Main menu

Pages

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 02
.
Samarin su uku suka nufi kofan dakin , suna tafiya cikin nutsuwa , kusan wani abun da zai baka mamaki shine tsayin samarin daya, hakanan ma yadda suke tafiya daya,
Gajeruwan tafiyace ta kaisu zuwa kofan dakin, mansir ya kama mabudin kofan da nufin ya bude, amma sai ya fasa sakamakon Karar kararrawa da yaji,
Ya juya ya dubi hassan dake gefen damansa yace
“Yanzu lokaci babu wuya, sai kace ba yanzu-yanzu muka kora yara zuwa Aji ba”
.
Jibrin wanda yaji dadin saurin fitowa break din da akai yana murmushi yace “ai yanzu-yanzu sai Allah, kana ina yanzu zaku hadu da mutum amma kafin faduwar Rana kaji labarin Rasuwarsa “
“Allah ya kyauta” hassan yafada lokacin da ya juya ya nufi Gadajen karafan dake dakin, yana isowa wajen gadon farko yai kwanciyarsa
.
Dukkansu suka zo sukai kwanciyarsu akan katifun dakin,
Jibirin yayi hamdala daidai lokacin daya yi mika,
Yace “ba karamin dadi naji ba da aka fito break dinnan da wuri” yayi maganar yana kallon mansir
,
Mansir yace “ai dole kaji dadi tunda baka son haduwa da Haidar, wata kila iyanzu haka ma ya yi ram da Aliyu”
,
Hassan ya yi ajiyar zuciya yace “tab kace Rakumi zata tatsiye kaza kenen, wannan Siririn mai kama da fallen takarda in ya shiga hannun Haidar, ai sai haidar ya karairayasa”
Dukkansu suka kwashe da dariya sakamakon jin maganar da hassan yayi,
.
“fadama batawa nasan yadda haidar ya fusata din nan ko da mu ya hadu sai ya sauke fushinsa akanmu, saboda irin izgilin da mukai masa, “
Mansir ya fada ,
Hassan ya sake yin murmushi yace “shi kuma Sarkin dariya ya sake tunzura shi, dama ina lafiyan kura bare ma tayi hauka, yanzu haka nasan haidar yana can a cike yai fam, kawai fashewa yake jira kuma ajikinmu zai fashe”
.
Jibrin wanda yafara lumshe idanuwansa alamun yana jin barci ya mike zaune ya dubi hassan yace “to tsoransa muke ji da har kake wani cewa wai ajikinnmu zai fashe, sai kace wasu jakuna, sai yazo ya hau jibgarmu mukuma mu tsaya muna kallonsa”
.
Mansir ya juya ga dubansa izuwa gefen jibrin yace “kaji cika baki sai kace wata uwar zaka tsinana izan ya tarfa ka,”
.
Jibrin ya mayarmasa “nasan cewa ni daya dai bazan iya taransa ba amma izan muka taru mu hudu ai zamu sa shi yayi laushi ka manta hausawa sukace sarkin yawa yafi sarkin karfi”
.
suka cigaba da hirarsu cikin nishadi suna darawa aduk lokacin da wani daga cikinsu ya fadi wani abun dariya.
.
Suna cikin hirar ne kwatsam sai suka ji karar banke kofan dakin da akai, da shike kofan na karfene sai ya bada wata irin sauti mai cika kunne
.
Aliyu ne ya shigo da gudunsa kai tsaye ya nufi wajen jibrin dayake zaune kan katifa
.
Lokaci daya hassan,mansir da jibrin suka hau tambayarsa ko me ke faruwa,
Aliyu wanda ya gagara magana sakamakon nishin dayake yi Fuskarsa a jike sharkaf da gumi , duk bayan dakika biyu sai yaja dogon nishi, fuskarsa na kallon kofan dakin
.
“Wai meke faruwa ne Aliyu ka shigo mana daki a hargitse sai uban nishi kake tamkar wanda ya zagaye duniya a kas”
Mansir ne ya fadi haka cikin alamun bacin rai
.
“kai ba tambayarka ake ba kayi shiru” jibrin ya fada yana girgiza kafadun Aliyu
Haryanzu Aliyu bai daina jawo da saukar da numfashi ba,
Hassan ya fuskanci dakwai abun daya taso Aliyu a guje, tunda gashi haryanzu idanuwansa nakan kofar dakin
.
Jibrin ya mike ya dube su yace “ina jin wani abun ne ya biyoshi bazan je na dubo naga ko menene”
Batare daya jira jin amsar da zasu basa ba ya tunkari kofan dakin
Da zuwansa bakin kofar sai ya leka waje, ya gama dube dubensa bai ga komai ba ya juyo yace da su jibrin ” abokai nifa banga komai ba, to wai kai SARKIN DARIYA mai ya tsoratar dakai haka, “
,
Mansir yayi tsaki yace “kun san sa da shegen tsokana kila ma wani ya tsokano ya biyosa”
.
Shi dai Aliyu jinsu kawai yake yaki yayi magana duk da cewa yanzu ya daina numfarfashin dayake,
.
Abun daya sa yaki fada masu ko waye ya biyosa yasan daya fada masu zasu gudu, daga karshe kuma haidar shi zai kama, Alhalin sune suka tsokanesa suka sanya yaji kunya cikin Aji, kuma ace sun gudu, so yake Haidar ya ritsasu cikin dakin,
.
Har Jibrin ya juyo da nufin ya dawo wajensu mansir sai idanuwansa suka dauko masa hoton abin da ya firgita shi, lokaci daya fuskarsa ta canja,
Haidar ya gani yana dumfaro dakin fuskarsa a murtuke babu alamun fara’a, sannan ga wata murtukekiyar bulala a hannunsa
,
Ba Haidar yake tsoro ba, murtukekiyar bulalar dake rike a hannun haidar itace abun da ta sanya lokaci daya ya rude,
.
A rayuwar jibrin babu abun da yake matukar jin tsoransa kamar bulala, a zamanin da suke juniyoyi a makarantar, izan siniyoyinsu su kazo bulala tun kafin su zo kansa zakaga ya fara hawaye, yana jimamin irin bulalar da zai sha
,
Har wayau da su ka zama siniyoyi,jibrin ya tsani yaga wani dalibi da bulala, ko yaga a na dukan wasu daliban, hakan ba karamin bata mai rai yakke ba musamman ma yaga siniyoyi su na dukan karamin yaro wanda baifi shekaru goma sha biyu 12 ba a duniya
,
Koda jibrin yaga haidar ya kusan karasowa sai ya kulle kofan dakin, cikin sauri ya zura sakatar kofar sannan ya jingina a jikin kofan yana mai sauke ajiyan zuciya
.
Mansir da hassan suka mike tsaye suka dumfari inda jibrin yake bakunansu cike da tambayoyi,
.
“Mai yake faruwa ne jibrin? Me ne ne wannan da har ya tsorataka”
Hassan ya tambaya yana duban razananniyar fuskar jibrin tamkar yana jiran ace kyat ya ruga
.
Mansir ya dafa kafadan jibrin yace “kana yiwa Allah ka fada mana me ka gani “
,
Haidar ya kariso bakin kofan dakin saide cikin rashin sa’a sai ya taras da kofan a rufe, ko tantama ba yayi yasan jibrin ne ya kulle, yayi murmushi azuciyar sa yace “wannan da tsoron Bulala”
.
,haidar na tsaye a bakin kofan dakin yana tunanin ta yadda zai yi ya shiga cikin dakin, ya dau a kalla mintuna biyar yana tunani sai kai da komowa yake , daga kofan dakin zuwa dayan kofan dakin,
,
“Ina kwana Siniyo Haidar”
“Ina kwana siniyo haidar”
Haidar wanda yayi nisa cikin tunani kwatsam sai tsinkayar wayannan muryoyin yay
i cikin kunnuwansa,
Ya kai dubansa ta inda muryoyin suka fito,
Kananan Yara ne masu karancin shekaru, suna tsaye a gaban haidar cikin fararen riga (t shirt) guntun hannu, da farin wando,
“Sagir,khabab ya kuke”
Haidar ya fada cikin fara’a yana mai shafa kan dayan yaron
.
“Lafiya siniyo” dukkansu suka hada baki suka fadi
“Zakuje ku yi break kenan ko”
“Eh”
“Toh Allah ya taimaka bazan koma Aji, sai ku kwankwasa kofan suna ta ciki, za su bude maku” haidar ya fada lokacin daya bi wani lungu maimakon yabi hanyar komawa Aji.
**
Duk abin da ke faruwa tsakanin haidar da su sagir, da tattaunawansu duk su jibrin suna saurara, da suka tabbata ya tafi sai jibrin ya bude kofan yana mai dube dube da waige waige koda zaiga haidar amma baiga kowaba sai khabab da sagir a bakin kofan dakin da kuma wasu tsirarun dalibai da suka dawo break da wuri,
.
Tun da ya bude kofan khabab da sagir suke gaishesa amma sam hankalinsa ba akansu yake ba, shi yasa bai amsa gaisuwar ba, suma ganin haka yasa suka shige cikin dakin.
.
Mansir ya dafa kafadarsa yace “jibrin wai tsoron me kake ji, Haidar ko me? Ka bar kofan a bude kazo mu koma ka kwanta kasan yanzu break yara da dama zasu ta dawowa daki don kari,”
.
Toh kawai ya iya cewa, fuskarsa sai tsatstsafo da gumi take yana sharewa ,
.
Suka koma suka zazzauna akan gadajen dake cikin dakin,
Lokacinne dalibai sukai ta shigowa dakin, wasu da riguna dogayen hannu wasu kuma da riguna guntayen hannu, da zarar sun shigo sai su kwashi gaisuwa wajen siniyoyinsu sannan su nufi wajen Sif (locker) dinsu , da dama daga cikin daliban suna daukan kofi ne su fice daga dakin zuwa DINING inda ake raba akamu, waasu kuwa marasa ra’ayin tafiya DINNING sai su jiga kwaki su sha su koma aji.
*****
“Ai na fada maku duk ku kwantar da hankalinku haidar yau ba zai dawo break ba, tun da gashi har an koma bai dawo ba”
.
Mansir yafada lokacin dayake duban Aliyu da jibrin
Jibrin wanda ya tsorata ainun kallo daya zakai masa ka tabbatar ya gama tsorata, yace “ni duk matsalata bawai zuwansa break bane, nasan duk wani boye boyenmu ayau sai munn hadu da shi,kada fa ku manta cikin dakinnan yake kwana tare damu,cikin dakinnan sif (locker) dinsa yake tamkar yadda namu suke, to tayaya zamu iya tsere masa,”
.
“Toh me cece matsalarka” Aliyu ya tambaya fuskarsa a sake yanzu kam duk wani tsoro ya kau daga fuskarsa,
.
Jibrin ya sauke ajiyan zuciya yace “wannan bulalar dake hannunsa, ta yayane zamu karbi bulalar nan,”
Aliyu ya kyalkyale da dariya har da tuma kafa akas, yana dariyan yana nuna jibrin da hannu
.
Mansir ma murmushi yayi don shi kansa jibrin ya ba shi dariya, to amma bazai iya dariyan ba gudun bacin ran jibrin.
.
Jibrin ya kufula sanadiyar dariyan da Aliyu yake mai yace “to meye abin dariya anan”
“Babu “aliyu ya fada lokacin daya fara sassauta dariyan nasa
.
“Mts, wai dan Allah na tambayeku? Me ke jikin haidar ne da har kuke tsoransa haka, kunga yau wallahi komu ko shi, haba kunzo sai wani shawari kuke akan mutun daya, don Allah ku tashi mu koma aji,”
Hassan wanda ya kishingide kan gado ya fada lokaci daya ya mike tsaye yafara tafiya yana nufan kofan dakin bai karisa bakin kofar ba ya juyo ya dubi abokan nasa wanda suka saki baki suna kallonsa ya sake ce da su “wai ba zaku tashi mu tafi bane ko qaqa, “
.
Cikin mamaki sai hassan yaga yanayin fuskokinsu ya sauya cikin bacin rai ya daka masu tsawa “wai ba zaku taso mu tafi bane, shi haidar din mala’ika ne da kuke tsoransa haka, haba wallahi kun bani kunya, haba sai kace ba mazaje ba yanzu kai mansir a haka kake ikirarin zakaje N.D.A din, ai kosu zasu tsorata bai kamata ace kai ka tsorata ba, yo waima me a kai akayi haidar dinne da kuke tsoransa haka, na tabbata ko cikin magagin bacci nake haidar bai isa ya tareni ba,, dun Allah kada ku bani kunya ku tashi mu tafi”
.
Aliyu wanda tuni ya bushe da dariya jin irin cika bakin da Hassan yake baccin yasan ba uwar da zai iya tsinanawa,
“To meye na dariya kuma, kaide aliyu halinka sai kai, ko an gaya maka kowa matsoraci ne kamanka, abu kaman a kama akarya” hassan yafada
.
Aliyu ya cigaba da kyakyata dariyarsa yana mai nuna wa hassan wani abu a bayansa, “yana cewa duba bayanka”
“Me ye wannan”
Jibrin yayi murmushi yace “kai de duba koma me ne ne ai zaka gani”
Hassan yayi tsaki yace “ku fada mani me ne ne wannan”
.
“Duba dai kaga ni” mansir yafada yana kokarin kunshe dariyar da ta zo masa
.
Cikin bacin rai hassan yace “bazan juya naga ko uwar……”
Maganarsa ta katse daidai lokacin daya juya yaga mutumin dake tsaye abayansa
.
Yana sanye da fararen kaya irin wanda yake jikin sauran samarin, fuskar nan tashi babu alamun fara’a damatsansa sun bunbumtsilo sunyi burda burda, babu abun da zai ba wa dukkan wanda yayi arba da shi tsoro face lafceciyar bulalar data ke hannunsa,
.
Haidar yayi murmushin mugunta sannan ya k ama kofan dakin ya garkame da kwado
.
Ya juyo ya dubesu yace
“Yau zaku basu labari”
.
Nine dai Shuraih Usman
Cikin littafina mai taken ABOKAI

Comments

table of contents title