+2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria

Download and read free hausa novels

GOYON KAKA complete PDF


DANDANO

Yarinya ce da baxata haura shekara takwas ba ta sheko da gudu cikin gdan nasu ko sallama babu,direct bandaki ta nufa abin data debo acikin rigarta ta xubesu a bakin ban dakin mangaro nagani da alama tsinkosu tayi ba wani excuse ta tura kofar bandakin saboda matsanancin fitsatin daya korota,

suman tsaye tayi sakamakon wanda ta gani a bandakin saboda tsabar tsoro a wando ta sako fitsarin,a 360 ta juya kotakan mangwaron batabi ba dakin kakarta ta shige gurin buya ta shiga nema can Allah y bata sa'a ta fada karkashin gado a lokacin kakar kuwa tana baccinta batasan mai yake faruwa ba.

Wanda ta bude a bandaki kuwa ransa duk y baci saboda bakin cikin yarinyar ta ganshi ba kaya a dalilin wankan da yake a gaggauce y karasa wankan y futo ransa duk a jagule matashine da baxai wuce 22 years ba ko daki bai shiga ba y wuce dakin kakar,masifa yakeyi tun daga tsakar gda yake kwalawa kakar kira danyasan xata iya boyeta kaka!kaka!!kaka!!!wlh yau saina kusa balla yarinyar nan kowa ma y huta ayi yarinya sai hatsabibanci,dannaga iskancinnaki gaba yakeyi tinda harkin kai ki leka mutum a bandaki yana wanka lokacin y karasa shiga dan duk babatun da yake a tsakar gidane kaka kuwa bata jishi ba saboda tana wata sabuwar duniyar cikin bacci.


Kaka!kaka!!kaka!!! ya kwala mata kira da karfi a firgice ta farka a baccin tana haba mai gdan wannan tashin hankalin kira kamar an kawo farmaki,tsaki yayi mtsss yace ni ina shegiyar jikarnan taki mai siffar aljanu,bata fuska tayi tace wlh Aslam ka kiyayeni,ubanme tayi maka xaka fara xaginta yarinyar ma da bata gidannan,tsaki yadanyi yace yace ai baxaki gane ba,tace eh mai xan gane,yace yarinya bakyason laifinta nidai kawai ki futomin da ita danyau saina babballata,islam cikinta ne yace kuwwwww tana xaxxaro ido tana addu'ar yasa karya ganta,dan tasan laifin datayi masa inya kamata xai iya kasheta,dan wlh yaya Aslam mugu ne,kaka ce ta juya tayi kwanciyarta tana kayi ka gama nidai a gidannan ko mai kama da islam ban ganiba tun rana data futa.


Juyawa yayi yace wlh nafasa yin satin yau xan koma dan aljanar jikarnan taki xata iya sakamin hawan jini,kaka tace kafi ruwa gudu umma tagaida aysha kuma karka kara kiran islam da aljana in baxata kirata da sunanta ba ka bashshi ba dole bane,islam sai data tabbatar da yaya aslam y futa sannan ta fara kokarin futowa.

Kokarin futowa takeyi daga maboyar tata kakace tajiyo mutsu-mutsu a karkashin gado tace au Ashe shegen berannan bai mutu ba aikuwa yau xan saka maka maga..bata karasa magana ba taga islam ta fito tana xaxxaro ido ,kaka ta kama baki tace lah ga ja'irar kaya yaushe kika shigo,xumbura baki islam tayi tace daxu nashigo.


Kaka tace to menene y hadaki da wancan mai bakar xuciyar yadda y xuciya daya kamaki dako makota baxasu iya kwatarki ba,karamin bakinta ta cuno gaba tace to ai daga gonar malam tanimu muke shine fa fitsari y matsoni tofa bansan fa yana bandakin yana wanka ba shine nashiga duk cikin dangarta take maganar,kaka ce ta tuntsire da dariya tace kaji yar nema daman nasan laifi kikayi masa,islam itama dariyar take tace Allah bada gangan nayi ba,kaka tace toh naji,islam tace yanxu ina yaya aslam din saboda futa xanyi xamu tafi rafi yau ana kamun kifi,

kaka ta karkatar da baki tace kinsan bakar xuciyarsa yace gda xai tafi,islam tace gwandama dama duk y takuramin y koramin abokanaina y hanasu shigowa gidannan sannan y hanani futa wasan dare,tashi tayi tace kaka saina dawo,kaka tace to amma baxaki hutaba naga yanxu kika dawo,tace au bari nadauko mangwaro na ki boyemin dan sai da mukayi dambe da hanne na kwato mangwaron nataho nasan intaxo tagan shi xata dauka,ta futa ta dauko ta kawowa kaka ta dauki daya tana wlh kuma kaka karki shamin kinjiko,kaka tace xancen banxa mai xanyi da kayan tsami xoki dauki abinki,dariya islam tayi tace Allah y baki hakuri kakata ta kaina ta fuce,a kofar shigowa dakin kaka sukayi kicibis da yaya aslam rangwashi y sakar mata a tsakiyar ka,

wani gigitacciyar kara ta saki sanadiyyar wani masifaffen xafi da taji y ratsata,a kuje ta fuce waje taci gaba da ihu,da gudu kaka ta taho har tana tuntube xani na faduwa tana daukaᗒ da aslam suka hadu xai shigo dakin hade girar sama da kasa kaka tayi tace me kayi mata,murmushi yayi yace haba ta wajena me kuwa xanyi mata tsorata dai tayi data ganni shine fa ta fice da gudu taxata xan daketa,dariya kaka tayi tace yauwa aina xata dukanta kayi narama mata,xaro ido yayi yace yanxu saiki dakeni tace ras ma kuwa,sallama sukaji anayi kaka ta xari mayafi aslam y mara mata baya malam tanimu suka gani y kawo karar islam da kawayenta da abokananta irin barnar da sukayi masa acikin gona,kaka tace karka yiwa jikata sharri yaushe taje gonarka,kana da wannan shegen saka idon da bakar rowa ta yaya har xasu dauki mangwaronka ka bassu,

yace ai katanga suka haura,kaka tace ni islam bataxo da mangwaro ba Aslam ne y dinga bawa malam tanimu hakuri dan yace mai gari xaije y fadawa,tsaki kaka tayi tace kaje birni ka fadawa sarki ba mai gariba,dakyar Aslam y shawo kan malam tanimu dan sai da y bashi 2k y hakura dan tanimu akwau san abin duniya lol,bayan sun shigo gida dan karamin tsaki
 
Aslam yayi yace wlh ke kika dada bata yarinyar nan in ba haka ba yaushe har tasan ta haura katangar mutum ta sato masa mangwaro dududu nawa take,kaka tace karyane fa sharri yakeyi mata,Aslam y nuna mangwaro akan gadon ta yace wancan fa,kaka tahau borin kunya tace to ayi mutum sai bakar rowar jaraba y shuka mangwaro mai warin gawasa kanshi y ishi yara y hanasu mai xai hanasu tsinkowa,Aslam yace wlh da inada iko da mayar da ita gurin aunty amarya xanyi tunda ba tarbiyya kikeyi mata ba,

harararsa kaka tayi tace to ko ubanka nina raineshi kuma nabashi tarbiyya,xaro ido yayi y kama baki yace Allah y baki hakuri,kaka tace naji,yace ai yayana wlh baxan kaisu riko ba balle kuma


*GOYON* *KAKA* xaki tayi tace wanema xai rikema yaya,yace eh naji kinsa ina bata lokaci sallama naxo miyi xan tafi,kaka tace haba Aslam au da gaske kake baxaka cika satin ba,yace gwanda natafi tunkan kikai ga duka tunda kin fara xagi tace nayi dukan ma indai kan islam ne sainayi maka,y futa yana kinjiko tace ga daddawa nasiya musu ka tafi da ita yace baxan dauki kayan wari ba yaja trolly bag dinsa yai gaba.


DOWNLOAD EBOOK
GOYON KAKA Complete
Name GOYON KAKA
Size 124kb
Author Umma Yahaya
File Type pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 14 September, 2020
descriptionhausa FICTION
BIRNIN AZZALUMAI 6 complete PDF


BIRNIN AZZALUMAI 

Kashi na shida 6
Complete ebook PDF

[post_ads]

Wannan shafi tamu mai Albarka kwanakin baya ta fara kawo maku wannan littafi tun daga kan na dayansa har zuwa na biyar to da yardan Allah ayau mun kawo maku na karshe Wanda shine karshen LITTAFIN Baki daya

Littafin BIRNIN AZZALUMAI na Abdulaziz sani m gini

Kadan daga

A sannan alkalin gasar ya shigo ya tsaya a tsakiyarsu ya
dadda tuna musu yanayin gasar da kuma dokokinsa..
Daga cikin dokar gasar shi ne in dai mutum ya fadi kasa
da bayansa babu damar a sake kai masa wani hari ko a
cutar dashi sannan kuma a cikin jaruman hudu duk irib
yanayin daza su shiga wani bazai taimaki wani ba kuma
duk wanda ya mutu a wannan gasa babu batun daukarr
fansa sbda dama gasa ce mai hadari ta sai da rai.
Alkalin yana gama yin wannan jawabin sai ya fice daga
cikin filin ya koma cikin yan kallo yana zauna daf da
jarumi zaunal.
Faruwar hakan ke wuya aka buga gangar fara gasa.
Nan take sai jaruman hudu suka ja baya kuma kowannen
su ya murtuke fuskasa alamar cewa ba sani ba sabo
kuma ba ragayya..
Kamar hadin baki sai dukkaninsu suka zare makamansu..
Husam da lasmir suna rike da takubbansu da
garkuwoyinsu, sarki zarmus da gimbiya zarisha kuwa
suna rike da takubba guda bibiyu.
Bayan jaruman hudu sun ja baya ga juna sai suka fara
kallon kalo kowannen su na nazarin abokin gwaminsa har
izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai suka rugo da
gudu izuwa kan juna.
Zarisha ta afkawa lasmir shi kuma sarki zarmus ya
afakawa Husam aka ruguntsume da azabbben fada ya
zamana cewa suna kai wa junansu sara da suka cikin
tsananin zafin nama tunga da jarumtaka.
Page 5.
Zidane kd.
Duk sa adda makamansu suka hadu sai dai kaji kara da
tartsatsin wuta na tashi.
Nan fa filin ya rude da shewar jama a .
Sai da jaruman hudu suka shafe kusan dakika dubu daya
da dari uku suna fafata azababben yaki batare da
dayansu ya sami nasarar koda kwarzana a jikin daya ba.
Babban abin da ya fi daurewa mutane kai shine duk salon
da sarki zarmus suka zo shi sai a gasu zarisha ma sun iya
hakama lasmir duk salon dasuka zo shi sai aga cewa sun
hasam sun iya..
Koda jaruman hudu suka ga sun shafe wannan tsawon
lokaci suna gurmurzu ba tare da sun sami wata nasara ba
sai duk suka ja da baya.

DOMIN DOWNLOAD NA LITTAFIN SAI KU DANNA HOTON KASANNAN 👇👇👇👇👇👇👇⬇️⬇️


[post_ads_2] DOWNLOAD BIRNIN AZZALUMAI 6
Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter