★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 03
.
Haidar yayi murmushin mugunta sannan ya kama kofan dakin ya garkame da kwado
.
Ya juyo ya dubesu yace
“Yau zaku basu labari”
.
Hassan ya firgita sosai lokacin daya juyo yai arba da haidar a bayansa,
Yana mamakin yaushe har ya shigo cikin dakin da baiji shigowarsa ba,
.
Ya zargi kansa kan irin subul da bakan da yayi na cewa baya tsoron haidar, fatansa dayane Allah yasa baiji maganganunsa na fari ba
.
Koda aliyu,jibrin da mansir su ka ji abun da haidar ya fadi sai dukkaninsu suka mimmike tsaye,
Cikin sigar wasa wasa Aliyu yace “ta faru ta kare wai an yiwa mai dami daya sata, haidar gaka gasu dama sune suka yi maka laifi, ni babu ruwana ba zan ta shi na wuce Aji” yana gama fadin hakan ya fara tafiya yana nufan kofan dakin ,
Yaji mamaki sosai daya zo ya wuce wurin da haidar yake tsaye amma haidar bai masa komai ba, hakan ce tasa ya fara tunanin haidar ya rabu da shi kenan, ya juyo ya dubi Hassan,mansir da jibrin yayi masu gwalo,
Ya kama kofan dakin da zummar ya bude amma sai kofar taki buduwa duka sakatun dake jikin kofan sai da ya cire su amma duk da haka kofan taki buduwa
,
Ya juyo ya dubi haidar yace “a’a haidar me kayiwa kofar ne ta ki buduwa”
,
“Sawa nayi a ka kullemu ta waje” haidar lokaci daya ya saki wata tattausar murmushi wacce ko ba a fada ba kasan na mugunta ce
.
Dukkansu suka zazzaro idanuwa jin abunda haidar ya fada,
Shi kuwa sai ya cigaba da cewa “muddin kuka ga kun fice daga dakin nan a yau to jikinku yayi laushine”
.
Hasan wanda har yanzu yake tsaye a inda yake dazu ya kasa koda motsawa ne ya daddage yace da haidar “haba haidar shin ka manta mu ABOKAI ne,ta yaya zaka yi ka jibgi abokin ka, yo inma zaka jibgemu, ai ni bana cikinsu don ko a lokacin da aka kunyataka cikin Aji dalibai suke dariya, ji nake tamkar nayi kuka saboda abun da akai maka, shakka babu naji haushi ainun na wannan cin fuska da akai maka, dazu dazu na gama yi masu fada kan abun da suka yi maka,
Na nu na masu sam bai dace ba, kuma bai kyautu ace wai mune mu kaiwa abokin mu haka ba,
Amma duk da haka izan kana kan bakanka na sai ka hukuntamu to kaiwa Allah kada ka dukemu da wannan bulalar”
.
Haidar yayi tsaki alamun sam bai gamsu da maganar da hasan ya fada ba ya dubi hasan yace “yi mana shiru, ko an fada maka banji abun da kake fada yanzu bane, to duk maganar ka a kunne na suke sauka, batun wai kada na dukeku da bulalarnan bai taso ba, don kuwa muddin ba da wannan bulalar na dakeku ba to hankalina bazai kwanta ba,”
Ya maida dubansa ga su mansir yacigaba “yanzu abun da nake son sani shine, waye ya kawo shawarar a ci mun fuska cikin Aji, sannan waya shirya, wa kuma ya bada umarni,”
A wannan karon cikin sigar wasa yayi maganar
.
Jibrin ya hadiyi miyau ya nuna mansir da hannu yace “mansir shi ya kawo shawara,muka hadu dukkan mu muka shirya”
.
“Dakyau amma fa kun iya shiri na tabbata da zakuyi wasan kwaikwayo da kun burge, akan wane dalili ABOKAI suka taru suka ci wa ABOKINSU fuska, cikin mutane ana tai masa dariya” haidar ya tambaya yana mai daga zundumemiyar bulalar dake hannunsa sama
.
“Babu,” jibrin ya bashi amsa
“Oh haka kawai don neman a tashi a tsaya, ” haidar ya bukata yanzu kam cikin sigar fara’a yake maganar
“Eh”
“Hausawa sun ce RAMA CUTA GA MACUCI IBADA CE , don haka kuma yanzu jikin ku zaiyi tsami dakyau ta yadda nan gaba ba zaku sake yi mani irin hakan ba”
Yana gama fadin hakan ya nufosu da zabgegiyar bulalansa,
.
Jibrin ya fara damka lokacin jibrin yana bashi hakuri da magiya akan kada ya dakesa, irin yadda jibrin ya takarkare yake magiyan kada haidar ya dukesa sai mutum ya dauka Ransa za’a cire
,
Ko ka dan magiyarsa batai tasiri a jikin haidar ba don kuwa sai da ya tsala masa bulala daya,
Wata iriyar Ihu da jibrin ya kwala, mai amo sai da takai dukkansu sun sanya yatsunsu sun toshe kunnuwansu, sakamakon ji da suke tamkar kunnensu zai dode
.
Ba shiri haidar ya yarda bulalar dake hannunsa a kasa sannan yasa yan yatsunsa ya toshe kunnuwansa, koda jibrin ya kyalla idanuwa yaga haidar ya yarda bulalar hannunsa, sai yayi maza ya dauki bulalar, lokacin da karar ihun nasa ta dauke dif tamkar ruwan sama ya tsaya
.
Haidar ne ya fara cire hannunsa daga kunnensa ya dubi jibrin wanda yake tsaye cikin takama da isa hannunsa na dama na rike da bulala, dayan hannun kuma yana susa baya da ita wajen da haidar ya zabga mai bulalar
.
Cikin isa jibrin yace yana dubansu dukkansu “yauwa yanzu ta zagayo kuma ta juyo kanku”
“Kan mu kuma kamar yaya kenan? Ban gane ba jibrin” aliyu ya tambaya cikin kokanto
.
Jibrin bai ma kula da maganar Aliyu ba sai ya dubi haidar dayake tsaye a gabansa ya daga bulalar sama ya tsala mai a baya,
,
Duk irin kokarin da haidar yayi don ya hadiye ihun dake kokarin zuwa masa yayi amma sai da ihun ta fito sakamakon irin radadin dayaji a bayansa, ya tabbata koda Rodi aka bugesa ba zai ji irin zafinnan ba,
,
Mansir da aliyu suka kyalkyale da dariya suna cewa “yauwa jibrin ai kayi maganinsa, kara masa don Allah”
,
Murmushi jibrin yayi sannan ya juyo ya dubesu cikin fara’a yace “ku yi dariyarku ta karshe a yau, don kuwa nan da minti daya dariyarnan taku zata juye izuwa kuka, “
.
“Wai me kake fadane tun dazu jibrin, sai dunkula magana kake kana jehomu da ita , yi mana gwari gwari yadda zamu fahimta” mansir ya fadi lokacin dayayi shiru ga barin dariyan
,
Har ila yau murmushi jibrin ya sake yi masu yace da su “ku sani cewa ku kanku ba zan barku ba domin daku a ka hada baki musamman ma kai hassan kaine ka yi ta cika baki kana zagin haidar kuma duk ya jika amma daya shigo sai ya hauni da duka, kai kuma mansir dama tun can baya ina kule dakai akan cemun da kake matsoracin Bulala to yau zan gwada ka naga ko kaima kana tsoron bulalarnan ko a’a, kai kuma Aliyu ina mai tabbatar maka daga yau baka sake yin dariya….”
.
Tun kafin ya karisa maganarsa Aliyu ya bushe da dariya yana mai cewa “tab ai kuwa saidai in kashe ne zakayi, amma ni babu abin da zai sa na dena Dariya a duniyar nan”
.
Haidar yana kwance a kas sai murkususu yake yana
susa inda jibrin ya tsala mai bulala,
Jibrin ya nufi su aliyu da zabgegiyar bulala a hannunsa yana mai cewa “ai kuwa yau zaka dandana kudarka aliyu”
.
Aliyu,hassan da mansir sun razana da sukaga jibrin ya nufosu da bulala a hannu domin su sun dauka wasa yake yi musu ba shiri suka hau gudu suna zagaye dakin da jibrin, ana cikin haka ne Aliyu ya shammaci jibrin ya wafce bulalar daga hannunsa,
.
Lokaci daya suka tsaya da guje-gujen da suke, haidar wanda tunda aka fara guje-gujen nan ya mike shima yana cikin yan gudun tserewa bulala don kuwa yasan in ya tsaya jibrin na iya kara zabga mai bulalar ,
.
Mansir da hassan suna murmushi suka kariso wajen Aliyu hasan na cewa dashi “an Gaisheka sarkin dariya yau rana daya dai kayi amfani,”
,
Aliyu ya bushe da dariya har yana hawaye ya dube su dayan bayan daya, tun daga kan haidar har zuwa kan jibrin yace “Takan mai uwa da wabi zanyi? Duk wanda ya tsaya jikinsa ya fada masa”
Yana gama fadin hakan ya dumfari haidar da bulalar a hannu
.
Nan fa aka fara sabon wasan zagaye daki, Aliyu yana dariya yana kai duka duk wanda ya samu nasarar laftawa bulalar sai kaji ya tsandara ihu ya fadi a kasa, amma cikin sauri zai mike ya cigaba da gudun,
.
Ana cikin hakane sai sukaji karar kofan dakin alaman ana kokarin bude kwadon da haidar yasa aka garkame dakin da shi,
Hakan yasa dukkansu suka tsaya kikam tamkar gumaka, cikin Sauri Aliyu ya boye bulalar a karkashin gado,
.
Kofar dakin ta bude hasken rana ya haskaka dakin fau har yana kashewa su haidar ido,
.
Idanunsu gaba daya yana kan kofar dakin don ganin waye wannan ke kokarin shigowa, addu’arsu daya Allah yasa ba malami bane domin indai malamine to sun san cewa yau sun kade domin kuwa wunin yau zasu yi shine dauke da fatanya ko Adda a hannunsu suna yankar ciyawa
.
Bakar Takalmi mai rufi ta fara lekowa cikin dakin a lokaci daya sai gangar jiki mai dauke da bakar takalmin ta bayyana a cikin dakin
,
Bakine amma ba baki kirin ba yana dauke da dan karamin kai , da yan kananun idanuwa, lafceciyar karan hancinsa wanda mutum sai yayi tsammanin dasa ta akayi a fuskar tasa itace ta bayyana muninsa,
Mutumin na sanye ne da riga T shirt mai dogon hannu sai wata zundumemiyar Wando mai barazanar share kasa akowani lokaci
Kallo daya zakai wa mutumin ka iya cankar shekarunsa, akalla bazai wuce shekaru arba’in da takwas 48 zuwa hamsin 50 ba
.
Dogon mutumin wanda kan sa ke barazanar taba silin din dakin yadan yi doro babu gashi ko daya akansa sakamakon kwakwal din da wanzami yayi masa , kannan sai sheki take a duk lokacin da rana ya haskata,
Ya dubesu dukkansu yace cikin gurbatacciyar hausar sa “meye haka library,utility ku da zaku kora yara su bar hostel su wuce clas s amma kune a hostel din”
.
Dukkansu suka yi zuru-zuru da idanuwa suna kallon mummunan dogon malamin,
Comments
Post a Comment