Results

DAN ADAM part 3

"Zan kiraki karki k'ara kirana." A hankali yanda bazai ji ba, wannan muryar ta k'ara kashe Raihana da dadi. (Wa'iyazubillah) ji ta yi kamar ta shiga wayar ta rukunkumeta, dole ta yi mata sallama ba don taso hakan ba.
     Deen ya karaso, ya kammala shirinsa zai koma ofis, ya dubeta lokacin da ta ke k'ok'arin ajiye wayar. Suka yiwa juna murmushi.
  "Har zaka koma?"
  Ta tambaya cikin kankan da murya.
Ya gyada kai.
"Zan koma, ga shi basu dawo ba kamar kada na tafi nayi zaman tayaki hira."
   Ta kasa jurewa ta dubeshi fuskarta na nuni da tsantsan farin ciki.
  "Wai don Allah kaine kuwa? Ashe akwai ranar da za ka nuna kulawarka a kaina har haka?" Sai kuma ta yi shiru a tunaninta ta yi azar6a6i, amma sai bai bata kunya ba ya amsa.
   "Idan ban kula da ke ba ai bazan iya kula da kaina ba kenan Dija, bakisan yanda nake jinki a zuciyata ba wallahi."
  Ta lumshe ido don jin dadin maganarsa gami da murmusawa.
  "Nagode Deen, yanzu kayi hakuri ka tafi ofis, ai idan ka dawo ina gidan."
   Ya nok'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro.
  "Aa." Sukayi dariya. Ya kar6i lambar wayarta don a baya ba shi da, sannan sukayi sallama. Ai yana fita ta hau doka tsallen murna, daga wancan kujerar sai wannan tana yi tana dariya.
   Ba ita ta nutsu ba saida su Munira suka dawo bayan la'asar alokacin har kiranta saida ya yi suka sha hira. A gefe Raihana na faman jaddadamata cewa ta rik'e amana ta cika alk'awari ta yanar gizo. Banda toh babu abinda ta ke cewa a fili kuwa ta ja tsaki don haushi.
                   ***   ***   ***
                       ABUJA
 
   KB ya ji haushi matuk'a akan abinda Faruk ya yi mishi, kuma ya tabbatar muddin ya ce zaiyi wani yunkurin na daukar fansa, to fa Faruk ba karamin aikinsa bane ya tona mishi asiri. A karshe ma sai ya ga menene abin tayar da jijiyoyin wuya akan wacce yasan ya ketare a komai, saidai ya fahimci tabbas akwai wani abun a zuciyar Faruk akan Ummi. Ya yi murmushi a yayinda ya ke kwance saman kujera da misalin karfe uku na rana.
  'Baka san wacce ta dace da wacce bata dace ba Faruk, duk abina bazan ta6a ajiye 'yar aiki a matsayin matata ba. Zubda aji kawai.'
  Ya ayyana a ransa sannan ya ja tsaki a karshe ya shafi goshinsa wanda ya kumbura ya yi dariyar da shi kadai yasan manufarsa.

Misalin takwas na dare, gidan babu kowa sai kalilan cikin iyaye da kuma yan aiki, sauran duk an tafi raka Amarya Baraka gidan mijinta. Amina na hanyarta ta komawa sashensu bayan ta yi aikin da Hajiya Babba ta sanyata na watsawa gaba daya jikokin nasu ruwa da sanyamusu kayan bacci, ta gyaresu tsaf ta shafa musu hoda sannan ta barsu anan falon k'asa suna kallon(Cartoon), alokacin Faruk ya sauko da zummar neman mai kira mishi Ummi, cikin sa'a ya had'u da ita, ita kanta Amina saida gabanta ya fad'i.
  'Ina Ummi ina wannan babban goron? Tab!' Ta ayyana a ranta, a fili kuwa durkusawa ta yi ta kwashi gaisuwa ya amsa yana mai dubanta.
  "Lafiya, idan kin shiga ki cewa Ummi ta sameni a inda muka had'u jiya."
   Ta amsa da to sannan ta bar wajen, tana shiga ta tarar da ita sai faman danne-danne takeyi a wayar ita Aminan, Amina ta kwace tana jan tsaki.
  "Kefa yanzu sai ki hargitsamin ita, ya kamata ki koyi sarrafa waya sai bala'in son wayar amma babu abinda kika iya ciki."
  Sukayi dariya, Amina ta bar dariya, fuskarta ya nuna alamun damuwa da kulawa.
   "Ummi ke din kina da babban matsayi gareni wallahi, ina son don Allah ki kula ki kuma dauki dukkan abinda na gayamaki. Nasan tabbas kina son Faruk shima kuma yana sonki , saidai ki dunga tunanin ke wacece ki kama kanki. Yanzu ki tashi ki je yana kiranki, yace ki sameshi a inda ku ka had'u jiya."
   Ummi ta yi dumm ta tabbatar dukkan abinda Amina ta fad'i gaskiya ce, hakazalika kauna ce ta sanya ta kwa6arta. Ta jinjina kai tare da yin murmushi.
  "In sha Allah Anti zan yi aiki da shawararki. Daman nima ina tsoron shiga kowace matsala adalilin Yaya Faruk."
  Amina ta yi murmushin jin dadin irin wannan matsayin da ta samu wajen Ummi wacce a shekaru bai fi biyu ko daya ta bata ba.
  "Nagode Kanwata, sai kin dawo."
Daga haka Ummi ta zura hijabinta ta fita bayan ta duba babu wanda ya ganta. Kai tsaye wajen (swimming pool) na gidan ta nufa ta murda kofar ta shiga.
   Zaune ta sameshi yana waya, ya juyo yana dubanta yana cigaba da wayar, alama ya yi mata ds ta rufe kofar, hakan yasa ta juyawa gami da rufewa, itama zata fi son hakan kada wani ya iskesu tare.
   Tana kokarin durkusawa ya ja hijabinta hakan yasa ta dubansa.
  Da ido ya yi mata alama da ta zauna gefensa akan daya kujerar. Ta numfasa gabanta na dukan tara-tara ta zauna. Ko kamshin turaren Faruk ta ji, takan ji sauyi a jini da tsokarta, ballantana akai ga jin muryarsa da kuma kallonsa.
     Tunda ta zauna bata dubeshi ba, shine ma ya karkato yana amsa waya yana karewa fuskarta kallo. Ga dukkan alamu da ogansa awajen aiki ya ke magana, ganin yanda ya ke bawa mutumin girma hakazalika batu ne na kudade da wasu takardu sukeyi. Maganarsa tafi yawa da harshen turanci.  A jikinta ta ji yana kallonta, ta dan juyo ta saci kallonsa, ya kuwa kafeta da ido kafafunsa saman kujerar ya tankwashesu. Ta kauda kanta ta yi shiru, ji ta ke tamkar ba zata iya rabuwa da Faruk ba, saidai hakan dole ne agareta, ko ta karfi ko kuma ta lumana. Ta karfin kuwa, daga yan uwa da danginsa ne, wadanda a karshe zasu ci zarafinta su korata kauyensu, ta lumanar kuwa shine ta bi shawarar Antinta wanda idan har ta kiyaye to fa baza'a kai ga sauran matakan ba masu ciwo. Saida ya kammala wayar sannan ya ce.
  "Bari kiga na kashe wayoyinnan, ko waye zai k'ara nemana saidai ya hakura na kammala da iyalina ko?"
  Kanta ya yi dumm, jin kowanne kalamansa ta ke yi tamkar sun fi gwal da daham tsada a wajenta. Da a bata komai na jin dadin rayuwa ta gwammace a mallakamata Faruk a matsayin mijinta, saidai me? Wutsiyar rak'umi ta yi nesa da k'asa.
Tunaninta ya katse sa'ilin da ya dora wayoyinsa a saman cinyarta. Ta dago ta dan dubeshi fuskarsa babu alamun wasa hakan yasa ta maida kanta ga duban wayoyinsa biyu manya wadanda ta tabbatar masu tsada ne saidai hankalinta yafi karkata ga son son jin abinda zai fito daga bakinshi.
   DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  53
   Washegari kuwa tun safe mutane suka soma tafiya, yan Adamawa kaf dinsu suka fice, Gwaggo surukar Mami bata zo wannan karon ba saidai ta aikowa Mami tsaraba hakanan ta aikowa Hajiya Babba g2udunmuwa.
     Sai bayan Azahar su Mami suka soma shirin tafiya. Ummi suma sun kammala hada komai nasu ta tsinci sak'on kira daga Mami. Mamin na daki daga ita sai Ihsan wacce jin cewar zata karasa hutunta a gidan su Faruk ya sanyata kasa rufe baki don tsabar farinciki. A haka Ummi ta shiga ta riskesu, Mamin na faman kimtsawa don tafiya.
   Bayan an gaisa ta ce. "Gani Mami."
Mami ta dubeta.
   "Yauwa Ummi, anan za ki zauna har muga abinda hali ya yi, saidai bayan komawata tukunna."
  'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Shine abinda Ummi ke ambata a can kasan ranta, ta ya ya zaayi a barta a gidan su Faruk, ina laifin ma idan sun je Kano ta je koda gidan su Hajiya Mama ne ko gidan su Inna?
  'Ai ba danginki bane.' Cewar wani sashen zuciyarta. Ta ji babu yanda ta iya don yan uwannata basu ma damu da sha'aninta ba.
   "Wai bakya ji ne wani sabon wulakanci ana ta yi ma ki magana kin yiwa mutane banza kamar tsararki?"
  Maganar Ihsan kenan wacce ta maidota hayyacinta batare da shiri ba.  Ta dubi Ihsan din wacce a take ta watso mata harara kamar idanunta zasu zazzago, gaba daya bakin cikin jin cewa har Ummi itama anan zata zauna ta ke, kamar ta shak'eta haka ta ke ji, tsaki ta ja ma a karshe ta fice daga dakin cikin kunar rai.
    Ummi ta maida hankalinta ga Mami.

"Toh Mami. Allah Ya kaiku lafiya, Ya gyara lamura."
    Har cikin ran Mami ta ji dadin addu'ar.
   "Amin. Kina iya tafiya."
  Ta mike jikinta babu kwari ta fita, tana zuwa dakinsu ta fad'a saman katifa ta yi tagumi. Haka Amina wacce ta fita kai kaya mota ta shigo ta risketa.
  "Aa ya ki ka zauna, yanzu fa zasu fito."
  A sanyaye ta dubeta ta sanarmata yanda Mamin ta ce. Amina ta numfasa.
  "Allah Ya sa alheri ne ya tsayar da ke Ummi. Nidai fatana ki kiyaye dukkan nasihuna gareki, ban zama mai cutarwa gareki ba."
   Ummi ta yi yak'e tana duban Amina.
"Wallahi Anti babban ma fargabata bai wuce Ihsan ba, na tabbatar zan sha wulakanci daga gareta."
  Amina ta girgiza kai da dan murmushi saman fuskarta wanda na yak'e ne.
  "Karki damu Ummi, Allah Yana tare da ke. Kedai kiyi takatsantsan da lamura, bari naje kada su Hajiya Mama su rigani fitowa."
     Ummi ta mike sanye gami da zura hijabinta a saman riga da siket na koriyar atamfa ta bi bayanta.
     A fusace ta shiga dakin babu ko sallama, hakan yasa su Ikram, Intisar harma Anti Aisha da Rahila dubanta.
  "Ke lafiyarki kuwa? Ku ganemin yarinya kamar mai iskokai yanzu kika fita kina murnar za'a barki garin masoyinki, kin shigo kuma kina fushi, meyafaru?" Cewar Rahila kenan.
   Ihsan ta zauna gefen gado inda Aisha ke sanyawa Tahir famfas ta ja tsaki.
"Wai don Allah meyasa Mami ta ke yin haka ne? Ya zaayi don nima zan zauna anan ace itama Ummi nan zata zauna? Wannan abun ya isheni, Mami bata da masaniyar yanda na tsani yarinyarnan wallahi da bata soma cewa ta zauna inda nake ba."
   Mamaki ya bayyana a fuskokinsu.
"Sannu sarauniyar wauta, sai akace zamanku a rumfa daya yana nufin matsayinku daya? Kai wallahi har gobe banga randa kuruciya zata fita kanki ba Ihsan."
  Fadin Rahila kenan kafin ta fice daga dakin rataye da jakar kayanta.
   Dariya sauran suka sanya, Intisar ta ja rigar Ihsan kadan.
  "Kina bani mamaki, kodai kishi kikeyi don Ummi ta fiki kyau ne? Wannan tsana haka?"
  Ihsan ta yamutsa fuska, kusan ma har da hakan saidai ita kanta tasan da abu k'alilan zata fi Ummi, shi dinma wuyarta Ummin ta samu hutu kamar yanda ta ke samu. Saidai kuma ta fusata sosai da zancen Intisar. Ta mike a fusace ta fita suna mata dariya wanda hakan ba karamin k'ara rura wutar kiyayyar Ummi ya yi a ranta ba.

    Amina da Ummi sune suka taimaka wajen fidda jakunkuna, Ummi a sace sai sharar hawaye take yi don har cikin zuciyarta bata so zaman garin Abuja, ga kuma fargabar kada Faruk ya yi wani abun da zai janyo mutan gidan su fahimci manufarsa a kanta.
   Haka suka tafi banda Adnan wanda ya ce ko zai koma ba yanzu ba. Mami dai ganin bai gama hucewa ba ne yasa ta kyaleshi.
    Ummi ta juya jikinta a sanyaye zata koma ciki, Ihsan da suka hada ido harara da dallara mata, Adnan kuws murmushi ya sakarmata.
  "'Yar Abuja." Ya fada cikin tsokana, murmushin yak'e ta yi mishi. Tana shirin barin wajen ta tsinci muryar Ihsan bayan Hajiya Babba ta riga ta koma ciki tana fadin.
  "Rashin dangi ne yasa ta ke yawo daga nan zuwa can, duk dai abin mutum bazai chanja iyaye ba. Kauyen dai da ake gudu nan ne asali."
   Daga haka ta tsinci muryar Adnan yana mata sababi bayan ya kai mata bugu ta kauce. Daidai da su Intisar basu ji dadin abinda ta aikata ba.
  "Bansan halin wa kika biyo ba, don danginmu ba ma wulakanta mutum, muna girmama DAN ADAM daidai gwargwado." Cewar Intisar kenan sannan ta juya ciki ranta babu dadi.
  Haka suka watse suka bar Ihsan cike da k'ara jin haushi da tsanar Ummi a nata ganin duk a kanta akeyi mata hakan.
    Ita kuwa Ummi duk yanda ta so shigewa daki kai tsaye don kanta da ta ke ji yana sarawa ga kuma wani kuka da ya ke tahomata hakan bai samu ba sakamakon kiran da Hajiya Babba ta yi mata. Ta karasa ta durkusa cikin ladabi.
  "Gani Hajiya."
Hajiya ta dubeta fuska a sake.
"Yauwa Ummi, sai kuma kika ga an barki a wajena ko? To ina so muyi zama na tsakani da Allah da ke, daman na riga nasan da kyawawan halayenki daga bakin Madina, ki k'ara a kan hakan. Gyaranki na dakina ne sai falon sama da kuma wannan na k'asan. Sauran dakunan kuwa suna karkashin kulawar Binta. Girki daman ba aikinku bane da wanke-wanke, kinji ko? Akwai mai yi na kwanaki ma ganin bak'i da yawa yasa nake cewa ku shiga, fatan kin fahimceni?"
  Ummi ta jinjina kai, ranta ko digon farinciki babu sakamakon har lokacin ranta a tsananin 6ace ya ke.
     "Na fahimta Hajiya kuma in sha Allah zan kiyaye zan kula."
    Hajiya Babba ta ji dadin furucinta ta sakarmata murmushi.
  "Na lura dai ranki bai miki dadi ba akan zaman da za ki yi anan, karki damu, na dan lokaci ne, da zarar na sanya an samomin wata za ko tafo, mai yiwuwa ma tare da su Ihsan."
   Jin an k'ara ambaton Ihsan sai ta ji duk zancen ya gundureta, ta daure ta k'akalo murmushi.
  "Lah bakomai Hajiya, ai can da nan din duk daya ne."
   Daga haka Hajiya ta sallameta. Tana shiga daki ta zube saman katifa, a hankali maganganun Ihsan suka dawo mata kawai sai ta fashe da kuka sosai har tana sheshshek'a. Wannan rayuwa ta soma isarta, Ihsan ta soma kaita bango, abin nata yana neman wuce gona da iri, ko don tana ganin ita din bata da wani karfin ikon da zata kwaci 'yancinta ne? To wane 'yanci ma ta ke da shi a yanzun tunda ba wani babban jigo abin tunk'ahonta wanda zai iya yin wani kata6us akan lamuranta? Kewar mahaifiyarta yafi komai damunta, ko babu komai ta tabbatar ba zata watsar da ita kamar yanda Mahaifinta ya yi ga rayuwarta ba.
   A karshe dai wani sashe na zuciyarta ya yi ta nusar da ita da muhimmancin Yarda da Kaddara, haka har dai zuciyarta ta danyi sanyi ta mike don d'auro alwalar La'asar.
       
   Yana zaune saman kujera a ofis cike da dumbin tunani da damuwa, ya daga kai ya dubi agogon bangon dake a ofishin nasu, agogon ya nuna karfe hudu saura mintuna uku, ya ja guntun tsaki gami da dafe goshinsa. Ya san zuwa wannan lokacin sun wuce, tabbacin farin cikinsa ta tafi saidai hausawa sun ce garin masoyi baya nisa, yasan ko yaushe ya yi niyya muddin ranar babu aiki zai iya kai mata ziyara. Saidai zai so matuk'a tafiyar ta kasance babu ita.
  'Akan wane dalili?' Cewar sashe na zuciyarsa, ya runtse ido gami da jingina kansa jikin kujera.

 
   


       
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

51
   "Ummi, ina muka kwana a zancenmu na jiya? Abin nufi me kika fahimta da yanayin da muke ji game da juna a zukatanmu?"
  Ta girgiza kai ta daure ta ce. "Babu."

Ya yi wani murmushi.
"Ai nasan zaayi haka." Ba ta ce komai ba, shi kuwa saida ya ja fasali sannan ya cigaba da magana.
   "Kin sani kamar yanda na sani Ummi, amma mu ajiye wannan a gefe."
Shiru ya dan biyo baya kafin ya dora.
"Bani tarihin rayuwarki idan da hali."
 
'Rayuwata?' Ta yi tambayar a ranta. Ganin ta yi shiru ya k'ara magana.
"Look Ummi, ki saki jikinki da ni please, ba ma ke ba, ni kaina ban yi sabo da hakan ba, sai kin zauna da Faruk za ki fahimci ko waye shi. Ban fiye sakin jiki da mutane na yi hira har haka ba, da dai cikin brothers na ne ko Hajiyata. So please Ummi ki min alfarmar nan, ki saki jiki da ni, ina so nan gaba ma mufi haka kusanci kinji ko?"  Ya k'arashe cikin rad'a gami da yin murmushi mai sauti, baiwar Allah idanunta suka cika da kwalla, ga samu ga rashi. Tana son abinda ba za ta ta6a samunsa ba don a yanzun da ya ke magana ji ta ke yi tamkar ana k'ara rura mata wutar kaunarsa. Bata ba shi amsa ba face ta shiga labartamasa labarinta iyakar wanda ta sani banda wanda batasani ba kuma bata ta6a samun labari ba, wato na zamantakewar mahaifinta da mahaifiyarta. To mai labarta matan ma ba shiga sabgarta ya ke yi, bai dauketa matsayin 'ya ba.
   Tiryan-tiryan ta ke bashi labari tana yi tana zubda ruwan hawaye har ta kai yanda aka kawota aikatau.
   Tana kaiwa karshe ta cigaba da kuka mai kona zuciya, ba don komai ba sai tunanin rashin gatanta da kuma na son abinda ba zata ta6a samu ba.
   Tattausan hannunsa ta ji a saman kumatunta yana share mata fuska, baki ta saki tana kallonsa, ba kwayar idanunta ya ke kallo ba, kyakkyawan farar fatarta ta ke kallo yayinda ya cigaba da magana yana murmushi mai kama da yak'e, fuskarsa dauke da damuwa da tausayi.
       "Kinzo inda za'a share miki hawaye da taimakon Allah, idan har Faruk na numfashi, in sha Allah zai zame miki haske a rayuwarki. A yanzu ta bakinki nake son ji."
  Sai lokacin ya dubeta, ita kuwa idanunta a lumshe suke sakamakon yatsunsa da ke akai yana sharemata kwalla. Daidai lokacin kuma ya dauke hannunsa daga kanta. Ummi bugun kirjinta k'aruwa kawai ya ke yi, ita dai bata ta6a jin yanayin nan kan kowa ba sai shi, ta kasa dubansa, anya kuwa zata iya daukar shawarar Antinta Amina? Kai, dole ta dauka don Antinta ba zata cuceta ba.
    "Kin yarda kin amince mu k'ulla alak'ar da zata kai mu ga AURE? Ta wannan hanyar kadai zan iya taimakon rayuwarki Ummina."
    Kamar ta tashi ta ruga a guje ta ke jinta, Faruk dama ya muryarsa ta ke wajen sanyi kamar mace ballantana kuma yana cikin yanayi na shaukin so da kauna. Ta dan matsa don rage kusancin da ya yi mata.
    "Kayi hakuri, ni babu wani abu da nake ji game da kai, ban dauke ka komai ba sai dan uwan Yaya Adnan kuma iyayen gidana, ka yi hakuri, bazan iya jefa zuciyata cikin abinda zan wahala ba."
   Daga haka ta kwashi wayoyinsa ta mik'a mishi, saidai ba shi da niyyar kar6a, asalima idanu ya zubamata yana murmushi. Ganin haka yasa ta ajiyewa a kujerar da ta mik'e zata tafi.
  "Ji mana."
  Ta tsaya cak gami da juyowa. Ya dauke wayoyinsa ya dubeta.
"Dawo ki zauna."
   Ba musu ta dawo ta zauna tana share hawayen saman fuskarta.
  Ya dawo ta gabanta ya durkusa.
"Hey, kalli tsakar idanuna ki ce ba ki amince ba."
  Ta kauda kanta tana jin tamkar ta fashe da kuka gaba daya ita ta gama tsorata ganin Faruk dagaske ya ke babu wani sassaunci.
    "Ummi say something please, ki ce wani abu mana."
   Ya fada cikin shagwa6a66iyar muryar da bai fiye amfani da ita ba sai ko a gaban Hajiyarsa. Ta girgiza kai.
  "Ni ban amince ba."
  Ya dubeta na sakanni ya na murmushi.
  "Dagaske ba ki amince ba?"
Ya fad'a yana mai kwaikwayon muryarta, abin ya so bata dariya ta kuwa saki murmushi.
  "Masha Allah, ko kefe. Naji wannan kuma nagode, amsa tuni na sameshi, hirar ce nakeson muyi don bakisan yanda nakejin dadin ganinki bane."
  Shiru babu wanda ya k'ara magana, can kuma ya sauke ajiyar zuciya ya kunna wayoyinsa.
  "Goma har ta kusa."
  Ya fad'a yana duban wayar, can kuma ya mik'e ya sanya wayoyin a aljihun wandonsa, ya yi amfani da tafukan hannayensa ya dafa gwuiwarsa gami da sunkuyowa yana dubanta.
  "Saida safe."
Ta gyada kai sannan ta gifta ta mike tsaye da sauri don daman tun dazu ta soma jin tsayuwar motoci a harabar gidan ta tabbatar yanzun su Mami sun iso.
   "Allah Ya tashemu lafiya."
  Daga haka ta yi gaba da sauri, koda ta isa ga kofar saida ta kasa jurewa ta juyo kanta ta dubeshi, shi ba shi ma da niyyar barin wajen don komawa ya yi ya zauna. Su ka yi ido hud'u da shi, ta dauke kanta da sauri-sauri ta bar wajen tana ji yana fad'in.
  "Ko na zo ne?"
Bata ko juyo ba balle ta tanka mishi. Ya yi murmushi karo na ba adadi sannan ya kwantar da kansa jikin kujera, kai tsaye hotonta ya lalubo wanda ya yi mata a wata rana da ta ke zaune tana wanki a (garden) da kuma na zanen da ya yi mata.
  "Ke tawa ce in sha Allah."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

55
                      KANO
Mami ta yi mamakin chanje-chanjen da ta gani wajen Mijinnata. Abin mamakin bai wuce yanda ya dage akan lallai su bata girkinta ba. A ranar kuwa suna isa ita ce ta shiga fadarsa. Saboda Fahad, Ramma ta kwana a gidan kasancewar yaranta suna kauye ziyarar dangin ubansu.
     Ta sha rok'o a wajensa akan ta yafemishi har ta gaji domin duk da nunamishin da ta yi komai ya wuce, bai iya sakin jiki ba. Ranar kam komai ya yi lafiya, ya sanarmata haka kawai ya soma tsintar kansa cikin halin tunani da kuma tsananin kewarta.
  Tsakanin mata da miji dai sai Allah, a wannan daren suka dinke har ma ya nemi kiran d'ansa don ya dawo ya soma shirin tafiya karatunsa.
    'Babu abinda ya fi karfin Allah.' Shine abinda Mami ta fad'a a zuciyarta cikin murmushi lokacin da ta saci kallon fuskar mijinta ta ga annurinsa ya dawo ba kamar da ba.

                     ***  ***  ***
                        ABUJA
    Misalin karfe shida a gaggauce ya kammala shirinsa ya fice zuwa aiki ko karyawa bai tsaya yi ba.
  Ummi tun misalin takwas suka soma ayyukansu, ta yi gyararrakinta tsaf, Binta itama ta kama nata. Hajiya Babba ta yaba kwarai da gyaran Ummi. Koda ta shigo ta iske falon kyal-kyal tana(mopping) ta kalli wajen kafin ta amsa gaisuwarta da murmushi dauke saman fuskarta.
  "Eh lallai, dole Madina ta so zamanki wajenta, ashe haka kika iya gyara? Lallai kam na yaba miki Ummi."
Wani murmushi ta yi har kumatunta saida suka lotsa, kwarai ta ji dadin wannan yabo da ta samu. Hajiya Babba ta yi dakinta, nan ma an kyalkyaleshi tamkar ba'a ta6a kwana cikinsa ba. Komai tsaf, hakanan ta ga bambancin aikinta da na Sa'a kwarai.
   Ummi duk jikinta babu dadi, duk da cewar tana son gujewa Adnan, rashin had'uwarsu a kwana biyunnan yana damunta, batasan dalilin son sanyashi a kwayar idanunta da ta ke yi ba. Hankalinta ya kai ga tafkekan hoton matasan yaran Hajiya Babba. Dukkansu sanye suke da shadda ruwan k'asa tazarce, ta sha surfani mai tsada. Hularsu mai surkin ruwan k'asa mai duhu da marar duhu, a tsaye sukayi hoton a farfajiyar wani  (hall), daga hotunan bayansu za ka tabbatar cewar a wajen wata walima ne.
  Ta kauda idanunta gami da sauke ajiyar zuciya, duk cikinsu babu wanda yafi haskakawa a idanunta kamar Faruk, ko don shi zuciyarta ke so ne?
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  54

A wannan ranar dakyar ya jure suka kammala suka tashi, a hanya Magriba ta riskeshi haka ya karasa gidan ya yi fakin duk jiki a sanyaye. Bai zarce ko'ina ba sai sashensa. Saida ya yi sallah ya watsa ruwa ya sanya bak'ar jallabiya a saman gajeran wandonsa sannan ya yi niyyar shiga cikin gidan.  Hankalinsa ya kai ga Adnan wanda ke kwance saman gado yana danne-dannen waya. Yatsun k'afarsa na hagu ya ja wanda ya tilastawa Adnan yin gefe da wayar yana mai sakin k'ara lokaci guda kuma da dariya. 
  "Kai my best."
  Faruk ya murmusa kadan.
"Baka da aiki sai(chatting) kwanakin nan,  ya dace na soma haramar kora ka makaranta naga ta (chatting)."
  Dariya Adnan ya cigaba da yi. Faruk ya zura silifas dinsa ya fice zuwa sashen Hajiyarsa.
    Bayan saukowarsa daga bene saida ya tsaya cak yana k'arewa hanyar dakunan yan aikin kallo, yasan Ummi zuwa yanzu ta yi mishi nisa. Ya sauke ajiyar zuciya gami da juyawa ya cigaba da tafiyarsa.
  A falo ya iske Ikram da Ihsan suna cin abinci suna hira. Ganinsa yasa duk suka dubeshi suna mai amsa sallamarshi. Yana duban Ihsan da mamaki ya jefamata tambaya.
  "A'a, baku wuce ba?"
  Ihsan cikin kashe murya ta ce "No sun wuce, ina nan sai bayan sati biyu zan koma."
    Bai wani ji dadi sosai ba, zaman Ihsan takura rayuwarsa kawai ne, ba yau ba ya soma lura da take-takenta, shi din ya kasance mai saurin fahimtar masu nunamasa so haka. Yana sane da Iklima ma, sai yanzu ne ma ya fahimci ta dan kwana biyu bata mishi koda sallama ba a whatsapp ballantana kuma akai ga kira.
   "Ok." Shine kawai abinda ya ce sannan ya k'ara gaba. Ihsan ta bi bayanshi da kallo har saida Ikram ta zungureta.
  "Kin shiga uku wallahi kedai, nikam har na daina mamaki."
Ihsan ta yi murmushi.
"Me kike nufi?"
"Ina nufin ki sanarmasa kina sonsa."

  Ihsan ta zaro ido.
"Zubda aji."
   Ikram ta yi kwafa.
"Tsaya kallon ruwa kwado ya yi miki k'afa."
  "Wai kina nufin akwai wacce ya ke so?"
  Ikram ta yi dariya.
"Bani da tabbacin hakan. Amma kada ki sake ki tsaya wani jan aji wallahi. Yayanki ne, koda zai wulakanta kowa banda ke."
  Ihsan dai ta yi shiru ta cigaba da kai loma, maganar Maminta kawai ta ke tunanowa inda ta yita bata shawara akan ta yi kokarin jawo hankalinsa ta kissa.
       
   Ya dan jima wajen Hajiyarsa har akayi kiran salla tukunna ya fito. Daga masallaci dakinsu.
    Ya dan jima wajen Hajiyarsa har akayi kiran salla tukunna ya fito. Daga masallaci dakinsu ya wuce, can su Ikram suka kai musu abincinsu, har lokacin sam ba shi da masaniya akan Ummi na Abuja. Koda ya shiga wajen Hajiyarsa, bata sanarmishi ba.

                   *** *** ***
                   KADUNA
  Wasa-wasa karamar magana ta zama babba, domin kuwa Deen da Dija soyewarsu sukeyi son ransu, saidai hirarsu ta fi a waya ko kuma idan sun yi sa'ar rana Munira bata gida. Tun ita Munira bata ganewa har ta soma zargin akwai wani abun. Kamar yanda Deen ke damuwa da harkar Dija sosai, abin mamaki har zuwa ta ke ta zauna a hau wasa da dariya da ita har ma su dinga wareta cikin hirartasu saidai ta yi shiru tana sauraronsu.
    Dija da kanta ta bawa Deen shawara akan lokacin komawarta gida ya yi idan har da gaske ya ke sai ya turo magabatansa. Alokacin ne kuma ya yi dumm, ya dubeta.
"Kina ganin hakan bazai janyomin matsala da Munira ba?"
  Ta ji haushin furucinsa, ta fahimci koda asiri ya ci shi akanta, tofa baisa ya mance da matarsa ba. Ta nunamishi idan ba zai iya aurenta saboda matarsa ba, shikenan. Anan kuma ya hau bata hakuri suka ajiye maganar yanda za'a 6ullowa lamarin.
  Kwanaki biyu da yin maganarsu ta tattara ta koma Ringim, Munira ta ji dadin tafiyarta don Allah shaida ta soma tunanin akwai wata alak'a tsakaninta da maigidanta wanda bata fatan zatonta ya kasance gaskiya.  Ta rik'i Dija yar uwa haka kuma da zuciya daya ta ke zaune da ita. Koda zasu rabu, tayi mata kyauta ta sutura da abin hannu, idan kuma zaa hada da wanda Deen ya yi mata, to fa ba komai bane.
                  ***   ***  ***
                     RINGIM
 
  "Lale da 'yan Kaduna. To, saukar yamma ce?" Baba Habiba ta fada tana mai dan tafa hannuwa kamar kawata Bingel a fagen nanaye (LOL). Dija ta sakarmata jakar kayanta ta kar6a da gaggawa tana mai k'arewa diyartata kallo da dumbin mamakin yanda akayi ta chanja, wani k'iba ta k'ara da kyau.
  Sai da dare bayan sun zauna ne suna 'yar hirarrakinsu, wayar Dija ta k'ara daukar k'ara a karo na biyar tun shigowarta gidan. Baba baki bude ta ke dubanta, ta rasa inda zata tsoma ranta don tsananin murna, ga dukkan alamu dai diyarta ta samu saurayi dan birni, lallai ba zasu yi sake ba.
     Bayan Dija ta ajiye wayar ne ta dubeta.
  "Ya sunansa?" Dariya ma tambayar ta bawa Dija, bayan ta gama kyakyatawa ta ce "Wa kenan?"
  Baba ta girgiza kai.
"Ke bafa za muyi sake ba, fadamin sunansa mu k'ara kamashi a hannu yanda bazai ta6a iya su6uce mana ba kafin zuwa lokacin da za'a tashi aurenku muyi shiri na musamman."
  Wani murmushi Dija ta saki.
"Zahraddeen sunansa."
  Baba ta zaro ido waje.
"Wanne kenan?"
  Babu ko d'arr ta amsa.
"Zahraddeen dai da kika sani, mijin Munira, shi nake so kuma ya ke sona."
   Baba ta yi tsit, Dija tiryan-tiryan ta labartamata ire-iren hidimar da yake mata har da kyautar kudi dubu talatin da ya yi mata da za ta taho ya kuma siyamata sabuwar waya tana nan cikin kayanta. Har ma da yanda suka ajiye magana da shi akan zai zo neman aure. Bayan ta kammala bayanin ta fiddo kudaden ta damk'a a hannun Babarta, ta zaro kwalin wayar shima daga jakarta tana mai nunamata. Baba Habiba ta zurawa kudin ido da wayar kafin ta washe baki.
"Ke Dije! Wadannan yanzu duk mallakinki ne? Shakka babu daman bokanya ta tabbatar min idan mijin aurenki ya zo za muyi mamaki gashinan tun ma ba'a je ko'ina ba na soma. Abun yi yanzu, gobe zan koma gidan bori na ji yanda zamuyi ayi komai cikin salama batare da ansamu matsala ba, don ta ubanki mai sauki ne, sai yanda nace."
  Wani ihun dadi Dija ta saki gami da rungume mahaifiyarta.
"Shiyasa nake bala'in sonki wallahi Baba."
  Suka yi dariya, nan suka soma shawara kan irin k'ulle-k'ullen da zasu sanya ayi bayan auren. Ko kusa Dija bata sanarmata komai akan Raihana ba gudun yanda zata yiwa kallon abin.
                  ***   ***   ***
                      KANO
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

56
 
    Har Ummi ta yi kwana biyu a gidan, Faruk ba shi da masaniya don gaba daya aiyuka sun mishi ca a ofis. Ba shi ya samu kansa ba sai ranar Asabar. Ranar kam ya sha bacci, bai farka ba sai sha daya. Kai tsaye wanka ya fad'a, bayan fitowarsa ya shirya cikin t-shirt fara tas da wando na (Adidas), bak'i mai surkin fari kadan sannan ya zura silifas ya nufi sashen mahaifiyarsa.
 
    Tafe take a hanyarta ta zuwa wajen(garden) don dauraye tsummokaran da ta kammala gyaran dakunan Hajiya da su. Kallon benen da zata yi ta ganshi yana saukowa shima a daidai lokacin ya bar duban wayarsa ya maida ga hanya alokaci daya kuma yana kokarin sanya wayar aljihun wando. Karaf idanunsa cikin nata, yanda ta tsaya bata motsa ba, shima ya tsinci kansa da mutuwar tsaye. Abu biyu ke yawo a kwakwalwarsa. Buri na son kasantuwar abinda ya ke gani yanzu tamkar mafarki da kuma tambayar daman tana gidan?
  Dakyar ya yi jarumtar k'arasawa har gabanta, alokacin ita kuwa ta sunkuyar da kanta cike da matsanancin fargabar abinda zai k'ara ce mata.
   Saida ya kai dab da ita har suna jin numfashin juna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya matsa, ya tabbata ita din ce ba gizo ta ke mishi ba. A hankali ya matsa baya, cikin rawar murya ta gaisheshi bayan ta durkusa. Ya amsa cikin jin wani irin nishadi a ransa, ta mik'e tsaye, tana shirin barin wajen maganarsa ta dakatar da ita.
  "Daman ba ki tafi ba?"
  Ta dan saci kallonsa, murmushi ta gani dauke saman fuskarsa wanda ya kara fiddo kyawunsa.
  "Eh."
  "Saboda ni?" Ya fada a tausashe bayan ya dan rankwafo da kansa yana kallon fuskarta.
   Ta k'ara satar kallonsa, shi dinma bai kauda nasa idanun daga kanta ba. Ta ji wani iri a jikinta, wai saboda shi. Maganar ma nauyi ta yi mata, ta kauda idanunta.
   "Mami ta ce na zauna zuwa wani lokaci."
   Ya ji dadin maganar, ba zai iya misalta farin cikin da ya shiga sanadin hakan ba. Ya dubi hanya babu wani ko wata da ke tahowa sannan ya dubeta.
  "Ummi, yau kenan za ki tayani hira?"
Ta zaro ido batare da ta dubeshi ba, cikin sauri ta girgiza kai.
  "Kayi haku..."
"Shiit." Ya dakatar da ita ta hanyar dora yatsansa a saman le66ansa.
  "No please, karki hana zuciyarki abinda ta ke so mana Ummi. Ko kina so wani abu ya faru da mu sanadin hana zukatanmu farin cikinsu?"
  Ba amsa sai idanunta da suka kawo ruwa, ya mik'e da rankwafawar da ya yi.
   "Shikenan, ki tafi, mu had'u wajen pool."
   Daga haka shiru ya biyo baya, karshe ma ya juya ya cigaba da tafiya. Da ido ta bishi, ta tabbatar shi babu abinda ya ke tsoratashi, kamar yanda babu matsalolin da ya ke hangomusu, ita kadai ta damu da duk wadannan.
  Koda zai shige saida ya juyo domin ganin yanayin da ta shiga, suna hada ido ta juya da sauri ta soma tafiya. Murmushi ya saki kafin ya karasa cike zuciyarsa cike da tsantsar farinciki. Daidai da Ikram da Ihsan sun ga chanji yau wajen yayannasu, don kuwa biyemusu ya yi akayita hira da dariya. Ihsan ji ta ke tamkar ta buga tsalle don murna da farinciki, yau ita Faruk ya dage hira da ita? Tabbas shawo kansa zai zo mata da sauki muddin ya d'ore a haka.
   A yan kwanakin da ta yi tsaf Hajiya Babba ta fahimci inda ta dosa, a farko bata gaskata Ikram ba da ta sanarmata cewar Ihsan na son Faruk ba, saida ta lura da kanta. Abin ya yi mata dadi, zata so hakan ta kasance, saidai d'annata ne batasan abinda ke ransa ba. A ganinta da wuya ya kaunaci yarinya mai rawar kai irinta, hakanan Ihsan sam bata da hakuri, ga saurin fushi. A raayin Hajiya Babba, bata kaunar abinda zai damu 'ya'yanta, kusan halinsu daya da Mami na son 'ya'ya.

   Acan kuwa Ummi tana isa ta zauna saman kujera gami da zubawa famfo ido, hankalinta gaba daya ba a wajen ya ke ba, ya tafi gaba daya ga tunanin Faruk.
'Dagaske fa ya ke.' Shine abinda ta fad'a a ranta, tabbas Faruk dagaske ya ke, asalima babu wani alama na tsoro ko fargaban abinda zai biyo baya. Yanzu ya zata yi? Bai bata damar cewa ba zata zo ba, ya riga ya yanke cewa lallai kawai ta zo ta sameshi. Ta riga tasan duk ranar da wani a gidan ya gano to fa tashin hankalin da zata shiga ba k'adan bane. Tagumi ta zuba tana tunano da Antinta, yau ne rana ta farko da ta soma jin bukatar waya a rayuwarta, ayau inda ace tana da  waya, tuni zata yi kiranta ta bata shawarar da ta dace. Ta ja guntun tsaki sannan dakyar ta mike ta soma aikin da ya kawota, saida ta kammala ta shanya sannan ta koma ciki.
    Misalin biyar na yamma tana zaune a k'asan bishiyar mangwaro tana wasa da ganyen, hankalinta gaba daya ya tafi ga tunanin Faruk, banda murmushi da wani annuri, baka ganin komai saman fuskarta. Ita tasan tana sonsa, bata ta6a son wani d'a namiji ba sai shi, saidai kawai bambancin dake tsakaninsu, shi kadai zai hanasu aure.
   Ta jima kafin ta sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta ga inda ta ji sautin dariyarsu. Ihsan ce da Ikram dukkansu sanye da kananun kaya, riga da siket, sun nad'e kansu da karamin dankwali. Hira sukeyi abinsu da dariya har suka iso wajen motar da tun zuwansu Abuja, Faruk tasan yana hawanta. Suna hada ido da Ihsan ta maka mata harara, Ummi ta kauda fuskarta. 'Kanki ake ji.' Shine abinda ta fad'i a ranta.
  "Har kun fito?" Tattausar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Ta so ta jure kada ta kalleshi, saidai hakan ya k"i yiwuwa, ji ta yi tamkar bazata nutsu ba idan bata ga tasa shigar ba. 'SubhanAllah!' Shine abinda ta fad'i a ranta. Riga tshirt ce yasa kalar(golden, long sleev) mai mannuwa a jiki, sai (blue jeans) ya sanya gilas dark brown, agogonsa na k'a'ida yana daure a hannunsa sai zobunansa da baya rabo da su. Ji ta yi tamkar numfashinta zai dauke tsabar kyawun da ta ga ya yi mata a idanu.
  To ba Ummi kadai ba, Ihsan kanta baki ta bud'e tana kallonsa, ji takeyi tamkar ta dora hannu a ka ta ce wayyo Allah, kamar ta matsa bakin Faruk ya furta yana sonta.
   "Wow Yaya Faruk, kayi kyau wallahi." Muryar Ikram ya katse Ummi da Ihsan daga tunanin da zukatansu suka lula. Ya dan rankwashi kanta yana dan murmushi.
   "Ko?" Ta yi dariya.
"Allah kuwa."
  Ya jinjina kai sannan ya zagaya zuwa mazaunin direba ya bude motar, Ihsan da sauri ta bude gidan gaba ta shiga, hakan bai wani dameshi ba, don shi bai dauketa wata aba ba face k'anwa.
   Ya bud'e motar kenan yana shirin shiga idanunsa ya kai gareta.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

57

Ita dinma har lokacin shi ta ke kallo, batasan tana da kishi ba sai a yanzun, Faruk ne da Ihsan wacce ta riga tasan tana tsananin sonshi, babu walwala a fuskarta hakanan bata daureshi ba, ta mik'e da sauri ta bar wajen ta nufi ciki. Ya
 dan dubesu.
  "Ina zuwa. Zo ki tayar da motar kafin na zo." Ya karashe zancensa da duban Ikram. Ba musu ta kar6i muk'ullin, basu kawo komai ba don babu wands zai yi tunanin wai Faruk zai dauki Ummi wata aba.
   Shi kuwa da sauri ya nufi hanyar da ta yi da zummar komawa sashensa saidai ya zarce kai tsaye wajen dakunansu da zummar kwankwasa mata.
Hawaye ta ke fitarwa da batasan dalilinsa ba, tasan dai tana jin zafi ne cikin zuciyarta na ganin Ihsan a gaban motar Faruk. (Ji karfin hali!) Tana shirin lek'ensu ta windo, ta ji bugun kofarsa yana kiran sunanta. A rude ta saurara ta ji, tabbas shi dinne, ta share fuskarta da sauri sannan ta bud'e k'ofar. Ya fidda gilashinsa yana dubanta, bata yarda ta kalleshi ba.
  "Kar kiji shiru Ummina, zan kai yaran nan siyayya amma bazan jima ba kinji?"
  Kai kawai ta gyada cike da jin haushi, da tana da iko da ta ce ya fadawa Ihsan ta koma baya saidai yin hakan wani nuna karfin hali ne wai 6arawo da sallama. Ita da ke cin arziki?
  "Ko za kije?"
  Ta girgiza kai a tsorace.
"Sai kun dawo."
  Ya daga kafada yana mai wani shagwa6e fuska kamar wani yaro.
"Allah kuwa idan kina so ki zo muje."
  "Don Allah kayi hakuri." Itama tayi maganar cikin marairaice murya don gaba daya tsoro ya cikamata ciki, bata so wani ya zo ya gansu tare.
  "Shikenan, me kikeso na siyomiki?"
  Hankalinta ya tashi ga shi ya tsare bakin hanya babu damar ta duba hanyar ta gani ko wani ya taho. Ta dubeshi gaba daya a rude ta ke.
"Ko menene."
  Ya fahimci duk a rude ta ke, murmushi ya saki yana mai juyawa.
  "Bari na tayaki duban hanyar." 
Ya dan kalla sannan ya dubeta har lokacin bai bar murmushin ba, kafada ya daga gami da daga gira kadan.
   "Karki damu, idan don Binta ce, tana tare da Hajiya, can na barota. Bazan tafi ba sai kin gayamin abinda kike so na kawo miki."
   "Na shiga uku." Ta yi furucin da bata shirya fitowarsa fili ba, ga mamakinta sai ta ga yana dariya har yana dan jijjiga kafada. Ta yi sakato tana kallonshi, bai ta6a yi mata dariya har haka ba, sai taga ya k'ara yi mata kyau matuk'a. Hon din da suka ji ya katse su, tasan su Ihsan ne. Ta dubi windo kafin ta juyo ta dubeshi. Ya dan daga gira. 
  "Kina 6atamusu lokaci."
  Ta rasa ya zatayi.
"Ka siyomin alawa." Ta fada kamar zata fashe da kuka. Ya kwaikwayi muryarta.
  "Guda nawa?"
  Ta yi mishi nunin biyu da yatsa. Ya murmusa.
  "Bye, sai na dawo."
  Kanta kawai ta gyada, ya juya ya tafi. Ta lek'o ta na kallonsa har ya maida gilashinsa, murmushi ta saki gami da juyawa ciki ta rufe kofar. Wajen windo ta k'arasa da saurinta tana lek'ensa, tana ganin yanda ya had'e musu gira tamkar ba shine ya gama yi mata murmushi harda dariya ba yanzun. Akan idanunta ya bude motar ya shiga, daga haka ta daina ganinsu sakamakon gilashin motarsa mai duhu ne. Sauke ajiyar zuciya ta yi gami da rike kirji tana dariya marar sauti idanunta a lumshe, dariyar Faruk kawai ta ke gani ta ke jin sanyi, yanda ya nunamata tsantsar kulawa har mamaki abin ya bata, ashe ire-irensu sukan ji dadin duniya? Da ace wannan farincikin zai dore da ta fi kowa sa'a a rayuwa. Ta numfasa gami da bin lafiyar kafet ta kwanta. Sauranta jiran dawowarsa da ganin da wacce ya zo, duk kuwa da tsantsar fargaba da ke cin kasan ranta. Bata so wani ya san alaka'ar da ke tsakaninsu...

  Ba su suka dawo gidan ba sai bayan Magriba. Yana fakawa suka fito kowacce hannunta rik'e da leda wanda kayan mak'ulashe ne zalla. Ihsan bayan sun danyi gaba ta dubi Ikram.
  "Wai duk wancan kayan zak'in da Yaya Faruk ya loda na shi ne sho d'aya?"
  Ikram ta harareta.
"Meya hanaki tambayarsa?"
  Ta yi dariya.
"Mezai kaini gangancin nan?"
  "Wai ma, kina ganin dai ya mik'o mana na Hajiya, kinsan dai nasa ne ko? Amma dai bansani ba ko anjima zai je hira."
Ta k'arashe cikin zolaya. Ihsan ta buga tsaki gami da k'ara d'aga kafa.
"Ke dama ai ba'a hirar arziki dake sai kin kwafsa a wani 6angaren."
  Ita dai Ikram da dariya kawai ta bita.
       
Shi kuwa gogan kai tsaye sashensa ya nufa, saida ya yi sallah ya fito ya lek'a su Hajiya kafin ya koma sashensa ya fito rike da ledar Ummi wacce ya yo mata siyayya.
   Daidai lokacin da ya kwankwasa mata, Binta ta fito daga bandaki, zaro ido ta yi domin mamaki da ya cikata. Me Yalla6ai ke yi a bakin k'ofar dakin Ummi har yana kwankwasawa? Ta so ta yi magana saidai ta kuma la6ewa don ganin wannan abin Al'ajabin. 
  Ummi ta shafa adduarta, idar da sallar isha'in ta kenan, mik'ewa ta yi ta nufi k'ofar gami da bud'ewa. Suka dubi juna ta gaisheshi, ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Ledar ya mik'amata.
  "Ajiye wannan sannan ki zo ki sameni."
  Gabanta ya fad'i, ta dubi ledar sannan ta dubeshi.
"Kar6i mana." Jiki a sanyaye ta kar6a.
  "Nagode."
Ya yi gaba gami da fadin.
"Ina jiranki."
  Ta juya ta koma ciki har lokacin jikinta babu kwari.
  "Anya batayi wauta ba? Meyasa ta kar6a batare da tunanin kada wani abin ya biyo baya ba?"
   Ganin dai babu wanda ya ganta, yasa hankalinta ya dan kwanta.
"Anyi na farko, in sha Allah shine na karshe." Ta fada a fili, sanin da ta yi babu wani aikin da bata yi ba ne ballantana wani ya nemeta yasa ta saurin mik'ewa bayan ta daga hannu sama.
  "Ya Allah ka taimakeni yau wannan bawa naKa ya fahimceni."
  Daga haka ta shafa sannan ta fice.
    Akan idon Binta, Ummi ta fito ta wuce, ganin Ummin na shirin waigowa ne yasa ta saurin komawa baya yanda bazata ganta ba, saida ta tabbatar ta bar wajen sannan ta shiga tafa hannuwa tana salati.
  "Tabdijam! Ashe dai duk jirgi daya ya kwasosu da Kb? Duk wannan shiru-shirun na wofi ne? Kuma wai Ummi?!" Tayi maganar a fili cikin nuna tsananin mamakinta. Lallai DAN ADAM mai wuyar gane hali ne.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  58
  Ba su suka dawo gidan ba sai bayan Magriba. Yana fakawa suka fito kowacce hannunta rik'e da leda wanda kayan mak'ulashe ne zalla. Ihsan bayan sun danyi gaba ta dubi Ikram.
  "Wai duk wancan kayan zak'in da Yaya Faruk ya loda na shi ne sho d'aya?"
  Ikram ta harareta.
"Meya hanaki tambayarsa?"
  Ta yi dariya.
"Mezai kaini gangancin nan?"
  "Wai ma, kina ganin dai ya mik'o mana na Hajiya, kinsan dai nasa ne ko? Amma dai bansani ba ko anjima zai je hira."
Ta k'arashe cikin zolaya. Ihsan ta buga tsaki gami da k'ara d'aga kafa.
"Ke dama ai ba'a hirar arziki dake sai kin kwafsa a wani 6angaren."
  Ita dai Ikram da dariya kawai ta bita.
       
Shi kuwa gogan kai tsaye sashensa ya nufa, saida ya yi sallah ya fito ya lek'a su Hajiya kafin ya koma sashensa ya fito rike da ledar Ummi wacce ya yo mata siyayya.
   Daidai lokacin da ya kwankwasa mata, Binta ta fito daga bandaki, zaro ido ta yi domin mamaki da ya cikata. Me Yalla6ai ke yi a bakin k'ofar dakin Ummi har yana kwankwasawa? Ta so ta yi magana saidai ta kuma la6ewa don ganin wannan abin Al'ajabin. 
  Ummi ta shafa adduarta, idar da sallar isha'in ta kenan, mik'ewa ta yi ta nufi k'ofar gami da bud'ewa. Suka dubi juna ta gaisheshi, ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Ledar ya mik'amata.
  "Ajiye wannan sannan ki zo ki sameni."
  Gabanta ya fad'i, ta dubi ledar sannan ta dubeshi.
"Kar6i mana." Jiki a sanyaye ta kar6a.
  "Nagode."
Ya yi gaba gami da fadin.
"Ina jiranki."
  Ta juya ta koma ciki har lokacin jikinta babu kwari.
  "Anya batayi wauta ba? Meyasa ta kar6a batare da tunanin kada wani abin ya biyo baya ba?"
   Ganin dai babu wanda ya ganta, yasa hankalinta ya dan kwanta.
"Anyi na farko, in sha Allah shine na karshe." Ta fada a fili, sanin da ta yi babu wani aikin da bata yi ba ne ballantana wani ya nemeta yasa ta saurin mik'ewa bayan ta daga hannu sama.
  "Ya Allah ka taimakeni yau wannan bawa naKa ya fahimceni."
  Daga haka ta shafa sannan ta fice.
    Akan idon Binta, Ummi ta fito ta wuce, ganin Ummin na shirin waigowa ne yasa ta saurin komawa baya yanda bazata ganta ba, saida ta tabbatar ta bar wajen sannan ta shiga tafa hannuwa tana salati.
  "Tabdijam! Ashe dai duk jirgi daya ya kwasosu da Kb? Duk wannan shiru-shirun na wofi ne? Kuma wai Ummi?!" Tayi maganar a fili cikin nuna tsananin mamakinta. Lallai DAN ADAM mai wuyar gane hali ne.
  Saida ta lek'a dakin ta gama bud'e ledar ta ga kayan mak'ulashen da ke ciki sannan ta fita tana had'iyar yawu.
  "Ina yarinya, wannan kam dole nima ki bani rabona."
   
  Acan kuwa Ummi ta iske Faruk durkushe gaban ruwa yana sanya tafin hannunsa na dama yana wasa da shi, fuskarsa a sake. Jin shigowarta yasa shi kallonta, ta kauda idanunta ta karasa bayan ta rufe k'ofar.
   Mikewa ya yi ya koma ya zauna, itama ganin haka ne yasa ta zama a dayan kujerar kamar yanda sukayi wancan karon saidai a wannan karon ya sanya kujerun suna kallon juna, hakan yasa shi bawa k'ofa baya ita kuwa tana fuskanta.
   "Na yi zaton bazaki zo ba ai."
Babu abinda ta ce sai wasa da gefen hijabinta da ta ke.
   "Ummina."
  Ba ta amsa ba sai kirjinta da ke lugude.
  "Wai meyasa ne kike kasa sakin jiki da ni? Idan da magana a bakinki ko fad'a."
   Ta ga dama ta samu, hakan yasa ta daurewa ta dubeshi.
"Don Allah Yaya Faruk ka yi hakuri ka kyaleni." Ta sauke idanunta daga kansa kafin ta cigaba da magana a raunane.
"Wannan abu ne da ko a mafarki ban ta6a ganin ya faru ba, 'yar aiki da auren d'an masu gida, kayi hakuri domin Allah, komai dake a ranka game da ni ka ajiyeshi gefe. Ni bazan iya abinda ka ke so ba, banason saka kaina cikin kowace matsala. Ka gafarceni amman idan akwai inda na kuskuro a maganata."

  Tun soma maganarta ya zubamata ido hannayensa biyu dunk'ule wuri guda. Ya lura iyakar gaskiyarta ta ke fad'a ba kuma don bata sonshi ba. Ya girgiza kai.
  "Meyasa ni ban ta6a hangen matsalar da kike yawan ikrari bane Ummi? Kina da tsoro, nasan kuma abinda ke tsorata ki wanda sam bai dace ba. Na farko dai nasan iyayena ba zasu hanani aurenki ba matukar na nuna musu ke ce za6ina, su din sun kasance maso abinda nake so, haka kuma yan uwana na tabbatar ba zasu hanani rayuwa da ke ba Ummi, koda ace kuma basu yi na'am da ke ba, to fa hakan ba zaisa na k'i aurenki ba muddin iyayena sun yarjemin.
Batu na gaba, ni ban daukeki daban da ni ba, Allah ne Ya haliccemu duka, ina yi miki kallo daidai da matsayina, ki ture dukkan wadannan kananun matsalolin Ummi, ki sauk'ak'awa zuk'atanmu, nasan kina jin abinda nake ji duk da cewar ba ki kama koda rabin k'afata ba."
  Shiru ya dan biyu baya, ya rankwafo kadan ya soma magana cikin rad'a.
  "Kin yarda kin amince na sanarwa Hajiya..."
  Bai kai ga karasawa ba ta hau girgiza kai tana dubansa da idanunta wadanda suka ciko da kwalla.
"A'a, a'a, don Allah kada ka fadawa kowa idan ba haka ba zan gudu."
  Ya dan hade gira jin kalmarta na karshe.
   "Saboda kada ki aureni ne za ki gudu?"
  Ganin yanda muryarsa ta chanja da kuma yanayinsa yasa ta yin shiru gami da duk'ar da kai. Ya lumshe ido.
  "Shikenan, tashi ki tafi."
  Ta kasa motsawa, sai ta ji bata kyauta mishi ba, shi kuwa har lokacin bai bude idanunsa ba, dagaske bai ji dadin furucinta ba, kenan akan ta aureshi, ta za6i guduwa?
    "Ka yi hakuri don Allah."
  Ya tsinci muryarta, da sauri ya bude ido don kuwa muryar ta nuna alamun kuka takeyi.  Kukan kuwa takeyi, ya girgiza mata kai.
"No Ummi please, banson hawayenki fa. Ni na hakura."
  Faruk ya cigaba da kasheta da dad'ad'an kalamai wadanda nan take suka kashemata jiki suka sukurkuta ta. Allah Ya mishi baiwar iya lafuzza masu dadi da saurin sace zuciya wanda shi kansa bai sani ba sai a yanzun da ya fad'a cikin soyayyar Umminsa. A wannan zaman da sukayi saida Faruk ya ci galaba don kuwa Ummi ta dan saki jikinta sun yi hira mai dadi har da dariya. Kowannensu yana jin zuciyarsa sakayau, gaba daya ji sukeyi tamkar a duniyar babu sauran bil adama sai su biyu tallin tal! A karshe ya duba wayarsa da ta soma k'ara, yayansa Likita ne(Ridwan). Ya dauka. Bayan sallama ya tambayeshi inda ya shiga, ga shi kuma a falon Hajiyarsu bai ganshi ba.
  Ya dubi fuskar Ummi wacce ke dan satar kallonsa, murmushi ylm    a yi ganin ta kauda kanta.
"Hira nake yi da surukarku amma ina nan zuwa."
   Daga haka ya katse kiran ya bar Ummi da sakin baki.
"To sarkin tsoro, rufe bakin."
Yana fadin haka ya mik'e tsaye.
"Bari na wuce Dakta ya zo. Sai mun hadu gobe kuma in sha Allahu ko?"
  Ta girgiza kai alamar aa. Ya ja dan guntun tsaki. "Kinga dadin waya kenan, da sai mu sha hira, amma dai ba wani abu."
  Daga haka ya yi mata sallama ya wuce, itama barin wajen ta yi da saurinta. Tana shiga dakin ta fidda hijabinta ta zauna, a yau ji take dukkan shawararwarin Antinta babu daya da ta iya dauka, ji take kamar ana k'ara rura mata wutar kaunar Faruk. Ta matso da ledar ta bude, ta yi mamakin ganin kayan kwalam har da su meatpie nad'e a jikin tissue guda uku, ga wani kullin leda karami wanda tana budewa ta ci karo da alawoyi kala-kala. Harda su cake da robar ice-cream manya biyu.
   "Assalamu alaikum." Da bude kofar da sallamar nata duk lokaci guda ne
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
  60
"Ya Salam, haba Ihsan, meyasa haka?"
  Ihsan ta mike zaune idanunta jage-jage da ruwan hawaye. Ta ja majina.
"Kinga lokaci ya k'uremin ko Ikram? Da ace na bi shawararki da banga wannan rana ba."
  Ikram tausayinta ya mamayeta, ta dafa kafadarta gami da girgiza mata kai.
"Aa, lokaci har yanzu da sauransa Ihsan. Na fadamiki ki cire kunya ki sanarwa Faruk abindq kike ji game da shi koda ta hanyar  kafar sadarwa (whatsapp)ne. Kada ki karaya da wuri."
   Haka ta yita lallashinta sannan ta fita wajen yan uwanta. Tana fita Ihsan ta dauki waya ta kira Maminta. Ko sallama bata iya yi ba ta fashe mata da kuka gami da labartamata abinda ake ciki. Mami ta shiga damuwa ainun.
  "Ihsan kina kyautatamasa kuwa kamar yanda nace?"
   "Babu abinda bana yi Mami, har gyaran dakinsa hana Ikram nayi na ke yi, amma wannan duk ba ya gani, ni yanzu na yanke shawarar sanarmishi irin illar da sonshi ya yiwa zuciyata."
  Mami ta karya murya.
"Kina ganin hakan zai fi?"
"Eh Mami."
  Mami ta jinjina kai, kwarai kuma tasan Faruk yana da mutunci, bazai so damuwar 'yar uwarsa ba.
   "Shikenan, ayi hakan. Amma ki san abinda za kice dai."
   Haka ta yita lalla6a diyarta, bata son abinda zai ta6a farincikin 'yar tata ko kadan. A karshe ta sanarmata cewa an soma shirye-shiryen tafiyar Adnan Dubai inda ya za6a. Maganar ta yi mata dadi, hakan ya rage zafin da zuciyarta ke yi ta dan samu nutsuwa. Falon da bata koma kenan ba!
                  ***   ***   ***
                      RINGIM
      TSAFI GASKIYAR MAI SHI...

Kwarai wannan zance haka yake, don a kwana uku kacal! Dija da uwarta sun yi dukkanin k'ulla-k'ullarsu sun dauke hankalin Deen tsaf daga kan matarsa, kacokam zuciyarsa ta koma ga Dija. A yau lahadi ya yi shirin zuwa Ringim, don tun cikin ranakun aiki ya ke son kawomata ziyara tana hanashi. Yau kam ko sanarmata baiyi ba sai ganinsa sukayi. A kofar gidan ya faka motarsa, ya kirata a waya ya sanarmata yana kofa. Ta yi mamaki har da tsalle da ihunta na murna, Baba Habiba itama ranta sakayau. Ta taimakamata ta shirya sannan ta mik'amata turare da kwallin da suka kar6o.
  "Saka 'yar albarka."
  Tana dariya ta soma da kwallin sannan ta feshe jikinta da turaren mai kamshin 'yan bori, wanda aka tabbatarmusu cewar Deen zai ji ba kamshin da ya fi so anan duniya sai shi.
  Daga haka ta fita ta sameshi, ai kuwa yana ganinta ya budemata kofa ta shiga. Nan take ya ji wutar kaunarta na k'ara ruruwa cikin ransa, sun sha hira inda ya matso dab da ita yana jin kamar ya sanyata jikinsa saidai ganin idanin mutane dake kansu yasa ta tsawatarmishi. Ya sanarmata cewa da zarar ya koma zai turo magabatansa, wannan yafi komai yi mata dadi don ta lura ya shiga hannu ta yanda shi kansa kwata-kwata ya bar shakkar dangin Munira su ji labari.
    Ya sha hira sannan ya tafi, a daren ya k'ara dawowa, har suka gaisa da Malam Yahuza wanda ya yita mamakin ganinsa kuma da sunan ya zo wurin diyarsa. Koda ya shiga ciki ya tambayi Habiba, ta sanarmishi ai da aure ya ke sonta. Hankalinsa ya tashi da wannan amsa da ya samu, ya so nuna rashin goyon bayansa saidai ba shi da wannan isar a gidansa, sai ma ya tsinci bakinsa da furta kalaman nuna jin dadin al'amarin ba don har cikin zuciyarsa hakan bane.
   Ita kuwa Dija da Deen murzar juna sukayi son ransu, dakyar suka rabu.
  Washegari Baba Habiba ta nufi wajen aminiyarta ta sanarmata komai, shewa Saude ta yi don abin ba k'aramin dadi ya yi mata ba.
   "Kice lokaci ya yi? Ai karku damu da abinda mutane zasu ce matar mutum fa kabarinsa, atoh."
  Dariya Habiba ta yi tana dan waige-waige.
  "Wai ina Mariya ne ban ganta ba tun zuwana?"
  Saude ta murmusa.
"Mariya kuma da farin jini, tana nan zaune Dauda dan gidan Zinaru ya aiko kiranta."
  Habiba ta dan yi jim.
"Anya Saude? Dauda fa kamar na ta6a ji ya yiwa wata budurwa ciki?"
  Saude ta girgiza kai.
"Bar mutane da shegen karya Habiba, yaron nan har nan ya ke zuwa mu gaisa, kar kiso kiga irin kyautatawar da ya ke yiwa Mariya. Kuma banda abinki, yarinya da bata fi shekara tara ba?"
  Habiba ta jinjina kai.
"Shikenan, amma gaskiya ki saka idanu."
Saude ta gamsu da zancenta.

                 ***   ***  ***
                     ABUJA
     Washegari Faruk da wuri ya tashi kawai don ya ga Umminsa. Ai kuwa yana sanya kai a falon Hajiyarsa na sama ya yi tozali da ita tana aikin shara.
    Ta dago kanta jin sallamarsa, ta amsa a hankali sannan ta russuna ta gaisheshi.
  "Lafiya, kin tashi lafiya?"
Ta amsa da murmushi dauke saman fuskarta.
"Alhamdulillah."
  Ya dubi falon sannan ya dubeta.
"Kai Ummi, duk girman falon nan haka kike share shi? Sannu kinji? Karki damu na wani dan lokaci ne."
  Ta dubi hanyar dakunan mutanen gidan, (Hajiya  tana sashen mijinta)sannan ta dubeshi cikin murya k'arama ta ce.
  "Ka yi hakuri ka kyaleni don Allah kaga a falon Hajiya ne, komai zai iya faruwa."
  Ya ta6e baki yana mai gyara tsayuwarsa.
  "Ke ni na soma gajiya da wannan tsoron naki, me kike tsoro ne alhalin wataran gidana zasu daukoki su kawo? Kalli,(ya dubi jikinsa sannan ya maida dubansa gareta, ko wanka banyi ba na zo kawai domin na ganki ki ji dadi shi ne kike korata, why?"

  Maganar ma ta so bata dariya saidai kasancewar ba a nutse ta ke ba yasa bata dara ba, wato don ta ganshi ta ji dadi?
  "Na ganka amma don Allah ka bar..."
Jin motsin murda kofar dakin kwanan su Ikram ne yasa ta saurin juyawa ta cigaba da shara. Ihsan din ce ta fito daga ita sai riga iyaka gwuiwa da dogon wando (cotton) na bacci. Kanta ko hula babu, Faruk ya juyo yana dubanta. Ta karemishi kallo daga shi sai dogon wando na bacci da singilet, yana tsaye hannuwansa cikin aljihun wandon, ya kauda kansa daga gareta, ta fito cike da mamakin abinda ya kawoshi da safe bayan ta riga tasan baya fitowa sai ya yi wanka ya shirya, ta kai dubanta ga Ummi, shara take yi abinta, babu wani abu da ta gani wanda zai sa ta tsargu cewar akwai wata a k'asa, saidai zuciyarta ta kasa nutsuwa akan ganin da ta yi mishi tsaye kuma shi kadai tare da Ummi.
  A sanyaye ta gaisheshi, ya gyada kai, daga haka ya juya ya fice. Ta bishi da kallo kafin ta dubi Ummi wacce ta yi kamar batasan wainar da suke toyawa ba.  Karasawa ta yi ta tsaya a gabanta tana mai take tsintsiyar, Ummi abin ya bata haushi, ji ta ke kamar ta tureta ta fadi k'as. Saidai a fili bata nuna komai ba, ta dago ta dubeta fuskarta ba walwala babu kuma fushi. Ihsan ta watsamata kallon tsana don ta lura yarinyar kamar ta k'ara gogewa a yan kwanakin da ta yi a Abuja.
   "Tun yaushe Yaya Faruk ya shigo?"
  Abin ya so bawa Ummi dariya, ta barwa cikinta.
"Yana zuwa kika fito falon."
Ihsan ta dan yi sakato tana dubanta kamar dai bata yarda ba don jikinta ya bata akwai wani abun, sai kuma ta ja tsaki.
  "Koma dai menene, mutum ya kiyaye yasan matsayinsa."
  Ummi ta dan rausaya kai.
"To me ya kawo wannan maganar kuma?"
Cike da mamaki Ihsan ta dubeta.
"Eh lallai, har anzo ga6ar da zan fadi magana ki tuhumeni akanta? Lallai wuyanki ya soma kauri."
'Tukunna ma dai Ihsan, matukar zaki cigaba da gasamin magana za kico karo da fin haka.'
  A fili kuwa ta ce. "Allah Ya baki hakuri."
  Wawan tsaki ta ja ta yi gaba ta zauna saman kujera gami da kunna talabijin, daman abinda ya fito da ita kenan, kallon wani(series)na 'yan Philippines wanda bata samun kallo da dare sai karfe takwas na safe suke maimaicin sati duk ranar lahadi.
   Ummi murmushi kawai ta yi sannan ta cigaba da shararta zuciyarta wasai.
   
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
   59
Ta daure ta 6oye razanar da ta yi, ta amsa mata. Karasowa ta yi tana mai zaro ido.
  "Ke Ummi yau asirinki dai ya tonu, ashe kema 'yar hannu ce, naga ma kusan kin fi Sa'ade sa'a don kuwa ke kamun babban goro kikayi."
   Ummi da ta rasa meke mata dadi a duniya ta cigaba da kallonta tana ji kamar ta saki fitsari.
  "Me..me..kike so ki ce?"
  Binta ta yi dariya kadan lokacin da ta zauna tana mai sa hannu ta janyo ledar.
"Eh lallai dole ki rude, ki kwantar da hankalinki ki ci arziki, ai ni idan har za ki dunga yagamin abinda kika samo to fa kar kiji komai don ba ko da matsala da ni. Ki bi sannu dai da mutan gidan da su Bala(mai kula da shukoki), su ne abin ji."
  Ta fiddo meatpie ta gutsira. Ummi dai banda innalillahi babu abinda take fada a ranta, Binta ta ganota saidai ta to musu mugun fassara, to daman ina zata aminta cewar soyayya na tafi tsakani da Allah, namiji kamar Faruk zaiyi mata?
  "Wallahi babu makamanciyar abinda ki ke zargi tsakanina da Yaya Faruk."
  Binta tana taunar meatpie ta watsamata harara.
  "Wai kina zaton ban ganku sadda ku ka shiga wajen wanka ba? Haba Ummi, wannan ba abin rufemin bane, nifa makwafciyarki ce, idan ban rufamiki asiri ba wa zai rufa? Tun yaushe ya soma nemanki?"
  Ran Ummi idan ya yi dubu to ya 6aci don jin wannan mummunan zaton da Binta ta yi mata.

  "Ina miki rantsuwa da Allah abinda kike tsammani tsakanina da Yaya Faruk ba haka bane."
   Binta ta yi sakato.
"To menene? A banza zai kawowa 'yar aiki kayayyaki har haka batare da cewa yana da buk'ata akanki ba? Haba Ummi, ko kunnuwana sun kai dubu bafa zan yarda da abinda ki ke fad'a ba. Kedai ki saki jiki kawai arziki ne ya zo miki, idan ma kin ci sa'a nan gaba ya daga darajarki a gidannan."
   Ummi ta runtse ido, ta fahimci Binta ta yi nisa cikin zargin abinda ba haka ba. Bai kuma kamata ta barta da wannan bahagon tunanin ba.
  "Tsaya ki ji gaskiyar magana, amma don Allah ki rufamin sirrina."
  Binta ta tsaya tana dubanta.
"Karki damu, ki saki jiki ki sanarmin, wallahi zan bar zancen a tsakaninmu."
  Ummi ta kwashe abinda ke faruwa ta sanarmata. Binta wacce ta daskare awajen ta kasa ko kwakkwarar magana, mamaki ne ya cikata kwarai dagaske, ba don ya ganewa idanunta ba da sai ta iya karyata Ummi nan take, saidai kuma har zuciyarta ta aminta da hakan. Ta cigaba da karewa Ummi kallo, ba k'arya tana da kyawun gani a yaba kuma a so, amma abin mamakin, akwai fiye da ita masu son Faruk saidai wai ace basu isheshi kallo ba sai ita?
  Ummi duk ta k'ara tsorata ganin irin kallon da Binta ke bin ta da shi, ga dukkan alamu bata yarda da zancenta ba ne. Wannan yasa ta kara riko hannunta.
  "Wallahi iyakar gaskiyar kenan, na gayamaki banda wannan babu abinda ke tsakaninmu, na rasa kuma yanda zanyi ya bar shiga harkata."
   Binta ta jinjina kai gami da sauke ajiyar zuciya.
"Tab! Babbar magana. Amma kin kusa kiyi wauta wallahi Ummi, da ace ni na samu wannan damar da babu ta yanda zanyi watsi da ita. Aure fa Ummi? Auren ma da matashi irin Yalla6ai Faruk? Gaskiya ki sake tunani, ki cire tsoro kamar yanda yace din ki tabbatar kin ba shi goyon baya. Karki damu ni don na rufamiki wannan asirin to ba komai ba ne wallahi. Idan ma na ce zan tona ai na shiga uku don nasan nima korata zaayi."
  Ta karashe da dariya, Ummi kuwa ta murmusa, hankalinta ya kwanta kadan.
   Ta dibarmata kusan rabin kayan sannan Binta ta fice zuwa dakinta bayan ta kara jaddada mata akan kada ta sake ta bari wannan dama ta kufcemata. Ummi da to kawai ta bita.
           
   Ihsan tunda ta ji abinda Faruk ya ce wa Dakta hankalinta ya tashi, ji ta ke kamar ta yi tsuntsuwa ta je sashensa ta ganewa idonta ko dagaske ne. Wai ashe dai yana da budurwa wacce ya ke so ta ke zaman jiran gawon shanu? Sam bazai yiwu ba! Sai a yau ta ji tana son bin shawarar Ikram, wato ta sanarwa Faruk yanda ta ke jinsa a ranta. Ta numfasa.
'Shi kadai ne mafita.' Ta ayyana hakan a zuciyarta.
   Mintuna biyar da haka, sai ga shi ya shigo falon. Suka dubeshi. Haidar ya ce. "Ina shirin bin sahu na ga 'yar gidan taka sai kuma gakanan."
  Faruk wanda tun shigowarsa ya ke murmushi ya zauna a saman kafet kusa da kafafun Babban Yaya, hannu yasa ya dauki ayaba guda cikin wanda suke ci.
   "Yanzu Dakta saida ka tonamin?"
  "Ana 6oye abin farinciki ne?" Cewar Dakta. Ya girgiza kai yana 'yar dariya.
  "Yanzu fa na soma yak'in, ban kai ga cin nasara ba."
  Sukayi dariya gaba daya har Ikram, Ihsan ji ta ke yi tamkar ta fashe. Gaba dayansu sun yarda don tunda suke da kaninnasu basu ta6a jin ya yi musu zancen kowace mace ba sai a yau din.
   "Dariyar me akeyi?" Fadin Daddy wanda shigowarsa gidan kenan daga waje, ya yi bak'o. Bayan ya karaso ya zauna suka dubeshi. Babban Yaya ne ya soma magana.
  "Daddy kaninmu ya samo maka suruka fa."
  Da mamaki ya dubi Faruk wanda banda murmushi da taunar ayaba babu abinda ya ke yi.
  "Dagaske?"
Faruk bai amsa ba. Daddy ya ji dadi a ransa.
"Kai Masha Allah, na ji dadin wannan lamari. Ai gwara ka soma shirin auren kafin na yi maka na dole."
Aka dara, Daddy ba ruwansa matukar yana da lokaci yakan zauna da iyalinsa suyi hira da dariya. Hajiya Babba ta sauko itama tare da wata budurwa da uwarta ta aiko daukar mata mayafai, bayan ta sallameta ta dawo wajensu, alokacin Ihsan ta sulale ta bar falon don tsabar takaici. Nan itama aka fesamata, murmushi kawai ta yi tare da addu'ar nemawa danta za6in Allah. Daga nan kuma hira ta 6arke, Ikram tuni ta ankara babu Ihsan a falon hakan yasa ta bi bayanta.
    A can karshen gadonsu ta risketa ta sanya kanta cikin filo tana kuka har da sheshshek'a. Ta karasa ta zauna a gefenta.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

61
  Zaune ta ke a (Garden) tana wanke kayanta kala daya, tana yi tana dan wak'e-wak'enta. Bata da masaniyar cewa Faruk na daga barandarsa yana kallonta, a gabansa abin zane ne. Ya jima yana dubanta da murmushi dauke a saman fuskarsa kafin daga bisani ya hau zanata. Iyakar fuskar kawai ya zana, bayan kammalawarsa ya mike ya sauka.
  Ba zato ta ji shi zaune a gefenta saman kujera. Ta dubeshi gabanta na dukan uku-uku sannan ta dubi hanya.
   "Kar6i wannan kiga, hoton matar da zan aura ce."
   Gabanta ya fadi, ta dubi takardar da ya kanannad'e sannan ta dubeshi, shi dinma ita ya ke kallo da son lura da yanayinta. Murmushin yak'e ta yi.
"Hannuna da ruwa, kada na jik'a maka."
   "Kar6i ba komai."
Ta sa hannunta wanda ya soma rawa ta kar6a. Koda ta bude, kallon tsoro ta yiwa zanen don kuwa wani kishi ta ke ji yana sukar zuciyarta.
   "Ta yi kyau, Allah Yasa alheri."

"Ameen, nagode." Ya fada yana dubanta, ya tabbatar bata kalli zanen sosai ba, wannan alamu ne na tana sonshi kuma tana kishinsa hakan kuma ya mishi dadi.
   Ya dan lek'a fuskarta.
"Za ki halarci bikin?"
Ji ta yi kamar ta kai mishi bugu, ashe komai da ya ke fadamata a baki ya tsaya? Daman itama ta yi wautar daukar zantukansa ta saka a rai. Yaudarar kai kenan. Ta kauda fuskarta gefe.
"Um."
Ya yi wani murmushi.
"Mungode."
Daga haka ya bar wajen, ta bi bayansa da kallo, daidai da fatarsa fara k'al kalar 'ya'yan hutu ne, ina ita ina shi ne? Bata kyautawa kanta da rayuwarta ba da har ta bari kaunarsa ta shiga ranta.
  Ta k'ara duban takardar cike ba tayi wata-wata ba ta d'aga da zummar yagawa saidai me? Karo ta ci da wata mai kama da ita, ta zaro ido tana k'ara duba sosai, shakka babu ita ce, har  dan lotsawar kumatunta. Kunya ta kamata, shikenan Faruk ya gane tana kishinsa tunda har ta kasa 6oyewa. Kamar ance ta daga kanta, sukayi ido hudu da shi daga barandarsa. Ya kashemata ido daya, ta yi saurin mikewa ta bar wajen tana murmushi tare da mamakin yanda akayi har ya isa ga dakinsa, kodayake ba wani nisa ne daga nan ba.  Ta adana takardar cikin kayanta, saida ta tabbatar ya bar wajen sannan ta koma ga aikinta.
           
  Ihsan ta dubi Ihsan fuska a washe.
"Kina ganin hakan yafi?"
  Ikram tana murmushi ta gyada kai.
"Kwarai kuwa, ke kanki kusan komai zai fi zuwar miki da sauki, kinga cikin kyautar da za ki ba shi sai ki isar da sak'onki ta nan."
Ihsan harda tsalle ta yi ta rungume Ikram.
"Yaushe ya kama ranar haihuwar tasa?"
  Ikram na dariya ta amsa.
"Jibi ne, sha shida ga watan (March), kada mu sanarmishi batun fatin, ya kasance mun bashi mamaki, saidai ya dawo gida ya tarar da komai."
  Sukayi dariya.
"Daidai kenan." Cewar Ihsan.
"Naji, taso muje mu yi shawara da Hajiya."
  Koda suka je, batun fatin kawai suka sanarmata, nan kuwa ta basu goyon baya dari bisa dari don Faruk tun yana da shekaru ashirin rabon da ayimishi wani birthday party. Ta taimaka musu da kudade suka soma shiri da sanin Daddy da yayyunsa maza har ma da matansu. Duk uban gayyar ma baida labari, asalima ya mance da wani batun ranar haihuwarsa da ta kusan zagayowa.
                    ***   ***   ***
                        RINGIM
   Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba don kuwa a ranar litinin Deen ya iso da wani baffansa wanda shi kadai ya samu dakyar ya lalla6a akan zai nema mishi auren Dija, iyayensa dai sunce babu hannunsu hakanan basu yarje mishi ba don wannan cin amana ne, saidai adalilin makancewa da ya riga ya yi a son Dija ko kusa bai dauki maganarsu da girma ba, haka ya samu wani kanin mahaifinsa ya shige mishi gaba. Koda suka zo ga Malam Yahuza, ba yanda ya iya hakanan ya kar6i kudin auren shi da wani makwafcinsa, a karshe aka tsaida maganar aure nan da wata daya kamar yanda Deen ya nema, Malam Yahuza ya zo mishi da korafin cewar sai ya shirya amma Deen ya tabbatar mishi matukar saboda kayan d'aki ne, to fa ya dauke mishi komai. Sun cika da mamaki kwarai, shi kuwa Deen ji ya ke yi idan har baayi auren nan ba, to kuwa so da shaawar Dija zasu iya mishi lahani.
   Kafin kace me, gari ya dauka cewar Malam Yahuza ya kar6i kudin auren Dija daga Zahraddeen miji ga'yar uwarta. Ai kuwa magana har gidan iyayen Munira. Sai ga mahaifiyar Munira da kanta, Bilkisu ta zo har gidan.
  A tsakar gidan ta iske Malam Yahuza da Habiba, da sallama ta shiga suka amsa. Habiba ta saki fuska.
"Aa, Bilkisu kece tafe? Karaso mana."
  Bilkisu ta zauna saman kujera yar tsugunno sannan ta dubi dan uwanta dake cin magani kamar ya ga kashi.
  "Yaya ina wuni."
"Lafiya." Ya amsa dakyar, ta gyada kai, bata wani damu sosai ba tunda daman haka ya saba amsa gaisuwarsu a wasu lokutan idan Habiba ta murda kambunta.
  "Wani labari na ji a gari shine na zo don tabbatar da gaskiyarsa."
  Habiba murmushi kawai ta ke, Malam Yahuza ya kara tamke fuska, acan kasan zuciyarsa ko kadan bai jin dadin abinda ke faruwa saidai ba halin nunawa tunda yana gaban sarauniyartasa.
   "Wane magana kuma?"
"Wai Zahraddeen zai auri Khadija?"
Kafin ya yi magana Habiba ta amshe.
"Gaskiyar maganar kenan Bilkisu, yanzu nake shirin aikamuku cewar ku zo amsar kayan saka rana da lefe jibi, sai kuma ga ki da kanki don Allah ki aika a gayawa sauran dangi na kusa da ke."
    Bilkisu ta rasa me za ta ce, tsananin mamaki da tsoron hali na DAN ADAM su ne suka fi cikata. Ganin abin ta ke yi kamar almara, kamar dai a ire-iren litattafan da ta ke sauraro a shirin Rai Dangin Goro, ashe da gaske yana zama gaske?
   Ta mik'e tsaye sakamakon ruwan hawaye da ya soma kwaranyo mata a saman fuska. Ta dubi dan uwanta.
"To madallah, nagode kwarai da wannan cin amanar zamantakewar, babu abinda zance muku saidai duk wanda ya yi mai kyau kansa, akwai ranar k'in dillanci. Tabbas kun nuna hali irin na DAN ADAM na butulci, amma bakomai, Allah Yana nan."
  Daga haka ta sanya kai ta fice tana share fuskarta da mayafi. Tana jin sababin da Habiba ta ke yiwa yayanta akan yana ji ta ci zarafinsu bai dauki wani kwakkwarar mataki ba.
   Koda Bilki ta isa gida saida ta sha fadan mijinta Malam Amadu akan dalilin da yasa bata bi maganarsa ba ta je gidan, ya kuma gargadeta akan kada ta sanarwa diyartasu tukunna har sai anga abinda hali ya yi. Daga wannan suka rufe maganar sai jimami da tunane-tunane.
                  ***   ***   ***
                      ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  61
                      ABUJA
  Tun wajejan uku na rana ta lura gidan kamar akwai wani shagalin da zaayi a dalilin gyara(decoration) da ta ga Ihsan, Ikram harma da Intisar (wacce ke fama da ciki wata uku) suke yi a (Garden). Abin kyalkyali suke sanyawa mai ban shaawa, ita tana gefe saidai a bata umarnin mik'o ruwan sha, mik'o balan-balan(balloon). Hada ido goma idan zasuyi da Ihsan, to fa saita watsa mata mugun kallo har dai a karshe ta raba kanta da kallonta. Hajiya Babba na zaune saman daya daga cikin kujerun da suka jera sai waya ta ke yi da surukarta(Jiddar Dakta Ridwan) akan batun (Cake) da(snacks) da suka bayar da oda. Abinci kuwa, Fadila matar Babban Yaya ce ta dauki nauyin girkawa a gidanta sannan ta zo.
    Suka dauko wani tangameman hoton Faruk wanda ya ya juya fuskarsa yana dan murmushi, kamar dai wanda bai so akayi hoton ba saidai hakan da ya yi ba karamin kyau ya yi ba, yana sanye da riga mai hula sai dogon wando a farfajiyar gidan, ya yiwa Ummi kyau sosai. Hoton an kafeshi a daidai inda suka sanya teburin ajiye (cake). Bayan komai ya kammalasannan Ummi da Binta suka tattare ledojin da sauran takardun da aka zubar a k'asa.
     Haidar shine ya yi musu taimakon sanar da dukkan wasu abokan karatun Faruk da suke a garin, hakanan a 6angaren Ihsan ta gayyaci wasu kawayenta biyu mazauna Abuja domin su zo ta nunamusu mutumin da ta ke fatan ya zama mijinta. Ikram itama kusan dukkan kawayenta ta gayyata, bayan Magriba suka sanya fatin.
    Duk wannan abu da sukeyi, Faruk ba shi da masaniya, zuwa dai lokacin yasan da cewa ranar ce ta(birthday) dinsa don tun sha biyun dare ya soma tsintar sak'onnin tayashi murnar cika shekaru talatin cif a duniya. Wasu ya basu amsa, wasu kuwa bai saman dama saidai ya aikamusu da alamar jinjina(like).
    Tun karfe shida, mutane suka soma zuwa, kowannensu ya ci ado kamar wani gagarumin biki akeyi musamman ma matan da suke zuci-zucin haduwa da Matasan yaran Gen Ahmad Danzaki ko wani cikinsu zai kyasa koda kuwa ace basu samu shiga wajen Faruk Danzaki ba. 
  Binta ta dubi Ummi.
"Oh ni Binta, ji yanda ake daukar kwalliya kamar baza"a mutu ba, ji sutura?"
  Ummi wacce har lokacin bata bar lek'en windo ba ta murmusa.
"Masu abu da abinsu?"
Ta6e baki Binta ta yi.
"Lallai kam, nasan dai duk don ya kyasa ne suke hakan, wasu ma ga dukkan alamu gayyar sod'i ne. To kwalelansu, Yalla6ai sai ke."
  Abin ya bawa Ummi dariya ta dara tana mai girgiza kai.
"Kai Binta, wai wa ya gayamaki hakan mai yiwuwa ne?"
   Binta ta yi kwafa.
"Ke kike ganin wuyarsa, amma na tabbatar karamin abu ne saidai kuma kin toshe kunnuwanki, ko kina da labarin Ihsan ma tana mutuwar son Yalla6ai?"
Ta yi kamar bata sani ba.
"Haba?"
  "Wallahi, jiya ina jinsu ita da Ikram tana zugata akan ta za6i kayan da zata sanya masu kyau sosai don ta burgeshi."
   Murmushi Ummi ta yi.
"Allah Ya tabbatar."
"Ba amin ba." Cewar Binta cikin sauri tana harararta, dariya kawai Ummi ta yi. Ta maida kanta ga duban windon inda ta nan suke lek'e, a ranta tana zuci-zucin ganin shigar da Ihsan din zata yi na sace zuciyar wanda ya riga ya fada tarkon kaunarta(ita Ummin).
   Misalin bakwai da mintuna kowa ya gama halartar wajen, ya yi daidai da dawowar Faruk gidan, ya yi hon yana duban kofar gidansu ganin motoci fin takwas a fake, mamaki karara ya bayyana saman fuskarsa, to me akeyi hakan?  Maigadi ya budemishi kofa ya shigo, a lokacin, kai tsaye wajen fakin ya isa, nan ma cike da mamaki ya ke duban(garden) din wanda a kusa da wajen ake fakin, duhu ne a wajen babu haske, haushi ya kamashi ganin ga shi akwai wuta, to meyasa Bala bai kunna fitilun wajen ba? Idan ma mutuwa kwayayen sukayi ai da sai ya sanarmasa tunda shi keda alhakin kula da komai na gidan, shi ya ke sanyawa a gyara, tun soma aikinsa ya daukewa mahaifinsa wannan nauyin.
      Ya fito kai tsaye yazo giftawa zai shiga sashensa, hasken fitilu suka dallare shi sakamakon kunnawa da akayi, ya dubi wajen da sauri. Mamaki tsantsa ya bayyana saman fuskarsa na ganin yanda wajen ya dauki ado ga wani tangameman hotonsa a wajen har da cake babba. Bai gama shanye mamakin ganin hakan ba, ya tsinci muryar su Ma'aruf dan Dakta Ridwan da sauran yaran Babban Yaya sun fito, dukkansu yaran  maza da mata cikin riga mai (coat) da wando, suna fadin. "Happy birthday to you!"
  Fuska a sake ya ke dubansu, bai kai ga gama shanye mamakinsa ba ya tsinci tafi da sowar tsoffin yan makarantarsu maza da mata wadanda basu kai ga yin aure ba da kannensa da kawayensu harma da yayyunsa maza suma suna masa wakar taya murna. Baisan lokacin da ya saki 'yar dariya ba.
   "What a surprise!"
Shine furucin da ya yi a fili na bayyana tsananin mamaki. Ko babu komai wannan abu ya burgeshi matuk'a, ya kuma ji dadinsa. Haidar ya dafa kafadarsa.
"Tafi ka chanja kaya, yau ranar murna ce."
  Ya yi murmushi sannan aka bashi hanya ya wuce. Ihsan wacce ta ci ado cikin doguwar riga(gown) kalar fari da ruwan hoda, gashinta mai tsawo an tufkeshi ko dankwali babu akanta ta yi kyau matuk'a, ta rungume Ikram tana ihun murna.
  "Kinga ni ko? Yaya Faruk ya ji dadin abinda mukayi."
  Ikram ta dara.
"Sai ma idan ya ji wacce ta kawo shawarar hakan."
Ta lumshe ido don dadi, suka sanya dariya.
   Acan kuwa saida ya watsa ruwa, daman ya yi sallar Magrib dinsa, wasu sabbin kaya ya gani ajiye a saman gado,  coat ne fari k'al mai bulun 'yar ciki masu dankaren kyau. Sun kar6eshi matuk'a, daidai da turare sabo fil aka ajiye mishi a saman gado, ya feshe jikinsa da shi. Shi kansa yasan ya kai a kirashi da Namiji.
   Tun da ya fito yanmatan suke binshi da kallo, ya karasa kai tsaye da Hajiyarsa ta rungumi kafadarsa tana jin kamar ta hadiyeshi don kauna.
"Kayi kyau Sadaukina."
Ya yi murmushi.
"Thank you Hajiyata."
Daga nan ya karasa ga inda aka tanadar mishi don zama, nan kuma shagalin ya soma. Aka kirashi ya yi jawabi na nuna tsansar farin cikinsa, sannan ya yi godiya ya koma mazauninsa yana k'arewa wajen kallo.
  'Ina Ummi?' Shine tambayar da ya jefawa zuciyarsa.
Baiwar Allah tana daga can wajen hanyar shiga dakunansu a tsaye tana kallo, tana gani Binta da karambani har da chanja sutura gami da karasawa wajen sosai amma ita ta ce sam bada ita ba, tana tsoron cin zarafin da Ihsan kan iya yi mata a cikin taron jama'a, tasan ba k'aramin aikinta bane ba. A can kasan ranta kuwa, tsananin kishi ne ta ke jinsa kamar ya kasheta na yanmatannan ta tabbatar kowaccensu shi ta ke hari, tana tsoron kadan ya zamana wata acikinsu ta burgeshi har ya ji yana kaunarta. Ganin da ta yi bazata jure ba ne yasa ta juyawa gami da komawa ciki.
      Shi kuwa daga nan inda ya ke zaune ya kasa nutsuwa haka nan ya ke daurewa kawai, ya yanke kek ya soma da sanyawa Babban Yaya a baki don tuni Hajiya ta koma ciki wajen mijinta, a ganinta taron na yara ne. Saida ya bawa yayyunsa kaf sannan suma suka bashi har suna 6ata mishi baki.
Daga nan kuma aka tafi sallah, bayan an dawo aka saka (cool music) inda kowa ya zauna aka hau ciye-ciye, Faruk dai ba magana ya kasa cin komai, burinsa kawai ya sanya Umminsa a ido, yana so ta tayashi murnar wannan rana itama.
  Tunaninsa ya katse sa'ilin da aka tsayar da wak'a, Haidar ne ya yi magana inda ya ce kafin a kammala ciye-ciye, za'a bawa Faruk dama ya zana musu macen da ya ke burin ace ta zama mallakinsa a rayuwa. Habawa, zo kaga ihu da sowa, kowa fadi ya ke hakan ya yi. Faruk ya yi wani murmushi kafin ya kai duba ga yanmatan da su ke zaune a wajen, kowaccensu da salon kallon da ta ke jifansa da  shi, har da masu chanja wajen zama yanda zai gansu sosai. Ya kai dubansa ga Ihsan wacce ta ke dubansa itama gaba daya kasan a tsorace ta ke. Duk waigensa bai ci karo da Sanyin Idaniyarsa ba, tunaninsa ya katse sa'ilin da aka janye teburin kek dake gabansa aka ajiyemishi karamin tebur mai dauke da alk'aluman zane da fente-fente. Sai(sketchboard) wacce aka sanya farar takarda a jiki.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
   
   63
    Ya dubi Haidar, duk wannan aikinsa ne, Haidar ya sakarmishi dariyar mugunta, sannan ya juya ga jama'ar ya bada umarnin kowa zai iya cigaba da ciye-ciyensa. Daga nan aka maida(cool music) din mai tashi a sannu-sannu.
   A hankali ya zare(coat) dinsa ya dora a saman cinyarsa ta hagu sannan ya dubi jama'ar wadanda suna ci suna dubansa.
  Ummi wacce tun sanarwar da Haidar ya yi ta tsinci kanta cikin mugun tashin hankali da fargabar abinda zai faru, tana tsaye ta kasa zama a dakinta karshe ta bude labule kadan tana lek'ensa.
   Cikin sa'a idanunsa ya sauka akanta, da sauri ta saki labulen gami da zamewa ta zauna kirjinta na luguden tara-tara na fargabar abinda ke shirin faruwa.
    Ya lumshe ido yana murmushi kafin ya dauki fek'akk'an fensir ya soma zanensa.
   "Wa Faruk Danzaki zai zana?"
Shine tambayar da kowannensu ke yi a junansu saidai babu tak'amaiman mutum daya da ya sani. Daidai da yayyunsa sun k'agu su ga fuskar masoyiyar dan uwannasu wacce basu ta6a sanin koda sunanta ba...!

   Toh fa!!!!
 
   
 Ummi a rud'e ta k'ara d'agowa gami da lek'awa. Hankali kwance ya ke zanensa banda murmushi babu abinda kake gani a saman fuskarsa. Wasu ruwan hawaye ne suka zubomata, shikenan yau babu ita ba k'ara kwana a gidannan. Da sauri ta juya ta soma harhad'a kayanta don bil hakki ita kadai tasan iyakar rudanin da ta shiga.
   Gogan kuwa, ya kwashi tsawon minti goma sha biyar kafin ya kammala ya mik'e tsaye, ganin haka yasa kowannensu mik'ewa, kowace budurwa awajen babu wacce kirjinta bai bugu da sauri-sauri don fargabar fuskar da zasu gani. Haidar ya k'ara tasowa ya iso gareshi, ya kai dubansa ga takardar zanen, ya k'urawa zanen ido, babu abinda kake gani sai manyan idanunta, ya yi alamun nikaf wanda ya rufe gaba daya fuskarta,  sai kadan daga siririn hancinta da ya dan fiddo mai dauke da karamin bak'in tabo daga sama. Ya kauda lasufika sannan ya harareshi.
  Haka mukayi da kai?"
Faruk da ke kokarin saka kwat dinsa ya daga mishi gira kadan.
"Ina kishin a ganta."
  Haidar ya jinjina kai yana dariya sannan ya kara duban hoton sosai.
"Kamar na ta6a ganin mai irin tabon nan, saidai bazan iya tuna a ina ba."
  Faruk ya murmusa kafin ya k'ara daukar alk'alami, daga k'asa ya rubuta farkon sunanta.
"H"
Haidar duk iyakar tunaninsa bai ganeta ba, a karshe ya daga kafada kadan gami da maida dubansa ga jama'a wadanda ke jin kamar su tashi su warci hoton su sha kallo. Baice komai ba ya juya zanen ya nuna musu.
  "Ga wacce Kanina ya zana, sunanta da harafin H ya soma, ya dai yi mana kwalelan fuskarta inda ya ce yana kishin a ganemishi kyakkyawar fuskarta."
   Dariya matasan suka sanya, ita kuwa Ihsan ido ta k'urawa zanen, ta kasa gane ko wacece ita.
  "Wace kenan?" Shine tambayar da da yawa daga yanmatan. Ihsan ta dubi Ikram cikin rawar murya don har ta soma kwalla.
  "Wa ki ka sani mai farkon suna H?"
Ikram wacce tausayin Ihsan ya mamayeta ta daga kafada kadan.
  "Bani da masaniya akan kowacece, Hafsa kadai na sani sai Hadiyya, yanzu duk sunyi aure ma."
   Ita kuwa Ummi jin maganar Haidar ne yasa ta tsayawa daga abinda ta soma na watsa kayanta cikin yar jakarta. Ta mike da sauri ta lek'a, saidai bata ganin zanen yanda ya kamata, hakan yasa ta fitowa wajen, a daidai bayan bishiyar dogon yaro ta dan la6e tana hangen zanen. Ta dan sauke ajiyar zuciya duk kuwa da cewar akwai sauran rina a kaba, ta shafi karan hancinta, tabbas bakin a tabon nan yana nan inda ya ke wanda ta samu asanadin wani ciwo da ta ji awajen tun tana yarinya. Gabanta na dukan tara-tara ta zaro ido.
'Yanzu idan aka gane ni da wannan tabon ya zanyi ni Hasiya?' Ta tambayi zuciyarta, tambayar da tasan amsar bai wuce na ta shiga uku ba.
   Lokacin da Haidar ya kammala addu'oin fatan alheri shi da budurwar da ya ke so, aka soma mikewa da kadan kadan ana mik'a mishi kyautuka. Ihsan ta so barin wajen don ita kadai tasan yanda ta ke ji, saidai Ikram ta lalla6ata gami da nunamata kada ta sake ta yi wasa da wannan damar, shi kadai ya yi mata saura, haka ta daure ta karasa gami da mik'a mishi kyautar da ta tanada domin shi wanda a ciki sak'on da ta ke son isar mishi ya ke. Ya kar6a yana mai dubanta, ko baa fada ba, idan ka kalli idanunta kasan ta yi kuka. Bai nuna ya gane komai ba, godiya ya yi mata sannan ta bar wajen da saurinta.
   Haka kawai sai Ummi ta ji tausayinta, tana son maso wani, son wanda ta ke yi don shi baisan tana yi ba. A sanyaye ta juya ta bar wajen ta koma daki. Bata yi mintuna uku da shiga ba ta ji an murda kofar da sallama an shigo. Ai batasan sadda ta mik'e tsaye ba tsabar kidimewa. Murmushi ya sakarmata sannan ya tura kofar ya rufe. Karasowa ya yi yana dubanta.
  "Matsoraciya Ummina."
  Ta yi raurau da ido, ya girgiza mata kai.
"Kar fa kice kuka zakimin."

   Ta yi k'asa da kanta. Yasa hannu a ha6anta ya dago fuskarta suka dubi juna ido cikin ido. Ta lumshe idonta don ba zata jure kallon kwayar idanunsa ba. Ya saukr hannunsa gami da sakin ajiyar zuciya. Allah kadai yasan irin wutar kaunarta da ke ruruwa a zuciyarta a kowane dak'ik'a.
Hankalinsa ya kai ga kayanta da rabinsu ta sanya a jaka ga wasu a k'asa.
  "Menene wannan?"
Ta dubi kayan sannan ta tuna ashe fa guduwa ta yi shirin yi.
  "Bakomai, linkesu nake yi."
Ya durkusa gaban kayan ya soma dagasu, duk ba wasu kayan kirki gareta sosai ba, ya girgiza kai kawai ya mike tsaye. Ta dubeshi kadan.
"Domin Allah ka tafi Yaya Faruk, kada a je nemanka."
   Ya rungume hannunsa a kirji.
"Wai kuwa Ummi kina kallon kanki a madubi kuwa?"
  Bai bari ta yi magana ba yasa hannu ya dauki hodarta dake gefe ya bude gami da juyamata, ta dubi dan madubin na hodar, kafin ta sauke idanunta kasa. Ya numfasa da murmushi saman fuskarsa.
  "Shikenan dai."
  Shiru ya biyo baya, tana ji Haidar na cigiyarsa ta lasufika akan ya zo sallamar bak'insa. Ta daure ta yi magana.
"Ina tayaka murnar wannan rana, Allah Ya k'aro shekaru masu albarka, Ya taimaki rayuwarka."
  "Amin. Allah Ya nunamana na aurenmu haka. Thanks my Ummi, zo muje ki rakani mu sallami bak'inmu."
   Ya kai hannu da zummar riko nata, ta ja baya da sauri tana girgiza kai.
"Ke na soma gajiya da 6oyon da muke yi, aurenki fa nakeson yi. Amma dai..."
  Ya jinjina kai kawai sannan ya juya ya fita, a kofar sukayi kici6us da Binta ta gaisheshi, fuska a daure ya amsa gami da fadin.
  "Ki kiyaye bakinki." Shi ne abinda yace, ta amsa da to cikin sauri, daga nan ya yi gaba. Da sauri ta fad'a dakin wajen Ummi. Ummi na ganin itace ta sauke numfashi don a farko da ta ji maganar da Faruk ya yi duk ta dauka ko da Ikram ya ke. Binta ta kama ha6a bakinta a washe.
    "Ke Ummi, abu fa ya soma zafi, anya kuwa nan gaba Yalla6ai bazai daukeki daga sashen yan aiki ya maida cikin gidansu ba, kafin daga baya ya daukeki cancak zuwa gidan aurenku?"
   Ummi ta yi dariya, maganar Binta ta karshe ta yi mata dadi. Ita kuwa Binta k'irr ta tsayar da ido tana duban fuskar Ummi kafin ta doka tsalle ta rungumeta tana ihun murna.
"Kece, daman nasan ke ce wallahi."
Ummi ta kwaci kanta tana kokarin rufewa Binta baki.
"Ki rufamin asiri kiyi shiru kada wani ya ji."
  Binta tana dariya ta yi mata nuni da tabon dake a saman hancinta.
  "Wannan tabon nayi mamakin yanda Yalla6ai ya ganoshi, naga sai an k'ura miki ido ake ganeshi."
   "Shiyasa nake gudun ranar da asirina zai tonu."
  Guntun tsaki Binta ta ja.
"To menene? Ke saifa kin zama jaruma wallahi. Ni kizo muje kaya aka bani na kai dakin Yalla6ai, ki zo ki tayani kwashe kyaututtukansa."
  Girgiza kai ta yi.
"Ki taimakeni ki je ke kadai babu inda zan je."
Dariya Binta ta saka.
"Kekam ban ga irinki a fagen tsoro ba."
Ummi ta bi ta da kallo kawai har ta fice.
  Haka shagalin ya k'are kowacce budurwa jiki a sanyaye don ba'a samu shiga ba ta ko'ina.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
 
  63
     Misalin tara na daren, falon Hajiya Babba babu kowa sai matasan yaranta da matansu, sai kuma su Ikram.
  Fadila ta kar6i hoton zanen daga hannun Jidda tana mai kuramishi ido itama. Jidda ta dubesu.
"Nikam kaina ya k'ulle ai, nayi iyakar yi na na kasa gane wacece wannan wallahi. Kai na karfen baka kyauta mana ba, yanda muka ci burin yau mu ga hoton matarka?"
  Ta karashe tana duban Faruk wanda abincinsa ya ke ci babu ko alamun damuwa a fuskarsa.
  "Ke dai bari kawai Jidda, ni kaina ya soma sarawa ma don kallon zanen." Cewar Fadila. Sukayi dariya, Hajiya Babba ta mike tana fadin.
"Um, idan dai Sadauki ne kadan daga aikinsa, a komai sai ya bada mamaki."
Daga haka ta barsu suka bita da kallo. Faruk ya dubi Haidar.
"Broda, ina fa da magana da kai."
  "Bakasan hanyar gidana ba?"
  Ya yi murmushi.
"Sau daya fa na ta6a zuwa gidanka tun kafin tariyarka, kaga kuwa na mance."
  "Aa Lil, baka kyauta ba kam." Cewar Dakta.
   Babban Yaya na murmushi ya cafe.
"Kuyi mishi uzuri, aikinsa babu hutu sosai."
    Haka sukayita hirarsu, a karshe bayan duk sun tafi, Ikram ta mike rike da takardar zanen zuwa dakinsu.
   Ihsan na kwance har kanta ya soma sarawa sanadin kukan da ta ci. Ta mike zaune gami da kar6ar takardar.
  "Duk iyakar tunani ban gane wacece wannan ba Ikram, saidai na rasa dalilin da yasa jikina ke bani kamar na santa, kuma na ta6a ganin kwayar idanun nan."
  Ikram ta jinjina kai.
"Ni kaina nakasa hakura da kallon zanen wallahi, gani nakeyi kamar nasanta."
Ihsan ta ja tsaki gami da wurgi da takardar.
"Me zan amfana da shi a saninta ma? Ni yanzu gaba daya na gaji da zaman Abija, gida zan koma."
  Ikram ta dubeta.
"Kada kiyi saurin karaya ina kara baki shawara, ni nasan taimakon da zan miki."
  Ihsan ta dubeta cikin rashin fahimta.
"Ban fahimceki ba."
Murmushi Ikram ta yi.
"Kedai ki bani lokaci."
  Jin hakan yasa Ihsan ta dan samu nutsuwa.
               
  A daidai gaban motar Haidar suka tsaya, Intisar na ciki tana jira su kammala. Haidar ya dubeshi.
  "Ina jinka."
Faruk ya gyara tsayuwa.
"I am serious fa, wacce na zana dagaske ita nake son aure, saidai ni a wajena ban dauki hakan matsala ba kamar yanda ku ma bana tunani za ku k'i farincikina."
   Haidar ya daga kafada kadan cikin rashin fahimta.
"Me ya kawo duk wadannan? Yarinyar musulma ce?"
"Eh."
"Tana da asali?"
"Kwarai kuwa."
Murmushi ya yi gami da dafa kafadarsa.
  "Idan akwai hakan, a ganina babu wata matsala, gayamin a ina ta ke?"
  Faruk na murmushin shima ya shafi sumarsa.
"Zan zo gidanka gobe daga ofis."

"Dayake taka ce zata kawoka ko? Ai yanzun na ga kafarka."

  Sukayi dariya sannan sukayi sallama ya shiga motar suka wuce.

                     ***   ***   ***
                        KADUNA
                 
    Munira tana zaune ta kurawa talabijin ido, saidai gaba daya hankalinta baya tare da kallon, Tasleem da Haris sai wasa da keke sukeyi ko kusa basu da wata matsala. Babban damuwarta bai wuce na auren da Deen ya sanarmata zaiyi ba da macen da sai su share awanni uku cikin dare suna waya, har yau batasan wacece ba saidai babu irin cin kashin da bata gani daga gurinsa tun soma soyayyarsa da yarinyar. Tunaninta ya katse sa'ilin da wayarta ta dauki k'ara. Ganin lambar yar uwarta Atika mai aure a Ringim yasa ta rage k'arar talabijin gami da dauka. Bayan sallama ko gaisawa Atika bata bari sunyi ba ta soma magana.
  "Wai kuwa Munira kinsan abinda ke shirin samunki kuwa?"
  Munira ta kara gyara zamanta kafin ta saki murmushi mai ciwo.
  "Na sani Yaya, to ya zanyi? Aure kaddara ce ai, shi ya sani."
  Atika ta saka salati.
"Ikon Allah, oh ni Fatima, ba dai kema sun shanyeki kamar yanda suka shanye Deenin ba? Wallahi na tausayawa rayuwarki Munira, cab!"
Munira ta ji gabanta na dukan tara-tara. Daman ya lafiyar giwa....
  "Yaya wai me kikeson cewa? Ko kina da labarin wacce zai aura ne? Ni wallahi nan da kike gani ko sunanta bazan iya kawomiki ba don a Yanzu bai daukeni wata abar ba yanzu ballantana ya sanarmin."
   "To wallahi Munira bacci bai ganmu ba, tashi tsaye ya dace muyi da addu'a, Deeni ba kowace zai aura ba face Dijar Baba Yahuza."
  Jin zancen ta yi tamkar saukar aradu, wani salati ta saka da karfi kafin kuma ta yi wurgi da wayar ta zube anan ta hau kuka.
  A guje yaranta suka yo kanta tare da Asiya mai tayata aiki.
  "Lafiya Hajiya?"
Ta kasa barwa cikinta, ta sanarwa Asiya matsalar da ta ke ciki yanzun. Asiya ita kanta hankalinta ya tashi ainun, daman ta zargi hakan tsakanin Dija da Oga, ita take ganin yanayin muamalarsu a gidan. Ta yi ta bawa Munira hakuri, karshe dai ganin yaranta sun shiga damuwa ta mike ta dauki wayarta da ke faman ruri ta yi daki. Atika ce, nan ta shiga bata baki da nunamata addua kadai ce mafita
  "Yaya ai ni na hakura da zama da Deen ma."
  "Me kenan kikayi idan kinyi hakan Munira? Ashe ma ta ci galaba kenan, kada ki soma wannan bahagon tunanin."
  Daga haka sukayi sallama. Munira ta cigaba da kuka har ta gode Allah, lallai DAN ADAM butulu ne, kayi mishi alheri ya sakamaka da sharri, ko a mafarki bata ta6a hangen haka ga Dija ba, bata ta6a kawowa zata ci amanarta har haka ba. Wannan rayuwa da me ta yi kama?
   Ta jima cikin wannan hali har dawowar Deen daga wurin aiki bata iya komai ba. Daman ba wani nemanta ya ke yi ba yanzun, taso zuwa ta sameshi saidai kuma ta ga rashin alfanun hakan. Wannan yasa ta zuba ido ganin yanda lamuran zasu cigaba da kasancewa, mik'awa Allah lamarin shi yafi kamar dai yanda Yayarta ta ce.

                ***   ***   ***
                    ABUJA
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
 
  64
                    ABUJA
  Intisar sanye cikin riga doguwa 'yar kanti, ta ci kwalliyarta daidai misali ta fito daga kicin dauke da kwanukan abinci ta jera saman tebur inda Haidar da Faruk ke zaune. Ta gaida Faruk ya amsa shima ya gaisheta. Abin ma ya basu dariya.
"Ba dariya, matar yaya ta ke ai."
Haidar ya harareshi da wasa.
"Sai yanzu ka sani?"
    Dariya kawai ya yi, Intisar dai bata saba irin wasan da Faruk ba don bai fiye sakarmusu ba, murmushi kawai ta danyi. Bayan ta gama(serving) dinsu ta bar wajen. Saida suka kammala ci sannan suka wuce masallaci bayan dawowarsu ne suka zauna a falon Haidar. Haidar ya dora kafa daya kan daya.
  "Ina sauraronka."
  Faruk ya mik'a mishi waya. Haidar ya kar6a yana kallo, ido waje kuma ya ke kallonsa.

"Wannan kamar Ummi yar aikin Mami."
Faruk cikin jin zafin yar aikin da ya kirata ya jinjina kai.
"Yes itace, a wurina ba 'yar aiki bace, budurwar da nake shirin aure ce, ita kuma nake son ta zama surukarku."
 
  "Kasan abinda ka ke cewa kuwa?"
"Kwarai kuwa, Ummi nake so da aure."
   Haidar ya dan yi jim kafin ya girgiza kai cikin sauyin yanayi,
"Bazai yiwu ba."
  "Saboda ita ba mutum ba ce?"
Faruk ya jefamishi tambayar rai a 6ace.
  Haidar ya dafa kafadarsa.
   "Cool down mana, ba nufina wai wani abin daban ba, saidai matsayinku ya bambanta, wannan abu ba mai yiwuwa bane, ka chanja tunani Faruk, da kamar wuya su Daddy su yarjemaka."
   Faruk ya murtuk'e fuska.
"Haka kake gani?"
Haidar da mamaki ya ke kallonsa.
"Kai baka gani?"
  Ya girgiza kai gami da kwantar da kai jikin kujera.
"Ban ta6a hangen hakan ba, ban kuma sani ba ko don na riga na yi nisa a kaunarta ne yasa ban gano ba? Ni yanzu kai na zo ka ban shawarar wanda ya dace na soma tunkara tsakanin Hajiyarmu da Daddy?"
  Haidar ya shafi goshinsa yana kara duban hoton Ummi sannan ya dubi Faruk.
"Ka sanarwa dukkansu alokaci guda. Ni a raayina, banga aibu a auren Ummi ba, na lura yarinya ce nutsastsiya sannan tana da kyawun hali da na fuska. Matsalar dai iyayenmu, idan sun amince shikenan, bansan raayin Babban Yaya da Dakta ba."
  Faruk ya dan ta6e baki.
"Nifa zan zauna da ita. Shawara kawai daman na zo nema awajenka, ka kuma tayani adduar samun nasara akansu."
   Haidar ya gyada kai yana dan murmushi.
"In sha Allahu, mai Ummi, zan tayaka. Amma wacece H din da ka zana?"
  Faruk ya dan dara gami da kashe ido daya.
   "Hasiya, real name dinta ne. Sunan mum dinta ta ci, amman ta rasu yanzu."
  "Kai Nawan." Cewar Haidar gami da ba shi hannu suka cafke kamar wasu abokai.
  "Wato komai nata ka sani? Duk ta yaya?"
  Faruk ya gutsira mishi labarin Ummi, ya dora da fadin.
"Tausayinta ne ya soma rinjayar zuciyata har na soma jin sonta a raina."
  Shi kansa Haidar ya tausayamata.
"Allah Sarki, rayuwa kenan, kowa da inda Allah Ya ajiyeshi, babu wanda yafi wani a wajenSa sai wanda yafi tsoronShi. Allah dai Ya datar da mu."
  "Ameen broda. Ni bari na k'arasa, waya nakeson zuwa na siyo."
  "Na wa kenan?"
Murmushi Faruk ya yi, Haidar ya dafa kafadarsa yana tayashi murmushin.
  "Lallai na yarda da Dakta ke cewa irinku da bakwa soyayya idan kun tashi yi to zakuyi mai ban mamaki."
   Abin ma sai ya bawa Faruk dariya, har wajen mota ya rakashi sannan sukayi sallama da zummar duk yanda Faruk sukayi da iyayen zai sanarmishi.
   
Hajiya Babba ta ajiye wayarta a gefe bayan ta gama amsawa ta dubi Ikram wacce ke zaman jiranta ta kammala.
  "Ina jinki."
Ikram ta yi gyaran murya ta soma magana.
"Hajiya daman akan Ihsan ne."
Cike da mamaki ta dubeta.
"Meyafaru da Ihsan din? Ko ta gaji da mu ne?"
   "A'a, daman..." (Ta kwashe tun farkon sadda Ihsan ta soma son Faruk har zuwa jiya da ta shiryamishi party na taya murnar ranar haihuwa.
   Hajiya Babba bayan gama sauraronta ta numfasa fuskarta dauke da damuwa.
  "Tun ba yau ba nasan yarinyarnan tana son Sadauki, saidai banga alamun Sadauki yana sonta ba."
   Ikram itama ta jinjina kai, tasan gaskiya ne.
  "Amma Hajiya bakya ganin a haka ya aureta idan yaso son ya shiga a hankali?"
   "Kina ganin zai yarda? Banason abinda za'a zo zumunci ya lalace, matukar akayi aure ba da son ran daya ba to shakka babu zai shafi zumuncinmu abinda bazan ta6a fatan naga ranarsa ba kenan."
  Ikram ta yi mamakin abinda Hajiyarsu ta ce, duk da tasan gaskiya ne, amma ai ya dace ta duba alak'a. Ita shaida ce akan yanda Hajiya ke tsananin kaunar dannata, batasan 6acin ransa tun yana karami kamar yanda ta samu labari daga yayyunsu. Ta bude baki zatayi magana Hajiya ta dagamata hannu.
"Ya isa hakanan, sai naji ta bakinsa, banason yi mishi katsalanda a lamari irin haka. Musamman lamari irin wannan na aure."
    Jiki a sanyaye Ikram ta mike zata fita daga dakin, ta dakatar da ita.
"Maganar ta tsaya iyaka nan, ban yarje miki sanarwa Ihsan ba."
   Ikram da ta rasa bakin magana, kai kawai ta gyada sannan ta fice har lokacin mamakin Hajiyarsu bai saketa ba, ko babu komai naka ai naka ne, saidai batasan hukuncin da zata yanke ba.
    Mintuna k'alilan da yin hakan, Faruk ya dawo gidan a gajiye, kai tsaye sashensa ya nufa ya yi wanka ya sanya doguwar jallabiya ruwan madara da wando kafin ya dauki wayar da ya siyowa Ummi na kamfanin HTC ya sanyata a chaji. A karshe ya nufi sashen Daddy.
  Acan ya iske Hajiya, suka gaisa kafin su shiga hira da iyayennasa. Can Daddy ya dubeshi.
"Son shekarunka talatin a duniya, ya ci ace zuwa yanzu ka soma tunanin aure."
  "Ai ina jin ya samu matar aure, bai kai da fad'amana wacece ba ko Sadaukina?"
  Murmushi ya yi yana mai shafar sumar kansa.
  "A ina take?" Fadin Daddy kenan yana mai gyara zamansa don yasan dagasken ne don dannasu koda wasa bai ta6a zancen kowace mace ba.
    "Ba ta yi nisa da mu ba sosai Daddy."
Hajiya da Daddy suka dubi juna, kafin su dubeshi.
"Ko 'yar gidan Alhaji Hamza? (Makwafcinsu)"
  Ya yamutsa fuska.
"A'a, asalima ita ba 'yar garin nan bace."
  "Wacece kenan?" Hajiya ta tambaya.
Ya yi shiru can kuma ya sunkuyar da kai.
  "Zan kawomuku ita ku ganta cikin satinnan In sha Allah."
   Suka gyada kai lokaci guda.
"Allah Ya kaimu." Fadin Daddy. Faruk da Hajiya suka amsa da amin, ita kuwa Hajiya ta soma tunanin kodai Ihsan ce?
DAN ADAM 
@RUFAIDA OMAR

64
Washegari Ummi ta kammala aikinta, tana shirin barin wajen Hajiya ta shigo, bayan ta gaisheta ta dakatar da ita da fad'in.
  "Ina jin zuwa Asabar zaki koma fa, ba don naso hakan ba sai don Madina da ta takura da zama ba mai tayata wasu hidindimun, ta ce yanzu ba wata matsala. Zuwa gobe za'a kawomin wata."
   Gaban Ummi ya fad'i, jikinta ya yi sanyi matuk'a. Shikenan ta kusa rabuwa da ganin sanyin idanunta. A fili ta k'irk'iro murmushi wanda ya yi kama da na yak'e.
  "To Hajiya, Allah Ya kaimu."
"Amin."
  Daga haka ta bar wajen da saurinta, tana zuwa (garden) ta zauna a kujerar da ta saba zaman wanki, ta ajiye bokitin mai dauke da tsummokarai, shiru ta yi tana tunani kafin ta daga kanta tana duban barandar dakin Faruk, shikenan ta kusa daina sakashi a ido koyaushe? Hawaye suka zubomata, ta jima tana shararsu kafin ta daurewa zuciyarta ta cigaba da aikinta. A ranar haka ta wuni jiki babu kwari, daidai da Binta ta lura da hakan, tambayar duniya ta yi mata saidai amsar daya ce.
"Babu komai."
Koda dare ya yi, ta taimakawa Binta da shirya tebur har lokacin bata da wani kuzari, abincin ma kasa ci ta yi sosai. Binta sai kai loma take yi, can ta dubeta.
"Wai menene matsalarki ne?"
Ta numfasa.
"Na fadamaki babu komai, kaina ke ciwo."
  Daga haka ta dan ja guntun tsaki ta mike.
  "Ni na k'oshi ma."
. Binta na kallonta ta wanke hannu ta bar kicin din zuwa daki.
"Um, ai shikenan idan ta yi wari ma ji."
  Daga haka ta cigaba da cin tuwonta. Ummi na tafe a sanyaye, wasa takeyi da jelar dankwalinta, yayinda ta fad'a duniyar tunani, ko kadan bata san inda take jefa kafarta ba, tasan dai hanyar dakinsu ta nufa. Babban damuwarta bai wuce Faruk ba, da kuma irin yanda take tunanin ko aurensu mai yiwuwa ne ko kuwa dai kawai iyakar soyayyar ce?
    Bata ankara ba ta ji ta yi karo da mutum har goshinta na ta6a kirjinsa, ta yi saurin ja baya a tsorace, sai kuma ta yi ido hud'u da hasken rayuwarta. Wani hadadden murmushi na gefen kumatu ya sakarmata. Sanye yake da riga marar hannu mai hula da wando(3quarter).
   Ta sauke idanunta kasa sannan ta russuna cikin rawar murya ta gaisheshi ya amsa sannan ya dubeta.
"Zo, ke na fito nema daman, na lek'a daki ban ganki ba."
  'Gwara da Allah Yasa ka ganni a hanya.' Ta ayyana a zuciyarta.
Ya soma tafiya zuwa samansa.
"Biyoni."
Ta yi sakato tana dubansa. Har ya taka matattakala uku, ya juyo yana dubanta. Tana tsaye cak, ya dan yi jim yana karemata kallo, ita dinma shi ta ke kallo a sace, can kuma sai ta daga kafafunta da sukayi mata nauyi ta soma bin bayansa. Ganin haka ya murmusa ya cigaba da tafiya tana biye da shi tana waige, cikin sa'a Binta ta zo wucewa da sauri ta sauka ta nufeta.
  "Ina zuwa don Allah, Yaya Faruk ke kirana, ki rufamin asiri."
Ta yi maganar cikin rad'a, Binta ta gyada kai tana dariya ciki-ciki don wannan soyayya tasu burgeta take yi, daga haka Ummi ta juya. Tuni gogan ya shige, a falo ta iske baya nan, tun da take bata ta6a yiwa sashensa kallon tsanaki ba, ko sadda Sa'a ta yaudareta ta kawota wajen KB, sam ba'a cikin nutsuwa ta ke ba. Falon adon fari da bulu ne, ya tsaru iya tsaruwa. Anan kasan (tiles) ta durk'ushe kamar yanda kowace yar aiki ta saba a gaban masu gida. A haka ya fito rike da kan waya da kwalinsa ya iso ya zauna saman kujera. Da hannu ya yi mata nuni da gefensa.
"Dawo nan Malama, saikace ba dakinki ba?"
    Ta saci kallonsa kawai ta dan yi murmushi kafin ta mike cikin tausayawa rayuwarsu, shikenan sun kusa yin nisa da juna duk da hausawa kance garin masoyi ba ya nisa. A kasa ta zauna saman kafet, shima ya zamo ya zauna a k'asan ta dubeshi saidai babu abinda ta ce.
  "Kamar kina cikin damuwa Ummina, sanardani abinda ya faru."
  Mamaki ya kamata yanda har ya fahimci yanayinta. Ta girgiza kai.
  "Bakomai."
Ba don ya yarda ba ya gyada kai sannan ya mik'amata wayar.
   "Rik'e."
Ta bude tafin hannu ya dora mata a kai.
   "Naki ne."
  Ga mamaki ta dubeshi.
"Ai..ai ni ban iya amfani da waya ba."
  Ya gyada kai da murmushi saman fuskarsa.
  "Nasan da hakan shiyasa na kiraki don koyamiki."
    Ji ta yi ranta ya yi wani mugun sanyi, saidai fa haduwar wayar ya tsoratata, bata ta6a ganin irinta ba.
   Jin kamshin turarensa ta yi daf da ita, hakan yasa ta dagowa a razane ta dubeshi, ya matso gefenta hankalinsa naga wayar, ya kar6a daga hannunta ya soma nunamata da yacce zata cire (pattern) wanda ya sakamata saboda tsaro. Sannan ya shiga ya soma da gwada mata budo sak'onni, da amsa waya, har gwada kiranta ya yi ta ga sunan "Hubbyna." Ya fito, bata san dai yanda zata fadi sunan a baki ba. Amma tasan wani abun ya ke nufi na soyayya.
   Sun dauki kusan mintuna fiye da talatin a haka har saida ya tabbatar ta iya yanda yake so, har (whatsapp) saida ya nunamata yanda zata amsa sak'onshi da mayarmishi da amsa, lambarsa kadai ce a wayar na gaba daya layukansu hudu masu tsada da ba wata diya mace da ta ta6a mallakarsu haka.
    Bayan ya kammala ya mik'amata kwalin.
  "Mun gama da wannan Ummina, yanzu maganar aurenmu ce ya ragemana."
Ta lumshe ido tana mai jin kamar ta saki ihun kuka, ya matsa yana fuskantarta.
   "Gobe juma'a nakeson bayyana ki ga su Hajiya matsayin wacce nakeso da aure."
     Ido waje ta ke dubanshi, hawayen da ta ke dannewa tuni ya fito ya soma sauka saman fuskarta.
    Ji ya yi wata iriyar kasala ta saukar masa, ya runtse ido cikin kasalalliyar murya ya ce. "Please stop it mana, na tsani ganin hawayenki ya zuba Ummi akan kuma dalilin da bai taka kara ya karya ba. Idan ke kin kasa jarumtar jure koma menene zai zo wanda bana fatansa ma, ni ya kikeson nayi ne? A'a Ummi, wallahi Faruk bazai iya daukar wani tsawon lokaci batare da Hasiya ba. Na soma gajiya, ni ban iya wannan rayuwar ta 6oye abinda zuciya da gangar jikina ke muradi ba. Bazan iya ba, gobe ki shirya, ina zuwa."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

66

A fili kuwa don ta kwantar mata da hankali. Ta nunamata bawani abu bane, ya dace ta koyi jarumta tun daga yanzu. Ta k'ara bata shawarar tashi tsaye da addua, inda ta tabbatar mata itama zata tayata. Ummi ta yi godiya sannan ta jawo ledar suka bude. Wani hadadden Atamfa (pink) ne mai turuwa, a wani 6angaren mai dan haske-haske, anyi dinkin riga da zani, koda Ummi ta daga rigar ta girgiza kai.
"Anya rigar nan zata yimin?"
"Tsaf ma kuwa, tashi ki gwada kedai."
Ba musu ta gwada, ai kam ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta cire suka cigaba da duba ledar, harda dan kunne da sark'a fashion mai kyau da agogo, harda turare kala uku da kayan kwalliya, abin bai tsaya anan ba har dasu takalmi fari kalar mayafin da ya sanyomata. Binta banda washe baki babu abinda takeyi, ita kuwa mai abin jikinta sanyi ya k'ara yi. Wayar ta k'ara dagawa tana juyawa.
"Kai Ummi ki godewa Allah, kin samu mijin da ya iya kula da matarsa wallahi."
  Murmushi Ummi ta yi.
"Kai Binta, har ya zama mijina?"
  "Haka nake miki fata 'yar kanwata, nidai nasan gudunmuwar da zan baki a wannan lokacin idan ya zo."
  Dariya kawai Ummi ta yi gami da girgiza kai, a ranta fatan hakan ya ksance takeyi.
Sun dan jima tare da Binta kafin ta mik'e ta yi mata sallama don ta soma hamma na jin bacci. Bayan fitarta ta maida kayan cikin ledar ta yi gefe da su.
   Alwala ta d'auro ta gabatar da nafila, ta jima tana addu'o'i kafin ta shafa ta koma makwancinta. Wayar ta k'urawa ido tana jujjuyawa, ta yi nisa cikin tunani wayar ta dauki k'ara.
'Hubbyna.' Shine sunan da ya fito, wani ajiyar zuciya ta saki gami da yin murmushi. Kafin ta dauka kamar yanda ya koyamata yacce zata yi.
   Sallama ta soma yi mishi ya amsa.
"Ba ki yi bacci ba, meyasa?"
Ta ji daddadan muryarsa har cikin jini da bargonta.
  "Bakomai." Shiru ya dan biyo baya can kuma ya yi magana.
"Ina fatan ba kuka kikayi ba?"
Da mamaki karara akan fuskarta ta girgiza kai.
"Ni..ni banyi kuka ba."
Ya yi murmushi mai sauti.
"Ni kuma jikina ya bani kinyi kuka Ummina, amman dai shikenan. Ya kika ga kayan, sunyi miki ko a chanja?"
  'Ni na isa nace basuyi ba?' Ta fada a zuciyarta batare da sanin ya fito fili ba.
"Har kin yi yawa indai awajen Umar Faruk ne. Ni ban ajiyeki nan kusa ba fa. Amma yanzu duk bazaki gane hakan ba sai bayan aurenmu."
  Ta lumshe ido tana mai jin wani kaunarsa sabuwa fil a cikin ranta.
"Inama hakan zata faru Yaya Faruk."
Furucin ya yi mishi dadi, ya fahimci ta soma sakin jiki da shi.
"Zai faru in sha Allahu Ummina, ki kwantar da hankalinki har zuwa ranar da Umarul Faruk zai mantar da ke dukkan bakkan ciki da iznin Allah, ranar da zamu kasance mata da miji abin so da alfahari. Matukar ni ne mijinki, bazan k'ara barin ki cikin hali na damuwa ba. Watakil sai kin gaji da ni, don daga ranar da na aureki, na daina zuwa aiki."
  Dariya sosai ya bata, sai gashi ta shiga yinta kwarai. Ya lumshe ido gami da k'ara rungume daya daga cikin kananun filon dake saman gadonsa. Shi kadai yasan yanda ya ke jin dariyarta. Ta tsaida dariyar cike da jin kunya. Murya kamar na wanda baya son magana ya ce.
"Naso ace kina gabana kike dariyar nan Ummi, yana daga cikin abinda ban ta6a gani ba daga gareki, kuma zanso na ganin."
   Ta sunkuyar da kanta tamkar yana ganinta ta hau wasa da igiyar hular t-shirt din dake jikinta.
  "Saida safe Yaya Faruk, bacci nake ji."
  "Ko na zo?"
Ta zaro ido kamar yanda ganinta, ya yi 'yar dariya.
"Matsoraciyata, na tabbatar kin tsorata. Shikenan saida safe, kiyi mana adduar fa."
  "To."
Daga haka sukayi sallama. Ta bi wayar da kallo tana murmushi. A karshe ta ajiyeta gefe, mikewa ta yi ta yi nafila sannan ta karanta istihara tana kallo a takarda kafin ta shafa ta kwanta.
                 WASHEGARI....!!!!

Cikin ikon Allah ta tashi da jin kwarin gwuiwa a zuciya da gangar jiki, kaso sitti na damuwarta ya ragu.
   Bayan Magriba ya shigo gidan, kai tsaye sashensa ya soma nufa. Bayan ya yi wanka ya nemi Ummi a waya, tana zaune tana harhad'a kayanta sanin da ta yi cewar gobe Asabar kuma a ranar Hajiya ta sanarmata shine na komawarta Kano, wayar ta katseta. Hannu tasa ta dauka, tasan ko waye mai kiran, gabanta na dukan tara-tara ta dauka da sallama. Ya amsa sannan ta gaisheshi.
  "Ki shirya Ummi, na dawo ina sama, da zarar na kammala abinda nakeyi zan sauko mu je."
  Ji ta yi kamar ta saki fitsari, ta daure ta gyada kai don bakinta ya yi mata nauyi. Shaf ta mance ma waya ce suke yi.
  "Ummi, meyafaru kuma?"
Ya tambaya a sanyaye. Sai lokacin ta dan samu ta yi magana.
"Bakomai, zan shirya."
Ya yi murmushi mai sauti.
"Ko kefa."
  Daga nan sukayi sallama. Ta yi k'uri tana duban wayar kafin kuma ta ajiyeta.
"Allah ka saukaka mana." Ta fada a fili, tana mai amsawa kanta.
     Shigowar Binta ya katseta, ta amsa sallamarta. Binta ta k'araso.
"Naga fa Yalla6ai ya dawo."
Ummi ta yi murmushin karfin hali.
"Munyi waya yanzu, yana nan kan bakansa, yanzun ma cewa ya yi na shirya."
  Binta ta jinjina kai.
"Sai ki tashi, hakanan za ki je kedai kiyita addua a ranki."
  Ta saka kayan, Binta ta gyaramata fuskarta, ta yi mata daurin dankwali mai hawa-hawa irin na zamani. Ta taimaka mata da sanya dan kunne da sark'an. Sai kuma ta saki baki tana kallonta.
  "Masha Allah, wallahi Ummi na k'ara ganin abinda Yalla6ai ya hango wajenki, Ummi bakiyi kalar 'yan aiki ba."
  Ummi ta girgiza kai bata iya cewa komai ba don a yanzun ita kadai tasan yanayin da ta ke ciki.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

  65
  Mik'ewa ya yi ya koma daki ta bishi da kallo cikin jin wani shauki na kaunarsa.
  'Kaico, Yaya Faruk an kusa rabamu.'
Ta fad'a a ranta, jikinta yana bata cewa komai ya zo karshe, watakil harda zamanta cikin zuri'ar tasu gaba d'aya, tasan maganar Antinta ya kusa tabbata wanda ta ce.

'Karki manta matsayinmu awajen mutanen nan, mu 'yan aiki ne, ba su daukemu komai ba face wannan Ummi. Bar ganin suna mana dariya, duk sadda muka bari wasu lamura suka afku ranar zasu tunamana cewar mu kaskantu ne awajensu, ranar zasu tunamana matsayinmu na marasa galihu.'
   Hannunsa ta ji saman fatar fuskarta yana sharemata ruwan hawaye. Ta dubeshi, fuskarsa kai ka rantse bai ta6a dariya ba.
  "Kinaso muyi fad'a kenan, na tsani nayita nanata magana d'aya. Karki so ki ji yanda nakejin zuciyata idan kina kuka, amma ke naga kamar kin fison damuwata."
  Karo na biyu da ta ji tana son fadamishi damuwarta.
"Kayi hakuri Yaya Faruk, saidai gani nakeyi kamar an kusa yimin katanga da kai."
   Ya zubamata ido baice uffan ba, hannunsa tuni ya sauke daga saman fuskarta. Can kuma ya soma magana.
"Fata nagari lamiri, ki saka a ranki in sha Allah babu wani abu da zai yanke alak'armu har ya zuwa aurenmu da rayuwar auren. Banaso kina kawo komai a ranki. Yau idan da dama, kada ki rage bacci ki tashi mu yiwa junanmu addua akan Allah Ya za6amana abinda yafi alheri. Kin iya karanta istihara?"
  Ta girgiza kai.
"Ban iyaba, saidai ina da Hisnul muslim."
  Ya gyada kai.
"Ki yi adduar istihara a yau Ummi, in sha Allah zamu ga daidai a lamuranmu. Ga wannan."
  Ya mik'amata wata leda, ta sa hannu ta kar6a.
   "Shi nakeso ki saka gobe idan na kiraki a waya, kinji?"
Ta gyada kai.
"Yauwa."
Daga nan ya sallameta ya yi mata rakiya har suka sauka daga matattakala sannan ya tsaya ta wuce.
"Zan kiraki." Ya fada da muryar rad'a. Ta dubeshi ta murmusa ya yi mata alamun (kiss) da baki, a kunyace ta wuce da sauri. Daga haka ya koma sama.
   Bayan ya kammala dukkan wasu ayyuka, ya soma duba kyaututtukan da yan uwa da abokan arziki suka ba shi, sai a yau ya samu wannan damar. Turaruka sunfi komai yawa, agogo kuwa kusan biyar ya samu, wasu kuwa kayan kwalam ne har da katina kala-kala. Hankalinsa ya kai ga na Ihsan, yasa hannu ya dauka ya bude. Kamshi ya soma ziyartar hancinsa....!

  Wani hadadden agogo ne sai kuma zobe na azurfa. Murmushi ya yi sadda ta ci karo da kati mai dauke da kalaman so. Ya bude ya karanta.
 
 "My friends told me that falling in love would be the most beautiful feeling in the world. After I fell in love with you, I realized that even the most beautiful feeling in the world would look ugly against your love. Frm Ihsan Modibbo."

   Ya ta6e baki kadan, ya cigaba da daga sauran katinan, duk kalamai ne na nuna soyayya.
   'Ya tabbata tana sona din kenan?' Ya ayyana a ransa kafin ya lumshe ido. Baya fatan shiga matsala saboda ita, a rayuwarsa bai ta6a shaawar kasancewa da kowace mace ba face Umminsa, ta makaro, bayajin zata samu wani gurbi a zuciyarsa, saidai kuma ta dan ba shi tausayi.
Ya dan ja guntun tsaki sannan ya mik'e ya tsallake kayan ya shiga harkar gabansa.
   
Ummi kuwa tana shiga daki ta tarar Binta na zaman jira. Binta na ganinta ta mike ganin yanda jikinta ya ke duk a sanyaye.
  "Lafiya?" Ba ta ce uffan ba, sai kayan da ta ajiye saman katifa ta zauna, batasan lokacin da kuka ya kufcemata ba. Binta wacce ta sandare tana kallon waya hankalinta ya komo ga Ummi.
"Me ya faru wai? Ki gayamin don Allah mana."
   Ita dai Ummi kukanta ta ke, ji takeyi inama yau ace mahaifiyarta na raye, ta rungumeta ta rarrasheta ta kuma bata shawarar da zai taimaki rayuwarta.
  "Allah Ya ji k'an ki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki,  na taso ban ta6a jin dumin uwa ba, na taso cikin wahala da tsanani na rayuwa har zuwa sadda aka maidani 'yar aiki. Babu wani mahalukin da ya ta6a rungumeni ya ji matsalata ya rarrasheni ya min addua acikin shak'ik'aina, Babana bai ta6a tarana ya yimin fad'a akan rayuwa ba, ko sau daya bai ta6a sakarmin fuska ba, asalima kyamata yakeyi, bai ta6a tambayar Ummi ko kin ci abinci ba, Ummi zan saki makaranta, Ummi ki kula da kanki, Ummi ki tsare mutuncinki, ko sau daya babu wani cikin yan uwana da suka ta6a nunamin kulawa ko k'auna. Babu, babu su Ummana, Ummana nasan da kina raye da wasu lamuran zasuyi sauk'i agareni, ayau ga wata rana babba da nake bukatarki Ummana, saidai kinmin nisan da bazan iya kamoki ba, kin koma ga Ubangijinmu da ya fini kaunarki, babu wani da ya ta6a ban cikakken tarihinki da kyawawan dabi'unki, asalima saidai ayita aibatamin ke, ana miki kazafi. Nayi rashinki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki."
  Daga haka ta k'ara sautin kuka mai tsanani, ta cukuikuiye jikinta wuri guda, a rayuwa koda a gaba wata sila tasa Antinta Amina da yar uwansu juyamata baya, koda shima Faruk zai juyamata, bazata ta6a mance da tarin kaunar da suka nunamata ba. Sun nunamata itama DAN ADAM ce. Faruk ya gwada mata cewar itama ta cancanci komai a rayuwa, ya dauketa a mutum, haka nan danginsu gaba daya, banda matsala ta Ihsan da kishiyar Mami, babu wani abu da ta ta6a fuskanta na cin zarafi cikin zuri'arsu. Watakil a gobe zama da su zai k'are. Ta daga kai tana mai duban dakin, sheshshekar kukan da ta ji ne ya tunasar da ita cewar bafa ita daya bace a dakin. Ta kai duba ga Binta, kuka takeyi kwarai. Ta share hawayenta tana mai dukar da kanta k'as.
  "Meyafaru Binta?"
  Binta wacce zuciyarta ta cika da dumbin tausayinta ta dago kai tana dubanta.
"Shakka babu ke abar a tausayawa ce Ummi, saidai ki yi hakuri, komai na rayuwa mai wucewa ne, babu abinda ya ke dauwamamme a duniya. Wataran sai labari, Ummi akwai wadanda idan kika ji matsalarsu sai ki gane naki ba komai bane, za ki gane ke lallai kina cikin rufin asiri, ina wadanda suke kare rayuwarsu a wahala babu ko digon jin dadin rayuwa? Ummi akwai matsalolin da suka sha gabannaki, wata ma iyayenta na raye uwa da uba, amma bata ji dadinsu ba ko kusa, kuma tana gabannasu. Ina ji a jikina za ki auri Yalla6ai in sha Allahu, kuma za ki ji dadi a rayuwa. Ki cigaba da mik'a lamuranki ga Allah, in sha Allahu zai magance miki. Nima ina so ki sanyani cikin layin masu kaunarki, har abada bazan cutar dake ba, wanda mukayi a baya ma, ina neman afuwarki, ajizanci ne na DAN ADAM."
   Ranta ya dan yi sanyi da jin zantukan Binta masu dadi. Haka ta cigaba da yi mata 'yan nasihu da misalai da wandanda suka fita shiga matsala kuma cikin ikon Allah ya wuce kamar baayiba. A karshe Ummi ta labartamata yanda Faruk ya ce na ta shirya gobe zai kaita gaban iyayensa matsayin wacce zai aura.
  'Tirk'ashi!' Shine abinda Binta ta fad'i a ranta
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
 
67

Ji takeyi kamar ta gudu tsabar rud'ani. Binta na sambatu tana feshe mata jiki dq turare, hakanan mayafinta shima ta bi ta fesheshi sannan ta yafamata akanta. Takalmin ta mik'omata ta sanya, banda Masha Allah babu abinda Binta ke kira don iyakar haduwa ta hadu, kai ka rantse dinkin aunata akayi.
  "Ni ganinki nakeyi kin saje da mutan gidan, babu wani bambanci."
  Anan ne Ummi ta murmusa don gani takeyi kawai zolaya ce don Binta ba laifi akwai barkwanci. Suna nan zaune Binta ta bata baki wayarta ta dauki k'ara. Ta yi sakato tana dubanta, ganin zata katse yasa Binta mik'amata.
  "Ki d'aga mana."
Ta kar6a hannunta har rawa yakeyi ta d'auka. A kunnenta ta kara, bai bari ta ce komai ba sai cewa da ya yi.
  "Fito."
Ji ta yi cikinta ya bada wani sautin k'ululu. Tuni ya katse kiran, ta mik'awa Binta wayar sannan ta dubeta idanunta har sun ciko da kwalla.
"Don Allah ki tayani addu'a."
Tausayinta ya kama Binta, Binta ta rik'e hannunta.
"Allah Yana tare da ke, na tabbatar zai taimakeki, ki saki ranki. Komai na Allah ne."
  Ummi ta mike jikinta a sanyaye ta fita. Ido hud'u sukayi da shi yana tsaye a bakin matattakala ya sanya kafarsa daya jikin bango yana danne-dannensa a waya. Ya yi mata kyau kwarai dagaske haka kuma ya bata mamaki, sai kace wasu Amarya da Ango duk yasa su yin shigar kaya masu kyau, shi dinma wani boyel fari k'al yaa sanya da hula wacce ta dace da kayan.  Tunda idanunsa suka sauka akanta, ya kasa daukesu, daskarewa ya yi a wajen kawai don  ya yi kamar zuciyartasa ma tsayuwar ta yi. Haka har ta k'araso wajenshi ta tsaya gefe tana wasa da jelar mayafin. Yasa hannu ya dago ha6anta, idanunsu cikin juna sannan ya kauda hannunsa.
  "Kinyi kyau matuk'a."
  Ta lumshe ido gami da kauda kanta cikin bugun zuciya mai sauri. To Faruk ina wani kyau a wajenta idan aka had'asu? Gaba daya ganinta ta keyi wani tsami akansa, ta k'ara raina ajinta kwata-kwata, har ta hangowa kanta irin kyamar da za'a nunamata yau. Watakil ma su Ihsan su yi mata dariya. Idanunta ya yi kwal-kwal. Hannu ta ji yasa ya janyo mayafinta ya dan rufe kusan rabin fuskarta da shi.
  "Muje." Ya yi maganar cikin dusashshiyar murya. A hankali suka soma takawa, Faruk shi kansa dakewa yakeyi don ba shi da yak'inin samun goyon baya, yana dai ji a jikinsa kawai zai yi nasara idan Allah Ya so.
  Haka har suka shigo falon Hajiya, babu kowa, daman hakan yafi buk'ata, yasan a wannan lokacin Hajiya na sashen Daddy, kai tsaye kofar zuwa sashen Daddy ya shige. Anan kofar falon ya dakata gami da umartar Ummi da tsayawa anan. Ba musu ta tsaya, ta bishi da kallo har ya shiga da sallamarsa, kirjinta ta dafe jin irin yanda ya ke bugu fiye da baya, addu'o'i kawai ta ke karantowa.
  Daddy da Hajija suka amsa sallamar dan nasu fuska a sake.
    Ya karasa yana taku a kasaitance ya zauna a gefen kafafun Daddy ya gaishesu. Suka amsa suna k'are mishi kallo. Daddy ya kasa hak'uri ya tofa.
  "Wai ni kodai wajen surukartawa za ka tafi ne? Wannan ado haka?"
  Ya shafi k'eyarsa da murmushi saman fuskarsa, Hajiya na dariya.
  "Daddy na je na dawo, kuma tare muke da ita ma yau za ku ganta."
  Sai Hajiya ta hau salati.
"Kai Sadaukina, haka kuma akeyi babu sanarwa? Maimakon ka fad'amin a shirya?"
  "To yanzu dai ai magana ta k'are tunda daman ya sanarmana a satinnan zai kawota, kinsan halin d'annaki komai nashi daban ne."
  Cewar Daddy yana duban matarsa kafin ya maida dubansa ga Faruk.
  "Tana ina ne?"
Faruk ya dubesu, su dinma shi suke kallo fuskokinsu a sake. Hakan ya k'ara mishi wani k'arfin gwuiwa, ya mik'e tsaye ya nufi hanyar waje.
  Ya dubi Ummi wacce ya tabbata a rud'e ta ke.
  "Addu'a zakiyi, Allah na tare da mu."
Ya fada cikin muryar rad'a. Ta gyada mishi kyau kafin ya bata hanya.
"Bismillah."
  Dagowa ta yi ta dan bude fuskarta ta dubeshi kamar zata yi kuka, ya jefeta da kallo mai sanyaya jiki, dole ta maida ta rufe fuskarta sannan ta saka k'afa da sallama, shima ya biyo bayanta. Iyayen suka amsa fuskarnan a sake, suka zuba mata ido har ta k'araso ta zauna, Hajiya dai gani ta ke kamar muryar da kuma tafiyar ba yau ta soma ganin irinta ba. Ta dai danne, ta amsa gaisuwar surukarta ta wacce ke ta bad'ad'a k'amshi. Kafin su kai ga tambayar wani abu, Dakta Ridwan ya yi sallama ya zo gaida iyayensa.
  Ya dubi Ummi sannan ya dubi Faruk yana 'yar dariya.
  "Ikon Allah, ashe na zo a daidai, da rabon ayi da ni."
Sukayi dariya iyayen, shi kuwa gogan murmushi kawai ya yi.
   Dakta ya gaisar da su Daddy sannan aka zauna yana fadin shi fa sai ya ga fuskar surukarsu.
  Ikram ce ta shigo rik'e da hannun yaron Dakta, Ma'aruf, wanda ke faman rigimar zuwa wajen ubansa. Nan itama ta yi sararo tana duban Ummi.
  "K'araso mana, yau fa babbar bak'uwa mukayi, matar Sadaukin Hajiya."
  Ikram ta dubi Hajiya, Hajiya ta kauda kanta, to me za ta ce? Idan Faruk ya ce ga wacce ya ke so ya zata yi? Batun Ihsan ne sai yanda sukayi da shi.
  "Mene sunanta ne?"
Daddy ya tambaya.
"Hasiya." Cewar Faruk, Ummi ta lumshe ido jikinta na rawa, tana gudun ace za'a bud'e fuskarta.
  Ikram ta saki hannun Ma'aruf sannan ta karaso tana yar dariya na dole.
"Nidai sai naga fuskar Antina."
  Kafin Ummi ta yi wani yunk'uri, ta d'an bud'e mayafin ta lek'a. Zaro ido ta yi gami da bud'e mayafin gaba daya tana salati.
   "Me..." Kowannensu ya mak'ale tambayar da ya yi niyya sakamakon fuskar Ummi da ta bayyana agaresu. Daddy yana mata kallon sani don tabbas yana ganinta jefi-jefi a gidan, saidai baisanta a suna ba ko matsayi.
  Hajiya ta ji jikinta ya yi mata nauyi ta dubi Faruk, shi dinma ita ya ke kallo, gaba daya alamun tausayi, tsoro da kuma firgici sun bayyana saman fuskarsa. Ta maida kallonta ga Ummi wacce ta ke kuka sosai ga jikinta da ke kad'awa kamar mazari.
  "Meke faruwa ne?" Fadin Daddy yana dubansu. Hajiya ta kasa kwakkwarar magana, karshe ma ta mik'e ta nufi dakin Daddy. Ikram da ta ke duban Ummi duba na tsana ta nunata da yatsa.
  "Daddy wannan ba kowa bace face 'yar aiki, a gidan Mami ta ke a Kano shi ne ta dan zo nan, ita Yaya Faruk ke son kawomuku matsayin suruka alhalin ita din ba..." Wani kyakkyawan mari ne ta ziyarci kuncinta daga uban gayya, ta rike kuncinta wanda ba karya ta ji marin matuk'a. Ya nunata da yatsansa mai rawa, idanunsa sun kad'a ainun.
  "Koda wasa, koda wasa ki ka k'ara wannan kuskuren sai kin raina kanki! Yaushe raini ya shiga tsakanina da ke?!"
  Dakta cikin 6acin rai ya ke dubansa.
"Ba ka da hankali Faruk! Akwai wani abu a kwakwalwarka, ina kai ina wannan? Akanta har ka d'aga hannu ka mari k'anwarka?!! Haba Faruk!! Wannan zubda k'ima har ina?!!!"
   
    Faruk ransa ya yi mugun 6aci, ya girgiza kai yana duban Dakta.
  "Na yarda k'ima da komai nawa su zube, sannan don Allah ba kai na kawowa Ummi ba, da ta yi maka da bata yi maka ba, wannan ruwanka."
Tsananin mamakinsa ne ya kama su, tunda suke da shi basu ta6a ganin kalar tashin hankali har haka akan fuskarsa ba sai a yau d'in, haka koda wasa bai ta6a yiwa wani cikin yayyunsa rashin kunya ba ko dai mayar musu da magana.
Daddy kallonshi ya ke yi yana nazari, shi yasan waye Faruk, mutum ne mai tsananin hakuri, kusan duk a yaransa daga Usman(Babban Yaya) sai shi a fannin hakuri, yakan hakura da abu duk son da ya ke mishi matukar wani cikin yayyunsa ya nuna baiyi ba saboda tsantsar kauna ta jini d'aya da ke gudana tsakaninsu.
  Ya maida dubansa ga Ummi yana nazari, can kuma ya dubi Ridwan.
  "Wuce gidanka."
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
 
69Ya bud'e dakinta, saidai Binta ya gani wacce ke yawo a
tsakar dakin tana jiran dawowarta, ganin Yalla6ai da kansa
yasa ta russunawa ta gaisheshi, batare da ya amsa ba ya
jefomata tambaya.
"Ina Ummi?"
Ta girgiza kai.
"Bata shigo ba tun bayan fitarta."
Ya juya kai tsaye wajen garden ya nufa, acan kuwa ya
ganota durkushe k'asan bishiyar mangwaro tana faman kuka
sosai. A gigice ya isa gareta ya durkusa kusa da ita. Jin
motsi ne yasa ta dago kanta da sauri, ganin shine yasa ta
numfasawa.
"Kaga abinda muka janyo ko? Ni nasan wannan lamari ba mai
yiwuwa bane."
Baisan sadda ya rik'o hannunta ba.
"Wa ya gayamaki bazai yiwu ba? Kada ki damu da abinda ya
faru domin na zo miki da kyakkyawan albishir, iyayena sun
amince da aurenmu."
Ta yi sakato tana kallonsa, babu alamun wasa ya ke yi,
ganin ta yi shiru ya girgiza hannunta.
"Ba mafarki ki ke ba fa Ummi, dagaske sun amince da
zancen aurenmu. Godiya ya kamata muyi ga Ubangiji."
Ta lumshe ido, ta rasa irin yanayin da ta ke ji a jikinta, ji ta
yi yana kokarin mik'ar da ita, a kunyace ta zare hannunta
daga nasa ta mik'e, jerawa sukayi suka soma tafiya tamkar
basu so, kallo daya idan kayi musu, zaka so kayita kallonsu
tsabar dacewa da sukayi da juna. Ya dubeta.
"Ummina shiru fa, kiyi magana please."
Ta share ruwan hawayen da suka k'i tsayuwa.
"Yaya Faruk."
Ya tsaya a gefen kujera mai lilo ya zauna, sannan ya yi mata
nuni da gefensa.
"Zauna nan."
Ba musu ta zauna jikinta a sanyaye. Ya juyo yana
fuskantarta yana ji tamkar ya had'iyeta don so da tsantsar
kauna.
"Ina sauraronki." Ya fada cikin kankan da murya tamkar
wanda baya son magana.
"Kamar fa 'yan uwanka ba..."
"Shiii.." Yasa yatsa a saman le66anta, ta kauda kai tana mai
takaicin yanda bayason ta kawomishi zancen abinda ya
kasance gaskiya kuma shima ya sani.
"Ya dace ka bani dama ka ji abinda zan fada Yaya Faruk,
akwai babbar matsala da kai ka ke mata kallon sassauk'a.
Yaya Faruk kana da labarin Ihsan na sonka?"
Ta karashe tana kallonsa, shima ita ya ke kallo, kenan dai
shi 6oyon ma da ya ke mata ta sani? Abu daya ne bazai iya
sanarmata ba, batun auren da Hajiya ta ce zaiyi da Ihsan don
bai dauki hakan mai yiwuwa ba, kuma ba wai don Hajiyartasa
bata isa ba, aa, sai don kokusa ba shi da tsarin had'a mata
biyu a gidansa. Saidai abinda ya ba shi mamaki, bai wuce ta
yacce akayi tasan da cewa Ihsan na kaunarsa ba.
Ya kauda fuskarsa yana mai dan hade gira.
"Ya akayi kika sani?"
Ta yi murmushi mai ciwo itama ta maida dubanta ga wata
shuka a wajen.
"Shi so ba'a 6oyonsa, itama nata ya fito fili, k'alilan ne
basu san tana sonka ba a gidan..."
"Kinga ya isa haka please, ya isa. Ke bakya kishina ne?
Bakya jin wani abu a ranki idan kina had'ani da wata bayan
ke? Bazan iya rayuwa da kowace mace ba bayan ke. Ummi
wai kinsan waye Umar Faruk kuwa?"
Ya k'arashe yana mai tsuramata ido da wani murmushi.
Daman ba kallonshi ta ke yi ba, wasa kawai ta ke yi da
yatsunta. Ya girgiza kai.
"Shikenan dai. Ban labari game da farin cikin da zaki yi
ranar da aka shafa fatiha?"
Maganar ma sai ta bata dariya, ta rufe fuskarta tana
murmusawa.
Karaf akan idanun Ihsan wacce ta fito don bawa wani mai
wankin gidan ya siyo mata kati don kiran Maminta, ta jima
tsaye tana kallonsu basu sani ba, hawaye kawai ke zuba daga
idanunta. Ta k'arewa Ummi kallo, ta yi wani kyau a suturar
dake jikinta, sannan ta dubi Faruk wanda ya bawa inda ta ke
baya, ya wani duk'ar da kai a gaban Ummi yana lek'en
fuskarta kamar mai shirin kai mata sumba. Nan duniya ta ji
ta k'ara tsanar Ummi, ta k'ara tsanar Faruk da wai suke
takara a sonsa da ita. Ina ita ina had'a masoyi da wacce
tasan ta fi? Faruk ya cuceta, inama bai soma son Ummi ba
ita ya so? Katin da bata bada an siyomata kenan ba, da gudu
ta koam ciki tana rusa kuka, a kicin ta yada zango ta yi mai
isarta sannan ta fito ta fada bandakin dake falon ta wanke
fuskarta ta koma sama zuciyarta na wani irin zafi.
Daddy ya cigaba da yiwa Hajiya nasiha mai ratsa jiki gami
da nunamata shi fa lamari na aure ba'a dole, ya amince da
bukatarta na aurawa Faruk duk su biyun saidai su dage da
mik'a lamarin ga Allah kafin komai, a karshe ya ce su bar
maganar nan zuwa kwanaki uku. Hajiya ta aminta da hakan,
ta kuma sanarmishi cewar a gobe Ummi zata koma Kano.
"Badai don maganarnan ba?"
Ta girgiza kai tana dan murmushi duk don ta kwantarwa da
mijinya hankali.
"Ko kusa, saidai Madina ta buk'aci hakan tun ba yau ba,
daman ina shirin sanarmaka sai wannan al'amari ya 6ullo."
Ya jinjina kai alamun gamsuwa.
"Shikenan ai, Allah Ya nunamana. Shima Ridwan zan ganshi
gobe, banason abinda zai kawo rikici tsakaninsu."
"Hakane." Hajiya ta amsa kafin ta mike don kawomishi
ruwan lipton wanda ya saba sha duk dare.
*** *** ***
RINGIM
Abu kamar wasa, k'aramar magana ta zama babba, don kuwa
tuni Deen ya damk'awa Dija mak'udan kudi ta had'o
lefenta. Tare da Saude da Baba Habiba suka shigo kasuwar
Kano, nan suka shek'o kayayyaki masu dan karen kyau da
tsada don har saida Deen ya k'aramusu kud'i. Yan uwa
daidaiku ne kawai suka halarci ganin lefen don kuwa
acewarsu abin kunya ne da abin tirr irin wannan cin amana da
suka yi ga Munira. Kuma tabbas Allah bazai barsu ba, to ance
wanda ya yi nisa ba ya jin kira, ko a jikinsu wai an tsikari
kakkausa, Malam Yahuza abin na damunsa a kasan zuciya
saidai babu abinda zai iya cewa, haka zai zauna tare da
Balarabe mahaifi ga Ummi ya yi ta gayamishi bayason
auren, shima kasancewar ba wani kata6us ne da shi a gidansa
ba, saidai ya ce "To ya zaayi banda hakuri da addua? Matar
mutum babu makawa sai ya aureta indai Allah Ya kaddaro
tasa din ce." Haka suna gani matansu suka shiga shirye-
shirye, an kai Dija wajen bokanya yafi sau biyar ana mata
tsafe-tsafe don ta mallaki zuciyar Deen. Aikam sai
haukacewa ya ke k'ara yi akanta, Munira dai yanzu abin ma
ya ca6emata don hatta Yaransu ba shiga harkarsu ya ke ba,
idan ka gansu kasan suna cikin tashin hankali marar
misaltuwa.
    Har ana washegari Asabar daurin aure, Deen bai samu
wata fuska daga yan uwansa ba, Munira kuwa a ranar ta
juma'a ta iso Ringim din suna k'ara jajanta lamarin da yan
uwanta, iyayenta kuwa nasiha kawai sukai ta binta da shi
akan ta yi hakuri ta rungumi kaddara.
DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR
 
68
Dakta daman a fusacen yake, hannun dansa ya rik'e ya bar
falon bayan ya jefi Ummi da mugun kallo wanda batasan ma
yana yi ba don kanta a sunkuye ya ke tana faman kuka da
sheshshek'a. Itama Ikram mara mishi baya ta yi a guje tana
kukan marin da ta sha.
Daddy ya dubi Ummi.
"Tashi ki je Hasiya."
Ummi ta mik'e tana had'a hanya ta fita, tasan daman
lamarin ba mai yiwuwa ba ne sam, tun yanzu ta soma
fuskantar tashin hankali ina kuma ga idan ta koma Kano?
Daddy ya zauna sannan ya dubi Faruk wanda ke tsaye yana
duban hanyar da Ummi ta bi cike da matsanacin 6acin rai,
har lokacin bai daina jin dacin maganganun yan uwansa ba ga
matar da yafi so duk duniya.
"Zo ka zauna."
Cewar Daddy cikin kwantar da murya yana mai mishi nuni da
gefensa. A hankali ya taka ya zauna a k'asa rai a jagule.
Shiru na yan mintuna ya biyo baya kafin Daddy ya soma
magana....Ihsan tsaye a falon Hajiya Babba ta yi tana jin yanda 'yar
hatsaniya ke tashi a sashen Daddy, ji takeyi kamar ta je ta
ga abinda ke faruwa. Tana nan tsaye Dakta ya fito a fusace,
ko lura da ita baiyi ba haka ya fice, bata kai ga cewa komai
ba Ikram ma ta sanyo kai, hawaye sha6e-sha6e saman
fuskarta, a guje ta yi saman Hajiya, baki sake ta dubi
saman, tana shirin maramata baya Ummi ta fito itama cikin
shigar da ta mugun kad'a hanjin cikin Ihsan, gabanta ya hau
duka da sauri-sauri. Suka dubi juna ido cikin ido kafin kuma
a sanyaye Ummi ta soma tafiya, har ta bar wajen bata iya ce
mata uffan ba, ta dafe kirji wanda ta ke ji kamar zai fad'o.
"Me Ummi kuma ta ke yi a sashen Daddy, da kuma shiga
irin haka?"
Ganin babu mai amsamata ne yasa a karshe ta yanke
shawarar bin bayan 'yar uwata tasan ko menene zata ji.
Daddy ya dubi Faruk cikin kwantar da murya ya soma
magana.
"Tun tashinka ban ta6a kamaka da laifi na k'arya ko
yaudara da makamancinsa ba Faruk, hakazalika ka kasance
mutum wanda bai 6oye abinda zuciyarsa ke so."
Daddy ya danyi shiru sannan ya cigaba da magana.
"Ni ba k'aramin mutum bane, ba alfahari ba, Allah Ya
azurtani da yara masu d'abi'u kyawawa hakazalika masu
iyakar kokari wajen kiyaye dukkan wasu dokoki na
Ubangijinsu, wannan karon sai aka samu akasi, zuciyata ta
kasa nutsuwa da za6inka na matar aure, ina ganin kamar da
wata manufa ta daban ka ke son auren wannan baiwar Allah
da idan a batu na dukiya ne da jin dadin rayuwa, to kai din
kana sama da ita, ina so ka gayamin tsakani da Allah, wane
irin so ka ke ji ga yarinyar nan? Bazan lamunci tozarta DAN
ADAM ba, don kowanne akwai darajarsa ta musamman, bazan
lamunci ka aureta daga baya azo a samu matsala ba. Ka
fadamin gaskiyar abinda ka ke ji game da ita."
Faruk ji ya yi kamar ya d'aga Daddy ya cillashi sama yana
ca6e don dad'i. Ya dan saki fuska.
"Tsakani da Allah nake sonta Daddy, asalima kaunarta ta
samo asali ne daga tausayinta da nake ji, wallahi ba ni da
haramtacciyar nufi akanta."
Daddy ya yi murmushi gami da dafa kan Faruk.
"Tun da kake a rayuwa, ka ta6a zuwar min da wata buk'ata
na k'i?"
Hakoransa a bayyane yana murmushi ya girgiza kai.
"Aa Daddy."
"To wannan ma bazan k'i ba, matuk'ar na yi bincike akan
yarinyar na samu kyakkyawan magana, baka da matsala. Ni
mai aura maka Hasiya ne."
"Da SHARADI.!"
Suka tsinci muryar Hajiya daga bayansu, Faruk a rud'e ya
ke dubanta, ta karaso idanunta na zubda ruwan hawaye ta
zauna saman kujera.
"Ki ka ce me?" Daddy ya fada da mamaki yana kallonta.
Ihsan ta iske Ikram a daki tana kuka da sheshshek'a, wai yau
Yayansu Faruk mai hakuri shine ya mareta akan wata banza
yar aiki Ummi? Wannan abu da cin rai ya ke.
"Ke wai meke faruwa? Tashi ko sanardani don Allah, ni
gaba daya na shiga rud'ani wallahi, naga Ummi da wani shiga
mai ban mamaki."
Ikram ta mik'e zaune tana dubanta cikin dacin rai.
"Za ki ganta da fin wannan ma wallahi muddin ba ki bud'e
baki kin fayyacewa iyayenmu yanda ki ke ji game da Yaya
Faruk ba, a yau Yaya Faruk ya kawo Ummi gaban su Daddy
matsayin wacce ya ke so da aure. Har akanta ya mareni."
Ihsan daskarewa ta yi tana duban Ikram, ji take kamar jinin
jikinta baya gudana yanda ya dace, kamar wata sokuwa ta
bude baki ta na kallonta. Ikram ta fayyacemata duk yanda
akayi tun daga farko har zuwa marin da akayimata da rikicin
Dakta da Faruk.
Hawaye ne kawai ke kwararowa daga saman fuskar Ihsan ta
kasa kata6us. Abin ne ta ke masa kallon mafarki. Ummi dai
'yar aiki, Ummin da ta ke ganin ta fita a komai na rayuwa,
ta fita kudi da ilimi kai harma da yawan dangi kuma
wadatattu da sauransu. Faruk matashi abin so da shaawa ga
duk wata mace mai lafiya, matashi irinsa da ko 'yar
shugaban k'asa ko wani basaraken, bata isa ta yi mishi kallo
daya ta kauda kai batare da ta yabawa tsarin halittarsa ba,
mata nawa ne ke son dace da samunsa? Su nawa ke rububi da
fatan inama ace suna da damar da zaisa ya kasance a
matsayin mijin aurensu?
Ta girgiza kai tana sheshshek'a tana mai cigaba da sak'e-
sak'en zuci.
Abin kaico, ya buge a auren 'yar aikin gidansu, wacce zai
iya samun dubu da suka fita komai ya aura. Abin kunya ne
da takaici ace wai suna takara akan namiji daya tilo ita
da'yar aikin gidansu, wannan kam raini ne da kaskanci
agareta, wannan zubewar k'ima da ajinta ne a idanun
kawayenta da duk wanda yasan irin mutuwar son da ta ke
yiwa Faruk. Ikram kasa zaman dakin ta yi ta fito falo don ta
ji da nata zuciyar dake mata wani irin daci, ga kuma tausayin
Ihsan din da ta ke ji. Wasu lokutan so baima san kan wanda ya
dace ya fad'a ba, ba don zargi babu kyau ba da sai ta ce
anya kuwa ba wani siddabarun Ummi ta yi ga yayannata ba?
Idan ba haka ba, ina shi ina wata Ummi? Ko diri da kyawun
fuskarta ne ya d'ebeshi? Ta jefawa zuciyarta tambayar, sai
kuma ta girgiza kai. Kayya da kamar wuya, idan don hakan
ne kadai akwai wadanda suka ketare Ummin masu kaunarsa
amman bai za6esu ba.
Hajiya ta share hawayenta don daga daki ta ji dukka abinda
ke gudana, hankalinta ya tashi jin wai yau yaranta sun samu
sa6ani akan zancen auren Faruk. Ga kuma a gefe da ta ke
tsoron abinda zai rushen k'akk'arfan zumuncinsu da
kanwarta Madina. Ba zata ta6a amincewa hakan ya afku ba,
don Ummi kuwa, kwarai yarinya ce mai hankali, ta cancanci
zama matar d'anta don a halayya bata ta6a kamata da wani
dabi'a mai muni ba, hakanan bata ta6a cin amanarta ba,
daidai da Madina ta sha yaba hankalin yarinyar.   Ta dubi
mijinta kafin ta maida dubanta ga Faruk wanda ya sunkuyar
da kansa cike da jin wani mugun tashin hankali. Yana
fargabar abinda zai fito daga bakin Mahaifiyartasa. Baya
fatan ace itama bata goyi baya ba, to amma a maganarta, ta
nuna goyon bayanta saidai ta ce da sharad'i.
"Kwarai kuwa Abban Ridwan, akwai sharad'i. Na amince ya
auri Ummi, amma ina so itama Ihsan ya aureta!"
Gaban Faruk ya bada sauti mai k'arfi, ya juyo a razane
yana duban Hajiya, fuskarta a daure wanda hakan ya nuna
babu alamun wasa a zancenta.
"Ita Ihsan din ce ta ce tana sona?"
"Na tabbatar kasan tana sonka Sadauki."
Daddy ya yi shiru. Faruk ya girgiza kai a gigice.
"Ni bana son..."
"Kaga, tashi ka tafi zan nemeka."
Cewar Daddy, Faruk ya mik'e ransa babu dadi ya fita, bai
ta6a sha'awar zama da mata biyu ba, ta ya ya Hajiya za ta
k'ak'aba mishi Ihsan alhalin tasan bai ta6a sonta ba?
Asalima bai ta6a soyayya da wata diya mace ba sai Ummi.
Hankalinsa ya koma ga Ummi, a wane ta ke ciki ne? Kai
tsaye ya nufi wajenta don bincikawa.
  DAN ADAM
@RUFAIDA OMAR

71

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "DAN ADAM part 3"

Post a comment