Main menu

Pages

KAMARSUCE DAYA part 24 & 25

KAMARSU CE DAYA 111-115 116-120
Official
By
AsmaBaffa
ZULY BEAUTY,ADABIYA ISAH,MRS
MUKHTAR,BIBA,RAMCY MAKEUP Wannan page naku ne.
AUTA ina godiya Allah ya bar kauna.
Mummy tana nan yanzu ba laifi ta rage
damuwa sai dai duk hirarta in dai ba zancen
Na’im zakayi ba to baza ta wani saurareka
ba,amma idan Na’im ne to fa ko kwana zakuyi bata gajiya,duk an ganota ma ko magana za
kayi in dai kana so Mummy ta nutsu to ka fara
kawo zancen Na’im kana karfafa mata gwiwa
cewar za a ga Na’im zai fito yana nan a raye.
Yau ma Aisha tazo tana so Mummy ta bata kudi
zata canja mota ta samu Mummy a daki ta zauna gefenta tare da cewa Mummy naji a
jikina Na’im ya kusa bayyana kwana
nan,Mummy ta washe baki tace ai
insha’allah,Aisha tace Allah yasa yana hannun
na gari,kinga dakinsa Mummy shi yasa kullum
sai na gyarashi gashi kinyi tunani da aka kara canjawa dakin komai kamar Aljannar Duniya ai
Bro yana dawowa za a ga Murna,Mummy tace
wlh kuwa ai kin sanshi da son harkar
wanka,Allah sarki Na’im dina Allah dawo min
dakai lfy,Aisha tace Ameen dai Momma zamu
shirya shagali ranar ai har anko da party zamuyi,suna ta hirar Na’im Mummy tana Jin
dadi sai Aisha tace Mummy yawwa dan Allah
tuna miki zanyi kudin motar da za a bani na
Canja,kisa ya Irfan Ya min Transfer dan Allah
Momma kar Na’im ya dawo ya ganni da
tsohuwar mota,Mummy dadi ya kamata fa tace duk motocin gidan nan Aisha gashi duk su
Irfan sun canja sababbi har na Na’im ma fa
saida su akayi aka kawo sabon yayi ki dauki
daya ciki,Aisha tace Mummy wannan ai sai irin
su Na’im sun min girma ina mace, waya
Mummy ta dauka tare da dannawa Irfan kira lallai yau ya yiwa Aisha transfer na Milyan biyar
zata canja mota,Irfan yace to Mummyn Na’im
zan bata.
Aisha da murna taci gaba da hirar Na’im a
gaban Mummy.
Borno state dangin Salma,Maimuna matar Hashim ta samu ciki wata Uku kenan,kullum
bata da lfy laulayi,amma Hashim sabo da
rashin godiyar Allah irin na Hashim duk ya
manta yanda Maimuna take bashi kulawa a
baya,yanzu kullum fada sukeyi,abu kadan tayi
masifa,sabo da baya samun yanda yake so lokacin tana Amarya duk ya manta,wulakanci
iri iri yake mata,Yana kallo tana Amai amma ko
surarta bazaiyi ba,
Yanzu ma yana Palo yana kallon Indian film
tana waje jikin pampo tana ta sheka Amai
amma ko kallo bata isheshi ba,haka ta gama da kyar jikin ta yana rawa ta wanke wajen tare da
gyara jikinta, ta dan matso jikin inuwa ta
kwanta a kasan wajen,sanyin kasan take so sai
da ta yayyafa ruwa me sanyi a kasan simintin
ta jikashi sannan ta kwanta a kai,nan kuma ta
jika dankwalin Atamfarta sharaf ta lulluba dashi tana jin dadin sanyin.
Hashim sai da ya gama kallonsa ya fito ko
tausayi babu ya kalleta shekeke tare da cewa
kar ki bata min Siminti da Amai fa ki kiyaye ki
karaci kazantarki,kazamar banza wlh aure zan
kara idan na gaji kin isheni,Maimuna ta kalleshi kawai hawaye ya gangaro mata ta dauke kanta
tace amma kasan ba dashi nazo ba kai ka
haddasa min wlh ban taba ganin marar Imani
irinka ba Hashim,ke karki kawo min raini zan
tattakaki ba ruwana da wani cikinki aikin
banza wata tsiya kike tsinana min,da dare cuta,rana Amai,ko yaushe cuta wanne hakkina
kike sauke min,malalaciya da an tabaki kice
zazzabi kike tsaki yaja yayi gaba tara da bugo
murfin kofar.
Masu zaman tsakar gida dai ana ta yi kullum ba
fashi ana tona asirin aure,ana siyan magunguna,masu kulle mazajensu da me dan
mukulli ma suna ta fama,Ubale ya gano abinda
suke masa duk ya koresu gida da saki daya
daya tare da rangado sabuwar Amarya
Iklima,Iklima akwai hankali da ilmi ga kula da
miji bata zuwa wannan hirar ta tsakar gida sai daí idan masu tallan maganin mata sunzo ta
siyi me inganci Ta tafi wajenta,
Nan matan suka Sa mata ido wai ita a dole
ustaziyya har habaici ake mata,Maimuna kuma
bata fita yanzu Sabo da ba lfy,aiki ma Iklima ke
zuwa tana gyara mata ko ina na gidan,har girki tana dan yi mata watarana.
Su Shehu ko zancen Salma basa yi ko da wasa
ma.
Affa kuwa dabbobinsa sai karewa sukeyi daya
bayan daya abin yana damunsa,Ummitu har da
kuka cikin shanu 60 saura 45 maimakon su godewa Allah sai su suka kara shiga bokaye
cewar Salma ce ta jawo musu ayiwa dukiyarsu
katanga da Salma da sauran makiya,Ummitu
tace mun riki bala’i da hannunmu har yanzu
sharrin yarinyar nan binmu yake yi Allah ya Isa
wlh babu wanda zai jawo mana sai Salma ita ce me kashin tsiya,Affa yace bama tare ma
Baza ta barmu mu huta ba ko mayyace ne? Wa
ya sani ai gwara mayu da wannan
yarinyar,haka dai su Affa ko me ya samesu
kullum zargin Salma sukeyi su basa ganewa.
Malam yana ta tuki tuni har sunzo Tafa hanyar Abuja,nan suka tsaya za a ci abinci,Na’im yace
shi bazai ci ba,Malam yace ka kiyayeni fa na
fada ma ka bar ganin ka warke ba ruwana da
kudinka ubanka zanci wlh gwara ma
kaci,Salma ta sheke da dariya,Zainura tace yo
kai me kyau tare da mu ma kaci abinci duk baka sani ba sai yanzu,to har tuwon Dawa ka
lashe a cikinka bare nan wajen yan gayu,Na’im
ya gallawa Zainura harara harda cewa Salma ki
fadawa kawarki ba ruwanta dani, Salma tace
Allah yaci abinci da Ku? Ganin basu gane ba
Zainura ta dinga raina musu hankali tace to har hannun Barira ya kwace nama ya cinye,Salma
ke kuma kinga wannan Ubaliye me makeken
baki da zamu taho? Salma tace ae me hakora
yellow Zainura tace to kinsha cin tuwo tare
dashi kika nace masa sai ya baki sidinsa,Na’im
ya dinga dariya yana toshe hanci,Salma harda kwalla,Zainura tace kai me Kyau Allah ne fa ya
ceceka Amma ka dade kana son Hadizalo
wannan wacce zamu taho tazo tana min
rada,Akwo tuni suka tuno suffar Hadizalon da
Zainura take Nufi,Na’im yace Oh God have
mercy on me. Malam yace kai kuzo mu tafi mana suka shiga
wani dan Restaurant na tashar aka basu
Sakwara da miyar Egusi,Zainura ta gyara Zama
tare da cewa Malam Allah dai ya dai ya biyaka
tana zuba lauma,Haka Salma ma,su
Umma,Na’im sai cakala yake cike da kyankyami,haka suka gama ci aka ci gaba da
tafiya,Zainura tayi bacci motar shuru kake
ji,Salma ma ta kwanta a kafadar Na’im har
suka karasa Abuja Lfy Na’im ya karbi tukin
motar kawai ya kaisu har bakin gate din
gidansu,Nan kowa ya saki baki banda Salma da Na’im duk da cewa an canja komai na gidan
new design.
Na’im ne ya fita ya buga gate din tunda ba
remote a hannunsa,Securities da gudu suka
yanyame gate din tare da dana bindigu,Zainura
har yau bacci take abinta Salma ta tasheta,tana mika da
Salati tace nan ne gidan ko kuwa
wajen shakatawa mukazo,Umma tace ke karfa
ki damemu ki nutsu,Zainura tace Umma daga
tambaya.
Securities suna ganin Na’im suka gigice da ihu
da murna,wasu da gudu suka fada cikin gida wajen Su Mummy gashi anyi sa’a yau Saturday
duk suna gida,Mummy suka ji ihu ana Oga
Na’im a gigice suka Mike gaba daya,Securities
suna Haki suka bada labari gasu can da Salma
da wasu dattijai tare da yarinya sa’ar Salma wai
Zainura,Mummy bata San Sanda tayi sujjada ba ta nuna farin ciki,haka su Irfan ma,sai kuwa ga
Na’im ya shigo da sallama,sai Salma,sai Malam
da Umma,Zainura tana baya sai kalle kalle
takeyi ta rasa inda zata kalla ma,
Tana shigowa ciki ta fara taka kafar a hankali
tana sanda kamar barauniya harda dukawa,tana lallabawa,Hunaif dariyar Zainura
ta kamashi kamar tana taka wata Kwalaba tana
gudu karta yanketa,Mummy baki har kunne
tana ku shigo dan Allah,nan ta rungume Na’im
da karfi tana Hawaye sosai shima Na’im haka
sun dade a haka,sai Su Irfanma suka rungumeshi ana ta murna da Hawaye,Aisha ce
ta karshe tace Bro mun shiga wani Hali na
rashinka we missed u so Much,Mummy kullum
sai tayi kuka,Malam yace to Alhmdllh komai ya
zo karshe,Mummy sai lokacin tace kuyi hakuri
dan Allah ku zauna,Zainura tana tsaye taki zama sai kalle kalle takeyi bata gajiya,Na’im ya
kalli Zainura yace to Zauna mana,
Zainura ta fashe da Kukan Dadi haka kawai aka
ji tana kuka,kowa saida yayi tunanin wani abu
ne ya sameta,Salma tace lfy Zainura?Zainura
tana goge hawaye tace ni ya zanyi Allah yana sona ta kara zubo da Hawaye tare da cewa
badan ikon Allah ba ya zanyi nazo garin nan
har cikin wannan Aljannar duniyar haka cikin
turawa,ni iya haka ma ya isheni darasi a
duniya,ta kalli Na’im ta goge hawaye tace ni
wlh na fasa auren Kanin naka kunnensa yayi ja da yawa gasu nan irinku daya ni jansa yayi min
yawa yasin.
Hhhhhhhh gaba daya palon suka dinga dariya
kamar me,Umma tace ke dalla zauna sarkin
surutun jarabar tsiya ke ko ina bakya kasa
magana? Zauna mana cewar Mummy tana dariyar Maganar Zainura,ta zauna kusa da
Hunaif ta tashi ta dawo Kusa da Irfan nan ma
ta mike ta dawo wajen Na’im tace alquran
mijin Salma yafi fuskar Rahma.
Akayi dariya nan ma ta dawo wajen Malam
tace ga na gida wanda na sani. Mummy tace ya kamata kuci abinci ku huta
kuyi wanka sai a zauna ayi maganar.
Salma ke da kike yar gida ki dauki Umma da
Malam din ki kaisu dakin dake kasa yafi girma
za sufi sakewa a can,Aisha ke ku tafi da Zainura
dakinki ki koya mata komai ta shirya. Salma ga dakinki nan dama ba wanda ke shiga
gyarawa kawai akeyi,kaima Na’im haka,kuje ku
fito aci abinci.Salma ta raka Malam da Umma
dama Malam da Umma su wayayyu ne suna
mu’amula da yan birni sun iya amfani dasu
duk da cewa na gidan su Na’im basu taba ganin irinsa ba saida Salma ta nuna musu, ta
wuce dakinta,Na’im tuni yaga yanda Bedroom
nasa ya koma kamar wata Aljannar duniya,ya
fada wanka,kayansu tuni guards sun kaiwa
kowa dakinsa.
Aisha da Zainura suka shiga Bedroom tare,Zainura tace duk wannan dakinki ne?
Aisha tayi murmushi tace ae mana Zainura tace
cab yo mu a kauye ba sai mu goma mu kwana
ciki ba,Kinga gidan su Zahrau kawarmu dakin
kamar akurkin kaji Amma su Bakwai suke
kwana daki daya,yara suyi ta tsula fitsarin kwance,Aisha tayi dariya tare da cewa mene
Akurki? Zainura anyi har Jss3 tace cage na
chickens hhh Aisha ta gane tace gaskiya
ne,muje kiyi wanka da dare kya bani labarin
kauyen naku,nan ta raka Zainura ta koya
mata,Zainura ga basira har ta iya,Aisha tace Daura Towel ungo karbi,Zainura ta rufe baki da
hannu tace a gabanki ki kallarmin jikina,kuma
wannan guntun tawul haka ni dai bani Zani a
Cikin jakata ina da abuna,Aisha ba musu ta
zuge yar jakar Zainura ta dauko Zani spear har
kamshi yakeyi ga brush dinta harda sabulu give guda da mudubi da Powder da jambaki ja
har jagira,Aisha tace a ranta wannan a kauyen
ma su daban suke gaba dayansu masu Tsabta
ne jibi har tasan tazo da brush da
toothpaste,harda kayan kwalliya,Nan dai ta
bawa Zainura Zani ta cire kayanta tayi wanka tana gama wanka akwai botiki a toilet din ta
wanke kayan da ta cire tas ta fito tace da Aisha
ina zanyi shanya? Aisha ta nuna mata bayan
corido nata ta shanya kayanta har pant data
cire bra ce kadai kuma bata sawa.
Zainura ta fito Aisha ta kalli gashinta har kafada baki me santsi na yan fulani yasha
kananan kitso sabo,Aisha tace yaushe kikayi
kitson nan?tace jiya aka yi min yau sunan
Kawarmu Allah yasa Malam ya taho dani nan
garin,Aisha tace uhm yayi kyau,ai kema fara ce
Amma kina ce mana jajaye? Zainura tace ba irinku ba ni ai bakace ko Salma ban kai
haskenta ba bare ku turawa.suna ta hira har
Zainura ta gama ta dauko riga da skert dinta
shima na sallah ne Lace ba wani me tsada bane
Amma dinkin dan dai dai ita tasa abinta harda
yin acuci Maza Sabo da kitsonta shuku ne, ta yafa bakin gyalenta bayan ta shafa Powder da
jambaki Amma bata Sa ko kwalli a idonta ba,ta
kalli Aisha tace to ina zan Sa jakata kar ta
hargitsa miki daki,ganin Zainura me tsafta ce
Aisha ta karba ta sa mata a sip bari daban da
bata Sa kaya,Zainura tace karki gaji dani naga kina danna waya na hau gadonki na kwanta ko
shimfida zaki min? Aisha tace gadona fa kika
ce? Ki tsaya a matsayinki karki ga na miki
mutunci ki zake kuma zan mai dake dakin
Salma ba wajena ba kina min kauyanci.
Zainura ta kalli Aisha tace toooo ikon Allah sai kice nima na fito da kalar daya halin nawa hali
biyu gareki,dana mutunci dana tsiya gidan
kikazo nima sune dani,kan Uba na miki
kauyanci kikace gadonki din me?an fada miki
bamu da gadon mu? Wlh baki Isa ki rainani ba
sai dai ki raina tsohuwarki da tace nazo wajenki danma kin mun mutunci ne da farko
Amma wlh da na nuna miki wace
Zainura,Zainura taja tsaki,Aisha taji haushi
kamarta wata yarinya karama yar kauye zata
zageta dan kawai ta sakar mata fuska ita dama
bata so Mummy tace yar kauye tazo mata daki ba,dama darajar Mummy taci har ta biyeta
sukayi hira Amma da badan Mummy ba wlh da
sai tayiwa Zainura duka a gidan.
Zainura ta fada saman gadon Aisha tana sani
tace sai an hau ma a yankani,Aisha ta matsa
gefe can tace ke nafa girmeki ba sa’arki bace Naga kina son rainani banza yar kauye zaki
shafa min dirty,Zainura tayi banza da ita tace
bazan biye miki ba mu zama daya Amma zanyi
maganinki kafin na bar gidan nan,Nan Aisha ta
dinga zage zage da mafisa tana ta ciwa Zainura
mutunci akan yan kauye ne. Mummy ce ta shigo ta dauka hira sukeyi ta kirki
tsakanin Aisha da Zainura,tace ku fito aci
abinci,Sun fito a hanya Aisha ta bangaje
Zainura,haka Zainura ta kyaleta kawai.
Malam,Umma,Salma,Zainura,Aisha
,Mummy,Irfan,Hunaif, Dada Babar Mummy, Na’im kadai ake jira,idan kuka ga wankan da
Salma tasha sai ku rantse daga Misira tazo
shigar larabawa tayi.
Abinci aka jera iri iri a palo ba a dining ba
Katon carpet aka Sa wajen.
Kamshi ne ya cika wajen wanda yasa kowa kallon inda ake tahowa ba kowa bane face

Na’im ya dau wanka cikin tsadajjiyar shadda
fara yana kyalli da sheki,Malam da Umma
kallonsa kawai sukeyi Kamar ba Muhd dinsu ba
Sam ya manta dasu ko tunasu baiyi,haka Salma
saida gabanta ya fadi Sabo da kyan da yayi,Mummy farin ciki sosai dasu Irfan da gani
Na’im ba wahala yasha a inda yake ba,domin
jikinsa hutu da jin dadi ya nuna ba wahala ba.
Kusa da Salma ya zauna tare da dan bugunta
kadan a baya irin na tsokana murmushi kawai
tayi cike da kunya Sabo da Mummy dasu Malam sun gani,Abinci aka baje kowa ya fara cin
abinda yake so,Zainura ce kadai take ta ruwan
ido ta rasa wanda zata fara da shi,Salma tace
kici mana,Zainura tace ni dai a zabar
min,Hunaif ya maka mata harara ya dauke kai,
Dada tace yau naga yarinya da tsiya sai an zabar miki ma? Nan Zainura ta fara ci itama har
suka gama ci kowa ya koshi
Malam ne yayi bismillah tare da Budewa da
addua sannan ya fara bayani akan abinda ke
tafe dasu,kowa yayi shuru yana sauraro.
Malam ya basu labari tun a inda ya tsinci Na’im sai Salma,da kuma irin zaman da sukayi cikin
jin dadi da kaunar juna har dalilin da yasa ya
daurawa Salma da Na’im aure tare da gabatar
da shedu masu karfi,har littafin da aka rubuta
da shedu ya basu Suka karanta,Mummy da
Sauran mutanen wajen murna,farin ciki tare da jinjina sukewa Malam,godiya suke musu ba
adadi,tare da fadawa Malam ba matsala dama
can Saurayi da budurwa ne kamar yanda Na’im
ya fada musu a kauye haka ma su Mummy suka
basu labari.
Dada harda Kukan Dadi da tausayi,haka Mummy ma,bayan Malam ya gama bayaninsa
ya sanar musu gobe zasu koma kauye,Mummy
dasu Dada suka ce sai sunyi sati suna ta
rokonsu da kyar suka yarda zasuyi kwana Uku
sunki yarda da Sati dayan.
Mummy tace yanzu basu tuna wacce rayuwa sukayi daku ba Malam ina so in ba damuwa a
bar mana Zainura a nan zuwa wani dan
kwanaki tana tuna musu rayuwarsu ta baya da
sukayi a kauye ko Allah zai sa Memory nasu na
baya ya dawo gaba daya,idan zuwa wani lokaci
bai dawo ba da kaina zan dawo da Zainura gida,Zainura Zaraf tace Allah Baffana bazai
yarda ba sai dai idan Malam ne ya masa
bayani,ni dai nafi son kauyenmu Yasin kina
gani yanda wannan Aisha take min rashin
mutunci a dakinta idan ana so na zauna sai dai
a hada mu daki daya da Salma idan ba haka ba Alquran kauyenmu zan tafi nima ina da iyaye
suna sona ko bamu da kudi na rungumi
talaucinmu bana maitar abin duniya.
Na’im yace sai dai a baki Room ke kadai dai
amma Salma tana da aure taya zaku kwana
tare bazai yuwu ba wlh ni kuma fa? Mummy ta harari Aisha tare da cewa nasan zaki
aikata dama kuma wlh sai ta zauna dake,ke
Zainura idan tayi miki ki rama ko zaginki Aisha
tayi ki rama ko dukanki tayi ki tabbatar kin
rama,Zainura tace an gama Mummy wlh
zubarwa yarinya hakora zanyi,Aisha tayi mukus da ita,Malam ya kira Baban Zainura yayi masa
bayani cikakke yace ba matsala Malam ai mun
yarda da kai.
Zainura ta dan bigi Salma ta kalleta tare da yi
mata signa da Ido tana kallon kayan abincin
wai su kwashe mana su wanke,Salma a hankali tace akwai masu yi,Zainura kowa naji tace mun
shigesu haka zamuyi ta yini muna kwana ba
motsa jini ba aiki daga wanka sai ci? Ni wlh
bazan iya ba na saba da aiki na zauna haka ai
sai jikina ya fara ciwo ni dai zan dinga taya yan
aiki muna yi tare dasu bazan iya zaman kashe wando ba,Mummy tace ba matsala ai Salma ma
tana aiki a gidan nan ta nuna Aisha kinga dai
wacce ko cokali bata dauka,Zainura ta kalli
Aisha tare da rike baki tace keeeeeeee kiyiwa
kanki fada kiyiwa kanki Kiyamullaini ki koyi
abin duniya haka za a miki aure Me gida yaji baki iya girki ba wlh koroki zaiyi,Mu yanzu
Mummy a kauye baki iya tuwo ba ai kin shiga
uku da gori,bakiga wata kawarmu ba Marsiyya
abin mamaki bata iya miyar taushe ba ranar
Juma’a batayin tuwon shinkafa miyar taushe
Juma’a guda aiko mijinta Lawwali ya kai kararta gida aka zaneta aka ce muje mu koya
mata,to kema Aisha idan baki iya ba Allah
Mummy kisa na koya mata kuma wlh sai na
dinga dukanta idan ina koya mata,Dada tayi
dariya tace ni dama ke aka barmin muka tafi
gidana mukayi zamanmu tare a saki a makaranta,Zainura tace keeeeeeee iya rufa ni
ki sayani a nan ma na dan rabe kafin na tafi
garinmu,Dada tace da gaske nake fa,Mummy
tace Hajiya ki Bari ta gama aikinta da nace idan
iyayenta sun baki shike nan ai,Dada tace Allah
kaimu. Malam tuni sun koma wajen da aka saukesu
suna hira Dada tana wajensu da
Mummy,Zainura tana zaune a Palo ita da Salma
sai ga Irfan Ya shigo ya Sha wanka ya kalli
Salma yace fatan dai yanzu ana Sallah matar
Yaya Na’im, Salma tace kai ka sani an fada ma yanzu da ne? Irfan yace ina Raheel wai?Salma
tace ni ban san wani Raheel ba wlh waye?
Ganin fa Aljanine kuma idan mutum yana
Aljanu idan ya warke baya Sanin me yayi ma
sai ya share zancen,Zainura tana zaune sai ga
Hunaif ma sun fito da Aisha suna ta faman dariya suna kallon wata katuwar waya,Hunaif
Yace Bro muyi game mana mun dade ba muyi
ba,Aisha tace zanyi nima,Zainura ta watsa mata
harara tare da dauke kai can kasa tace uwar
iyayi ba a iya girki ba,Aisha taji ta,Salma ma
harda dariya,Irfan suka fara game sosai Zainura tana kallon abin mamaki kuma tana
ganewa kafin kace me ta gane yanda ake game
din to akwai basira,Aisha bata wani Iya ba
cinyeta suke tayi,Sai muryar Zainura suka ji
tace zan iya nima a bani abun muyi da
wani,Suka sheke mata da dariya,Irfan yace ke ko Aisha bata iya ba sabo da ke ba brain zaki ce
ayi dake,Hunaif yace to ko Handle zata iya
rikewa ne? Muryar Na’im suka ji yace hey guys
ba a haka fa wannan shirme ne idan zakuyi da
ita kuyi idan baza ku bata tayi ba mene na
mata dariya. Irfan yafi Saukin kai yace to ke taso muyi na
dura miki kaya,kuma baki isa kin daina ba sai
an gama komai cin da za ayi miki,Zainura tana
dariya tace to,Hunaif ya bata Handle dinsa ita
da Irfan,Zainura Uwar basira sai ga Irfan Ya
kasa cinta,sai wahala yake Sha,tana ta dariya bata ci ba shima Bai ci ba,suna ta yi,Hunaif ya
dinga mamaki da sauran mutanen,Da kyar
Irfan yaci daya da zero suna tayi ta farke dayar
daya da daya,har game time ya kare 1-1 suka
tashi,kuma a haka Irfan yafi kowa iya
game,Hunaif yace sai ya cinyeta suka farayi da Zainura ta masa 2-1,Aisha ta karba ta mata 5-3,
suna gamawa ta jefar da Handle irin shegiyar
nan tare da cewa Ku kiyaye hada kwanyata da
taku haka Allah ya yini ni,dukkanku yanzu zan
iya yin kalolin muryoyinku tafiyarku da komai
naku,ni ba a ja dani ko a kauye,Na’im ya zauna gefen Salma da tayi shuru tana mamakin
Zainura da basira ko ita duk zamanta gidan
bata iya ko gwada game din ba.
Na’im taji ya kwanta mata a jiki tare da cewa
muje Bedroom Ki tayani hira yanzu naga Alama
gudu na kikeyi,Salma tace uhm ni bazanje dakinka ba,Zainura tace ke yar Iska wannan
karya kike a gabanmu wlh kuke tsotsar juna
bakwa kunyar uban kowa har kinfi me kyau
maita,wanne iskanci ne bakuyi ba sai yanzu
zaki dinga karya,to wlh ba abinda me kyau
baiyi dake ba domin mu shaida ne,Irfan ya dinga dariya
kamar me yace yawwa Zainura
kike ko?gwara ki dinga tona musu asiri
wlh,Hunaif ya kalli Zainura yace ke mene tsotse
juna Zainura tace kaji yaro kato da kai baka
sani ba duk iskancin da samari keyi yanzu,yo
kai daga ganinka Alla ai ka dan yiwa mata wani abu,yanzu Ko a kauyenmu su Ubale,Ashiru,Ha
bu,Audu me kifi,Dan Isya me Rake sun San
Iskanci bare kai me Jan kunne,Irfan yana dariya
ya Kalli Hunaif yace kaga ka jawowa kanka
hhhh kuma gaskiya ta fada mene baka yi ba
dan Iskanci zaka tambayeta. Zainura tace wlh duk yaran gidan nan daga Me
kyau sai kai Irfan kunfi kowa kirki amma
wannan mai fuska kamar tana Mura bata da
kirki,shi kuma Hunaif ya fiye iyayi
yanyanyanyan ta gwada maganarsa nan ma
suna ta dariya,Na’im sai gani akayi bashi ba Salma a palon,Irfan yace Ina Salma da Bro?
Zainura ta tabe baki tace wannan ka daina
zancensu da kunga abinda suke a kauye Wlh
Allah baza kuyi magana ba yan Iska ne na
gaske.Irfan yace ke kinga Illarki baki waye ba
da na kaiki yawo tunda kina da hira da abin dariya,Zainura ta rike kugu tace koya min ka
gani idan ban iya ba yau din nan zan rikide na
koma yar birni,Hunaif yace Aisha ce zata koya
miki,Salma baza ta koya miki ba wannan mijin
nata bazai barta ta samu time naki ba,Aisha
tace kuna dai ji Mummy tace ko zaginta nayi ta rama har duka,Zainura tace kuma kin San ni
tantiriyar yar duniyace wlh kina min sai na
miki ko Mummy batace ba,ke Allah na tuba da
dasu Zainab aka taho ai da tuni kina asibiti
Alquran ki godewa Allah ni aka kawo nan, Ke fa
Aisha na fuskanci gani kike kinfi sarauniyar Ingila wayewa ko? Ke gani kike ba wacce ta
kaiki haduwa ko? Aisha tayi fari tace sosai
ma,Zainura ta fara dariya tare da cewa Yasin
kinji na rantse tun a Tafa da muka tsaya cin
abinci naga wacce ta dameki ta shanye,ke tun
a Mararrabar Jos tasha naga wacce ta fiki ki daina bata lokacinki haka Salma nan ta
mitsitsikeki a komai,tausayi kike bani yasin,ni
kaina duk sanda na Zama yar gayu sai na
wuceki.
Irfan da Mummy data shugo suka dinga yiwa
Aisha dariya tana Jin haushin Zainura. Da dare ma da Zainura ta shiga zata kwanta
Aisha sai bargo ta jefo mata wai ta kwana a
kasa tunda bata da mutunci,Zainura ta shareta
ta shimfida abinta ta kwanta ta shaki baccinta.
Bangaren Na’im da Salma kuwa tunda ya
janyeta Bedroom dinsa Kuka takeyi wai ta tuna Affa da Ummitu sai ta tafi wajensu,ba yanda
Na’im baiyi da ita ba taki yarda,shi dan
Iskancinsa ma yake so yayi ko kadan ne amma
Salma taki yarda sai wani kukan banza takeyi
kan su Ummitu da Yan uwan Babanta,shi yasa
ta kasa sakin jiki a gidan tunda suka zo,da kyar tayi bacci ya rungumeta shima yayi
baccin,washe gari Zainura ta riga kowa tashi
tayi brush da wanka ta shirya ta tayi sallah ta
fito Palo da sanyin safiya ko haske gari baiyi ba
ta zauna tare da sa wata cikin yan aiki kunna
mata TV, taga yan aiki suna ta gyare gyare wasu suna kitchen ana shirya girki,ta shige ciki
ta karbi mopper akayi aiki da ita aka gama,ta
shige kitchen aka karasa girki da ita tana kallon
abincin yan gayu,Irfan ya shigo daga Gym ya
shiga kitchen dakko fresh milk da ruwa ya
hango Zainura an tsege daurin ture kaga tsiya tana yanka Albasa a cikin kwai.
Shi tana birgeshi yanda take wayayyiya bata
duhun kai na yan kauye bata tsoron kowa
harkarta takeyi kamar yar gidan,Muryarsa taji
yace ke da safe har kin fito? Zainura ta washe
baki tare da rufe idonta wai kunya ta ganshi da dan wando short da yar riga,tace Laaaa kai ko
kunya haka kuke yawo tumbir billahillazi
Rahamanu ni bazan kalleka haka ba,Idonta a
rufe tace ina kwana,yace lfy lau yana dariya su
Kansu yan aikin dariya sukewa Zainura wai
bata waye ba,tace mu dai ka fita sai kace Gambo dan Fulani a kauyenmu haka yake
yawo aiko kowa dan iska ake ce masa
Yasin,Tabe baki Irfan yayi tare da daukan
abinda yazo dauka yayi waje yana ganin
kauyancin Zainura yayi yawa.
Na’im da Salma sun tashi Na’im yana zuba murmushi yace wai dan Allah baza ki fada min
ba nayi Iskanci ko bamuyi ba?Salma tana
dariya tace nifa ban gane ba bazan iya ganewa
ba,tana kwance ya hau samanta tare da rike
hannayen Salma wai sai ya duba wlh ya
gani,Salma tana dariya suna ta kokawa suna dariya,ina wayarka ta kauye da faifan CD ka sa
mana mu gani mana cewar Salma,ki bari sai
Next weekend sai mu saka a Palo gaba daya a
kalla me akayi a bikin,Salma tace Allah ya
kaimu.
AsmaBaffa

Comments

table of contents title