Main menu

Pages

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 12
.
“Ok na fahimce ka sai yanzu na gano abin da ka hango maganarka dutse daka ce hankulan mutanen Nijeriya sai ya tashi, to amma izan na dauko maganarka ta farko kace Gobe, kana nufin yau da dare kenan zamu fita aikin ko kaka”
Jagwa ya fada yana kokarin sake zaro wata sigarin
.
Audu ya mike tsaye ya zaro karamar bindigarsa wacce ako wanne lokaci take soke a kugunsa, ya kafa bakin bindigar a lebbansa sannan ya juya akalar bindigar ta kalli bakin kofar dakin,
“Al’umman Nijeriya,Gwamnatin Nijeriya bala’I bisa kanku, Masifa bisa kanku babu mahalukin da zai kareku daga wannan masifar da ta tunkaro ku,” Audu na gama fadin hakan ya fice daga dakin
****** ****
Masoya suka ce Soyayya ruwan zumace kauna ruwan rakece, hakika maganarsu ta tabbata akan Aliyu da zara’u,
Zara’u ta tsinci kanta cikin wawakeken kogin soyayya, inda ta runga ninkaya cikin Annashwa,
Tun daga ranar da zara’u ta furta wa Aliyu kalmar Kauna, suka fara gina soyayyarsu bisa koyarwan Addini, suna kula da junansu sosai, ya kasance kusan kullum Aliyu,haidar,mansir,jibrin da hasan a benue market suke wuni ,
.
Zara’u ta yi farin ciki ainun da samun masoyi mai matukar kaunarta, hade da manyan yayu hudu masu kula da ita,
Tana jin dadin kasancewa cikin su, sabida akowanne lokaci cikin fara’a suke, sukegusar mata da h, sun dauketa tamkar yar’uwarsu ta jini, a da can suna kiran kansu da Abokai biyar, amma yanzu kiran kansu suke da YAN UWA shida,
,
A dan kankanin zaman da zara’u tayi da abokan ta fahimci cewa igiyar abotarsu mai karfice, sannan ta san halayen kowa daga cikinsu, gami da tarihinsu,
Kaman kullum yau ma Abokan ne tare da zara’u a tsaye a bakim gate din makarantar, haidar ya tare acaba guda biyu, ya juyo ya dubi zara’u wacce ta kafe Aliyu da idanu, shima Aliyu idanunsa akan ta suke baya kiftawa,
“Kanwarmu zo ki hau ku tafi, ki bar mayen soyayyar nan,”
Haidar ya fada
Zara’u tayi murmushi ta juyo ta dubi manyan yayyunata tace da su, “nagode sosai yan’uwana, sai gobe izan Allah ya kaimu”
Tana gama fadin hakan ta juya ta nufi wurin da babur din yake har ta kai wurin sai ta tsaya ta, ko ba’a fada mata ba tasan idanuwan Aliyu akanta suke
Zara’u ta juyo ta fara takawa a hankali har ta karisa wurin abokan mansir ne yace “me ya faru kuma kika da wo ko kinyi mantuwane a benue market naje na dauko maki”
“Magana zan da sahibina”
Zara’u ta fadi tana kallon Aliyu
Cikim zumudi Aliyu ya kariso gabanta murmushi dauke akan fuskarsa,
“Dama so nake na fadamaka, gobe zan yi maka babbar kyauta, wacce baka taba tsammani ba,”
Zara’u ta fadi tana wasa da yatsunta , Aliyu yayi murmushi har fararen hakwaransa suka bayyana yace “kice gobe nayi kyakkyawar tanaji kenan,”
Ta gyada masa kai , jibrin ya kariso wajen yace “to sarkin masoya ai kabarta ta tafi gida ko, ko so kake ai wa kanwarmu fada a gida”
“To zara’u sai goben in Allah ya kaimu” aliyu ya fada,
Jibrin,haidar,hasan da mansir suka hada baki lokaci daya suka ce “to Allah ya kiyaye hanya yar karamar kanwarmu,”
“Ameeen” ta fadi daga nan ta hau babur din . Mai babur din daya gaji da tsayuwa ya tayar sannan ya bashi wuta, shi ma dayan mai babur din daya lodi, kulunan abincin ya bisu a baya.
*********
Irin zunzurutun Zumudin zuwan gobe da Aliyu yake bata faduwa, ya gagara sukuni Allah Allah yake gobe tayi don yaga irin kyautar da masoyiyar tasa zata bashi,
.
Babu mutumin da zai arba da Aliyu a wannan rana bai fahimci cewa yana cikin farin ciki ba, A ranar rawa ya runga yi gami da tsalle,
Ya addabi sauran abokan nasa da surutu yana fadin “kai soyayya da dadi abokai ya kamata kuma ku fara ko don ku dandani irin dadin dake cikinta wanda ya dare Zuma dadi”
” duk wanda baya soyayya bakaramin kwaransa akai ba”
“Masoyiyata ina jiranki, ina fa sonki, jinin jikina nakine masoyiyata, jinin jikinki nawane masoyiyata, sonki yai mani kamu a zuciyata, ya ratsa cikin jini da bargon jikina,”
.
“Ka ga Aliyu don Allah kai mana shiru muyi barci mana, ka duba agogo ka gani yanzu karfe Goman dare ne fa, amma duk kabi ka damemu da waka, in da gaske begen masoyiyarkan kake me yasa baka bita gidansu ba” Jibrin ya fadi yana gyara kwanciyarsa
“To naji nayi shiru, amma fa ni bazan iya barci ba,” Aliyu ya bashi amsa
Jibrin yayi tsaki ya dubi haidar,mansir da hasan wayanda sukai nisa cikin bacci yace
“Can ta matse maka mudai kam munyi Zaria”
……..
Abokai da yan uwa ku gafarceni, littafi na daya ya kare a nan,
Shin yan ta’addan zasu sami nasarar cika kudirinsu
.
Yaya alakar Abokan zai kasance daga karshe,
Wani kyauta zara’u ke kokarin baiwa Aliyu
*
Ni Marubucin littafin SHURAIH USMAN nace sai mu tara a littafi n a biyu don jin cigaban wanga labari a wani loton
.

Comments

table of contents title