Main menu

Pages

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 10
.
“Anya Aliyu zai zo kuwa ga shi har Hudu tayi “
Zara’u ce ke fadin hakan cikin zuciyarta, Tun dazu ta idar da Saida Abincinta a iya saninta karfe Hudu, bai taba yi mata a makarantar ba, uku da wani abu take barin makarantar,
Cikin kasala ta mike tsaye ta isa wurin kulolin abin cin ta fara harhada kayayyakin ta, har ta gama har hadawa zuciyanta na muradin ganin Aliyu bata taba jin tana zumudin ganin sa ba irin yau don yau ya kasaance tamkar babbar ranace gareta.
.
Ranar da zata bayyana masa abun da ke kunshe cikin zuciyarta wanda da can kunya ya hanata fadi,
“Ke zara’u me zai hana ki dan tsaya kiyi jiransa zuwa hudu da rabi indai bai zo bane sai ki tafi gobe kwa hadu”
Wani sashi daga cikin zuciyarta ya sanar da ita, lokaci guda tayi na’am da shawarar da barin zuciyartar ta bata, bayan ta gama kikkimtsa kayanta waje guda sai ta koma ta zauna akan dogon bencin dake bayan ta
…..
Kamar daga sama sai zara’u ta jiyo muryan Haidar yana doka ma mutanen wurin sallama cikin barkwanci,
Wata jibgegiyar tsohuwa mai nanannen hanci ne ta amsa sallamar kana tace “a’a abokai yau kam kun makara dan tuni munci kasuwa yanzu haka shirin rufe kasuwar muke”
.
“Ayya yar tsohowa ai muma yau ba Kasuwar mukazo ci ba, wacce muka saba zuwa wajenta tun da can yanzuma wurinta muka zo” Mansir ya fadi cikin barkwanci yana kallon yar tsohuwar
.
Wata bakar mata mai Jiki bazata wuce shekaru talatin ba dake gefe tana Suyan doya ta juyo ta kallesu tace “tab to kun makaro don tuni wacce kuka zo wurintar ta wuce Gida”
“Kenan har yanzu doya bai kare ba, to ma ta ya za’ai ya kare alhalin mai doyar tana ehm ehem ehmmm”
Jibrin yafadi yana murmushi,
“Kai kunga banason shekiyanci dun Allah ku wuce wajenta ga zara’un can tana shirin Tashi”
Bakar matar ta fadi
Dukkansu sukayi dariya suka nufi wurin da zara’u take, inda sabo sun saba a duk lokacin da suka zo benue market sai sunyi barkwanci da matan dake wajen, musamman ma maman Ladi,
.
Wani irin farin ciki take ji mara misaltuwa lokaci daya ta tsinci kanta tana mai murmushi
Su janet dake gefe suna kula da yanayinta suka dan matso kusa da ita janet ta dafa kafadarta tace
“Ga su Aliyun sunzo don nasan su kike jira inba haka ba da tun dazu kin wuce Gida”
.
“Assalamu’alaiki hasken Idaniyata” Aliyu ne ya rangada sallama cikin murya mai sanyi,dadi hade kwantarwa masoyi rai,
Cikin fara’a ta dago kai ta dubesu su Biyar ne kamar yadda ta sansu
Ta amsa sallamar Cikin daddadan murya wadda har tafi na Aliyu dadi,
Janet ce ta mike zumbur ta dubi Aliyu tace
“Ai gwamma da kazo Tun dazu take jiranka, “
“Da gaske kike ” Abokan biyar suka bukata cikin hade baki,
“Hmm. To in ba Aliyu take jira ba wa take jira ita da take tashi karfe uku amma gashi yau har hudu da rabi , to me take jira”
Dayan budurwar tafadi tana kallon zara’u wacce ta ke kallon kasa
Janet tace “barta kawai blessing, aliyu zara’u tana sonka fa kawai dai kunya ce ta hanata………”
.
“Ke yi mana shiru da Allah” zara’u ta katseta da fadin hakan,
Ta mike tsaye ta dubi Aliyu shi da Abokansa tace “Aliyu”
Cikin wata iriyar murya ta kira sunan nasa
“Na’am zara’u”
Ya amsa cikin farinciki da doki na jin abun da zata fadamasa, yasan dai yau dolenta ta kauda kunya gefe guda ta fadi masa abun da ke ranta game da shi
.
Zara’u ta jinjina kai, ta daga kwayar idanunta ta kalli idanun Aliyu wanda yake kafe a kanta
“Aliyu ayau zan kauda kunya na fada maka matsayinka a zuciyata, Aliyu nasan cewa kana matukar sona, kana matukar kishina, ka na Zumudin Ganina,to kasani nima ina Sonka, babu mutumin dana ke zumudin gani sama da kai, a duk lokacin da zan rabu da kai na kanji ba dadi, na kanji dama nayi shekaru dakai kana fada mani dadadan kalamanka, I NA SON KA aliyu”
.
Tsalle Aliyu yayi cikin murna suma abokan nasa suka mara masa baya suka runga ayayyaku wanda suka kirashi da MURNA ko celebration,
Tsirarun dalibai da mata masu saida abinci a benue market sai dariya suke don in da sabo to sun saba da ganin abokan a irin wannan yanayi a duk lokacin da suke farin ciki,,
.
“Maman jona wai me ya samu yarannan haka suke ta tsalle tsalle suna yi wa mutane ihu” mama ladi ta tambayi wata mata kirista dake gefenta tana saida fanke,
“Ba zai wuci akan yarinyar can bace” maman jona ta fadi,
Tsaki maman ladi tayi kana tace “aiko anyi yan iskan yara”

zara’u taji wani sanyi ya ziyarci ranta nan take wani dausayin cakudadden dusar kankara ya tarwatse a zuciyarta sanyi mai ni’ima ya mamaye zuciyar gaba daya,
.
Bayan Abokan sun gama murna da jin furucin daya fito daga bakin zara’u sai suka matso gabanta, suka dubeta mansir ya yi murmushi yace
.
“a gaskiya mun yi farin ciki sosai zara da kika aminta da abokinmu kika dauke shi a matsayin saurayinki da yardar Allah wannan soyayya taku sai ta kaiku ga aure “
.
“Ameen mansir, ki sani cewa dukkan wani damuwa na Aliyu damuwar muce,bakin cikinsa bakin cikin mu ne, hakanan farin cikinsa farin cikin mu ne, daga yanzu kema kin zama wata sashe a cikinmu”
Jibrin ne yafada yana kallon zara’
.
Hassan ya matso kusa yana murmushi ya dubi zara’u yace “zara’ ga Amanar Abokin mu kuma jigon farin cikinmu mai sakamu nishadi a kowanne irin yanayi, Dan Allah ki kula mana da shi kada ki sanya shi kuka, domin izan yayi kuka to muma duka sai munyi kuka”
.
Zara Wacce kanta ke duke yana kallon kasa, tun sa’in da abokan suka fara bayanin ta sadda kanta kas tana jin zantukansu
Ta dago kai a hankali tace “in Allah ya yarda ba zan taba baku kunya ba”
.
Haidar ya dubi sauran abokan nasa yace “sai muyi sauri mu kwashi kulolin nan mu wuce …”
Batare da sun jira ya idar da maganarsa ba suka fara kwashe kuloli da sauran kayan abincin,
.
Zara’u ta mike da sauri tace dasu “da kun barsu don yanzu mai kwashewa zai zo”
.
Haidar yayi murmushi sannan yace “ki dauke mu a matsayin yayunki zara, yayu har hudu baza su iya barin karamar kanwarsu ta kashe kudinta wurin daukan wayannan kananun kayan ba”
Yana gama fadin hakan ya ciccibi wata murgujejiyar kula ya aza a kansa
.
Hasan wanda ya dora yar karamar kula akansa hannunsa na dama na rike da farin roban penti, ya juyo ya dubi zara’u yace “kamar yadda aboki haidar ya fadi, daga yau kin zamo kanwarmu, agabanmu dai ba zaki sake wani aikin wahala ba,”
.
“Naji dadi gami da farin ciki da samun yan uwa hudu, da Masoyi masu jajirtacciyar zuciya ,masu burin su kauda wa kanwarsu da dukkan bakin cikin ta, ina ma da Allah ya halicceni a matsayin kanwa daga cikin dayanku” zara ta fadi cikin murya mai kashe jiki,
Dukkansu jikinsu yayi sanyi, lokaci daya suka fahimci halin da Zara take ciki,
Siraran hawayene suka fara zarya akan kyakkyawar fuskarta ta sanya hannu cikin sauri ta share,
Aliyu ya dubeta yace “Masoyiya meye kuma na kuka ai yanzu duk mun zama daya”
Yafadi cikin sigar wasa,
Mansir ya matso kusa da ita yana kokarin ture Aliyu yace “da Allah ban wuri, tun ba aje ko’ina ba har ka fara sanya mani yar kankanuwar kanwa kuka, yi shiru yar kankanuwar kanwata,ga Alawa nan na kawo maki” ya ciro chaculeti yana mika mata,
Ta mika hannu ta karba tana mai murmushi
“Amma fa kada ki baiwa wannan dan kwadayin dun nasan sai ya nemi ya sha” haidar ya fadi yana kallon Aliyu,
Lokaci na farko da Aliyu ya fara kame
dariya amma duk da haka sai da ya murmusa wadda hakwaransa suka baiyana,
“Masoyiya zaki shanye kuwa ki hanani” Aliyu ya fada yana kallonta da murmushi akan fuskarsa
,
Noke hannu tayi alamun ta hana sannan tace “ai yayana yace kar na baka” cikin muryan yara tayi maganar, hakan ya sanya su duka suka kwashe da dariya har sauran matan benue market masu saida abinci dake gefe suna kallonsu wayanda abun yayi matukar basu sha’awa
Inna mai doya ta bude faffadan bakinta mai kama da kofan gari tace “ja’irar yarinya, ashe itama son Aliyun take”
.
Abokai biyar da budurwa zara suka durfafi gidan su zara’ a haka sukaita hira cikin Annashwa nishadi gamida farin ciki,
Farin ciki a xuciyar zara baya faduwa, ta sam u kanta cikin wani irin yanayi na farin ciki irin wadda bata taba tsintar kanta ciki ba,
*****

Comments

table of contents title