+2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria

Download and read free hausa novels

MAZAN KO MATAN part 5 karshe
MAZAN KO MATAN
Rubutun Shuraih Usman
@shuraih 99%
Part 5
KARSHE

Cikin matukar razana da daburcewa ta ce
"Bakina kaman yaya?"
Tayi maganar tana mai kare masu kallo sama da kasa
.
Mu biyarne tsaye a gabanta, yayinda ni da mujahid muke gaba gaba
,
Na lura da yadda safiyya ta tsorata sosai,
Bisa ganin mutanen ukun dake bayanmu
,
Kattine majiya karfi, kowannensu ya hakimce hannuwansa, sai muzurai suke tamkar saci babu,
Ransu a bace tamkar wayanda aka aiko masu da sakon mutuwa,
,
Kallo daya zakai masu ka gane ko su waye, sakamakon kayan dake jikinsu,
Na lura tunda muka iso angwan jama'a ke binmu da ido ,
Suna sanyene da dogon wandon uniform nasu da kuma riga mai gajeran hannu, a kafadun rigan akwai wasu kore koren layuka,
Sun saka hullana kafiya naci, wacce take dauke da tambarinsu na bindigu guda biyu, an rubutta VIGILANTEE gROuP OF NIGERIA a kasan tambarin
,
Nai murmushi sakamakon ganin yadda cikin kankanin lokaci har safiyya ta razana da ganinsu,
Na fara magana bayan dana sauke ajiyan zuciya
"Wato ainahin safiyya kinsan hausawa sukace ranar wanka ba a boyen cibi, "
Ta kankance kai cikin rashin gane inda maganata ta dosa
,
Koda mujahid yaga na kamo wata hanyar wacce ba haka mu ka tsara ba sai yai maza ya amshe maganar
"Malam ba zakai mata bayani ba ko, so kake yanzu nasa su GAJIMARE sui ta labtarka"
,
"Safiyya dama wayan dana baki jiya ba wayata bace, wayan abokina ne, na dai shirga maki karyane kawai, don ki kulani, Tun jiyan yake nemana na bashi wayansa, sai dazu muka hadu, shine dana fada masa wayan ta bace yanuna shi sam bai san wannan zance ba, shi isa ya hadani da vigilantee ni kuma ayanzu gaskiya bani da kudin da zan iya biyansa, shi yasa nace da su muzo wajenki tunda ke ce ki ka salwantar da wayar, "
Nayi shiru ina mai saddar da kaina kas
,
"Yo kai shuraih haka mukai dake "
Cikin mamaki na dago kaina mukai ido hudu da ita "nace haka mukai dakai" ta sake tambayata
,
Nai kasake nama rasa amsan da zan bata
Ta dubi mujahid tace mai "malam kaine mai wayar"
"Eh nine" ya bata amsa yana wani shan kunu
"Dun Allah kaji mani maganar nan, jiya fa yazo wajena da waya a hannunsa na karbe wayar ina danne danne, saboda da doki ya tafi ya manta da wayan a wajena,
Da sanyin safiya sai gashi ya zo wajena in bashi waya, na lallaba na bashi hakuri nace mai ya dawo an jima ya karba saboda akwai wakokin dana ke son turawa wayata,! Toh kaji yadda mukai amma yanzu kuma ya kwaso min ku, toh mai zam maku ni?"
.
Ta karashe maganar tana ware hannayenta
Tsaban mamaki ma sakin baki nayi gala lala ina kallonta sakamakon jin abunda ta fada, lallaima yarinyarnan ta cika yar rainin hankali na fadi haka a zuciyata
.
Mujahid ya jinjina kai yace "ince dai wayar din tana nan"
"Eh tana ma cahji yanzu" ta bashi amsa
Mujahdi ya dubeni sannan ya dubeta yace
"Dauko min wayar din toh"
Ta juya ta shige cikin gidan
,
Shigewanta gida keda wuya mujahid ya fashe da dariya ni kaina me zanyi inba dariyan ba,
Sai da mukayi mai isanmu sannan nce"kai mj amma ka kawo shawarafa, yanzu badon kaiba da shikenan, yarinyarnan ta cimin waya kenan"
,
"Hmm ai na fadamaka mata saide ka barsu kawai, don sun wuce tunaninka yanzu duba kaga yadda ta kare kanta, wai ita batace an sata ba"
"Barta kawai bari ta kawo wayan yau MAZAN KO MATAN"
Nai kwafa ,
Karar Kiciniyar bude kofa da mukaji shi ya ankarardamu tana zuwa hakan yasa muka tsuke bakinmu mukai shiru,
Mujahid ya bata ransa in ka gansa kamar ba shi bane mintukan da suka wuce ya runga dariya har da buga kafa ba
,
Ni kuwa dama fuskarnan tawa tafi kamaa da na tausayi,
Safiyya ta fito wayan na rike a hannunta, na dama
Ta mika ma wa mujahid wayan, ya karba yadan dudduba sannan ya miko mani,
Cikin zumudi na karba a nan take yanayina ya canza, na dudduba wayan gaba da baya sama da kasa gefe da gefe naga babu abunda aka cire a ciki, daga nan sai na kunna wayar na shiga camera, na ware murya nace ma mujahid selfie na daga wayar sama yan bangan bayana suka washe baki, mujahid kuma yai murmushi, nima dai murmushin nayi kafin na capta mana selfie din,,
.
Cikin mamaki baki bude safiyya take kallonmu yayinda muke antaya selfie,
Na dubeta bayan dana zura wayar din cikin aljihuna, fuskata na dauke da murmushi "malama safiyya, wai da wani suna ya kamata na kirakine ,MAI WAYO,YAR RAININ HANKALI ko kuma BARAUNIYA"
Ta dubeni cikin tantama "kaman yaya ban gane nufin kaba"
Na dubi mujahid nace "mj kaji wai bata gane ba dun Allah taimaka ka ganar da ita"
,
Mujahid yai murmushi yace "malama BARAUNIYA, toh ai wayansa ne, kawai dai plan muka hada maki, YAR RAININ HANKALI, wai ita MAI WAYO har da......"
Tun kafin mujahid ya karisa maganarsa ta juya da gudu ta shige gida, ta banko kofan gidan
.
Mun dan jima a tsaye a kofan gidan muna sharara dariya, kafin muyi tafiyanmu
Bayan mun sallami yan bangan da dari biyar
,
Tafiya nai na samu dangado na bashi wayansa a inda ya hauni da masifa ta inda yake sgiga bata nan yake fita ba,
,
......
Yammaci ne mai dauke da ni'ima , domin tarin ababen kayatuwar da suka lullube yammacin, garin ya danyi duhu alamun hadari a yayin da iska mara karfi mai matukar dadi ke yawo a cikin yammacin,
,
Mutane da dama sun dan tsorata da wannan hadarin har ta kai sun fara gudu domin isa masaukinsu,
Cikinsu har dani dana fito gangaren tudu wajen sahibata sadiya, inda muka sha hira sosai tamkar kar mu rabu da juna
,
Sa'I sa'I nakan kalli hannuna mai dauke da wani koren zobe nayi murmushi,
Bawai hannunan bane ke sanya ni murmushi a'a Zoben dake sakale a dan yatsana shike sanyani nishadi har murmushin yake fita batare dana sani ba, zoben da masoyiyata kuma abar kaunata sadiya ta sanya mani yau,
A hakan na runga murmushi har na iso Gida,
Ina Tunanin yadda na hadu da sadiya,
Da farkon haduwana da ita,
Koda na tuna sanadiyar haduwata da ita sai na tsinci kaina ina mai fashewa da dariya,
"Ba'asamu safiyya yar karya ba an samu, sadiya sanadiyar karya?" Na furta a fili
.
.
Alhamdulillah
Anan na kawo karshen wannan gajeran labarin na wa,
Dafatan ya nishadantar
,
MAZAN KO MATAN
Shuraih Usman
********************
,
Zaku jini a cikin tsohon littafina mai taken
A RANAR SALLAH
Nan bada jimawa ba
,
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%

MAZAN KO MATAN part 4

Duk da cewa na san ta Gane ni amma sai na matse nayi tamkar ba nine jiya muka hadu ba
Na matso kusa da ita fuskata na kallon kasa cikin boye murya nace
"Dan bani hanya yan mata"
Batare da musu ko gardama ba ta matsa mani na wuce,
Zuciyata sai bugawa take ina tunanin shin bata ganeni ba kuwa,
Wata zuciyar tace ai data ganeka da iyanzu baka kawo nan ba,
,
Daidai ina shirin ficewa daga gidanmu naji muryanta tana kiran suna na
Duk da banso na tsaya ba amma sai na tsinci kaina ina mai tsayawa
,
Cikin takunta na rangwada fuskarta a bace ta tako wajena,
"Yan mata naji kaman kin kirayi sunana"
"A,a ni ba sunanka na kiraba, this property is not for sale nace"ta bani amsa
Zuciyata ce tai dumm nan take naji kunya ta lullubeni,
Nai karfin hali cikin borin kunya nace
"Dun Allah sadiya ki hakuri da karyan dana shirshirga maku jiya, dun Allah kar ki fadawa wa umma na"
,
Tai murmushi wanda ya bayyana kyawawan hakoranta kafin tace
"Hmm shuraih kenan, shin an gaya maka ni karamar yarinyace, ko ce maka akai ni ban sanka ba, ai tun da dadewa na sanka kuma har wajen kanikancinku na sani, kai ne dai nake tunanin baka waye ni ba, sai gashi jiya kai fakare kanata shirgawa kawayena karya"
,
Na saki baki galala ina kallonta da mamaki
Nace "yo amma mei yasa tun jiyan baki tonan asiri ba"
Tai murmushi kafin tace
"SO, "
Na jaddada kalman a zuciyata SO kuma
Tamkar taji abun dana fada a zuciyata
"Eh shuraih , tun ba yau ba ziciyata ta kamu da tsananin sonka, hakan yasa na dunga bibiyan al'amarinka,a kowacce rana sai na tafi wajen aikinku domin kawai naga fuskarka, da sonka nake kwana da shi nake tashi, saide na rasa ta yadda zan sanar maka,
Cikin sa'a sai gashi jiya Allah ya wullo ka gareni, naji dadi sosai daka yaba ni, duk da cewa a jiyan tafarkin daka kama na karyace, sam ban ga laifinka ba, domin da bakai hakaba toh kawayena ma ba za su tsaya ba bare har takaisu ga sauraranka, ina Sonka Shuraih, ina sonka"
,
Sam ban gaskata abun da kunne na suka jiyemun ba don na fi daukan hakan ga rudana da kunne na suke mani
Wai tayama za'ace ni da nake m.......
"Ina sauraronka shuraih, shin kana sona kuwa"
Sadiya ta katse mani zancen zucina da fadin haka
,
********************
Ta fiya nake kaina a kasa ina tunanin abubuwan da suka faru dani cikin dan kankanin lokaci haka
,
Shakka babu wannan rana ta zo mani da sa'a
Duba da yadda lokuta kankani da suka wuce
Kyakkyawa kuma dirarriyar budurwa ta furta cewa ni take so,
,
Yanzu kam ko tunanin safiyya bana yi
Har ga Allah naji darsuwan Son sadiya a zuciyata
Duk da cewa bata kai safiyya komai ba, amma itama Allah ya azurtata da kyakkyawan sura dadai gwargado
,
"99%! 99% !! 99!!!"
Tamkar daga sama naji ana kwala min kira
Na gane muryan mai kiran
Ya karaso ya bani hannu muka tafa
Mujahid ne yana sanye cikin farar riga mara hannu, a gabanta an rubuta FILA da manyan baki, sai bakar jeans mai aljuhu biyu a kaurinta (two pocket)
Yaci zanzaro sai kace wani tsohon hedimaster,
" mj ya akai ne"
"Dai dai wallhi kasan meye?"
Ya tambayeni
"A'a"
"To Dangado fa yana ta nemanka don yanzu na hadu da shi, malam ranshi ya baci,ya tambayeni kai nace mai ban ganka ba,"
Nayi murmushi kafin nace
"Dan Allah kyaleshi"
"Wai me ya hadaku da shine" mujahid ya tambayeni
Ban boyemai komai ba na fede mai biri har wutsiya dan gane da abun daya faru da wayan dangado,
Mujahid ya fashe da dariya bayan daya gama sauraran labarin,
,
Dariyarsa bata bani haushi ba don mun ruga da mun saba haka da shi
"Kai amma 99% yarinyar nan ta raina maka hankali wallahi"
Na dubeshi cikin rashin fahimtar yanda zancen nashi ya nufa
"To wani rainin hankali ne taimun "
Na tambayeshi
"Ta boye waya tace maka an sata kai kuma ka yarda, wallahi ni banga ranan da zaka wayeba 99%, ga ka dai kaman wayayye"
Kirjina yaba dumm sakamakon jin abunda mujahid ya fada
Na dubeshi nace "to kai ya akai kasan cewa ta boyene"
Ya sake fashewa da dariya akaro na biyu
Wannan karon kam ya bani haushi, naja tsaki nace "kaga malam tambayrka nake fa "
"Yo kai 99% sai kace kwakwalwanka bayaja, haba, tayaya za'a ce barayi sun shiga gidan Alhaji Kawu sunyi sata anma mutanen angwa basu ji labari ba har yanzu, ai kaima kasan inda da gaskene har Gidan rediyon N B S sai sun san da labarinnan "
Na jinjina maganarsa kafin nace "tabbas maganarka abar dubawa ce, amma yanzu yaya zamuyi mu amshe wayar din a wajenta"
Yayi murmushi yace
"Ai maganin biri karen maguzawa,allah na tuba mu yanzu har wata tayi mana wasa da hankali, ka ganni nan Na mijine ni, nasan mata sosai duk wani takunsu a kaina yake, dun haka zo kaji"
Na matso kusa da shi ya kitsamin
********************
Kofan tangamemen gidan ne ya bude
A yayinda kyakkyawar budurwan ta fito daga ciki ba wata bace face safiyya tana sanye da rigan kanti da wando ta yafa wani dan bingilallen gale iya kirjinta,
Turus tayi tana kallonmu cikin razana
Yayinda bakinta yafara rawa "shuri-shur-shuraihu me a faru"
Nai murmushin mugunta kafin nace
Bakinki ne safiyya
.
Mu hadu a part na gaba
,
Toh wasu baki kenan

MAZAN KO MATAN part 4

Duk da cewa na san ta Gane ni amma sai na matse nayi tamkar ba nine jiya muka hadu ba
Na matso kusa da ita fuskata na kallon kasa cikin boye murya nace
"Dan bani hanya yan mata"
Batare da musu ko gardama ba ta matsa mani na wuce,
Zuciyata sai bugawa take ina tunanin shin bata ganeni ba kuwa,
Wata zuciyar tace ai data ganeka da iyanzu baka kawo nan ba,
,
Daidai ina shirin ficewa daga gidanmu naji muryanta tana kiran suna na
Duk da banso na tsaya ba amma sai na tsinci kaina ina mai tsayawa
,
Cikin takunta na rangwada fuskarta a bace ta tako wajena,
"Yan mata naji kaman kin kirayi sunana"
"A,a ni ba sunanka na kiraba, this property is not for sale nace"ta bani amsa
Zuciyata ce tai dumm nan take naji kunya ta lullubeni,
Nai karfin hali cikin borin kunya nace
"Dun Allah sadiya ki hakuri da karyan dana shirshirga maku jiya, dun Allah kar ki fadawa wa umma na"
,
Tai murmushi wanda ya bayyana kyawawan hakoranta kafin tace
"Hmm shuraih kenan, shin an gaya maka ni karamar yarinyace, ko ce maka akai ni ban sanka ba, ai tun da dadewa na sanka kuma har wajen kanikancinku na sani, kai ne dai nake tunanin baka waye ni ba, sai gashi jiya kai fakare kanata shirgawa kawayena karya"
,
Na saki baki galala ina kallonta da mamaki
Nace "yo amma mei yasa tun jiyan baki tonan asiri ba"
Tai murmushi kafin tace
"SO, "
Na jaddada kalman a zuciyata SO kuma
Tamkar taji abun dana fada a zuciyata
"Eh shuraih , tun ba yau ba ziciyata ta kamu da tsananin sonka, hakan yasa na dunga bibiyan al'amarinka,a kowacce rana sai na tafi wajen aikinku domin kawai naga fuskarka, da sonka nake kwana da shi nake tashi, saide na rasa ta yadda zan sanar maka,
Cikin sa'a sai gashi jiya Allah ya wullo ka gareni, naji dadi sosai daka yaba ni, duk da cewa a jiyan tafarkin daka kama na karyace, sam ban ga laifinka ba, domin da bakai hakaba toh kawayena ma ba za su tsaya ba bare har takaisu ga sauraranka, ina Sonka Shuraih, ina sonka"
,
Sam ban gaskata abun da kunne na suka jiyemun ba don na fi daukan hakan ga rudana da kunne na suke mani
Wai tayama za'ace ni da nake m.......
"Ina sauraronka shuraih, shin kana sona kuwa"
Sadiya ta katse mani zancen zucina da fadin haka
,
********************
Ta fiya nake kaina a kasa ina tunanin abubuwan da suka faru dani cikin dan kankanin lokaci haka
,
Shakka babu wannan rana ta zo mani da sa'a
Duba da yadda lokuta kankani da suka wuce
Kyakkyawa kuma dirarriyar budurwa ta furta cewa ni take so,
,
Yanzu kam ko tunanin safiyya bana yi
Har ga Allah naji darsuwan Son sadiya a zuciyata
Duk da cewa bata kai safiyya komai ba, amma itama Allah ya azurtata da kyakkyawan sura dadai gwargado
,
"99%! 99% !! 99!!!"
Tamkar daga sama naji ana kwala min kira
Na gane muryan mai kiran
Ya karaso ya bani hannu muka tafa
Mujahid ne yana sanye cikin farar riga mara hannu, a gabanta an rubuta FILA da manyan baki, sai bakar jeans mai aljuhu biyu a kaurinta (two pocket)
Yaci zanzaro sai kace wani tsohon hedimaster,
" mj ya akai ne"
"Dai dai wallhi kasan meye?"
Ya tambayeni
"A'a"
"To Dangado fa yana ta nemanka don yanzu na hadu da shi, malam ranshi ya baci,ya tambayeni kai nace mai ban ganka ba,"
Nayi murmushi kafin nace
"Dan Allah kyaleshi"
"Wai me ya hadaku da shine" mujahid ya tambayeni
Ban boyemai komai ba na fede mai biri har wutsiya dan gane da abun daya faru da wayan dangado,
Mujahid ya fashe da dariya bayan daya gama sauraran labarin,
,
Dariyarsa bata bani haushi ba don mun ruga da mun saba haka da shi
"Kai amma 99% yarinyar nan ta raina maka hankali wallahi"
Na dubeshi cikin rashin fahimtar yanda zancen nashi ya nufa
"To wani rainin hankali ne taimun "
Na tambayeshi
"Ta boye waya tace maka an sata kai kuma ka yarda, wallahi ni banga ranan da zaka wayeba 99%, ga ka dai kaman wayayye"
Kirjina yaba dumm sakamakon jin abunda mujahid ya fada
Na dubeshi nace "to kai ya akai kasan cewa ta boyene"
Ya sake fashewa da dariya akaro na biyu
Wannan karon kam ya bani haushi, naja tsaki nace "kaga malam tambayrka nake fa "
"Yo kai 99% sai kace kwakwalwanka bayaja, haba, tayaya za'a ce barayi sun shiga gidan Alhaji Kawu sunyi sata anma mutanen angwa basu ji labari ba har yanzu, ai kaima kasan inda da gaskene har Gidan rediyon N B S sai sun san da labarinnan "
Na jinjina maganarsa kafin nace "tabbas maganarka abar dubawa ce, amma yanzu yaya zamuyi mu amshe wayar din a wajenta"
Yayi murmushi yace
"Ai maganin biri karen maguzawa,allah na tuba mu yanzu har wata tayi mana wasa da hankali, ka ganni nan Na mijine ni, nasan mata sosai duk wani takunsu a kaina yake, dun haka zo kaji"
Na matso kusa da shi ya kitsamin
********************
Kofan tangamemen gidan ne ya bude
A yayinda kyakkyawar budurwan ta fito daga ciki ba wata bace face safiyya tana sanye da rigan kanti da wando ta yafa wani dan bingilallen gale iya kirjinta,
Turus tayi tana kallonmu cikin razana
Yayinda bakinta yafara rawa "shuri-shur-shuraihu me a faru"
Nai murmushin mugunta kafin nace
Bakinki ne safiyya
.
Mu hadu a part na gaba
,
Toh wasu baki kenan

MAZAN KO MATAN part 3

Duk da na dan razana sosai da jin muryansa amma hakan baisa na mike naje na bude kofan ba
Illa ma kasake danayi ina kallon kofan
,
Shakka babu nasan muddin na bude kofan toh fa sai dangado ya tayar mani da hankali,
Don in ta kai ta kawo ma cewa zaiyi mu tafi gidan su safiyya,
,
Kofan dakin ne ya cigaba da kara yayin da dangado yake dukansa iya karfinsa,
,
Nai ja tsaki sannan na rarumo bargona wanda a nai filo da ita na lulluba a jikina, nai kwanciyata
**********
,
Sauri nake ta zabgawa , burina shine na isa gidan su safiyya duk da nasan cewa zan fuskanci matsala a wajenta wajen karban wayan amma na ruga dana hattama irin karyan da zan lauya mata ,
,
Yo dama gani da dogon kafa uwa wani rakumi,
Cikin kankanin lokaci na isa kofan
Cikin sa'a na hango yaron dana aika jiya yana wasa a gefen gidan, na yafuto shi da hannu,
Da gudunsa ya iso gabana
.
Na jingina da bangon gidan bayan na aika yaron ya kirawo min safiyya na duba agogon hannuna
Karfe bakwai da minti goma sha uku na safiya
Nai mamaki ainun, da yadda lokaci baya ja da gudu
.
Yaron dana aika ya futo yace dani "wai tana zuwa"
Hankalinsa gaba daya yana wajen wasan daya ke yi,
Na sallameshi da cewa "toh"
,
Ban wani dade ba safiyya ta bude kofa ta fito
Kayan da suke jikinta jiya sune haryanzu amma a wannan lokacin hulan sanyine akanta sabanin Fatala(kallabi)
,
Tayi zunzurutun kyawu amma ni bata kyawun nake ba yanzu duk matsala ta ta bani wayan dangado ne,
Bayan mun gaisa nace da ita
"Safiyya dan bani wayannan danA baki jiya da dare"
YaDda nayi maganar ma kadai zai tabbatarmata da cewa cikin Ujila nake
,
Tai kasake tana kallona kafin daga bisani tai murmushi, don ta jawo hankalina gareta, a zuciyata nace aikin banza, ayanzu kam murmushin kinnan bazai tasiri ba"
Afili kuwa cewa nai "yi sauri dun Allah wallahi sauri nake ,"
.
Sai waige waige take tako ina a haraban angwan
Nasan ba komai take nema ba Illa mota, a zuciyata nace KARSHEN MAKARYACI tazo,
,
"Yo amma ina motarka"
Safiyya ta tambayeni tana kara kallon wajejen
Nai murmushi "tana gida, me yafaru"
"Babu komai kawai de ina tambaya ne,"
Tai shiru bata sake cewa kala ba
"Akwai wasu muhimman documents a cikin wayannan kuma yanzu nake so nai amfani da su, dan Allah yi sauri ki dauko mani,"
,
Na lura da yadda yanayinta ya canza ya koma salon tausayi, ta kankantar da murya can kasa tace "dama jiranka nake kazo na sanar da kai abun daya faru"
,
"Me yafaru " na fada cikin zazzaro idanuwa don na dauka screen din wayar ta fashe ne
"Wallahi jiya da daddare barayi suka shigo gidanmu, sun yi mana sata mai yawa kuma sun amshe wayarka"
**************
Wasu taurari idanuwana suke hango mani, taurarin sun kasu kashi biyu kashi na farko jajayene kashi na biyu kuwa bakakene
Jajayen taurarin nan suka hadu da babaken to amma maimakon su bada haske kala daya, sai suka bada wani bakin haske mai dauke da dugo dugon jajaja,
,
"Shuraih ga kokonka, kosen yana cikin dakinka"
Na mike tsaye ina kallon mai maganar kanwata ce, banyi kasa a guiwa ba na dau kokon na nufi cikin dakina,
Abun dana fara cin karo da shi shine kosen da aka ajjiye mani,
Na zauna na dau kosen na cilla cikin bakina, maimakon naji dandano mai dadi, sai naji akasin haka, wannan yasa na mike tsaye na fito bakin kofan dakina na tofar da ragowan kosen dake bakina
,
Tun da safiyya ta fada mani wai wayan an sace naji gabadayan lakan jikina ya mutu, babu yadda na iya haka na barta tai shigewarta gida
,
Da kyar na dawo gida don kuwa juwa ke dibata a hanya sai tangadi nake tamkar dan giya sabon shiga,
*
Na dau kosen da kokon na fice daga dakin ba inda na nufa sai wajen ummata don kuwa ita ke toya kosen , tun daga nesaa na runga jiyo hayaniyar mutane sama sama ,
"Baba sai nine"
"Na riga shi zuwa"
"Na naira hamsin zaki samun baba"
,
Irin wayannan hayaniya suke tashi a rumfan umma mai kose sunan da jama'a ke kiranta da shi kenan sabanin ni da Umma kawai nake kiranta
,
Dukda tarin mutanen dana tarar a wajen tuyan kosen sun zagayeta hakan bai hanani cusa kai ba na rrunga tutture su dolensu suka bani hanya na iso gindin wutan na durkusa nace
"Umma bazan iya cin wannan kosen ba , wallahi daci yake min"
"Toh yau kuma salon iskancin da ka fito da shi kenan ko kaka?" ta bani amsa lokacin datake kokarin saka dusan kosen cikin mangyada
Nai shiru kafin daga bisani nace
"Allah kuwa umma daci yake"
"Toh me kake son nai maka"
"Naira hamsin zaki bani naje nasha farin shayi"
"Toh amshi" ta mikomin hamsin din
Na amsa ina mai cewa "na gode umma"
Na mike tsaye da nufin na fuce daga rumfan
Idanuwana ne sukai arba da ita, nan take kirjina ya buga da karfi, nai tunanin ko idanuwana ne keyimin gizo hakan yasa na mummutsikesu da hannayena, amma har yanzu ita nake gani a tasaye a gabana hannunta rike da gudan naira dari , ranta a bace,
Ba kowa bace illa Sadiya budurwan dana runga shirgawa karya jiya ahanyata na dawowa Gida
.
Toh ya zata kaya
Ku biyo alkalamin Shuraih 99%

MAZAN KO MATAN part 2

Tamkar na fashe da kuka haka nake ji
Sabuwar wayace kwananta Uku da siya,
Sabuwa ce gal a leda ya siyota Dubu 50,
Kirar infinix
.
Shi kansa shiga cikin motan ma gagarata yai na jingina a bakin kofan ina yiwa kaina jimami dun kuwa ko shakka banayi nasan sai na biyasa wayansa
.
Karancinn mutunci ne da Dangado,
Baya daukan asara a kayansa ,
,
Na dulmiya cikin kogin Tunanin inda akai har wayan ta bace,
Tunani kala kala suka runga ziyartar kwalkwalwata a yayin dana ke daukan wasu wasu kuwa nai fatali da su,
,
Wani farin Tunanine ya kwankwasa wa kwakwalwata kofa duk da dai cewa na gaji da tunanukan, hakan baisa nai fatali da shi ba, sakamakon ganinsa da nayi fari fat, sabanin tunanukan baya bakake wuluk
.
Nai sauri na bude Tunanin nan, sai ga Hoton yadda akayi har wayan tabar hannuna
Wani dan guntun murmushine ya subuce daga lebbana, wayanda suka bushe karangus
.
Nan take naji wata irin kwanciyan hankali ta ziyarceni, dukkan fargabana suka kau, raina yai fari tas,
Na juya da nufin na shige mota naje na amso wayan a inda na barsa
,
Akame na tsaya kikam numfashina ya kusan daukewa, sakamakon abunda idanuwana ya hango mani
,
Wasu tsala tsalan yan matane su Uku suke jerowa akan titi, dukkansu jajayene tamkar wasu larabawa ,
Hankalina yafi karkatuwa ga ta tsakiyarsu, wacce ta kasance gaba dayansu ta dara su a kyawu,
.
Ta mallaki madaidaicin fuska, mai dauke da kana kanan idanuwa,a yayinda tai wa girarta ado da eyeshadow,
Tana sanye da koren doguwar riga har kasa mai dauke da rotsi rotsin ja,
Ta rike jaka irin nasu na mata ,
In ka ganta a cikin wayannan yan mata tamkar wata ran daren goma sha biyu,
.
Tun dana ke a rayuwata ban taba ganin mace da irin wannan kyawu a zahiri ba sai de a talabijin,
Suna tafiya suna hira,
Zuciyata ta fara fisgata tamkar mayen kurace a jikina, babu yadda banyi ba don na hana zuciyata muradin kyakkyawan halittan nan amma abu ya faskara
Hakan yasa na nufi wayannan yan mata fuskana cike da murmushi,
.
Irin kallon da suke mani shi ya tabbartar mani da cewa ko kallo ban ishe su ba, yo amma da shike nima gwarzon namijine sai na dake a zuciyata nace yau dai ko MAZAN KO MATAN
,
Na rangada masu sallama da muryata wacce nai kokarin sirantata tamkar zanja ayan kur'ani,
Suka amsa cikin hadin baki,
Kowaccensu ta daure fuska tamkar an aiko masu da sakonnin mutuwa,
Murmushi kawai nayi don nasan na jan aji ne
,
"Sannun ku yan mata, tun daga nisa na hango ku, sam bai kamata ace kaman ku kuna taka sayyada ba, hakan ce tasa nai tattaki na iso , ga mota ta a can kuzo muje na rage maku hanya"
,
"Hmm mungode wallahi don ma mun kusan isa inda zamu"
Ta bangaren dama ta bani amsa
Nai murmushi mai nuna halin ko in kula don na riga dana san halin yan matan yanzu nace "Ok wai dama gani nayi ya kamata , amma tunda kun nuna bakwa bukata no problem, da shike nima baqone a nan garin yau nazo daga Abuja, sakamakon wata shara'a da muke da wani wai shi Alhaji Sale "
,
Na lura da yadda dukkansu yanayinsu ya canja duba da irin yadda suka karemani kallo, a zuciyata nace ku gama kare mani kallo da kyau ,
Har na juya na da nufin zan tafi sai kuma na sake juyowa na dubesu nace Don Allah na tambayeku mana
,
"Muna jinka" wacce tai magana dazun ta bani amsa
"Ina ne gidan Abdullahi Adamu, senator naku"
"G R A" ta sake bani amsa
Cikin tantama nace "ina ne kuma G R A"
Ta fara yimani kwatance sai ta iddar sannan nace mata
"Wallahi sam bana gane kwatance don Allah ku taimaka ku kaini kunga daga nan sai na sauke ku a gida,"
Sai da na lallabesu sosai sa'annan suka yarda har suka shiga cikin motar Arona na jasu,
Na lura da tauraruwata tun da na hadu dasu bata furta ko kalma daya ba,
Ina tuki na na saita madubin gaban direba saitinta yayin dana ke kallon kyakkyawan fuskarta sai sheki yake tamkar zinariya,
,
Na juyo na dubeta murmushi akan fuskana
"Tauraruwa ke bakya magana bane"
"Tauraruwa" ta nanata sunan
Salon yadda ta kira sunan ma abun burgewane, zakin muryanta ne yaso ya sanyani sakin sitiyari
,
"Sunan bai yi bane" na tambaya
Shiru tayi
"Kin dace da sunan ne shi isa , domin kuwa kinfi kama da larabawa , "
Dukkansu yan matan suka kyalkyale da dariya
Sai da sukai mai isarsu sannan dayan tace
"Kai amma da abun dariya kake"
"Wallahi gaskiya na fada, dun kinsan ni a saudi nayi karatuna, yo ko yammatan larabawan baza su nuna maki kyawu ba tauraruwa,
Yanzu haka da kuka ganni a garin nan wallahi wani dan damfara ya keson ya cuci mahaifina yanzu haka ma mun shiga kotu da shi,
Sunansa wai SALE , shi isa dukkan wani kadarorinmu muka bi muka rubuta cewa is not for sale don mu gargadi jama'a, kinga ma wancan ginin, "na nuna masu wani tangamemen gini wanda ake kan aikinsa, ajikin ginin an rubuta da manyan baki THIS PROPERTY IS NOT FOR SALE,
,
Na cigaba "ai duk wani gida,mota,babur,fili da dai sauransu da kukaga an saka THIS PROPERTY IS NOT FOR SALE toh na mahaifina ne, muna sanya wannan rubutunne don mu gargadi mutane "
,
Haka dai na runga jansu da hira ina sharara masu karya babu kunya bare tsoron Allah
har muka isa G R A suka nuna mani gidan dana bukata.
Daga nan na juya akalar tafiyar zuwa angwan da suka ce da ni a nan suke,
Cikin kankanin lokaci muka iso gangaren tudu da taimakon daya daga cikinsu inda take tai mani kwatance, bata san cewa na fita ma sanin angwan ba,
.
****
Suka fito daga cikin motan yayin da suke yimin godiya,
Fitowa nayi na dubesu nace babu komai ai
"Gashi kuma zaku tafi baku fadamin sunayenku ba, ko namban waya baku bani ba "
,
Wacce tafi kowannensu surutu tace "ni dai sunana Rashida, wannan kuma ta nuna tauraruwata da yatsa sadiya waccan kuma balki
,
Na nanata sunan a raina sadiya gashi dai ta hadu amma sunan na tsofaffi ne a fili kuwa murmushi nayi sannan nace "suna mai dadi, ni sunana Shuraih 99% inkiya mai dala"
,
******
Ina kwance kan kakkarfan katifan dakina wanda sau tari yasha sanya mani ciwon baya ,
Na tuna lokacin dana bar kofan gidansu sadiya yayinda rashida ta bani nambarta
Tunani nake yanzu gobe a ina zan samu aron kaya da mota dun kuwa nace masu gobe zan kawo masu ziyara,
Ina cikin wannan sake saken ne barci yai awon gaba da ni
,
Kaman a mafarki sai ji nai ana bubbuga kofan dakina,
Na bude idanuwana masu dauke da mayataccen barci a hankali,
A sannan ne kunnuwana suka sake tsinkayo karar bugun kofan tamkar za'a balla kofan haka ake bugunta
,
Cikin zafin rai na mike zaune na dubi kofan dakin
Har na bude baki zan yi maganna, sai na tsinkayi muryan DANGADO yana cewa
"Kai shuraihu! shuraihu!! Shuraihu!!! Ka bude kofan nan ka bani wayata,"
.
.
Ai dangado kai sai de kayi hakuri
Amma wayarka tabi........

MAZAN KO MATAN part 1

MAZAN KO MATAN
Na Shuraih Usman
Gajeran labari
Part 1
Tangamemen Gida ne iRin na zamani
Wanda ya kawatu ainun, domin kuwa a gaba dayan fadin unguwar gidanne gida na farko da a ka sana'anta da Bene
Gidan wani dan majalisa ne mai ci
.
Ina tsaye a bakin gate din gidan hannuna na dama rike da makulli ,yayin da hannun haguna yake boye cikin Aljihu,
Lokaci lokaci nakan yi wasa da makullin hannuna ta hanyar jujjuyasa
.
Wani yaro na gani ya fito daga cikin gidan zai karisa bakin titi, da guduna na tsaida shi ta hanyar kwala mai kira , yaron ya tsaya yana dubana tamkar wanda yaga wani Aljani ,
"Dun Allah yayarka Safiya tana gida kuwa"
Na tabayi yaron
"Eh tana gida" yabani amsa
"Dun Allah kai mani wata Alfarma man"
"Ina jin ka"
"So nake ka kiramin ita"
"Hmm " kawai ya fada sannan ya juya ya nufi cikin gidan
.
Duk da dai nasan abunda zai biyo baya hakan bai sa naji ko darr a zuciyata ba,
Bayan dan gajeran lokaci sai ga yaron ya fito
Haryanzu irin kallon dayai mani waccan karon itane dauke a idanunsa ,
Bayau na saba zuwa zance wajen safiyya ba don kuwa nakai wajen wata biyu, ina zuwa wajenta dai dai da rana daya ban taba fashi ba
.
Duk abun da nake yi komenene, koya wannan abu yakai ga muhimmanci muddin karfe takwas din Dare yayi, toh take zan saki abunnan na nufi hanyar gidan su safiyya
,
Wani tarin abun takaici kuwa shine Tunda nake zuwa wajen safiyya dai dai da rana daya bata taba yimin kallon mutunci ba,
Ko tafito ma sai de ta gaggasa mani magana tai tafiyarta, wani sa'in ma a gabana samarita masu hannu da shuni suke zuwa sui awon gaba da ita, cikin dankareren motoncinsu
,
Bazan taba mantawa ba akwai wata rana da na zo , naci sa'a ta fito, ranan ina sanye da kayan aikinane na bakanike. Ko tsayawa canzaasu ban ba, kuru kuru safiyya ta fadamani wai wari nake
Muna tsaye da ita a wajen sai faman bata baki nake ina furta mata lufuzan soyayya masu sanya zuciya tai taushi,
Wata dankareriyar motace kirar range rover ta faka wani mutum sanye da manyan kaya ya fito daga cikin motan.
Koda safiyya ta kyallara ido taga waNnan mutumin sai ta nufeshi tana mai murmushi
,
Ni kuwa nai tsayuwata a kofan gidan cikin zaman jira lokacin data zo shigan gida
.
Sam bana damuwa da irin tarin wulakancin da safiyya take nuna mani, duk da bata fito fili tace bata sona ba,
Nasan abu daya ne ya shiga tsakanina da ita
Kuma shine ya darsa rashin kaunata a zuciyar safiyya
Wannan abu kuwa shine NAIRA
,
Bakaniken mota ne ni,cikin kanikawan ma yaron aiki nake,
Aduk lokacin dana dan samu kudi sai na tafi kasuwa na sayomata yan man shafawa, da sabulai na iya karfina na kawo mata, amma ko godiya bata taba min ba sai de ta amshe tai su ta kara gaba wajen masu zuwa da dankara dan karan motoci
.
Wannan abu ya dade yana cimin tuwo a kwarya
Su kansu Abokaina ma tsiya suke min sai kaji suna kirana da dan wahala ,
,
Wannan yasa na yanke shawarar canja salon takuna tunda na fito a gaskiyana abu yaki aiki toh bazan jarraba dayan ko zaiyi aiki
.
Wannan nema yasa naje na samu wani dan unguwanmu ana kiransa Abba Yelo, na naimi daya taimakamin da Aron Motarsa na Dare daya kacal,
Daga nan na garzaya wajen Abokina MJ na nemi ARon kayan kanti sababbi a wajensa
,
Nai wanka na feshe jikina da turaren Daki na ci kwalliya sa'annan na dau makullin motar dana ara nai ficewata daga gida,
Koda na fito kofan gida mutane da dama basu gane ni ba, don kuwa sun saba gani na cikin tsummokaran Over size dina
To yau gani sai kace wani hamshakin mai dala ne
.
Na shiga cikin motan nai hanyar Gangaren Aboki
Fakawa nayi a kofan gidan su DANGADO na nemi daya bani aron wayarsa infinix finger print, da kyar da sidin goshi ya bani, yayin daya cikani da gargadi
*****
"Wai tana zuwa" yaron ya fada
Cikin isa na zura hannu cikin Aljihuna na dauko naira hamsin na ba ma yaron, sosai yayi godiya sannan ya kara wuta
,
Bayan dan wani lokaci sai kofan gidan ya bude safiyya ce ta fito tana sanye da riga da siket wayanda sukai matukar yi mata kyau, hasken fuskarta wanda akullum karuwa yake,
Tun daga nesa naga tana mini kallon daga ina
Wannan yatabbatar mani da cewa bata gane ni ba
"Assalam" tai sallama
Na amsa sallamar cikin kausasa murya yanda na amsa sallaman zai tuna maka da marigayi IBRO Allah ya jikansa
,
"Malam waye kai sannan daga ina kake" ta jero min wayannan tambayoyi bayan data jingina a jikin motan Aro na
Nai murmushi sannan na Cire bakin tabarau din daya ke kan fuskata
Cikin dan razana ta washe baki "shuraih!"
Na gyada mata kai
Munyi hira sosai yayin da yawancin hiranma safiyya ne ke zancenta , don ni hankalina yana cikin wayar hannuna wanda tun da muka fara hira na fiDdo,
Ni kaina nayi mamakin yadda safiyya ta zage muna hira yau tamkar ba itace safiyyan da ke cemin ina Wari ba,
Na tattakure na shiga shirga mata karya ba kakkautawa
Don kuwa ce mata nai ai Dangote kanin babana ne Uwa daya Uba daya
Sun rabu ne tun suna yara kananu
Koda ta nemi sanin abunda ya rabasu sai na sake shirga mata wani karyan inda nace mata
Ai tun lokacinnan babana suna zaune a kano wata rana sun fita yawo shi da dangote shine barayin mutane suka sata shi, tun daga ranan basu sake haduwa sai jiya, da dangote yazo wucewa ta nan garin sai Allah ya hadasu
,
Ta sake tambayana yadda akayi suka shaida Juna
Nai murmushi nace mata ai naka nakane babu ta yadda zaka mance da dan uwanka, hatsari dangote yayi a hanyan KARAN SHANU shi kuwa mahaifina yai kokari ya taimakeshi ya futo da shi daga cikin motan to ta haka ne har dangote yaga wata sarka a wuyan mahaifina , wannan sarka itace shedan gidanmu don nima ina da ita,"
Safiyya ta kalleni cikin mamakin zancena
,
Na basar da kallon datai mani
Ta budi baki da niyyar sake jefomin wani tambayan nai sauri na katseta da fadin
"Yanzu haka ma dangoten yana nan a gidanmu, shin kina bukatar ganin sa ne?"
Nai kasake ina shirin jin amsar daza ta bani, ni kaina na san nayi gangancin fadin wannan zance,
,
"Ai kuwa zanso na gansa ,kash sai de yanzu babana yana gida amma gobe kam dolenka ka kaini kodan ma muyi hoto"
Tafadi cikin zumudi
murmushi nayi mai nuna cewar na tsira daga wannan takin,
,
Munyi hira sosai daga nan na sallemeta inda na zaro last cash dina Dubu daya na bata, ita kanta dubu dayan sai da nayi kwanaki bakwai ina tarata , na bude motan aro na na kara gaba,
Zuciyata fal da farin ciki domin kuwa ji nake tamkar nafi kowa a duniya
,
Ina kan hanyata ta komawa gida sai na Tuna da abun da ya kusan sanyani hatsari,
Hankalina ya tashi, idanuwana suka zazzaro
Gabana yakama faduwa
"Wayan DANGADO"
A fili na fada yayin danake lalube aljihuna
Nai saurin faka motan a gefen titi
Babu inda ban bin cika a cikin motar ba amma ban ga wayan ba
Na tuna irin tarin gargadi da kashedin da runga kwarara mani kafin ya bani wayan
.
Fans dafatan kuna biye da Alkalamin 99%

MAZAN KO MATAN gabatarwa

MAZAN KO MATAN
Na Shuraih Usman
Gajeran labari
.
soyayya takan ginu akan turba dabam dabam,
Masoya da dama suna gina soyayyarsu akan tafarkin gaskiya ce, yayinda kadan daga cikinsu masu zalama da son abun duniya ke gina ta su bisa tafarkin Karya,yaudara, aci moriyar ganga ayar da fata,
,
Na zabi dana gina tawa soyayyar cikin rukuni na daya wacce nasan duk jimawa sai ta rushe,
,
Ku biyo alkalamin Shuraih 99%
A wanga gajeran labari

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 11

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 11
.
.
TUNA BAYA
.
A yammacin ranar wata laraba ne a hanya ta ta dawowa gida daga kasuwa na hadu da shi sai aikin turi yake yayi dukun dukun da shi kuma ya hada gumi
.
Na gaggauta yin fakin a gabansa kadan sannan na bude motar na fito sanye nake da koran boyel kai na da koriyar hula na tari gabansa, "baba barka da yamma"
Hannu yasa ya katso wani bakin gumi daga goshinsa "yawwa barkan ka dai"
Na karkace "ka gane ni kuwa?"
"Bangane ka ba"
"To nine a salin mai babur din nan wanda ka siye dhi dubu uku a wajena"
Ya zuba min ido kuri" anya kuwa kaine? Kai ba kai bane"
Na rike kugu "nine mana baba ba a wajen dan baballe mai gyara ba"
Ya gyada kai "shakka babu acan na siya , amma ni wanda na siya a wajensa siriri ne baki, amma kai ko gaka da yar kibarka kuma jajur da kai"
.
Na bushe da dariya "baba ai rayuwa ce ta canza baka ganni a mota ba, wallahi nine da gaske"
"Na yarda yaro amma wallahi sam ban gane kaba"
Na dubi babur din daya kara rugurgujewa sannan dattijon
"Baba yaya babur kuwa"
Yakara share gumi "babur ko dai wahala, ka ganshi nan ni na rasa mai hawan wani ni da shi"
"Kamar yaya kenan?"
"Eh mana idan yakai ni mil uku ni sai na kaishi hudu, yanzu batunnan daga dakata nake turin nan baka ganni futu-futu ba?"
Dariya ta kamani har sai dana sunkuya
Yaci gaba "wani abin haushi idan ina son fita karfe bakwai na safe sai dai na fara bugu tun shida domin nayi dari bai tashi ba, babu arziki na rrinka saka yayana idan wannan yayi yau wancan yayi gobe, suma sai suka fara zullewa rannan da na rufe su da fada sai suka nuna min kafafunsu na ga kowacce a kumbure"
.
Don dariya sai danayi kwalla(ai nima kaina 99% sai da dariya tarike ni)
Na sassauta murya "to baba siyar min da shi mana?"
Wani kallo yayi mai kaifi "kai yaro ban dan tsoho"
Na girgiza kai "ba tsokana bace ba, da gaske siya zanyi kayi masa kudi na ji"
Ya daga kai sama cikin tunani daga bisani ya sauke shi "to kawo dubu guda taya naji"
Wata sabuwar dariyar ta kwace min da kyar na samu na tsayar da ita
.
Na nufi mota a hankali aljihun (glove compartment) na bude na lalo kudi Naira dubu talatin nabashi , domin shima dai yaci arziki
.
Ya fashe da kuka "yaro Allah yayi maka Albarka Allah ya jikan iyaye,kai addu'o'I dai dabam dabam har cewa yayi na tsuguna ayi min Addu'a ni kuma ban yi musu ba, anan naji wani sabon salo wai a karanci kul ya kafa bakwai bakwai ga Annabi
.
Da muka kammala na mike wasu yara na kirawo suka sakan babur din a but, na biya su lada mutane suka yi ta kallona cikin tunanin me zan dda babur din mai kama da tsohuwar garwa Abinda basu sani ba , kaiwa zanyi a kera shi duk randa nayi nishadi na rinka hawa, wani sabon salon na TARAR ARADU DAKA
.
Toh Alhamdulillah
Jama'a a nan na kawo karsshen wannan litafi na tarar Aradu daka
Sai kunjini a sabon littafi
.
Marubuci:- Umar Lawan Abdul
Typing:- Shuraih Usman
Post:- Shuraih 99%
Wepsite:- www.keffiansonline.cf

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 10

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 10
.
.
Ayau bamu sami kowa agidan ba ita kadaice a ciki ta tare mu da murna abun daya sa dan sanyi sanyi,
Bayan gaisuwa da yar guntuwar hira sai ta dubi farida "duba karkashin gado ki jawo alkwatinnan"
.
Ta tashi cikin tsananki a hankali ta fito da akwatin ta janyo shi zuwa inda muke a zaune, ita ma ta sake zama
Ta sake dubata "maimaita abunda kikace dani jiya"
Ta gyara zama "nace na baiwa mijina duk kasona "
"To umar kaji ", tana maganar ne a lokacin danake gab da fita hayyacina
.
Mummy taci gaba sanin kankane umar da zanga wani abu zai cuci farida bazan bari, agazawa zan yi har karfina ya kare , ko na kashe shi ko shi ya kashe ni, saboda haka ra'ayin farida shine ra'ayina ni ba na barmaka nawa"
.
Zuciyata ta bugu da karfi bayan danaji batun mai kama da almara ko mafarki, nan da nan na fara yunkurin cewa wani abu amma ina bakina babu yawu
Sai dana tashi na shawo ruwa sannan na sake dawowa ko zama ban yi ba "ina sam bazai taba yiwuwa , yaya ma ku yanke wannan danyen hukunci, ina zan kai milyan saba'in"
"Kwantar da hankalinka umar" mummy kenan ke lallashina
"Wannan kudi na mu ne, kuma mu kace mun bayar wallahi kuma babu sake, bamu manta da wahalhalun da kasha ba saboda mu to dan wannan kudade wallahi basu isa biyanka ba, ga su nan ko ka dauka ko kaki dauka mu dai kai muka bawa, kuma ba zamu fasa ba, garama ka dauka asiri rufe babu wanda yasan me ake ciki"
.
Ta miko wata takarda" gata nan takardarmu ce"
.
*******
.
Duniya ta zame min sabuwa, bayan dana ji ni tsundum a kogin milyoyi, duk na bi na canza na koma wani umar din sabo dabam da barawon agogo, daban da mashayin burkutu,kuma daban da mai sana'ar miyagun kwayoyi
.
Banyi duhun kai ba wajen tsegun ta wa Alhaji halin da a ke ciki nayi , ya taya ni murna, ya kuma bani shawara ta gari , ya shigar da suna na a tela dinsa ta kamfani, ni ne nake yo odar kaya na kashin kaina abinda ya sanya nake samun riba mai matukar romo
.
Na sami nasarar siyawa yayana rantsararren gida , na kuma masa mota sabuwa, bayan dana makare masa rumfa da kaya iyayena ma maido su kusa dani nayi, domin suma asha zakil da maiko tare da su shima mahaifina na siya masa mota, na kuma daukar masa direba dake jansa
.
Wani babban abin farin ciki shine auren da mummy tayi ta kuma Auri Alhaji Amin mai gidana, abun daya zama dadi kan dadi
.
Manazarta yau fa zakui hakuri da wannan ne
Amma kila na idda maku anjima
Domin kuwa na dau alwashin sai na dangana wannan littafin da bango
.
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Daga:- www.keffiansonline.cf

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 9

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 9
.
.
Bani da amsar data wuce eh na amince musaMman a wannan hali da sai inda tayi da ni
Ta matso da bakinta ta jonashi da nawa Abun da yafaru ya mantar dani lissafin dangina,
Shakka babu yau ne ranar shayar da juna zuma da madara
.
Zaune muke a falo muna makale da juna lokacin da kaunarta a raina ya karu da fiye da kaso tamanin cikin dari, ban iya sanin dalili ba amma meyiwuwa saboda bushashhar daren jiya ne daren da nake ta fatan Allah ya cigaba da maimaitashi
.
Ta kewayo hannayentaa biyu cikin wuyana "baka tambayeni a bunda mummy tace dani ba sanda za'a kawoni"
Na kura mata idanu "yaya zan tambayi sirrin da da uwa farida?"
Tayi murmushi "amma ka bayar dani ai sirrikana banga wanda zan boye maka ba"
Na karkace kai dana ji abun data fada"to me tace maki"
"Cewa tayi ta bani sati guda idan taga baka canza ba ni da ita"
"Na canza kamar yaya?"
Takara murmushi "kamar yadda mutun kan canja idan ya samu kwanciyar hankali,kuma na kudiri aniyar canja ka din ,zan mayar maka da jikina muhalli na hutawa, zanyi iya yina domin ganin cewa wata damuwa bata samu matsuguni a ranka ba, ta hanyar dandana maka kauna salo salo, salon rana zai kayatar da kai a yayinda na dare zai dameshi ya shanye
.
Nayi kasake dani"ni dama har akwai wani salon kauna da rana"
Tayi dariya "hala baka sanshi ba,to zaka sanshi daga yanzu "
Ta mike tsam , daki ta shiga ta bar ni nana cikin tunanin shin me zata yi, bayan yan dakiku da basu fi kaza ba sai ta fito
Numfashina ya tsaya cak bayan da naga shirin data yi, hakika in banyi a hankali ba farida so take ta zautani
.
Ta sunkuyo gare ni gami da kama hannuna tashi mu koma daki ko?"
Na zuba mata idanu
"Kunyarka din me zanji,idan naji kunyarka cutarka zanyi, ba zaka sami kaunar da kake bukata ba, to amma izan so kake naji kunyar ka fada min"
Shiru nayi ni cece bayan ta riga ta fara sangartani tuni na mike na bita dakin domin ganin abunda zatayi da ni ko tantama banayi zan sha riba buhu buhu
.
********
.
HALACCI
.
Bansan abunda ya sanya mummy cewa mu hallara agidanta ba sai dai koma menene na san muhimmi ne, musamman danayi la'akarri da cewa da tarewarmu ba afi sati uku ba, muka shirya tsaf sannan muka nufo waje a lokacin da muke rike da hannun juna tafiyace irin ta ma'auratan dake cikin soyayyarsu
.
Muka kulle gidan sannan muka duru a mota na ja mu a lokacin da farin ciki ke mamaye da zuciyata kana iya gane hakan bisa ga la'akari da yanda muke hira cikin murmushi, hatta kallon da mukeyiwa juna na musamman ne, mai bada hannu ya tsayar damu alokacin da muka iso wani junction, sai na taka burki na juya ga abar kaunata muka cigaba da hira
.
Bayan dan lokaci na waiwayi gefena,waiwayar da ta sanya wani abu ya tuko min a zuicya, wani mutumne dake kan babur ya saki baki yana kalle min mata, don mayata ko kiftawa baya yi
.
Na miko hannu waje "haba malam me kenan haka?"
Ya gaggauta kawar da kansa ni kuma na shiga fadace-fadace ina ruwan matsiyaci anyi zakara, tsugunne bata kare ba, can na hango wani mai mota shima , haushi ya kamani na sa hannuna na janyo mayafinta ta yanda ya rufe fuskarta, ta aka nayi maganin mayu
.
Bamu isa gidan ba sai da muka bata mini talatin yayinda da muka isa kuma sai muka ga bakon abu, wata jibgegiyar motar jeep ce , motar da ba mu sani mai ita ba, haka muka shiga gidan cikin rudani, sallama muka fara yi muryoyi da yawa suka amsa sallamarmu
.
Mutum biyar muka samu a zaune Mummy sai wasu maza guda biyu, a gefe guda kuma wasu matan, to wayannan kuma su wane ne, tambayar danayiwa kaina kenan, bayan dana ga ita kanta farida bata shaidasu ba, muka gaisa da kowa , muka zauna sannan mummy ta dubi farida "kin gane su kuwa
Girgizaa kai "tayi ban gane su ba"
"To yayyanki ne"
A guje ta tafi ga matan suka rungume juna , dukkaninsu suka fashe da kuka , na ci gana da kallon ikon Allah lallai dan uwa rabin jiki an manta da duk abunda ya faru a baya, bayan ya n koke koke da maganganu suka saki juna sannan suka sake sabuwar gaisuwa da mazan
.
Ta share hawaye "ina baba take"
"Baba tana asibiti cutar paralise ce ke damunta "
Wannan jawabi ya sanya farida kara fashewa da kuka ni ma kuma sai dana tausaya
Mai kama da babban cikinsu. Yaci gaba "kamar yadda kika san cewa akwai mu to yau gamu, nasan kin san sunayenmu amma da wuya ki iya bambancemu, to ni ki kirani kamal, shi kuma faisal waccan kuma fauzah yar uwartta salimah
Kuma abunda ke tafe damu neman gafara ne da afuwarku bisa abunda ya afku a baya mun ga abubuwa da zamu iya kira isharori wallahi ni din nan sama da shekara kenan kullum ina mafarki da baba, yakan nuna ni da yatsa yace"Allah na jiran isowata " to hakan ya tashi hankalina, kuma nasan ko me nene ya jawo ga kuma mahaifiyarmu yau shekararta goma da cutar kullum abu kara muni yake kuma na tabbata ba komai bane illa hakkinku"
Ya share hawaye "ku duba zumunci ku kuma dubi 'yan uwantaka ta addini ku yafe mana abinda ya faru ku dauka cewa shaidan ne ya rudemu, domin raba kawunan mu"
.
Mummy ta share hawaye "ku manta da komai Allah ya yafe mana gaba daya, mu dama ba mu dauka da zafi ba"
Ya shiga godiya yan uwansa ma suka taya shi bayan da aka natsu sai ya jawo wani akwati ya dubi mummy
"To hajiya kudinku dake wajenmu sun tunkari bilyan daya, to amma wallahi babu inda zamu samo su domin duk dukiyar ta lalace, yanzu dai mun taho da dan abinda ya samu in ya so sai a rubuta idan da raboon zamu biya saura zamu rinka kawo wa a hankali, har Allah yasa a warware komai"
Ta girgiza kai "sam mu baza mu biku bashi ba , abunda aka samu Allah ya amfana sauran mun yafe"
Ta waiwayi farida "koke me kika gani"
Gyada kai tayi "haka ne mummy"
Babban ya sake fashewa da kuka, da kyar aka samu yayi shiru yasa hannu ya bude akwatin tayi wata yar kara sannan ya dage murfin sai ga su kuru kur, tamkar wasu shashasun takardu, zallar dalar aamerica ce numfashina ya dauke ban taba ganin kudi masu yawa haka ba, da alama sun tunkari milyan dari
.
Yaci gaaba da bayani "ga sunana dalar america ce kwatankwacin naira miliyan saba'in idan an zanza su,
shi kenan anyi tsiyar zai rabani da mata ta, a kuma lokacin da bazan juri rabuwar da ita ba, nasan dai da wuya ta zauna dani alhali ta fini kudi, bisa kiyashi sama da naira milyan hamsin duk natane kaico ! Su umar an shiga bayan jaje
.
A washe garin ranar kawo kudi ta sake gayyatarmu , nidai nayi karfin hali muka je ia raina ina mai taraddadin kar tace na sakar mata yarta , yanzu wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa
.
AYYA UMAR
Na tayaka murna da wani daukaka daya ke zuwa maka nan gaba
.
Toh fa akwai dambarwa akan wata tsohuwar Al'amarin Umar, mai cikawa mutane angwa da kara, shin ko kunsa me wannan
.
Ina mika sakon ta'aziyata ga iyaye, da abokai na rashin Abokinmu da mukayi MALAM, wanda Allah ya dauki ransa shekaran jiya da daddare,
Allah ya jikansa
Allah yasa ya huta
Allah ya gafarta masa
Allah yasa Aljannah ce makomarsa
Allah yasa innamu yazo mu cika da imani
AMEEN summa AMeeen wa Ameeeeeeeeeen
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 8

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 8
.
.
Jerin kwanaki suka mirgino gareni cikin farin ciki da walwala, duk wani mutum na jiki yasan cikakken labarina, na shirya da yayana ,iyayena suka yimin uzuri sannan abokaina suka runga zuwa daya bayan daya duk abinda ya afku gareni

ya zama kamar an yi ruwa an dauke bani da sauran bakin ciki yayana da kansa ya nemi dana koma gidansa, na kasance cikin jin mamakin yanda abubuwan suka faru, a Naira dubu hamsin malam Abba ya sa aka koreni , jamil kuma shine me sanar da abubuwan da ke faruwa a kasuwa! Tasa kwangilar yayi tane a Naira dubu dari da hamsin
.
Labarin nasa yana da takaici shi ya sanar da mutumin aiken da aka yi min da kudi shi ya sanar da shi ajiyar agogo, nayi mamaki da kansa mutumin yazo ya dauke shi ta hanyar amfani da master key kuma shi yakai agogon har dakina, wani abun haushi jamilune ya sanya min sailula a aljihun riga bayan da ya dade yana dakona, shi din ne dai ya baiwa mutumin samfurin makullin dakina, ta hanyar luma nawa a sabulu, a fadarsa lamarin ya fari wata rana daya ara bisa karyar zai bude lemo da wanda aka yanka ne karuwa tayi amfani wajen bude dakina a ranar data yi karyar na saba daukota kwanan gida
.
Kamar yadda aziz yayi min alkawari hakace ta faru ba'a dauki lokaci ba aka kaimu kotu, aka shiga tafka shari'a wadda aka kammala ta a zama biyar
.
Baya ga laifin kashe mutum uku a baya da kuma wahalar da ni an samu shaidanin da laifin sana'ar miyagun kwayoyi a wani gida da su ke kira birght house, can a wata unguwa nesa da cikin birnin duk wani mutum mai alaka da shi sai da yansanda suka kwakuloshi , aka yankewa kowa hukunci daidai da laifin daya yi Uban gayyar ya biya diyya Naira MILYAN HAMSIN-HAMSIN ga iyayen mutane uku daya kashe, MILYAN ASHIRIN bisa batamin suna ragowar kudin kuma ribar kafa ne aljihun gwamnati za su shiga, kafin daga bisani a rubuta masa takardar sake mazauni daga duniya zuwa kushewa shi da duk mukarrabansa na kusa
.
********
.
Na kimtsa tun da sassafe domin halartar wata tattaunawa da ake son yi tare dani a gidan mommy, jagoranta shine Alhaji Aminu tsohon mai gidana, hakika yanzu na zama mutum babu sauran wani tabo a tare danu bayan da aka shafe sama da wata guda kafafen yada labarai suna yayin labarina, nayi ta ganin mutane kungiya-kungiya kuma na kusa
.
Ban amince da cin ko naira daya daga diyyar da aka bani ba balle nayi amfani da su wajen huldar aurena, wanda ya rage mako guda kacal a daura shi na kugure a raina zan nemo tsarkakkun kudi duk inda suke, domin karasa tsaftace soyayyarmu, maimakon amfani da kudin da aka same su ta hanyar sayar da miyagun kwayoyi ksafta su nayi sai kace wani gwamna ko ciyaman, na lateef daban na Aziz ma haka wani kason kuma ga yan sanda da aziz yayi aiki da su, ragowar kudin tura su nayi kauyenmu aje can a gina katuwar makaranta
.
Da karfe tara daidai na isa gidan su mummy tuni kowa yana nan ni kadai ake jiran isowata mazaunin da aka bani ya dace da ni gani ga gimbiyata muka rinka satar kallon juna
.
Alhaji aminu ya numfasa"Umar na kirawo ka ne domin na yaba maka namijin kokarin da kayi na baka hakuri gami da baka kyautuka na musamman saboda jarumtar daka nuna umar na amince wa raina kaine mutum mafi da cewa da tallafawa harkokina bisa la'akari da jajurcewarka da kuma cika alkawarinka
Ina gayyatarka fare ni kuma da fatan zaka amsa gayyatata
.
Na gyada kai"na amsa"
Yayi murmushi "to ina godiya"
Ya miko hannu ya dauko wata yar jaka a hankali ya budeta ya zaro wasu takardu daga ciki
.
"Matso nan" ya nema yana mai dubana
Na tashi na kewaya ya ajjiye min biro "sai kasa hannu takardun gidana ne zan mallaka maka ni na koma sabon gida"
Cikin makyarkyata da rawar hannu nayi rubutun ina jin lamarin kamar tatsuniya katoton gida ma'abocin wadatar da furanni zai zama mallakina ina kammalawa ya sanya shedu suma suka sa hannu sai ya miko min takardun gaza sa hannu nayin karba sai na fashe da kuka yajjiye min su gami da komowa ga lalubo wata takardar
.
Ya dago kai ga dubana "wadannan kuma takardun motane ya zama wajibi na siya maka abin hawa saboda harkar makudan kudade da zamuyi sai dai kayi hakuri ba wata mai tsada bace, Honda civic ce, tana garejin gidan sabuwa ce fil ba'a taba hawanta ba ga takardun da makullin yanzu ma kana iya zuwa ka dauki kayarka"
.
Wani sabon kukan ya kubuce min farida ma ta tayani da zubarda hawayen, tana mai sa hankaci tana share min nawa
.
Ya dora "bazan barka haka ba, kana bukatar kudi a hannu ga (cheque) cek nan na naira milyan , farida miliyan daya hajiya ma haka, dawainiyar biki kuma duk na dauketa daga lefen ango zuwa kayan dakin amarya da duk kudaden da za su ci ko su sha, da duk motocin da za'a bukata da duk kudaden da za'a kashe zan ware maku milyan daya"
.
Bani kadai ba duk mutanen dake wajen sun zubar da hawaye muka jerawa Alhaji kundi kundi na godiya
.
Ya kade babbar rigarsa "babu komai ai ni ne da riba na dade ina neman amintacce ban samu bayanzu kuwa da Allah ya bni ba zanyi sake ba"
.
Mummy ta dube shi "naji kayi maganar lefe
mu ba ma bukatar lefe sadaki kawai mukeso shima don Allah ya wajabta shi"
Ya girgiza kai "ina ! Za a yi lefe, kamar yanda kowacce ya ake yimata lefe, akwati bakwai ya isa?"
"A'a a'a kar ka soma" mummy kenan
Yayi murmushi "saide kiyi hakuri da ni , dabi'ata kenan idan nayi niyya bana fasawa, ba kuma zan canza yau ba"
.
*******
.
Idan kana neman bikin aure da aka yi abubuwan ka sami namu, sai ka juya an sake iya sakewa ba kuma tare da kwabona ba duk a rigar arziki [ni kaina Shuraih 99% sai da na halarci wannan biki]
.
Akwai farin ciki marar misali yayin mu ka tsinci kawunanmu mu biyu a daki , bayan da muka gabatar da salloli da Addu'o'I da ake nema daga ango da marya, muka zuge kaji gami da tauna kwainar kwai, muka kuma sha duk abunda rai zai so ya sha, babu abunda ya rage a lokacin illa cin ribar wahalarmu
Na bude tafin hannuna "sako naki a nan zamuyi alkawari"
Ta sako nata hannun tana mai murmushi wata kunya ta kamani sakamakon jin hannunta dana yi taushi tubus tamkar wani ingantaccen soso ne da babu coge, na hakkake cewa I......
.
Ku dai cigaba da bibiya don kuwa da kwai wani babban al'amari dake shirin faruwa game da iyalan Mummy
.
Nine naku Shuraih Usman
Inkiya 99%
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 7

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 7
.
.
Ya kunna wata yar karamar rediyo, daga ita ne muka ji duk abubuwan da ake tattaunawa, bamu mu rasa komai ba, har zuwa sanda suka rataye ka, da ace basu fito da wuri ba ritsa su yan sanda zasu yi, to amma fitowar da su sai ta taimaaka, domin da ba su fito ba din ba, za'ayi abin nan da ake kira anyi ba ayi ba, domin babu shakka da sunji alamar motsi harbinka zasuyi domin baza su so ka kubuta ba, suna kokarin hawa mota ne aka far musu in har kana cikin hayyacinka baza ka gaz jin harbin bindiga ba, suma fito na tasu sukayi akayi kare jini biri jini, sun raunata yan sanda uku su kuma an kashe musu mutum daya, biyu kuma sun shiga hannu bayan da akayi musu raunuka munana, akwai kato gabjeje shine mutumin dake wahal da kai ya kwana karkashin kulawar yansanda a daren jiyan dai an tura yan sanda uku asibiti su kula da farida gudun afkuwar wani abu"
.
Wani dadi ya cika zuciyata tuni na dungura goshi akas cikin sujjada dayiwa Allah godiya ban san adadin mintunan dana karar ba n dago fuskata cike da hawaye
"Lateef kayi min komai kayi min abinda ban san kalmomin da zanyi amfani da su ba domin godiya, kayi min abinda wani mutum ba zai taba yi min ba, ka ceci raina ka kuma kyautata rayuwata, ka tsamo zuri'armu daga bakin cikin da zai dauwama har abada"
.
Ya dafa kafadata "kar ka damu umar, nayi don Allahh don kuma kaunata da kai, zanyi farin ciki idan kuma na ganka da farida a matsayin miji da mata don kuwa kun sha gwagwarmayar da bata cancanci tashi a banza ba"
Na juya ga aziz hawaye na kwaranyowa daga idona "aziz me zance da kai? Na gode bata wadatarba, madalla tayi kadan to ina kalman?"
.
Yayi murmushi hutar da bakinka bana bukatar godiya wannan shine aikina akansa nayi rantsuwa , kuma don nayi ake biyana, abinda kawai nake nema kataya mu addu'ar Allah yaba mu damar sauke nauyi ya kuma bamu ladan abun da mukayi dai dai , inda muka kuskure yayi mana afuwa da rangwame idan ka yi haka shi kenan"
Ya mike tsaye "zan tafi wajen aiki kumaa zan kokarta wajen ganin na sami ganawa da yayanka, zan warware masa komai shi kuma sai ya tunkari iyaye"
.
Na fashe da kuka "na gode ! Nagode!! Aziz Allah ya cika maka burikanka"
Yayi murmushi "amin nima na gode"
Muka mike tsaye domin rako su waje shi da mutanen da suka zo tare
Ya fuskance ni bayan da muka fito "umar bincikenmu zai rutsa da mutum uku, principal malam Abba, da kuma Abokan zamanka na kasuwa da alama suna da hannu a abubuwa da dama
.
Yadan saurara daga bisani ya dora "zan yi iya yina don ganin shari'ar bata dauki lokaci ba! Za'ayi a kare a sati daya babu bukatar mai raunin ya warke, tunda raunin bai shafi gabobin hankali ba kafafu wane da hannu, zanyi wannan kokarin"
Na ci gaba da jera masa kundin godiya ahaka muka rabu
*********
Ina saka kafata dakin ta taso a guje na san nufinta shine rungume ni ni kuma bazan so haka ba musamman saboda ganin manya kusa da mu, cikin hikima na dan goce gami da riko hannunta don gudun kar tasha kasa
"Dakata farida da sauran lokaci"
Ta fashe da kuka "wayyo Allah umar da yanzu an cuceni da an takaita rayuwata"
Naja hannunta zuwa kan gado a hankali na zaunar da ita nima na zauna
"Umar barkanmu fa !"Zan cen mummy kenan tana mai zubar da hawaye,
Nayi murmushi barka dai"
Ta jinjina kai "wai hikimar Allah komai yana da karshe yau karshen wannan yazo"
Na sunkuyar da kai"wallahi kuwa haka lamarin Allah yake"
Ta mike domin ficewa daga dakin tasan tilas zamu bukaci ganawa
Futarta taba farida damar matsowa kusa dani "umar yaka ji da ranka?"
Nayi murmushi "naji abinda yafi dadi dadi abunda ya haure farin ciki fari abunda za a soma kwatanta shi da murna ba"
Ta lumshe idanu"naji wanda ya ninka naka sau dubu, shi yasa na warke a tsakanin awoyi goma kacal dana sami labarin cewa ka kusa zama angona"
"Aina kika sami labarin ke kuwa?"
Tayi "a cikin mafarki, naga har an daura mana aure ina baka madara a baki a cikin wani lambu mai matukar kayatarwa"
Raina yayi fari dajin kalaminta "to ni kuma fa me na baki ko ban baki komai ba"
Ta kara lumshe ido"ka dandana min zuma mai mugun zaki" na jinjina kai you're right da sannu zaki dandaneta a farke da sannu zaki gane abunda ake kira soyayya atare da ni"
Tayi murmushi "ka cika garaje kai fadarce babu cikawa , ni kuma ka bari ka gani sai ka ringa kai karata wajen mummy"
"Wahalar dani zakiyi kenan?"
Ta gyada ki "kwarai kuwa,bazan barka ka sake ba sai ka dandana kudarka , amma fa da zunzurutun kauna"
Muka more da dariya
Tadan kimtsa "Umar za'abari ka aureni kuwa?"
"Me zai hana"
"An baka wata baka so"
"A ina ki kaji?"
Ta kwantar dakai "lateef ya fada min komai na dade ina mamakin yadda ka shirya wa kanka zafi saboda ni"
Nayi murmushi "manta d wannan na fada miki dalilin auren, kuma yanzu ya kau ki dauka cewa abubuwan da ki ka gani a mafarki ba mafarki bane, ki dauka cewa an yine a gaske, kuma. Za'ayi din"
."Ka tabbta?"
"Na tabbta"
"Oh I love you"
"I too" muka kara morewa da dariya
..........................
AYYA UMAR ANSHA DAKYAR
TO AMMAFA AKWAI WATA...........
.
www.facebook.com/hausaebooks

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 6

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 6
.
.
Na tsakiyarsu ya zo gabana "malam umar sai defa kayi hakuri don kuwa yau zan aikaka kiyama , saboda na gama wasa da kai, dun haka yanzu zan rataye ka kowa ya huta
.
Daga nan kuma sai ace abun duniya ne sukai maka yawa ka kashe kanka,"
Yana zuwa nan a maganarsa sai ya kece da dariya mara dadin sauraro, suma gabza gabzan da suke bayanshi suka tayashi suna masu kyakyatawa
.
Sun dau lokaci suna wannan dariyar alokacin da ni kuma na gama sallama rayuwata jira kawai nake mutuwata ta zo ta daukeni don na tabbata bazan tsira daga hannun wannan mugun mutumin ba
.
Babu abun da ya fara zuwa araina face yadda farida zata kasance izan na mutu nasan watakila itama ta mutun domin kuwa babu ta yadda zata iya rayuwa in batare da ni ba saboda zunzurutun so da kauna da take yi min
.
Alokacin dana tuna da iyayena sai wani kwallan bakin ciki ya yagangaro daga idona, sai a sannan na fara nadaman irin abunda nai masu, nasan ba shakka nabar masu abun gori a zuria gashi ni kuma zan riski ajalina a hannun wayannan mugayen mutane,
.
Katon dazu ya sake dubana lokacin daya tsuke bakinsa ga barin yin dariya, yace "kash Umar da alama naga kana son rayuwa a bankasa sai de nayi maka kashedi kaki ji dun haka sai a gaida Kiyama, "
Yana gama fadin hakan sai ya sanya kafarsa ya ture teburin da kafana yake kai , teburin na faduwa sai na zazzago kasa,
Igiyar dake daure a wuyana ta shake ni tamau na dunga wuntsila kafa funa ina neman taimako a haka har wani hazo ya ziyarci idanuwana, daga nan ban san Abun daya fsake faruwa dani ba
.
*******
A firgice na. Farka ina kiran Inna lillahi wa inna ilaihirr ra'ji'un,
Na tsinci kaina acikin wani dan madaidaicin daki ina kwance akan gado ga mutane uku a gefen kaina,
Na mike na dubi mutanen wayanda sam basu yi mani kama da mutanen dazu ba, don kuwa wayannan sun yi shiga ce irin na ma'aikata, sunci zanzaro sai kace mr mugopark
.
Wani daga cikinsu ya kariso ya miko min I.D card ,na duba a gaggauce na Hukumar 'yan sanda ne
Suna : Azizu jakande
Matsayi: Inspector
.
Take sunan ya fado min arai babu shakka kanin lateef ne wanda yace zai tuntuba da maganata sai na saki jiki
.
"Ka amice?" Ya nemi ra'ayina
Na gyada kai "na amince"
"To ina wanda ka kashe?"
Na girgiza kai "ban kashe kowa ba"
Duk suka bushe da dariya
Ya dubi wani dan sanda "ku mai da mu a motarku wajen yana da nisa"
Ya kame "an gama yallabai"
*****
Ina zaune a dakina mutane uku kewaye da ni, na farko lateef ne sai kaninsa Aziz da kuma wani ban san ko waye ba, na dubi agogon bango karfe takwas na safe da minti hudu
$
A sannane lateef ke cewa "Umar Allah ya kiyayeka ka tsallake rijiya da baya, ba dan an kawo agajin gaggawa ba da yanzu ana zaman jimami"
Na dube shi "wai yaya abun ya kasance?"
Ya gyara zama "izan zaka tuna min yi maganar kanina da kai, a daren jiya na taho da shi nufina ku gana, a sannan cikin sa'a na sami kofar dakin ka a bude, sai na kwankwasa amma shiru baka amsa ba, ganin ganawar dare ya kamata ayi saboda la'akari da cewa an zuba ido akanka, sai na yanke shawarar shiga na ta sheka, hakan nayi kokarin zartarwa ina saka kafa naji sailula na ringing dana duba sai na ganta kusa da kafata na sunkuya na dauka gami da nufar shimfidarka domin na baka ka amsa kiran, banga kowa a shimfidarba, na zaci bandaki ka shiga sai na danna ok domin baiwa mai kiran uzuri
Ina fadin "hello'
Wata kakkausar murya ta biyo baya "kai malalaci in ce ka shirya ko? Yanzu zamu aiwatar da nufinmu"
Nayi shiru ina sauraron murdadden sakon muryar kuma taci gaba "kana iya hutar da kanka, kayi zamanka a daki nan muka zaba maka amatsayin kabari, ko kaje wani wajen sai mun maido ka"
.
Da fadin haka na tsinke layin da wurwuri na gane mai maganar da kuma inda ta nufa sai nayi saurin durfafar ban daki na kwankwasa da karfi amma ban ji amsa ba jin haka ya sanya ni turawa wayam na sami shi babu kowa a ciki, da sauri na gayyato kanina na labarta masa abin da ake ciki
.
Ya jinjina kai "zo mu ja jiki, yanzun nan kaga sun zo"
Banyi musu ba muka fice daga dakin da sauri bayan da ya ajiye wata yar na'ura, mukaa nufi wani lungu muka rakabe, da labewar mu yayi waya head quarter' din yan sanda 'yan sanda goma ya nema masu zafi iya aiki, fadi inda zasu zo , ko minti ashirin ba ayi ba suka karaso, 'yan dakiku suka harba agogo wadanda su suka isa tattaunawa a kuma kaso rukuni-rukuni
.
A cikinsu ne kuma fitilar mota ta hasko layin ta durfafo kai tsaye yadda muka zata din haka ta afku a kofar dakinka ta tsaya bayan dan lokaci wani ya fitoo, kwankwasa kofar dakin yayi, kafin daga bisani ya tura kai ciki, ya dan jima kadan me yiwuwa minti biyu, watakila kuma uku ko hudu a cikinsu ya fito ya sake dawowa ga motar bayan 'yan maganganu duk kofofin suka bude, wasu kartin mutane biyun suka fito, 'but' suka daga inda anan suka kinkimo buhu, bamu raba daya biyu ba wajen tabbatar da cewa kai ne a ciki, suka shige dakin da kai
.
Na dubi kanina "mukai agaji
Girgiza kai yayi "tukunna dai akwai sauran lokaci"
.
Kuyi hkri da short page dinnan
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
www.facebook.com/hausaebooks

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 5

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 5
.
.
Muna nan tsugunne cikin jimami, wata nurse tazo tayi mana sallama, sannan taci gaba" hajiya an fito da yarki daga dakin na'urori an bata daki mai lamba sha hudu, zo muje ki gani"?
.
Muka mike gaba daya babu wani alamun karfi a jikina tamkar wanda aka wuni laftar masa jiki,
Mummy ta dubi nurse din "a wanne hali take yanzu?"
"Eh to mu karasa din ina ga ana iya cewa da sauki tunda tana iya yin numfashi sama sama"
Tsoro ya kara cika zuciyata, a wannan hali muka isa dakin tsa hannu ta tura kofar ta shiga sannan muka bita abaya,
Kwance tage rigingine idan baka kura ido ba bazaka ga alamun numfashinta ba, tamkar wata gunki ce ko zane
Na girgiza kai cikin tausayawa a kuma lokacin da zubar hawayena ke daduwa
Mummy kuwa tagumi tayi da alama ta gama fidda rai hawaye a fuskarta wani na bin wani
.
Nurse din ta dafa kafaddarta "ki kwantar da hankalinki hajiya me yiwuwa nan da awa biyu zata iya wartsakewa, damuwa ce tayi mata yawa kdan ya rage jininta ya hau, amma Allah ya kiyaye, wata kila gobe iwar haka ma ta iya takawa da kafafunta"
.
Daga ni har mummy babu wanda zancen ya shiga akwai shakku cikin tashin farida a irin wannan dan kankanin lokaci, tana iya yiwuwa tunda su jami'an lafiya ne, suna da sani akanta, tana kuma iya kin yiwuwa jawabin nata ya kare ne a matsayin wani salon kwantar da hankali
Muna nan zaune cikin halin zama mai kama da makoki ga wadanda radadin mutuwar ke cinsu, sai kofa ta bude wani ne dan siriri dogo da ganinsa kasan kwararren likita ne,biye da shi akwai wasu nurse guda biyu
.
Ya dubemu "ku dan bamu dama, zamu dan bata wani taimako'
Muka mike a tsaye tare batare da bata lokaci ba muka nufi waje
Na duba agogona karfe goman dare na juya ga mummy" zan je na dawo in Allah ya yarda nan da minti talatin
Ta gyada kai "to shikenan"
*****
Na san makulli na bude dakina batare da bata lokaci ba nasa kafa ciki ba komai ne ya maido ni illa na kwashe yan tsirarun kudadena da suka rage, aniya ta shine siyawa mummy abinci da su, bayan dana kula cewa itama bata ci komai ba, sai dai ba anan gizo ke sakar ba ko na kai mata ma ba lallai ba ne taci
.
Bayan dana debe sune na fara kokarin ficewa a daidai lokacin ne wata kara ta gauraye ko ina na,cike da mamakin abunda ke iya yin wannan kara, shakka babu agogon bangona bashi da alarm , ban kuma mallaki wani abu mai alarm ba
.
Shawarar dana fara yankewa itace nayi ficewata , amma sai karar taci gaba abinda yasan ya ni canza shawara , na fara yan dube dube domin gano daga inda karar ke fitowa, bayan dan lokaci na fahimci wajen akan katiata ne sai na nufi can ina mai kwadayin ganin ko me ne ne, mamaki ya kama ni yayin da na yi arba da mai yin, na'urar sadarwa ce ta hannu, ni dai ban mallaketa ba kuma baki nake yi ba ballantana nayi zaton wani ne ya manta ta,
Na kasance cikin shawarwarin abunda ya kamata nayi wata zuciyar tace tsallake ka fita,wata kuma tace dauki ka saurari kiran daga nan ma sai ka san ko ta wace
.
Nayi kasadar durkusawa na dauka kirar samsung ce mai kyawun gani, har yanzu bata daina callara kara ba, cikin ganganci da karambani na danna O.K ban bata lokaci ba wajen karata a kunne na
"Hello wane ne"
Aka amsa a daya bangaren "Mala'ikan mutuwane"
Error page error page error page
An samu matsalar fallayen littafin anan amma ga abuinda ya kunsa
.
"Hello wane ne"
Aka amsa a daya bangaren "mala'ikan mutuwane"
Gabana ya buga, hankalina ya tashi sakamakon muryar danaji, ba kokonto tabbas na shaida wannan murya, ba muryan kowa bane illa na mugun mutumin nan daya jefa rayuwata cikin tashin hankali
Mutumin ya cigaba da fadin "kai yaro ka tsorata ne , to gwamma ma ka saduda don kuwa mun riga da mun gama wasan da mukeyi da kai, don haka yau zaka bakunci kiyama dafatan kayi aiki mai kyau, sannan ina shaida maka gwamma kayi zamanka a cikin dakinka domin kuwa anan muka zaba zamu kasheka, amma in kaso kana iya tafiya duk inda zaka, mu kuma zamu bika mu kamoka sannan mu dawo dakai har dakin naka sannan mu hallakak..."
.
Ban tsaya ya karasa maganar ba na datse kiran ta hanyar kashe wayar, sannan nayi cilli da ita ta gwaru da bagon dakina
.
Gabana sai faduwa yake , na fito daga cikin dakin na kulle sannan na nufi hanyar asibiti ,
Ina tafiya ne kawai amma hankalina bashi a jikina, tunane tunane kala kala babu wanda banyi ba acikin zuciyata,
Domin kuwa nasan wannan mutumi bashi da imani kuma baya da tausayi tabbas zai iya aikata abunda ya furta
.
Ina cikin tafiya ko lura da gabana banayi, kwatsam sai ji nayi wani abu ya dake ni akai zan yi ihu amma naji wata basamudiyar hannu tayi caraf ta rufe mani baki,
Koda na lura sai naga wani katon mutum ne ya rungume ni ta baya ya kuma sakayo da hannunsa ya rufe min baki, ina ta wutsil da kafafuwana domin na kwaci kaina daga hannunsa amma yafi karfina, babu irin kokarin da banyi ba , haka wannan mutumin ya dauko wata hankici daga aljihunsa ya sanya a hancina, wani daddan kamshi na sheka daga nan ban san me ya faru dani ba
******
Farkawa nayi a gigice sakamakon ruwan sanyin daya sauka a fuskana, cikin firgici na bude idanuna, ba karamin razana da kidima nayi ba sakamakon yanda na tsinci kaina,
.
Igiyane mai kauri daure a wuyana igiyar an jashi yaje sama aka daurashi a jikin fankan dakina,
Hannuna suma a zagaya da su ta bayana sannan suma aka dauresu tamau
kafafuwana kuwa suna saman wani dan karamin kujera wanda da ba don shiba toh na tabbata da yanzu ina kiyama,
.
Hahhahahahahahah, sautin dariya naji acikin dakin nan idona yakai wajen da nake jin dariya take idona yai arba da wasu girda girdan karti su Uku, dukkansu suna sanye ne da bakaken kaya, jaket, da kuma jeans,
Na tsakiyarsu ya zo gabana "malam umar sai defa kayi hakuri don kuwa yau zan aikaka kiyama , saboda na gama wasa da kai.........
.
KAI UMAR
A TUNANINKU UMAR ZAI TSIRA
KUWA

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 4

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 4
.
.
A guje na shige babbar rigar liman ina neman ceto" ka ceceni liman , idan suka tafi dani kasheni zasu yi"
.
Da nasan haka ce zata faru da ban kwatanta shiga rigar ba, wani rin dundu yayi min da naji tamkar zan amayar da kayan cikina
.
Yafara fada cikin bambami da daga murya "mutumin banza suma kashe ka din mana, wacce tsiya barawo zai tsinana idan an kyale shi? Ni dai Allah ya ceceni da ban riga na aura maka 'ya ba , ace kamata ya aurawa barawo 'ya"
.
Wani sabon salallami ya fito daga bakin wata mata"lailaha illallahu, dama barawo ne malam"
"Barawo ne mana motar mutane ya sato, masu ita ne suka zo masa da 'yan sanda, bakanikensa ne ya tona shi"
"Amma Allah wadaranka" inji wata 'yar tsohuwa, ko rara daya biyu banayi mahaifiyar liman ce, sai dai ba zanso addu'arta ta karbu ba
.
Cikin halin riko na sai na dubu ta taru 'yan bangar suka nufi waje dani, kafata ko takalmi babu tuni na watsar da su, cincirindon da jama'a sukai a waje yayi matukar girgizani, da ganin fitowarmu suka dauki hayaniya, kowa yana fadin abinda yake ganin yayi daidai da shi, cikin motar aka watsa ni, batare da saurarawa ba aka nufi nahiyar gida dani
.
Tarar da mahaifina zugum a soro yana hawaye ya rikitani, na tabbata bakin cikin abinda ke faruwa ne yake cinsa, naji tamkar na tashi drama din na dakatar da ita na kuma fayyace gaskiya, sai dai xuciyata bazata bari ba, ita take jagoranta ta, yayin da ita kuma so yake sarrafa ta, abinda yafi hakan tashin hankali shine samun mahaifiyata tayi zaman dirshen a tsakar gida, kuka ,karaji da kururuwa duk tana yinsu, wannan ya sanya na tsani kai na, bakin cin takaici da damuwa duk suka baibayeni, na amincewa raina na fayyace komai domin samawa iyayena kwanciyar hankali, babu shakka hakan shine zai fi
.
Da wannan tunani na fara kokarin banbare wandona dake rike a hannun wani kato , shi kuwa sai ya kara dakume ni a zatonsa wani salon ne na kara kyautata drama din
"Sakar ni malam" na fada afusace
Ba sakin nawa yayi ba, matse ni yayi iya kacin matsewa gami da yarfa min biyar yana huci, tamkar na rama naji yayin da zogi ya ratsani, to amma sai nayi ta maza na kasance cikin halin daure fuskata hawaye ya zubo min dana kara nazarin halin da mahaifiyata take ciki, ba zan iya kiyasta bakin cikin da take ciki ba na dai tabbata tana tattare da damuwa.
.
"Dauko lambar mu tafi" wani kato ya daka min tsawa, bana bukatar shiga wani waje hannu na tura cikin rumbu na fito da ita, abinda ya sanya yan kato da goran kara tasa keyata, gab da zamu shige soro na kara waiwayowa na dubi mahaifiyata, kafin kuma na tarar da mahaifina a soro, lissafi duk ya dagule , ina ma zuciyata zatayi min alfarma na fayyace komai, sai dai ina ba zata yi min ba, soyayya dake cike da ita ta baibaye ta, wanda hakan ke sauyata gargadi ne cewa farida kubuce min zata yi
******
Ina zaune shiru cikin tariyo abinda ya wakana akauyenmu , a lokacin da su kuma yan kato da goran ke tariyo abubuwan dariya, sai dai atare dani banga abun daya isa ya sanya ni dariya alokacin ba, na rinka tuno halin tashin hankalin dana bar iyayena aciki, na sani izan ba sa'a ba na bar abun da za' aita goranta wa zuri'armu har a nade kasa, wannan itace dabi'ar zaman kauye, barawon Albasa ma akan haana jikansa diya, ballantana kuma ni aka ce barawon motane
Toh ya kukejin littafin (Shuraih Usman)
.
Lateef ya danka masu kudin aikinsu naira dubu biyar, suka watse suna godiya, suka bar mu mu biyu ni dashi,
Ya dubeni "ina fata komai yayi yanda ake so"
Na gyada kai "komai yayi lateef sai dai kuma ina mai jimamin abubuwan da suka faru, ko tantama bana yi iyayena suna cikin bakin ciki"
.
Ya girgiza kai cikin jimami daga bisani ya kara matsowa kusa dani
"Umar na shawarce ka da wani abu mana"
"Wani abu kemar me fa"
Ya sunkuyar da kai "ka gafarce ni bisa abin da zan fada a gani na ka hakura da farida zai fi sauki"
Na kura masa ido kawai a kuma lokaci guda hawaye ya fara gangarowa daga kumatuna nasa hannu na share sannan na mike tsaye
"Lateef da ace zuciyata zata iya jure haka , da tuni na aiwatar da shi, sai dai ina! Ba zayta jure ba tun farkon gani na da farida ta rigaya ta mallake ni, bana aiwatar da komai sai abinda zan faranta ranta, kuma kasan wani abu a halin yanzun ba auren tane abin daya fi damuna ba, burina shine na tsamo ta daga kangin rayuwar data ke ciki, na daura niyya kuma zan cigaba da fafutaka iya raina, ko bani ba farida zata auri wanda ranta ke so, ta dandani dadin rayuwar aure ita da mijinta?" Na sunkuyo kusa da fuskarsa "ka shaida lateef na rantse da Allah na bayar da rayuwata fansa ga murmushin fuskar masoyiyata"(ina masoyan gaskiyan suke)
(Ga ni nan Shuraih Usman
.
Ya jinjina kai gami da kuramin idanu, daga bisani ya ajiye wani ingarman numfashi
"Lallai umar kayi nisa, ba kumaa zaka taba jin kira ba, saidai duk da haka ina da wata shawarar, ka mika rahoton hannun 'yan sanda zasu taimaka wajen zakulo duk abinda ke faruwa"
Na girgiza kai "bazan yi haka ba lateef , irin wannan binciken yana bukatar hanya ko kudi, ni kuwa hanya ta zuwa masallaci kawai, ka sani kudi kuwa bana bukatar cewa da kai komai"
.
Ya mike tsye gami da dafa kafadata "Umar nima bani da kudin amma ina da hanya kuma hanya wadda take da karfi, yaya zaka yi idan nace kanina inspector ne? Da taimakon Allah da jajurcewa ta muka samu yakai matsayin, sa'arda yana karatu ko naira daya ya kashe, nine na bashi ita, to zan taimaka maka zan tuntube shi da batun, kuma zai yi duk abinda ake so batare da ka kashe koda naira daya ba"
.
A wannan lokaci danake cikin tashin hankali abune mai wuya na iya yin murmushi, saidai na jibgewa lateef kundi-kundi na godiya, yayi murmushi 'kar ka damu Allah ne ya hada mu, bamu san irin amfanar juna da zamuyi ba arayuwa"
*****
Ban tsaya yin komai ba in banda wanka , haka na nufi asibiti yunwa na kwakular cikina, tunda na saka kafata a ginin asibitin tunane tunane suke ta tsere a raina, mafi muni shine mai cewa mai yiwu wa farida ta rigamu gidan gaskiya
A inda na bar mummy jiya, yau ma anan na tarar da ita bata canza kaya ba, ban kuma ga alamar tayi wanka ba, canji daya dana iya gani shine yau tafi jiya rama, ta dago kai sa'ar da na tsaya a kanta ba gaisuwa ce agabanmu ba mai jiki na fara tambayarta,
.
Ta kwantar dakai "to ina iya cewa da sauki tunda dai shi ake nema, amma ni tun jiya har yanzu ban ganta ba, kowa na tuntuba sai yace na dai saurara wai ana cigaba da kokari , umar ina zaton ma mutuwa tayi suke boye mun"
Hawaye ya zubo a fuskata, shiru nayi cikin rashin sanin me zance da alama fitar da rai da farida ne, ya mantar da mummy tambayata yanda na karke da iyayena, to ana ta kai waya ke ta kaya?.
.
Jama'a sai fa kunyi hakuri kwana biyunnan don ina busy sosai, amma zan ringa kokari koda short ne ina kawo maku
.
Sannan ina taya Abokina YARIMA A GANGARIYA murnar , domin kuwa iyalinsa ta haifa masa ya mace , Allah ya rayata, ya sa mahaddaciyar Alqur'ani,
Ameen
.
Nidinne dai Shuraih Usman
Daga:- www.facebook.com/hausaebooks

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 3

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 3
.
.
Na marairaice "tawace baba"
Bai kara komai ba sai ya tafi ya rabu dani na dan tsaua jim sannan na nufi cikin gida
.
A wajen mahaifiyata farin ciki na tarar da kyakkyawar maraba, ta gabatar min da abinci da kuma fura, Na fito wajen lateef gayyatarsa nayi muka shiga cikin dakin da aka ce nawa ne nida laraba, na ajiye masa abincin ni kuma na koma gefe guda.
"To taso muci mana"
Nayi tsaki "bai da muhalli a ciki na"
Hakika bai kamata nayi haka ba, ko don gudun kar ya zargi wani abu musamman saboda bambancin kabila dake tsakaninmu ga kuma dukiyarsa da muka taho da ita, Amma ina! Shi sam bai kawo haka arai ba tuni yaci tuwo yasha fura, daga bisani yaja fulo ya tuntsure, anan yabar ni ina ta kulle kulle arai har safe,
.
Tun da sassafe lateef ya hau tabe tabe ! Ba wani gyara ne na gaske ba, juyen baikin mai ne da yan abubuwan daba a rasa ba, wajen karfe dayan rana ya kammala, na sallame shi ya tafi, bayan da nace ina zuba idanu, wani lamarin da mahaifina ya tuhume ni akai shine ganin na kwance Number plate(Lamba) na ajiye, wannan ma ya sanya masa shakku a zuciya, na shiga gida na sami mahaifiyata, izini na nema akan ina so mu gana da amaryata, ban sami matsala ba, kai tsaye ta aika gidan ta sanar da su, aka ajiye karfe hudu a matsayin lokacin daya kamata na je, wanka na yi na yi fess dani sannan na hau mota na shiga zagaya gari, duk inda na bi sai abini da kallo, wai su abin mamaki ne saurayi kamata da mota mallakin kansa, ni abin har ya kan bani da riya, ba wata motar kirki bace, irin tsohuwar yayin nan ce da ake yiwa lakabi ajalin tafiya(tab
.
Kafin wani lokaci labari ya game ko'ina Umar ya sayi mota, aka rinka zuwa yiwa iyayena barka, sai dai abinda basu sani ba gab barka take da komawa jaje, meyi wuwa awoyi biyu nan gaba
.
Karfe hudu shaura na durfafi gidan liman , bayanda nayi sallar la'asar, kafin n kara sa, shi ma ya fito daga masallaci yana zaune a wani katon buzu yana jan carbi naje na durkusa gwiwa biyu na gada shi, ya amsa gami da shi min albarka, wai har yarom kirki yake kirana, na tashi zuwa gindin mota ta bayan da muka kammala
.
Na harde hannaye a kirji, gami da jingina sosai da motar daidai nake kallon mutane taamkar wani dan birni mai ji da kansa a taron kauyawa
.
A karo na tara na kai idona ga kofat gidan liman , babu abinda nake son gani illa fitowar laraba yarinyar da aka ce da ita ake shirin daura mana aure gobe, koda yake fuskarta bata nuna komai ba, amma amma adadin majalisun tattaunawa dake zuciyata har sun wuce kirge, wadda nafi jin haushi itace mai cewa idan bayeraben ya gaza aiwatar da shirin yaya zanyi.?
.
Shakka babu wannan tunani ne dana ke wwadai da shi, koda a mafarki kuwa ba zan so ya wakana ba, duk kuwa da cewa aiwatar da shirin wani tashin hankali ne babba, amma a wajena tashin hankalin shirin yafi rashin masoyiyata, a wani sashin kuma tafarfasa zuciyata take yi tana kuna, ba don komai ba, sai don abubuwan uku da ahalin yanzu suke tare da ni, Na farko tsana ta da ganin yarinyar dana aika ayo min kiranta, araina zan fi son kallon abu mafi muni fiye da kallon fuskarta, ba don komai ba sai don kasancewarta mai son mallake wani matsayi dana alkawartawa farida shi, hali na biyu kuwa zulumi da jimamin abinda zai biyo bayan shirin danayi, ko tantama babu zai zamo bacin rai da bakin ciki mai girma ga iyayena, zan tafi na barsu cikin tashin hankalin da ban san abinda ya kamata na kwatanta shi da shi ba, tun da na gano haka kuwa kamata yayi na fasa sai dai ina, zuciyar ta yi nisa ban da tunanin mallakar farida bata tuna komai
.
A gefe guda kuwa rashin sanin halin da farida ke ciki ne ke dagula min lissafi, ko ba komai dai na tabbata tana jin jiki, in haka ne kuwa dole ne nayi gaggawar komawa kusa da ita, a cikin wannan hali na hango 'yan mata biyu fitowa daga gidan liman
Fuskar daya na iya gani ma'abociyar tsage 'yan baka da uku-uku dayar kuwa ta rufe fuskarta da farin mayafi, abun d ya tabbatar min da cewa itace wadda ake so na aura, tsayuwarsu a kusa dani ta sanya wani abu yuko min arai, na tsane su iya tsana tamkar na rufe su da duka naji araina, dayar ce ta fara gayar dani, karfin hali nayi na amsa batare da nuna wani abu a fuska ba
.
Daga bisani ta juya ga dayar "laraba baku gaisa ba"
"Ina wuninka" ta maganar ne cikin murya mara kara
Na amsa "lafiya lau" daga haka ban kara komai ba
Batare dana shirya ba , dayar ta janye mayafin da yarinyar ta rufe fuskarta, hakan yabani damar ganin abinda fuskarta ta kunsa,
Doguwa ce ma'abociyar dogon hanci da dan karamin baki idanunta dara dara farare da suka wadatu da gashin gira, idan aka cire hassada mai wannan siffar ita ake kira da kyakkyawa, irin kyawun da duk wanda matarsa ta zama haka bazai rinka nisa da ita ba kuma na sani hikimar mahaifina kenan ta nema min aurenta, sai dai hikimar bata amfanar ba , domin ina tare da wadda ta dame ta ta sahnye, kyakkyawar da idan tana nan duk wata mai kyau ta kan dusashe
.
A zahiri na san yadda ake hira da masoyi sai dai ban san yadda ake hira da mutumin da bai da kima a rai ba, shiru nayi ina sake saken wani batun da bam, abinda na tabbatar zai jefawa 'yan matan shakku a rai, kuma a lokacin na tabbata fuskata ta nuna damuwar dana ke ciki
Kamar an watso su sai gasu suna nufo mu da gudu-gudu, bakake wuluk da su kamar tawagar tururuwa, gayyar irin yan kungiyar nan ne vigilante group (kato da gora) suna cikin motarsu kirar hyundai samfurin pick up (a kori kura) duk da cewa na san su wakilai ne na tashin hankali, wadanda. Lokacin dauke suke da manyan kwandunan takaici, sai na kasance cikin farin cikin zuwansu, ko shakka bana yi a yau din nan maganar auren zata ruguje, sai dai na tabbata duk wani mutunci da kima dana ke da su zasu bi hadarin kaka
.
Na kai idona ga nahiyar da liman yake zaune yana aikin jan carbi, nayi farin ciki dana ga cewa shima yaga zuwansu, ba shi kadai ba hatta ilahirin jama'ar dake rukunin hankalinsu yana kansu baya ga wata gayyar 'yan bin kwakwaf da sukaa biyo su da gudu ban yi mamaki ba a kauye dan kato da gora da dansanda duk sunansu daya
.
A guje yan matan suka nufi gida yayin da motar taja birki gab da mu, wata kura ta turnuke tamkar a fagen fama , suk kuwa ba su bata lokaci ba wajen durowa, kai kace wasu kwararrun sojoji ne da suka sami horo
"Yawwa shine, ga motar nan" lateef kenan wanda yake daure da ankwa, ala dole wai shi bakaniken mota ne,
Dajin haka sai nayi fitar burgu, ni ma gidan liman din na shiga,
"Ku tare shi, kar ku bari ya sha"
Zancen wani gabjeje kenan daga yan kato da goran, saidai ya makaro domin tuni na tsunduma aciki
"Ku ceceni zasu kasheni" wannan shine abin da nake fada. Banyi wata wata ba na nufi wani lungu dana ke zaton na ban daki ne, bayan dana yi fatali da wata kwaryar nono na kuma firgita agwagi, abinda ya sanya matan dake gidan fara salallami, iya kacin iya wata nake makyarkyata da kuma kumfar baki, harshena kuma yana furta na banu na lalace
.
Hakan sai ya sanya matan kasancewa cikin rudani bisa rashin sanin abinda ya firgitani, a wannan hali liman ya ba zamo cikin gidan da sauri, akwai gayyar yan kato da gora biyar biye dashi, na tabbata iznin shigowa suke nema, na fara kwalla ihu, ina shirin kama katanga, biyu ne daga cikin yan kato da goran suka rike min kafafu, jawo ni sukayi na fado kafin wani ya dubi fuskata ya yarfa min biyar, wani irin radadi gami da zogo suka keta fuskata naji kamar ance masu su dakata , to amma sai naci gaba da jurewa, ........
WAIWAI TOH FAH
YAU UMAR DAKANSA
YA YAYIMO KATON DUTSEN RIGIMA
DON TOSHE DUK WANI RAMI DA ZAI KAWO CIKAS A TSAKANINSA DA FARIDA
.
Nidinne dai shuraih Usman
Inkiya 99%
Kuyi like na shafinmu www.facebook.com/hausaebooks

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 2

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 2
.
.
Tayi shiru tsawon lokaci , daga bisani tayi karfin hali "umar zama bai same ni ba, dole ne muje dakai na roki arziki,in har aka daura maka aure,to farida kuwa shikenan"
Na girgiza kai "mummy ba zakije ba , zuwanki ba zai fa'idantar ba, nasan iyayena in sukace baki ba zasu canja da fari ba, ki bari ni zan samo mafita"
"A wadannan 'yan awoyi Umar?"
"Asu din kuwa , ina jin radadin raba ni da farida bazan jure ba zanyi duk abinda zan iya don ganin bata faru ba"
"To don Allah ka taimaka ga Allah nake dogara amma na san farin cikin 'yata na tattare da kai"
Na mike "kar ki damu zanyi fafutaka iya yina har komai ya faru yanda ake nema"
Itama ta mike muka kama hanyar fita daga asibitin a haka har gamu a titi, ta dafa kafadata "Umar haka ceci rai , ka tallafawa rayuwar marainiya"
Na gyada kai "Mummy zan yi"
***
Nayi shiru a shagona, cikin tunanin hanyar da zanbi na tarwatsa maganar aurena, shakka babu jan aiki ne wanda fasa goron dutse da cokalin roba zai fishi sauki, na sani a irin dattaku na mahaifanmu maganar fatar baki bata isa ta rusa auren ba, babu wata kalma da zata sanya mahaifiyna ya janye , idan haka ne to kuwa sai an yi amfani da hikima kenan, akan ce hikima ce da ni, in har ba karya ake yi ba to hikimar tayi aikinta.
Na fara sake-sake da warware-warware da ni masaki ne abunda na saka zai samar da katon gwado, wanda na warware kuwa zai samar da abawa kwarkwaro kwarkwarkwaro.
.
Haka na kasance , na saka da yawa na warware da dama, har ya zuwa lokacin dana sako wata badakala, na maida hankali ga nazari akanta sosai, hakika in har bukata ta shine a fasa aure to za fasa shi sai dai fa za a yi babban tashin hankali, na kuma bar wani katon tabo da zaici gaba da radadi a jikina, bayan na barwa dangi da yan uwana dalar gyadar bakin ciki da damuwa, wadda idan ba sa'a ba guguwar mutuwace kadai ke iya bajeta
.
Na mike tsaye cikin jin karfin guiwar na aiwatar da abinda zuciyata ke shaida min aikin ceton rai ne, na amince da uzurin data bayar amma fa dole ayi gyara, Anya akwai wani rai da zan je fa kaina wannan tashin hankali domin ceto shi, idan ka dauke ran wadda a halin yanzu zanyi don ita? Ba a saka iyaye wadannan layin su da bam, amsar dana samawa kaina ba a halicci ran ba, ashe kenan ceton soyayya zanyi bana rai ba, lallai jiki bawane zuciya kuma sarauniya sai dai so ita kanta sama yake da ita, yana juya ta ya sarrafa ta duk inda yaso, babu yadda zatayi dole ta yi biyayya ga duk hiron da yayi, komai dadi komai wuya, (ni Shuraih Usman Na jinjina ma sarkin Masoya
*****
Na dubi lateef cikin halin bijiro masa da bukatata bayan dana kwashe labarin rayuwata kaf na sanar da shi, ba don komai na yi haka ba sai don na sami duk taimakon dana ke nema
Yayi shiru yana jinjina lamarin daga bisani ya dago kai "hakika umar rayuwarka tattare take da rikici, kai gwarzo ne da har ka iya jurewa wannan tashin hankali, mai kwakkwalwa kamar ni ba zai jure ba , na tabbata da ni ne da tuni nayi watsi da ita, idan ma so ya hana ni, to zallar bakin ciki da tashin hankali zasu haukatani"
.
Na saurari duk abinda ya fada, na sani mutum dari tara da casa'in cikin dubu asu mara masa baya, sai sa'ar gaske goma su tsaya tare dani.
.
Ya katse min tunani "yanzu wane taimako kake bukata?"
Na gyara zama sannan na fara tsara masa duk shirin dana yi har na kammala baice kala ba, sai dana gama ya girgiza kai"ina ba zai yiwu ba, wannan wani tashin hankaline sabo , ne yiwuwa ma wanda duk ya zarce na baya muni, wai umar a hankalinka kake kuwa?"
.
Na gyada kai "kwarai kuwa, ina cikin cikakken hankalina, shin ba farar rigace dakai ba? Ka shigo dakinnan rike da bakin carbi, ko kuma wannan hular taka ba koriya bace"
.
Ya gyada kai "duk haka ne"
"To kagani ina cikin hayyacina, dole ce ta sanya ni tsarawa kaina haka a wannan lokaci da komai ya kure ita kadaice hanyar da zata fiddani, kai dai abinda nake so ka taimaka min da abinda na nema"
.
Ya kwantar da kai"to zanyi in har abinda kake bukata kenan, sai dai ina duba sakamakon da za'a samu a gaba, lamarin zai zame maka heater din dumama ruwa a cikin garwashin wuta"
Na daga masa hannu"kar ka damu da wannan idan ana sabo da bala'I nayi, kuma ka sani dare daya ya rage wa jemage, shine daren mutuwarsa"
Ya jinjina kai "zuciyarka ta kekashe ina shakkar a fasa aga bata canza ba daga zallar tsoka zuwa kashi"
Na mike tsaye "akan farida tafi hakanan, mulmulallen bakin karfene da wuta ke gazanar kashi"
****
Tun da muka dauki hanyar garinmu hira ta yanke mana, a motar lateef muke taxi da ya ke haya da ita, Ni ne driver yayin da shi kuma lateef ke sanye da kaya dukun dukun tamkar bakaniken da ko abu ya mutu zai iya tayar da shi, wannan shine shirin dana yi imanin zai yi min magani
.
Sai dai a wannan lokaci in har ana neman sarkin ganganci to lateef ne , daya san irin abubuwan dake kai kawo azuciyata da bai yarda naja shi ba, sam bana hayyacina zuciyar ta tafi ga tunani, karfe goman dare daidai nayi fakin a kofar gida a lokacin majalisar iyayenmu bata tashi ba, ina ganin yanda suka juyo gare mu banyi mamaki ba a duk rukunin babu mai mota sai hakimi, kuma shi kadai ya mallaki wayar sadarwa, wanda su da dama can mahaifinmu ke tafiya cin arziki izan yana son yayi magana da mu
Muka fito tare da lateef a hankali na nufi wajensu domin gaida su
.
Har kasa na zube duk na gaida su cikin girmamawa sannan na mike domin shiga gida
Mahaifina ya biyone a baya "kai tsaya"
Na dakata
Ya iso gareni, banga walwala a fuskar sa ba, ya kalli nahiyar motar "wannan kuma fa?"
Na fara murza yan yatsu "tawa ce baba"
"Kana nufin ka sayi mota"
Gyada kai nayi
"Yaya akayi yayanka bai fada min ba?"
Na sunkuyar dakai "ai yau na karbota, bashi nake bi aka biyani da ita"
.
Yayi nazari na tsowon lokaci daga bisani ya dora "wancan mutumin fa waye shi?"
"Bakanike ne"
"Bakanike kuma? Me ne ne fa'idar tahowa da shi?"
"Eh ina so ne yayi min gyara da safe"
Ya nuna ni da yatsa "kai umar duba nan karfa ka jawo mana bala'I muna zaune kalau, in har akwai cikakkiyar gaskiya menene na azarbabin tahowa da bakanike? Ba za kabar motar a can a gyara ba, sannan ka dauko, ka shiga taitayinka in har ka san bata ka bace ka gaggauta ficewa garinnan da ita, ka je ka mayarwa da masu ita a barsu, kar ka goga mani Kashin Kaji
.
Tambaya
SHIN WAYE ZAI IYA KINTATAR SHIRIN DA UMAR KE SHIRYAWA
.
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Domin dauko littatafanmu zuwa kan wayoyi da kwamfitarku a matsayin hausa-ebooks sai ku shiga nan kuyi like
Like:- www.facebook.com/hausaebooks

TARAR ARADU littafi na Uku 3 page 1

TARAR ARADU
Littafi na Uku 3
Umar lawan Abdul
Typing Shuraih Usman
Page 1
.
.
Na kara kiran sunanta tun iya karfi "farida" Amma shiru farida batako motsaba
.
Na rikice na kuma dimauce hankalina ya nemi gushewa tuni alamomin tambaya suka runtumo kaina shin me haka yake nufi? Farida suma tayi ko mutuwa? In har mutuwa tayi baga abunda zai hana na bita ba, na mike tsaye tsayuwar taki yiwuwa, sai na sake komawa na tsugunna
Bakina na kara a kunnenta na kara kiran sunan da karfi , shiru haryanzu bata canja zani ba, sai na fashe da kuka kukan da bazai taba zama magani ba, ban san adadin mintunan da na karar ba a wannan hali nidai na kiyasta awa ko fiye
.
Ana haka na jiyo takun kafafu ban iya tashi domin dubo ko wayeba bada jimawa ba sai gata a ciki, Mummy ta dawo tayi sallama bata yi ba nidai ban sani ba , ta dubeni a rikice "umar me ya faru?"
.
Rudun dana shiga gami da rikici mai kama dana tsufa suka sanya ne furta a zancen da ba shi ya kamata ba, dubanta nayi kai tsaye "ta mutu"
.
Ta dora hannu aka "ta mutu"
Eh! Nace mata ba a'a ba
Akwai tashin hankali ganin yanda matar ta fashe da kuka gaba daya "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, shikenan farin ciki yayi nisa dani 'yata daya jal dana kwallafa raina akanta ta tafi, Ya lillah"
Itama sai ta zube anan muka ci gaba da kukan tare , cikin rashin samun wanda zaiyi karfin halin lallashin wani, kimanin minti goma muna wannan hali, a sannan ne wani sauti ya fito kamar minshari, farida ce taja dogon numfashi, mummy ce tafara mikewa "umar suma tayi ba mutuwa ba"
.
Na tashi nima gami da matsowa kusa da ita numfashinta ya fara fita ahankali
Na dubi mommy "yaya za a yi?"
"Asibiti zamu tafi , titi da nisa kafin a dauko mota an bata lokaci gashi tana bukatar agajin gaggawa, da ina da cikakkiyar lafiya dana goyata"
"Ni zan goyata mummy sai mu tafi"
.
Ina maganar ne cikin halin zubar da hawaye.
Ta girgiza kai "farida tayi maka nauyi"
"Babu komai, lokaci yana kara kurewa"
Ta kimtsa ta sosai sannan ta taimakamin na goyata, muka fito daga gidan a gaggauce ga duk wanda ya ganmu dole ne ya tausaya mana.
Mu dai gamu muna tafiya cikin halin rudu, da sauri, ga kuma mara lafiya goye a bayana, Bakunan jama'a suka juri fadin Allah yabada sauki
.
Tafiyace mai nisa Amma banji alamun gajiya ba a haka har muka riski asibiti, muka sami motar da muka sakata
****
Na cigaba da kai kawo a dogon zauren asibitin zuciyata fal damuwa, sakamkon rashin sanin halin da farida zata wanye, daga lokaci zuwa lokaci nakan dubi mummy wacce ke zaune cikin tagumi, tun data zauna hawaye bai daina zarya ba a fuskarta,
Tsawon lokaci likitocin suna kanta, bayan abun daya tunkari awa biyu wata Nurse ta fito na ga sanda ta kira mummy take shaida mata wani abu
Na nufi wajen bayan da suka kammala
.
"Yaya akayi"
Ta share kwalla da gefen mayafi "cewa sukayi tana kan hadari, zai yi wuya ta iya numfashi da kanta yanzu, sai dai da taimakon na'ura"
Kaina ya sara da karfi hakika wannan wata hanyace ta nisa da rayuwa da yawa sun zarce a irin haka nan, me yiwuwa farida ma haka ce zata faru, kuma duk ni naja, da ban bata labari ba dayanzu tana nan kalu, kaito na!"
.
Mummy ta cigaba "umar inaga kakoma gida , awa ashirin da hudu suka ce zatayi"
Nayi karfin halin kai idona ga kallonta "to mummy izan na tafi wa zai rinka taimakawa"
Ta zurawa kasa ido kuri "ida wata ya wannan yanzu ma badon kai ba jigata zata yi sosai, umar biyanka sai dai mahalicci"
Na daga mata hannu " kar ki damu, na cancanci yin komai don farida na matukar lallabani"
.
Aka sami shiru na dan lokaci a cikin sane ma na sami damar yin tunani, sai yanzu alkawarin dana daukarwa mahaifina na komawa ayau ya fado raina, hakika babu makawa na cikashi, to amma ya kamata na tsallake na bar farida a wannan hali? Alhali idan nayi nazari zan ga cewa dukda ran da bani da lafiya bata nisa dani,
Na tuno yanda da kanta taje bakin bariki ta daukeni zuwa asibiti (karken littafi na daya 1,) na tuna yadda take kwana ta kuma yini a wajena ,batare da tunani ko tsoron afkuwar wani abu ba, kudadenta da lokutanta duk ta kashe a kaina, saini yanzu bata da lafiya sai na tsallake na barta da mahaifyarta saboda itace dolenta? Kai dasake akwai butulci zalla a cikin aikata hakanan, sai kawai na fashe da kuka,
.
Mummy ta dafa kafadata "umar sai hakuri na sani kana kaunar farida sosai mai yiwuwa ma fiye da ni, sai sauki idan Allah yayi hukuncinsa ya za'ayi?"
Na share hawaye "mummy bari wannan zance farida ba mutuwa zatayi ba, tana da sauran kwanaki"
Ta kwantar da kai "to Allah yasa hakanan dan idan farida ta mutu ban san inda zan saka kaina ba, na sani ko wace uwa tana kaunar danta, amma ni nasan kaunata da farida na musammance ba kowacce uwa zatayi ma danta kaunar da na ke yiwa farida ba, saboda ita naki aure shekaru sha shida kenan, domin ni bazan barta a wani waje ba, kuma ni bazan je da ita agolanci ba, karta rasa walwala da jindadi,
Me yiwuwa wata rana agoranta mata wanda da haka ya faru duk kimar mijin na rabu da shi"
.
Tausayin mummy ya kamani ni sai yanzu na san dalilinta na kin yin aure na dade ina ta yan kame-kame , kyakkyawar mace kamar ta da bata haura shekara talatin da biyar ba ace bata da aure shakka babu abin a duba ne
.
Na kara yin kasake ina tunanin wacce za a yi, hakika abubuwan da gazawata zata fito fil yawa ne da su, bazan auna a wajen farida ba kuma bazan dauki nauyinta kamar yadda take daukar nauyina ba, abun danake magani naira dubu shida suma daga kudin data yimin kyauta ne a baya, na fara kashe su a asibiti sai taci gaba da daukar dawainiyata,
Wani abun kuma ita kanta dubu shidan tana dakina anan na boye don gudun kada ta hadu da tsautsayi, in har ta halaka banga inda zan samu sisin kwabo ba
.
Na dubi agogon hannuna karfe biyar da minti hudu, hakika ya kamata nasan wacce za'ayi idan zaman zaman idan kuma komawa kauyen komawar
Na yanke shawarar tuntubar mommy sai na dubeta sa'ar data ke cikin tagumi
"Mummy ina mai bada hakuri nayi bakin ci da zan matsa daga nan sai dai babu yanda zanyi mahaifina nayiwa alkawari cewa lallai zanje yau kuma ga abinda ya faru"
.
Ta cira kai "kar ka damu kaje wajen mahaifinka umar yanzu ma abun da kayi ya isa Allah ya rabaka lafiya da su"
Na amsa "amin" sannan na ci gaba
"Mummy idan farida ta tashi ki shaida mata cea ta kwanatar da hankalinta ba zamu rasa juna ba, na tafi fafutukar sama mana mafita gobe-gobe zan dawo"
Ta kalleni cikin bkuatar karin haske" menene ya ke faruwa?"
Na sunkuyar da kai "babu komai"
"A'a Umar kar ka boye min , ka dauka cewa agare ka ina matsayin uwa"
Hawaye ya biyo kumatuna nasa hannu na share sannan na fara da cewa wani rikici ne ya bullo tsakani na da iyayena an kai masu labarin na zama dan iska shine suke so na koma can da zama kuma an nema min aure, wai jibi ma za'a daura shi, labarin naba farida ta shiga wannan hali
.....
Kai MALAM UMAR
Haryanzu fa akwai.......
.
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
.
Yi maza ku like na page namu www.facebook.com/hausaebooks
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter