Results

TARKON MUTUWA littafi na takwas 8 complet

TARKON MUTUWA
Littafi na takwas 8
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- Habibullah kbr
Post:- Shuraih Usman
Littafi na bakwai
Part 8 A
.
Lokacin da nasmal yaji tambayar da hatyan
yayi masa ta cewa
ta yaya shikadai zai iya kare miluyoyin rayuka
kuma ta yaya zai iya fuskantar wannan mahaukaciyar
macijiya
saiya kyalkyale da dariya
lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa y dubeshi yace
yakai abokina inaso ka sani cewa bawai don kafi kowa
karfi da iya yaki
ba ne akace kai zakayi wannan aikiba sai saboda
kaine yanzu kake kan kadaminka
ma'ana duk wani jarumi mai sa'a yanzu abayamka yake
kuma duk wanda yaja dakai saiyaci kasa
taurari sun nuna hakan kuma masana tarihi
da masu binkice sun tabbatar da cewa kaine
jarumi na farko wanda yaja da sarki shamsal
a nahiyar ku yakai labari
her gaba da gaba kunyi dashi amma bai sami nasara akan
ka ba
shin kana da wata tambayar ne wacce kake son jin
amsarta yanzu?
lokacinda jarumi hatyan yaji wannan tambaya sai yayi
shiru
yana dan tunani ya kasa cewa komai
daga can kuma saiya dago kansa ya dubi nasmal yace
wacce irin jarrabawa zakuyi mini acan birnin
wacce indai na tsallaketa zan iya kareku daga sharrin
wannan macijiya?
idan her zan haye jarrabawar nan na kareku
mai yasa bazanyi kokarin kare sauran kasashen duniyaba
wadanda zasu fuskanci wannan matsala?
dajin wannan batu sai nasmal yayi murmushi sannan
yace
komai mukaddarine babu wani shiri ko sihirin da zai iya
sauya kaddara
hatyan ya gyada kai yace mai yasa kana matsayin dan
sarki guda amma ka taho daji farauta akasa haka
batareda ka hau dokiba
alhalin tafiyace ta tsawon kwanaki uku?
nasmal yace
mu agarin mu duk wanda yakeyin doguwar tafiya akan
doki ragone
amfanin doki kawai shine ayi ado da biki dashi
yanzu sai muci gaba da tafiya domin mu isa can gida
akan lokaci
saboda nasan jama'armu zasu kosa da isowarmu
koda gama fadin hakan sai yarima nasmal ya juya
ya nufi hanyar da zata kaishi her birnin nasu
da ganin haka sai sadirat ta rugo wajen hatyan tace
waishin maganganun me kuke tayi ne?
ko kallon ta hatyan baiyiba ya juya ya nufi nasmal
yana mai cewa zakiji komai idan muka isa can birnin su
cikin hanzari itama tabi su hatyan sunata yin sauri
domin su riski yarima nasmal
Acan birnin sarauniya badi'atul nauwara kuwa
lokacin da ta kadaita acikin turakarta tareda
tsohuwa ummulkhairi afarkon dare saita mike tsaye
ta tube kayanta dake jikinta ta dubeta tace
saiki fara aikinki
dajin haka sai tsohuwa ummulkhairi tayi murmushi tace
haba ranki ya dade shin kin mantane cewa
nan acikin turakarki ta barci muke ai saidai
mu karasa cikin kewaye ki shiga cikin bahon wanka
tunda wanke jikinki za'ayi gaba daya
badi'atul nauwara tayi murmushi ba tareda tace komaiba
saita shige izuwa cikin kewaye ummulkhairi na biyeda ita
abaya
nantake badi'atul nauwara ta shige cikin bahon wanka ta
zauna
itakuma ummulkhairi saita bude jakarta ta debo wani
garin magani
ta zuba acikin ruwan bahon ta kama cuccuda jikin
badi'atul nauwara
aikuwa sai bakin shunin ya dinga ya ribga fita
tamkar ana wanke kura da ruwa
nanda nan fatar jikin badi'atul nauwara tayi kyau kamar
yadda take da
sannan taje ta caba ado na fada sannan sukaje gaban
madubi
suka tsaya ummulkhairi na gyara mata adon
koda badi'atul nauwara ta karewa kanta kallo
taga tsananin kyawunta da allah ya bata kuma ta tuno
da cewa wanda takeso yana can cikin hatsari
sai nantake idanunta suka ciko da kwalla har hawaye ya
zubo mata
bata an karaba
koda ta fahimci cewar ummulkhairi taga zubar
hawayenta sai kunya ta kamata
don haka saita yunkura cikin sauri domin ta goge
hawayent
sai ummulkhairi tayi farat tace
kada ki tsayarda wannan hawayen naki ya shugabata
domin zubarsace kadai zai rage radadin dake cikin
zuciyar ki
ki sani cewa uwar gidana ma mai girma anisa
kullum sai ta zubar da irin wannan hawayen naki
kuma akan irin dalilinki ma'ana matsalarku dayace
koda jin wannan batu sai badi'atul nauwara ta juyo da
sauri ta kama kafadun ummulkhairi ta ruke da karfi tace
waishin me kike nufi da wannan batu naki?
ummulkhairi tayi ajiyar zuciya sannan tace
keda kawarki anisa kunason saurayi daya
kuma dukkanku
baku taba son waniba faceshi
kowacce acikin ku zata iya sadaukar da soyayyar ta ga
'yar uwarta
saboda aminci da kauna duk ku biyun kun boye sonda
kukeyiwa hatyan
zangaya miki wani sirri guda daya bisa gaskiya
sirrin kuwa shine anisa ce ta fara son hatyan
tun kafin ki sanshi amma tunda suka rabu basu sake
haduwaba sai
awannan karon da ya baro kasarsu
shikansa har gobe yana da burin sake haduwa da ita
domin baiga fuskartaba awancan lokaci
dolene kusan hanyar da zakubi ku warware
wannan matsalar taku acikin sauki yadda dayarku
ba zata rasa rayuwarta ba kokuma taci amanar 'yar
uwarta
lokacin da ummulkhairi tazo nan azancenta sai
hankankalin badi'atul nauwara ya dugunzuma ainun ta
rasa abinda ke mata dadi
aduniya kuma saita kamu da tsananin mamaki ta dubi
uummulkhairi tace
yanzu keda duk kinsan wadannan abubuwa
amma baki sanar daniba donme zakiyi mini haka?
ummulkhairi ta numfasa tace idan her na sanar dake
wannan al'amari tamkar naci amanar uwar gijiyata ce
tunda itama ban sanar da ita abinda na saniba
nice na matsa akan saina biyoki zuwa nan sannan zan
wanke miki wannan shuni
domin mu tattauna akan wannan matsala
ki sani cewa
uwargidana anisa tana tsafi kuma tsafi yana tasiri akanta
ke kuwa bakya tsafi kuma tsafi baya tasiri ajikinki
ninan da kike ganina na kasance gawurtacciayr matsafiya
don haka nasan abubuwa da yawa ayanzu haka
babban makiyin masoyinku wato sarki shamsal yana
turawa su hatyan
mugayen masifun da zasu hallakar dasu
da farko
ya tura musu sihirtattun zakuna da kadoji sun tsallake
sharrinsu
yanzu kuma zai tura musu da dabbar da tafi dukkanin
dabbobin duniya bala'i da hadari
wacce ake kira da uwar macizai
kodajin wannan batu sai idanun badi'atul nauwara suka
zazzaro
kuma hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe
ta dubi uummulkhairi tace
tabbas na sami labarin uwar macizai awajen mahifina
ya gaya mini cewa babu wani matsafi da zai iya taso uwar
macizai
daga barcin da takeyi face wani boka guda daya
kuma bokan yafi shekara dari da hamsin da mutuwa
tayaya yanzu zakice sarki shamsal zai taso ta?
ummulkhairi tayi ajiyar zuciya tace ba sarki shamsal bane
zai taso taba
bokansa ne daizur kuma yakasance jika ga wancan bokan
daya mutu
na tamanin da takwas kuma ya gaji duk wani sihirin tsafi
daya bari
tunda mahaifinki ya baki labarin uwar macizai
kinsan duk irin bala'in da zata haifar aduniya idan ta
bayyana
manyan bokayen duniya sun gano cewa mutum dayane
zai iya kashe wannan macijiya
bokayen dake nahiyar bakaken fata sunyi imani cewa
jarumi hatyan ne zai iya kashe wannan macijiya
amma mu anamu binkicen na nahiyar fararen fata
munyi imani babu wanda zai iya kashe wannan macijiya
face jarumin da baya tsafi kuma tsafi baya tasiri jikinsa
sannan kuma dolene ya kasance ma'abocin wani sabon
addini wanda ake kira musulunci
kaf nahiyar bakaken fata babu wani jarumi da baya tsafi
kuma tsafi baya tasiri ijikinsa
awannan nahiya tamu kuma kece kadai jarumar da take
da wannan baiwa
amma kuma baki kasance ma'abociyar wannan sabon
addini ba
shin kinsan wannan addini wanda ake kira musulunci?
kodajin wannan tambaya sai sarauniya badi'atul nauwara
tayi shiru
tana tunani izuwa wasu 'yan dakiku sannan tayi farat tace
mahaifina ya bani labarin wannan addini kuma
ya bar mini wani littafi wanda yake dauke da cikakken
bayani akan wannan addini da yadda ake shigarsa
kodajin wannan batu sai farinciki ya turnuke
ummulkhairi
tace ya zama wajibi ki shigeshi idan har kinason ki ceto
rayuwar masoyinki
kuma ki ceto dubunnan ruyukan dake wannan nahiyar
tamu da kuma nahiyar bakaken fata
da zarar kin gama karanta wannan littafi gamida shiga
cikinsa
saikiyi shiri kibisu jarumi hatyan izuwa wannan birni
da suka nufa na bakaken fatav domin acan ne macijiyar
zata fito ta cikin teku
idan ta gama dasu jarumi hatyan da wannan birni zata
dawo
ta rushe duk kasashen dake wannan nahiya
hatta birnin sarki shamsal
kuwa domin shikansa boka daizur bai isa ya iya sarrafa
macijiyarba ya shugabata idan baki hanzarta yin
abindana umarceki ba kawarki anisa da masoyinki hatyan
zasu rasa rayuwar su
kafin ummulkhairi ta ta gama rufe bakinta tuni sarauniya
badi'atul nauwara
ta falfala da gudu izuwa cikin daki
sai takama bude buden akwatunan da aka tara aciki
wadanda sunfi guda dubu ta rinka binkice su daya bayan
daya
A can birnin sarauniya anisa kuwa lokacinda sarki
shamsal ya baiwa boka daizur umarnin
taso uwar macizai da gaggawa sai boka daizur
ya fiddo madubin tsafinsa ya ajiyeshi agabansa
ya fara karanta wadansu dalasiman tsafi
sudai wadannan kalmomicguda dari ba uku ne kuma
boka daizur na gama karanta sune uwar macizai zata
farka daga barcin da take
koda boka daizur yazo kan kalma ta casa'in da biyar
sai kawai sukaga an banko kofar dakin da suke ciki
afusace cikin tsananin fushi sarki shamsal ya mike tsaye
yana mai zare takobinsa
kawai saiyaga sarauniya anisa ta shigo tareda dakarunta
na yaki kimanin su dari uku
kowannensu ya dana kibiya akan baka sun saita sarki
shamsal da boka daizur
afusace anisa ta dubi sarki shamsal cikin daga murya tace
saboda kawai ka hallaka mutum biyu kacal
zaka fito da abin da zai iya hallaka duniyar gaba daya
wannan wanne irin rashin imani ne hade da son zuciya
to kasani cewa idan kuka ci gaba da kokarin aiwatar da
wannan nufi naku
kaida bokan nan naka kibiyoyi dari ukune zasu nutse
ajikinku
yanzu alhakin kasheku ba ahannuna yakeba
kuma ka sani cewa ba wai tsoronka nakejiba
tundaga farkon zuwanka amma ka sani cewa kazo gabar
da dole sai nayi kokarin dakatar dakai
sa'adda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai sarki
shamsal ya turbune fuskarsa yace
yake wannan karamar karuwa vkiyi sani cewa
ni murucin kan dutse ne ban fitoba saidana shirya
tayaya kike tunanin cewa zaki iya hanamu aiwatar da
wannan babban aiki to ga fili ga mai doki sai mu zuba mu
gani
maza bisa kanki
maza kisa dakarunki su harbemu idan her kibiyoyin naki
zasu iya cutar damu
kafin sarki shamsal ya gama rufe bakinsa tuni anisa ta
baiwa dakarun nata umarnin suyi harbi
koda kibiyoyin suka fito daga cikin baka sai suka kame
asama suka kama da wuta gaba dayansu suka kone
kurmus
suka zube kasa amatsayin toka
faruwar haka keda wuya sai sarki shamsal ya mike tsaye
yana mai kyalkyalewa da mahaukaciyar dariya sannan
yace
Yanzu kuma me zaki iyayi?
shin zakiyi amfani da karfin sihirinkine wanda yafi namu?
kai boka daizur maza ka karasa wannan aiki
nikuma ka barni da wannan sarauniya naga iya gudun
ruwanta
nasan kin gama da hadimaina da suke waje amma ki sani
inzaki hada gaba daya dakarunki su zo su hadu anan basu
isa su tsayarda muba
her boka daizur ya budi baki zaici gaba da karanto
wadannan dalasiman tsafi sai sarauniya anisa ta daka
masa tsawa ya tsuke bakinsa sannan ta dubi sarki
shamsal afusace tace
tun daga kuruciyata zuwa girmana nake tanadi akanka
domin tun zamanin iyaye da kakanni masarautarku suke
kuntatawa
masarautun da suke wannan nahiya tamu ka sani cewa
dan hakkin daka raina shike tsone maka ido tabbas ka fini
shekaru
kafini karfin damtse amma baka fini iya yaki da tsafiba
kawai na boye tawa baiwarne amma yanzu zan nunata
idan ka kasheni sai kuci gaba da aiwatar da nufinku
idan kuma nice na kasheka shikenan na kawo karshen
mulkin zaluncinku awannan nahiya
anisa na gama fadin haka saita cire rigar da take jikinta
mai kama da alkyabba tayi wurgi da ita saigata cikin
shigar yaki
wadansu tufafine ajikinta na bakar fata kuma matsatstsu
takalmin kafarta ma na bakar fatane dogo iya kauri mai
madauri
wata zabgegiyar takobice agadon bayanta
nantake sarauniya anisa ta dubi dakarunta tayi musu
wata inkiya
nantake suka fice daga dakin suka turo kofa suka rufe ta
waje harda sa makulli
anisa ta dubi sarki shamsal cikin alamun tsananin kiyayya
tace
na sallama rayuwata don ceton masoyina hatyan
da 'yar uwarsa sadirat da kuma miliyoyin rayukan
da kakeson salwantarwa ka sani cewa
nida sarauniya badi'atul nauwara ne muka taimakawa
hatyan ya tsira daka dukkanin harinka
acan teku inda kuka rutsashi kana shirin sare masa hannu
badi'atul nauwara ce tazo ta naushi bayanka
kafin ka juya ta daukeshi daga wajen
anan garin kuma nice na batarda duk wata shaida
alhalin yana cikin wannan gidan sarautar aboye
abinda yasa kuka kasa gano hakan da karfin sihirinku
shine
sarauniya badi'atul nauwara tama cikin garin nan kuma
kasan cewa
tsafi baya tasiri indai tana wuri
koda gama fadin haka sai anisa ta gyara tsayuwarta ta
zare takobinta sannan ta gyara rukon garkuwarta
awannan lokaci fuskar sarki shamsal ta fara gyatsine
saboda tsananin fusata don haka sai shima ya zare tasa
takobin cikin kakkausar murya yace
na rantae da girman kabarin ubana sainayi miki kisan
wulakanci
tunda dasa hannunki acikin zagon kasan da akayimini
kuma koda annobar uwar macizai bata hallaka kawarkiba
sai na bita har birninta nayi mata irin kisan da zanyi miki
kodajin wannan batu sai anisa ta bushe da. dariya tace
yanzu nan kai aganinka zaka tsira da rayuwarka ne
her ka cika wannan buri da kake furucinsa?
idan baka saniba ka sani domin na fuskanci kana da
jahilci
akan sanin tarihin duniya her kullum kuma har abada
mulki da zalunci baya dorewa
kafin kai anyi manyan sarakuna da suka fika karfin
damtse
dana sihiri da karfin mulki da zalunci amma akaron
banza suka dinga gushewa
kafin anisa ta gama rufe bakinta
tuni sarki shamsal ya dako tsalle daga inda yake tsaye
tamkar daga kan sifirin yake
ya kawowa sarauniya anisa mugun sara akafadarta
da nufin ta tsargeshi gida biyu
ba zato ba tsammani sai yaga ta kare saran
ba tareda karfin saran yasa ta fadi kasaba kafin ya kawo
mata wani harin tuni
ta doki kirjinsa da gwuiwar kafarta ta hagu,
saboda karfin dukan saida yayi baya taga taga
amma ya tsaya cak ya sake taso mata suka sake
kacamewa da azababben yaki
mai matukar ban tsoro da ban al'ajabi
shidai sarki shamsal yana yakin ne da dukkan karfinsa
cikin kunar rai domin zuciyarsa tafarfasa take kamar zata
kone
yana mai yiwa kansa tambaya cikin zuciyarasa yana mai
cewa
yanzu dama akwai macen da zata iya tarata da yaki
awannan nahiya amma ban saniba?
tayaya wannan yarinya t iya yaki haka kuma ta kasance
mai bakin zafin nama irin wannan
gamida tsagwaron karfin damtse?
shikuwa daizur jikinsa ne ya kama kyarma saboda
tsananin tsoro
domin baiyi zaton anisa ta kai wannan matsayiba
kuma duk abinkicensa na tsafi bai taba ganin sirrintaba
saida sarki shamsal da anisa suka shafe sa'a guda suna
wannan gumurzu
acikin wannan daki
ya zamana cewa sun lallata duk wasu kujeru da kayan
alatu da suke cikin dakin
amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin
dayaba
shikuwa boka daizur dayaga masifar tayi yawa saiya
rikide
ya zama dan mitsitsi tamkar kuda
ya makale acan saman rufin dakin yaci gaba da kallon
wannan gumurzu
LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT
Nidinne dai shuraih Usman
Daga www.facebook.com/hausaebooks
TARKON MUTUWA
Littafi na takwas 8
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- Habibullah kbr
Post:- Shuraih Usman
Littafi na bakwai
Part 8 B
.
lokacin da sarki shamsal yaga sun shafe tsawon
sa'a guda suna kaiwa juna sara da. suka cikin
tsananin zafin nama juriya da bajinta amma
babu wata nasara kuma anisa bata gaji ba
saiya ja da baya ya gyara tsayuwarsa yana
tunanin salon fada da zai sake
dashi da Ita awannan lokaci duk hannayensu radadi suke
saboda gajiyar ruke
kotar takobi kuma duk takubban nasu sun daauki zafi
sosai
kamar acikin wuta aka gasa su
koda anisa taga sarki shamsal ya danja da baya sai
tayi masa dan murmushi na yarda da kanta tace
nasan kayi mamaki yadda nake da kwarewa
da juriya irin taka ba komai ya jawo hakanba
face nayi binkice akanka sosai kuma na samu duk irin
horon daka samu
sarki shamsal ya maidawa anisa martanin murmushi
yace
ai abu daya zakiyi ki burgeni me zai hana mu zubar
da makaman mu mu gwada 'yar kashi?
koda jin wannan batu
sai anisa ta sake bushewa da dariya tace
ashe bani d hankali kenan
idan her baka manta ba ai tunda farko na gaya
maka ccewa kafini karfin damtse to sabodame zanyi
gangancin jarraba nawa akan naka?
ka sani cewa indai akwai takobi ahannuna
karfin damtsenka ba zaiyi ta siri akaina ba
amma idan kana shakkar hakan
to ka sauya salon yakin naka k gani zaka sha mamaki
yau sai na rushe dukkan burinka na duniya
kuma cikin biyu dolene daya ya faru ko ni na kasheka
ko kuma kai ka kashe ni ko kuma muyi ragas
sa'adda sarauniya anisa tazo nan azancenta sai
sarki shamsal ya bushe da dariya sannan yace
ke karamar karuwa ki sani cewa duk wanda
ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, ke sa'ar dana ce don
haka
na fiki wayo kuma nafiki sanin tuggun yaki
na fiki shan gwagwarmayar duniya kuma na fiki sa'a
yau shekara ta arba'in da bakwai kenan ina kan sharafina
duk abinda nasa agaba na sainaga bayansa
don haka ke baki isa ki rushe mini burinaba
caraf saii anisa ta tari numfashinsa tace
wannan shine babban kuskurenka arayuwa
domin kana mantawa cewa dolene mai laya
ya kiyayi mai zamani, ka sani cewa sarki goma zamani
goma
mu 'ya'yan yanzu kwakwalwarmu tafi taku dogon nazari
gamida
hangen nasa da kuma basirar binciko abubuwan cigaba
wannan dogon surutun da mukeyi bashida amfanin
komai face bata mana lokaci kawai mu gani akasa
ni burina ka sauya salon yakin naga yadda ta kaya
kafin sarki shamsal ya bude baki yace wani abu
tuni anisa ta dako tsalle daga inda take ta kawo masa sara
,naushi, da bugu da hannayenta da kafafunta
duk alokaci guda cikin bakin zafin nama sarki shamsal
yayi kokarin kare duk hare harenta amma duk da haka
saida
ta sami nasarar yankansa akan kwanjinsa na hannun
dama kuma ta doki kirjinsa yaje ya manne ajikin garu
kawai sai gani tayi kamar an cilloshi daga cikin baka
kafin tayi wani yunkuri shima y rama abinda
tayi masa ya yanketa akan cinyar hannunta na dama
kuma ya daki kirjinta ta fadi kasa wanwar saboda karfin
dukan
nasa ya ninka nata harsaida ta furzar da jini daga bakinta
tana kwance akasa sai sarki shamsal ya dako tsalle
ya kawo mata suka aciki da takobinsa
anisa ta mirgina can gefe guda ta kaucewa sukar takobin
ta doki kasa
ta lume kafinya zaro takobin ta mike tsaye zumbur
sun sake kacamewa da azababben yaki saida suka sake
shafe wata sa'a gudar suna wannan dauki ba dadin
ya zamana cewa kowannensu ya sake samun nasarar
yankar abokin
gwaminsa sau biyu
wato dai kowannensu anyi masa rauni uku amma saboda
azabar naci da juriya
basu fasa ci gaba da artabun ba
koda sarki shamsal ya fahimci cewar bashi da tabbacin
samun nasara
akan sarauniya anisa saiya daga kansa sama ya dubi boka
daizur
wanda ya zama dan mitsitsi ya daka masa tsawa yace
wai shin me kake jirane ai tunda na tare maka wannan
hatsabibiyar
maza ka karasa aikinka
koda jin haka sai boka daizur yai wuf ya fiddo
madubin tsafinsa yaci gaba da karanta wadannan
dalasiman tsafi daga inda ya tsaya
al'amarin daya dugunzuma hankankalin sarauniya anisa
kenan
ta kara zage damtse wajen kokarin kaiwa boka daizur hari
domin ta hallaka shi amma sai sarki shamsal
ya tareta suka cigaba da bakin artabu mai matukar ban
tsoro
wanda komai zai iya faruwa
kafin cikar rabin sa'a boka daizur ya gama karance
wadannan dalasiman tsafi
faruwar hakan keda wuya sai uwar macizai
wacce ke kwance akan karkashin teku tana barci
na tsawon shekaru dari da arba'in ta yunkura
ta taso izuwa saman tekun, yunkurin da tayine
yasa tekun tayi girgiza ta kama ambaliya
ashe wannan tekun mahadace
ta dukkan tekunan duniya
hakan ne ya haifar da girgizar kasa ako'ina acikin duniya
ya zamana cewa tekun ta kama ambaliya ruwa
na shiga gari yana cinye mutane da gidaje
babu inda ba'aga wannan tashin hankalinba
don haka anan birnin sarauniya anisa tana cikin yin
wannan yakida sarki sshamsal ne tekun ta balle
ta fado cikin gari gaba daya gidan sarautar saidaya ruguje
kuma ya nutse acikin ruwa, mutane da yawa
suka hallaka wasu suka jirkita sarki shamsal da boka
daizur
kuwa akan wani akan wani katako suka dafe
ruwa ya tafi dasu bisa taimakon karfin sihirin tsafinsu
suka tsira
itama sarauniya anisa tsafi tayi t kira wani sihirtaccen
tsuntsunta
ta dira akansa ta kama shawagi asararin samaniya
tana ganin irin mummunar barnar da ruwa yayi mata
wanda ya haddasa asarar dubunnan ruyuka da dukiya
mai yawan gaske
saboda bakin ciki da takaici nantake sarauniya anisa
ta fara zubar da hawaye ,bisa dole ta sauko kasa
izuwa cikin ruwa ta fara kokarin ceton rayukansu
Al'amarin su jarumi hatyan kuwa ya rage saura baifi
sa'a daya da rabi su isa birnin su yarima nasmal ba
kawai sai suka jiyo rurin uwar macizai adaidai lokacin da
ta
yunkura ta taso sama daga cikin tekun
nantake kasa ta kama girgiza
babu shiri su hatyan suka ruke hannayensu
don kada su fadi kafin su nemi matsera
kasa ta fara tsatstsagewa
daga bayansu tana ruftawa kasa tana kusantata
babu shiri duk su ukun suka falfala da azababben gudu
har hatyan yayi dan nisa saiya tuna cewa ai 'yar uwarsa
sadirat
bata da karfin gudu irin nasa don haka saiya waigo
da baya a firgice yana mai tsayawa
hatyan ya kurma uban ihu sakamakon hango abindake
shirin faruwa
kasa ce ta zabtare adaidai inda sadirat take
ta tafi izuwa kasa zata nutse
ba zato ba tsammani sai yaga yarima nasmal ya dako
tsalle
izuwa gareta ya cafo hannunta
kuma nantake ya rikide ya zama katon tsuntsu yayi sama
da ita
ya juya da baya ya tunkaro hatyan
dukda tsananin gudu irin na hatyan sai gashi
zaizayar kasa na neman cimmasa domin tazarar
dake tsakaninsu bata wuce taku biyuba
saura taku daya kacal kasar ta cimmasa ne tsuntsu
nasmal
ya sureshi yayi sama dashi sai gashi su biyu shida 'yar
uwarsa
suna reto ajikin kafafun tsuntsun
adaidai wannan lokacine suka iso birninsu yarima nasmal
tun daga sama sukaga irin mummunar barnar da girgizar
kasa
ta haifar musu sai hankalinsu ya dugunzuma
saboda fiye da rabin gidajen birnin sun lume acikin ruwa
ga gawarwaki nan na mutane da dabbobi suna yawo akan
ruwa
har asannan kuma kasa bata daina girgizaba
lokaci guda kuma sai komai ya tsaya cak!
aka daina girgizar kasar
ashe ba komai ya janyo hakanba face uwar macizai ce
ta tsaya cak!
abakin gabar teku baya ta gama fitowa da dukkannin
jikinta
gaba daya kawai saita daga kanta sama ne
ta dubi gabas da yamma kudu da arewa tana shakar
numfashi
da kamshi sirrin yin haka kuwa shine tanaso
ta jiyo inda kamshin hatyan da 'yar uwarsa sadirat yake
ta kai farmaki wajen ashe abinda ya hana ta jiyo kamshin
nasu
shine girman fuka fukan tsuntsun
tsuntsun yaci gaba da tafiya dasu acikin sama
harsaida suka iso tsakiyar gidan sarautar birnin
wanda kadan daga cikinsa ne ya ruguje kuma tuni
a lokacin ma'aikata nata kokarin gyara gamida kwashe.
ruwan dayayi ambaliya acikinsa
sarki da mukarrabansa na kai kawo acikin gidan sarautar
suna kallon masifar da ta faru kawai sai sukaji wata iska
mai karfi acan sama
koda suka daga kawunansu sama sukaga katon tsuntsu
dauke da mutane biyu suna saukowa kasa
sai suka kamu da tsananin farinciki
nantake garin ya kaure da kade kade gamida
bushe bushe da kuma wake wake
wani gagarumin buki ake kamar ma an manta da wannan
masifa data faru
tsuntsun na sauke su hatyan da sadirat sai
shima ya rikide ya zama nasmal ya rungume shi
yana mai cewa lale marhaban da dana babban gwarzo
tabbas saura kiris mu fita daga muguwar fargabar
da muke ciki tundaga gashi ka kawo mana
wanda muke sa ran zai kare mu daga wannan masifa
koda gama fadin hakan sai sarkin ya janye jikinsa daga
cikin na nasmal
yaje ga hatyan ya rike masa hannu suka gaisa yace
marhaban da jarumi hatyan daga makeri satyan
kuma almajirin sarkin mafarauta na birnin bindal
dukda cewa hatyan ya san al'amarin tsafi sai da
yayi mamakin yadda wannan sarki yasan komai
haka dangane dashi
〇 sarki ya cire hannunsa daga cikin na hatyan
ya mikawa sadirat itama suka gaisa ya dubeta
cikin murmushi yace
sannu da gwagwarmaya 'yata hakika kin fuskanci
tsananin fargaba acikin wannan tafiya amma kiyi hakuri
komai ya kusan zuwa karshe da izinin abin bautarmu
da yake sadirat bataji yarensa ba bata san me yafadaba
saitayi kasake tana kallonsa, al'amarin daya sa
dariya ta kwacewa hatyan kenan ya dubeta yace
barka da zuwa yayi miki gamida jajen wahalar da
mukasha
kodajin haka saita rissina ga sarki tana mai nuna
alamar godiya awannan lokaci ne mahaifiyar nasmal ta
ratso ta tsakiyar taron ta rugo gareshi
suka rungume juna tana mai murnar dawowarsa
mahaifiyar tasa ta juyo ta kurawa sadirat hannu
sannan ta dubi nasmal tayi masa murmushi
gamida inkiya wacce tasa sarki da dukkan jama'ar dake
wajen
banda hatyan da sadirat suka bushe da dariya
nantake sadirat taji ajikinta cewa lallai akwai wani abu
akasa
wanda ya shafi dan sarki kuma ya shafeta
tunda saida aka kalleta kuma akayi inkiyar
sannan akayi wannan dariya
adaidai wannan lokaci ne babban boka na birnin
ya ratso cikin taron yaransa biyu na biye dashi
bokan ya kasance dogon mutum mai kirar samudawa
kuma mai suffar jarumai
indai a fagen jarumtakane birnin kaf
yarima nasmal ne tsaransa basu taba jarraba
jarumtakar junaba amma kowa na shakkar kowa
ana kiran wannan boka da suna aimar
aimar ya gaji bokancin birnin ne awajen ubansa
kuma fiyeda shekaru dari biyu baya zuriyarsuce ke ruke
da wannan mukamin
aimar ya kasance matashi kamar yarima nasmal
kuma mutum ne mai tsananin kishin kasarsa
da jama'arsa wani abun mamaki shine da yarima nasmal
da boka aiman basa ga maciji
amma kuma basu taba zage zage ba ko fada
saidai kace na ce kuma duk masifar da zata sami daya
dayan bazai taimaka masaba
atakaice dai akwai tsama q tsakaninsu wannan tsama ta
samo asaline
tuun suna yara 'yan kimanin shekaru tara tara
abindaya faru shine wata rana sa'adda suka shiga daji
farauta
sai suka hango wata barewa acan nesa dasu kadan
nantake sukayi gasar cewa babu wanda zai harbi barewar
da kibiya saidai suyi gasar gudu
wanda duk y kurewa barewar gudu ya kamata ta zama
tasa
agaban sarki da mahaifin aimar aka kulla wannan gasa
nantake kuwa aimar da yarima nasmal suka bi barewar
da gudun tsiya
izuwa cikin jeji tun su sarki na hangosu harsai da suka
bace musu da gani
shidai karfin gudu baiwane kawai ba tsafi bane
ko tsagwaron kwarewa yarima nasmal yafi aimar karfin
gudu da juriyar daukarr lokaci
amma shi aimar din maguji ne na gaske don haka
da farko sa'adda suka fara tseren gudun sai da suka shafe
rabin sa'a suna gudun kafada da kafada aka rasa wanda
zai tserewa wani
idan nasmal yaga aimar ya dan bashi tazara
sai shima ya dage ya riskeshi duk wannan abindake
faruwa tazarar su da barewar batafi kamu goma ba
koda suka sake shafe rabin sa'ar sai aimar ya fara sarewa
saboda gajiya aikuwa sai nasmal ya bashi tazarar tsawon
taku biyar
kawai sai gani yayi baifi saura taku biyuba tsakanin
nasmal da wannan barewar
aikuwa sai aimar yasa kafa ya tade nasmal ya fadi kasa
yanaji yana gani wannan barewar ta tsere cikin tsananin
fushi
nasmal ya mike tsaye ya zare takobinsa yayi kan aimar
kawai sai aimar ya tsaya cak yana kallonsa yana
murmushin mugunta
koda nasmal yazo dafda aimar ya daga takobin sa sama
sai ya kasa sara masa
aimar ya tuntsure da dariya yace
maza ka kashe magajin dirkan wannan birnin ai kasan
hukuncin kisane
koda jin wannan batu sai jikin nasmal yayi sanyi
ya sauke hannunsa kasa kuma ya maida takobinsa
ya dubeshi afusace yace
daga yau nida kai babu abota babu taimako kuma babu
yarda her abada
Lokacinda boka aimar ya iso gaban ssarki shima da
yaransa guda biyu
sai suka rissina suka gaida sarki sannan aimar ya durkusa
yace
ya shugabana munyi babban sa'a da nasmal ya rikide ya
koma tsuntsu
alokacin daya daukosu hatyan da 'yar uwarsa
domin girman fuka fuknsane ya hana uwar macizai
jin kamshin su hatyan har suka iso nan gidan sarautar
amma da zarar daya daga cikinsu ya fita daga nan zataji
kamshin sa ta taso
idan kuwa ta taso komai da kowa saiya hallaka
yanzu muna da damar da zamu gabatar da wannan gasa
domin mu gani ko jarumi hatyan ne bakon jarumin da
zai iya kashe wannan uwar macizan
koda boka aimar yazo nan azancensa sai kan hatyan ya
daure yace
a ransa au har a yanzunma babu tabbacin cewa nine zan
iya kashe wannan macijiya harsai an gudanar da wata
gasa
aikuwa indai hakanne to tsafi ya zama shirmen banza
tunda baya iya tabbatar da abu guda daya
lokacin da sarki shamsal yaji batun boka aimar sai yayi
murmushi yace
wannan yayi kyau yanzu tunda day uwar ba zata
motsa ba face daya daga cikin wadannan baki ya fita
daga cikin nan muna da dan kwanciyar hankali
saboda haka sai bakin namu suje suci abinci
su huta inyaso saida yamma mu gabatar da wannan gasa
gama fadin haka keda wuya sai yarima nasmal ya kama
hannun
hatyan ya jasu domin su tafi makwancinsu
amma sai aimar yayi wuf ya sha gaban sadirat
ya dubeta cikin murmushi kuma ya bude baki cikin
yarenta yace
lale marhaban da zinariya abar kyalkyali wacce
na dade ina jiran ganin haskenta ya sadirat 'yaga makeri
satyan
Cikin tsananin mamaki sadirat ta bude baki
da nufin ta tambayi aimar yadda akayi ya santa
kuma ya iya yarenta ,amma sai nasmal ya shiga
tsakaninsu ya dubeshi yace
baka da ikon yin magana da wadannan baki nawa face da
izini na
Wannan yasa nima Shuraih Usman nace kui hakuri da karanta wannan littafi sai ranan Asabar
Zamu cigaba
,
Daga www.facebook.com/hausaebooks
TARKON MUTUWA
Littafi na takwas 8
Abdulaziz Sani madakin Gini
Typing:- Habibullah kbr
Post:- Shuraih Usman
Littafi na bakwai
Part 8 C
.
Gama fadin hakan keda wuya sai nasmal ya kama hannun
hatyan dana sadirat ya jasu da sauri
suka nufi wani bangaren daban na gidan sarautar
alokacin da sadirat ta ringa waigen aimar
shikuma ya bita da kallo dauke da wani tattausan
murmushi
mai nuna cewa ya dade yana kaunarta da begenta
tuni kishi ya turnuke yarima nasmal bisa ganin yadda
sadirat ke waigen aimar domin azatonsa ta kamu da
sonsa ne
hatyan da sadirat sunyi sha'awa mutuka bisa ganin yadda
tsarin ginin gidan sarautar yake
da kuma irin kayan kawar da aka zuba masa
kasancewar yasha banban da irin nasu
cikin wani katon gida aka shiga dasu
mai dauke da babban falo
aka barsu kan kujeru na alfarma aka zaunar dasu
kuyangi bayi da hafiman dake cikin gidan sun haura guda
dari
nan da nan aka kawowa hatyan da sadirat abinci mai
daraja iri iri har kimanin kala goma
nandai suka zauna tareda yarima nasmal sukaci suka sha
bayan sun sami nutsuwa ne nasmal ya rinka
yiwa hatyan bayanin yadda al'adunsu suke
da kuma harkar masarautarsu da addininsu
wanda yakasance suna bautar wadansu aljanune
duk abinda nasmal ya fada sai hatyan ya fassarawa
sadirat izuwa yarensu
wadansu abubuwan idan sukaji saisu bushe da dariya
domin sai suga su agarinsu wannan abin ma kauyanci ne
hakadai idan suka yita hira har dare ya raba
duk tsawon wannan lokaci sadirat ta lura cewa
nasmal satar kallonta kawai yakeyi amma da zarar yaga
zasu hada idanu sai yayi sauri ya kauda kai
hakanne yasa ta gane lallai ya kamu da tsananin santa
nantake ta tuno da irin kallon da boka aimar ya dinga yi
mata
da kalaman da yayi mata wanda ya tabbatar da
soyayyarsa agareta
koda sadirat tazo nan atunaninta saitaji zuciyarta ta buga
da karfi
kawai saita tambayi kanta tace
to waishin nida bantaba yin soyayyaba ban ma san yadda
akeyiba
taya zanyi soyayya da wadannan samari biyu wanda
dukkannin su suna nuna mini so?
tabbas kowannensu yana da siffar kamala gamida
kyawun daya kamata asoshi
shikenan kaddara zata fitar da wanda yafi dacewa
wɑɳɳɑɳ รɦiɳɛ ɑɓiɳɗɑyɑ Բɑʀu gɑรu ʝɑʀuɱi ɦɑtyɑɳ
ɓɑyɑɳ รuɳ iรɑ ɓiʀɳiɳ Բɑʀkѳ ɳɑ ɳɑɦiyɑʀ ɓɑkɑkɛɳ Բɑtɑ
ɑʆѳkɑciɳɗɑ ɗɑɓɓɑ tɑ ɓɑyyɑɳɑ wɑtѳ uwɑʀ ɱɑcizɑi
a can birnin sarauniya badi'atul nauwara abinda ya
kamata tayi
batayi kasa aguiwa ba saita kama binkice acikin gidan
sarautar tana neman littafi mai dauke da tarihin addinin
musulunci
da kuma shikansa addinin da yarda ake shigarsa
saida suka shafe kusan rabin sa'a tanata dube dube
sannan ta ganshi acan kasan wata doguwar durowa dake
manne ajikin bango
cikin farinciki ta zauna ta bude littafin ta fara karatunsa
tundaga farko har karshe
afarkon yammaci ne ya fara karatun littafin wanda ya
dauke hankalinta
gaba daya yasata manta da batun yunwa ,kishirwa, gajiya
da barci
domin arayuwarta bata jin managanu masu ratsa jikiba
kamar na cikin littafin
bata tabajin kalmomin hikimaba d basira irinsu
nantake jikinta gabe daya yayi sanyi kuma
zuciyarta tayi imani da duk abinda take karantawa
taji ta gamsu dari bisa dari cewar wannan littafi akwai
ayoyin alkurani mai tsarki aciki
tareda hadisan manzon allah s.a.w aciki
koda sarauniya badi'atul nauwara tazo inda aka rubuta
kalmar shahada
saita karantata afili bata saniba
aikuwa sai nantake taji tsigar jikinta duk sun karbi kalmar
kuma sunyi imani da ita
awannan lokaci tsohuwa ummulkhairi na zaune
acan gefe daya tana kallon badi'atul nauwara
kuma tana sauraronta koda sarauniya badi'atul
ta biya kalmar shahada afili sai bokanya ummulkhairi ta
firgita ainun taji kamar an watso mata wuta bata san
sa'adda ta kurma uban ihuba
ta fadi can gefe daya tana haki kamar wacce tasha faman
gudu
hakanne yasa badi'atul nauwara ta kara imani
domin ta tabbatar da cewa tsafi da sauran addinai
karyane
addinin musulunci shine gabansa kuma shine addinin
gaskiya
cikin murna da hanzari badi'atul nauwara ta mike tsaye
zumbur da nufin taje tayi shirin tafiya izuwa nahiyar
bakaken fata
don tunkarar uwar macizai sai kawai sukaji birnin gaba
daya ya kama girgiza kasa na neman darewa
al'amarin daya razana bokanya ummulkhairi khairi kenan
domin ta gane cewa uwar macizai ce ta taso daga
karkashin teku
saboda tsananin razana bokanya ma nantake jikin
ummulkhairi ya fara karkarwa, idanuwanta suka zazzaro
tamkar tasha yaji
kai atakaice dai batama san sa'adda bawali
ya kwace mataba daboda tsananin razana
itakuwa sarauniya badi'atul nauwara lokacin da taga
wannan masifa ta taso dakinda suke ciki
yana neman rushewa saikawai ta bude wannan littafi
dake hannun ta ta fara karanta wani wuri
da aka jero inda sunayen allah kyawawa suke ta aiyana
aranta cewa
tana neman taimakonsa
Allah mai girma, fara karanto sunayen allah tsarkaka keda
wuya a cikin bakin badi'atul nauwara
sai aka daina girgizar kasar, komai ya dawo daidai tamkar
wani baitaba faruwa ba a birnin
al'amarin daya matukar daurewa ummulkhairi kai kenan
ta tamu da tsananin mamaki
lokacin sarauniya badi'atul nauwara da bokanya
ummulkhairi suka fito daga cikin wannan daki
suka iso fada sai suka cika da tsananin mamaki bisa
abinda suka yi arba dashi da kuma abinda sukaji
bakomai suka gani ba face 'yan gudun hijira
sama da mutane dubu dari daga sauran makotan birane
sun cika fadar suna koke koke wasu sun jikkita
sun sami raunika da yawa ajikinsu, suna fadin cewa
birninsu ya rushe gaba daya kuma ruwa yaci garin
nan dai badi'atul nauwara ta suka akayi bincike sai aka
gano cewa birninta ne kadai ba'a sami wannan masifa ba
amma ko ina anyi asarar dubunnan ruyuka
koda jin wannan batu sai bokanya ummulkhairi taja
dogon numfashi tace
tabbas addinin musulunci shine addinin gaskiya
ya shugabata kiyi sani cewa darajar sunayen ubangijin
musulunci da kikayi ta karanrowa dazu shine
ya kare birninki daga wannan masifa ta bayyanar uwar
macizai
lallai yanzu na gamsu cewa addinin musulunci shine
addinin gaskiya
kece kadai zaki iya kashe wannan mmacijiya
don hhaka dolene ki gaggauta yin wannan tafiya
inba hakaba kuwa masoyinki dakuma kawarki suna daf
da mutuwa
dakuma rayukan miliyoyin mutane
sannan zaki iyayin hakan idan imaninki g ubangijin
musulunci yana nan acikin zuciyarki bai gusheba
kodajin haka itama badi'atul nauwara ta maidawa
ummulkhairi murmushi
cikin kankanin lokaci aka shiryawa sarauniya badi'atul
nauwara guzuri akan wani ingarman doki
kafin ta tafi saida ta tara gaba daya jama'ar birninta ta
basu labarin gaba daya abinda ya faru
tundaga lokacin da taje birnin kawarta sarauniya anisa
kawo izuwa yanzu
koda jin wannan labarin sai gaba dayan jama'ar birninta
suka durkushe kasa bisa guiwoyinsu
suna masu cewa mun bayarda gaskiya da ubangijin
musulunci
kodajin haka sai farinciki ya lullube badi'atul nauwara
nantake ya dubi ummulkhairi tace
kekuma fa menene matsayinki yanzu?
ummulkhairi tayi murmushi tace
nima nayi imani da ubangijin musulunci
nantake badi'atul nauwara ta mikawa ummulkhairi
wannan littafi tace
inason gaba daya jama'ata ki shigar dasu cikin wannan
addini mai girma
kuma ki koyar dasu komai na cikinsa
nantake badi'atul nauwara tayiwa jama'ar ta sallama
sannan ta kama d0kinta ta hau
harta yunkura zata tafi sai ummulkhairi ta yi sauri t ruko
dokin ta dubeta tace
ya shugabata ki zamo mai juriya da hakuri aduk halin da
kika tsinci kanki aciki
ki sani cewa ubangijin da kikayi imani dashi
ayanzu zai jarraba ki da tsananin wuya domin yaga iya
karfin imaninki
lallai masu hakuri suna tareda nasara
koda jin wannan batu sai badi'atul tayi murmushi tace
ku tayani addu'ar samun nasara domin kashe wwannan
muguwar macijiya ne kadai zaisa
gaba daya jama'ar dake nahiyar mu da sauran nahiyoyi
suyi imani da wannan addini na gaskiya
tana gama fadin haka saita kada linzamin dokinta ta juya
da baya tana mai zaburarsa. da gudu
ta fice daga cikin birnin gaba daya
alokacin da ummulkhairi da sauran jama'ar garin suka
bita da kallo
tun suna hangota harsaida ta kure musu da gani suka
daina hangota yazamana cewa sai kurar dokinta
lokacin da sarki shamsal tareda boka daizur suka sami
nasarar tsira da rayuwarsu
daga cikin tekun da kyar da sidin goshi akan wannan
katako
saida katakon yayi tafiyar sa'a uku da rabi dasu
sannan ya kawo su bakin gabar teku
dukkannin su sun galabaita ainun
sakamakon tsananin galabaitar da sukayine tasa barci ya
sace su basu sani ba
ruwa na watsosu bakin gabar tekun sai sarki shamsal ya
fara farfadowa daga barcin
koda ya bude idanunsa yaga boka daizur nata shara barci
bai farkaba ssai nantake dabara ta fado masa yace
yauwa yanzu tunda boka daizur bai farkaba zanyi amfani
da wannan damar na dauko madubin tsafinsa
na duba domin naga halin da kasata take ciki
shin wazirina ya ruke mini amanata da nabar masa kuma
awane hali dana yarima zainur yake
gama aiyana hakan keda wuya sai sarki shamsal ya
zura hannunsa acikin aljihun boka daizur ya dauko
madubin tsafinsa
ya shafeshi da hannunsa na hagu
nantake madubin ya nuna masa duk aabinda ya faru
tundaga ranar da suka baro kasar
da yadda yarima zainur ya shirya juyin mulki ya kashe
gaba daya makusantar sarki shamsal
ya hada kai da sauran 'yan majalisar yaci gaba da tafiyar
da harkokin mulkin son zuciya fiye da wanda yakeyi
sannan kuma
yazamana cewa sama da mutum dubu hamsin ne
suka hallaka sannan kuma rabin gidan sarautar ya ruguje
amma yarima zainur da mukarrabansa babu mutumin
daya hallaka daga cikinsu
koda gama ganin wannan al'amarin
sai zuciyar sarki shamsal ya fara tafarfasa kamar zata
kone
donhaka baisan sa'adda ta kurma uban ihuba
karfin ihun nasane ya tashi boka daizu gada barcin da
yakeyi
boka daizur ya farka afirgice alokacin daya ji kamar
kunnensa
zai dode ya mike zumbur
kafin yayi wani yunkuri sai sarki shamsal yayi wuf ta zare
takobinsa
ta dora kaifinta akan makoshinsa ya dubeshi jiki na
tsuma yace
saboda me ka yaudareni kaki gaya mini gaskiyar abinda
yake faruwa abirnina?
ashe dana yarima zainur yayi juyin mulki ya kashe duk
makusantana masu biyayya agareni
ba tareda fargabar komaiba boka daizur ya sa hannunsa
ya ture takobin sarki shamsal daga wuyansa ya dubeshi
afusace yace
wanene ya gaya maka cewa ana hada gudu da susa duka
alokaci daya ai sai ayi biyu babu
masifar dake gabanka ta wannan yaro tafi ta barnar da
danka yayi maka
tunda aduk sa'adda ka koma gida zaka iya gyara duk
barnar da yayi maka
ka dawo da komai daidai kamar yadda ka tafi ka barshi
amma idan kayi sakaci wannan yaro hatyan ya tsira da
rayuwarsa
to kanaji kana gani zaizo har masarautarka
yacika da yaki kuma yayi maka kisan gilla
koda jin wannan batu sai gardama ta karke
atsakanin sarki shamsal da boka daizur sukayita gardama
da cacar baki
har ran sarki shamsal ya baci
baisan sa'adda ya fusata ba ainun ya shammaci boka
daizur ya gabza masa naushi a wuya
saboda karfin naushin saida boka daizur ya kife kasa
sumamme
ko motsin kirki baiyiba sai kawai sarki shamsal ya juya
ya nufi hanyar da zata kaishi birnin sa yabar boka daizur
akwance
agabar teku tamkar gawa
sarki shamsal baisan sa'adda ya rinka falfala guduba
acikin daji yana sauri burinsa kawai shine
yaga ya isa birnin sa domin ya kawar da bakin ccikin
zuciyar sa
abinka da wanda ya saba shafe kawanaki yana gudu
saigashi tafiyar tasa tanayin sauri burinsa kawai shine
yaga ya iso birninsa saiya gaji ainun sannan yake tsayawa
ya huta ko ya yada zango
hakadai yaci gaba da wannan gudu ba sassauci
har tsawon kwanaki sannan ya fara hango birninsa
daga can nesa al'amarin daya sa ya kara aimi kenan
domin ta iso
ashirinsa kai tsaye kawai kai tsaye zai wuce izuwa fadarsa
kuma yana isa zai hau dakarunsa da sara da suka
daduk wanda ya baiwa yarima zainur goyon baya yayi
juyin mulki
sannan ya kamo yarima zainur din yayi masa kisan gilla
agaban kowa domin sauran 'yan majalisar tasama
susan cewa ba sassauci ga duk wanda ya bada hadin kai
awannan juyin mulki da akayi alokacin da baya nan
koda sarki shamsal ya iso kan wata gada wacce
akayita asaman wani rami mai zurfi wanda dagashi
sai kofar shiga birninsa ya ci gaba da gudu akan gasar
tamkar zai tashi sama
yana isowa tsakiyar gadar ne
yaji birnin gaba daya ya kama girgiza aikuwa
sai gadarma ta fara tangal tangal zai fado kasan ramin
saiyai wuf ya cafo gadar ya fara reto akan gadar
alokacin da akaci gaba da yin girgizar kasar itama gadar
ta kama rawa tana reto
tana neman fadowa kasa cikin ramin
al'amarin daya dugunzuma hankankalin sarki shamsal
kenan
domin ya fahimci cewar duk ma abinda ke faruwa
uwar macizai ce ta sake motsawa idan kuwa taci gaba da
motsi
to yanaji yana gani zai mutu akasan wannan rami ba
tareda yaje tayi abinda yazo yiba
koda ayyana hakan sai takaici da nadama suka kamashi
yace aransa
yanzu dai gashi nida kaina na taso abinda zai zama ajalina
gamida rushewar duniya gaba daya kawai
saboda son zuciyata da son rayuwar duniya
tabbas zanyi biyu babu inda na dauki shawarar boka
daizur ban taho nan ba da yanzu
san iya saka shi ya tsayar da uwar macizai
koda sarki shamsal yazonan atunaninsa sai hankankalinsa
ya sake dugunzuma
saboda
asannan ne ya tuna cewa ai bayan ya gama duba
madubin tsafin na boka daizur cikin ruwa ya cillashi
koda boka daizur ya farfado daga suman da yayi
sakamakon naushin da yayi masa bazai iya tsayarda uwar
macizai ba
wɑɳɳɑɳ รɦiɳɛ ɑɓiɳɗɑ yɑ Բɑʀu gɑ รɑʀki รɦɑɱรɑʆ
ɓɑyɑɳ yɑyi kuรkuʀɛɳ รɑɓɑwɑ uɱɑʀɳiɳ ɓѳkɑɳรɑ
LIKE AND COMMENT IS OUR ENCOURAGEMENT
.
Anan muka kawo karshen littafi na takwas 8
In Allah ya kamu gobe zamu dora da na tara 9

.
Kafinnan dai nidinne Shuraih Usman
Inkiya 99%
www.facebook.com/hausaebooks

Related Posts

There is no other posts in this category.

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "TARKON MUTUWA littafi na takwas 8 complet"

Post a comment