Results

TARKON MUTUWA littafi na Uku 3 complet na Abdulaziz Sani M gini

TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- Shuraih Usman
Littafi na uku 3
Part 3 A
.
Kawai sai sadirat ta rungume hatyan cikin
farinciki mara misaltuwa tace shikenan mun tsira
daga sharrin abokan gabarmu
yakai dan uwana yanzufa saura kiris mufice daga
wannan nahiya gaba daya.
kodajin wannan batu sai hatyan yayi doguwar
ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya yace
akwai matsala yake yar uwata.
kiyi sani cewa har acikin wannan jirgi da muke
akwai yan leken asirin sarki shamsal da yawa.
tun afarkon shigowarmu cikin jirgin nan na
fahimci hakan.
inba don mun chanja kamannin muba da farat
daya zasu gane mu.
duk da hakan sai munyi mugun taka
tsantsan,gaskiya sarauniya badi'atul nauwra
tabamu babbar gudun mawa wacce ba zamu
taba mancewa da ita ba.
inbadon ita ba da yanzu bamu iso nan ba.
sardila ma ta taimakemu sosai
ni ina mamakin irin wannan sa'a tamu ma har da
muke haduwa da masoyan da suke taimakon mu
alhalin basu sanmu ba muma bamu sansu ba
ki sani cewa ko isasshen barci bamu isa mu
dinga yi ba acikin wannan jirgi domin makiya
zasu iya amfani da damar hakan su gane ko mu
su waye su cutar damu.
kada ki manta cewa a mace ko araye sarki
shamsal yake son ganinmu.
kodajin wannan batu sai hankalin sadirat ya
dugunzuma tace to yanzu yadda bamuyi wani
barcin kirkiba jiya da daddare yaya zamuyi
yanzu?
nifa kaina har ciwo yakeyi saboda jin barci.
hatyan yace yanzu ke ki kwanta kiyi barci ni
kuma zanyi gadinki idankika tashi daga barcin
dan kanki sai nima na kwanta kiyi gadina ammafa
da zarar kinji wani motsi komai kankantarsa ki
tasheni daga barci
saboda komai zai iya faruwa ako yaushe kuma
kadaki yarda da kowa acikin jirgin nan koda kuwa
ma'aikatan jirgin ne.
dajin haka sai murna ta kama sadirat ta kwanta
ta kama barci abinta tamkar ba'a cikin tashin
hankali takeba.
shikuwa jarumi hatayn sai ya dubi hoton zanen
wani gunki dake jikin bangon dakin na wata
sarauniya .
nantake sai ya tuno da sarauniya badi'atul
nauwar nanfa ya tuno da lokacin da suka fafata
kazamin yaki da ita kawo izuwa lokacin data
kwaye fuskarta
suka yi arba da juna.sannan ya tuno da irin
maganganun da ta yi masa da yarda akarshe ta
taimakesu suka fice daga cikin birninta har suka
iso wannan waje .
koda jarumi hatyan yazo nan atunaninsa sai yaji
akaron farko yaji son ya sake ganin wani mutum
wanda suka taba haduwa kuma suka rabu.
ma'ana babu abinda yakeso a.rayuwarsa sama
da sake saduwa da sarauniya badi'atul nauwara.
to wai shin menene dalilin da yasa naji ina son na
sake ganinta?
amsar da hatyan ya kasa baiwa kansa kenan.
ashe ita ma sarauniya badi'atul nauwara ta tsinci
kanta itama cikin irin wannan hali wanda hatayn
ya tsinci kansa acikinsa wannan dare lokacin data
koma gidan sarautarta
ta shiga cikin turakarta ta kwanta akan gado
bayan ta sanya rigar barcin ya gagareta
domin nantake ta shiga tuna duk abubuwan da
suka faru tsakaninta da jarumi hatyan.
abin daya fara burgeta a tare dashi shine
tsananin jarumtakarsa da juriyarsa ta yaki
gumurzu wacce ta zamo iri daya da tasa
abu na biyu shine da yakara burgeta shine
alokacin data bayyana fuskarta da jikinta a
gareshi
bataga yayi irin dimaucewar da maza suke yi ba
idan suka ganta.
kuma bataga yayimata kallo ba wanda yake nuna
yana sonta ba.
kawai dai yayi mata kallon mamaki bisa ganin
kyawun da Allah ya bata.
anya kuwa hatyan bashi bane irin namijin da na
dade ina nemaba .
wanda nake ganin cewa shine yafi dacewa da ya
zama abokin rayuwata.
to ai kuma hatyan ba sa'a na bane akalla na
girmeshi da tazarar shekaru takwas zuwa tara.
koda yake ai babu ruwan so da girma,kudi ko
matsayi idan har hatyan shine irin masoyin da
nake nema to tabbas zanyi masa ragowar
jarrabobin da zan tabbatar da hakan da zarar
mun sake saduwa.
haka dai sarauniya badi'atul nauwara taci gaba
da yin wannan tunani har barci ya saceta bata
sani ba.
Acan birnin bindal kuwa lokacin da sarki shamsal
yaga gaba daya dakarun guda dubu dari hudu
wadanda aka tura farautar su jarumi hatyan
izuwa kowanne bangare na kasar sun dawo babu
wata nasara
sai ransa ya baci kuma hankalinsa ya
dugumzuma ainun yarasa abinda ke masa dadi
aduniya .
nantake sarki shamsal ya tura aka kirawo masa
boka daizur ya dubeshi yace
yakai abin dogaron bindal kayi sani cewa abari
ya huce shi yake kawo rabon wani.
duk da cewa mun baza dakarun mu da yan leken
asirin mu izuwa dukkan kasashen dake wannan
nahiya kuma mun baza hotunan wadannan yara
ako'ina.
zuciyata na yawan bugawa da karfi akan wannan
al'amari inaji a jikina cewar wannan yaro zai iya
tsallake dukkan tarkokin mu.
bazan iya ci gaba da zaman ranar da za' akawo
min labarin cewa an kamasuba a wata kasa .
kasani cewa idan har ya sami nasarar fita daga
wannan nahiya tamu abune mawuyaci mu iya
kamashi kuma komai daren dadewa sai ya dawo
kasar nan cikin gagarumin shiri domin daukar
fansa gami da karbar karagata.
abinda nake so dakai shine kaje kayi shiri kazo
mu tafi farautar wannan yaro a yau dinan ba
zamu dawo gidaba face mun riskeshi mun tsinke
masa kai.
asannan ne zan sami nutsuwa da kawanciyar
hankali
lokacin da sarki shamsal yazo nan a zancensa sai hankalin
boka daizur ya dugunzuma ainun fiye
da ko yaushe ya sunkuyar da
kansa kas yayi shiru yana tunani har zuwa
tsawon yan dakiku daga chan.
saiya dago da kansa ya dubi sarki shamsal cikin
alamun damuwa yace
ya shugabana tashin hankalina dai
guda dayane.
yanzu idan zaka tafi wa zaka barwa jiran
karagarka?
kodajin wannan tambaya sai sarki shamsal yayi
dariya sannan yace kwantar da hankalinka bazan
bawa yarima rikon karagata ba
saboda nasan shashashane ba abinda zai iya sai
yiwa mata wayo da hikima wacce zai iya
zartarwa,ka duba ka gani tun baifi shekara tara
ba nake bashi horon yaki gashi ya gajeni a
sadaukantaka.
amma gashi akaron banza yaro dan shekara
ashirin da daya kachal ya sare masa hannu
sa'adda suka fafata
Zainur bai dace da ya gajeni ba.
duk da cewar ina matukar kaunarsa
amatsayinsa na dana guda daya jal aduniya
zan bar rukon karagata a hannun waziri,
nayi imani cewa idan har kaine zakayi mini jagora
acikin wannan tafiya da zamuyi to tabbas acikin
kwanaki kadan zamu gano inda wadannan yara
suke mu riskesu.
sa'adda sarki shamsal yazo nan a zancensa sai
boka daizun yayi ajiyar zuciya yace
hanya dayace zamubi mu gano inda wadannan
yara suke acikin kankanin lokaci.
hanyar kuwa itace dolene mu nemo sarkin
mafarauta a duk inda yake,
idan muka hada karfi da karfe ni dakai zamu iya
kamashi a hannunmu yayi mana jagora izuwa
inda wadannan yara suke a cikin kwanaki kadan.
to amma shima fa ya bace mana bat bamu san
inda yakeba yanzu.
bisa binciken da nayi yana nan a cikin daya daga
cikin da zuzzukan dake wajen wannan birni namu
ya buya kuma ya saddakar da cewa zai karasa
sauran rayuwarsa
tunda bashi da kowa aduniya sai tsafinsa da
kuma dukiyar daya tara amma babu "da "bare
jika kuma babu dangi.
sa'adda boka daizun yazo nan azancensa sai
sarki shamsal ya kamu da tsananin farinciki ya
bushe da dariya .
yayita kyakyatawa kamar bazai daina ba.
daga chan kuma sai ya tsuke bakinsa ya turbune
fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa
ya dubi boka daizun yace
ai mai nema yana tare da samu,
maza kaje ka kammala shirinka adaren yau
zamu bar garin nan mu tafi farautar sarkin
mafarauta a cikin dazuzzukan kasarnan.
ba zamu daina farautarsa ba harsai mun ganshi
mu idda nufinmu akansa.
ba tare da wata gardama boka daizun ya rissina
yace
angama ya shugabana
nantake boka daizun ya tafi izuwa gidanshi
shikuwa sarki shansal sai ya tura aka kirawo
yarima zainur tare da dukkan yan majalisarsa
yasanar dasu hukuncin daya yanke na tafiya
farautar sarkin mafarauta tare dasu hatyan.
sannan kuma ya sanar dasu cewa yabar rikon
karagarsa ahannun waziri.
kodajin wannan batu sai hankalin yarima zainur
ya dugunzuma ainun kuma yaji ransa ya baci bisa
jin cewa bashi aka barwa rikon karagar mulikba.
shin hakan yana nufin sarki bazai bashi
gadon sarauta ba kenan?
menene dalilin da zai sa ya hanashi alhalin shine
kadai dansa aduniya ?
wata zuciyar sai tace dashi ai saboda ka zama
muskini ne mai hannu daya
abin kunya ne ace magajin wanan karaga musaki
ne
aikuwa idan sarki yayi mini haka saina shuka masa
bakin cikin dazai tafi dashi can kabarinsa.
kamar yadda sarki shamsal ya shirya haka
al'amarin da ya kasance.
wato acikin wannan dare boka daizun ya
kammala dukkan shirye shiryensa yazo gareshi
ya tarar dashi ya gama dukkan shirinsa tuni har anbada
rikon karagar mulkinsa.
nantake sarki shamsal yaja matarsa gefe daya wato
mahaifiyar yarima zainur inda babu wanda zayaji
abinda zasu tattauna
ya dubeta cikin nutsuwa yace
yake matata kiyi sani cewa danki baiji dadin
hukuncin dana yankeba
na karanta hakan acikin idanunsa.
to abinda nake so dake shine kiyi kokarin nusar
dashi dalilin yi hakan agareshi kuma ki tausasa
zuciyarsa don kada yayi yunkurin cin amanata
ko yin wani abu na ba dai dai ba,kinfi kowa sanin
halina.
ni cinnaka ne bansan na gidaba
idan har ya shiga gonata bazan daga masa
kafaba duk da tsananin son da nake masa
zan iya rasa dana na sami wani amma idan na
rasa karagata ko mutuncina
da darajata na rasasu kenan har abada.
ni ba ragoba ne kuma ban gaji ragonta ba.
kakana da ubana har suka bar duniya ba'a taba
zubar da digon jininsu ba daga jikinsu ba afilin yaki
haka nima don haka banga dalilin da zaisa na
haifi ragon da zai kasa kare wannan martabarba.
ko me zai sami yarima a rayuwa ragwancinsa ne
ya janyo masa. da
wannan furuci nake miki bankwana sai na dawo.
koda gama fadin hakan sai sarki shamsal ya
rungume matarsa suka kankame juna har zuwa
tsawon yan dakiku daga can sa ya janye jikinsa
daga jikin nata ya sumbaci goshinta.
awannan lokaci yarima zainur yana tsaye yana
kallonsu.
maimakon sarki shamsal yaje inda yarima zainur
yake ya runguneshi su yi bankwana dashi sai
kawai ya daga masa hannu kuma ya juya masa
baya ya tafi izuwa inda dokinsa yake ya kama ya
hau.
ba tare da wani bata lokaciba suka kama hanya
shida boka daizun suka fice daga cikin gidan
sarautar aka bisu da kallo kawai har suka bace
da gani
adaidai wannan lokacine hawaye ya subutowa
yarima zainur ya tabbatar da cewa lallai son da
sarki yake masa ya disashe.
tun daga ranar da yarima zainur aka sare masa
hannu sarki yaja da baya dashi yadaina so da
kauna da kulawa kamar yadda ya saba nuna
masa.
sai da su sarki shamsal suka shiga cikin
dazuzzuka guda dari da ashirin da daya suna
neman inda sarkin mafarauta yake basu
ganshiba.
awannan lokacine sukaji sun sare suka fitar da
rai ga samun ganinsa gaba daya.
adaren kwana ashirin da dayan suka shigo dajin
karshe wanda indai basu ganshi acikinsa ba to
babu inda zasu ganshi sun san cewa ya fice
daga cikin yankin kasar gaba daya.
Awannan lokaci sun gaji likis kuma gashi dare ya
soma rabawa don haka sai suka kafa tanti domin
su yada zango.
bayan sun gama kafa tantin sai suka fahimci
cewa ruwan shansu ya kare don haka sai boka
daizun ya dubi sarki shamsal yace ya shugabana ruwan
shan mu
ya kare don haka zan tafi nema ko zanga rafi
akusa.
dajin haka sai sarki shamsal yayi murmushi yace
ai wannan ba laifi bane.
nan take boka daizun ya dauki battocin ruwansu
guda biyu ya nausa gabas
boka daizun na cikin tafiya sai ya hango alamun
wuta a nesa dashi.koda ganin haka sai boka
daizun ya fara tafiyar sanda yana kuma karanta
wadansu dalasiman tsafi acikin ransa
.
Nidinne dai shuraih Usman
Inkiya 99%
Nake posting
.
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- Shuraih Usman
Littafi na uku 3
Part 3 B
.
Nantake ya bace bat aka daina ganinsa kuma sai
gashi yana tafiya a sama bisa iska maimakon a
kasa bisa turba yadda za'a rinka jin takun
sawayensa.
Nanfa ya durfafi inda ya hangi hasken wuta
sannu a hankali ya dinga kusantar wajen sai yaga
ashe wata yar karamar bukkace awajen kuma
agaban bukkar aka kunna wuta ana gasa wata
barewa amma babu kowa awajen.
Har boka daizun ya iso daf da barewar wacce ta
gasu sosai har tana digar da mai baiga kowaba.
nantake boka daizun ya hadiyi yawu bisa ganin
wannan gasashshen nama domin tunda suka fito
shida sarki shamsal a tsawon kwanaki ashirin da
dayan ko sau daya basu ci nama ba.
abincin guzurinsu kawai suke ci basuyi farauta
ba ko sau daya ba.
har boka daizur yakai hannunsa zai yanki wannan
nama yaci sai kawai yaji an daka masa tsawa.
a firgice ya waigo bayansa domin yaga wanda
yayi masa wannan tsawa.
take kuwa yayi arba dashi.
bakowa bane ba face sarkin mafarauta.
nantake aka fara kallon kallo.boka daizur yaji
kamar ya bude bakinsa ya kwallawa sarki
shansal kira amma sai yaki.
tsawon 'yan dakiku suna yiwa juna kallon kar ta
san kar sannan sarkin mafarauta ya bushe da
dariya
lrin ta mugunta yace
sannunku da isowa dajin hajarul ausad
yau kwanana bakwai acikinsa ina jiraku.
anan ne za'a yita ta kare atsakanina daku.
ko dai na hallakaku ko kuma ku hallakani.
domin nasani cewa baku fito domin ku
hallakaniba.
sai domin ku kamani da hannunku ku tilasta mini
nayi muku jagora izuwa inda su hatyan suke.
kai yanzu a tunaninka hakan agareni abune mai
sauki?
nasani cewa idan kuka hada karfi da karfe kai da
sarki zaku sami nasara akaina .
amma taya kake zaton cewa zan baku wannan
dama?
ai tuni na dauki dukkan matakai na hana faruwar
hakan.
kafin sarkin mafarauta ya gama rufe bakinsa sai
boka dazun ya shamma ceshi yayi nuni da
hannunsa zuwa kansa.
nantake wata irin gagarumar iska mai karfin
gaske ta suri sarkin mafarauta tayi sama dashi
ta rinka yin katantanwa dashi asararin samaniya.
nan danan yaji yana neman fita daga hayyacinsa.
ai kuwa shima sai yayi nuni da hannunsa izuwa
kan boka daizun.
take shima irin wannan iska ta sureshi tayi sama
dashi ta dinga katantanwa dashi.
sai gashi duk su biyun sun fita daga hayyacinsu.
babu shiri kowanne ya janye hannayensa suka
fado kasa tim a amtukar galabaice suna
numfashi sama sama kamar ransu zai fita.
maimakon su hakura sai sukaci gaba da yakar
juna suka rinka watsawa kansu mugayen
abubuwa kamar macizai,kunamai,da sauran kwari
masu mugun dafi suka rinka cizonsu da
harbinsu.
nan da nan ko ina ajikinsu ya rinka kumbura suka
dinga faduwa kasa suna ihu da birgima suna
zubar da jini daga cikin bakinsu.
duk wanda ya gansu cikinsu wannan hali dole ne
ya ce duk mutuwa zasuyi.
kawai kuma sai suka rinka tashi sama tamkar
tsuntsaye masu fukafukai suka rinka yiwa
junansu karo da ka afuska.
sannan suka rinka naushin junansu .nan da nan
suka sake galabaita ainun.
jini ya dinga zuba daga sassan jikisu suna cikin
wannan haline boka daizun ya kyallara ido yaga
wata shudiyar laya mai dunkulallen dutse a
wuyan
sarkin mafarauta.
shikuwa sai ya rike hannunsa da kyau sukaci
gaba da dukan junansu ahaka.
awannan lokaci suna shawagine asaman wani
tsauni wanda kasansa ramine mai zurfin gaske
kuma can karshen ramin ramin kogine wanda
ruwansa ke gudu da karfin gaske .
kwatsam ba zato ba tsammani sai sarkin
mafarauta
yaga sarki shamsal yayi tsalle ya taso sama
izuwa kansa tamkar daga cikin baka aka cilloshi.
kafin sarkin mafarauta yayi wani yunkuri tuni
sarki
shamsal ya gabza masa wani wawan naushi
afuska
damar da boka daizun ya samu kenan ya cizge
wannan shudiyar layar daga wuyansa.
nan take sarkin mafarauta ya sallamo kasa izuwa
kasan wannan rami mai zurfi.
saboda zurfin ramin su kansu su sarki sai da
suka leko kasa amma basu iya ganin sarkin
mafarauta ba.
cikin tsananin farinciki boka daizun ya daga
wannan sama ya kura mata idanu.
nantake sai ga hoton su hatyan a cikin jirgin
ruwa
akan teku.
koda ganin wannan hoto sai shima sarki shamsal
ya kamu da tsananin farin ciki ya dubi boka
daizur yace
yanzu daga nan zuwa inda su hatyan suke
tafiyar kwanan nawa ce?
boka daizur yayi ajiyar zuciya yace idan akan
doki zamu tafi tafiyar kwana goma sha tara ce.
kuma kafin mu riskesu tuni jirgin ruwan ya isa
birin istanbul.
kaga kenan ba zamu riskesuba acikin tekun
idan kuwa suka isa birnin istanbul acikin kwanaki
uku kachal zasu fita daga wannan nahiya gaba
daya
idan kuwa suka fita shikenan dukkan shirin mu ya
rushe.
koda boka daizur yazo nan azanncensa sai sarkki
shamsal ya firgice yace.
yanzu mene abinyi yakai abin dogarona?
boka daizur yayi shiru yana tunani har izuwa
tsawon 'yan dakikku.
daga can kuma sai yace zan iya kirkirar
tsuntsun dazai daukemu yakai mu har bakin
wannan teku a cikin kwana daya da yini daya.
muna zuwa saimu dauki hayar karamin jirgi mai
gudun gaske wanda zamu iya riskar jirginsu
hatyan kafin su isa birnin iistanbul.
kodajin wannan batu sai farinciki ya turnuke
sarkmi shamsal yace maza kayi wannan tsuntsun
tsafi mu tafi yanzu ba tare da bata wani
lokaciba.
kodajin haka sai boka daizun ya zauuna akan
tsaunin dirshan ya debo wadansu 'ya'yan wuri
guda hudu daga cikin aljihunsa yazube kasa
gabansa.
kawai sai ya zaro wuka acikin kubenta a kugunsa
ya yanki tafin hannunsa.
ya rinka diga jininsa akan 'yayan
wurin yana karanta wadansu dalasimai na tsafi.
cikin kankanin lokaci saiga wata irin
gagarumar iska ta rinka kewaye
'ya'yan wurin wacce ta addabi sarki shamsal da
boka daizur din da kansa tamkar zata suresu tayi
sama dashu.
jim kadan sai wadannan 'ya'yan wuri suka rikiide
suka zama wani jibgegen tsuntsu wanda yafi
girman jimina biyu.
batare da bata wani lokaciba sai sarki shamsal
da boka daizur sukayi sauri suka hau kan
tsuntsun
ya tashi dasu sama ya luluka sama acikin
gajimare yana falfala azababben gudu
Ashe alokacin da wannan ta taso sai wannan
koriyar sarka ta sarkin mafarauta ta sulalo kasa
daga aljihun boka daizul
ta gangara kasan wannan tsauni ta fada
cikin kogin ba tareda boka daizur ya ankaraba.
sai da su boka daizur suka shafe tafiyar yini
guda akan wannan tsuntsun suntafi sannan ya
tuno
da batun wannan sarka
nantake ya fara laluben aljihunsa.
koda ganin haka sai sarki shamsal ya dube shi
cikin damuwa yace
waishin mene kake nema?
maimakon boka daizur ya bashi amsar wannan
tambaya
sai ya dauko madubin tsafinsa ya shafeshi da
hannunsa na hagu.
take duk abindaya faru ga sarkar ya bayyana
akan madubin
koda sukaga cewa sarkar ta fada kasan wannan
tsauni sai suka takarkare suka rusa uban ihu
atare
cikin tsananin bakin ciki tamkar suyi kuka saboda
sunsan cewa indai suna tare da wannan sarka to
duk inda su hatyan suke sai sun samo su
sarkar ce kadai zata iya bayyana wannan surrin
yanzu dogaronsu daya ne.
wato dolene suyi iya yinsu su riski su hatyan a
cikin wannan teku.
kamar yadda boka daizur ya fada haka al'amarin
ya kasance
wato acikin kwana daya da yini daya wannan
tsuntsun tsafi ya sauko ya ajiye su abakin
wannan teku
inda tashar jirgin ruwa take .
da zuwansu sai suka siyi wani karamin jirgin mai
gudun tsiya suka shiga ciki su biyu kachal.
boka daizur ne ya dinga sarrafa jirgin da sihirinsa
ya rinka kara gudunsa suka dinga ratsa cikin
teku tamkar sararin samaniya suke ratsawa
tafiyar sa'a uku kachal sukayi suka hango jirgin
su hatyan
nantake farinciki ya baibayesu
kawai sai sarki shamsal ya dauko takobinsa ya
fara wasata
saboda yasan cewa dolene tasha jinin babban
makiyinsa nan da cikar dan lokaci.
a chan cikin jirgin su hatyan lokacin da dakaru
da ma'aikatan jirgin
suka hango wani jirgin ya durfafesu yana wani
mahaukacin gudu na ban al'ajabi
wanda basu saba gani ba sai hankalinsu ya
dugunzuma ainun sukayi zaton ko jirgin yan
fashine don haka suka zare makamansu.
suka zauna cikin shirin kota kwana.
dudufniyar dakarun jirgin data ma'ikatance tasa
suka farga suka san cewa lallai akwai wani
bakon al'amari da yake shirin faruwa
cikin hanzari hatyan ya fiddo wani dan karamin
madubin tsafinsa da baifi girman tafin hannunsa
ba ya shafeshi
nan take yaga jirgin daya biyo nasun kuma yaga
wadanda suke cikin jirgin wato
su sarki shamsal da boka hatyan
koda ganinsu sai hatyan ya mayar da madubinsa
cikin aljihu
sannan ya dubi sadirat yce
duk abinda zai faru karki fito daga cikin wannan
dakin
harsai na umarceki
yana gama fadin haka sai ya zare takobinsa
kuma
ya dauki garkuwarsa.
koda ganin haka sai hankalin sadirat ya
dugunzuma tace
duk yadda akayi sarki shamsal ne ya riske mu
har nan domin baka daukar garkuwa idan zakayi
yaki da wadansu dakaru ko jaruman da basu
amsa sunansuba
dajin haka sai hatyan yace
tabbas kin canka daidai amma abinda nakeso
dake shine
ki kwantar da hankalinki nayi miki alkawarin babu
abinda zai sami daya daga cikin mu
kawai ki bani rabin sa'a kachal zanje na hana su
karasowa nan din ma
ki sani cewa muna shiga birnin askandariya kuma
da zarar mun shiga chan din
shikenan mun tsallake duk wani taarkon sarki
shamsal
koda gama fadin hakan sai jarumi hatyan ya juya
ya fice daga cikin dakin ya tafi izuwa saman
jirgin rike da takobinsa tsirara
adai dai wannan lokacine wata kurciya rike da
wata takarda ajikin kafarta ta dira acikin jirgin
dirarta keda wuya sa wani badakare yazo ya
kama kurciyar ya cire mata takardar dake jikinta
ya warware
ya karantata afili kamar haka
nine sarki shamsal tareda bokana daizur na
tunkaroku sbd
masu laifin da nake nema suna cikin wannan jirgi
kada ku bari su fita gani nan isowa yanzun nan
koda gama karanta wannan wasika sai barden ya
juyo ya dubi hatyan wanda suffarsa ke Kama da
ta
bafatake dan shekara arb'in da wani abu ya kura
masa idanu yace
wanene kai?
kodajin wannan tambaya sai hatyan yace
wannan wacce irin tambayace ta rainin hankali?
duk wanda ka gani acikin jirginnan ai bafatakene
kuma birnin askandariya zasu don aiwatar da
kasuwanci
dajin wannan batu sai badakaren ya dakawa
hatyan tsawa yace
karya kakeyi tunda kuka shigo jirginnan kai da
dan
uwanka naji ban yarda dakuba don haka kune
masu laifin dasarki shamsal yake nema
.
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- prince auwal auzab
Post:- Shuraih Usman
Littafi na uku 3
Part 3 C
.
To kasani cewa kun kawo kanku gurin da ake
nemanku domin gaba dayan mutanen da suke
cikin jirgir nan 'yan leken asirin sarki shamsal ne
babu ta inda zaku iya guduwa
gama fadin hakan keda wuya sai barden da
ma'aikatan jirgin da dakarun suka bushe da
dariya
ba zato ba tsammani sai sukaga shima hatyan ya
bushe da dariya
awannan lokaci jirgin su sarki shamsal ya
kusanto wannan jirgin da su hatyan suke dan tazarar
dake
tsakaninsu bata wuce kamu arba'in ba.
koda ganin haka sai hatyan ya dubi matukin jirgin
nasu
suna hada idanu sai matukin jirgin ya dauke kan
jirgin ya durfafi wani katon tsauni dake cikin
tekun
kodaganin haka sai hankalin kowa ya
dugunzuma
kafin dayansu yayi wani yunkuri tuni sunyi karo
da tsaunin
take jirgin ya tarwatse ya nutse akasan ruwan
koda sarki shamsal da boka daizur sukaga abin
daya faru ga jirgin su hatyan sai hankalinsu ya
dugunzuma.
daizur yace ya shegen yaron nan yayi tsiyar .
amfani yayi da karfin sihirin tsafinsa ya haddasa
wannan hadarin jirgin muyi sauri mu karasa muyi
nutso izuwa kasan ruwan mu lalubo inda suke
tun kafin su sami damar tserewa nan da nan
kuwa jirgin su sarki shamsal ya iso bakin wannan
tsauni
da isowarsu sai sarki shamsal ya kwabe kayan
jikinsa ya daka tsalle ya fada cikin tekun ya
kama lalube acikin tekun ya kama dube dube
akasan ruwan
ba abinda ya gani face gawar tsirarun dakarun
jirgin da ma'aikatansa suna ta ninkaya
sunata kokarin ceton rayukansu da nufin su isa
kan tsaunin amma sauran gaba dayan 'yan
uwansu sun zama gawa kuma ba komai face
sassan jikin jirgin da soke jikinsu alokacin
dayayi wannan hadarin ya tarwatse.
sarki shamsal yaci gaba da dube dube har cikin
rugurgujajjen jirgin sai da ya duba ko'ina
baiga hatyanba da 'yar uwarsa sadirat ba
cikin kaduwa da mamaki sarki shamsal ya taso
izuwa saman tekun ya nufi inda jirginsa yake
kawai sai ya hango boka daizur kwance asaman
jirgin kamar gawa
ga jini na yoyo a hancinsa da bakinsa.
cikin tsananin kaduwa da fushi sarki shamsal ya
takarkare ya kwarara uban ihu
mai tsananin firgitarwa kawai sai ya kwalawa
hatyna kira yana cewa kai karamin alhaki
matsoraci
Ka fito fili idan ka isa na sani cewa kana nan kusa
babu ta inda zaka iya gujemini tunda muna cikin
tsakiyar teku
wannan tsauni ne kai dai mafaka sai kuma jirgina
guda daya gashi.
kafin sarki shamsal ya gama rufe bakinsa sai ya
hango jarumi hatyan tare da 'yar uwarsa sun mike
tsaye akan tsaunin wanda yakasance dan karami
atsakiyar tekun.
awannan lokaci jarumi hatyan ya cire rigarsa.
kirar jikinsa ta sadaukai duk ta bayyana
kwanjinsa ya kumbura kuma duk jijiyoyin jikinsa
sun tashi sunyi burdin burdin.
fuskarsa sai gyatsine takeyi saboda fishi yana rike
da takobinsa tsirara
koda ganin haka sai sarki shamsal ya bushe da
dariyar farinciki
saboda yasan cewa komai yazo karshe .
tuni ya cire rigarsa kawai sai shima ya
daka tsalle daga cikin jirgin sa ya dira akan
tsaunin ya zamana cewa tazarar da take
tsakaninsa da hatyna bata wuce taku biyarba
idan mutum yaga sarki shamsal da jarumi hatyan
awannan lokaci yaga banbancin girman jikinsu da
kirar jikinsu dolene ya tausayawa hatyan domin
kamar a ajiye dan tsakone a gaban shirwa
sarki shamsal ya ninka hatyan sau uku a komai.
nanfa aka fara kallon kallo tsakanin sarki
shamsal da jarumi hatyan alokacin dajikin sadirat
ya fara karkarwa saboda tsananin tsoro kuma ta
fashe da kuka .
hatyan ya daka mata tsawa yace
na gaya miki babu abinda zai samemu
ki tuna cewa wannan azzalumin sarkin
makiyinmu ne kuma azzalumi ne shi
bai dubi zaluncin da dansa yayi mana ba na
kashe iyayenmu sai don kawai na sarewa dansa
hannu shine yakeson hallakamu.
to ka sani ba yau zan mutuba saina rayu na
girma na zama babban mutum
asannan ne zan dawo birnin bindal na kasheka
agaban danka yarima zainur domin daukar fansar
ran iyayenmu
wannan alkawarine na daukarwa kaina kuma
saina cikashi.
sa'adda jarumi hatyan yazo nan a zancensa sai
sarki shamsal ya bushe da dariyar mugunta
lokaci guda kuma ya murtuke fuskarsa yace
banyi farautarka ba don abinda kayiwa dana sai
domin na tsare mutuncina da karagata
bokaye sun tabbatarmini da cewa idan har na
bari kakai shekara talatin da biyar aduniya to
tabbas zakazo har cikin gidana ka cini da yaki
ko ayanzu bisa irin abubuwan da kayi na
dabara,basira da hikima na gamsu cewa nan
gaba zaka iya yimini juyin milki
nayi mamakin yadda ka sammaci gaba dayan
mutanen cikin jirginnan kasa jirgin yayi hatsari
suka mutu
dai dai kune suka rayu da kyar bayan sun galabaita
nayi mamakin yadda akayi.ka shammaci boka
daizur ka sumar dashi har naga jini yana zuba
daga bakinsa da hancinsa
waishin naushinsa kayi ko kuwa bayansa ka
sudado ka buga masa makami?
sa'adda jarumi hatyan yaji wadannan tambayoyi
sai yayi murmushi yace
ai duk wadannan abubuwan danayi suna daga
cikin sirrin gumurzu da makiya
bazan iya sanar dakai yadda nayi musu ba don kada
kayi mini satar hikima.
kada ka isheni da surutan banza muyi abinda
zamuyi amma nayi maka alkawarin bazaka iya
kasheniba anan kuma nima bazan iya kasheka ba
sai wancan lokaci da nayi alkawari.
gama fadin hakan keda wuya sai jarumi hatyan
ya daka tsalle daga inda yake a tsaye tamkar an
harboshi daga cikin kibiya ya kawowa sarki
shamsal wawan sara a kafada da nufin ya cire
masa hannu
cikin baki zafin nama sarki shamsal ya sunkuya
takobin ta sari iska
kafin hatyan ya juyo da baya asaman tuni sarki
shamsal ya damki makoshin hatyan ya shakeshi.
sai gashi kafafun hatyan na wutsul wutsul asama.
idanunsa kuwa suka juye bai san sa'adda ya saki
takobinsaba ta fadi kasa.
koda hatyan yaji ya fara jiyo kamshin mutuwa sai
tattaro karfinsa gaba daya ya gabzawa sarki
shamsal wawan naushi afuska
take sarki shamsal ya saki wuyan hatyan ya fado
Kasa amatukar galabaice yana tari gami da tofar
da jinin wuya.
shikuwa sarki shamsal saida ya yi baya taga taga
saboda karfin naushin a lokacin da yaga wasu
taurarun wuya akan idanunsa
Asannan ne yaji danshi akan hancinsa
koda sarki shamsal ya shafo hancinsa yaga jini
saiya fusata ainun irin fusatar dabai taba yiba
arayuwarsa
ya kwarara uban ihu wanda ya firgita duk wata
halittun dake kan wannan tsauni har da
wadandama suke cikin wannan teku
saboda wannan ne karon farko da wani jarumi ya
samu nasarar fitar da jini daga jikinsa duk da
cewar ya halacci yakoki da dama gami da gasar
jarumtaka ba adadi
ba tareda sarki shamsal a zare takobi ba saiya
ruga izuwa kan hatyan ya sake damkar wuyansa
ya shakeshi a tsaye ya rinka gabza masa naushi
a fuska tun hatyan na kokarin kare kansa harya
kasa
nandanan fuskar hatyan ta kumbura tayi suntum,
idanuwansa ma sukayi luhu luhu
hakika duk wanda ya fika karfi sai dai kayi masa
Allah ya isa
duk da jarumtakar hatyan gami da juriyarsa sai
gashi ya zama kamar tsumma ahannun sarki
shamsal domin ko daga hannunsa baya iyawa
koda sadirat taga halinda hatyan ya shiga saita
sunkuci wani dutse ta rugo da gudu izuwa kan
sarki shamsal ta maka masa dutsen akai
take dutsen ya fashe ba tare da yayi masa ko
kwarzane ba
kawai saiya maketa ta zube kasa sumammiya
sannan yaci gaba da gabzawa hatyan naushi
afuskarsa har saida ya sumar dashi sannan ya jefar
dashi akasa
hatyan ya baje akasa tamkar gawa domin babu
abinda yake motsi ajikinsa kamar gawa.
asannan ne sarki shamsal ya zare takobinsa yazo
ya durkusa agaban hatyan ya kamo hannunsa na
dama
ya daga shi sama sannan ya daga takobinsa da
nufin ya sare hannunsa kamar yadda yayiwa
dansa yarima zainur
kwatsam ba zato ba tsammani sai sarki shamsal
yaji an doki kirjinsa da mugun karfi
saboda karfin dukan saida sarki shamsal ya
wuntsula baya sau uku akan tsubirin
kafin ya watstsake ya juyo yaga wanda ya doki
kirjin nasa tuni an dauke hatyan da 'yar
uwarsa sadirat an jefasu cikin wannan jirgi nasu
sarki shamsal
abinda idanun sarki shamsal suka iya nuna masa
kawai shine an jefar da boka daizur gabansa
alokacin aka tuka jirgin akayi gaba dashi da gudu
nan take sarki shamsal yayi amfani da karfin
tsafinsa don ya dawo da jirgin amma sai tsafin
yaki tasiri
kafin shudewar 'yan dakiku masu yawa tuni jirgin
ya bace acikin tekun
koda ganin haka sai sarki shamsal ya sake kurma
uban ihu a karo na biyu ya kamu da tsananin
bakin ciki harsai da kwalla ta cika masa idanu
adaidai wannan lokacine boka daizur ya farfado
daga dogon suman da yayi
afirgice ya mike zaune ya dubi gabas da yamma
,kudu da arewa yaga babu jirginsu babu abokan
gaba.
ADAI DAI NAN NE LITTAFI NA
UKU YA KARE
AMMA IDAN ALLAH YA KAIMU GOBE ZAMU
DORA DA LITTAFI NA 4
.
Kar dai ku manta haryanzu kuna tare da Shuraih Usman
Inkiya 99%
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

Related Posts

There is no other posts in this category.

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "TARKON MUTUWA littafi na Uku 3 complet na Abdulaziz Sani M gini"

Post a comment