★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 05
.
********
ABOKAI ne kuma AMINAI sun rike abotansu da gaskiya da Amana, ba’a taba jin kansu,
A gaba daya ilahirin makarantar babu ABOKAN da suka rike ABOTA da muhimmanci kamar su,
.
Dalibai,malamai da masu aikatau a makarantan suna matukar jin dadin wannan ABOTA ta su, A kowanne lokaci zaka gansu Tare babu abinda yake Rabasu face shiga bandaki,
.
Suna Rayuwansu cikin farin ciki da Annashwa, in ka gansu sai ka rantse cewa Abotansu ta samo asaline tun daga yarinta, amma maganar gaskiya Makarantan Government College Keffi itace tayi sanadiyar haduwarsu har suka zamto ABOKAI,
.
Arayuwarsu komai daya suke yi, ko aikine aka bai wa daya daga cikinsu toh tare zasu yi aikin,
Basa taba Rabuwa da Wasa da dariya, musamman ma Aliyu wanda ya kasance mai yawan Dariya,
,,,,,,
Haidar daga jihar BENUE yake a karamar hukumar Makurdi iyayensa marasa Karfine, amma suna da rufan Asiri daidai gwargwardo,
Adaddafe da Taimakon Ubangiji Haidar ya kammala makarantar Primary,
.
To saboda hazakarsa da kuma kokarinsa yasa gwamnatin BENUE ta dau nauyin karatunsa na sakandire inda ta turo sa makarantan Maza na kwana, a jihar Nasarawa, karamar hukumar keffi
.
Haidar shi dai baza’a kirashi da Dogon mutum ba hakanan baza a kirashi Guntu ba,
Haka kuma ba’a kirashi da mummuna ba, domin kuwa yana da kyawun fuska daidai gwargwado launinsa launin tarwada ne, ya mallaki dogon fuska mai dauke da dakwa-dakwan idanuwa da dogon karan hanci,gami da karamin bakinsa wanda ya samu mazaunai a kasan Kasumbarsa,
.
Yana son sanya matsastsun kaya hakan ne yake bayyana kirar jikinsa,
Haka nan yana da saurin fushi amma cikin kankanin lokaci yake saukowa
.
Sam baya damuwa da zaman makaranta duk da cewa yanayin makarantan batai masa ba, sannan ga takura da matsin lamba da suke samu daga Siniyoyinsu a lokacinnan yana JSS1,
……………
Jibrin dan jihar KANO ne daga karamar hukumar WARAWA,
Marayane shi, tun tasowarsa har izuwa girmansa bai san wanene mahaifinsa ba, shi dai abun da ya sani shine mahaifiyarsa inna Laure ta sa nar da shi cewa babansa ma’aikacin Soja ne, ya rasa ransa ne a sanadiyar YAKIN MAI TATSINE,
.
Mahaifiyarsa inna laure bata da karfi
Alokacin daya ke Primary tuyan kosai take, da taimakon Allah da taimakon tuyan da take yi take samu take biya mai kudin makaranta, a haka har ya idar da makarantar primary din a daddafe,
.
Daga nan gwamnati ta dau nauyin karatunsa inda ta turasa makarantar maza ta kwana Government college keffi a jihar Nasarawa karamar hukumar keffi,
.
Jibrin dogone , yana da kewayayyiyar fuska mai dauke da guntun karan hanci, da kananun idanuwa, da faffadan baki,
Kyakkyawane don babu yarinyar da zata hada idanu da shi bataji yayi mata ba,
Ya kasance mai yawan son wasa da dariya amma bai cika son magana ba,
.
Dakinsu daya da Haidar kuma Alokacin Aji daya suke don dukkaninsu suna Jss 1
Tun basu saba da junan su ba har suka fara sabawa, daga karshe kuma suka zama ABOKAI
,
…………
Mansir Dan jihar Kaduna daga karamar hukumar Jaba
.
Iyayensa masu haline don kuwa sun mallaki tangamemen Gida a angwan G.R.A angwan da sai masu hannu da shuni ne ke samun gurbin zama,
Tun lokacin da mansir yake makarantar firamare yana da hazaka daidai gwargwado , bayan ya idar da makarantar firamare a lokacin dududu baifi shekaru goma sha bakwai ba A duniya 17
,
Arayuwar mansir ya tsani makarantar kwana, (boarding school) tun wani majigi (fim) daya kalla yaga yadda daliban makarantan kwana suke rayuwa sai yaji sam rayuwarsu bai masa ba,
.
Ba karamar ja in ja akayi ba lokacin da mahaifin Mansir Alhaji Tijjani yazo da maganar zai kai Mansir makarantan kwana na Maza acan Nasarawa, kalubale na farko da Alhaji Tijjani ya fara fuskanta cikin Gidansa kenan don kuwa mahaifiyar Mansir hajiya Zulai taja ta kafe kan cewar ita bata yarda adau danta tilo data mallaka Aduniya a kaisa wata can uwa duniya da sunan karatu ba, shima kuma Mansir bai amince ba, sai daga baya Alhaji Tijjani ya lallashi hajiya zulai da maganganu masu taushi inda ya nuna mata dukkan wani abun da ya samu bawa to mukaddari ne daga Allah
.
Mansir kyakkyawa ne fari sol da shi yana matukar kama da mahaifiyarsa hajiya Zulai, fuskarsa a shimfide take yana da yan dara-daran idanuwa gami da dogon karan hanci mai kananan kofofi, da dan karamin baki ma’aboci fararen hakwara, gashin kasumbarsa da gashin gemunsa sune suke kara fidda kyawunsa
.
Mansir ya tsinci kansa a garin keffi cikin Makarantan Government College keffi, alokacin yana Jss 1 ajinsu daya da su haidar da jibrin sai dai hostel na su ba daya bane, haidar su suna Gongola House ne, shi kuma Mansir yana Katsina Ala house,
Akowanne lokaci mansir bashi da aiki sai dai ya sami waje ya zauna yayi ta tunanin Gida aduk lokacin daya fara tunanin gida zakaga hawaye na kwaranya daga idanuwansa
.
Haidar ne yafara kula da yanayin mansir, ya tabbata mansir ya shiga kadaici ne, wannan yasa akullum yake shishshigewa Mansir har suka saba sosai, suka zama ABOKAI UKU, sukan zauna suyi ta hira yadda kewan gida bazai dame su ba
…….
HASSAN dan jihar Nasarawa daga Karamar hukumar KARU
Hasan ya kasance dogone yana da haske amma ba sosai ba , ya mallaki kewayayyiyar fuska ma’abociya murmushi, yana da madaidaitun idanuwa gami da madaidaicin baki.
.
Mahaifinsa Alhaji Tanimu da mahaifiyarsa hajiya Balki suna da ‘ya’ya Uku, biyu maza daya mace, A dokan gidansu hasan duk wanda ya idar da karatun firamare, to kai tsaye zai wuce makarantar kwana ne na maza dake KEFFI
.
Alokacin da hasan ya idar da karatun firamare , kai tsaye aka kawo shi Government College Keffi,
.
Hasan ya kasance mutum mai son jama’a amma ba kasafai ya cika son magana ba, yana daukan lokaci kafin kaji ya budi baki yayi magana,
Ya samu mazauni a hostel na KADUNA HOUSE shima Ajin sa daya da su jibrin,mansir da haidar
,
Da shike shi mutun ne mai son mutane Aduk lokacin dayaga su haidar a tare yakanji dadi a ransa ganin yadda suke rayuwa, a hankali ya fara shishshige masu har shima ya zama daya daga cikinsu suka zamto ABOKAI HUDU
………..
SARKIN DARIYA ko ince ALIYU daga Abuja yake iyayensa ba kananan mutane bane,
Aliyu siririne yana da dogayen siraran kafafuwa masu barazanar Karyewa ako wanne lokaci, ga yar fingilalliyar jikinsa wadda jikin wani karamin yaron ma yafita kauri
farine sol yana da faffadan fuska da yan mitsi-mitsin idanuwa gami da tsukakken baki a kowanne lokaci fuskarsa bata rabo da Annashwa
.
Aliyu mutum ne mai son fara’a gami da annashwa shi yasa akowanne lokaci hakwaransa basa Rufuwa, babu abun da yake gundurar mutane da shi sama da dariya, wannan yasa Abokansa da dama ke kiransa da SARKIN DARIYA
.
Mahaifin Aliyu Alhaji Mudi bai samu wata matsala ba ayayin dayayi yunkurin turo Aliyu makarantar kwana,
.
A lokacin da aka sanya Aliyu cikin makarantar maza ta kwana Government College Keffi an sakashi a JSS 1 kuma hostel nasu daya da Hansan don shima a Kaduna house yake
.
Hasan shine wanda aka hada shi da aliyu don ya nuna mai makaranta da kuma dokokinta dariya sosai Aliyu yarunga yi yayin da hasan ke fada masa dokokin makarantar
.
Sati bata zagayo ba sai da Aliyu,Hasan,Mansir,Haidar da Jibrin suka hawa jirgin Abokai daga Abokai suka wuce jirgin Am
inai daga wannan jirgin suka shilla babban jirgin Yan’uwantaka
ABOKAI BIYAR ko YAN UWA BIYAR
Comments
Post a Comment