowa
Alhaji yai gauron numafashi ya mika hannu ya karba ,
nikuwa alokacin nawa numfashi ya dauke (nima nawa ya
kusan daukewa da kyar na seta hanaklina ,lol Shuraih
99%)
Akwai kallon yaya haka ?
Da fuskokin mutanen ke dauke dashi bayan kallona na
tsayin lokaci da alahaji yayi sai kawai yakada kai ya fita .
******* ************** *********
Ahalin yanzu duk wani amincin dake tsakanina da jama'a
akasuwa yakau .
Hakan bakaramin kuntata min yakeba
Alhaji dai yadena aikena ko'ina izan kuwa nazauna kusa
da mutum ko carbi ya fitar sai ya mayar da abinsa aljihu.
Wai gudun kar na faki idonsa na dauke.
Duk inda na nufa kuwa kaga ana C.I.D na hatta da randa
izan zan sha ruwa sai atsareni da ido wai duk karna faki
ido na tura modar aljihu
(hahaha sai ni masoyi shuraih 99%)
Kai abubuwan takaici dabam-dabam
Ahaka na cigaba da zama cikin zullumi da bakin ciki .
Izan kaga na saki raina to tabbata muna tare da farida
don gudun karta gane halin dana keciki.
Inanan rakube a cikin kanti sai gwani alhaji ya shigo .
Da ganinsa kaga babban mutum akwai wani mutum biye
dashi alhaji ya mike tsaye suka gaisa
Sannan ya sami waje ya zauna
"Alahi agogonne na kawomaka"
Yafada lokacin dayake duban mai gidan mu
"Yauwa! Ansamo"
Alhajinmu ya tambaya
"Kwarai kuwa"
inji wacan mutumin
Lokacin dayake karbar wani dan akwati daga hannun
mutumin da suka zo tare,
Da bude akwatin sai ga wani walwali, agogone na danyen
gold mai matukar tsari ,
Alhaji ya jinjina kai
"To shikenan sai mun hadu"
Mutumin ya mike
"To sai na ganka"
Suka yi sallama yatafi alhaji yaba ma jamilu akwatin
"Ungo wannan kaimin motata, ka bude aljihy(glove
compartment) ka sanya min aciki"
Ya karba yatafi ba'a jima ba ya maido wa alhaji makullin
"Nakai"
Aka cigaba da harkoki anahaka har loakcin sallar la'asar
yayi , nida Alhaji muka fara tafiya masallaci da muka
dawo sai jamilu da ibrahim suka tafi,
Ana haka ne akayo wa alhaji waya ya dauka suka fara
tattaunawa,
Wani mutunne yakeso abashi cikakken addreshin wani
kamfani a ingila
Alhaji ya dubeni loakcin daya ke mikomin makulli
"Don Allah kaduba kan seat din baya akwai wani karamin
littafi kadauko minshi kayo sauri"
Na karba na tafi aguje ba'adadeba na dawo da littafin
.Alhaji yabashi adreshin sannan yabani na mayar ,
akacigaba da sabga .har lokacin tashi yayi akabani kudin
mota kamar yanda aka saba nakama hanyar gida.
********** ********** *********
Nayi mamakin irin wannan sammako da alhaji ya bugo a
yau mu dukkaninmu ya rigamu zuwa.
Hatta ibrahim wanda shi yake tafiya da makullai.........
YAU KUMA WATA KALUBALECE
KE KALUBALAN TAN UMAR
Don't trouble troubles
Till troubles trouble you
Shuraih 99%
Zan cigaba

TARAR ARADU littafina daya 1 page 10

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 10
********** ********** ********
Ahankali kwanaki suka cigaba da zukewa irin zukar da
takarda ke yiwa ruwan biro.
Ahaka nafara kirga makonni
Ko kusa bazaka hada samuna na kasuwa dana makaranta
ba.$
Bada dadewaba nafara haskaka kantin.
Sakamakon iya mu'amala da jama'a da kuma ilimina
hatta kantinan makota idan akayi bakon bature ni suke
zuwa su kira.
Wannan si yasa akafara yimin lakabi da bakin bature.
Na shiga ran alhaji matuka sai yafara aikena wurare
dabam dabam sai ya zamto kullum da alhaji yafito toni
nagama zama .
Jeka nan tafi can kai wannan karbo wancan, kai dade
sauransu.
Amma duk samunnan danake yi dinki daya kawai nayi.
Sauran kudadena kuwa nakan kashesune aharakan hada
lefena.
Wannan yasanya watarana daya daga cikin abokan aikina
yake tambayata
"Wai kai umar mai kake da kudine?'Ullum kana samu
amma ba'agani jikinka"
Nayi dariya
"Jamil kenan kowanne mutum kasan yanada manufa,
abin dayasa kake ganin halka bawai kwalliya kuka fini son
yiba.
Bukatun kudi danakedasu shiyasa kukaga ina tattalawa"
Yarike baki
"Kai kuwa wani irin bukatune wayannan dahar sai ka
takura kanaka zaka biya?
Nagafa ko aure baka dashi"
Nakalleshi
"To mai aurene kawai yake da manyan bukatu?ka tsaya
idan lokaci yayi zaka gni"
Dai dai wannan lokaci alhaji yashigo ,wata kyakkaywar
sailulace ahannunsa.
Ni dai tunda nake bantaba ganin kan waya mai kyawun
na Alhaji ba.
Wannan yasanya akullum alhaji yana waya nakan bishoi
da ido har yagane yanda nake nuna sha'awata da kan
wayar wannan yasanya shi yimin karin bayani akan
muhimmancin kan wayar.
Ya kuma shaidamin naira dubu dari biyu yasiya nayi
matukar mamaki da jin haka .
Dubu dari biyu ai kudin kyakkyawar motane .
Da alhaji yazo ya tsaya akusa damu
Sai naji ashe suna tattaunawa ne da wani mutum mai
harkar setlit.zance da akeyima zai kawo setlit ne guda
biyar.
Kuma duk za a sanyasune a sabon gidan da alhaji yake
ginawa.
Ni alahaji har mamaki yake bani komai nasa sai ya
burgeka.to amma mai zaiyi da wannan sabon gidan alhali
ko haihuwa bai taba yiba.
Hirar tasu takare akan cewa za'a aikomasa da kudin gobe
da rana.
(Umar harka fara bani tausayi)
Shuraih 99%
********** ************* ********
Ina cikin cin abin ci alhaji yakirani sai yamiko min key din
motarsa
"Je ka kabude but akwai wata jaka kadaukomin"
Nakarfa na tafi da gaggawa
Ina dauko jakan saina gane kudine aciki babu tantama sai
na baiwa alhaji zan tafi ya tsaidani
Ada nayi zaton zasukai miliyan daya ashe dubu dari da
hamsinne bako maine yajawo hakan ba sai kasancewarsu
yan wazobiya
Ya dubeni
"Kaga kudinnan kakai wa malam abba mai dishi su"
Anan IBB malam abba yake amma naira dari biyu
akabani kudin mashin.
Nafito na tsaya abakin titi shiru babu wani dan acaba
mara fasinja .
Wannan yasa na yanke shawarar nafara tattakawa akafa
har zuwa loakcin da zansamu dan acaba.
Nayi tafiya mai dan nisa .
Kawai sainaji anyayimeni nayi sama bansan
komaeneneba.
Saidai na jini acan gefe guda nayi kokarin namike amma
ina juwa ta daukeni dole nakoma na zauna .
Sai bayan yan dakiku nayi kiliya .saboda haka na lalubi
jakata
Amma babu ita kuma babu dalilinta .
Tashin hankali shin wai meyafaru danine
Bandai san takamaiman abinda ya yayimeniba.
Kuma gashi babu mutane a eriyar wajan
Na duba jikina babu inda naji ko da kwarzane toni yanzu
yazan saka kaina zuwa zanyi wajen alhaji ko kuwa
karasawa zanyi inda aka aikeni?
Duk biyun dai kusan ma'anarsu daya kusan duk inda naje
dai bani da abin fada.
Wannan yasa na share waje kawai na zauna (da yafimaka
umar lolx shuraih 99%)
Ina wajen la'asar tayi.nahada kai da gwuiwa na rasa me
yake min dadi.
Kawai sanaji ana tabani.
Dana daga kai sainaga ashe jamil ne.
"Lafiya kazo nan kazauna"
Na maida kaina batare dana bashi amasa ba
"To kazo alhaji yana kira"
Da kamar bazani ba sai wata zuciyarta ce jeka.
Na bishi muka rankay zuwa kasuwa.
Alahaji ya dubeni
"Ya akayine umar nayi waya ance baka kai kudinba"
Na sunkuyar da kaina kasa cikin rashin sanin abinda
yakamata nafada
"Ina kudin suke"
Sai naji bakina suna fadin
"Sun bata"
"Kamar yaya sun bata?"
Yatambaya cikin mamaki.
Ni kaina nasan bakina yayi gidadanci daya bada wannan
amsar.
Na bayyana masa duk abinda nasani.
Ya dade yana kallona daga bisani ya mike tsaye game da
faidn
"Allah ya kyauta"
******* ************ ********
Nacigaba da zama akasuwa cikin rashin jin dadi
dominkuwa ina fuskantar wani irin kallo daga abokan
aikina .
Alhaji ma kuma ya canza taku .
Ahalin yanzu baya aikena nakai kudi ko kuma na karbo
,nasan bakomai bane ya jawo hakan ba illa bacewar jakar
kudi.
Wannan yasanya akullum takaicin duniya na damuna .
To amma yana iya abin sai hakuri .
Bayan dana karya kumallo sai najawo wata bakar jaketna
na dora sakamakon sanyi da akatashi da shi.
Sai kawai na nufi kasuwa muka ci gaba da hulda kamar
yadda muka saba ........
WATA AZAL DIN KUMA
Keep following
Its shuraih 99%
Zan ci gaba

TARAR ARADU littafina daya 1 page 9

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 9
Saida nashafe wata guda cur harda kwana shida amma
kullum naje sai yace ba'azo an tayaba dana lura sai naga
nima in naje har nadawo ko kuda ban taba gani ya sauka
akai ba .
Wannan ya sanyani yake shawarar na bari sai sati-sati
narika zuwa.
Ina nan ahaka atsakiyar sati nabiyu wanda har nafara cin
bashi saiga wani yaro har gida
"Wai kazo anzo sayen baburrinka"
Nan danan na zari takalma .
Don tsabar sauri kamar na tsahi sama.
Duk da cewa yaron da gudu ya koma amma duk kusan
tare muka isa.
Wani dattijone rigarsa duk dauda yayi furtutu dashi.
Da gani sana'arsa bazata wuce saida harawar dabbobi ba
na sunkuya na gaidashi
"Kaine me wannan babur din"
" Nine baba "
Na amsa masa
"To nasaya naira dubu uku"
Kaina yasara jin kudin tamakar za'asiyi mataccen keke
"Haba baba kadai fadi gaskiyar abinda kasaya"
Ya kalleni
"Kai yaro dattijo kamata baya ciniki da tayi inka sayar to
inbaka sayar ba nakara gaba"
"Kadai kara baba"
Nasake cewa dashi, sai kawai yakada kai yatafi hakika ba
zai kara ba.
Na tuna da dadewar baburdin awajen kotayawa ba'ayi
ba.
Kuma lallai innabari dattijonnan yatafi balallaine asiyaba,
sai kawai nabishi dagudu ina cewa
"Dakata baba"
Baiko saurareni ba ganinhaka yasanyani shan gabansa
"Ansiyar maka baba"
Ya kalleni fuska a turbune yacoi gaba da tafiyarsa,
Nan nashiga hadashi Allah da annabi da kyar na samu
yadawo yabiya .
Na baiwa mai gyaran dari uku yaron daya kirani kuwa
naira hamsin.
Sauran kudin nayi aniyar in na biya bashi sai in ajiye in
rika gutsura ahankali.
***** ************ ********
Nayi tagumi sakamakon wannan tsaka mai wuya dana
shiga al'amarine da banga alamun karewarsaba
"Salamu alaikum"
Akafada daga kofar shagon muryar yaya nane.
Na amsa gami da kokarin mikewa ,sai gashi yashigo.
Nayi masa sannu dazuwa da kuma barka da yamma .
Yasami kujera yazauna
"Umar nasamo maka aiki awajen wani mutum
akasuwarmu"
Sai naji tamkar natsahi narungumeshi tsabar farin ciki,
nafara jero godiya kala da bam da bam
"Ya'isa ya'isa"
Yace dani sa'arda yake dagamin hannu
"Tsaya kaji yadda al'amarin yake"
"To yaya"
Nafada sa'arda na kara matsowa .
"Kasaida hankalinka sosai ayaransa na yanzu babu wani
cikakken mai ilmi.
Shi kuma burinsa akullum yasamu wanda zai
taimakamasa wajen harkar oda.
To ammam shiru kakeji, duk wanda yasamo daya fara sai
cin amana ya biyo baya.
Saboda haka inhar kai gaskiya ka gama warkewa"
Bakina har kunne saboda tsabar farin ciki
Na cigaba da godiya shi kuma yatashi yafita.
Na daka wani tsalle nafada kan katifa.
Waini umar nine zan zama dan kasuwar kwari.
Dama gani dason birni.
Kawai sai nafara mafarkin zaune
Wai ganinan nasha boyel zan hau mota kawai sai sailulata
tayi kara.
$dana fiddo sai naji ashe farida ce kecewa
"Mai gida kayo sauri kazo muatafi yawon shakatawar"
Sai nace
"To ganinan zuwa "
Kawai sai nabude motata na shiga kai naitayin shirme
kala kala tun kafinma naje naga kasuwar.
Da dare banyi wani barcin kirki ba saboda tsabar doki.
Sau uku ina murda hannun agogona ina kara awa guda
guda wai don saboda gari yayi maza ya waye.
Sai na tuna ashe saurin ba'a agogo bane.
Ahaka na hakura saidai naita duba loakci.
Akalla dai naduba sau saba'in ahaka akayi assalatu da
mukaje masallaci muka dawo sai kawai nashiga wanka .
Alhali yayan nawa sai karfe goma yake fita
Akalla dai jiran awa hudu nayi
Da lokaci yayai muka fita .
Rumfar da mukaje katotuwace dabana zaton tana dana
biyu.
Rumfar kawai dazata fita sai dai na Alhaji saminu da
umar lawan yabada labarinta acikin littafinsa "SAURA
KIRIS"
Mutum biyune aciki kuma duk matasa ne kamarni
yayana ya tambayesu Alhaji sukace karfe uku yake fitowa
Wannan yasanya ni faduwar gaba
"Ai munyi dashi nazo dashi da safe"
Yayana yace daso
"Ok kudanyi jiransa"
Wani acikin yaran yafada
Anan muka samu benci muka zauna
Nayi taraba idanu ina kallon masu wucewa.
Aciki na hango wani mutum yana tafe ana faduwa ana
gaisheshi.
Farine dogo mai dan kauri.
Badomin nasan mai martaba sarkin kano ba to da sai
nace shine wannan .
To ammma ko babu komai wannan bai kai mai martaba
sarkin kano farin jini ba.
Amma shima yana dade daidai nasa.
Sai naga yana matsowa garemu
"Ga shinan"
Yayana yafada sai muka mike tsaye domin karramashi.
Daya iso sai nayi kamar yadda naga yayana yayi wato
muka durkusa har kasa muka gaidashi,
"Yaya sunanka dana"
Alhaji ya tambaya , na sunkuyar dakaina yayin danake
cewa
"sunana umar"
"Allah sarki"
Yace dani
"Sunan naka da dadi"
Ya hadani dana cikin kantinan yace sununamin abinda
zanyi.
Aranar wuni nayi ina mimmiko kayayyaki.
Da akatashi aka bani dari biyu na hau mota sallama kuma
akace sai sati sati.
********** ********** ********
Ahankali kwanaki suka cigaba da zukewa irin zukar da
takarda ke yiwa ruwan biro.
TO FA ABI YAFARA KYAU GA UMAR
KUTAYASHI MURNA SAIDAI BANSAN
KO NAN GABA BA
@mr shuraih 99%
.zan ci gaba

TARAR ARADU littafina daya 1 page 8

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 8
Fuskata cike da alamun karaya
"Don Allah yallabai ka taimakeni"
"To wane tai mako kuma zanyi ma?
Kai dana fadamak maganar har taje ma'aikatar ilmi.
Katashi kawai kabani waje kaine kajawo wakanka"
Nayi tsawon minti biyu awajen banko motsa ba.
Daga bisani sai na tattara takarduna na dube shi
"To shikenan yallabai Allah ya taimaka"
Bai amasa maganar tawaba na fito daga ofis din cike da
mamakin wannan lamari.
$hakika zancene mara tushe ballantana makama.
Kuma lallai anzalunceni ayanda aiki yake wuya.
Ballantana kuma a wannan lokaci danake kokarin
mallakar masoyiyata farida.
Hawaye yazubo min daga idona lokacin danake kokarin
barin ginin ofis din.
Ahaka nanufi wajen babur dina saidai na yanke shawarar
na tura shi waje tukuna.
Domin tashinsa anan ciki zai iya juyo da hankalin kowa
nikuma banaso aga tafiyata.
Nafara turawa ahankali
"Mallam umar ina zuwa hakane"
Tambayar mai gadi lokacin danake kokarin fita"
" zanje nagabatar dawani uzurine"
"To adawo lafiya"
Ya maido amsa naci gaba da turawa , saida nayi nisa da
ginin makarantar sannan na tasheshi.
Nahau zuciyata na mai matukar tafarfasa saboda wannan
al'amari ahaka na karasa gida cikin rashin kuzari.
********* ********** **********
Nan fa aiyuka suka yimin yawa kullum inafama da
matsaloli guda biyu
Neman aiki da kuma zaman banza.
Aduk sanda nake zaune nakan debe kewa da littatafan
hausa na(umar lawan)
Kamar su LINZAMiN DAN ADAM'
BABBAR MADAFA
SaURA KiRIS
Kai dama wasu masu dama.
Kwanaki suka cigaba da karfa karfa.
Akalla ko wacce ta maimaita sau takwas.
Wato wata biyu kenan.
Amma har yanzu banga wata alama dazata bani karfin
guiwa akan samun aiki ba.
Na ziyarci kanfaninuwa da ma'aikatu amma shiru kake ji
Kai kace wani arnen dajine yaje neman aiki da takaradan
tsire .
Tuni yan kudaden dake hannuna sun tafi karaye.
Wannan ya tilasta min canja salo.
Idan wajen dazanje ba mummuman nisane dashi ba
nakan daba sayyada.
Badon kamai ba sai don tsadar man fetur .
Wanda kudin rabin galan sun isheni sati uku ina gwaguya.
Da lamari yakai yakawo sai nadaina zuwa ko'ina,
Daga gida sai gidansu farida.
Ahalin yanzu ina gindin babur dina ba ko'ina zani ba sai
gidansu farida.
Na tashi babur din bayan dana sha fama.
Nahau na nufi goron dutse.
Bada jimawaba na'isa gidan
Tun kafin na sauka farida tafito domin tarata.
Muka rankaya cikin gida .
Muka gaisa da babarmu wadda ayanzu sai ka rantse ni ta
haifa ba farida ba.
Muka zarce falon shakatawa na zabi kujera daya na
zauna.
Farida ta zauna akan hannun kujerar idanuwanta kyar
akaina .
Kullum nazo haka take taraiyarayata takasa tsaye takasa
zaune.
Itace ta zauna ahaguna,
Ta dawo dama ta tsaya akaina , ta zauna agabana kaidai
abubuwa da bam- da bam nikaina nasan farida tana
kaunata irin kaunar da bantaba zaton zata yiminba ta
dubeni bayan data ajiye min tataccen lemo
"Umar dan Allah ina roko agareka"
Na kalleta bayan dana zuki ruwan lemon
"Inajinki"
Taci gaba
"Kaje ka kawo sadaki sai adaura mana aure izan ma baka
da kudi bari na baka"
Na kalleta a firgice
"Farida bari ma wannan zance ni da yanzu bana aiki yaya
za'ai nayi maganar aure? Dame zan rikeki farida"
Tayi dariya
"Kaji ka da wani zance to menene amfanin albashina?
Albashina ya ishemu
Wajan zama kuwa dama basai nafada ba, mummy ta
koma sama sai ta barmana nan kasa idan kuma bakason
zama da'ita sai nakama mana haya.$
To me kuma yarage? Ballantana kasan mummy ba'irin
sauran mata bane.
Kaima kagani dakanka "
Nagirgiza kai
"Duk naji jawabinki amma ban karbi rokonkiba.
Ki kuma tuna nayi miki alkawarin akwati biyar kuma
bazan saba ba "
Ta dakatar dani
"Bari wannan zancen umar aicewa kayi idan kana da hali.
Kuma baka dashi yanzu kaga ba saba alkawri kayiba"
Nayi dariya
"Ai halin danake nufi farida shine rai da lafiya , ahalin
yanzu ban rasa ko dayaba"
Ta daure fuska
" Nidai inhar nizakayiwa to banaso, mummy ma kuma
bazata karbaba "
Nayi dariya
"To mummy din taki ce ke kadai"
Ta kalleni
"Naji batawabace nikadai ba kuma bari ganin kafini gata
agunta dakayi magana sai tace haka za'ayi bama ta
sauraron zancena, to wallahi akan wannan bazata
goyama bayaba.
Kawai saita goyi bayanka akan abin dzaka takura? To akan
wannan kam gakucan da mummy arana"
Na mike tsaye
"To zaki gani nasan yadda zanyi na shawo kanta"
Itama ta tashi
"Barima zato bazata taba yarda ba"
****** ************ *******
Zama yayi zama tuni kudaden hannuna sun gama karewa
.
Wannan ya tilastamin saida akwalar baburdina.
Na turashi inda akeyimin gyara nace asanyamasa ganye.
Haka kuwa akayi.
To ashe aiki aka samamin bansani ba
Saida nashafe wata guda cur harda kwana shida amma
kullum naje sai yace ba'azo an tayaba dana lura sai naga
nima in naje har nadawo ko kuda ban taba gani ya sauka
akai ba .
TOFA GA BABUR INA MAI SAYA
SAIYA TUNTUBENI
@mr:- shuraih 99%

TARAR ARADU littafina daya 1 page 7

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 7
Domin ahalin yanzu inna rasata ma zuciyata na iya
bugawa to kaga da wuya ya kasheka gara dadi ya kasheka
to waima da yake cewa zai yi wasa dani kamar dani biri
yana gani mutane zasu bari a dauramin igiyya a kuguna
arinka ja a kasuwa ne?
Ashe makenan dubunsa ta cika .
$sai najini ina mai murna da wannan matakin dayace zai
dauka ,
To amma karramani dayace zai yifa yadda ake karrama
kudi.
Nadade ina tunani daga bisani nagane babu wani karamci
da kudi suke samu fiye da kashe su,
To kasheni za'ayi kenan kwarai kuwa babu tantama
kasheni zaiyi kamar yadda ya kashe uku abaya,
To amma wannan bai dameni ba dukwanda ya mutu
kwanansa ne ya kare.
********* ********** ********
Na dubi farida bayan dana lume acikin kujera
"Allah yakaimu ranara daza mukasance kamar haka
acikin daki daya a matsayin miji da mata"
Tayi murmushi
" Amin umar Allah yakarbi addu'arka har yanzu banji
kana maganar daurin aureba"
Nakai idona gareta
"Akwai dalili farida shiyasa kikaga banyi magana ba"
Ta maido hankalinta gareni
"Wane dalili"
"So nake nagama hada lefe"
Tarike baki
"Wani irin lefe kuma umar"
Nakalleta lefe kala nawa kika sani?
Aiduk inda kikaji ance lefe akasar hausa ana nufin kayan
da mai nemar aure zai kaiwa wadda yake nema"
Ta karkada yatsa
" Sam karma ka soma don kokayima bana so mummy
ma bazata karbaba.
Sadaki kawai zaka kawao shima bamai yawa ba"
Nayi dariya
"Farida arayuwar da akeyi irin na yau duk masoyi yakan
nuna kaunar dayake yine ta hanyoyi irinsu lefe.
Bawai ina nufin wajibi bane kokuma abin dayake makale
da shari'a
A'a saidai inda hali akwai bukatar kayi lefe mai yawa
domin toshe bakin masu kushewa. Saboda an riga anbata
lamarin aure
" Tayi tsaki
"To kai ina ruwanka da masu kushe kabi hadisi mana
daya kecewa mafi albarkacin mace mafi karancin
sadakinta"
Najin jina kai
"Babu shakka farida hakane ni kaina na kanki abubuwa
na bidi'a
To amma tunda wannan baisabawa shari'a ba nayi aniyar
yi miki lefe na ban mamaki.
Domin kaucewa wasu kananun maganganu, kisani yanzu
duniya ta zuba ido akanki , idan muka yi aure babu lefe ,
maganar daza ta yi ta yawo shine neman kai ake daka
shiyasa ko lefe ban yimiki ba.
Ni kuma inaso innuna ma duniya cewa kaunar ki nake
jini da tsoka don babbar abinda natsana bai wuci ace ba
auren soyayya mukayi ba"
Ta bata rai
"Tokai ina ruwanka afadi duka abinda za'afadi magana
zata warwaremana aurene"
"Jini farida na rantse da Allah indai ina da iko sai nayi miki
akwati biyar"
Ta mike tsaye
"Kasan kuwa abin da kake fada? Ni yar gidan wata
shugaban kasace daza'a yimin akwati biyar"
Nayi murmushi
"Kinfi yargidan ko wane shugaban kasa a wurina babu
kamar ki aduniya.
Farida ki shaida ina yimiki kaunar dazan iya bada sadaki
da raina"
Ta girgiza kai
"Gaskiya umar banyadda kayimin akwati biyar ba"
Na mike tsaye
"Bakin Alkalami yabushe farida "
******* ********* *********
Na zage rubutu da cak , yaran anaji shida sun nutsu,
Inajin dadin yadda yara ke bani hankalinsu izan ina bada
assignment.
Najuyo na dubesu adaidai lokacin dana kare rubutu.
Ian shirin fara bayaninewani yaro ya durkusa agabana.
"Sir principle yana magana"
Nayio mamakoin abinda zai sa principle kirana awannan
lokaci.
Hakika yakan kiarani fiye da kowani malami wani loakcin
kira mai ma'ana wani lokacin kuma hayaniya kawai.
Na ratsa yara kai tsaye kuma na nufi kofa .
"Gani yallabai"
Nafada aloakcin danake kokarrinn zama akan kujera
hannuna furtutu da garin cak.
Yadago daga barin rubutun dayake ,ina iya hango
idanunsa kadan kadan ta cikin bakin gilashin daya
makala.
Fuskarsa kuma ta nunamincewa yana so ya gabatar da
wani bayani dayake dauke dashi muhimmi
" Wato umar nakirakane saboda wata matsala data dade
tana faruwa nasha ji da kunnena kuma andade ana kawo
min kara, wani irin turancine kake koyar dayara abin ko
ka'ida babu?
Ya zakarinka koyar dayara turanci broka , ko anfada
maka nan kasuwar sabon garice?
Gaskiya bazai yiwu mu tafi dakaiba mai cigaba muke
nema bawai mai kawo ci baya ba.
Saboda haka daga yanzu.........."
Yayi shiru baiyi magana ba na cika da mamaki wainine
nake koyarda turanci broka .
Wannan zacene mara tushe shi kansa pricinple din
baikaini iya yturanci ba.
Nakan fitar da kalma bayan kalma yadda kasan baturen
gaske
Wanda hakan yasa ake min lakabi da toni blayer.
Amma duk gashi ana kokarin kiransa a matsayin broka.
Na dubi principle
"Yallabai wayanda suka kawo maka koken sun gabatar
maka da shidace"
Yadaka min tsawa
" Wata shaida tunda nima naji da kunnena"
Ya watsomin takardu
"Tuni mun rika mun mika matalarka a ma'aikatan ilimi
kuma sun bamu madadinka, kana iya hangowa ta
window gashi can atsaye"
Nawai waya domin ganin wanda ake kira madadina wani
mutum ne mai yawan suma da gashin baki.
Najuwo ga principle fuskata cike da alamun karaya.........
...
TOFA UMAR YaFARA SHIGA
@mr:- Shuraih 99%
To be con.........
Keep followin.....

TARKON MUTUWA littafi na biyu 2 complet cigaba

kodajn wannan batu sai hatyan ya kyalkyale da
dariya yace
kome kike takama dashi ni daidai da kene.
ina shawartarki daki gagauta ficewa domin muma
tafiya zamuyi mu bar muku birninku tunda kun
matsa mana
sarauniya ta sake bushewa da dariya a akaro na
biyu tace ai bakin alkalami ya riga ya bushe .
babu ta inda zaku iya fita daga garin nan batare
da an kamakuba.
nan da cikar rabin sa'a dakarun sarauniya
kimanin dubu dari uku zasu zo suyiwa unguwar
nan kawanya kunsan kuwa sarkin yawa yafi
sarkin karfi
kuma kasani cewa ko tsafi kuke takama
dashi tofa baya tasiri acikin garin nan.
saboda sarauniyar mu bata tsafi kuma baya tasiri
akanta.
tana gama fadin haka sai ta zare takobinta tana
mai gyara tsayuwarta ta dubi hatyan tace .
ka mika wuya ko na yi maka raunin da zaka mutu
da tabonsa.
koda sarauniya tazo nan ajawabinta sai shima
hatyan ya zare takobinsa
kuma ya gyara tsayuwarsa kamar yadda tayi
yace
"na rantse da kabarin iyayena idan ban sami
nasara akanki ba kema baki isa ki sami nasara
akaina ba "
gama fadin hakan keda wuya sai duk su biyun
suka ruga da gudu izuwa kan juna suka
ruguntsume da azababben yaki mai matukar ban
tsoro da ban al'ajabi wanda ya firgita sadirat
ainun ta ruga izuwa karkashin wani katon tebur
na karfe dake tsakar gidan ta dunkule jikinta
tamkar bushiya
amma saboda shegen naci nason ganin
jarumtakar mutum biyun sai ta ci gaba da kallon
gumurzun nasu
sai da suka shafe kusan rabin sa,a suna kaiwa
juna sara da suka cikin bakin zafin nama da
bajinta ba tare da dayansu ya sami nasara ba,
koda ganin haka sai suka sauya salon fadan suka
hada da tsalle gami da kwance kwance da kuma
kai naushi da bugu.
da zarar hatyan ya sami nasarar naushin
sarauniya a fuska ko a kirji kafin ya kaimata wani
naushin sai kaga ta rama kamar yadda yayi mata
nanfa suka hadawa junansu jini da majina
tun suna yin fadan da karfin jikinsu da kuzarinsu
sai daya zamana cewa dakyar suke iya
daga hannayensu
kai da gani kasan cewa karfinsune yazo daya
suna cikin wannan haline sukaji ana kwankwasa
kofar gidan da karfi
dajin hakan sai sarauniya ta ja da baya ta daina
fadan sannan ta daga muryarta da karfi tace
ku dakata anan waje kada wanda ya shigo
take su hatyan suka gane dakarun sarauniya ne
sukazo kuma ga yadda suka jiyo dudufniyar su
da alama suna da yawan gaske
kawai sai sarauniya ta mike tsaye ta fuskanci
jarumi hatyan ta cire mayafin data rufe fuskarta
dashi
koda su hatyan sukaga kyakkyawar fuskarta da
jikinta sai suka rude
sarauniya badi'atul nauwara tasa hannunta ta
goge jinin dake jikin lebenta sannan ta dubi
hatyan cikin murmushi tace
nice sarauniya badi'atul nauwara mai mulkin
wannan birni mai suna madinatul salkuf.
yanzu haka dakaruna sun iso wannan
unguwar sun zagayeta babu ta inda zakubi ku
iya guduwa ku tsira amma zan kubutar daku
saboda dalili daya.
dalilin kuwa shine
naji kayi rantsuwa da kabarin iyayenka
hakan ya nuna mini cewa ku marayune kamar ni
wato baku da iyaye .
duk da cewa banji tarihin rayuwarkuba kuma
bansan laifin da kukayi wa sarki shamsal ba.
amma jikina ya bani cewa kuna da gaskiya
zaluntarku kawai zai yi .
zan baku dama ku gudu amma yakai wannan
gwarzon jarumi kayi sani cewa ina binka bashin
wannan fada.
lallai sai mun sake haduwa domin mu fitar da
raini
na dade ina neman jarumin dayake da karfin
damtse da iya yaki irin... auwzab... nawa ban samuba sai
kai
a yanzu
dolene mu karasa yakinmu .domin mu banbance
tsakanin aya da tsakuwa anan gaba idan muka
sake haduwa anan gaba .
ku zauna acikin gidannan ku kwana.kada ku
fito sai asubah tayi.
asubah nayi ku nufi yammacin garinnan.kuyi ta
tafiya zaku iski tashar jirgin ruwa .
ku hau jirgi ya ketare daku iyakar wannan kasa
tawa zaku riski wani gari agaba.
zan baku gudun mawoyin da zasu ceceku.
koda ta gama fadin hakan sai ta juya ta fice
daga cikin gidan.
tana fita sai ta janyo kofar gidan ta rufe inda tayi
arba da dakarunta tare da boka azwan yana
jagorantar su.
sun ruko saldirat a hannu sunyi cirko cirko.
kawai sai sarauniya badi'atil nauwar ta dubi boka
azwan tace
ku saki saldira bata da hannu akan boye
wadannan masu laifi domin basa cikin wannan
gida .
maza ku ruga gaba dayanku izuwa gabashin
birnin nan.
can sukayi da gudu bisa dawakai kada ku barsu
su ketare iyakarmu.
kodajin wannan batu sai boka azwan da gaba
dayan dakarun suka ruga izuwa inda dawakansu
suke suka hayesu suka zaburesu da gudu suna
masu tunkarar gabashin birnin .
tafiyar su keda wuya sai sarauniya ta dubi
sardila tace
shiga ki baiwa su hatyan kulawa mai kyau .
asuba nayi ki tashesu daga barci subar garinnan.
tana gama fadin haka sai ta juya tayi tafiyarta ta
kutsa kai cikin unguwar tana mai rufe fuskarta
tamkar bata kasance sarauniyaba.
sardila ta fada cikin gidan da sauri ta rufo kofa.
kamar yadda sarauniya ta tsara haka al'amarin
ya kasance .
asubah nayi sai sardila ta tashesu daga barci
suka kimtsa sannan sukayi bankwana.
nantake hatyan ya bude jakar guzurinsa.
ya debo dinare dubu da biyu ya mikawa sardila
yace.
ga kudin hayar gidanki dana abincinki.
dajin haka sai sardilat ta kasa karbar kudin kuma
nantake idanunta suka ciko da kwallah har
hawaye ya zubo mata tace
yaya ina matsayin marainiya zan kasa taimakon
marayu yan uwana?
maraicine yasa na taso acikin irin wannan
rayuwa da kuka ganni aciki
tun ina yarinya shekara takwas aduniya na iya
aikin wahala domin na tserar da mutuncina
karuwanci sata da caca duk nayi agarin nan
amma ban taba taimakon wani da darhami
dayaba arayuwata.
ahalin yanzu na mallaki gidaje da gonaki,shanu
da tumaki barkatai,
idan an lissafin masu arzikin garinnan dolene
asani acikin su.
duk abinda nayi muku na bar muku domin nabar
tarishi arayuwata cewar nataba taimakon yan
uwana marayu da wannan haramtacciyar dukiyar
dana tara
ku sani idan natuna wannan dukiya sai naji na
tsani kaina kuma naji mutuwa
kawai nake sonyi domin bata da amfani
rayuwata. dan babu da uwa ko masouyin kwarai.
koda sardilat tazo nan azancenta sai ta fashe da
kuka al'amarin daya kara karyar da zuciyar
hatyan da sadirat kenan suma sukaji suna
matukar tausayinta don haka ba susan sa'adda
suka rungumeta ba duk su biyun suka fashe da
kuka aka rasa wanda zai rarrashi wani
atsakaninsu saboda suma nasu maraicin suka
tuno.
sai da suka dan jima kankame da juna sannan
suka janye jikinsu daga cikin nata
nandai suka kwashe kayansu tayi musu rakiya
har izuwa bayan gari inda suka hau dawakansu
suka sukwanesu suka durfafi hanyar da sarauniya ta
umarcesu subi.
tun kafin su isa inda tashar jirgin ruwan take
hatyan yayi tsafi suka sake rikidewa izuwa siffar
fatake kuma mazaje yan kimanin shekaru arba'in
da daya.
da isarsu bakin gabar jirgin ruwan sai suka iske
wani babban jirgi ya gama lodi wanda jama'ar
dake cikinsa akalla sunkai dari shida da arba.in.
shidai wannan jirgi hawa biyune ma'ana akwai
dakaru akasansa da samansa.
sai kuma can karshen saman inda mutum ke
ganin ruwan tekun afili.
mafi yawan jama'ar dake cikin wannan jirgi
fatakene wadanda suka nufi birnin askandariya
domin can ne inda jirgin ya nufa.
indai mutum ya isa birnin askandariya tofa yana
daf da fita daga nahiyar gaba daya.
saida su hatyan suka ninka kudin shiga jirgi
sannan suka sami damar shiga jirgin sannan suka
sami damar shigar da dawakansu.
aka kai dawakan inda aka tanada don dawakai
nanma suka biya kudin shigar dasu.
daga nan aka tafi dasu izuwa dakinsu suka shiga
suka baje akan shimfida cikin farin ciki bisa
ganin cewa suna daf da tsira da rayuwarsu daga
sharrin sarki shamsal
Anan muka kawo karshen littafi na biyu
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
.
Like our page
www.facebook.com/hausaebooks

TARKON MUTUWA littafi na biyu 2 complet

TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- Shuraih Usman
Littafi na biyu 2
Part 2A
.
Duk inda sarkin mafarauta yake ka tura aje azo
maka dashi amma bari na bincika naga inda
yakedin.
koda gama fadin haka sai boka daizun ya zura
hannun cikin aljihu ya fiddo madubinsa na tsafi
ya ajiye a gaban sarki sannan ya shafi madubin
da hannunsa na hagu maimakon madubin yayi
haske ya nuna abinda ake so a gani sai yayi
duhu dudum ba a ganin komai ko da ganinin haka
sai boka daizun yayi ajiyar zuciya yace
hakika ai sarkin mafarauta yaudararka yayi kuma
yaci amanarka tabbas da taimakonsa wannan
yaro hatyan da 'yaruwarsa suka sami nasarar
guduwa
kodajinhaka sai bakin ciki ya turnuke sarki
shamsal yasake kurma uban ihu akaro na biyu
kamar zai fashe da kuka
sai daya shafe kusan dakika dari da ashirin yana
huci da numfarfashi tamkar wani kumurcin maciji
sannan yace
yakai abin dogarona kayi sani cewa zama bai
kamaniba
dakaina zan tafi farautar wanna yaro domin na
kasheshi tungabanin lokacin da zai dawo ya
riskeni harcikin masarautata ya cini da yaki
taimakon da nake nema awajenka guda dayane.
inason ka banj hadimanka na aljanu kamar guda
dari biyar wadanda zasu dauki manzannina
sukaisu izuwa ga dukkan kasashen dake wannan
nahiya tamu .
zasu kai wasiku ne gami da hotuna masu dauke
da taswirar hatyan da yar uwarsa
acikin kowacce wasika zan gaya kowanne
sarki dayasa abaza hotunan hatyan abirni da
kauye duk inda aka gansu akamasu a tsare su
akurkuku.
sannan kuma zansan ya lada mai tsoka na
dubban darhami ga duk wanda ya sami nasarar
chafkesu.
inason cikin kwananki uku kachal agama rarraba
wadannan wasiku da hotuna
kodajin wannan batu sai boka daizun ya kyalkyale
da dariyar mugunta yace
ya shugabana hakika kazo da shawara mai kyau
domin itace hanyar da zakabi ka hana hatyan da
yaruwarsa samun damar fita daga wannan nahiya
kuma acikin kankanin lokaci zasu dawo hannuka
tabbas kwakwalwarka tana aiki sosai gami da
hangen nesa
kodajin wannan zuga sai sarki shamsal ya bushe
da dariyar farinciki yashiga yiwa kansa kirari
batare da bata lokaciba sarki shamsal ya tura
akazo da wani makocin satyan sannan aka
kirawo masanin zane
take makocin ya baiyyana kamannin fuskar
hatyan da fuskar yar uwarsa sadirat
cikin kankanin lokaci mai zanen yafitar da
taswirar tamkar sune awajen ba zanasu akayiba
shikuwa boka daizun sai yayi tsafi takardar zanen
ta tsaga kanta har guda dubu dari .
daga nan kuma sai aka tara manzanni aka
rarraba musu wasiku da hotunan hatyn.
dayawa aka kirawo aljanu suka tafi dasu izuwa
dukkan kasashen dake nahiyar
++ AUWZAB
al'amarin yarima zainur kuwa sai daya kwana
ashirin da daya akwance yana jinyar dungulmin
hannunsa sannan ya warke ya sami karfin jikinsa
.
duk lokacin daya kalli dungulmin hannunsa kuma
ya tuno da cewar bai sami nasarar yiwa sadirat
fyadeba .
saiya fashe da kukan bakinciki daga wannan
lokaci
yammatan birnin bindal suka sami nutsuwa da
kwanciyar hankali domin yarima zainur bai sake
yiwa wata fyadeba.
kawai ma sai yazamana cewa ya daina neman
mata koda karuwai kuwa
kuma bashi da wani buri wanda yafi yaji cewa an
kamo hatyan da yaruwarsa sadirat
idan har sukazo hannu to yaci alwashin saiya
cika burinsa akan sadirat agaban hatyan kuma
yayi amfani da lafiyayyen hannunsa ya sare
hannun daman hatyan
kullum yarima zainur cikin sambatu yake na fadin
wannan buri nasa kamar wanda ya zautu .
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN
BINDAL BAYAN KASHE IYAYEN JARUMI HATYAN
SUKUMA SUNYI GUDUN HIJIRA TARE DA
YAR'UWARSA SADIRAT SUN NAUSA DAJI BA
TARE DA SUNSAN INDA SUKA DOSA BA.
al'amarin su jarumi hatyan kuwa lokacin daya
zaburi dokinsa da gudu izuwa cikin daji
sadirat na goye abayansa saisuka ci gaba da
tsala gudu akan doki baji ba gani kamar ba zasu
taba tsayuwaba.
saida suka shafe sa'a uku suna yin gudu sannan
dokin ya fara gazawa ya zamana cewa ya rage
karfin gudunsa kai sai da takai cewa ma dokin ya
galabaita ya
fara sassarfa kamar zai durkushe kasa
koda ganin haka sai jarumi hatyan ya ja linzamin
dokinsa ya sauka .
saukarsu keda wuya sai hatyan ya saki dokin ya
kadashi ya ruga izuwa wani bangaren dajin
cikin kaduwa sadirat ta dubi jarumi
hatyan tace
ya zaka sallami dokin alhalin bamu san iyakar
inda tafiyarmu zata yankeba.?
kodajin wannan tambaya sai jarumi hatyan yayi
doguwar ajiyar zuciya yace
ai wannan doki amfaminsa ya kare awajenmu
tunda ya taimkemu wajen bawa makiya tazara
mai yawan gaske
amma idan mukaci gaba da fiya dashi sawayen
kofatonsa ne zasu tona mana asiri.
yake yar uwata ki kwantar da hankalinki kiyi sani
cewa indai kina tare dani babu abinda zai
sameki.
sadirat tace
ni kaina ina jin hakan ajikina amma abinda nake
jiye mana shine yankewar guzuri ni kam
Hankalina atashe yake saboda naga abincin daya
rage acikin jakarka kadai.
kodajin wannan batu sai hatyan yai murmushi
yace ai indai muna cikin jeji ji nake kamar muna
gidane agaban umma.da.abba
kodajin haka sai idanun sadirat suka ciko da
kwalla,
hawaye ya subuto mata ta rungume hatyan
kuma ta fashe da kuka tana mai cewa
yanzu shikenan mun rasa abba da umma har
abada.
kuma ko kabarinsu bazamu sake ganiba?
wata.kilama a.filin Allah akabar.gawarwakinsu
anan zasu bushe harsu dai daice
sa'adda jarumi hatyan yaji wannan batun na
yar uwarsa sadirat sai shima zuciyarsa ta karaya
har hawaye ya.subuto masa ya dubeta yace
gawar iyayenmu bazata tabeba domin na
tabbatar da cewa sarkin mafarauta zai kwashesu
yayi musu kabari
kada ki manta cewar komai daren dadewa sai
munkoma birnib bindal na dauki fansar ran
iyayenmu
lallai saina.kashe sarki shamsan agaban idanun
yarima zainur kuma na haye kan karagar
mulkinsa domin kawo karshen zaluncinsa.
yanzu dai bari mu nemi inda zamu dan yada
zango muci abinci mudan huta
sannan muci gaba da tafiya.
kodajin haka sai mamaki da tsoro ya
kama.sadirat tace
yanzu kana nufin kace adaren nan zamuci gaba
da tafiy maimakon mu sami inda.zamu fake mu
kwana?
hatyan yace ai tsayuwar mu adaren nan har takai
ta sa'a guda hatsarine agaremu saboda na
tabbatar
da cewa sarki ya turo dakarunsa subiyo
bayanmu kokarina shine mufuta daga kasarnan
gaba daya mu shiga wata kasar .
daga chan ma ci gaba da tafiya harsai
mun fice daga nahiyar nan gaba daya
sannan zamu sami kwanciyar hankali .gama fadin
haka keda wuya sai hatyan ya kama hannun
sadrat ya jata suka kara gaba amma saitaga ya
kan sunkuya kasa ya debi kasa ya shinshina
kuma taga ya sauya hanya .
al'amarinda yayi matukar bata mamaki kenan ta
dubeshi tace
waishin mene.ma'anar wannan abu da kakeyi?
hatyan yace inayin haka ne domin na gano zamu
samu rafi a kusa domin musa kuma muyi
guzurinsa da yawa kiyi sani cewa ruwa yafi
abinci
mahimmanci arayuwar dan adam domin zamu iya
kwananki bakwai babu abinci amma ba zamu iya
jure kishirwa ta yini ukuba
aikuwa kamar tsafi sai sadirat taga sun iso kusa
dawata korama mai dauke da ruwa garaigarai .
ruwan tafiya yake da gudu yana kwaranya kasan
wani dutse .
cikin farinciki suka ruga izuwa bakin koramar
suka sa hannayensu suka kwarfo ruwan suka
sha.
daga nan sai htyan ya bude jakar guzurinsa
yadauko abinci wanda bai wuce loma gomabaa
suka ci tare suka sake kora ruwa
gama hakan keda wuya saiya cika battocin su da
ruwa
ya mika mata ta rike yace yanzu zan goya ki
abayana zanyi gudu dake na tsawon kwanaki
ashirin.
duk sa'adda kikaji kishurwa ko yunwa ki dauki
abincin da yake cikin battarki kici kuma kisha
ruwan battarki
ki sani cewa a tsawon kwana ashirin ba zamu
tsaya ba domin ki huta koda kuwa kin gaji da
zama abayana
lokacinda hatyan yazonan azancensa sai sadirat
tayi mai kallon mahaukaci tace ni bantaba jin
inda bil'adama ya yita jure guduba harna
tsawon kwanaki ashirin ba baci basha ko kuwa
kana nufin wani
aljanin zamu hau?
wai shin idan ma wata lalura ta kamanifa
tafitsari ko kashi?
kodajin wadannan tambayoyi guda biyu sai
jarumi hatyan ya bushe da dariya yace aikuwa
zan baki mamaki saboda ni tun ina da shekara
goma aduniya duk sa'adda na shiga daji farauta
sainayi kwana ashirin ina gudu baci sai shan
ruwa.
kuma wannan gudu da nakeyi tsere nake da wata
sihirtacciyar bauna harsai na kure mata gudu na
risketa mun fafata kazamin yaki
akarshe saidai wuya tasa ta juya da gudu ta
barni
gudun kwana ashirin da nakeyi dadai yake da
tafiyar kwana saba'in da tara akan doki
wannan gudu nawa baiwa ce zallah
ina nufin da ita aka haifeni
kodajin wannan batu sai mamaki ya turnuke
sadirat.kuma hankalinta ya sake kwanciya taji ta
sake samun nutsuwa ta cewar wannan kani
nata.zai iya kareta daga sharrin sarki shamsal
batare da bata lokaciba kuwa sai hatyan ya
rankwafa sadirat ta hau bayansa ya goyata
sannan ya daureta tamau ajikinsa
battar ruwansa kuwa na ruke ahannunsa na
dama takobinsa kuwa na.sakale a cinyar sa
tadamansa
kawai sai ya falfala da azababben gudu izuwa
cikin daji nanfa sadirat ta dinga ganin abu kamar
wasa.
domin saboda karfin gudun hatyan har tashi
sama yake yana tsallake gajerun bishiyoyi da yan
duwatsu da kwazazzabai .
wani lokacin kuma sai taga kamar akan iskar
cikin sararin samaniya suke tafiya saboda karfin
gudun
sau tari bata sanin sa'adda barci yke dauketa
kuma.duk sa'adda da ta farka da taji kishirwa sai
ta bude battarta ta kwankwada.ta koma barcinta
.
abu dai kamar wasa sai suka shafe kwana
ashirin
suna.tafiya.
tuntana kirga kwanakin har lissafin ya kwace
mata ta manta
abinda yafi daure mata kai shine tunda aka fara
wannan tafiya bata gajiba kuma bataji kashi ba
ko fitsariba.tamkar bataci ta sha ba
abinda kawai takeji shine yunwa da kishirwa
kuma.da.zarar taji su din sai ta dauko abincinta
da battar ruwanta wadanda suke jikinta kawai
taci kuma.tasha
.
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Like our eBooks page
www.facebook.com/hausaebooks
TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- Shuraih Usman
Littafi na biyu 2
Part 2B
.
A ranar kwana na ashirin dinne suka hango kofar
wani babban gari daga nesa
awannan lokaci safiyace
cikin farinciki hatyan ya tsaya da gudu ya kira
sunan sadirat
amma sai yaji shiru bata amsaba
koda yadan waigo sai yaga ashe barci takeyi
nan take ya kwanceta daga
bayansa sannan ya shimfideta akasa.
asannane yaji wata irin muguwar gajiyar
gudun dayasha ta zo masa gamida
matsananciyar yunwa
don haka baisan sa'adda ya sulale kasa ba
karar faduwar tasace tasa sadirat ta farka daga
barcin da takeyi .
tana bude ido taga hatyan akwance akasa jikinsa
na kakkarwa tamkar mai cutar farfadiya
cikin rudewa ta kamoshi ta dora kansa akan
cinyarta ta yayyafa masa ruwa
nantake yayi dogon ajiyar numfashi ya budi baki
dakyar yace
da ita ta bashi abinci
cikin rawar jiki ta bude jakar guzurinsa ta fiddo
abinci wanda bai wuce loma biyarba
tarinka bashi abaki da hannunta
abincin na karewa ta kora masa da ruwa
asannanne hatyan ya dan dawo cikin hayyacinsa
ya dubeta yace
nagode da kika ceceni daga yunwar kwana
saba'in da tara
cikin tsananin mamaki ta dubeshi tace bangane
yunwar kwana saba'in da tara baca, nake cewa kayi
gudun kwana ashirin zamuyi?
hatyan yace ai guduna na kwana ashirun daidai
yake da tafiyar kwana saba'in da tara akan doki
kinga kenan tafiyar da mukayi yanzu ta kusan
wata ukuce
wannan ne dalilin da yasa komai saurin dakarun
da sarki shamsan zai turo su kamamu
bazasu iya riskarmu ba
yanzu dai ga wani babban gari nan agaban mu
kuma dolene mu gaggauta shiga cikinsa
domin haryanzu jikina rawa yakeyi saboda yunwa
inason na sami abinci isashshe naci na koshi
ammafa bazamu iya shiga cikin garinba kai tsaye
dolene muyi yar dabara saboda tsaro
gama fadin hakan keda wuya sai ya dafa
kafadarta ya karanta wadansu dalasimai na tsafi
faruwar hakan keda wuya sai nan take shi ya
rikide ya zama tsoho rike da sanda ahannunsa
ita kuma saita zama yarinya karama yar kimanin
shekara goma
kawai sai ya dubeta yace
sunanki sahalu maza yimin jagora mushiga cikin
garin nan muna bara
batare da wata gardama ba kuwa sadirat ta
kama sandar dake rike ahannunsa tajashi
suka nufi kofar babban birnin kai tsaye bada
wata fargaba ba
da isowarsu bakin kofar birnin suka kamu da
tsanani mamaki kuma tsoro ya shigesu amma sai
suka basar
suka ci gaba da bara don kar mutane su ganesu
bakomai ne ya basu tsoro da mamaki ba face
ganin taswirar fuskokinsu
bisa takardu an lika ako ina a jikin bango baja
baja
kuma ajikin taswirar an rubuta cewa wadan nan
manyan masu laifine na sarki shamsan
don haka ana nemansu ruwa ajallo
duk wanda yakamasu ko yafadi inda suke za'a
bashi ladan dinare dubu dari ....gaskiya ni auwzab nasan
inda suke zanfada abani rabona.....
hatyan da sadirat na cikin karanta wannan bayani
abakin kofar birinin sai shugaban dakarun dake
tsaye awajen
wani narkeken katone sai ya dubesu yace kai
wannan almajiri
su waye ku kuma taya akai kuka iso nan alhalin
kai makahone shikuma dan jagoranka yaro ne
dan karami?
kodajin wannan tambaya sai hatyan ya rikirkice
irin yadda tsofaffi keyi yace
yaro harkasa hantar cikina ta kada saboda
wannan tsawa taka
mu bakine daga kasar misra kuma tare muke da
wani ayari na fatake acikin jirgin ruwa
jirgin namune yayi hadari a kusa da gabar
wannan birni naku
ya nutse akarkashin ruwa
kadanne daga cikinmu suka ragu shine muka
rarrabu acikin daji saboda firgita.
dakyar muka gane hanya muka iso nan
kodajin wannan batu sai wani can daga cikin
dakarun yace
hakika wannan makaho yayi gaskiya domin tun
shekaran jiya ire iren wadannan fatake suka
shigo garin nan suka bada labari irin wanda
wannan ya bayar
kodajin haka sai shugaban dakarun yasa aka
budewa su hatyan kofa suka kunna kai ciki
suka durfafi cikin gari kai tsaye ba tare da
fargabar komaiba
nan dai suka tambayi hanyar kasuwa aka nuna
musu .
kawai sai hatyan yace da sadirat
ki nemi babban wuri inda ake sayarda abinci mai
rai da lafiya ki kaimu
Kodajin haka sai mamaki ya kamata tace
yaya mu da bamu da kudi zakace muje wajen
abinci mai tsada ?
kodajin haka sai hatyan yayi murmushi yace
waya gaya miki bamu da kudi?
to ki sani cewa duk kudaden da sarkin mafarauta
ya tara mini suna hannuna.
ba wai abinci mai tsada ba hatta gidan kwana
mai tsada zamu kama haya
amma ba zamu wuce kwana ukuba agarinnan
zamu kara gaba
don kada asirin mu ya tonu ..ni auwzab zantonama kuwa
ehe...
kuma kinsan cewa so mukeyi mubar nahiyar
gaba daya
ba tare da sadirat tayi wata gardama ba.
sai taci gaba da jan hatyan sukaci gaba da tafiya
acikin kasuwar har suka iso wani babban gidan
abinci
kai tsaye suka kunna kai ciki
suna shiga suka iske jama'a azazzaune sunacin
abinci
ai kuwa sai jama'a suka zuba musu idanu gaba
daya.
abu na farko dai kowa yana mamakin abinda ya
kawo almajiri irin wannan gidan abinci mai tsada
haka
idan har yana da kudin siyan abincin da manyan
mutane suke siya to lallai yana da makudan
kudade ajikinsa
hatyan ya yiwa gaba daya mutanen dake dakin
siyan abincin kallo daya amatsayin shi makahone
sai yaga cewa daka dakarun birnin acikin batar
da kama sai wadansu jarumai masu kirar karfi
kuma mafi yawansu suna rike da takardun
taswirarsa data sadirat.
acan gefe daya kuma sai yaga wani boka azaune
akan tebur shi kadai
tunda suka shigo gidan bokan ya kurawa hatyan
idanu ko kiftawa bayayi
nantake hatyan yasa jinin jikinsa yasan cewa
wannan boka ya gane koshi waye
kawai sai hatyan yayiwa sadirat rada akunne
yace
muje kan wancan teburin da babu kowa mu
zauna
kuma duk bala'in da zai faru anan karki kuskura
ki tashi daga inda kike
kodajin wannan batu sai hankalin saidirat ya tashi
don tasan cewa dolene ayi fitina acikin wanan
dakin abinci.
nan sadirat ta ja hatyan takaishi izuwa teburin da
babu kowa akai suka zauna
har a sannan kallonsu akeyi da mamaki
zamansu keda wuya sai wata ma'aikaciyar gidan
abincin doguwar mace mai dan kyau
wacce shekarunta bazasu haura talatinba
tazo garesu
tadubi sadirat tace dan samari me za'a kawo
muku?
farat daya sai hatyan ya tari nunfashin sadirat
yace
ni katuwar kaza zaki kawo mini gami da shin
kafa da ruwan inibi
kodajin haka sai matar ta bushe da dariya tace
haba shiyasa jikinka yake da kyau baba
fatar jikinkama bata da alamar tsufa
dolene ka zamo lafiyayyayen namiji mai kwari
zan iya aurenka inda kana sona
kodajin haka sai sadirat ta murtuke fuskata dubi
matar tace
nidai ki kyalemin babana kije ki kawo mana
abinci kawai kuma nima irin nasa zaki kawo min
matar tai murmushi tace
babu laifi idan da yayi halin ubansa
ai barewa batayi guduba danta yayi rarrafe
koda gama fadin hakan sai matar taje ta kawo
musu abinci a farantai biyu ta ajiye agabansu
nanfa suka kama cin abincin hannu baka hannu
kwarya saboda rabonsu da cin abinci mai dadin
haka tunkafin su baro birnin bindal.
koda jama'a suka ga yanayin cin abincin su hatyan
sai suk bushe da dariya saboda azatonsu
kauyawane don basu saba cin abinci maidadin
haka ba.
wannan boka fuskarsa amurtuke bai yin dariya
kuma bai dauke kansa daga kansu hatyan ba har
suka kammala cin abincin.
bayan sun kammala cin abincin har sun wanke
hannunsu sun karasa shan ruwan inibin sai
hatyan ya sanya hannunsa acikin jakar guzurinsa
ya dauko zinare sannan ya ware iya kudin
abincinsu ya bayar
ashe daga cikin jaruman da suke zaune agefe
daya kimanin su ashirin barayine
kuma suna lura da jakar guzurin da ke hannunsu
hatyan
kawai sai daya daga cikinsu yazo wajen su
hatyan ya zare wuka ya dora awuyan hatyan ya
daka masa tsawa yace
kai tsohon banza maza ka bani jakar guzurinka
ko kuma yanzunnan na shaftarema makogwaro
tuni awannan lokaci jikin sadirat yafara karkarwa
saboda tsoro
shikuma hatyan yayi kamar yatsoratan
ya yunkura kamar zaisa hannunsa ya cire jakar
amma sai yayi wuf ya kwaci hannun barawon
ai kuwa sai barawon ya kwalla uban ihu ya saki
wukar dake hannunsa ta fadi kasa saboda ji yayi
kamar hannunsa zai karye
kawai riko yaji irinna sadaukai koda
ganin haka sai yan uwan barawon suka mike
zumbir suka zare makamansu suka afkawa
hatyan.
kafin su riskeshi tuni sandar hanunsa ta rikida ta
zama takobi
nanfa suka rugumtsume da azababben yaki
aka fara kakkarya teburan abinci jama'a suka far
kama gudu da ihu
kafin kace wani abu saura wannan boka da
dakarun birnin kawai atsaye gefe daya suna kallon
gumurzun da akeyi
sai kuma wannan mace wacce ta kawowa su
hatyan abinci atsaye gefe daya tana ihu da fada
wai an lalata mata dukiya
ashe gidanabincin nata ne
cikin abinda bai wuce dakika dari da shirinba
hatyan ya kakkarya wadannan barayi kimani su
ashirin ya zubar dasu kasa sunata koke koke
takobinsa kawai kare hare harensu ya keyi da ita
amma bata sha jikin ko dayabada tsagwaron karfin
damtse ya gama dasu
shikansa wanna boka da dakarun birini da mai
gidan abincin sunyu matukar mamakin karfin
hatyan
itakuwa sadirat tunda aka fara fadan saita
dunkule akan kujerar da take zaune ta hade kanta
da cinyoyinta.bata dagoba saida taji gidan yayi
tsit batajin komai sai koke koken kartin da hatyan
ya karya .
adai dai wannan lokacine wannan matar mai gidan
abincin ta taho da sauri wajen hatyan tace ina
kuma zaku tafi baku biyani kudin babbar barnar
da kukayi min ba?
kodajinhaka sai hatyan yayi murmushi
yace nawa zamu biyaki?
matar tayi masa wani murmushi irin na
karuwanci tace
tunda dai kaine ka biya dinare hamsin charaf sai
sadirat tace
haba yan wadannan tsofaffin kujerun da teburan
da aka karya sune dinare hamsin
sai matar ta rufe sadirat da fada tace
shin bakya ganine anfasa min tambula da kofuna
guda dari
ko kece mannadinin hari sai an biyani dinare
hamsin ko kuwa rijiya ta bayar guga ya hana
dajin haka sai hatyan ya tari numfashinta yace
kadaki danu ga dinare dari ma
nan take ya debo dinare dari ya bata .
ai kuwa sai matar ta daka tsalle ta sumbaci
hatyan agoshi sannan tace idan kuna neman
gurin kwana a unguwar daisul nake gida mai
lamba goma
kofata abude take agareka basai ka biya ba
shidai hatyan baice da ita kalaba kawai sai ya
dafa kafadar sadirat yace zo mu tafi
nan take takobin dake hannunsa ta rikide ta
koma sanda
sadirat ta kama sandar suka nufi hanyar fita
daga gidan abinci
amma sai wannan boka da dakarun birni kimanin
su saba'in suka sha gabansu
Bokan ya dubi hatyan fuskarsa a murtuke yace
kana zaton zaka iya yaudarar kowane da dan
guntun sihirinka na tsafi?
to nagane ku ko ku su waye
kaine hatyan wannan yarinyar kuwa yar uwarka
ce
sadirat
kune wadanda aka baza hotunanku ako ina cikin
garinnan kuma sarki shamsal ne yake nemanku
ruwa a jallo
kuna zaton zan iya bari ladan dinare dubu dari ya
wuceni?
koda bokan yazo nan azancensa sai wannan
mace mai gidan abinci ta zazzaro idanu cikin
tsananin mamaki
jikinta na kyarma ta kurawa hatyan idanu
hatyan ya dubi bokan cikin murmushi
na yarda ka gane ko mu su waye amma ina mai
shawartarka daka cire hannunka daga cikin
wannan lamari idan kuwa
kaki to zakayi biyu babu
ma'ana ka rasa ladanka sannan kuma ka rasa
lafiyarka
idan ka matsama ranka ma zaka rasa haba day~
kodajin wannan batu sai wannan bokan ya bushe
da dariyar mugunta yace
ai inda ba kasa nan ake gardamar kokawa
fa ga fili ga mai doki sai akasa tseren muga
abinda
zai faru
da jin haka sai hatyan ya tura sadirat ta koma
bayansa sannan ya daga sandarsa sama
take ta sake zama takobi
ai kuwa shima bokan sai ya zare takobinsa ya
dubi dakarun sarkin yace
ku ku koma gefe daya ni zan kamasu a hannu mu
tafi dashi gidan sarki
ba tare da gardama ba dakarun suka koma gefe
daya
dasu da sadirat da mai gidan abincin
suka zama yan kallo
nan take su hatyan suka ruguntsume da
azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban
al'ajabi.
sai da suka shafe kusan dakika tamanin suna
kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama da
juriya da bajinta ba tare da dayansu ya sami
nasara akan dayaba
koda hatyan yaga zai bata masa lokaci sai yaja
da baya ya dubeshi cikin murmushi yace
yakai wannan boka hakika na yarda ka iya
yaki amma bari na gwada karfin damtse mu gani
kafin bokan yace wani abu tuni hatyan yadako
tsalle ya gabza masa wawan naushi a fuska
saboda karfin naushin saida ya kife da ribda ciki
alokacin dahar hakoransa guda sukayi fitar burgu
daga bakinsa ya baje kasa sumamme
koda ganin abin da faru ga bokan sai dakarun
suka firgita suka ja da baya suka baiwa su
hatyan hanya suka wuce
ita kuwa wannan mata mai gidan abinci sai ta
biyo hatyan da gudu ta sha gabansa tace
amma fa ka cika gwarzon jarumi mai tarwatsa
maza
don Allah ka dawo izuwa aininhin siffarka mana
naga kyakkyawar suffarka
dajin haka sai hatyan yayi murmushi agareta
yace
kada kidamu zamu sake haduwa
kawai sai ya juya ya dubi wandannan dakarun na
garin idan kuka sanar da sarkinku kun gammu
sai na kasheku dayanku bazai tsiraba
ku fadawa bokan nan wannan sakon idan ya
farfado daga suman da yayi
yana gama fadin haka ya kama hannun sadirat
yajata suka fice daga gidan abincin suka sake
nausawa cikin gari
suna tafiyar sauri sauri gudu gudu
acan gidan abinci kuwa wannan boka bai
farfadoba daga dogon suman da yayiba sai
bayan
rabin sa'a
afirgice ya mike zaune ya kama kalle kalle
kawai sai yaga an gyara wajen fes kamar ba'ayi
yakiba agun.
duk karyayyun kujerun da teburan an kwashesu
an
zuba wadansu sababbi
ga kostomomi azaune suna cin abinci kowa na
harkar gabansa
dakarun da sarki ya hadashi dasu kuwa don
aiwatar da wannan aiki babu ko mutum daya
daga cikinsu
koda ganin haka sai ya mike tsaye zumbur ya
fara neman wannan mata mai gidan abinci
kawai sai yaji an taba kafadarsa ta baya
afirgice ya waiga sai yaga ashe wadda yake
nemace
cikin alamun tsananin damuwa da zumudi
ya dubeta yace
yake sardila ina wadannan yaran sukayi?
sardila tayi dariya sannan tace ai kayi babban
kuskure da bakayi amfani da karfin sihirinka ba
tun farko
boka azwan ya numfasa yace ai wannan yaron
ba karamin takadiri bane
nasan tsafinsa babbane.
abin danake so dake shine zan zuba ido akan
gidanki domin zai iya kawo miki ziyara tunda dai
kin bashi adreshinki
yanzu zan koma gidan sarauta na sanar da
sarauniya halin da ake ciki domin ta karo mini
yawan dakaru
ai komai hatsabibancinsa sarkin yawa yafi sarkin
karfi
kada ki kuskura ki barshi ya sake guduwa idan
har yasake dawowa
koda gama fadin haka sai boka azman
ya ruga waje ya kama dokinsa ya kwance ya
haye kuma ya zubureshi da gudu izuwa gidan
sarki

shidai wannan babban birni ana kiransa da suna
madinatul sarkuf
kuma yana karkashin mulkin wata sarauniya mai
suna badi'atul nauwara
badi'atul nauwara ta kasance kyakkyawar
budurwa ta gaban kwatace kuma shekarunta
ashirin da daya cif cif wato ita da jarumi hatyan
sa'annin juna ne
badi'atul nauwara shahararriyar mayakiyace
kuma basadaukiya
wadda tasha jarumantaka ne anono domin uwarta
ce shugabar sadaukai ~ na kasar gaba daya
mahaifinta kuwa wanda tagaji sarautar a
hannunsa
shine sarkin yakin birnin kafin ya zama sarki
amma shi ma yau shekararsa shida da rasuwa.
mahaifiyarta ta rasu sakamakon ciwon hanta da
yaci karfinta
badi'atul nauwara bata tsafi kuma baya tasiri
akanta
saboda tsananin jarumtakarta da iya yakinta
da sanin tuggun yaki wanda mahaifinta ya koyar
da ita shi yasa duk sarakunan dake kusa da ita
suke shakkarta.
jama'ar gari kuwa suna matukar kaunarta saboda
yawan adalcinta
aduniya babu abinda badi'atul nawwara ta tsana
kamar zalunci
taga adalci a tsakanin talakawa da masu mulki
da attajirai ta kanyi amfani da kudin baitil mali ta
siye kayan abinci a hannun manoman garin ta
rage farashinsa ta siyarwa da talakawa don
magance yunwa da talauci akasar
wannan halayya ta sarauniya badi'atul nauwara
tasa yan majalisarta da manyan attajiran kasar
suka tsaneta
kuma sun sha shirya hanyar da zasubi su kawar
da
ita daga kan mulkinta amma sun kasa
bisa dole suka hakura suka barta akan karagarta
lokacin da sakon sarki shamsal ya riski
sarauniya badi'atul nauwara taga hoton jarumi
hatyan dana yar uwarsa wadanda shekarunsu
basu kai talatin ba
sai bata dauki abinda wani mahimmanci ba
saboda taji ajikinta cewar duk yadda akayi ba wai
laifi sukayiba zaluncin sarki shamsal ne kawai
ya fado kansu
Abinda tayi kawai shine ta kirawo azman ta
hadashi da dakaru ashirin kacall tace ta dora
alhakin kamo hatyan a hannunsa.
tayi hakan ne don kada ace batayi komai ba
amma tasan cewa boka azman da wadannan
dakaru basu isa su kamo wadannan masu laifiba
tunda harma suka iya guduwa daga birnin
shamsal.
'ya'yan sarakai dana attajirai da dama na wannan
birini sun nemi auren sarauniya badi'atul
nawwara
amma sai taki yarda da dukkaninsu
lokacin da fadawanta suka matsa mata akan ya
kamata tayi aure domin ta kare martabarta da ta
masarautarta
sai ta dubesu tace
duk wadanda suke sona da aure ba don Allah
suke sona ba sai domin dukiya,mulkina,da
kyawuna.
da yawansu suna son su aureni ne saboda su
sa; lusuranci da wannan gidan sarautar
domin wata rana mulkin ya koma gidansu.
bazan taba yin aureba koda zan tsufa na
mutu akan karagata ba
face na.sami masoyi wanda zai soni soyayyar
gaskiya ba tareda da yasan koni wace ba
kuma.saina.tabbatar da cewa.badon
kyawuna.yake sona ba
sannan kuma dolene yafini karfin damtse da
jarumtaka
ta hakane kadai nasan cewa zai iya kare.hakkina
da mutuncina.
sarauniya badi'atul nauwara na zaune acikin
fadarta. fadawa da manyan mutanen gari
ana.zaune ana yin fadanci
saiga boka azman ya shigo cikin fadar aguje
kuma adimauce
da zuwansa gaban karagar sai ya zube akasa
yana rawar murya da jiki yace .
ya shugabata yau naga wadannan masu laifi
wadanda sarki shamsal yake nema ruwa ajallo.
kodajin wannan batu sai fadar ta rude da mamaki
gami da kace na ce
harsaida sarauniya badi'atul nauwara ta daga
hannu sannan akayi tsit tamkar mutuwa tagifta
badi.iatul nauwara ta ce
a ina kagansu kuma yaya akayi baka kamosu ba?
nantake boka azman ya kwashe labarin abinda
ya faru agidan abincin sardila ya zaiyane
kodajin wannan labari sai jama'a suka sake cika
da mamaki akaci gaba da hayaniya .
ita kuwa saruniya saitayi shiru tana tunani har
tsawon .yan dakiku
dagachan sai ta dago da kai ta dubi boka azman
tace
tabbas wannan mai laifi ba karamin jarumi bane
zanso nayi arba dashi naga irin jarumtakar tasa a
zahiri
abinda nakeso dakai shine zan kara baka dakaru
guda arba'in ku sake nemansu.
tunda dai duk irin kamannin da mai laifi zai juye
sai ka ganeshi zaku iya kamoshi.
boka azman ya dubi sarauniya cikin alamun
tsananin damuwa kamar zaiyi kuka yace
ya shugabata dakaru sittin fa kenan kacal kika
bani
ai kamata yayi ki bani dakaru dubu dari domin
hatsabibancin wannan mai laifin ya wuce yadda
kike zato
kodajin haka sai sarauniya tayi murmushi tace
kai dai kawai kace ka tsorata dashi amma yaushe
ace
akan mutum daya jal zan baka dakaru dubu dari.
kaje kayi aikinka kawai idan ka kasa ni zan yi da
kaina.
tana gama fadin hakan sai ta mike tsaye ta
kirawo shugaban dakaru tace
maza aje a bawa boka azman karin dakaru
arba'in kuma a bashi kudin abincinsu dana
wahalhalinsu.
kaji aikin mai adalci wacce bata danne hakkin
kowa shugaban dakarun ya russuna yace
an gama ya shubata
nantake shida boka azman suka fice daga fadar
ita kuma
sarauniya badi'atul nauwara ta shige izuwa cikin
gidan sarautar nantake fadawanta ma suka
watse .
kowa ya kama gabansa.
lokacin da sarauniya badi'atul nauwara ta shige
can cikin kuryar turakarta ta sanya kayan barci
sai ta zauna akan gefen gadonta
alokacin da wata kuyangar ta kawo mata ruwan
inibi a kofi ta karba ta dan kurba
kadan sannan ta jiye kofin.akan tebur
har ta yunkura zataje ta kwanta sai maganganun
boka azman suka fado mata arai .
nan take ta mike tsaye ta dauko taswirar fuskar
jarumi hatyan da yar uwarsa sadirat ta kura
musu idanu har izuwa tsawon dakiku
take ta gane cewa ai wadannan matasa yan
uwan junane dolene su kasance uwa daya uba
daya
sabodame sarki sarki shamsal yake neman
wadannan yan uwan biyu a raye
ko a mace ko a raye har ma ya sanya lada mai
tsoka.haka ga duk wandaya kawosu?
tabbas ina bukatar naji cikakken labarin
wadannan yan uwa domin nasan hanyar da zanbi
na taimakesu
tunda dai suna cikin kasata a halin yanzu.
idan har inason jin labarinsu kuwa dolene sai dai
nayi bad da kama na tafi nemansu da kaina
gama fadin hakan keda wuya sai sarauniya
badi'atul nauwara ta baje akan gadonta domin
tayi barci
inyaso idan dare ya soma yi sai tayi bad kama ta
shige cikin garin.
al'amarin su jarumi hatyan kuwa lokacin dasuka
sake karadawa cikin gari sai ya dafa sadirat
akafada
nantake suka sake rikidewa suka koma 'yan mata
guda biyu kuma bakaken fata don kada wani
wanda ya gansu a gidan abinci ya sake ganinsu a
siffar almajirai
da dan jagora ya shaidasu .
nan dai suka ci gaba da tafiya ko waige basayi
harsaida suka je karshen kasuwar sannan suka
zauna
sukayi kamar ciniki sukayi don bagarar da masu
farautarsu .
lokacin da sadirat taga sun shafe lokaci
maitsawo zaune awajen saita dubi
hatyancikin.alamun damuwa tace waishin zaman
me muke tayine a nan wurin?
baka tsoron a sake shaidamu azo da dakaru
masu yawan gaske ayi mana shigar rago?
kodajin wannaan tambaya sai hatyab yayi
murmushi yace
waishin sau nawa ina fada miki cewa indai kina
tareda ni ki daina tsoron kowa?
akwai dabarar da nake shiryawa wacce ita kadai
zamubi mu tsira da rayuwarmu mu kwana hankali
kwance
inyaso da asubah .kafin gari yayi haske sai mu
kara gaba
.......toh me karatu anan zan
tsaya sai watarana domin kuwa bana samun comments
yadda nakeso kamar 20 zuwa sama idan nasamu zanci
gaba da kawo muku littafin da kuma wasuma masu dadi
nine naku 99% bye bye friends
.
Like our page www.facebook.com/hausaebooks
TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- Shuraih Usman
Littafi na biyu 2
Part 2C
.
Haka dai hatyan yayita jan sadirat da hira har
magaruba tayi
adai dai wannnan lokacin ne sardila mai gidan
abinci ta taso daga sana'arta
ta gaban su hatyan ta wuce amma ko kallon su
hatyan batayiba.
sai da ta danyi nisa da tafiya sannan hatyan ya
kama hannun sadirat suka mike tsaye suka
kwashe kayansu da sauri suka bi bayanta cikin
sanda da buya ba tareda tasan suna binta ba.
sai da suka yi nisa da barin harabar kasuwa
sannan aka iso wani wuri mai kama da daji
sannan hatyan ya baiyana tsulum agaban sardila
acikin ainihin siffarsa.
tana ganinsa ta firgita ainun ta wangamebaki
zata rusa ihu
amma sai yayi wuf ya toshe mata baki da tafin
hannunsa
ya dora mata wuka akan.wuyanta yace
idan kika yi mini ihu saina yanka ki.
kiyi duk abindana umarceki idan kina son ki tsira
da
rayuwarki.
gama fadin hakan keda wuya sai ya janye
hannunsa daga kan bakinta
alokacin ne tayi doguwar ajiyar zuciya
ta dubeshi cikin alamun tsoro tace
me kake so nayi ma?
awannan lokacin ne sadirat ma ta fito daga cikin
duhuwar da take boye ta tsaya abayan hatyan.
hatyan ya dubi sardila yace
so nake ki kaimu gidanki mu kwana amma ba
wancan gidan da kika saba kwana ba .
ki fadi ko nawa kike so mu biyaki.
kodajin wannan batu sai hankalin sardila ya
kwanta tayi murmushi tace
shin zaku iya biyana dinare dubu daya.
dajin haka sai sadirat tayi farat tace
haba kwana dayan da zamuyi jal
shine saimun biya dinare dubu
to nawa ne kudin gidan gaba dayansa
sardila tace karfa kimanta cewa masu laifine zan
boye na basu mafaka.
me kike zaton zai faru idan asirina ya tonu?
duk abindana mallaka agarin nan sai sarauniya ta
kwace kuma karshe aturani kurkuku
duk da cewa kuwa sarauniyar mu mai adalci ce
gama fadin hakan keda wuya kawai suka hango
boka azwam tare da dakaru da gudu sun fito
daga cikin kasuwar
cikin hanzari duk su ukun suka fada cikin

TARAR ARADU littafi na daya page 6

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 6
Ta nuna min dakin farida.
"Tana nan inaga shiryawa takeyi"
Ba'ajimaba ta leko
"Umar shigo mana"
Na karasa ,bayau na fara shiga dakinba yanada tasari
matukar tsari.
Akalla yalunka nawa ko uku ko hudu.
Na cusa kaina bayan nacire takalmi.
Tuni tagama shiryawa tana daure gashin kanta ne da
ribbon.
Na kalli dressing din nata na doguwar riga mai hade da
wandonta,da kuma gyaran mayafi. Hakika sun yimata
kyauw
Ni kaina sai na tabbatar da cewa farida tafi karfina.
Sai kuma na sami zuciyata tana mai rayamin cewa afasa
tafiyar kar naje wani ya ganta ya kwacemin ita.
Maganarta ta katsemin tunanina
"Muje ko umar"
Nafito yayin data biyoni.
Mahaifiyarta ta kallemu ta jinjina kai gami da cewa
"You match each other"
Cikin wani harshen dabashi da banbanci dana turawa ,
nida farida muka kalli juna gami da musayar murmushi.
Bisa gaskiya .
Gasikaya ne abinda tafada ta dubemu
"Kuna da camara ko"
Na girgiza kai
"Bamu da camara"
"Tafiyar taku bata cika ba, a london duk duk inda zamuje
da Alhaji da camera muke tafiya haka kuma zaka rinka
gani ga duk saurayii da budurwa"
Ta mike tsaye
"Bari dauko muku tawa"
Ta shiga daki bada jimawa ba ta fito.
Yar karamar camara ce mai ban sha'awa, ta bude kwalin
film ta loda, sannan ta dubemu
"Kuzo nafarayi muku kala daya"
Muka jeru nida farida muna jiran muga ta dauka,
maimakon haka sai ta kama dariya, tafara magana
"Karfa nace muku kauyawa, ahaka za'ayi hoton? To
ma'anar me yabayar? Kubari kuga yanda za'ayi"
Ta nuna mana wata fulawa dake tsakiyar gidan
"Ku koma can, kusa fulawar a tsakiya"
Muka kamar yadda tafada.
Sannan tace
"To kai umar tsinki fure ka mika mata ke kuma miko
hannu ki karba, ku kumayiwa juna murmushi"
Mukayi kamar yadda tafada , sannan hoton,
Kyamarar taja film automatically.
Ta mikomin kyamarar
"To kunga yadda ake hoton soyayya , idan anyi aure
kuma akwai wani salon daban,dasannu zan nuna muku
shi duk randa aka daura maku aure"
Nayi dariya
"Mungode mummy"
Surukartawa tana burgeni, yadda take bidani ta hanyoyi
na musamman babu abin da yadameta tamkar ba suruka
ba.
"To zamu tafi mummy"
Farida tace daita
"To adawo lafya"
Gab da zamu shiga soro tafara magana
" Ina kara tunatar dakufa"
Muka waiwayo domin jin abidna zata fada , tayi
murmushi
" Kun dace da juna "
Muka kalli juna nida farida mukayi musayan murmushi.
Sannan muka juya gareta gaba daya.
Akuma lokaci guda muka hada baki
" Thank you mummy"
******** ********** ********
Na bude shagona bayan dana dawo daga koyarwa .
Bayan na ajiye takardu sainafara tunanin yin wanka.
Na dubi ruwan wankan wanda ni kawai yake jira na
watsashi, adai dai lokacinne aka turo kofar cikin gidar
"Umar ana waya"
Inji matar yayana na dubeta
"Wanene yake waya? Ko baba ne?"
Ta juya hannu
" Ba baba bane yadaice kai yake son yagani"
Na jawop kofar shagopn na bita ciki, ina zuwa na dauka
na kara akunne
"Hello! Wake magana?"
"Ina ruwanka koma waye? Kadai kasa kunne da kyau kaji
abinda za'afada"
"Ina jinka"
Nace dashi yacigaba
"Karabu da farida tun kafin karasa ranka,karabu da ita
tun kafin ta zamto maka cowon ajali"
Na gwale ido saboda tsoro , akuma lokaciguda dana fara
tambayarsa cikin rawar murya .
"Saboda me"
Yadaka min tsawa , duk da awayane saida cikina tai kuka
"Karabu da ita muddin kai kanason rayuwarka ,inkuma
duniya ta isheka sai kafada
"Wai me isa"
Nakara tambayarsa
"Farida bazatayi aure ba har abada"
Lafazinnasa yabata min rai bansan sa'an danace
"Kar ya kake ba"
Ya barke da dariya wadda saida na kauda kan wayar yaci
gaba.
"Dan samari da karambani kake inakai ina karyata abin
da'aka ba ka labarinsa"
"Karya kake"
Nasake fadi
"Farida zatayio aure kuma ni zata aura"
" Shikenan babu mamaki amma dai ba'awannan duniyar
ba"
Na fusata
"Kai makaryaci awannan duniyar kuwa"
Yasake dakamin tsawa
"To shikenan tun da zaka iya TARAR ARADU DAKA .naga
kai mai musune, zamuyi wasa dakai yanda akeyi da dan
biri,sannan a karramaka kamar yadda ake karrama kudi"
Kafin nasake magana ya ajiye kan wayar.
Na dawo shago duk jikina a mace .
Babu mutumin nanne da farida tabani labari.
Inkuwa hakane hakika ina kan hadari.
Sai na kudure azuciyata bazan bawa farida labari ba.
Domin hakan zai iya tashin hankalinta harta fara hangen
kin yiwuwar aurenmu.
Ni kuwa bazanso hakaba. Sannan kuma na kudiri aniyar
bazan shaidawa yayana ba.
Domin kuwa shaidamasa kamar cinna ma takardar
alkawarinmu aurenmu da farida wutane,
Domin babu makawa zai rabani da'ita
Nikuwa ahalin yuanzu duka biyun sakamako daya zasu
bayar, tamkar shida atara da uku ne,da kuma uku atara
dashida,kowanne tara kenan
To hakama in har kaunar farida zata jamin mutuwa to
hakama barinta zaijamin.
Domin ahalin yanzu inna rasata ma zuciyata na iya
bugawa to kaga da wuya ya kasheka gara dadi ya kasheka
to waima da yake cewa zai yi wasa dani.....
@mr:-Shuraih 99%
Zan cigaba

TARAR ARADU littafi na daya page 5

TARAR ARADU
Littafina daya (1)
Written:- shuraih 99%
Page 5
Ni kuwa gani da farinjini.
Aka rinka zuwa wajena naki fita don saboda ina ganin
hanani karatu za'ayi. Don babu abinda irin da daddare
narinka nazari , ahankali na kammala digirina akan
mathematics .
Nakuma yi bautar kasa, sai maganar aure . Nan muka
fara soyayya da wani matashi habib , dan kasuwar kwari
ina mutuwar sonsa ana kokarin samana rana .
Watarana yazo tsallakawa titi dominisa wajen motarsa
wani mai mota yazo ya bankeshi.ko shurawa baiyiba .
Mai motar kuma yagudu"
Sai naga hawaye nazuba daga idonta .
Tacigaba
"Naci kuka har na gode Allah bayan komai yalafa sai
muka kulla da wani ma'aikacin savannah bank mai suna
isma'il soyayyar dayake nuna min hartamantar dani na
habib.
Asheshima ba rabonane ba.
Babbar motace tabi takan motarsa starlet.
Da kyar akaringa banbaro namarsa gashi kuma cikin
darene abin ya afku.
Ba'asan inda mai motar yayiba.
Hankalina yayi mugun tashi yanda kasan nayi hauka
sabida yanda nakeson isma'I'll banso habib ba,
nakasance cikin damuwa yanda samarina ke mutuwa
haka , sai natina zancen mutuminnan shkekaru biyu dasu
ka gabata.
Babu shakka shirinsane anan na shidawa mahaifiyata.
Tace saidai Addu'a tunda ba'asan inda yake ba .kuma ni
kaina tundaga ranar bansake jin duriyarasa ba.
Aifa wannan abubuwa dasuka faru suka sanya akafara
yimin son rakumin yara.
Sai dai mutum yabar kaunar dayakeyimin azuciyarsa
amma babu damar ya baiyana.
Na nesa kuwa ko mutum yafara zuwa sai naga ya janye
narasa dalili.
San dade ana haka sai wani dan'uwana yace yaji yagani
babu wani mamaci sai wanda kwanakinsa suka kare.
Saboda haka yace mahaukaci yahau kura
Sabida haka muka cigaba da soyayya abin gwanin
birgewa har ya mantar dani duk nabaya aka samana
rana.
Sai da abin yarage sati daya kawai akka tsinci gawarsa a
tsakiyar titi.
Aifa daganan sai zamto mujiya ma tafini farinjini.
Babu wani saurayi da yake fuskan tata"
Saita fashe da kuka har nayi zaton bazatayi shiruba.
Nima saida kwalla tazubo min don tausayawa taci gaba
"Wannan shine dalilin dayasa kaga naki amasa maka,
domin kuwa duk wanda ya kulla alakar soyayya dani
sunansa matacce, nikuma banso wani abu ya sameka.
Na dauki kaddara akan cewa Allah bai yi zanyi aure ba.
Domin kuwa har sai na sami wani ya dan kaunace ni
sannan zan ji sarai. Wanda ahalin yanzu abune mara
yiwuwa"
Nadaga mata hannu
"Dakata farida ni ina kaunarki"
Ta girgiza kai
"Bazai yiwuba umar banaso ka mutu sabida kaunar
danakeyi maka"
Na dubeta
"Don Allah farida da gaskene kina kaunata?"
Ta gyada kai
"Wallahi umar inayi maka kaunar da bantabayi ma wani
kamar taba"
Na mike tsaye
"To in hakane farida na daura damarar neman aurenki
koda zan mutu"
Na sun kuyo kusa da fuskarta.
"Wallahi farida babu wata wuya dazatasa na dakata"
Ta girgiza kai kuma alokacin data kirawo sunana ahankali
"Umar ,zaifi kyau kaje kasami. Wata domin samawa
kanka kwanciyar hankali"
Na bata fuska
"To ba kya kunata kenan"
Ta girgiza kai
"Bahaka bane"
"To kice kina kaunata da aure"
Tayi shiru kawai tana dubana
"To shikenan farida barinatafi tunda bakya klaunata"
Najuya cikin hanzari ,ta tare kofar na kalleta babu alamar
fara'a a fuskata
"Way or reply"
Nace da ita , murmushine yafara sauka akan lebenta
,sannan tafara fadin wasu kalmomimasu tsada
"Ina kaunarka da aure umar"
Sai wani farinciki ya mamayeni, kaunarta ya kara shiga
raina murmushi ya kubuce min.
Akuma lokaci guda dana sula le akan kujera.
Ban kula da hadarin dana ke akai ba.
"Za kiga abinda ake kira tsantsar kauna farida"
Shine abinda bakina yafara fada.
******* ********** ********
Tun daga ranar danaje gidan su farida sai ya zamo a
kowane lokaci in ina tafiya akan babur nakantafine cikin
taka tsantsan.
Kai kace mai keken daya doro ciyawa gaba da baya kuma
ya debi garke tumaki,badon komaiba kuwa saidon samun
garkuwa daga mutumin da farida tace min shine
sanadiyyar mutuwar masi neman arenta har mutum uku
Na kirga adadin makwanni cikin tafi daya.
Amma har yanzu banga abinda ya sameni ba nida farida.
Munyi matukar shiga ran juna.
Soyayya agida sannan wani salon dabn a makaranta.
Mahaifiyarta tayi matukar faribciki da soyayyarmu, baka
da baka ta fadamin
Duk samarin farinda dasuka shede bataga wabda suka
dace da juna kamar niba.
Allah yabar ku tare har abada naji dadin maganar.
Yau ranace ta lahadi da kuma muka shirya zuwa yawon
bude ido dabi da masoyiyata.
Sabbabin jacket nasiyo musamman don tafiyar ta kara
armashi
Nahadu iya haduwa. Ga wanda bai sanniba zai dauka dan
wani ne daga yayan jiga jigan garinnan nan kuwa ba haka
lamarin yakeba.
Na iso gidan su farida da misalin karfe hudu, ahalin yanzu
nazama dan gidan salllama kawai nayinashiga,
Na tarar da mahaifiyarta tana karanta wat mujallar Africa
banyi mamaki ba
Sakamakon cewa na dade da sanin cewa tan jin har shen
nasara sakamakon zama a kasar ingla na tsuguna na
gaisheta ta amasa da fara'a bisa dukkanin alamu shigar
tawa ta burgeta.
Ta nuna min dakin farida......
@mr shuraih 99%
Tobe con....
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter