ABOKAI
Shuraih Usman
Part 4
.
Faffadan filine a shimfide,ciyayi dogaye da guntaye sun
cunkushe filin,
In ka dauke gaban filin, babu abinda ciyawa bai mamaye
ba a filin,
.
Suna tsaye daga gaban filin ta inda babu ciyayi, In ka
dauke dogon malamin kowanne acikinsu fuskarsa babu
alamun fara’a
.
Tsololon malamin wanda hasken Rana ya haskake masa
kwal-kwal tana surnano gumi sai walkiya take ya dubi
daliban dake tsaye a gefensa cikin fararen kaya jampa
yace
.
“Ana cikin class ana koyarwa ku kuwa kun kulle kanku
cikin daki a hostel sai wasan banza kuke, “
.
Haidar,Aliyu,mansir,jibrin da hassan suka yi shiru basu ce
komi ba, fuskarsu a turbune , suna ta hararar junansu,
.
Malamin ya dauki dutse a kasa ya yi jifa da ita ta cikin
ciyayin, ya lura sosai da inda dutsen ta fadi, ya dubi
mansir yace mai “utility prefect”
“Sir” mansir ya amsa
“Go and stay in that place where that stone fall” (jeka
daidai inda dutsen nan ya fadi )
“Ok sir” cikin gudu mansir ya nufi wajen da dutsen ya
fadi,
Ba wata tazara ce mai yawa ba tsakanin wurin da su
haidar suke tsaye da wurin da mansir yaje ba
.
“Good tun da ba zaman class din kuke so ba, kun fi son
kuyi ta wasan banza cikin hostel, to gaku ga ciyawa ga
kuma Rana, sai kuyi ta tumbuke ciyayin nan da
hannuwanku har zuwa can wajen da mansir yake tsaye”
Malamin ya fada yana duban su Aliyu
Yacigaba da cewa “did you understand”
“Yes sir ” dukkansu suka amsa mai
***********
“Qur’ani na gaji, tab wannan aiki haka sai kace za a biyani
to kwarankwasa ko biyana za ai na ci kudina, “
Aliyu ne ke fadin hakan lokacin da ya durkushe a kasa,
fuskarsa ya jike sharkab da gumi, ya tube farin rigar dake
jikinsa ya ajjiye a gefe, hakan shi ya tona asirin jikinsa da
akoda yaushe yake boye cikin Riga, gaba daya kasusuwan
jikinsa sun bunbumtsilo,cikin sa a shafe take tamkar na
jarirai
.
“Zaifi maka kyau ka mike mu karisa, dududu ma yaushe
muka fara aikin da har zaka fara yi mana Raki”
Jibrin wanda ya dukufa sai fisgar ciyayin yake yana
tumbukesu daga tushi ya fada,”
,
Aliyu ya juyo ta gefen jibrin yace da shi “to ‘dan mai
noma, aka gaya maka kowa irin kane daya saba da aikin
wahala, ni dai kam na gaji bazan iya cigaba da cire ciyayin
nan ba, haba dubi hannuna kaga yadda bororo ya fito
yanzu yanzu”
Yafada yana kallon hannunsa wanda yayi ja,
.
Haidar,Mansir da hassan sun dukufa sai cisgar ciyayin
suke iya karfinsu, don burinsu shine suyi sauri su iddar
da wannan babban aikin da aka basu kafin dalibai su fito
daga aji,
Don sun san muddin suka bari dalibai suka fito suka
cimmusu suna wannan aikin musamman ma yan ajinsu
toh sun runga yi musu tsiya kenan,
.
Aliyu ya mike tsaye cikin ciyayin ya dauki rigarsa ya sanya
a jikinsa ya juyo ya dubi abokan nasa wayanda suka
dukufa sai tumbuke ciyawa suke, lokaci daya ya bushe da
dariya yana dariyar yana nuna hasan da yatsa,
.
Ko duban wurin da yake ba suyi ba saboda inda sabo sun
riga sun saba da halin Aliyu shi arayuwarsa da Abun
dariya da Abun ban haushi duk Dariya ake masu wannan
yasa suka sanya masa suna SARKIN DARIYA
.
Sai da yayi dariyarsa ta isheshi sannan ya ce da su “ni na
wuce ta hostel zanje na kwanta” yana gama fadin hakan
ya nufi hanyar da zata sada shi da dakin kwanan dalibai
na Gongola (GONGOLA HOUSE)
.
“Al’amarin Aliyu sai Addu’a shi komai Aduniyar nan
dariya yake basa,”
Mansir ne yake fadin haka bayan tafiyar Aliyu
.
Jibrin ya dago kai ya dubi mansir yace “tab ai ni tunanina
ma aljanu ne suka shafe shi,”
,
“Ba aljanu bane iskanci ne kawai, shin kun taba ganin
yana dariya a gaban Zara’u”
Haidar ya fada yana kokarin tumbuke wata doguwar
karkashin kwado mai karfi
.
Suna cikin hiranne suka hango Aliyu ya nufo inda suke
cikin gudu, da ganinsa sai dukkaninsu suka tsaya da aikin
cire ciyawar da suke, suna jiran ya kariso suji ko menene,
.
Da isowan Aliyu dukkansu suka tare shi suna tambayarsa
mai ya faru,
“TARAKUTA na gani cikin hostel namu, shine ku ka ga na
juyo da gudu”
Aliyu ya fada
.
Mansir yayi tsaki yace “to uwar me yake a hostel yanzu,”
.
“Dojoji yake nema wayanda basa zuwa class, ya hada su
da aiki kamar yadda ya hadamu”
Hasan ya fada lokacin da ya juya ya koma kan aikinsa
.
Haidar yayi tsaki yace “ai kuwa yana da babban aiki
gabansa,”yana gama fadin hakan yacigaba da tunbuke
ciyawan karkashin kwadon da suka cunkushe filin
….
Akalla sun dau sa’a biyu zuwa Uku kafin su idar da aikin
da malamin da suka kira da TARAKUTA ya sasu
.
Asalin sunan malamin Mr john Mai lafiya, shine Labour
master na makarantan, aduk sa’in da dalibi yayi laifi toh
wajensa ake turosa ya yanka mai aiki (Function),
Hakan yasa daliban makarantan suka sanya masa suna
TARAKUTA amma wani sa’in su kan kiransa da TRAPOZIE
amma a bayan idon sa,
….
Lokacin da suka idar da aikin yayi daidai da lokacin da
karar ansakuwar Kararrawa ya karade makarantar,
wanda yake nuni da antashi daga class,
.
Dalibai suka yi ta futowa rututu daga ajujuwa suna nufar
hostel nasu,
Kai tsaye haidar,Aliyu,mansir,jibrin da hasan suka nufi
hostel,
,
Jikinsu ya jige sharkaf da gumi yadda kasan an tsamosu
daga Rijiya, in kadauke Aliyu dukkansu babu riga a jikinsu
sai farin singileti, sun rataya rigar a kafadarsu
.
Kowanne daga cikinsu tunanin dayake daban, da isarsu
cikin dakin su, suka nufi gadajensu Dalibai sai gaishesu
suke, amma su basu ma san sunayi ba,
Don in ba sun kwanta sun huta bane, basa tunanin zasu
kara Moruwa a wunin Ranan
.
Aliyu ne kadai ya zauna akan Gadon ya dubi daya daga
cikin Yaran dake dakin yace da shi “emma dauki bokitin
nan ka debo min ruwa a solar”
“Ok siniyo” dan karamin yaron wanda bazai wuci shekaru
17 ba ya fadi
.
___ ______
Mai Karatu shin su waye wayannan ABOKAI biyar din
Haidar,Jibrin,Mansir,Aliyu da hasan
,
Mai karatu kada ka gaji maza biyoni cikin littafin ABOKAI
Comments
Post a Comment