★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 01
.
.
Makarantan secondary ta Government College Keffi makaranta ce mai dadaddan tarihi a Nigeria ,shuwagabanni da dama sun yi karatu a makarantar ,
Asalin makarantar Turawane suka samadda da ita a Kaduna shekaran alif dari tara da arba’in da bakwai 1947
A shekarar Alif dari tara da hamsin da biyar 1955 ne aka matsar da makarantar zuwa Jihar Nasarawa a karaman hukumar Keffi
,
Mutane da dama daga sassan Nigeria suna Turo yayansu makarantar don suyi karatu,
,**********
Haraban makarantar a yalwace take da dogayen bishiyu ma’abota dogayen Rassa da yawan ganyayyaki, shiyasa ako wanne irin yanayi ake ciki makarantar bata rabuwa da daddadan iska ,
Dayawa daga cikin malaman makarantan lokacin da rana tayi sanyi , sukan fito shan daddadan iskar dake yawatawa a cikin makarantar inda suke yin shimfidu karkashin manyan bishiyoyin dake kusa da gidajensu,
Dalibai kuwa wayanda suka kasance siniyoyi a irin wannan daddadan yanayin sukan fitarda da katifunsu waje daidai kofan dakinsu su yi kwanciyarsu
***
Harabar makarantar a cunkushe take da dalibai sakamakon fitowa karin kumallo (break) da akai
Gaba dayan daliban suna sanye da fararen kaya, bambamcin dake tsakanin daliban a bayyane yake, domin kuwa yan JSS 1 zuwa JSS3 suna sanya riga T shirt mai guntun hannu , SS1 zuwa SS2 suna sanya riga T shirt mai Dogon hannu, su kuwa yan SS3 Jampa suke sanyawa.
Wasu matasa ne su biyu suke tafiya, suna sanye da fararen uniform din makarantar, kallo daya zakai masu ka gane yan SS3 ne saboda irin uniform din da ke sanye a jikinsu, daya saurayin yana gaba yayin da dayan yake biye da shi, saurayin dake baya sai magana yake tayiwa saurayin dake gabansa amma yayi banza da shi,
“Haba haidar, wai ba kiranka nake ba ka wani yi banza dani”
“Magana fa nake maka haidar”
Matashin saurayin wanda bazai wuce shekaru ashirin ba ya rugo da gudu ya sha gaban dayan saurayin wanda ya hade fuska
“Haba haidar, tun daga aji (class) nake biye dakai sai magana nake tai maka amma kai shiru”
Fusataccen Saurayin da aka kira da haidar ya dubi matashin dake tsaye a gabansa ya kare masa hanya, yace “kaga malam matsa min na wuce”
“Anki a matsa maka din, sai ka fada mani menai maka dakake hushi da ni” saurayin ya fada
Haidar wanda ransa ya gama baci fuskarsa a turbune yace “Aliyu ka matsan a hanya kafin na kirga biyar, in kuma kaki toh zan maka abun da baka tsammani”
.
Aliyu ya kyalkyale da dariya harda tuma kafa akas da alamu maganar da haidar yayi ce ta sakashi dariya yace “lallaima to ina jiranka duk abun da zakayi kayi, amma bazan taba matsa wa anan ba”
,
Azahirin Gaskiya izan ka dubi Aliyu ka dubi haidar zaka ga cewa kusan Aliyu TARAR ARADU yake, don ko makaho ya shafa jikin Haidar ya kuma shafa na Aliyu zai bambance su,
Aliyu siriri ne fingil da shi, mutane da dama suna yimai kallon yana da cutan sickla , farine sol akullum fuskarsa bata rabo da dariya don shi a rayuwarsa bai iya murmushi ba
Dalibai yan ajinsu har Sara suka sa masa da zarar sun ga hakwaransa sun bude sai su hau tsokanarsa suna ce masa Sarkin dariya, bakinsa baya rufuwa, duk irin tsiyan da zasu yi masa bazai sa ya kulasu ba, kuma bazai fasa dariya ba haka rayuwarsa take Abu kalilan akayi na dariya sai ya kyakyata,
.
Sabanin Haidar wanda ya kasance mai matsakaicin tsayi , kafafuwansa a kafe suke da kasa, jikinsa a mummurde suke duk kayan daya ke sanyawa suna matseshi hakan shike bai wa mutane daman ganin irin kiran jikin da Allah yai masa, doguwan fuskarsa wacce a koyaushe bata rabo da fushi , hade da madaidaitun idanunsa, way’anda sukai ja sakamakon fushin daya ke ciki
“Nace ka matsa ko”
Haidar ya sake fada a karo na biyu cikin sigan Gargadi
“Ni kuma nace bazan matsa ba” Aliyu ya mayar mai cikin tinkaho da yarda dakai
,
Haidar yana cika yana basewa yafara kirge
“Daya, biyu, nace biyu fa ,uku,hudu Hudu fa Aliyu ka matsan a hanya”
,
Babu abun da zai baka mamaki da Aliyu face ganin shi ko a jikinsa tamkar ma bai san Haidar na wani kirge ba,
“Hudu, biyar” haidar na gama kirgen ya daga hannunsa da nufin ya kwarara mai mari sai kuma ya sauke hannun nasa batare da ya mari Aliyu ba
,
Aliyu yayi murmushi yace “menai maka”
Haidar yafara waige waige yana zazzare idanu alamun yana neman wani abun,
Har ya karici waige waigensa idanunsa basuyi nasarar ganin abun da yake nema ba, ya janyo jakan dake rataye a bayansa ya zage zif din jakar,
Ya sanya hannu yana lalubo wani abu
Aliyu kuwa yana tsaye sai murmushi yake tabbas da Aliyu yasan ko me haidar yake nema da tuni ya ari na kare,
Lokaci daya fuskar haidar ta fadada da murmushi ya dago kansa ya dubi Aliyu yana masa murmushi,
“Ko kaifa malam amma dazu ka wani ci magani, sai kumbure kumburen banza kak…..”
Maganar Aliyu ta katse lokacin da idanuwansa suka kai kan BULALAN dake rike a hannun Haidar
Lokaci daya ya hadiyi yawu
“A’a haidar mai kuma zakai da bulala”
Aliyu ya fada yana kokarin ja da baya,
Haidar yayi murmushin mugunta ganin hakansa ta cimma ruwa yace “wani wawa zan zane”
“Amma badai kana nufin ni bako” aliyu ya fada yana murmushin dole,
“Da wa kake son na zane in ba kai ba” haidar ya fada daidai lokacin daya fyado ma Aliyu bulalan duk da cewa Aliyu yayi kokarin kaucewa amma sai da bulalan ta sameshi a hannu , ya tsandara yar karaman ihu ya arta ana kare
,
Haidar ya bishi a guje nan suka kasa tsere,
********
Dogon dakine wanda yafi kama da akirashi da dakin asibiti, an yiwa dakin shudin fenti,
Tun daga tsakiyan dakin har zuwa karshenta manya manyan SIF din katakai ne a jejjere,daga karshen dakin kuwa Gadon karafane guda uku , da katifu akansu,
Samarine su uku a zazzaune akan gadon farko suna hira,
Dukkansu samarin suna sanyene da Fararen Jampa masu guntayen hannuwa, izan da mutum zai lura da kyau zai ga Hatimin makarantar (baje) dore akan karamin aljihun gaban rigan samarin ,
A jikin bajen akwai hoton bakar damisa tana gurnani, a saman hoton an rubuta ‘Government College Keffi’ a kasan hoton an Rubuta ‘Nulla deditio’
,
Daya daga cikin samarin wanda yake barin hagu
Fuskarsa na kallon kasan dakin yace “kunga ya kamata kui tashi mu koma Aji don nasan yanzu haka an fara karatu,”
,
Saurayin dake zaune a tsakiyan samarin ya dubi saurayin dake barin dama yace “kuma fa maganar Hassan gaskiyace , Mansir tashi mu koma aji, kada ‘house captain’ yazo ya same mu a hustel, nasan kai tsaye wajen house master zai kai karanmu”
Mansir yayi hamma tare da yin hamdala, ya mike tsaye yadau jakansa daya ajjiye akan wata katuwar Sif
“Ai sai mu wuce Ajin koh” mansir ya fadi yana kallon sauran samarin
Hassan ne ya fara mikewa ya na dube dube har kasan gadon saida ya duba amma baiyi nasarar samun abunda yake nema ba,
“Jibrin, a’ina ka ajje mana jaka”
Hassan ya tambayi saurayin dake zaune akan katifan
Saurayin da aka kira da jibrin ya mike tsaye yace “muje tana can na barota a Aji”
……………….
Comments
Post a Comment