+2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria

Download and read free hausa novels

ABOKAI littafi na biyu 2 part 5

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 5
.
Kwamishina ya katsesa ta hanyar daga mai hannu yace "ka same ni a ofishina yanzu" yana gama fadin haka ya fice daga magarkaman,
Cikin fushi Acp kamalu ya dubi dan ta'adda sidi dake zaune yana murmushin mugunta yace "naso ace na sameka da wannan alburushi, ka godema Allah daya turo kwamishina ya sa hannuna ya kuskureka,"
.
"Shin a tunaninka me yasa kwamishina ya hanaka hallakani, nasan zakai zaton ko shima dan hannuna ne, A'a kawai de yarana ne sukai aikinsu na tabbata nan da awanni ashirin da hudu zan fice daga kazamin ofishin nan naku cikin girmamawa"
Dan ta'adda sidi ya fadi hallau murmushin mugunta na shimfide akan fuskarsa
.
Zuciyar acp kamalu ta fara tafarfasa, ma'aunin fusatarsa takai 100% cikin fushi ya fice daga magarmakan don ko muddin ya tsaya ya cigaba da sauraren maganganun da dan' ta'addan ke fada masa wayanda sukafi madaci daci a zuciyarsa zai iya bindige dan ta'addan har lahira,
.
____
"Menene amfaninsa garemu da kuma Al'umma yallabai, mutumin daya kasance bara gurbi bashi da buri da ya wuci daukan rayukan al'umma, dan ta'adda fa kenan yallabai yayi kisa cikin mutane, shin me ne alfanun kareshi"
Acp kamalu yafadi cikin salama yana fuskantar kwamishina Abdullahi makeri
.
"Bawai na hanaka kasheshi bane So nake kafin ka kasheshi ka kalli wannan majigin" kwamishina ya fada lokacin daya mikawa acp kamalu wayan dake hannunsa
Acp kamalu ya karbi wayar, yana kai dubansa kan fuskar wayarne yayi arba da babban tashin hankalin da baiyi tsammani faruwansa ba,,
Daliban makarantar government College ne rututu a cikin makeken daki, dayawa daga cikin daliban babu abunda suke sai kuka,
A zagaye da daliban wasu mutane ne cikin bakaken kaya sun rufe fuskokinsu da bakin kyalle idanuwansu kadai ake iya gani, mutanen suna rike da dogayen bindigogi kirar AK47 a hannuwansu, daya daga cikin mutanen ya fito tsakiyan dakin ya tsaya ya fara kalle-kalle yace
"Daliban makarantar government College keffi ne muka kwamuso. A bisa kama mana shugaba da hukuma tayi, ku hukuma kui sani cewa kun taro babban tashin hankalin da bata da ranan karewa, " dan ta'addan na zuwa nan a maganarsa sai ya kamo dalibi daya daga cikin daliban dake zazzaune suna kuka ya dora bakin bindigarsa a kan saurayin yace "mun baku nan da sa'o'I ashirin da hudu ku sako mana shugabanmu SIDI in ko ba haka ba, zamu kashe daliban nan duka," yana gama fadin haka ya danna kunamar bindigarsa, nan take karar fitar Alburushi ta karade dakin, saurayin dalibin dake gabansa ya fadi kasa matacce gefen kansa a fashe, jini na bulbulowa ta cikin kan
.
Koda daliban dake cikin dakin sukaga haka sai dukkansu suka gigice, zuciyoyinsu ya fara dukan tara-tara, tsananin tsoro,firgici ya lullubesu, cikin kankanin lokaci Dakin ya hautsine da ihu gamida kukan dalibai,
.
Dan ta'addan daya kashe dalibin ya dakawa daliban tsawa yace "shut up"
A matukar firgice daliban suka hadiye kukansu hawaye na kwaranya daga idanuwansu,
"Wannan fansa ce, fansar kashe dan uwana da kukai, izan har baku sako mana shugabanmu nan da awanni ashirin da hudu ba kamar yadda na fadi sai na kashe dukkan daliban nan na aiko maku da gawarwakinsu" dan ta'addan ya fada sannan ya fice daga dakin.
_____
"Inna lillahi wa'inna ilaihii ra ji'uun," acp kamalu ya fadi, lokaci guda gumi ya fara karyo masa, ya ciro hankicin ya share gumin daya karyo mashi,
Kwamshina yace "A jiya da daddare ne aka saka video din a youtube, nima constable Ubaidu ne ya nuna min, dazu da safe, nasan yanzu kusan dukkan mutanen kasannan sun kalli video din nan"
.
"Yanzu yallabai menene mafuta," acp kamalu ya tambayi kwamishina
"Ba maganan gaggawa bane,dole sai mun zauna da manyan kasannan anyi shawara, kasancewar makarantar ba gama gari bace, Daliban ma da akai garkuwa dasu yawancinsu ba yan jihar nasarawa bane , "
Kwamishina ya bashi amsa yana mai mikewa tsaye ya fice daga ofishin,,,
___
Iyayen Daliban da yan ta'addan sukai garkuwa da su, sun shiga wani irin hali yayin da mummunan labarin ya riskesu sun koka sosai gameda tsaron makarantar, da yawa daga cikin iyayen daliban sun fito kafar yada labarai suna masu rokon gwamnati data taimaka ta saki dan ta'addan
.
Har yanzu mutane sun kasa gane fuskan dalibin da dan ta'addan nan ya kashe, sakamakon dan duhu duhu da hoton video din yayi,
.
Wannan mummunan lamari mara dadin saurare ita ta sanya cikin gaggawa shugaban kasan Nijeriya Umar Bahaje ya dawo gida Nijeriya,
Saukarsa a filin jirgi keda wuya yan jarida sukai masa maraba da tarin tambayoyinsu wayanda yawanci duk akan batan daliban makarantar government college ne, "yallabai wani mataki za'a dauka gameda batan yaran makaranta"
"Yallabai za'a fanshe su da dan'ataddan kenan"
"Yallabai shin an gano ko waye dalibin da yan ta'addan suka kashe?"
Irin wayannan tambayoyi da makamantansu sune yan jaridan sukaita korawa shugaban kasa su
Shugaban kasa umar bahaje ya gyara zaman farin tabaransa ya dubi yan jaridan yace dasu "dafarko dai Ina mika sakon ta'aziyata ga iyayen dalibin da ya rasa ransa, duk da haryanzu ba'asan ko waye ba, da yardan Allah nan da sa'o'I kalilan zamu dawo ma iyayen yara, da 'yayansu cikin koshin lafiya,"
Yana gama fadin hakan yai wuce warsa inda jami'an tsaro suka take masa baya
***=======***
Yan ta'addan ne su Uku a zazzaune saman manyan lallausan kujerun da suka bada gudumma wajen kawata tangamemen falon,
Hankulansu ya tafi ga tangamemen talabijin bango dake manne a jikin bangon falon, inda aka hasko shugaban kasar nijeriya yana korawa yan jaridu bayanai,,
"Lallai shugaban kasa ya yanke kyakkyawan shawara, da ya yarda zai sako Oga, "
Audu ya fada yana duban jagwa,
Jagwa yayi tsaki gami da yamutse fuska yace "ai dolensu su sako oga, ku suna so ko basa so"
"Kwantan bauna zamuyi masu, da zarar sun sako oga mu dana wa la'anannen dan sandan nan tarko, dun kuwa sai mun fanshe rayuwar dan 'uwanmu"
Aba yawo ya fada cikin bacin rai
Audu ya jijjiga kai yai kwafa ,

ABOKAI littafi na biyu 2 part 4

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 4
.
***=====****
Makarantar government college na dauke da sashi-sashi gamida bangare-bangare, kasantuwar makarantar ta kwanace yasa aka gina gidaje da dama aka kebancewa malaman makarantar,
Hatta gidan shugaban makarantar ma a cikin makarantar take kuma bata da banbanci da sauran gidajen
.

Shugaban makarantar government college mai suna malam yahuza ne kwance a saman tangamemiyar gado mai sanda, dattijon ya kasance baki ne ya saki baki yana surnano munshari, bakajin sautin komai a cikin madaidaicin dakin face sautin munsharinsa mara dadin sauraro
,
Bayan shudewan kankanin lokaci, wayar salulan dake ajjiye a saman hannun gadon da dattijon ke kwance akai ta fara burari sautin wakar mamman shata na futa daga cikinta,
.
Cikin kasala dattijon mai suna Yahuza ya mike zaune yana mai mika,
mika hannu yayi ya dau wayar tasa, ya danna sannan ya kara a kunnensa, "hello me yafaru ne muhammed da sanyin safiyarnan, ka danno min kira, "
Dattijo yahuza ya fada yana mutsistsika idanuwansa,
Lokaci guda dattijon ya zazzare idanuwa alamar kaduwa cikin daga murya yace "Inna lillahi wa'inna ilaihirraj'un , yaushe abun ya faru" ya fada sannan ya sauko daga kan katifar , alamun baccin dake tunkushe a idanuwansa da zu sukai fitar burgu,
.
"Okey muhammed ga ninan zuwa yanzu" dattijo yahuza ya fadi yana mai ajjiye wayar akas,
Cikin sauri ya shirya cikin manyan kaya zariya, ya fice daga dakin,
Yana fitowa daga cikin dakin ya nufi wani sashe na makarantar cikin sauri
Irin yanayin yadda yake tafiyar ma ya isa ya fahimtar da mutun cewa a matukar razane dattijon yake,
______
"Yallabai ina kwance a gidana shugaban dalibai (headboy) ya kirani a waya yake sanar dani wai daliban Gongola house da benue house an tashi da safiyarnan ba'a gansu ba daga siniyoyin har juniyoyin,
Ban yi kasa a guiwa ba na kiraka na sanar dakai"
Bakin mutumin da ke zaune akan kujera ya fada yana fuskantar malam yahuza,
.
"Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'uun, wannan masifa dame tai kama, Allah kadai yasan ko me ya faru da daliban nan, amma yanzu bamuga ta zama ba, dole mu sanarwa da jami'ai yanzu don asan halin da alke ciki"
Dattijo ya fadi yana duban mr mohammed dake zaune a gabansa, lokaci guda ya ciro wayar salulan dake aljihunsa ya yayi dan latse-latse a wayar kana ya kara a kunnensa
____
Cikin kankanin lokaci Labarin batan yaran makarantar government college keffi ya karade ilahirin Nijeriya tamkar ruwan dare, ya kasance ko wata gidan talabijin, gamida gidan rediyo labarin suke, hatta a kafar sadarwa ta zamani (social media) sai da mutane sukai ta yayata labarin
Inda wasu mutanen 'yan kara wa labari gishiri ke cewa Aljanu ne suka kwashe yaran, dama tun can ana rade-radin akwai aljanu da gwaigwai a makarantar,
Irin wayannan labarai na shaci fadi suke ta zagaye kafar sadarwa,gidajen talabijin hade da gidjen rediyo
.
Acp kamalu dan jihar Zamfara ne acan yayi karatun islama da na boko har ya kaiga shiga jami'a duk da mahaifinsa malam Koje ba wani karfi ne da shi ba amma hakan bai hana ya dage sosai ganin ya samawa kamalu karatun boko ba, har dannasa kamalu wanda ya kasance mai matukar hazaka, ya kai ga zama dan sanda mai babban mukami,
.
Tun daga lokacin da kamalu ya fara aiki sai ya kasance yana tafiyar da aikinsa cikin gaskiya, baya taba sassauta wa masu laifi, ko karban Rashawa,
Irin yanayin jajircewarsa cikin aikin yasanya manyansa suka runga sauya masa wuraren aiki ,
.
Sanin irin kwazonsa da jajircewarsa akan aikin nasa ya sanya aka damka masa kes din sidi kashe babba kashe yaro, da yaransa inda aka daura mai alhakin kamosu,,,
___
Acp kamalu na zaune cikin ofishinsa yana nazarin wasu takardu,yana sanye ne da shudin rigan kanti mai dogon hannu hade da farar wandon jeans, ya maida hankali sosai wurin nazarin takardan dake ajjiye kan teburin daya tokare gabashi da yamman ofishin,
.
Kofan ofishin ne ya bude wani tsamurarren dan sanda ya shigo yana zuwa ya sarawa Acp kamalu, yace "sir dan ta'addan nan ba karamin dan ta'adda bane babu irin azabar damu gana masa ba amma yaki fada mana wanda ke basu aiki, yanzu haka ya na can a kwance a magarkama sai dariya yake tamkar zautacce,"
,
Acpn kamalu ya mike tsaye batare daya dubi tsamurarren kurtun dan sandan ba yace mai "ok ku koma bakin aikinku kawai bazan je na duba shi"
"Ok sir" dan sandan ya fadi sannan ya juya ya fice daga dakin,
,
Fitansa ke da wuya acp kamalu ya fito daga ofishin nasa ya nufi bangaren magarkama kai tsaye ya wuce magarkamar da aka kulle dan ta'adda sidi a ciki,
Yana shiga yayi arba da dan ta'addan shimfide a kasa yana murmushi, Sidi ya dago kai ya dubi acp kamalu yace "jiya kace muddin ban sauya ra'ayi ba zaka kawar dani a yau, shin kazo ka kawar danin ne"
,
Acp kamalu ya jawo wata kujeran karfe da ke girke a cikin magarkaman, ya zauna ya dubi sidi "har yanzu ina kan bakata, dun haka in kana da wasiyya maza ka fadota tun kafin harsashin bindigata ta ratsa cikin kwakkwalwarka" yafada alokacin daya zaro karamar bindiga daga mararsa,
.
Dan ta'adda sidi ya bushe da dariya, yana yi yana kyakyatawa wannan dariyar itace ta fusata acp kamalu, cikin fushi ya dirkawa dan ta'adda sidi Alburushi a kafan hagunsa,
'
Tsananin zafin da ta ziyarci kafan dan ta'addan ne ta sanya babu shiri ya kwarma ihu, wacce tai ansakuwwa a ofishin yan sandan baki daya,,
Har yanzu bakin bindigar Acp kamalu yana fuskantar Sidi, "ai ba lokaci daya zan kasheka ba, sai na jiyar dakai dacin mutuwa kafin na hallaka ka"
Acp kamalu ya fadi dan ya tsantsa na kokarin danna kunamar bindigar
.
"Kasani cewa muddin ka kashe ni to ka tsokano tsuliyan dodo ne, domin kuwa yarana baza su taba bari ku zauna lafiya ba, iyanzu da kuka kamani ma nasan ba shiru zasuyi "
Dan ta'adda sidi ya fadi cikin yanayin mugun hali,
.
"Kamar yadda muka kamaka muka kasheka, suma haka zamu kamosu mu kashe shu," acp kamalu ya fadi haryanzu bakin bindigarsa na fuskantar dan ta'addan dake kwance magashiyan akas, kafarsa ta hagu tana bulbulo da jini,
.
Dan ta'dda sidi ya cije baki sakamakon radadin da kafar tasa ke masa wanda yake haurawa har tsakiyan kansa, yaja doguwar nishi yace "shawara nake baka kada ka kasheni, kada ka kasheni"
,
Acp kamalu yayi tsaki "shawarar taka ta banza,amshi wannan"
Yafadi yana mai kokarin sakin Alburushi daga bindigarsa,
Kwamishina Abdullahi makeri ne ya shigo magarkaman a guje Dede lokacin da acp kamalu ke kokarin kashe dan ta'addan,
Cikin kankanin lokaci ya fahimci abun da mataimakin nasa ke kokarin yi hakan yasa ya kariso a guje don ya tsaida matemakin nasa,,
Yana karasowa wurin ne Karar fitar alburushi gamida ihun dan ta'adda sidi suka karade magarkaman..
__
Kusan abubuwa uku ne suka faru lokaci daya,
Ihun da dan ta'adda sidi ya kwarma, danna kunamar bindiga da Acp kamalu yayi gamida sauri da kwamishina yayi ya ya canja akalar hannun acp kamalu ta fuskanci wani sashi daban na magarkamar ta hanyar dukan hannun da yayi da kafarsa
.
Dan ta'adda sidi ya sadakar cewa ya mutu, a firgice ya dafe gefen cikinsa, amma cikin mamaki sai yaji babu wani radadin daya ziyarci jikinsa, yayi karfin hali ya mike zaune yana dudduba jikinsa ko zaiga inda acp kamalu ya harbesa, amma babu..
.
A fusace acp kamalu ya juyo don ganin wanda yai doki hannunsa
Lokaci guda ya kame sannan ya sarawa kwamishina, yace "yallabai naga babu amfanin ajjiyesa tunda yaki fadan waye ubangidan sa shine nai.."
Kwamishina ya katsesa ta hanyar daga mai hannu yace "ka same ni a ofishina yanzu"

ABOKAI littafi na biyu 2 part 3

ABOKAI
Littafi na biyu 2
Marubuci Shuraih Usman
Typing:- by Shuraih Usman
© Shuraih 99% 2019
Part 3
.
Agurguje daliban suka karisa fita daga dakin,
*****=====******
Lokaci guda haidar,jibrin,Hassan da mansir suka mike daga wurin Aliyu suka fara dumfarar yan ta'addan, izan ka kalli fuskokinsu zaka tsinkayi babban tashin hankali shimfide akan ta hakanan kuwwan fansa na tashi daga cikin idanuwansu,
.
Yan ta'addan biyu suka seta bakin bindigoginsu yana fuskantar ABOKAN,
"Ku tsaya a inda kuke ko yanzun nan mu aika daku,inda na aika dan uwanku" Audu ya fadi yana kokarin sakin harsashi
Cikin zafin nama silli ya wafce bindigarsa lokacin daya fahimci kudurinsa yace "haba Audu so kake ka batamana shiri, bafa kisa ya kawo mu nan ba, "
.
Ran Audu a bace ya dubi silli yace "dan ubanka bakaga su neman kashe mu suke ba, zuwa garemu sukefa" Silli ya juya ya dubi Abokan har yanzu suna kokarin kusanto inda suke,
Ba shiri Audu da silli suka fara ja da baya don sunyi matukar razana da yanayin da suka tsinkaya a fuskar ABOKAN
.
Haidar,jibrin,hassan da Mansir tafiya suke idanuwansu a rufe basa ganin komai face yan ta'addan nan, babu abunda ke tashi a zuciyoyinsu face wutar fansa, ....
Haka suka cigaba da nufar yan ta'addan da bakar fuska, duk da kashedi gami da barazanar da yan ta'addan ke yi masu hakan bai sa sun tsaya ba,,,
.
"HhhhHhhhhhjjjjj" sautin nishi ya fara tashi daga bayan Abokan, cikin sauri Abokan suka juya lokacin da suka jiyo sautin ko tantama basa yi sautin na fitowa ne daga jikin Abokinsu Aliyu dake kwance a kasan dakin,,,,
Da gudu suka isa wurinsa, suka iske idanuwansa a bude hancinsa na surnano nishi sama-sama
.
Mansir ya mike ya debo ruwa a karamin kofi ya zuba wa Aliyu aka, sannan ya bashi ya sha,
Duk wannan Abu dake faruwa yan ta'addan biyu suna daga nesa a tsaye, hakanan daliban dakin ma suna takure a gefe daya, zuciyoyinsu cike fal da tsoron shedanun yan ta'addan nan,,
.
Audu ya fisge bindigarsa daga hannun Silli sannan ya nufi wurin Abokan wayanda suke durkushe,
Hasan ya tallabo bayan Aliyu suka zaunar da shi, har yanzu bai gama dawowa cikin hayyancinsa ba,
"Aliyu kana jina? Nine Aboki" haidar ya fadi yana jujjuya tafin hannunsa a gaban fuskar Aliyu
Kwatsam ba zato ba tsammani sai gani Abokan sukai an janye Aliyu daga zaunen da yake, an daga shi sama,
.
"Kai wai su waye ku ne? Me mu kai maku ne " hasan ya fadi cikin muryan bacin rai
Audu ya zaro doguwar wuka daga mararsa ya aza a wuyan Aliyu sannan yace "Mune Guguwan Annoba, anai mana inkiya da Gobara daga Kogi, mune muka gagari nahiyar Africa, ba ku mana komai ba, hakanan ba cutar da ku muka zo yi ba amma muddin ku kayi taurin kai kuka bin umarninmu to dukkanku sai mun hallakaku sannan mu aiwatar da kudurinmu, kuma takan Dan uwan kunnan zamu fara"
.
"Me kuke son mui maku, dun Allah kada ku kashe shi koma menene zamuyi maku" jibrin ya fadi hawaye na bin kumatunsa
Silli ya kariso wurin
Audu ya dubeshi yace " a fara aiki silli"
Rufe bakin Audu ke da wuya Silli ya dubi daliban yace da su " ku wuce mu tafi"
Ba musu daliban dake a matukar tsorace wayanda adadinsu yakai ashirin suka nufi kofan dakin, ,,,
Suna zuwa bakin kofan ne suka ci karo da abinda ya sanya da yawa daga cikinsu sakin fitsari a wando,
.
Doguwar bakin bindigace ta faro danno kai cikin dakin sannan Aba yawo ya shigo dakin fuskarsa tamau ya dubi daliban dake bakin kofan,ya daka masu tsawa "dan ubanku baza kuyi sauri ba"
A firgice cikin tsananin tsorata daliban suka fita daga dakin
Suna futowa suka yi arangama da wasu daliban,,
.
Audu ya saki Aliyu cikin matukar galabaituwa Aliyu ya sulale zai fadi kasa, kafin ya kai kasan haidar da mansir suka dago shi, haidar ne yayi goho mansir ya dora masa Aliyu a bayansa sannan suka fice daga dakin...
....
Cikin kankanin lokaci yan ta'addan suka yashe gaba dayan dakunan kwanan dalibai na GONGOLA HOUSE da BENUE HOUSE, cikin sa'a basu samu wani mishkila
.
Gungun dalibai ne da adadinsu yakai dari biyu 200 hade da shaidanun yan ta'adda hudu ke ratsa cikin dokar dajin, dajin yayi tsit sakamakon dare daya tsala in kadauke kukan kananun kwari dana tsuntsaye gamida karar taka busassun ganyayyaki da daliban ke mutanen ke takawa babu wani sauti dake tashi,,,,
.
Doguwar tafiyace ta kai su ga inda yan ta'addan suka faka doguwan motarsu har a lokacin Abokan biyar na tare da juna zuciyoyinsu a cike da bakin ciki, bawai kwashe su da yan ta'addan sukai bane ke damunsu , Halin da dan uwansu,Amininsu kuma Abokinsu Aliyu ya fada shine babban abun dayai matukar tayar musu da hankali
.
Kafin wannan daren da Abokan suka kirashi da MUMMUNAN DARE Abokan sun kasance suna rayuwa cikin farin ciki, Annushwa, gamida fara'a
Amma bayan wanzuwar daren sai farincikin dake rayuwansu ta juye izuwa bakin ciki, Annashwar da suke wa junansu ta rikide izuwa ruwan hawaye,,, akoda yaushe fuskokinsu cikin fara'a take, da yawa daga cikin dalibai sukan ce da su "ABOTAR ku tana birgemu,"
"Ina ma ina daga cikinku"
"Ban taba ganin ABOKAI irin ku ba Arayuwata"
Irin wayannan maganganu dama wasu sune dalibai,malamai da ma'aikatan makarantar ke cewa da su
.
Jagwa dake gaban daliban ya nufi bayan doguwar motar ya bude murufinta, yai wa daliban inkiya da hannu kan cewa su shige cikin motar,
...
****=====****
Sidi kashe babba kashe yaro asalinsa dan Adamawa ne, tun yana shekarun yarinta ya shiga Duniya neman kudi, A lokacin bai fi shekaru goma sha biyar ba, ya kware sosai wajen sane da yanke aljihun mutane, ya yawata gari gari a sassan Nijeriya, kafin daga baya ya koma fashi da makami inda ya hada gungun yaransa su biyar wayanda suma duk a yawon duniyar suka hadu,
.
SIDI kashe babba kashe yaro yayi ta'adddanci babu adadi a kasan Nijeriya , a ka'idansa muddin aka futa aiki to babu babba babu yaro duk wanda ya kawo wargi kashe sa ake, hasalima ta nanne ya samo sunan KASHE BABBA KASHE YARO
.
____
Karamin dakine mai wadataccen fadi, hasken kwayayen lantarki ya karade dakin,
Acp kamalune zaune kan kujera, a gabansa kuwa dan ta'adda Sidi kashe babba kashe yarone,
Acp kamalu yaja doguwar numfashi ya idanuwansa na kan dan ta'addan da kamanninsa suka canja yace "kana baiwa kanka wahala kana kana bama shari'a wahala, izan da ace ka sanar damu abubuwan da muke bukatan ji daga gareka da tuni yanzu haka kana magarkama, amma taurin kanka ya hanaka, kasani nan da gobe muddin baka fada mana wa ke saka ku aikata ta'addanci ba, to ni da kaina zan harbeka"
.
Koda dan ta'adda sidi yaji haka sai ya bushe da dariya sai da ya dau lokaci mai tsayi yana dariyar, sannan yai shiru, cikin dakewa yace "me nene mutuwa, kai kake tsoronta bani ba, don ni kullum acikinta nake, yan sanda ku ke tsoron mutuwa amma mu yan ta'adda bama tsoronta hasalima bamu santa ba"
.
"Ai ko gobe zan dandana maka dacin mutuwa" Acp na kamalu ya fadi sannan ya mike tsaye ya nufi kofan ficewa daga dakin, sai da yakai bakin kofar dakin ya juyo ya dubi dan ta'adda sidi yace "na baka daga yau zuwa gobe, ka canja shawara domin kuwa babu makawa gobe sai na alburusheka"
Yana gama fadin hakan ya fice daga dakin,
Dan ta'adda sidi ya sake fashewa da dariya a karo na biyu ya dau tsawon lokaci yana kyakyatawa, lokaci guda ya tsaida dariyan da yake ya dauki wani sanda dake ajjiye a gefensa da taimakon sandan ya mike tsayi, cikin dingisawa ya nufi gabashin kusurwan dakin, ya daga kai sama yana kallon CCTV camera dake like a saman bangon dakin, yayi murmushi mai ciwo sannan yace "ku yan tsinannu da sannu zakuyi nadamar abun da kuka aikata mana,"
......
Jami'an yan sanda biyu dake zaune a cikin ofishin acp kamalu suna kallon abun dake faruwa tsakanin Acp kamalu da dan ta'adda sidi a cikin na'ura mai kwakwalwa, suka jinjina kai
"Kana ganin yallabai zai iya kashe shin " jami'in dake gefen dama ya fadi yana duban dayan dan sandan
"Ai muddin yallabai ya fadi magana to se ya cikata, hala baka da labarin irin jajircewansa, sabida gaskiyansa hade da kwazonsa a aiki yasa ake tayi masa canje canjen wurin aiki, kuma duk garin da yaje sai ya share yan iskan cikinta ya zuba su cikin kwandon shara, bindige dan ta'adda a wurinsa ba wani abune mai wahala ba,"
Dan sandan dake gefen hagu ya fadi yana kokarin mikewa tsaye
"Tab lallai lamarinsa ya girmama"

Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter