Main menu

Pages

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 11
.
******
Labarin kama dan ta’adda Sidi kashe babba kashe yaro ya karade gaba daya Ilahirin Garin Nigeria da kewayenta, inda gidajen watsa labarai da jaridu gami da kafar sadarwa sukai ta yayata labarin,
.
Dogon dakine da ya tsaru iya tsaruwa , a tsakiyar dakin an girke wani dogon teburi na gilashi daya kusan mamaye dakin,
An zagaye teburin gilashin da wasu kyawawan kujeru masu matukar laushi,
.
Kwamishinan yan sanda Abdullahi makeri ne sanye cikin kayan Gida yana zaune akan daya daga cikin kujerun da sukai wa teburin kawanya fuskarsa na duban wani mutum dake zaune a gefensa
.
Mutumin daya kasance fari yana da kiba ga katuwar tumbi nan daya ajje tamkar mai ciki, yana sanye da fararen kaya zariya ya yafa babbar riga akanta,
,
Lokaci daya farin mutumin da shekarunsa baza su wuce hamsin da wani abu ba ya juya da dubansa ga karshen dogon dakin, cikin sauri shima kwamishinan yan sanda Abdullahi makeri yai duba izuwa karshen dogon dakin inda wani makeken talabijin ke kafe a jikin bangon dakin,
.
Wata kyakkyawar matace cikin shigan hausawa aka nuno cikin talabijin din tana cewa
“A jiya ne talata yan sandan garin kano bisa jagorancin mataimakin kwamishina kamalu suka kai harin sumame ga yan ta’addan nan da suka addabi Nijeriya a wani hotel mai suna city hotel dake karamar hukumar warawa inda sukayi mummunan artabo da yan ta’addan, daga karshe yan sanda sukai nasarar harbin dan ta’adda daya, suka kuma kame shugaban yan ta’addan mai suna SIDI kashe babba kashe yaro,
A tattaunawar da muka yi da Acp kamalu shugaban rundunar da suka kai sumamen ya shaida mana cewa daya daga cikin yan leken asirin da suka barbaza a cikin garin kano ne ya sanar da su maboyar yan ta’addan, basuyi kasa a guiwa ba ya demi jami’ai suka nufi hotel din , Acp kamalu ya kara da cewa jami’I daya ne yaji Rauni a kafadarsa yayin artabonsu da yan ta’addan kuma iyanzu yana nan ana kula da shi a asibiti,
Shi kuma shugaban yan ta’addan yana nan a tsare a wajen yan sanda duka duka dai anan muka kawo maku karshen labaran namu na yau….”
.
Farin mutumin yayi gyaran murya kana ya dubi kwamishina yace “gaisheku jami’an mu, kunyi aiki mai kyau muna alfahari daku”
“Mun gode yallabai” kwamishina ya fadi yana murmushi
“Wani asibiti kuka kai Jami’in da aka harbesa a kafada ,”farin mutumin da aka kira da yallabai ya bukata
“General hospital sir”
.
“Ok, bazan…….”
Maganar tasa ta katse a sakamakon karar ansakuwwar wayarsa data karade dakin,
Farin mutumin ya saka hannu cikin burmemiyar babbar rigarsa ya ciro wayar , kai tsaye ya kara wayar a kunnensa daga can bangaren aka ce
“Assalamu’alaika you’re excellency Abubakar Bappa the governor of kano state “
“Wa’alaikassalam you’re excellency Umar bahaje the President of Nigeria”
Farin mutumin da sai yanzu na fahimci shine Gwamnan kano ya fadi yana murmushi
“Na samu labarin artabun da jami’an mu sukai da yan ta’addan nan , dafatan kun baiwa jami’in da yaji raunin kyakkywan kulawa”
Aka fadi daga can bangaren
“Eh yallabai yanzu haka ma yana cikin koshin lafiya” gwamna Abubakar bappa ya fadi
“Nan da yan wasu kwanaki zan shigo Nijeriya, sannan ina son dan ta’addan da aka kame din nan kulawarsa ta koma hannun Sojoji, saboda gudun mishkila”
.
“Yallabai me zai sa ba zamu barshi a wajen yan sanda ba tunda yanzu haka yana nan suna gana masa azaba iri iri, don ya fadi wani ta’addanci ne suke shirin aiwatarwa nan gaba, sannan su waye ke taimaka masu”
“Ok kuyi duk abun da kuke ganin yafi dacewa, sai anjima ABOKI na”
“Yauwa bahaje sai anjima”
Gwamna Abubakar bappa ya fadi kana ya mayar da wayar cikin aljihunsa fuskarsa cike da murmushi
Ya dubi kwamishina yace “ku cigaba da tsare dan ta’addan, zan neme ka zuwa wani lokacin, menene sunan dan sandan da yaji raunin ma”
“Mudassir,” kwamishina ya basa amsa
Lokaci guda gwamna ya mike tsaye ya gyara burgujejiyar babbar rigarsa “a bashi dubu hamsin hade da hutun tsawon lokaci har sai ya warke”
Ya fada yayin da ya soma tafiya yana dumfarar kofar fita daga dogon dakin
“Ok sir”
*****=========*******
Garin Kaduna,
“Audu yanzu me ya kamata muyi,duk yaran da oga ya bukata na kawo su amma kuma Oga yanzu yana can hannun yan sanda”
Jagwa ya fadi yana kallon Audu wanda Ransa ke matukar bace,
Audu yayi ihu gamida karaji ya daga hannunsa sama ya doki karamin teburin gilashin dake gabansa wanda akai musamman don ajje abinci da abun sha,
.
Karar tarwatsewar teburin gilashin gami da ihun da Audu yayi ne ya sanya mutanen dake Harabar Gidan suka durfafo dakin da su Audu suke cikin Gudu,tafiyar kankanin lokaci ce ta sadasu da dakin gaba dayansu suka zazzaro kananun bindigogi daga kugunsu suka afka cikin dakin,
.
Rundunan Mutanen da akalla sun kai Goma sukai kasake da bindigun a hannunsu sai kalle kalle suke, daya daga cikin mutanen ne yace “yallabai ca muke ko wani abunne ya faru da muka ji ihu da kuma karar fashewar gilashi “
.
“Babu komai ku koma kan bakin aikinku” jagwa ya fadi yana kokarin ciro wani abu cikin aljihunsa
Fakitin sigari ya ciro ya zare kara daya ya kafeta a labbansa, kana ya ciro kyastu ya ya kunna ma sigarin wuta,
“Yanzu me ya kamata muyi don ganin oga ya fito” jagwa ya fadi yana feso hayaki ta hanci ta baki
.
“Abun da nake tunani kenan don kunsan in babu oga to babu ta yadda aikinmu zai yiwu” Aba yawo dake can kuryan bango ya fadi
Audu yayi murmushin kuna sannan yace “tabbas yan sandan Nijeriya sun tsokano wa kansu tsuliyan dodo, sun taro babbar masifar da bata da karshe tun da har suka kama mana shugaba sa’annan suka kashe dan’uwanmu, gobe goben nan mutanen Nijeriya zasu fara yi wa gwamnati bore, domin kuwa a gobe ne mutane zasu farka da mummunan labari wacce zata tayar da hankulansu”
.
“Ban fa fahimci maganar kannan ba, shin me zamu aikata da har zai tayar da hankulan mutanen Nijeriya”
Aba yawo ya fadi yana kokarin matsowa kusa da Audu,
Audu ya fashe da dariyar kyeta yana duban jagwa da aba yawo yace “mummunan Tuggu na shirya wacce zatai silar abubuwa da dama ciki kuwa har da asarar rayuka”
“Wacce iriyar Tuggu kuma” jagwa ya bukata
“GARKUWA, (kidnapping)” audu ya bashi amsa
“Wa zamu yi garkuwa da shi, mr president ko wa,” jagwa ya sake tambayar audu yana zukan guntun sigarin dake hannunsa
“Government College Keffi, daliban makarantan gaba dayansu zamu sace, “
.
“To babban magana, lallai kuwa da babban aiki gabanmu amma kuma kake cewa gobe kasan akalla sai mun shafe sati muna shirya yadda zamuyi mu shiga makarantar”
Aba yawo ya fada
Jagwa yayi murmushi ya yadda guntun ragowar sigarin dake hannunsa akan Tiles din dakin yace “duk bama wannan ba, dakwai makarantu bila’adadin a Nijeriya me yasa ka zabi Government College keffi a cikinsu”
.
Audu ya sake barkewa da dariya wacce tafi kama da kukan jaki a karo na biyu kana yace “gaba daya jihohin Nijeriya talatin da shida , ta hadu ne a makarantar, domin kuwa kowacce jiha tana da dalibi a makarantar”
“Kayi mani gwari gwari kasan ban cika gane hausan nan taka ba” jagwa ya bukata
Audu yayi murmushi sannan yace “ina nufin bawai mutanen jihar nasarawa ne kadai a makarantar ba, akwai dalibai daga sassan nijeriya, wayanda karatu ne ya kawosu garin, kasan makarantar kwana ce”
.
“Ok na fahimce ka sai yanzu na gano abin da ka hango maganar
ka dutse daka ce hankulan mutanen Nijeriya sai ya tashi, to amma izan na dauko maganarka ta farko kace Gobe, kana nufin yau da dare  kenan zamu fita aikin ko kaka”
Jagwa ya fada yana kokarin sake zaro wata sigarin

Comments

table of contents title