+2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria

Download and read free hausa novels

ALLAH GATAN BAWA complet

ALLAH GATAN BAWA

Complete 
Mallakar Zahra Muhammad Surbajo

DOMIN DOWNLOAD NA LITTAFIN ZUWA KAN WAYOYINKU SAI KU DANNA RUBUTUN KASANNAN👇👇👇👇👇

[post_ads]
[post_ads]

Kadan daga cikin Littafina
Azaune take akan dakalin kofar gidansu hannunta dauke da kara tana wasa dashi
yayin dasauran yaran makwabtansu suma suke nasu wasan ita kuma tana binsu da
ido domin ita Bata da yencin shiga cikinsu tayi wasan yarinyace yar kimanin
shekara takwas da haihuwa wacce Allah yajabceta da lalura irinta zubar da miyau
sanna kafarta daya dahannunta daya duk ashanye suke intana tafiya tana jefa
kafarne yayin da hannun yake makale a kirjinta
wannan lalurarce tasa yara da sauran mutanen garin kyamatarta ko wasa basayi da
ita sede tazauna agefe tana kallonsu

*Asalin labarinta*

Ilham bukar shetima shine sunanta na aynihi mahaifinta malam bukar shetima
hafaffen garin medugurine acikin garin bama inda fadace fadacen daakeyi
ayankinsu yayi sanadiyyar mutuwar iyayensa hakanne yasa yayanke shawara shiga
cikin ayarin yan gudun hijira domin yin hijira daga yankinnasu. Bashi kadai bane


agurin iyayannasa su biyu ne shida dan uwansa mesuna imamu amma rudin
dagarin ke ciki yasa suka bacema juna yayi kukan bakin cikin mutuwar iyayensa
da kuma bacewar yayansa Wanda besan awanne hali yakeba shiyasa yarungumi
kaddara yayi hijira
Acikin ayarin yan gudun hijirarne yahadu da wata budurwa wacce itama ankashe
iyayenta( Bata da kowa )me suna maryam tunda suka hadu yake tausayamata
sabida ita macece shiyasa yashiga dawainiya da ita har suka shigo garin kano
bayan ansaukesu asansanin yangudun hijirane washe gari yakirata gefe inda
yashawarceta dasuyi aurene zefi kulawa da ita sabani basu da aure Batare da Bata
lokaciba ta amince inda dattawan cikin yan gudun hijirar sukadaura musu aure
bayan yabata sadaki nera dubu biyar
tundaga lokacin yadukufa gurin kwadago acikin gari har Allah yataimakeshi
yakama masu hayar gida me daki biyu acan garin wudil sabida beda halin
kamamasu acikin gari be kaunar zamansu acikin sansanin "yan gudun hijirarne
shiyasa yakamamasu haya bayan tarewarsu badadewa Allah ya albarkacesu
dasamun karuwa ta cikin suncigaba da kulawa da cikin har zuwa haihuwa inda
Allah yasa maryam tahaihu lafiya tasamu "ya mace yarinyar kyakkyawace ajin
farko sabida daga uwa har uban shuwa arabne sede kallo daya zaka mata kafahimci
Bata da lafiya maana nakasasshiyace basuyi kasa agwuiwaba suka samata suna
inda taci sunanta ilham bayan suna ilham iyayenta sundukufa neman magani amma
duk inda sukaje amsa daya akebasu bazata warkeba tunda da lalurar aka haifeta
hakan yasa suka hakura suka mikama Allah lamarinsu
ilham na dada girma lalurarta nakara bayyana ahaka har aka yayeta bayan yayetane
Allah yasake basu wata 'karuwar inda wannan haihuwarma tasamu mace suka
samata sunan mahaifiyar bukar fateema suna kiranta ameera bayan haihuwar
ameera basu sake haihuwaba har zuwa yanzu da ilham kede shekara takwas ameera
kuma biyar
rayuwa suke mecike da tsanani sabida malam bukar me karamin karfine wani
lokacin ko yafita bayasamun dakon haka yake dawowa ahaka yakokarta yasa su
ilham awata makarantar gwammanti ta pramary ilham na aji uku ameera aji biyu
duk à tunaninsu ilham bazata iya komai amakarantaba amma Allahyataimaka yasa
tana ganewa sede ko tambayarta akayi bazata iya fadaba sede gwaranci dan


harshenta akarye yake. ko amakaranta tsokanarta suke yara sede ameera tatunda
taremata dukda itama bawani wayo garetaba ita ilham kuwa sede taita dariya
miyau nazuba tadauka wasa suke mata, to ko sundawo gidama yaran unguwa
bakyaleta sukeba shiyasa mahaifiyarsu batason ilham nafitowa sabida ko ina
hantararta akeyi tun mamansu na magana har tadena sabida tasan *Allah gatan
bawane*

*Cigaban labari*

tanana zaune yaran suka fara tsokanarta itako se dariya take harda kwantawa miyau
nazubowa daga bakinta, jiyo hayaniya da mahaifiyarta tayine akofar gida yasa tayi
saurin lekawa daki inda tabarsu suna wasa da ameera ga mamakinta ba ilham sede
ameera datakeyin homeworke dinta dasauri tadauki hijab dinta tasa tayi kofar gida
sabida ta tambatar da ilham akeyi ayko ilai tana fita tayi tozali da ita tana dariya
yara natsokanarta suna watsamata kasa bakinciki besa tayi yunkurin hanasuba illa
iyaka dauko ilham datayi tashiga gida daita itako baabinda yadameta se dariya
take .

DOMIN CIGABA DA KARANTAWA SAI KU DANNA KASANNAN DON DOWNLOAD NA LITTAFIN👇👇👇👇👇
[post_ads]
[post_ads]

ga duk wayanda suke samun matsala ta wurin downloading ebooks namu kuma suke da bukatar mu rubuta masu copy din littafin mu turo masu ta whatssap ko profile nasu
SAI KU TUNTUBI mamallakin shafin Shuraih Usman
Ta facebook profile nashi
Kota nambar waya 08140419490
Kota adireshin Email
shuraihusman@gmail.com
Sai de ku sani wa hakan zamu cajeku wasu kananan kudade
its Shuraih Usman 99%

BAKANDAMIYAR GUMURZU kashi na shida 6

BAKANDAMIYAR GUMURZU 

Kashi na shida 6
Na Umar Abdulhadi Mati
Karshe

DOMIN DOWNLOAD NA LITTAFIN ZUWA KAN WAYOYINKU SAI KU DANNA RUBUTUN KASANNAN 👇👇👇👇👇
[post_ads]
[post_ads]

Kai!! dakata sarki nawwar ya dakawa boka nazara tsawa cikin murya mai cike da fushi, kafiya, haɗe taurin zuciya ya fara magana "shin ka manta da ko wanene sarki nawwar kada fa ka manta nine ƙi gudu mai sanya maza gudu, bazan karya tarihin jarumtakar ahlinmu ba in gudu in bar ƙasata da alummata ba.
Yayinda su sarki nawwar ke wanan tattaunawa shikuwa aljani fargam juyawa yayi ya dakawa sauran mayaƙansa tsawa yana mai cewa" me kuje jira da sauran waɗanan "yan tsakin ku karasa su mana", nan take aljana zarma ruwan bala'i, sadauki saljam, sadauki salka, aljana zabariyya, dodo zalƙim, da sauran sadaukan da sukayi saura na daga jinsin aljannu ,dodanni, mutane sukayi kururuwa haɗe da afakawa rundunar sarki nawwar nan take masifaffen yaƙi ya ƙara kaure a tsakanin mai taken a mutu ko ayi rai domin kowani ɓangare yaƙi yake da zuciya ɗaya da niyyar akashe shi ko ya kashe nan take kura ta tashi tayi sama wutar yaƙi ta fara ruruwa tana toroƙo.
Saidai wanan karon lissafin ya canza domin mummunar ɓarna akeyiwa rundunar sarki nawwa domin wanan karo aljana zarma wasu baƙaƙen takubbane take yaƙi dasu wanda lokaci ɗaya take kai sara hagu da damarta duk sara idan takai takan sare kan mutum ukku ko biyu, itakuwa aljana zabariyya wani baƙin mashine a hannunta wanda da takai suka ko duka saidai kaga mazaje na zuba kamar gobara a gonar auduga, ɓangaren sadauki saljam ma babu kyau duk da cewa ƙafarsa guda akwai ɗori na karaya hakan baisa ya gaza ba domin duk sadaukin da ya raɓeshi sunansa gawa , haka sadauki salka shikuwa babu makami a hannunsa saidai duk sadaukin da ya tunkaro sa na take zai watso masa koriyar wuta ta ƙoneshi ƙurmus, ɓangaren su dodo zalƙim da kalkus kuwa abin yafi na ko ina muni domin kowannesu da yakai jimƙa ko raruma saidai kaga ya damƙo mazaje ukku ko huɗu ya ruɓurɓushesu ya watsar da karyayyun sassan jikinsu kokuwa kaga yadda kasan takar da sun kama mutum yana ihu haka zasu yagashi biyu.
Haƙiƙa kisan da ake yiwa dakarun sarki nawwar abin ya munana, saidai suma fa suna yiwa rundunar aljani fargam ɓarna musamman ma sarkin yaƙi farha wanda ya haukace idanunsa sun rufe ragar gazar maƙiya kawai yake ba aljani, ba dodo ko mutum duk wanda ya shigo gabanshi sunansa gawa domin lokaci ɗaya yake kai sara da duka da ƙafa da mangara da hannu, itama ɓangaren basadauki haka abin yake, sai kuma dakarunan guda shidda masu sanye da jajayen kaya wanda suke tsaron lafiyar sarki nawwar wanda tuni sun jima da saukowa ƙasa..... Ebook created by Shuraih Usman 99%

DOMIN CIGABA DA KARANTAWA SAI KU DANNA RUBUTUN KASANNAN 👇👇👇👇👇
[post_ads]
[post_ads]

ga duk wayanda suke samun matsala ta wurin downloading ebooks namu kuma suke da bukatar mu rubuta masu copy din littafin mu turo masu ta whatssap ko profile nasu
SAI KU TUNTUBI mamallakin shafin Shuraih Usman
Ta facebook profile nashi
Kota nambar waya 08140419490
Kota adireshin Email
shuraihusman@gmail.com
Sai de ku sani wa hakan zamu cajeku wasu kananan kudade
its Shuraih Usman 99%
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter