+2348140419490

Keffi Nasarawa State, Nigeria

Download and read free hausa novels

download CIKIN WAYE complet Hausa novel PDF and TXT

 

CIKIN WAYE complet
Name CIKIN WAYE
Size over than 1MB
Author Fatima Sunusi Rabiu
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 1 may, 2020
descriptionUnknown

download PDF, TXT : KAINE SANADI complet hausa novel

 
KAINE SANADI complet
Name KAINE SANADI
Size over than 1MB
Author Fatima Sunusi Rabiu
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionUnknown


download PDF and TXT - NI DA YAYA LAMEER complet Hausa novel

 
NI DA YAYA LAMEER complet PDF and TXT
Name NI DA YAYA LAMEER
Size over than 1MB
Author Fatima Sunusi Rabiu
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 1 may, 2020
descriptionnone


AJALIN SO complet hausa novel PDF, TXT and DOC

 

AJALIN SO complet
Name AJALIN SO
Size over than 1MB
Author Surayya Hms
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionhausa touching heart 💞 love story

AMJAD hausa novel PDF, TXT and DOC

 

AMJAD complet
Name AMJAD
Size over than 1MB
Author Dijensy
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionhausa touching heart 💞 love story

ANAL complet hausa novel PDF, TXT and DOC

 
ANAL complet
Name ANAL
Size over than 1MB
Author Aliyu Ultimate 3mc
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionhausa touching heart 💞 love story


FUREN JUJI complet Hausa novel PDF, TXT and DOC

FUREN JUJI complet
Name FUREN JUJI
Size over than 1MB
Author Zainab idris Makawa
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionhausa 💞 love story


KAREENATY KAWATA complet Hausa novel PDF, TXT and DOC

 

KAREENATY kawata complet
Name KAREENATY kawata
Size over than 1MB
Author Dija
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionhausa touching heart 💞 love story

RABUWA CE SANADI complet Hausa novel PDF, TXT and DOC


RABUWA CE SANADI complet
Name RABUWACE SANADI
Size over than 2MB
Author Maimuna basheer
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionhausa touching heart 💞 love story

RASHIN RABO complet hausa novel PDF, TXT and DOC

 

RASHIN RABO complet
Name RASHIN RABO
Size over than 1MB
Author Meelat Musa
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionhausa touching heart 💞 love story

RAYUWAR NUR complet Hausa novel PDF and TXT and DOC


RAYUWAR NUR complet
Name RAYUWAR NUR
Size over than 1MB
Author Ma man Nurul Huda
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 30 April, 2020
descriptionhausa touching heart 💞 love story


TAGWAYEN MAZA complet Hausa novel PDF and TXT and DOC

 

TAGWAYEN MAZA COMPLET
Name TAKARI
Size less than 2MB
Author Fatima Zahra
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 27 April, 2020
descriptionhausa love story

DOWNLOAD PDF
DOWNLOAD TXT
TAKARI complet Hausa novel PDF and TXT


TAKARI COMPLET
Name TAKARI
Size less than 1MB
Author Zainab idris makawa
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 27 April, 2020
descriptionhausa love story

DOWNLOAD PDF
DOWNLOAD TXT

TASKAR AJALI book 2 complet Hausa novel PDF and TXT

 
TASKAR AJALI book 2
Name TASKAR AJALI
Size less than 1MB
Author Abdulaziz Sani madakin gini
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 27 April, 2020
descriptionhausa adventure story

DOWNLOAD TXT

DOWNLOAD PDF
TASKAR AJALI book 1 complet PDF and TXT hausa novel

 
TASKAR AJALI book 1
Name TASKAR AJALI
Size less than 1MB
Author Abdulaziz Sani madakin gini
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 27 April, 2020
descriptionhausa adventure story

YAR BARIKI complete hausa novel ebook DOC & PDF

 YAR BARIKI Book 1
Name YAR BARIKI
Size less than 1MB
Author Rufaidah Omar
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 26 April, 2020
descriptionhausa love story


YA MACE KYAUTAR ALLAH ebook PDF & TXT

 


YA MACE KYAUTAR ALLAH complet
Name YA MACE KYAUTAR ALLAH
Size less than 1MB
Author Aashman
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 26 April, 2020
descriptionhausa love story


YAR GWAGWARMAYA complet hausa novel ebook TXT & PDF

 
W
YAR GWAGWARMAYA complet
Name YAR GWAGWARMAYA
Size less than 1MB
Author Nasmat
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 24 April, 2020
descriptionhausa love story


YAZEED KO YASEER complete hausa novel ebook TXT & PDF

 


YAZEER KO YAZEED complet
Name YAZEER KO YASEER
Size less than 1MB
Author Aishat Faruq
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 24 April, 2020
descriptionnoneZAKKATAH complet hausa novel ebook TXT & PDF

 

ZAKKATAH complet
Name ZAKKATAH
Size less than 1MB
Author Gital
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 22 April, 2020
descriptionlabari mai taba zuciya


DOWNLOAD PDFDOWNLOAD TXT

ZAFIN SO complet Hausa Novel ebook TXT & PDF

 ZAFIN SO complet
Name ZAFIN SO
Size less than 1MB
Author Amrah & Halifa
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
ebook compiler Shuraih 99%
date modified 22 April, 2020
descriptionkayataccen littafin marubuta biyu na soyayya mai taba zuciyan dukkan wani masoyi dake soyayya


DOWNLOAD PDFDOWNLOAD TXT

ZAMA DA KISHIYA complet hausa novel ebook txt + pdf

 

ZAMA DA KISHIYA complete
Name ZAMA DA KISHIYA
Size - 1MB
Author Feedohm
File Type txt and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
date modified 21 April, 2020
descriptionNo description


DOWNLOAD PDF

CLICK HERE FIRST

CAME BACK AND CLICK HERE TO DOWNLOAD


DOWNLOAD TXT

CLICK HERE FIRST

CAME BACK AND CLICK HERE TO DOWNLOAD

ZURFIN CIKI book 1 complete Hausa novel eboom

 ZURFIN CIKI book 1
Name ZURFIN CIKI
Size - 1MB
Author unknown
File Type text and pdf
uploader Mr Dlhausanovels
date modified 21 April, 2020
descriptionNo description


DOWNLOAD PDF
DOWNLOAD TXT
download LOKACI NE complet ebook TXT

 

LOKACI NE
Complet littafin Fauziya M bala
Ebook TXT

Mun karanta littafinnan a baya a wannan kafa tamu amman bamu kawo ebook nashi ba toh Alhamdulillah yanzu mun hada ebook TXT na littafin sai ku downloading nashi a nan kasa


download RIBAR BIYAYYA complet apk + ebook

RIBAR BIYAYYA
Hausa novel by SAWWAMA QAWWAMA
ebook TXT, and Application

Littafin Ribar biyayya na gwarzuwa kuma fasihiyar marubuciya Sawwama Qawwama littafin yayi dadi Sosai yadda bakwa zato hakan yasa muka hada muku ebook nashi da application ga masu wayan android

Zaku iya dauko littafin anan kasa

Ga masu wayan Android sai ku dauko Application din anan kasa


Ga masu bukatan Ebook TXT sai su dauko shi anan kasa
ABOKAI book 1 part 12

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 12
.
"Ok na fahimce ka sai yanzu na gano abin da ka hango maganarka dutse daka ce hankulan mutanen Nijeriya sai ya tashi, to amma izan na dauko maganarka ta farko kace Gobe, kana nufin yau da dare kenan zamu fita aikin ko kaka"
Jagwa ya fada yana kokarin sake zaro wata sigarin
.
Audu ya mike tsaye ya zaro karamar bindigarsa wacce ako wanne lokaci take soke a kugunsa, ya kafa bakin bindigar a lebbansa sannan ya juya akalar bindigar ta kalli bakin kofar dakin,
"Al'umman Nijeriya,Gwamnatin Nijeriya bala'I bisa kanku, Masifa bisa kanku babu mahalukin da zai kareku daga wannan masifar da ta tunkaro ku," Audu na gama fadin hakan ya fice daga dakin
****** ****
Masoya suka ce Soyayya ruwan zumace kauna ruwan rakece, hakika maganarsu ta tabbata akan Aliyu da zara'u,
Zara'u ta tsinci kanta cikin wawakeken kogin soyayya, inda ta runga ninkaya cikin Annashwa,
Tun daga ranar da zara'u ta furta wa Aliyu kalmar Kauna, suka fara gina soyayyarsu bisa koyarwan Addini, suna kula da junansu sosai, ya kasance kusan kullum Aliyu,haidar,mansir,jibrin da hasan a benue market suke wuni ,
.
Zara'u ta yi farin ciki ainun da samun masoyi mai matukar kaunarta, hade da manyan yayu hudu masu kula da ita,
Tana jin dadin kasancewa cikin su, sabida akowanne lokaci cikin fara'a suke, sukegusar mata da h, sun dauketa tamkar yar'uwarsu ta jini, a da can suna kiran kansu da Abokai biyar, amma yanzu kiran kansu suke da YAN UWA shida,
,
A dan kankanin zaman da zara'u tayi da abokan ta fahimci cewa igiyar abotarsu mai karfice, sannan ta san halayen kowa daga cikinsu, gami da tarihinsu,
Kaman kullum yau ma Abokan ne tare da zara'u a tsaye a bakim gate din makarantar, haidar ya tare acaba guda biyu, ya juyo ya dubi zara'u wacce ta kafe Aliyu da idanu, shima Aliyu idanunsa akan ta suke baya kiftawa,
"Kanwarmu zo ki hau ku tafi, ki bar mayen soyayyar nan,"
Haidar ya fada
Zara'u tayi murmushi ta juyo ta dubi manyan yayyunata tace da su, "nagode sosai yan'uwana, sai gobe izan Allah ya kaimu"
Tana gama fadin hakan ta juya ta nufi wurin da babur din yake har ta kai wurin sai ta tsaya ta, ko ba'a fada mata ba tasan idanuwan Aliyu akanta suke
Zara'u ta juyo ta fara takawa a hankali har ta karisa wurin abokan mansir ne yace "me ya faru kuma kika da wo ko kinyi mantuwane a benue market naje na dauko maki"
"Magana zan da sahibina"
Zara'u ta fadi tana kallon Aliyu
Cikim zumudi Aliyu ya kariso gabanta murmushi dauke akan fuskarsa,
"Dama so nake na fadamaka, gobe zan yi maka babbar kyauta, wacce baka taba tsammani ba,"
Zara'u ta fadi tana wasa da yatsunta , Aliyu yayi murmushi har fararen hakwaransa suka bayyana yace "kice gobe nayi kyakkyawar tanaji kenan,"
Ta gyada masa kai , jibrin ya kariso wajen yace "to sarkin masoya ai kabarta ta tafi gida ko, ko so kake ai wa kanwarmu fada a gida"
"To zara'u sai goben in Allah ya kaimu" aliyu ya fada,
Jibrin,haidar,hasan da mansir suka hada baki lokaci daya suka ce "to Allah ya kiyaye hanya yar karamar kanwarmu,"
"Ameeen" ta fadi daga nan ta hau babur din . Mai babur din daya gaji da tsayuwa ya tayar sannan ya bashi wuta, shi ma dayan mai babur din daya lodi, kulunan abincin ya bisu a baya.
*********
Irin zunzurutun Zumudin zuwan gobe da Aliyu yake bata faduwa, ya gagara sukuni Allah Allah yake gobe tayi don yaga irin kyautar da masoyiyar tasa zata bashi,
.
Babu mutumin da zai arba da Aliyu a wannan rana bai fahimci cewa yana cikin farin ciki ba, A ranar rawa ya runga yi gami da tsalle,
Ya addabi sauran abokan nasa da surutu yana fadin "kai soyayya da dadi abokai ya kamata kuma ku fara ko don ku dandani irin dadin dake cikinta wanda ya dare Zuma dadi"
" duk wanda baya soyayya bakaramin kwaransa akai ba"
"Masoyiyata ina jiranki, ina fa sonki, jinin jikina nakine masoyiyata, jinin jikinki nawane masoyiyata, sonki yai mani kamu a zuciyata, ya ratsa cikin jini da bargon jikina,"
.
"Ka ga Aliyu don Allah kai mana shiru muyi barci mana, ka duba agogo ka gani yanzu karfe Goman dare ne fa, amma duk kabi ka damemu da waka, in da gaske begen masoyiyarkan kake me yasa baka bita gidansu ba" Jibrin ya fadi yana gyara kwanciyarsa
"To naji nayi shiru, amma fa ni bazan iya barci ba," Aliyu ya bashi amsa
Jibrin yayi tsaki ya dubi haidar,mansir da hasan wayanda sukai nisa cikin bacci yace
"Can ta matse maka mudai kam munyi Zaria"
........
Abokai da yan uwa ku gafarceni, littafi na daya ya kare a nan,
Shin yan ta'addan zasu sami nasarar cika kudirinsu
.
Yaya alakar Abokan zai kasance daga karshe,
Wani kyauta zara'u ke kokarin baiwa Aliyu
*
Ni Marubucin littafin SHURAIH USMAN nace sai mu tara a littafi n a biyu don jin cigaban wanga labari a wani loton
.


ABOKAI book 1 part 11

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 11
.
******
Labarin kama dan ta'adda Sidi kashe babba kashe yaro ya karade gaba daya Ilahirin Garin Nigeria da kewayenta, inda gidajen watsa labarai da jaridu gami da kafar sadarwa sukai ta yayata labarin,
.
Dogon dakine da ya tsaru iya tsaruwa , a tsakiyar dakin an girke wani dogon teburi na gilashi daya kusan mamaye dakin,
An zagaye teburin gilashin da wasu kyawawan kujeru masu matukar laushi,
.
Kwamishinan yan sanda Abdullahi makeri ne sanye cikin kayan Gida yana zaune akan daya daga cikin kujerun da sukai wa teburin kawanya fuskarsa na duban wani mutum dake zaune a gefensa
.
Mutumin daya kasance fari yana da kiba ga katuwar tumbi nan daya ajje tamkar mai ciki, yana sanye da fararen kaya zariya ya yafa babbar riga akanta,
,
Lokaci daya farin mutumin da shekarunsa baza su wuce hamsin da wani abu ba ya juya da dubansa ga karshen dogon dakin, cikin sauri shima kwamishinan yan sanda Abdullahi makeri yai duba izuwa karshen dogon dakin inda wani makeken talabijin ke kafe a jikin bangon dakin,
.
Wata kyakkyawar matace cikin shigan hausawa aka nuno cikin talabijin din tana cewa
"A jiya ne talata yan sandan garin kano bisa jagorancin mataimakin kwamishina kamalu suka kai harin sumame ga yan ta'addan nan da suka addabi Nijeriya a wani hotel mai suna city hotel dake karamar hukumar warawa inda sukayi mummunan artabo da yan ta'addan, daga karshe yan sanda sukai nasarar harbin dan ta'adda daya, suka kuma kame shugaban yan ta'addan mai suna SIDI kashe babba kashe yaro,
A tattaunawar da muka yi da Acp kamalu shugaban rundunar da suka kai sumamen ya shaida mana cewa daya daga cikin yan leken asirin da suka barbaza a cikin garin kano ne ya sanar da su maboyar yan ta'addan, basuyi kasa a guiwa ba ya demi jami'ai suka nufi hotel din , Acp kamalu ya kara da cewa jami'I daya ne yaji Rauni a kafadarsa yayin artabonsu da yan ta'addan kuma iyanzu yana nan ana kula da shi a asibiti,
Shi kuma shugaban yan ta'addan yana nan a tsare a wajen yan sanda duka duka dai anan muka kawo maku karshen labaran namu na yau...."
.
Farin mutumin yayi gyaran murya kana ya dubi kwamishina yace "gaisheku jami'an mu, kunyi aiki mai kyau muna alfahari daku"
"Mun gode yallabai" kwamishina ya fadi yana murmushi
"Wani asibiti kuka kai Jami'in da aka harbesa a kafada ,"farin mutumin da aka kira da yallabai ya bukata
"General hospital sir"
.
"Ok, bazan......."
Maganar tasa ta katse a sakamakon karar ansakuwwar wayarsa data karade dakin,
Farin mutumin ya saka hannu cikin burmemiyar babbar rigarsa ya ciro wayar , kai tsaye ya kara wayar a kunnensa daga can bangaren aka ce
"Assalamu'alaika you're excellency Abubakar Bappa the governor of kano state "
"Wa'alaikassalam you're excellency Umar bahaje the President of Nigeria"
Farin mutumin da sai yanzu na fahimci shine Gwamnan kano ya fadi yana murmushi
"Na samu labarin artabun da jami'an mu sukai da yan ta'addan nan , dafatan kun baiwa jami'in da yaji raunin kyakkywan kulawa"
Aka fadi daga can bangaren
"Eh yallabai yanzu haka ma yana cikin koshin lafiya" gwamna Abubakar bappa ya fadi
"Nan da yan wasu kwanaki zan shigo Nijeriya, sannan ina son dan ta'addan da aka kame din nan kulawarsa ta koma hannun Sojoji, saboda gudun mishkila"
.
"Yallabai me zai sa ba zamu barshi a wajen yan sanda ba tunda yanzu haka yana nan suna gana masa azaba iri iri, don ya fadi wani ta'addanci ne suke shirin aiwatarwa nan gaba, sannan su waye ke taimaka masu"
"Ok kuyi duk abun da kuke ganin yafi dacewa, sai anjima ABOKI na"
"Yauwa bahaje sai anjima"
Gwamna Abubakar bappa ya fadi kana ya mayar da wayar cikin aljihunsa fuskarsa cike da murmushi
Ya dubi kwamishina yace "ku cigaba da tsare dan ta'addan, zan neme ka zuwa wani lokacin, menene sunan dan sandan da yaji raunin ma"
"Mudassir," kwamishina ya basa amsa
Lokaci guda gwamna ya mike tsaye ya gyara burgujejiyar babbar rigarsa "a bashi dubu hamsin hade da hutun tsawon lokaci har sai ya warke"
Ya fada yayin da ya soma tafiya yana dumfarar kofar fita daga dogon dakin
"Ok sir"
*****=========*******
Garin Kaduna,
"Audu yanzu me ya kamata muyi,duk yaran da oga ya bukata na kawo su amma kuma Oga yanzu yana can hannun yan sanda"
Jagwa ya fadi yana kallon Audu wanda Ransa ke matukar bace,
Audu yayi ihu gamida karaji ya daga hannunsa sama ya doki karamin teburin gilashin dake gabansa wanda akai musamman don ajje abinci da abun sha,
.
Karar tarwatsewar teburin gilashin gami da ihun da Audu yayi ne ya sanya mutanen dake Harabar Gidan suka durfafo dakin da su Audu suke cikin Gudu,tafiyar kankanin lokaci ce ta sadasu da dakin gaba dayansu suka zazzaro kananun bindigogi daga kugunsu suka afka cikin dakin,
.
Rundunan Mutanen da akalla sun kai Goma sukai kasake da bindigun a hannunsu sai kalle kalle suke, daya daga cikin mutanen ne yace "yallabai ca muke ko wani abunne ya faru da muka ji ihu da kuma karar fashewar gilashi "
.
"Babu komai ku koma kan bakin aikinku" jagwa ya fadi yana kokarin ciro wani abu cikin aljihunsa
Fakitin sigari ya ciro ya zare kara daya ya kafeta a labbansa, kana ya ciro kyastu ya ya kunna ma sigarin wuta,
"Yanzu me ya kamata muyi don ganin oga ya fito" jagwa ya fadi yana feso hayaki ta hanci ta baki
.
"Abun da nake tunani kenan don kunsan in babu oga to babu ta yadda aikinmu zai yiwu" Aba yawo dake can kuryan bango ya fadi
Audu yayi murmushin kuna sannan yace "tabbas yan sandan Nijeriya sun tsokano wa kansu tsuliyan dodo, sun taro babbar masifar da bata da karshe tun da har suka kama mana shugaba sa'annan suka kashe dan'uwanmu, gobe goben nan mutanen Nijeriya zasu fara yi wa gwamnati bore, domin kuwa a gobe ne mutane zasu farka da mummunan labari wacce zata tayar da hankulansu"
.
"Ban fa fahimci maganar kannan ba, shin me zamu aikata da har zai tayar da hankulan mutanen Nijeriya"
Aba yawo ya fadi yana kokarin matsowa kusa da Audu,
Audu ya fashe da dariyar kyeta yana duban jagwa da aba yawo yace "mummunan Tuggu na shirya wacce zatai silar abubuwa da dama ciki kuwa har da asarar rayuka"
"Wacce iriyar Tuggu kuma" jagwa ya bukata
"GARKUWA, (kidnapping)" audu ya bashi amsa
"Wa zamu yi garkuwa da shi, mr president ko wa," jagwa ya sake tambayar audu yana zukan guntun sigarin dake hannunsa
"Government College Keffi, daliban makarantan gaba dayansu zamu sace, "
.
"To babban magana, lallai kuwa da babban aiki gabanmu amma kuma kake cewa gobe kasan akalla sai mun shafe sati muna shirya yadda zamuyi mu shiga makarantar"
Aba yawo ya fada
Jagwa yayi murmushi ya yadda guntun ragowar sigarin dake hannunsa akan Tiles din dakin yace "duk bama wannan ba, dakwai makarantu bila'adadin a Nijeriya me yasa ka zabi Government College keffi a cikinsu"
.
Audu ya sake barkewa da dariya wacce tafi kama da kukan jaki a karo na biyu kana yace "gaba daya jihohin Nijeriya talatin da shida , ta hadu ne a makarantar, domin kuwa kowacce jiha tana da dalibi a makarantar"
"Kayi mani gwari gwari kasan ban cika gane hausan nan taka ba" jagwa ya bukata
Audu yayi murmushi sannan yace "ina nufin bawai mutanen jihar nasarawa ne kadai a makarantar ba, akwai dalibai daga sassan nijeriya, wayanda karatu ne ya kawosu garin, kasan makarantar kwana ce"
.
"Ok na fahimce ka sai yanzu na gano abin da ka hango maganarka dutse daka ce hankulan mutanen Nijeriya sai ya tashi, to amma izan na dauko maganarka ta farko kace Gobe, kana nufin yau da dare  kenan zamu fita aikin ko kaka"
Jagwa ya fada yana kokarin sake zaro wata sigarin


ABOKAI book 1 part 10

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 10
.
"Anya Aliyu zai zo kuwa ga shi har Hudu tayi "
Zara'u ce ke fadin hakan cikin zuciyarta, Tun dazu ta idar da Saida Abincinta a iya saninta karfe Hudu, bai taba yi mata a makarantar ba, uku da wani abu take barin makarantar,
Cikin kasala ta mike tsaye ta isa wurin kulolin abin cin ta fara harhada kayayyakin ta, har ta gama har hadawa zuciyanta na muradin ganin Aliyu bata taba jin tana zumudin ganin sa ba irin yau don yau ya kasaance tamkar babbar ranace gareta.
.
Ranar da zata bayyana masa abun da ke kunshe cikin zuciyarta wanda da can kunya ya hanata fadi,
"Ke zara'u me zai hana ki dan tsaya kiyi jiransa zuwa hudu da rabi indai bai zo bane sai ki tafi gobe kwa hadu"
Wani sashi daga cikin zuciyarta ya sanar da ita, lokaci guda tayi na'am da shawarar da barin zuciyartar ta bata, bayan ta gama kikkimtsa kayanta waje guda sai ta koma ta zauna akan dogon bencin dake bayan ta
.....
Kamar daga sama sai zara'u ta jiyo muryan Haidar yana doka ma mutanen wurin sallama cikin barkwanci,
Wata jibgegiyar tsohuwa mai nanannen hanci ne ta amsa sallamar kana tace "a'a abokai yau kam kun makara dan tuni munci kasuwa yanzu haka shirin rufe kasuwar muke"
.
"Ayya yar tsohowa ai muma yau ba Kasuwar mukazo ci ba, wacce muka saba zuwa wajenta tun da can yanzuma wurinta muka zo" Mansir ya fadi cikin barkwanci yana kallon yar tsohuwar
.
Wata bakar mata mai Jiki bazata wuce shekaru talatin ba dake gefe tana Suyan doya ta juyo ta kallesu tace "tab to kun makaro don tuni wacce kuka zo wurintar ta wuce Gida"
"Kenan har yanzu doya bai kare ba, to ma ta ya za'ai ya kare alhalin mai doyar tana ehm ehem ehmmm"
Jibrin yafadi yana murmushi,
"Kai kunga banason shekiyanci dun Allah ku wuce wajenta ga zara'un can tana shirin Tashi"
Bakar matar ta fadi
Dukkansu sukayi dariya suka nufi wurin da zara'u take, inda sabo sun saba a duk lokacin da suka zo benue market sai sunyi barkwanci da matan dake wajen, musamman ma maman Ladi,
.
Wani irin farin ciki take ji mara misaltuwa lokaci daya ta tsinci kanta tana mai murmushi
Su janet dake gefe suna kula da yanayinta suka dan matso kusa da ita janet ta dafa kafadarta tace
"Ga su Aliyun sunzo don nasan su kike jira inba haka ba da tun dazu kin wuce Gida"
.
"Assalamu'alaiki hasken Idaniyata" Aliyu ne ya rangada sallama cikin murya mai sanyi,dadi hade kwantarwa masoyi rai,
Cikin fara'a ta dago kai ta dubesu su Biyar ne kamar yadda ta sansu
Ta amsa sallamar Cikin daddadan murya wadda har tafi na Aliyu dadi,
Janet ce ta mike zumbur ta dubi Aliyu tace
"Ai gwamma da kazo Tun dazu take jiranka, "
"Da gaske kike " Abokan biyar suka bukata cikin hade baki,
"Hmm. To in ba Aliyu take jira ba wa take jira ita da take tashi karfe uku amma gashi yau har hudu da rabi , to me take jira"
Dayan budurwar tafadi tana kallon zara'u wacce ta ke kallon kasa
Janet tace "barta kawai blessing, aliyu zara'u tana sonka fa kawai dai kunya ce ta hanata........."
.
"Ke yi mana shiru da Allah" zara'u ta katseta da fadin hakan,
Ta mike tsaye ta dubi Aliyu shi da Abokansa tace "Aliyu"
Cikin wata iriyar murya ta kira sunan nasa
"Na'am zara'u"
Ya amsa cikin farinciki da doki na jin abun da zata fadamasa, yasan dai yau dolenta ta kauda kunya gefe guda ta fadi masa abun da ke ranta game da shi
.
Zara'u ta jinjina kai, ta daga kwayar idanunta ta kalli idanun Aliyu wanda yake kafe a kanta
"Aliyu ayau zan kauda kunya na fada maka matsayinka a zuciyata, Aliyu nasan cewa kana matukar sona, kana matukar kishina, ka na Zumudin Ganina,to kasani nima ina Sonka, babu mutumin dana ke zumudin gani sama da kai, a duk lokacin da zan rabu da kai na kanji ba dadi, na kanji dama nayi shekaru dakai kana fada mani dadadan kalamanka, I NA SON KA aliyu"
.
Tsalle Aliyu yayi cikin murna suma abokan nasa suka mara masa baya suka runga ayayyaku wanda suka kirashi da MURNA ko celebration,
Tsirarun dalibai da mata masu saida abinci a benue market sai dariya suke don in da sabo to sun saba da ganin abokan a irin wannan yanayi a duk lokacin da suke farin ciki,,
.
"Maman jona wai me ya samu yarannan haka suke ta tsalle tsalle suna yi wa mutane ihu" mama ladi ta tambayi wata mata kirista dake gefenta tana saida fanke,
"Ba zai wuci akan yarinyar can bace" maman jona ta fadi,
Tsaki maman ladi tayi kana tace "aiko anyi yan iskan yara"
...
zara'u taji wani sanyi ya ziyarci ranta nan take wani dausayin cakudadden dusar kankara ya tarwatse a zuciyarta sanyi mai ni'ima ya mamaye zuciyar gaba daya,
.
Bayan Abokan sun gama murna da jin furucin daya fito daga bakin zara'u sai suka matso gabanta, suka dubeta mansir ya yi murmushi yace
.
"a gaskiya mun yi farin ciki sosai zara da kika aminta da abokinmu kika dauke shi a matsayin saurayinki da yardar Allah wannan soyayya taku sai ta kaiku ga aure "
.
"Ameen mansir, ki sani cewa dukkan wani damuwa na Aliyu damuwar muce,bakin cikinsa bakin cikin mu ne, hakanan farin cikinsa farin cikin mu ne, daga yanzu kema kin zama wata sashe a cikinmu"
Jibrin ne yafada yana kallon zara'
.
Hassan ya matso kusa yana murmushi ya dubi zara'u yace "zara' ga Amanar Abokin mu kuma jigon farin cikinmu mai sakamu nishadi a kowanne irin yanayi, Dan Allah ki kula mana da shi kada ki sanya shi kuka, domin izan yayi kuka to muma duka sai munyi kuka"
.
Zara Wacce kanta ke duke yana kallon kasa, tun sa'in da abokan suka fara bayanin ta sadda kanta kas tana jin zantukansu
Ta dago kai a hankali tace "in Allah ya yarda ba zan taba baku kunya ba"
.
Haidar ya dubi sauran abokan nasa yace "sai muyi sauri mu kwashi kulolin nan mu wuce ..."
Batare da sun jira ya idar da maganarsa ba suka fara kwashe kuloli da sauran kayan abincin,
.
Zara'u ta mike da sauri tace dasu "da kun barsu don yanzu mai kwashewa zai zo"
.
Haidar yayi murmushi sannan yace "ki dauke mu a matsayin yayunki zara, yayu har hudu baza su iya barin karamar kanwarsu ta kashe kudinta wurin daukan wayannan kananun kayan ba"
Yana gama fadin hakan ya ciccibi wata murgujejiyar kula ya aza a kansa
.
Hasan wanda ya dora yar karamar kula akansa hannunsa na dama na rike da farin roban penti, ya juyo ya dubi zara'u yace "kamar yadda aboki haidar ya fadi, daga yau kin zamo kanwarmu, agabanmu dai ba zaki sake wani aikin wahala ba,"
.
"Naji dadi gami da farin ciki da samun yan uwa hudu, da Masoyi masu jajirtacciyar zuciya ,masu burin su kauda wa kanwarsu da dukkan bakin cikin ta, ina ma da Allah ya halicceni a matsayin kanwa daga cikin dayanku" zara ta fadi cikin murya mai kashe jiki,
Dukkansu jikinsu yayi sanyi, lokaci daya suka fahimci halin da Zara take ciki,
Siraran hawayene suka fara zarya akan kyakkyawar fuskarta ta sanya hannu cikin sauri ta share,
Aliyu ya dubeta yace "Masoyiya meye kuma na kuka ai yanzu duk mun zama daya"
Yafadi cikin sigar wasa,
Mansir ya matso kusa da ita yana kokarin ture Aliyu yace "da Allah ban wuri, tun ba aje ko'ina ba har ka fara sanya mani yar kankanuwar kanwa kuka, yi shiru yar kankanuwar kanwata,ga Alawa nan na kawo maki" ya ciro chaculeti yana mika mata,
Ta mika hannu ta karba tana mai murmushi
"Amma fa kada ki baiwa wannan dan kwadayin dun nasan sai ya nemi ya sha" haidar ya fadi yana kallon Aliyu,
Lokaci na farko da Aliyu ya fara kame dariya amma duk da haka sai da ya murmusa wadda hakwaransa suka baiyana,
"Masoyiya zaki shanye kuwa ki hanani" Aliyu ya fada yana kallonta da murmushi akan fuskarsa
,
Noke hannu tayi alamun ta hana sannan tace "ai yayana yace kar na baka" cikin muryan yara tayi maganar, hakan ya sanya su duka suka kwashe da dariya har sauran matan benue market masu saida abinci dake gefe suna kallonsu wayanda abun yayi matukar basu sha'awa
Inna mai doya ta bude faffadan bakinta mai kama da kofan gari tace "ja'irar yarinya, ashe itama son Aliyun take"
.
Abokai biyar da budurwa zara suka durfafi gidan su zara' a haka sukaita hira cikin Annashwa nishadi gamida farin ciki,
Farin ciki a xuciyar zara baya faduwa, ta sam u kanta cikin wani irin yanayi na farin ciki irin wadda bata taba tsintar kanta ciki ba,
*****


ABOKAI book 1 part 9

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 09
.
***
Karamin wajene mai dauke da manyan bishiyu guda hudu bishiyoyin sune suka taimaka sosai wajen yiwa wurin rumfa da rassansu, na daga cikin abun dake kara wa wajen ni'ima shine daddadan iskan dake futowa ta cikin bishiyoyin da suke wurin
.
Tsirarun mutane ne a wajen suke kasuwancinsu yawancinsu matane masu saida Abunci da kayan kwalama, daga gaban wajen da dalibai suke kira da beneu market dogon bencine a girke saman kututturin itace a gaban bencin da kadan wani teburin katako ne mai dauke da manyan kuloli na abinci sai Robobin zuba abinci dake gefe cikin karamin roban penti
.
Tana zaune akan dogon bencin tayi tagumi, lokaci lokaci takan mike tsaye tayi waige waige da alama dai wani abun take nema,
Kamar ko wani lokaci yanzuma ta mike tsaye ta kai dubanta hanyar dakin kwanan dalibai tana waige waige ko idanunta zasu ci karo da Abunda take nema
!!
Wasu yan mata biyu wayanda kallo daya zakai masu ka gane ba Musulmai bane suna zaune a gefenta sun kula sosai da yanayinta hakan yasa suka dan matso kusa da ita,
"Zara, me kike lekawa ne haka tun dazu kin kasa samun sukuni sai leke leke kike"
Daga cikin matan daya ta fadi cikin gurbatacciyar hausa,
Zara tayi ajiyar zuciya ta juyo da kyakkyawar fuskarta ta dubi yan matan wayanda suke sanye da kananan riguna da fingilallun Siket tace
"Ba komai Janet"
Bakar budurwan da aka kira da jenet tace "ko dai Aliyu kike lekene"
"A'a aliyu kuma me zai sa na riga lekensa"
Zara ta fadi
"So mana," janet ta bata amsa tana duban budurwar dake gefenta
Cikin halin ko'in kula zara tace "So kuma haba waya fada maki cewa ni ina sonsa,"
Dayar budurwar tayi murmushi tace "zara kenan kina so kina kaiwa kasuwa, in bakiyi sauri kin amshi soyayyarsa ba kina ji kina gani wata zatai maki kwace"
.
Zara tayi shiru taki cewa komai ta sadda kanta kas tana Tunani a hakikanin gaskiya tana matukar Son Aliyu to amma tana jin kunyar fadamasa,
.
Tun Aliyu yana SS2 zangon karshe ya hadu da zara a benue market,
Wata rana suna dawowa daga Aji zasu wuce zuwa hostel ,
Suna tafiya suna hira cikin wasa da dariya Aliyu sai dariya yake kyakyatawa, kamar ance ya kai dubansa benue market, ya na kai dubansa benue marker yayi arba da ita tana kokarin, zuba shinkafa a roba,
yana ganinta yaji zuciyarsa ta harba, cikin kankanin lokaci wani kifiya mai dauke da dafin sonta ya soke shi a zuci,
.
Lokaci daya ya tsayar da dariyar da yake, ya tsaya cak yana kallonta,
Tana da matsakaicin tsayi gami da matsakaicin Jiki,farace amma ba sosai ba ta mallaki doguwar fuska mai dauke da kananun idanuwa hade da dogon karan hanci gami da tsukakken baki mai siraran labba wayanda ta rinesu da jan baki,
.
Tana sanye cikin doguwar riga har kasa, ta suturce jikinta da shudin hijabi har kasa,
Zuciyar Aliyu ta tafi ga zara, ya saki baki galala yana kallonta, tun da yake a rayuwarsa babu macen daya taba gani yaji kwatankwacin abun daya ji akan zara kanta, yasha arba da kyawawan mata wayanda suka dare zara kyawu kira da komai amma ko kadan basu taba burgesa ba bare har takai ga yaji yana sonsu,
Lokaci na fari da ya fara jin wani abu akan mata, lokaci na farko daya fada cikin Kogin Soyayya,
Babu abun da ya kara rikitashi sai da lebbanta suka fara motsawa, lokacin datake kokarin mikawa wani yaro canjinsa,
.
Kai tsaye ya nufi wurinta fuskarsa na kallonta idanuwansa kafe a kanta,
"Sarki ina zaka je"
Haidar ya tambaya yana kokarin bin bayansa
Aliyu wanda hankalinsa yayi gaba bai ji abunda haidar ya fada ba ya cigaba da tafiyarsa,
Da gudu haidar ya karisa wurinsa tun kafin ya isa benue market ya kama kafadarsa yace "haba Aliyu na yi maka magana yafi baki uku amma kayi biris dani"
"Yi hakuri aboki wallahi hankalina ne yayi gaba" aliyu ya fadi yana duban haidar
,
Mansir,jibrin da hasan suka kariso wajensu
"Haba malamai muna cikin tafiya kun zo kun tsaya anan alhalin kun san halin da nake ciki"
Mansir ya fada yana kallon Aliyu
Hasan ya kara da fadin "kun fa san dukkanmu yunwa ce ke hajijiya damu, kai aliyu ba dazu kai ta kukan ba'a tashi daga aji wuri ba, to gashi an tashin kuma kunzo kun tsayar damu"
Jibrin kam shiru yayi, fuskarsa babu yabo ba fallasa , ya dafe cikinsa da hannunsa na dama
Haidar ne ya yace da su "kuyi hakuri abokai Aliyu ne yayi kamu shine ya biyo kamun ni kuma na rakosa"
Jibrin yadan yamutsa fuska yace "wani irin kamu kuma"
Haidar yayi murmushi yace "Suruka ya samo mana"
Dukkansu suka zazzare idanuwa suka hada baki wajen cewa "da gaske, wacece"
Shi kansa Aliyu bai san yadda akayi har haidar ya gano sa ba to amma abun da bai sani ba shine alokacin da ya saki baki yake kallonta, haidar na kula da shi, har sanda ya nufi benue market shi yasa haidar ya bishi a baya,
.
Cikin zumudi da rawar jiki jibrin ya matso kusa da Aliyu kai kace ba shi bane dazu yayi lamo dafe da ciki, yace "aboki wace ce ne"
Aliyu yayi murmushi yana mai kallon inda zara'u take Zaune,
Dukkansu suka juya da dubansu izuwa kanta,
"Kai tubarkallah" mansir ya fadi
"Amma kayi dace Aboki" jibrin ya dora
"Shin ka sanar da ita kuwa" Hasan ya fadi
"Ya kamata muje yanzu ka sanar da ita" haidar ya fadi yana kokarin janyo Aliyu, a hankali aliyu ya zame hannunsa daga na haidar yace da su "daga ganinta bakuwa ce don ni ban taba ganin ta a nan ba to amma hakan ba shi zaisa na gagara sanar da ita Ina Son ta ba, amma ba yanzu ba ku bari sai mun zauna mun yi shiri"
.
Tun daga wannan Rana sai ya kasance a kullum Abokan biyar sai sun kaiwa benue market ziyara kuma kai tsaye wajen Zara'u suke tafiya, Aliyu yayi ta cikata da surutai, tun yanayi bata kulashi har dai ta fara Kulashi, tun bata damuwa da shi har takai ta fara damuwa da shi, ganin cewa ta saki jiki sosai da shi sai suka hadu shi da abokansa suka fada mata kudurinsa, sai dai har yau shiru kakeji , babu amsa amma Aliyu ya riga yasan cewa tana sonsa , kunya ne ya hanata furta masa
.
Aranar yau ne Zara'u ta kudurce a ranta zata sanar da Aliyu Amsar tambayarsa, ta kudurce zata kauda kunya ta fadamasa cewa ita ma tana sonsa, a iya saninta duk lokacin da aka tashi daga Aji abokan basa taba wucewa zuwa hostel har sai sun yada zango a beneu market, sun dubata
.
To amma yau sabanin kowanne rana Awa biyu kenan da tashi daga Aji amma bataji duriyan abokan ba, hakan yasa sa'I sa'I take  mikewa tsaye tana leke ko zata hangosu don tana da tabbacin zuwansu
,,


ABOKAI book 1 part 8

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 08
.
Karar fitar harsashi daga bakin bindiga gami da ihun da Oga sadi ya saki shine abun daya Razana sauran yan ta'addan,
.
Cikin zafin nama yan ta'addan suka zare bindigoginsu suka fara yiwa yan sandan dake waje ruwan harsashai,
.
Jami'an yan sandan suka cigaba da sakin wuta ya zamana cewa suna musayar harsashi tsakaninsu da yan ta'addan
.
Shakka babu yan ta'addan sunyi mamaki kan yadda akayi har aka gano suna boye cikin hotel din, cikin bacin ran an harbi shugabansu a kafa, yan ta'addan suka ta sakin wuta ba sararawa
.
A cikin musayar wutar da ake ne wani jibgegen dan sanda ya kwalla ihu ya fadi kasa kafadarsa na hagu na bulbulo da jini
.
Da wuri yan sanda biyu suka kinkimi katon dan sandan da aka harba a gefen kafada su kai waje da shi
Da yan Ta'addan suka tabbatar cewa muddin aka cigaba da wannan gumurzu to nan bada dadewa ba Alburusan bindigoginsu zasu kare a samu nasarar kamasu sabida haka sai jagwa ya zo gindin tagar dakin ya doketa da hannu take gilashin da ke jikin tagar ya tarwatse
.
Ya juya yawa Balbali inkiya da hannu kan cewa su zo su fara fita shi zai ji da yan sandan
Batare da bata lokaci ba Balbali ya nufi tagan dakin wanda ke can kuryar dakin , jagwa ya dawo bakin kofa ya cigaba da sakin harsashai daya harba harsashi daya sai ya dakata yaji ko harsashin tayi nasarar aikata abun da ake bukata
.
Sabanin yaji ihun jami'an tsaron sai de ya sake jin wata karar fitar harsashi ta durfafo dakin hakan tasa yake boyewa a jikin bangon dakin
,
Jagwa,aba yawo da Audu suka durfafi tagar dakin bakin bindigunsu na fuskantar kofar dakin da yake a bude , jira kawai suke wani mai kararrar kwana ya leko,
Kimanin dakiku talatin kenan da lafawar musayar wutar, bakajin karar komai cikin dakin in ka dauke nishin da oga sadi yake,
Yana kwance a kasa ya rakube da jigin bango hannunsa na rike da bindigarsa ya saita bindigar a daidai saitin kofar dakin, kafarsa ta hagu kuwa sai bulbulo da jini take tamkar an yanka Kaza
.
Cikin kankanin lokaci jagwa da Aba yawo suka fice daga dakin ta taga, Audu yai wa balbali inkiya da hannu kan cewar su dau Oga sidi su tafi da shi
.
Audu da balbali suka ciccibi oga sidi sukai sama da shi suka dumfari tagar dakin da zummar su fice da shi toh a lokacinne Al'amarin ya faru, Al'amarin daya yi matukar fusata dan ta'adda Audu, Al'amarin da ya kusan Zauta dan ta'adda Audu,
.
Mataimakin kwamishina kamalu ya jinjina bindigarsa da yadubi wasu yan sanda biyu dake gefen hagunsa yai masu inkiya da hannu
.
Lokaci daya yayi Gungure ya wuce ta gaban kofar dakin fuskarsa da bakin bindigarsa na kallon cikin dakin
.
Abun daya ga yan ta'addan na kokarin yi shi ya sanya cikin sauri ya harba harsashin bindigarsa
,
Audu na na wajen dakin ta taga Balbali yana ta ciki yana kokarin daga Oga sidi Sama ya tsallake tagar , Audu kuma kokari yake ya tallabo kafafuwan Oga sidi ta yadda da zarar ya haure tagar to a hannunsa zai fado
Balbali ya baiwa kofan dakin baya bindigarsa na ajjiye a gefen Tagar , kokarinsa shine oga Sidi ya far ficewa,
,
Karar da Balbali ya kwala gami da karar fitar harsashi shine abun da yayi matukar Razana Audu, balbali ya fadi a kasa Rikica kai kace giwa ce ta fadi, ko shurawa bai yi ba yace ga garin ku nan
.
Audu da oga Sidi sun yi matukar Razana da harbin Balbali da akayi nan take audu ya fara kokarin janyo oga sidi daga cikin dakin
.
Jami'an Yan sandan gaba daya suka kunno kai cikin dakin suna masu sakin wuta,
.
Ganin jami'an tsaro sun kunno kai cikin dakin kuma ya tabbata in har suka shigo dakin zasu iya hallaka sa
"Audu ka sakko mu tafi"
.
"Me kake jirane Audu ka sakko mu tafi"
"Kassako man audu"
"Zasu iya kashe ka muddin sukai arba da kai"
"Ka sakko mu tafi"
Audu ya tsinkayi muryan yan 'uwansa Jagwa,Aba yawo da Taku,
Ya kai dubansa izuwa kasan hotel din ta inda yake jiwo sautin muryoyinsu
.
Ya hango su akan Rufin wani gida, kasan Hotel din kuwa mutane masu yawa suka mamaye suna kallon abun da ke faruwa
.
Bakin bindigar wani dan sanda ne ya leko cikin dakin, ganin haka sai audu ya daga bindigarsa yana kokarin sakin wuta amma sai bindigar tayi Turjiya , ta na kukan rashin Alburusai,
.
Audu yai harbi da bindigar ta bakin kofar dakin lokaci guda yayi tsalle ya rabu da jikin Hotel din yana mai kallon oga Sidi wanda ya tabbata ba makawa zai jami'an tsaro sun kamashi
.
.....
Babban kurskuren da yan sandan suka yi shine da suka dunguma baki dayansu suka afka ma yan ta'addan , izan da sun bar wasu a wajen harabar hotel din da babu makawa sai sun yi Nasarar Kame yan ta'addan
.
Koda Dan ta'adda Audu ya dirgo saman Rufin wani Gida, bai tsaya wata wata ba ya Ruga da gudu ta wani sashe mai karancin mutane
.
********
Hasan,Aliyu,Mansir,Jibrin da haidar suna sanye cikin riga riga mai launin ja da fari dogon hannu da Jar doguwar wando
.
Tafe suke cikin Annashwa da farin ciki
"Sarkin dariya yanzu dai sai ayi kokari a kame dariyar ko" mansir yafadi cikin murmushi yana kallon Aliyu
.
Aliyu wanda ya natsu sosai yadda kasan frofesa za shi wajen wani muhimmin taro yayi murmushi gami da gyara kwalan rigarsa ya sake tsuke zanzaron da yayi sannan yace "in Allah ya yarda"
.
Dukansu suka kyalkyale da dariya,
Kai tsaye suka nufi Kasuwar makarantan wurin da ake saida Abinci da sauran Abubuwan kwalama, dalibai suna kiran wurin da BENUE MARKET,
Kasancewar kasuwar yana kusa da BENUE HOUSE shi yasa aka lakaba masa wannan suna
.
"Aboki kafa yi dacen budurwa sai de..."
Haidar ya fadi yana murmushin tsokana
Mansir ya ce "sai de mai"
Jibrin yayi murmushi yace "sai de ita zahra'un batayi dacen saurayi ba, haba mutun kullin baki a bude wannan wata rana ai sai ka cije ta" ya karisa maganar yana dariya
,
Dukkansu suka dara in ka dauke Aliyu daya sha kunu ya bata rai, hasan ya matso kusa da Aliyu ya dora hannunsa akan kafadar Aliyu yace "Aboki ka rabu da zancensu na soki burutsu nasan ita kanta Zahra'u tana sonka domin kaidin ba karamin kyakkyawa bane, gaka da haiba da cika Ido, "
Aliyu yayi murmushi yace "nagode aboki kai kadaine ke goya ma soyayyata baya kuma da yardan Allah nan da yan lokaci kalilan zata sanar dani cewa tana sona a gabanku yan kushe"
Yafadi yana kallon su haidar
Dariya sosai jibrin yayi kafin yace "tab kace ma kai kake kidinka kuma ka ke rawar ka "
.
"Ai ya sanar da ita sai de har yau shiru kake ji babu amsa" mansir ya fadi yana duban jibrin
"Toh Allah yasa dai ba son maso wani kake ba wanda hausawa suka ce koshin Wahala"
Haidar ya fada
.
Haidar,jibrin da Mansir sukai shewa sai dai ganin Abokan nasu biyu sun bata rai
Yasa jibrin ya dan matso kusa da hasan yace "haba aboki sarkin dariya kada kayi Fushi ni nasan yarinyar tana matukar sonka, kawai dai tsiyace muke maka"
Haidar ya kara da fadin "shin kai baka lura da irin kallon data ke maka bane aduk lokacin daka je Benue market,izan da wata rana zaka lura da irin kallon to tabbas da ka tsinkayi zuzzurfan So na gaskiya Makare a cikin kwayar idanunta"
.
"Irin murmushinn data ke yi ma ya isa hujja domin murmushine dake dauke da sakon Zuciya,aboki muna tare dakai yau sai ta sanar damu matsayinka a Zuciyarta"
Mansir ya fada yana kokarin tallafo habar aliyu wanda ya saki fuska , har zuciya Aliyu yaji dadin maganganun Abokan nasa,
.
Lokaci guda yaji wani kwarin gwiwa ya shigeshi cikin dakewa y ace "maganarku Gaskiya abokai ayau ya kamata nasan matsayina a wurin ta don haka mu je mu same ta"

 


ABOKAI book 1 part 7

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 07
.
Motar yan sanda ce ta faka a gaban tangamemen Hotel din, wanda a saman sa a ka rubuta da manyan haruffa CITY HOTEL,
Daidai kun mutanen dake zazzaune a harabar gaban hotel din da masu sai da kayayyaki duk hankulansu ya koma ga motar yan sandan
.
A.C.P kamalu ya fara fitowa daga motar yana sanye da bakar riga big kwala da damammen wandon jersey . Bindigarsa kirar pistol tana soke a kugunsa cikin kubenta,
.
Yana fitowa wasu kattin yan sanda su biyar suka firfito daga cikin motar sanye da bakaken kaya, sai zazzare idanu suke tamkar za su ci babu
.
A.c.p kamalu yayi mika gami da hamma yayi hamdala kai tsaye ya nufi cikin Hotel din
Daddaikun Mutanen da suka mai da hankali wajen kallon yan sandan sai suka cigaba da sha'aninsu don inda sabo sun saba da ganin yan sanda a hotel din, sai de abin da ya daure masu kai shine ganin mataimakin kwamishina na yan sandan Garin Kano da kansa, wanda kusan kowa a garin kano ya sansa saboda yana yin aikinsa cikin Gaskiya,amana da adalci,
.
*********
Tsattsaikan daki ne mai matsakaicin tsayi gami da fadi, dakin a kawace yake da kayan kawa,
Jibga-jibgan karti ne su biyar a cikin dakin ko wannensu na rike da karar Sigari a hannunsa
.
Daya daga cikin kartin ya kai sigarin cikin bakinsa ya zuka sannan ya cire ya buso hayaki ta baki da hanci,
Yace da sauran "dafatan dukkaninku kuna cikin shiri akan aikinmu na gaba"
,
"Kada ka damu Oga Sidi dukkan mu a shirye muke "
Wani kato dake can zaune akan Gado ya fada yana mai zazzare idanuwa
Katon da aka kira da oga Sidi wanda da gani shine shugabansu yana sanye da jibgegiyar shudin rigar sanyi gami da bakar wando fela, ya sake zukar sigarin a karo na biyu ya buso hayaki ya jijjiga kai yace "abin dana ke so da ku shine kai AUDU " ya dubi katon dake zaune kan gado
"Zaka je BENUE ka taho da yaran mu na can, kai kuma JAGWA" ya karkatar da dubansa izuwa kan wani kato mai sanye da hula hana salla ya na zaune akan dan karamin firji,
"Zaka je IKEJA ka taho da yaran mu na can, sai kai BALBALI" ya karkato da dubansa izuwa kan wani garjejen kato dake tsaye jikin bangon dakin ya tokare kafarsa daya da bangon dakin yayin da dayan kafar tasa ke damfare a kas
"Zaka nufi TUNGA cikin jihar Nasarawa dakwai wani yarona mai suna TAKU ku taho tare da shi daga nan sai dukkanmu mu hadu a maboyarmu ta Kaduna, don harinmu na gaba shine babban Bankin Nigeria dake Abuja wato CENTRAL BANK OF NIGERIA, "
Ya dakata ya zuki sigari ya fesar da hayaki sannan yaci gaba,
"ABA YAWO "
"Na'am Oga Sidi" wani kato dake kusa da Oga Sidi ya fadi cikin garjejiyar muryarsa
"Kai zaka tsaya tare dani don zamu kai wa Malam ziyara , saboda neman sa'a, kasaan cewa babban aikine a gaban mu dole muna bukatar a nema mana Sa'a "
.
"Hakan yake Oga kuma sai munyi nasara a wannan aiki namu"
Balbali ya fadi lokacin daya fesar da hayaki daga bakinsa
*********
A.c.p kamalu ya shigo cikin hotel din kai tsaye ya nufi wani ma'aikacin hotel din mai kula da Dakunan Baki,
"a.c.p kamalu ma'aikacin dan sanda " yafada yana nuna wa ma'aikacin hotel din I.D card na sa,
"Yalla bai, me za mu taimaka da" ma'aikacin hotel din ya bukata cikin tsoro
"Nasan cewa kana da labarin wasu yan ta'adda wayanda suka fitini Al'ummar Nigeriya"
Mataimakin kwamishina kamalu ya fadi yana wasa da yan yatsunsa
.
Lokaci daya fuskar ma'aikacin hotel din ta sake birkicewa cikin in ina yace "yallabai badai yan ta'addan nan da suka kashe Gwamnan jihar Nasarawa ba, yan ta'addan da sukayi garkuwa da shugaban yan kwadagon Nigeriya"
.
"Eh sune" A.c.p kamalu ya bashi amsa cikin yanayi na ko'in kula
"Inna lillahi wa'inna ilaihirra ji'uun, wallahi yallabai ban san su ba bani da gami da su yallabai"
Ma'aikacin hotel din wanda ya gama birkicewa ya fadi cikin wata irin murya
.
"Ai ba cewa nayi ka sansu ba ko kana da gami da su, na samu rahoton cewa wasu daga cikinsu suna fake a cikin hotel din nan hakan yasa na debo jami'an tsaro don na kamasu"
.
"Alhamdulillah yallabai har naji sanyi cikin raina"
.
"Amma duk da haka dakwai aiki daya da zaka yi mun"
.
"Wani aiki kenan yallabai " matsoracin mutumin ya fadi yana duban a.c.p kamalu
************
"Oga Sidi bamu tabayin aiki mai kwari wanda ya laso kudade ba kamar na kashe gwamnan jihar Nasarawa har miliyan,Dari fa yallabai ya biya mu"
.
Jagwa ya fadi yana duban aba yawo
Oga sidi yayi wani abu wadda a zatonsa murmushi yayi "kada ku damu yara, kudaden da zzamu samu a aikinmu na gaba sai ya ninka wanda muka samu a kisan gwamnan jihar Nasarawa sau Goma"
.
Balbali ya dubi Oga sidi yace "kace babbar bankin Najeriya zamu kai wa hari shin ya zamuyi da jami'an tsaron dake ciki da waje na bankin"
.
Koda oga sidi yaji haka sai ya bushe da dariya mara dadin sauraro yadau sakanni ashirin yana dariyar kafin daga baya ya tsuke bakinsa sannan ya daure fuskarsa tamau tamkar ba dazu ya gama tikar dariya ba
"Balbali da halama har yanzu dakwai sauranka cikin wannan aiki namu, shin tsoro kake ji ko me, Jami'an tsaro me akayi akai jami'an tsaro da har zasu sanya mu fasa aikin da muka sa agaba, ya akayi har muka kashe gwamnan jihar Nasarawa Alhaji sagir mai duka, cikin jami'an sa muka kashe shi, shugaban yan kwadagon najeriya shima cikin jami'an tsaron muka sace shi kuma muka karbi kudin fansa har milyan saba'in a kansa, yaron ministan kudi na najeriya cikin makarantan Sojoji N D A muka saceshi.
Shine har iyau kake fadamani wasu jami'an tsaro,
Ni SIDI kashe babba kashe yaro, bana tsoron jami'an tsaro kuma a gabanka ganin idanunka zamuje har bankin , na kashe jami'an tsaron mu debe kudade mu yi tafiyarmu"
.
"Hakan take Oga sidi wannan Gaskiya ce"
Balbali yafadi yana feso hayaki
.
Suna cikin hirar ne sukaji ana kwankwasa masu kofa cikin sauri dukkansu suka zare bindigoginsu daga kugunsu suka daga bindigogin sama lokaci daya duk suka dawo jikin bangon da kofar dakin ke manne a jiki suka tsatstsaya cikin shirin kota kwana.
.
Oga sidi ya dubi abokan ta'addancinsa yace da su cikin kankanuwar murya "cool down Gayu bazan duba ko waye"
.
Suka gyada kawunansu
"Waye wannan" oga sidi ya bukata
"Yallabai ma'aikacin hotel din ne"
Matsoracin mutumin ya fadi jikinsa na kyarma
Ya dubi bayansa inda tarin jami'an tsaro suka zagayeshi , abin ya daure masa kai ainun ganin har da masu goge-goge a hotel din da masu kula da fulawowi da masu kai abinci cikin jami'an tsaron suma kuma suna rike da bindiga kirar pistol a hannunsu sun saita bakin bindigar yana kallon kofar dakin,
Jira kawai suke mai tsatstsauyi ya bude kofar
.
"Me ya faru "
Oga sidi ya fadi yana saukar da bindigarsa kas
"Kwanu kan da kuka ci abincine na zo kwashewa"
"Ok " oga sidi ya fadi lokaci daya ya na kokarin bude kofar dakin,,,,,,
Shakka babu da dan ta'adda SIDI KASHE BABBA KASHE YARO yasan abun da zai biyo bayan bude kofar , da bai yadda yayi gangancin bude  wa
.
Gaba dayan yan ta'addan suka sauke bindigoginsu suka soke a gefen kugunsu,
**=**


ABOKAI book 1 part 6

ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 06
.
.
Sati bata zagayo ba sai da Aliyu,Hasan,Mansir,Haidar da Jibrin sai da suka hawa jirgin Abokai daga Abokai suka wuce jirgin Aminai daga wannan jirgin suka zamto Yan'uwan Juna
ABOKAI BIYAR ko YAN UWA BIYAR
..........
Motace kirar Hilux ke ta dirgar gudu a tsakiyar titin, babu abunda zai baiwa mutun mamaki face ganin yadda motoci ke mammatsawa suna baiwa Motar hanya,
.
Ba abun mamaki bane izan akayi la'akari da jiniyar dake tashi daga cikin motar da kuma Rubutun dake jikin motar,
.
Hilux din ta faka a gaban babban ofishin yan sanda na jihar Kano,
Kofar motar ta bude wani bakin mutumi yana sanye da koren riga T shirt da shudin wandon jeans, kafafuwansa na boye cikin takalmi sau ciki,
Dogon mutumin mai kirar kattai ya nufi cikin ofishin,
.
Faffadan ofishi ne wanda aka kawata shi ainun da kayan kawa, ma'aikatan yan sanda ne rututu cikin ofishin suna sanye da bakaken uniform sai kai da komowa da shiga da fice suke wasu kuwa na zazzaune akan kujera suna rubutu,
Wasu suna cikin magarkama suna jibgar masu Laifi,
.
Da shigar bakin mutumin cikin Ofishin sai gaba dayan yan sandan masu sanye da bakaken kaya suka mike tsaye suka Sarawa bakin mutumin,
.
Bakin mutumin ya yi wani abu wanda shi a zaton sa murmushi yayi, ya nufi wani sashe na ofishin
Wani tsamurarren dan sanda ya biyoshi yana ce masa "Yallabai"
Bakin mutumin ya juya ya dubi tsamurarren dan sandan dake gabansa wanda ko tantama babu ba wata abun kirki yake tsinanawa ba cikin aikin yan sandan
.
Kai tsaye bakin mutumin yakai hannunsa ga gaban rigar tsamurarren dan sandan inda sunan shi ke rubuce ,
"Kwastabul sabi'u,"
Bakin mutumin ya fada da garjejiyar muryarsa mai kama da sautin bajimin sa yana kallon tsamurarren dan sandan dake gabansa sannan yaci gaba
"Sunan kenan"
"Eh yallabai"
"Kamar naji ka kirani dazu" bakin mutumin ya tambaya cikin kokonto yana jujjuya dan yatsansa atsakiyar kansa
.
"Eh yallabai dama kwamishina ne yace da zarar kazo na fada maka yana neman ka a ofishinsa" kwastabul sabi'u ya fada yana kokarin gyara zaman wularsa dake barazanar subucewa ta fadi kasa daga kan katuwar kansa
.
"Ok " bakin mutumin yafadi lokaci daya ya juya ya nufi wani sashi na ofishin
*******
"Haba A.C.P Kamalu kada ka bamu kunya ba mana, kasan cewa ta'addancin mutanen nan yayi yawa ya kamata ace an dakatar da su, yanzu na gama waya da shugaban kasa ya bamu umarnin duk sadda muka gano maboyarsu, to muyi kokari mu sanar wa da rundunan sojoji don su kamasu, amma ni sam bana bukatar sojoji su shigo cikin kes din shi yasa kaga na kiraka domin kusan yadda zakuyi gobe ku kamo mutanen nan"
Dan guntun mutumin ya dasa aya yana mai duban bakin mutumin dake gabansa
.
Guntun mutumin wanda bazai wuce shekaru hamsin ba 50 yana zaune a kan kujera sanye da shudin uniform na yan sanda,
.
Yana da wadataccen hasken fata , fuskarsa a kewaye take yana da dakwa-dakwan idanu, ya mallaki dogon wawakeken hancin mai kama da kofan gari gami da madaidaicin baki,
Mulmulallen kansa dake dauke da daidaikun fararen gashi shine ya bayyana asirin Saikon da ya kusan zaftare rabin kan, guntun mutumin mai tarin gashin Kasumba da gemu yana zaune akan kujera ga Tangamemen Teburin katako a gabansa , takaddu ne da files burjik a saman teburin katakon, sai wani karamin Allon katako mai dauke da sunan guntun mutumin, cikin manya da kananun haruffa aka rubuta Abdullahi makeri dorayi COMMISSIONER OF POLICE Allon katakon yana fuskantar gefen kujeran da bakin mutumi mai sanye da koren riga da shudin jeans ke zaune
.
Bakin mutumin da aka kira da kamalu yace "yallabai da yardar Allah gobe tamkar yan ta'addan nan sun shigo hannu ne saboda dakwai yan leken asiri dana tura suka gano mani maboyarsu , jira kawai nake Allah ya kaimu gobe rai da lafiya mu shigan masu"
.
Kwamishina abdullahi yayi murmushi wacce duk da ya dan tsufa amma sai da ta fidda kyawun fuskarsa yace "yauwa kamalu, shi yasa nake jin dadinka don kai baka wasa da aiki kuma duk aikinka sai an samu nasara, shima wannan muna fatan asamu nasarar din"
"Ameen Yallabai" kamalu yafadi
"Ma'aikata nawa zaka diba yayin aiwatar da sumamen" kwamishina Abdullahi ya bukata
"Ina ganin ma'aikata 20 sun yi"
Mataimakin kwamishina kamal u yafadi yayin daya ke kallon kasa
"Ok"
***********ABOKAI book 1 part 5

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 05
.
********
ABOKAI ne kuma AMINAI sun rike abotansu da gaskiya da Amana, ba'a taba jin kansu,
A gaba daya ilahirin makarantar babu ABOKAN da suka rike ABOTA da muhimmanci kamar su,
.
Dalibai,malamai da masu aikatau a makarantan suna matukar jin dadin wannan ABOTA ta su, A kowanne lokaci zaka gansu Tare babu abinda yake Rabasu face shiga bandaki,
.
Suna Rayuwansu cikin farin ciki da Annashwa, in ka gansu sai ka rantse cewa Abotansu ta samo asaline tun daga yarinta, amma maganar gaskiya Makarantan Government College Keffi itace tayi sanadiyar haduwarsu har suka zamto ABOKAI,
.
Arayuwarsu komai daya suke yi, ko aikine aka bai wa daya daga cikinsu toh tare zasu yi aikin,
Basa taba Rabuwa da Wasa da dariya, musamman ma Aliyu wanda ya kasance mai yawan Dariya,
,,,,,,
Haidar daga jihar BENUE yake a karamar hukumar Makurdi iyayensa marasa Karfine, amma suna da rufan Asiri daidai gwargwardo,
Adaddafe da Taimakon Ubangiji Haidar ya kammala makarantar Primary,
.
To saboda hazakarsa da kuma kokarinsa yasa gwamnatin BENUE ta dau nauyin karatunsa na sakandire inda ta turo sa makarantan Maza na kwana, a jihar Nasarawa, karamar hukumar keffi
.
Haidar shi dai baza'a kirashi da Dogon mutum ba hakanan baza a kirashi Guntu ba,
Haka kuma ba'a kirashi da mummuna ba, domin kuwa yana da kyawun fuska daidai gwargwado launinsa launin tarwada ne, ya mallaki dogon fuska mai dauke da dakwa-dakwan idanuwa da dogon karan hanci,gami da karamin bakinsa wanda ya samu mazaunai a kasan Kasumbarsa,
.
Yana son sanya matsastsun kaya hakan ne yake bayyana kirar jikinsa,
Haka nan yana da saurin fushi amma cikin kankanin lokaci yake saukowa
.
Sam baya damuwa da zaman makaranta duk da cewa yanayin makarantan batai masa ba, sannan ga takura da matsin lamba da suke samu daga Siniyoyinsu a lokacinnan yana JSS1,
...............
Jibrin dan jihar KANO ne daga karamar hukumar WARAWA,
Marayane shi, tun tasowarsa har izuwa girmansa bai san wanene mahaifinsa ba, shi dai abun da ya sani shine mahaifiyarsa inna Laure ta sa nar da shi cewa babansa ma'aikacin Soja ne, ya rasa ransa ne a sanadiyar YAKIN MAI TATSINE,
.
Mahaifiyarsa inna laure bata da karfi
Alokacin daya ke Primary tuyan kosai take, da taimakon Allah da taimakon tuyan da take yi take samu take biya mai kudin makaranta, a haka har ya idar da makarantar primary din a daddafe,
.
Daga nan gwamnati ta dau nauyin karatunsa inda ta turasa makarantar maza ta kwana Government college keffi a jihar Nasarawa karamar hukumar keffi,
.
Jibrin dogone , yana da kewayayyiyar fuska mai dauke da guntun karan hanci, da kananun idanuwa, da faffadan baki,
Kyakkyawane don babu yarinyar da zata hada idanu da shi bataji yayi mata ba,
Ya kasance mai yawan son wasa da dariya amma bai cika son magana ba,
.
Dakinsu daya da Haidar kuma Alokacin Aji daya suke don dukkaninsu suna Jss 1
Tun basu saba da junan su ba har suka fara sabawa, daga karshe kuma suka zama ABOKAI
,
............
Mansir Dan jihar Kaduna daga karamar hukumar Jaba
.
Iyayensa masu haline don kuwa sun mallaki tangamemen Gida a angwan G.R.A angwan da sai masu hannu da shuni ne ke samun gurbin zama,
Tun lokacin da mansir yake makarantar firamare yana da hazaka daidai gwargwado , bayan ya idar da makarantar firamare a lokacin dududu baifi shekaru goma sha bakwai ba A duniya 17
,
Arayuwar mansir ya tsani makarantar kwana, (boarding school) tun wani majigi (fim) daya kalla yaga yadda daliban makarantan kwana suke rayuwa sai yaji sam rayuwarsu bai masa ba,
.
Ba karamar ja in ja akayi ba lokacin da mahaifin Mansir Alhaji Tijjani yazo da maganar zai kai Mansir makarantan kwana na Maza acan Nasarawa, kalubale na farko da Alhaji Tijjani ya fara fuskanta cikin Gidansa kenan don kuwa mahaifiyar Mansir hajiya Zulai taja ta kafe kan cewar ita bata yarda adau danta tilo data mallaka Aduniya a kaisa wata can uwa duniya da sunan karatu ba, shima kuma Mansir bai amince ba, sai daga baya Alhaji Tijjani ya lallashi hajiya zulai da maganganu masu taushi inda ya nuna mata dukkan wani abun da ya samu bawa to mukaddari ne daga Allah
.
Mansir kyakkyawa ne fari sol da shi yana matukar kama da mahaifiyarsa hajiya Zulai, fuskarsa a shimfide take yana da yan dara-daran idanuwa gami da dogon karan hanci mai kananan kofofi, da dan karamin baki ma'aboci fararen hakwara, gashin kasumbarsa da gashin gemunsa sune suke kara fidda kyawunsa
.
Mansir ya tsinci kansa a garin keffi cikin Makarantan Government College keffi, alokacin yana Jss 1 ajinsu daya da su haidar da jibrin sai dai hostel na su ba daya bane, haidar su suna Gongola House ne, shi kuma Mansir yana Katsina Ala house,
Akowanne lokaci mansir bashi da aiki sai dai ya sami waje ya zauna yayi ta tunanin Gida aduk lokacin daya fara tunanin gida zakaga hawaye na kwaranya daga idanuwansa
.
Haidar ne yafara kula da yanayin mansir, ya tabbata mansir ya shiga kadaici ne, wannan yasa akullum yake shishshigewa Mansir har suka saba sosai, suka zama ABOKAI UKU, sukan zauna suyi ta hira yadda kewan gida bazai dame su ba
.......
HASSAN dan jihar Nasarawa daga Karamar hukumar KARU
Hasan ya kasance dogone yana da haske amma ba sosai ba , ya mallaki kewayayyiyar fuska ma'abociya murmushi, yana da madaidaitun idanuwa gami da madaidaicin baki.
.
Mahaifinsa Alhaji Tanimu da mahaifiyarsa hajiya Balki suna da 'ya'ya Uku, biyu maza daya mace, A dokan gidansu hasan duk wanda ya idar da karatun firamare, to kai tsaye zai wuce makarantar kwana ne na maza dake KEFFI
.
Alokacin da hasan ya idar da karatun firamare , kai tsaye aka kawo shi Government College Keffi,
.
Hasan ya kasance mutum mai son jama'a amma ba kasafai ya cika son magana ba, yana daukan lokaci kafin kaji ya budi baki yayi magana,
Ya samu mazauni a hostel na KADUNA HOUSE shima Ajin sa daya da su jibrin,mansir da haidar
,
Da shike shi mutun ne mai son mutane Aduk lokacin dayaga su haidar a tare yakanji dadi a ransa ganin yadda suke rayuwa, a hankali ya fara shishshige masu har shima ya zama daya daga cikinsu suka zamto ABOKAI HUDU
...........
SARKIN DARIYA ko ince ALIYU daga Abuja yake iyayensa ba kananan mutane bane,
Aliyu siririne yana da dogayen siraran kafafuwa masu barazanar Karyewa ako wanne lokaci, ga yar fingilalliyar jikinsa wadda jikin wani karamin yaron ma yafita kauri
farine sol yana da faffadan fuska da yan mitsi-mitsin idanuwa gami da tsukakken baki a kowanne lokaci fuskarsa bata rabo da Annashwa
.
Aliyu mutum ne mai son fara'a gami da annashwa shi yasa akowanne lokaci hakwaransa basa Rufuwa, babu abun da yake gundurar mutane da shi sama da dariya, wannan yasa Abokansa da dama ke kiransa da SARKIN DARIYA
.
Mahaifin Aliyu Alhaji Mudi bai samu wata matsala ba ayayin dayayi yunkurin turo Aliyu makarantar kwana,
.
A lokacin da aka sanya Aliyu cikin makarantar maza ta kwana Government College Keffi an sakashi a JSS 1 kuma hostel nasu daya da Hansan don shima a Kaduna house yake
.
Hasan shine wanda aka hada shi da aliyu don ya nuna mai makaranta da kuma dokokinta dariya sosai Aliyu yarunga yi yayin da hasan ke fada masa dokokin makarantar
.
Sati bata zagayo ba sai da Aliyu,Hasan,Mansir,Haidar da Jibrin suka hawa jirgin Abokai daga Abokai suka wuce jirgin Aminai  daga wannan jirgin suka shilla babban jirgin Yan'uwantaka
ABOKAI BIYAR ko YAN UWA BIYAR


Hey, we've just launched a new custom color Blogger template. You'll like it - https://t.co/quGl87I2PZ
Join Our Newsletter