Results

TARKON MUTUWA littafi na bakwai 7 complet

TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- Habibullah kbr
Post:- Shuraih Usman
Littafi na bakwai
Daga:- http://fb.com/hausaebooks

Part 7A
.
Lokacinda hatyan ya fadawa wadannan
dubunnan
manyan zakuna ya zamana cewa yana kai musu
sara
da suka ta ko'ina cikin bakin zafin nama da
jarumtaka
sukuma suka rinka kai masa mangari, cizo
yakushi suna yanyameshi, amma saboda zafin
namansa da tsagwaron jarumtakarsa sai suka
kasa samun nasarar yakusarsa shimaa kuma
duk da cewa yana makesu suna zubewa kasa
saiyaga sun taso zumbur sunci gaba da kawo
masa mugayen hare hare saida suka kusan
shafe rabin sa'a suna mugun artabu ba tareda
dayansu
ya sami nasara akan dayaba
awannan lokaci hankalin jarumi hatyan ya
dugunzuma
ainun saboda kaifi da tsini baya tasiri ajikin
zakuna kuma. ko kadan babu alamar gajiya
atareda zakunan kamar ko yaushe kara musu
kuzari akeyi, shikuwa saiya fahimci cewa idan
aka
cigaba da wannan fafatawa ahaka her izuwa
tsawon wani lokaci to tabbas zai iya jigata
zakunan su cimmasa amma babban tashin
hankalinsa shine batun 'yar uwarsa sadirat
da take kwance magashiyan acan gabar koramar
kuma baisan halin da take ciki ba
nan take hatyan ya aiyan a ransa cewa lallai
wadannan zakuna sihirtattune na musamman
idan kuwa hakane to turosu akayi musamman
don su kasheshi tareda 'yar uwarsa sadirat
babu wanda ke dauke da wannan alhakin
face sarki shamsal
tabbas wannan dayane daga cikin irin mugayen
tarkunan da sarki shamsal ya kafa musu
koda gama ayyana hakan
acikin zuciyarsa saiya fara tunanin hikimar
dazai yi amfani da ita wajen ganin ya gaggauta
kawar da wadannan zakuna dabara ta fadomasa
ya gane cewa saidaifa yayi amfani da tsagwaron
karfin
damtsensa da kuma dabarun fada saboda
yayi kokarin amfani da karfin sihirinsa na tsafi
yakiyin
amfani saboda ansha gabansa awannan fannin
acikin shammace gamida tsananin fushi sai
jarumi hatyan
ya shammaci daya daga cikin zakunan ya gabza
masa wawan naushi a idonsa guda daya
saboda
karfin naushin take ruwan idon zakin ya tsiyaye
zakin yayi tsalle sama yayi wata irin kururuwa
mai ban tsoro ya fado kasa tim
ya baje wanwar ko shurawar kirki baiyiba
koda
jarumi hatyan ya ga ya sami nasara saiya kamu
da tsananin farinciki kuma ya kara kaimi yaci
gaba
da bugun zakunan cikin zafin nama da jarumtaka
aikuwa nandanan yaci karfinsu ya bazar da sama
da guda dari shida tabbas idan kaji ana ki gudu
to sa gudune baizoba lokacinda zakunan suka
ga hatyan yana ragargazar 'yan uwansu suna
zama
gawa sai suka tarwatse suka kama gudu acikin
daji
dukkaninsu suna neman wajen buya
koda jarumi hatyan ya ga zakunan sun watse
daga wajen sunbar gawarwakin 'yan uwansu
birjik
saiya rugo da gudu izuwa inda sadirat ke kwance
da isarsa daf da ita sai ya durkusa yana shirin
tallafo
kanta kenan saiyaga ta bude idanunta ta dubeshi
cikin murmushin karfin hali
cikin tsananin farinciki yayi sauri ya cire wani
kyallen dake jikinsa ya daure raunin dake kanta
saboda her asannan raunin bai daina digar jini ba
sannan ya dauke ta da hannu biyu yakaita bakin
wani dutse yayi sauri ya bude jakar guzurinsa
ya fiddo magani ya shafa akan raunin nata
kuma ya bata tasha ta hadiya sau uku
faruwar hakan keda wuya sai taji karfin jikinta
asannan ne ta sake dubansa cikin murmushi
akaro na biyu tana mai gyara zamanta tace
yakai dan uwana nayi farinciki dana ganka
araye inda ace ka tafi ka barni bansan yadda
zan cigaba da rayuwaba, koda ta tsawon dakika
guda kuwa lokacinda sadirat tazo nan abayaninta
sai jarumi hatyan yayi murmushi yace
ai nine zance da
kin tafi kin barni bansan yadda zan cigaba da
rayuwaaba
babu mamaki hankalina ya gushe
nan take koma na hadiyi zuciya na mutu
saboda
bakin ciki tunda bani da sauran kowa aduniya
sai........
kafin hatyan ya gama fadin abindake bakjnsa
sai sadirat tayi sauri ta rufe bakinsa da tafin
hannunta tace karka fadi haka domin
inaji ajkina cewa
muna da sauran rayuwa awannan duniya
bazamu mutu ba harsai munga bayan makiyan
mu
alkawarine sai mun dawo birnin bindal
mun dauki fansa
akan sarki shamsal da dansa
yayinda sadirat tazo nan abayaninta sai farinciki
ya
lullube hatyan ya rungume ta akan kirjinsa
yana mai cewa, kinyi gaskiya yake 'yaruwata
lallai duk wuya duk rintsi sai mun cika burin mu
sadirat ta numfasa tace waishin yanzu menene
abinyi agaremu? shin zamu yada zango ne anan
tsawon wadansu 'yan kwanaki ko kuwa zamuci
gaba da tafiyane har mu riski garin dake gaban
mu
dajin wannan tambaya sai jarumi hatyan yayi
ajiyar zuciya sannan yace
yake 'yaruwata ci gaba dayin wannan tafiya
tamu ayanzu yana da matukar hadari saboda
akwai matsananciyar gajiya ajikina sakamakon
gwagwarmayar da nayi da wadancan sihirtattun
zakuna koda jin wannan batu sai mamaki ya
kama
sadirat tace yanzu kana nufin kace duk wannan
masifa da kuma shiga aiki ne na sihirine?
hatyan ya gyada kai yace kwarai kuwa kuma
wannan masifa somin tabi ce kawai abinda
nakeso dake kawai shine lallai ko yaushe ki
kasance kina tareda ni
kada ki kuskura ki rinka nisanta dani
koda
kuwa da tazarar taku ukuce
sadirat ta gyada kai tana mai nuna cewa zata
kula
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GASU
JARUMI HATYAN
BAYAN SUN SAMI NASARAR FITA DAGA CIKIN
NAHIYARSU
GABA DAYA INDA SUKA SHIGA SABUWAR
NAHIYA TA BAKAKEN FATA
Lokacinda tsoho lamzis ya fita ya bar boka
daizur
da sarki shamsal a zaune sai boka daizur ya
kasa fiddo madubin tsafinsa
kawai sai ya runtse idanunsa yayi kamar yana
bincikene, al'amarin daya fusata sarki shamsal
kenan
ya daka masa tsawa yayi firgigit kamar wanda
ya farka daka barci, sarki shamsal ya dubeshi
yace
kada ka bata mini lokaci abanza kawai ka dauko
madubinka ma tsafi ka binciko mana mugun
halinda su hatyan suke ciki tunda tuni mun
aika musu da zakunan sihirin da zasu hallakasu
aduk inda suke
koda jin wannan umarni sai boka daizur yayi
sauri
ya zura hannunsa acikin aljihun wandonsa
jikinsa na rawa ya fiddo madubin ya ajiye shi
agabansa cikin matukar karfin hali kuma
zuciyarsa
na daka ya dora tafin hannunsa na hagu akan
madubin ya shafeshi, ba zato ba tsammani
sai boka daizur yaga madubin nasa ya washe
daga duhu zuwa haske nan take saiga hoton
duk abinda ya faru gasu jarumi hatyan nan
acikin daji da yadda hatyan ya fafata da
wadannan
zakuna harya kashe wasu da yawa daga cikin su
koda gama ganin abinda ya faru sai fuskar
sarki shamsal ta kama gyatsine saboda tsananin
fushi ya kasa cewa uffan harsaida boka daizur
ya shafi madubin tsafin nasa yayi baki sannan
ya dubeshi yace
yanzun nan zamuyi shiri mubi su jarumi hatyan
izuwa wannan nahiya da suka shiga ta bakaken
fata
lallai sai mun cimmasu nayiwa hatyan da 'yar
uwarsa kisan
gilla, kodajin wannan batu sai idanun boka daizur
suka zazzaro ya dubi sarki shamsal cikin
matukar firgici
yace
haba ya shugabana shin ka mantane cewar
yana daga cikin dokokin magabatanka cewa
jininku baya shiga wata nahiyar?
idan kuwa ya shiga bazai dawoba araye
kuma
saiya rasa komai da kowa arayuwarsa
idan her kabi su hatyan
waccan nahiyar bazaka taba cika burinka ba
akan sa kuma ba zaka koma birninka na bindal
ba
abinyi kawai shine muci gaba da tura musu
mugayen tarkunan da basu isa su iya tsallakesu
ba
komai sa'arsu da nasararsu lokacinda sarki
shamsal yaji wannan bayani na boka daizur
sai hankalinsa ya dan kwanta ya sunkwui da
kansa
kasa yana mai tunani da nazari daga can
saiya dago da kansa ya dubeshi yace
jiya da daddare lokacinda muka dan runtsa
nayi wani mafarki daya dan sosa mini rai lallai
akwai wani bakon abu dayake faruwa abirnin
bindal
inaso ka duba mini yanzu domin muga ko
menene
abinda ya faru bayan tafiyar mu
koda jin wannan batu sai boka daizur yaji
zuciyarsa
ta buga da karfin gaske, al'amarin daya sa shi
kansa
ya firgita kenan kuma ya kamu da tsananin
mamaki
domin bai san dalilin dayasa yaji tsoro ya
shigeshi ba
amma saiya dubi sarki shamsal cikin murmushi
yace
haba ranka ya dade yanzu her akwai wani abu
wanda zai faru abirnin bindal ya baka tsoro
aiko ma menene da zarar mun koma zamu
kawar dashi cikin dakika daya
kafin boka daizur ya gama rufe bakinsa, tuni
sarki shamsal
ya tari numfashinsa yana mai cewa
ai dan hakkin daka raina shike tsone maka ido
irin wannan sakacin nakane yasa hatyan ya
wanzu abinrnin bindal
ba tareda mun sani
boka daizur ya rissina yace
hakika abinda ka fada gaskiyane
amma ka sani cewa taura biyu bata taunuwa
alokaci daya domin hankalinka zai iya rabuwa
biyu
idan kuwa ya rabu ana samun rashin nasara
zaifi kyau mu gama da matsalar su hatyan
domin tafi kowacce matsala hatsari
sa'adda sarki shamsal yaji wannan batu saiyaja
dogon
numfashi gamida ajiyar zuciya sannan yace
yanzu menene mugun abu na biyu wanda zamu
turawa su hatyan lallai inason su hallaka kafin
su isa wannan babban birni dake gabansu
wanda ake kira da suna birnin kanyasi
.
http://keffiansonline.cf/littatafan-hausa/tarkon-mutuwa-littafi-na-bakwai-7-part-a

Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99% ke posts
Daga taskar:- Shuraih 99%


TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- Habibullah kbr
Post:- Shuraih Usman
Littafi na bakwai
Part 7 B
.
Kodajin wannan batu sai boka daizur ya bushe da
dariyar
mugunta sannan yace ya shugabana abinda
zamu tura musu bakomai bane face uwar
macizan duniya
na rantse da darajar gemun uban koda za'a tara
irinsu jarumi hatyan guda dubu masu irin sa'arsa
da
karfinsa da jarumtakarsa sai wannan macijiya
ta hallakasu farat daya ba'a tabayin macijiya
mai girma, karfi da mugun hadariba aduniya
tun daga farkon wanzuwar duniya kawo iyanzu
kamar uwar macizai ba
nine kadai zan iya fito da wannan macijiya
daga cikin kogin da take zaune sama da shekaru
dari uku da talatin domin akwai kalmomjn tsafi
na musamman da za'a iya kiranta dasu
kuma na gajesune daga wajen kaka na na bakwai
kodajin wannan batu sai mamaki ya kama sarki
shamsal
yace, yakai dirkar birnin bindal nifa karamin yaro
nakejin labarin uwar macizan duniya awajen
iyayen da kakannina, ance in da zata mikar da
tsawonta
yakai kamu dubu ashirin kuma kaurinta yakai
na katuwar bishiyar kuka sannan babu wani
kwaro ko dabba mai karfin gudunta bisa doron
kasa
domin tana iya zuwa birnin sin daga birnin kisra
acikin sa'a shida da rabi tana shekara goma
sha daya akwance tana barci ba tareda ta bukaci
abinci ko ruwa ba amma da zarar ta farka daga
barci
na tsawon shekaru goma sha daya sai ta cinye
dabbobi kimanin guda goma dubu masu girman
rakuma sannan take koshi, ruwa kuwa idan ta
kafa kanta
bakinta abakin karamar korama tana iya zuketa
kaf acikin 'yan dakiku masana tarihi sun tabbatar
da cewa sau daya wannan macijiya ta taba
baiyana aka ganta sa'adda tayi tafiyar kasa
daga birnin kisra zuwa sin ance awannan
shekara
duk wani gini dake cikin biranen biyu saida
suka rushe, duk inda ta shafa da jikinta saidaya
haifar da rami mai zurfin kamu dari gamida
fadin kamu arba'in, tekuna da koramai da
fadamai
saida suka rika ambaliya suna hadewa da
junansu
bishiyoyi sai da suka kakkarye guda daya bata
tsayaba
duwatsu kuwa fashewa suka dinga yi suna
bindiga
saboda azabar zafin wutar dake fita daga cikin
bakin uwar macizai
kai atakaice ance wannan macijiya ita kadai zata
iya hallakar da duniyar nan duk acikin kwanaki
da basu wuce dubu da dari uku ba, ita dai
wannan
macijiya an tabbatar da cewa babu wata halitta
a wannan duniya mai karfin ta kuma babu wani
makami
dazai iya daran jikinta ko ya hudata
taya zaka iya fito da wannan macijiya alhalin
ance
sau daya ta taba fitowa tun azamanin kakana na
bakwai
yau shekara dari da ashirin kenan?
tabbas inda zaka iya fito da itaka turawa su
hatyan da 'yar uwarsa
to tabbas na yarda cewa zata hallakasu
acikin
dakika daya jal koda kuwa sunfi kowa sa'a da
tsawon rai
lokacinda sarki shamsal ya zo nan azancensa
sai boka daizur ya bushe da dariyar mugunta
cikin nuna isa gami da yarda da kansa sannan
ya dubi sarki shamsal cikin nutsuwa yace
ya
shugabana tabbas zan nuna maka cewa
ni
bokane, dan boka kuma jikan boka lallai zaka
san cewa babu wani boka acikin duniyar nan
da yakai ni karfin sihiri
koda jin wannan batu sai sarki shamsal ya bushe
da dariya sannan ya dubi boka daizur a
wulakance
gami da rainin wayo yace
hakika ku bokaye akwaiku da kuri kuma kun iya
zabga karya ko kunya bakwaji ,shin ka mantane
cewar abaya
sarkin mafarauta ya gagareka ka kasa hallakashi
da karfin sihirin tsafinka saida ka shammace shi
ka jeho shi kasan wannan rami mai tsawo?
yayinda boka daizur ya ji wannan batu sai yayi
murmushi yace
ya shugabana hakika abinda ka fada gaskiyane
amma inaso ka sani cewa kowanne mutum
yana da irin baiwarsa komai karfin sihirinka
kuma komai jarumtakarka bai zama dole ka zamo
mai sa'a
da nasara ba acikin al'amuranka ba kai da kanka
yanzu matsalar da kake fuskanta kenan akan
wadannan makiya naka gashi dai kafisu karfin
sihiri dana damtse amma gashi sun gagareka
saboda sun kasance masu sa'a koda boka daizur
yazo nan azancensa sai jikin sarki shamsal
yayi sanyi kuma yayi shiru tsawon 'yan dakiku
kadan baice komaiba daga can saiya dago kansa
ya dubi boka daizur yace inason naga uwar
macizai
a zahiri amma kafin nan ka nuna mini ita a
madubin tsafinka
a shekarar data fito daga kogonta dake birnin
kisra taje birnin sin
nikam inason naga abubuwan da suka faru
sakamakon fitowar ta awannan lokaci
sa'adda boka daizur yaji bukatar sarki shamsal
saiyayi doguwar ajiyar zuciya ba tareda ya kara
cewa komaiba ya fito da madubin tsafinsa
ya ajiye shi agaban sarki shamsal ya shafeshi
da hannun hagu, dajine mai matukar kwarjini
saboda yanayinsa
ya fita daban dana sauran dajijjikan duniya
abinda yafi yawa wannan daji shine manyan
tsaunika
da koguna, da kuma ramuka masu zurfin gaske
da fadi su kansu bishiyoyin wannan daji na
musamman ne
irin wadanda idanuwa basu saba gani ba
kawai
sai dajin gaba daya yayi girgiza, bishiyoyi suka
rinka tunbukowa daga cikin karkashin kasa
da kansu suna zubewa kasa
duwatsu kuwa komai girmansu sai gashi suna
mirginawa
da gudu suna karoda 'yan uwansu da sauran
bishiyoyi
al'amarin daya firgita dabbobi da tsuntsaye kenan
suka kama guje guje da iface iface, tsuntsayema
ba shiri suka rinka sauya sheka amma duk da
haka basu tsiraba
sai dai kaga suna fadowa kasa matattu saboda
wani irin huci mai zafin tsiya da yake fitowa daga
jikinta ya mamaye sararin saman, ba komai ne ya
haddasa hakanba face fitowar uwar macizai
daga cikin kogon da take boye, shikansa kogon
dutsen
da farko saiya kama tsatstsagewa ,uwar macizai
na motsa jikinta saiya fara rugujewa kafin ta
gama fitowa daga kogon ya gama rushewa
gaba daya ya baje kasa
tana yin tafiya ne akan kasa dajin gaba daya ya
hautsine
koda sarki shamsal yayi arba da kan uwar
macizai
acikin madubin tsafin boka daizur yaga tsananin
girmansa kuma yaga kaurin jelarta da tsawonta
saiya firgita ainun baisan sa'adda yadan ja da
baya ba
domin gani yayi kamar zata faso madubin tsafin
ta lankwameshi, ashe boka daizur ya ga yadda
ya tsorata daizur bai san sa'adda dariya ta
kwace
masa ba shikuwa sarki shamsal saiya dake
kuma ya murtuke fuskarsa yana maici gaba
da kallon madubin tsafin abinda y kara daurewa
sarki shamsal kai shine ganin yadda macijiyar
takeyin azababben gudu akan kasa tamkar
an harbo kibiya
cikin dakiku kadan ta fice daga cikin wannan daji
take ta fara shiga birane duk garin data ratsa
saidai kaga ana girgizar kasa, mutane na hallaka
gidaje na rushewa kuma gobara ta dinga tashi
haka dai macijiyar tayi ta haddasa bala'i a duniya
ta rinka baje kasashe harsaida ta isa birnin sin
ta fada cikin wani teku sannan komai ya lafa
masana tarihi da masu bincikesun tabbatar da
cewa
ba'a tabayin annobar mutuwa ba aduniya kamar
wannan lokaci
da uwar macizai ta bayyana
lokacinda sarki shamsal ya gama ganin al'amarin
uwar macizai
WAI IDAN AGASKENE TAYAYA ZAKA TSIRA IDAN
KA HADU DA WANNAN MACIJIYA A INDA KAKE
ZAUNE KO KUMA ME ZAKAYI MATA? DAGA
HABIBULLAH KBR
acikin madubin tsafin boka daizur saiyaja dogon
numfashi
gamida ajiyar zuciya kuma sai nan take ya kamu
da Tsananin farinciki ya dubi boka daizur yace
na rantse da darajar kabarin kakana idan har ka
iya fito
da wannan macijiya daga ccikin tekun da ta
shiga
ka aikata izuwa su hatyan acikin dakika daya jal
zata
hallakasu kodajin wannan batu sai farinciki ya
turnuke boka daizur ya kyalkyake da dariyar
mugunta
alokacinda ya sake shafar madubin tsafin da
tafin
hannunsa yayi duhu daga haske kuma ya dauke
shi
ya sashi a aljihunsa boka daizur ya dubi sarki
shamsal cikin nutsuwa gamida alamun damuwa
sannan yace ya shugabana fito da wannan
macijiya
abune mai sauki tamkar cire silin gashi daga
cikin tandun mai amma fa akwai wata matsala
guda daya, kodajin haka sai shamsal ya dubi
boka daizur yace
menene matsalar?
daizur yayi ajiyar zuciya yace idan wannan
macijiya
ta fito awannan karon sai anyi asarar rayuka
ninki ukun wanda akayi a wancan zamani sannan
kuma wannan masifa zata iya shafar birninka
na bindal babu mamaki ma ta shafi danka da
matarka
kodajin wannan batu sai sarki shamsal ya bushe
da
dariyar mugunta lokaci guda kuma
sai ya turbune fuskarsa yace
nifa akan biyan bukatata ran kowa da komai
ba agabana yakeba kawai ka fito da wannan
macijiya
kodajin haka sai mamaki ya kama boka daizur
amma sai yayi shiru baice kalaba

http://keffiansonline.cf/littatafan-hausa/tarkon-mutuwa-littafi-na-bakwai-7-part-b

Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Jamuje jagoran posting


TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- Habibullah kbr
Post:- Shuraih Usman
Littafi na bakwai
Part 7 C
.
ACan kuma dajin da su hatyan suke kuwa
bayan
sun gama tattaunawa sai suka kafa tanti suka
shiga ciki suka zauna bayan sun bude jakar
guzurinsu
sunci sun koshi sai suka kwanta suka kama barci
abinsu tamkar acikin gidajensu suke, abinka
da gajiyayyu nantake barci ya dauke su
basu suka farka ba
saida gari ya waye hasken rana ya bugo cikin
tantin
sadirat ce ta fara farkawa koda taga hatyan
yanata faman
shara barci abinsa bashi da niyyar farkawa ma
saita mike tsaye ta fito daga cikin tantin
da fitowar ta saita kama
kalle kallen dajin inda ya bata sha'awa matuka
saboda
kyawunsa da ni'imarsa wacce ta bambanta ainun
da irin dazuzzukan dake nasu nahiyar
abinda ya kara
burgeta shine ko kadan babu sanyi awannan
nahiyar
wanda zai dami mutum sai wata irin iska mai
dan karan dadi dake busawa
sadirat ta daga hannayenta biyu ta mike
gami da hamma
tajin yunwa sannan sai ta fara tafiya acikin dajin
tana maici gaba da tafiya acikin dajin tana mai ci
gaba da kallon bishiyoyi, furanni da koramai
masu yayewa dukkan bakin cikin ta ahakanne
sadirat tayi dan nisa da inda tantin su yake
bata saniba harta iso bakin wata korama mai
ban sha'awar gaske itadai wannan koramar
ruwan dake zubowa cikinta daga kan wani dutse
yake zubowa kuma ruwane garai garai mai
haske da sheki da haske hartana iya ganin
fuskanta
akan ruwan tamkar madubi koda ganin wannan
koramar sai sadirat taji babu abinda takeso
sama da tayi wanka acikin wannan koramar
amma kuma sai tsoro ta kamata tace acikinta
ya za'ayi na kwabe kayana acikin wannan daji
na shiga wannan korama alhalin bansan
abubuwan
dake cikinsa ba kuma bansan abinda ka iya
zuwa mini ba na bazato gama ayyana hakan
keda wuya
sai ta kama dube dube da leke leke saida ta
duba gabas da yamma kudu da arewa kuma ta
duba
sama da kasa amma bataga komai ba kuma
batajin motsin komai ba koda kuwa na kwaro
ko tsuntsu kuma bataga alamar sawun wata
halitta ba
hakanne yasa zuciyarta tayi sanyi taji ta sami
nutsuwa da kwanciyar hankali ba tareda fargaba
ba
saita kwabe dukkanin kayan jikinta ta rataye
su ajikin wata koramar ta shiga cikin koramar
ta kama yin wanka abinta…
tsawon 'yan dakiku tana cikin hakan ba tareda
fuskantar wata
matsalaba sai kawai tajiyo muryoyin wasu
mutane
daga bayanta suna magana cikin wani yare
wanda bata taba jin irinsa ba arayuwarta
cikin firgici sadirat
ta juyo kuma ta yunkura da nufin ta fito da gudu
daga cikin koramar amma sai taga ashe tuni
mutanen sun iso kusa da ita
samari ne matasa su uku dukkaninsu bakaken
fata ne
wanda ke tsakiyarsu yakasance dogo wankan
tarwada domin bashi da duhun fata kamarsu
kuma dole asashi a sawun kyawawa da gani ba
tambaya
yanayin shigar da yayi ya fito daga gidan sarauta
irin na wannan nahiya domin rigarsa da
wandonsa
masu tsadace kuma ya daura sarkar lu'u lu'u
awuyansa
yana da yalwar gashi tamkar mace wanda ya
tattare shi
ya daureshi agadon bayansa riger tasa mai
yankakken hannuce hakanne ya bayyana surar
jikinsa
irinta sadaukai mai tarin kwanji, murdewa, su
sukuwa rahowar
matasan dake tatedashi shiga sukayi irinta
dakaru
kai da gani kasan cewa masu tsaron lafiyarsa ne
kowannensu na ruke da takobi da garkuwa
kuma suna sabe da kwari da baka abayansu
shikuwa wannan dan sarki babu wani makami
ajikinsa face kwari da baka
ga dukkan alamu dai farauta ce
ta shigo dasu cikin wannan daji
koda wadannan samari uku sukayi arba da
sadirat
acikin wannan koramar sukaga tsananin kyanta
kuma sukaga launin fatarta ba irin tasuba saiduk
suka firgita suka ruga izuwa bayan wata bishiya
suka buy suna leke atsakaninsu da ita itadai
sadirat
so take ta fito daga cikin koramar ta ruga izuwa
inda
ta rataye kayanta ta dauka ta sanya amma
saboda kada suga tsiraicinta shiyasa ta kasa
fitowa
su kuwa tsammani sukayi aljanace ba mutumba
domin basu taba ganin mace mai kyan sadirat ba
ana cikin hakane idanun dan sarkin suka kaikan
bishiyar da sadirat ta rataye kayanta
koda tag suturarta sai ya gane tabbas wannan
mutum ce ba aljana bace
domin inda aljanace zata iya dauko kayanta da
kanta daga inda take ta suturce jikinta
koda gama ayyana haka sai dan sarkin ya kamu
da tsananin mamaki ya
sake tambayar kansa yace
to tayaya akai tazo nan kuma daga ina tazo?
ko kuwa aljanune suka satota daga wata nahiyar
duniya suka kawota nan?
saboda son jin amsar wadanan tambayoyi
sai dan sarki ya fito daga bayan wadannan
bishiyar da suka buya ya tunkari inda sadirat take
koda sadirat taga dab sarki ya durfafota saita
firgita ainun tayi zaton ko shima mai irin halayyar
yarima zainur
ne wato so yake ya lalata mata rayuwa
nantake sadirat ta takarkare ta kwarara uban ihu
mai karfin gaske, aikuwa sai iska ta dauki sautin
ihunta ta kaishi
har cikin kunne jarumi hatyan wanda ke kwance
acan cikin tanti yana faman sharar barci
kamar an saceshi
nan take hatyan ya farka adimauce azatonsa
mafarki yakeyi
amma saiya sake jiyo sautin ihun sadirat daga
can nesa hatyan ya mike tsaye zumbur ya fito
daga cikin tantin
aguje ya nufi bangaren da yake jiyo ihunta
wohoho! mai abu da abinsa kura da kallabin kitse
nanta hatyan ya dinga falfala azababben gudu na
masifa
irin wanda bai taba yiba arayuwarsa
domin aduniya babu
abinda daya tsana sama da abinda zai taba
lafiyar
wannan 'yar uwa yasa al'amarin wannan dan
sarki kuwa lokacin dayaga sadirat
ta firgita dashi
ta kama ihu sai ya fara yi mata magana cikin
yaren sa yana cewa
ni ba cutar dake zanyiba tambaya zanyi miki
abinda ya manta shine ai batajin yarensa da yaga
ta rude
sosai sai ya nufi inda ta rataye kayan nata ya
daukosu
da nufin ya kaimata ta suturce jikinta
koda ya tunkareta yana murmushi ita kuwa tana
mai ci gaba da kwalla ihu saikawai suka jiyo
sautin gudu abayansu
shida dakarun nasa
kafin suyi wani yunkuri tuni jarumi hatyan ya
gabzawa wadannan dakarun naushi
afuskokinsu
suka zube kasa alokacinda jini yayi fitar burgu
daga cikin bakunansu, suka baje sumammu
kuma ya dako tsalle a sama ya daki kirjin dan
sarkin da kafarsa
dan sarkin yaja da baya kadan yayi baya taga
taga
amma saiya tsaya kyam yana ruke da suturar
sadirat
suka fara kallon kallo da hatyan
su kansu sunyi matukar mamakin yadda suffer
jikinsu da tsawonsu yazo daya
shida h
hatyan su kansu sai da sukayi mamakin yadda
tsawonsu
yazo daya kamar hassan da hussaini banbancin
kawai shine
sun banbanta alaunin fata da kamannin fuska
kai da ganin irin kallon da suke yiwa junan nasu
kallone na shakkar juna itadai sadirat saita
sakeyin
kasa cikin ruwan koramar ta takure jikinta da
hannayenta
don boye jikinta
al'amarin daya fusata hatyan kenan bisa ganin
yadda dan sarki yaci gaba
ruke suturar sadirat ahannunsa kuma ya kura
mata ido kawai sai hatyan ya sake dako tsalle
asama ya kawo masa wawan naushi a fuska
cikin zafin nama dan sarkin ya sunkuya hannun
hatyan ya naushi iska
nanfa suka kachame da masifaffen yaki suka
wanzu
suna masu kaiwa junansu naushi da bugu
hannu da kafa suna kokawa ,wannan ya dan
wancan wancan ya danne wannan
nanfa mamaki ya turnuke sadirat domin kawai
gani tayi karfinsu yazo daya
da zarar daya daga cikinsu ya naushi daya say
kaga shima dayan ya rama daidai yadda akayi
masa
saida suka shafe lokaci mai dan tsawo suna
wannan artabu ya zamana cewa sun hadawa
kansu jini
da majina amma babu wanda ya sami nasara
akan abokin gwaminsa kuma her asannan
wadannan dakaru biyu na dan sarki basu
farfadoba daga suman d sukayi
kuma suturar sadirat tana hannun dan sarkin

Nidinne Shuraih Usman
Inkiya 99%
Jagoran posting na wannan Gida Lamba daya 1
A gaba dayan duniyan fcbk

Ko da kwai mai jane akan wanga batu nawa

TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- Habibullah kbr
Post:- Shuraih Usman
Littafi na bakwai
Part 7 D
.
Hatyan yaga wankan hula zai kaisu dare saiya ja
da baya ya zare takobinsa yana mai gyara
tsayuwarsa ko daganin haka sai dan sarki ya
dakatsalle izuwa inda dakarunsa suke kwance a
kas ya fisgo takobin daya daga cikinsu ,ya zareta
kuma shima ya gyara tsayuwarsa a wannan
lokacine ta razana ainun domintasan cewa
wannan gumurzu bazai yi kyau ba.
matasan biyu zasu iya cutar da juna sun rugo da
gudu izuwa kan junansu sunt ruguntsume da
sabom masifaffen yaki.
kaico! yaro in baka yi bani wuri wanda ya iya ya
huta kuma wahala sai jurarre, ba jinta sai kwarre
,lokacin da wadannan matasa biyu suka cakuma
da yaki ya zamana cewa suna kai wa junansu
sara da sukacikin bakin zafin nama juriya da
bajinta sai hankankalin sadirat ya dugunzuma
ainun fiye da ko yaushe domin yaki ne mai
mugunhadari da ko yaya aka sami kuskure zasu
iya yin ragas ko kuma dayansu ya sheka
barzawu.
saida suka shafe kusan rabin sa'a
suna wannan gumurzu kuma kowannensu
yana yakine da dukkan karfinsa kuma afusace
duk wanda aka kawowa
sara ya kauce ana samun bishiya saidai kaga an
rabata biyu
komai kaurinta saboda karfin saran
a tsawon wannan lokaci babu wanda ya sami
nasarar
koda lakutar jikin daya bisa dole kanwar naki
suka ja d baya
taku biyar biyar sukayi cirko cirko kamar zakaru
saboda tsananin gajiya kamar hadin baki sai da
kowannensu
ya buda hannayensa kuma suka daga takubbansu
sama suka ruke hannayensu biyu
kawai sai suka rugo da gudu izuwa kan ju
na
cikin tsananin fushi gami da mugun nufi kai da
gani
kasan cewa indai akayi wannan gamo dolene
labari yasha banban kodai su yi ragas ko kuma
dayansu ya sami nasara akan dan uwansa
saura baifi taku biyuba kacal su hadu kawai sai
sadirat
ta kurma uban ihu hakanne ya janyo hankalinsu
suka sauke takubbansu suka dubi inda take
kawai kura musu idanu tayi tana karkarwar jiki
sakamakon iskar data fara kadawa mai sanyi
acikin dajin
koda ganin haka sai dan sarkin ya cilla mata
tufafin nata
t cafe sannan ya juya mata baya ganin hakanne
yasa jikin hatyan yayi sanyi ya mayar da
takobinsa cikin kufe
a lokacin d shima ya juyawa saditammrat baya
tana sanya
suturar tata shima dan sarkin ya yi jifa da tasa
takobin
sannan mikawa hatyan hannu suka gaisa
cikin alamun rashin yadda
hatyan ya bashi hannunsa suka gaisa
adaidai wannan lokacin ne dakarun dan sarki su
biyu suka
farfado daga dogon suman da sukayi suna bude
idanunsu
sukaga shugaban nasu da hatyan suna gaisawa
saisuka kurawa juna idanu suna mamaki aka
rasa wanda zaice wani abu,
alokacin ne sadirat ta kammala sa suturarta
ajikinta
ta fito daga cikin koramar ta taho daf da hatyan
ta tsaya
suma wadannan dakaru biyu sai suka matso
dafda shugabansu
suka tsaya kwatsam ba zato ba tsammani sai
dan sarki yaji hatyan ya budi baki
cikin irin yarensa yace
yakai yarima nasmal da ga sarki damhas kayi
sani cewa
tuni abaya maigidana sarkin mafarauta na garin
mu
ya bani labarin ku kuma ya koyar dani yarenku
tun ina yaro karami domin abinciken da yayi tun
asannan
yasan cewa nan da wasu shekaru zanzo
nahiyarku
ya gaya mini cewa ya taba zama a cikin wannan
acikin wannan babban birni naku na tsawon
shekaru uku
tabbas zaka gasgata zancena idan na nuna maka
wani abu yanzu duk da cewa kana yaro karami
sa'adda mahaifinka ya baiwa sarkin mafarauta
wannan abu
lokacin da hatyan yazo nan azancensa sai
sadirat
da wadannan dakaru suka cika da mamaki domin
basu taba zaton cewa hatyan
ya iya wannan yareba shima yarima nasmal sai
murna
da mamaki suka kamashi ya dubi hatyan cikin
murna da murmushi
yace
shin ku mutanen wani gari ne wanda ake kira da
suna bindal?
hatyan ya gyada kai alokacin daya bude jakar
guzurinsa
ya fiddo wani hatimin sarauta wanda akayi shi da
karge zagayayye mai dauke da zanen
tsuntsu da kibiya wanda ya kasance alamace ta
masarautarsu
ya mikawa nasmal cikin tsananin mamaki nasmal
ya karbi
wannan hatimin ya kalleshi dakyau
nantake fuskarsa ta fadada da murmushi kuma
ya kamu da farinciki kawai saiya rungume hatyan
yana mai sumbatarsa
tamkar wanda yaga wani dan uwansa na jini
wanda ya dade basu haduba cikin hanzari da
mamaki gami da dan fishi hatyan ya janye jikinsa
daga jikinsa yace
menene ma'anar wannan farinciki naka?
maimakon nasmal ya baiwa hatyan am sar
wannan tambaya da yayi masa
saiya dubi wadannan dakaru nasa guda biyu yace
maza ku koma gida ku sanar da sarki cewa
jarumin da muke jira yazo
yayi maganin masifar da muke jira ya iso ina tire
dashi a daji
yana gama fadin hakan sai nasmal ya dubi
hatyan yace
waccan yayarka ce ko kuma gudun hijira kukayo
daga waccan nahiyar
dajin wannan tambaya sai hatyan ya gane cewa
lallai wadannan mutane
suma manyan matsafa
don haka kawai sai ya gyada kansa alamar cewa
hakanne
nasmal yayiwa sadirat wani irin kallo mai dauke
da alamar tambaya
wanda yasa nantake taji zuciyarta ta buga da
karfi
akaron farko arayuwarta a tsakaninta da da
namiji
nasmal ya juya ya dubi dakarunnasa biyu yace
me kuke jirane tun dazu na baku umarni baku
tafiba
dajin wannan tambaya sai daya daga cikinsu
ya budi baki da kyar muryarsa na rawa yace
ya shugabana yanzu idan muka koma gida babu
kai me kake zaton sarki zaiyi mana?
zai iya zaton cewa cutar dakai mukayi yasa
akashe mu
ka sani cewa munyi rantsuwa akan cewa zamu
tsare rayuwarka
da lafiyarka kuma duk runtsi bazamu dawo gida
babu kaiba
sa'adda yarima nasmal yaji wannan batu sai yayi
murmushi
sannan ya mikawa daya daga cikinsu wannan
hatimin sarauta yace
kuna isa gida ku baiwa sarki wannan hatimin
kuma ku gaya masa sakon dana baku farinciki
zaiyi yasa ayi muku goma ta arziki
kodajin haka sai farinciki ya lullube dakarun
suka juya da baya suka ruga izuwa cikin daji
nasmal ya juyo ga hatyan ya sake yiwa sadirat
irin
wannan kallo da yayi mata abaya sannan ya dubi
hatyan yace
nasan akwai tambayoyi abakinka agareni ka
fadesu naji
hatyan ya yi dab guntun murmushi yace
kafin na fada maka tambayoyina
zan baka shawara guda daya
zaifi kyau ka nisanci 'yar uwata domin mallakarta
ko mallakar zuciyarta daidai yakeda tunkarar
mayakan duniya duka
'yar uwata bata taba son wani da namijiba domin
zuciyarta
batasan komaiba face son iyaye da yi musu
hidima
tundaga kuruciyarta zuwa girmanta na tsani naga
wani da nimiji ya kusanceta
sai saboda tsoron kada ya siye zuciyarta ya
aureta
domin idan ya aureta dolene ya rabani da ita
alhalin bantaba rabuwa da itaba daidai da rana
daya ba tun daga girmana kawo zuwa yanzu
sa'adda hatyan yazo nan azancensa sai yarima
nasmal ya bushe da dariya
sannan ya dafa kafadarsa yace
nayi murna daka gane cewa na kamu da son 'yar
uwarka
farat daya kuma nayi murna daya kasance
batajin wannan yare da mukayi
na ruki alfarma daya daga gareka da kada
kasanar da ita abinda muka tattauna yanzu
amma ka sani cewa ta sace zuciyata kamar
yadda ka sace zuciyar
badi'atul nauwara da sarauniya anisa haka itama
'yar uwarka ta sace zuciyata
idan son masoyi laifine to kafara tambayar kanka
meyasa kake begen badi'atul nauwara da anisa
kuma ka tambayi kanka yadda zakayi da
soyayyar 'yan mata
biyu alokaci guda.
tabbas zuciya bata da kashi kuma shi so
barawone
baya sallama bare asan sa'adda zai shigo gida
atsayar dashi
lokacin da yarima nasmal yazo nan azancensa
sai
jikin hatyan yayi sanyi matuka baisan sa'adda
ya koma gefe daya ya zaunaba yayi jugum yana
mamaki
yadda akayi yarima nasmal yasan sirrinsa koda
ganin haka
sai itama sadirat ta matso kusa da hatyan tana
waigen yarima nasmal
tanayi masa wani irin kallo mai nuna alamar
rashin yadda da kuma damuwa
hakanne yasa hankankalin sa ya tashi yace
a ransa yace tabbas zansha wuya kafin na siye
zuciyar
wannan yarinya domin akwai alamun cewa
batasan menene ma soyayyaba
sadirat ta durkusa agaban hatyan ta dafa
cinyoyinsa
tace
ya dan uwana shin mai kuka tattauna da wannan
saurayin
kuma zaman me mukayi awannan wuri ba zamu
cigaba da tafiyba don mu isa birnin dake
gabanmu?
sa'adda hatyan yaji wannan tambaya daga bakin
'yar uwarsa sadirat sai yayi ajiyar zuciya yace
wannan saurayi da kike gani shine yarima nasmal
babban dan sarkin dake mulkin babban birnin
dake gabanmu
farautace ta kawosu cikin wannan daji kuma
dazu na yakeshi ne
saboda rashin sani da zargin ko so yake ya cutar
dake
amma na gane cewa ba haka bane
mahaifinsa aminin sarkin mafarauta ne
hatimin da kikaga na bashi acikin jakata dazu
na sarkin mafarauta ne ya banishi kuma ya bani
labarinsu
tun ina yaro karami
haduwata dashi yanzu kaina ya daure amma sai
naji amsar tambayoyin
dazan yi masa yanzu sannan zan fita daga cikin
duhun dana fada
kodajin haka sai takaici ya kama sadirat ta ciza
yatsa
ba don komaiba sai don batajin yaren su yarima
nasmal
tabbas tasan cewa bakomai hatyan zai sanar da
itaba
bisa abindake faruwaba
hatyan ya mike tsaye ya koma wajen nasmal
ya dubeshi yace
wacce masifa ce kuke tunanin zan kare muku
ita?
tambayoyi na sungi guda goma agareka amma
duk wannan tambayar tafi sauran mahimmanci
kodajin wannan batu sai dan sarkin yayi
murmushi yace
me kakeci na baka na zuba? kayi hakuri zan baka
amsar wannan tambaya taka
amma say bayan munje wani wuri anan gaba
kadan
kafin mu isa birnin mu na nuna muku wani abu
ka sani cewa daga nan zuwa birnin mu tafiyace
ta kwanaki uku kacal
shiyasa na tura dakaru na sukai labarin zuwanku
kafin mu isa domin a sami damar shirya muku
bikin tarbarku
cikin mamaki hatyan yace kawai saboda ni
almajirin
aminin mahaifinka ne sai a shirya bikin tarbarmu?
nasmal yayi murmushi yace
itama amsar wannan tambayar tana cikin ta
farko
ku tashi mu tafi mu fara wannan tafiya domin
kwana uku ba tafiyar sa'a uku bace
dajin haka sai hatyan ya dubi sadirat yace 'yar
uwa zakiyi tafiya
da kafafunki ko kuma na goyaki
sadirat tayi murmushi wanda ya bayyana
tsananin kyawunta tace
ai yanzu nafi sha'awar nayi tattaki domin na
rinka
kallon ni'imar wannan daji da kyau kafin hatyan
ya budi baki yace wani abu tuni yarima nasmal
ya juya masa baya
ya nausa cikin daji da sauri da ganin haka sai
hatyan ya kama hannun sadirat sukabi bayan
nasmal da sauri
kamar yadda nasmal ya fada haka al'amarin y
kasance
wato tafiyar kwana uku kacal sukayi suka iso
wani
tsohon gari wanda gaba daya gidajen cikinsa sun
rushe
duk wata bishiya dake cikin garin ta tunbuko
daga cikin karkashin kasa ta bushe wasuma sun
kone
duwatsu kuwa sun farfashe babu komai a cikin
garin kuma babu
wani abu mai rai face tsirarun kwarangwalolin
bil'adama ko ina acikin garin
kai da gani kasan cewa fiye da shekaru dari baya
rayuwa awannan wuri
babban abinda daurewa hatyan da sadirat kai
shine sunga
wani wawakeken rami mai zurfin kamu saba'in ya
ratsa tun farkon har zuwa karshen garin
to shin mutum miliyan nawane sukayi aikin haka
wannan rami?
wane irin masifaffen yaki akayi a wannan gari
her aka rushe gidajensa gaba daya her aka
konashi?
ta cikin wannan rami mai girman gaske aka shiga
dasu hatyan
koda suka iso karshen garin sai sukaga ramin ya
nufi
wani katon kogi wanda ya nausa her zuwa wata
nahiyar daban
suna zuwa daidai wannan wuri ne yarima nasmal
ya ja tunga ya tsaya sannan ya dubi hatyan yace
wannan rami da muka shigo ta cikinsa ba komai
bane face
sawun wata macijiya wacce babu wata macijiya
mai girmanta
aduniya ana kiranta da suna uwar macizai
kodajin wannan batu sai hatyan da sadirat suka
zazzaro idanu
hatyan ya dubi nasmal yace
anya kuwa baka samu tabin hankaliba? ya za'ayi
asami macijiyar da zata haifar da wannan rami
amatsayin sawunta kawai
ya kamata idan zaka gillara karya ka yi wacce
za'a yarda dakai
domin ba mahaukata bane agabanka
nasmal yace ba hauka bane lallai zaka gasgata
zancena
idan lokacin ganin zahiri yayi
makiyinku wanda ya turo muku zakunan sihiri
domin su hallakaku shine
yanzu zai taso wannan macijiyar daga cikin
karkashin teku
ta biyoku har birninmu ta hallaka ku idan tazo
baku kadaine zaku hallaka ba
komai da kowa dake birnin mu indai mai raine
saiya hallaka
bama birnin mu ba kafin macijiyar ta iso birnin
mu
saita baje birane dubu ashirin da daya akan
hanyar ta
ya kasance anyi asarar rayuka sama da miliyan
dubu
dari bakwai, yakai abokina binkice ya nuna cewa
kaine kadai zaka iya tserar da wadannan
dubunnan miliyoyin rayuka
amma kaima din saika haye wadansu jarrabobi da
zamuyi maka acan birnin mu
koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke
hatyan
baisan sa'adda maganar zuci ta fito filiba yace
tayaya ni kadai zan iya kare miluyoyin rayuka
tayaya zan iya fuskantar wannan mahaukaciyar
macijiya?
.
ANAN muka kawo karshen littafin tarkon mutuwa na bakwai 7
,
Zaku jini a littafi na takwas nan bada dadewa ba
Kafinnan dai nine Shuraih Usman
Inkiya 99%
Ke jagorantan kawo maku wanga littafi daga typing din Habibullah kabr
.
Sai kun jimu nan da yan wasu lokaci

Related Posts

There is no other posts in this category.

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "TARKON MUTUWA littafi na bakwai 7 complet"

Post a comment