ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 06
.
.
Sati bata zagayo ba sai da Aliyu,Hasan,Mansir,Haidar da Jibrin sai da suka hawa jirgin Abokai daga Abokai suka wuce jirgin Aminai daga wannan jirgin suka zamto Yan’uwan Juna
ABOKAI BIYAR ko YAN UWA BIYAR
……….
Motace kirar Hilux ke ta dirgar gudu a tsakiyar titin, babu abunda zai baiwa mutun mamaki face ganin yadda motoci ke mammatsawa suna baiwa Motar hanya,
.
Ba abun mamaki bane izan akayi la’akari da jiniyar dake tashi daga cikin motar da kuma Rubutun dake jikin motar,
.
Hilux din ta faka a gaban babban ofishin yan sanda na jihar Kano,
Kofar motar ta bude wani bakin mutumi yana sanye da koren riga T shirt da shudin wandon jeans, kafafuwansa na boye cikin takalmi sau ciki,
Dogon mutumin mai kirar kattai ya nufi cikin ofishin,
.
Faffadan ofishi ne wanda aka kawata shi ainun da kayan kawa, ma’aikatan yan sanda ne rututu cikin ofishin suna sanye da bakaken uniform sai kai da komowa da shiga da fice suke wasu kuwa na zazzaune akan kujera suna rubutu,
Wasu suna cikin magarkama suna jibgar masu Laifi,
.
Da shigar bakin mutumin cikin Ofishin sai gaba dayan yan sandan masu sanye da bakaken kaya suka mike tsaye suka Sarawa bakin mutumin,
.
Bakin mutumin ya yi wani abu wanda shi a zaton sa murmushi yayi, ya nufi wani sashe na ofishin
Wani tsamurarren dan sanda ya biyoshi yana ce masa “Yallabai”
Bakin mutumin ya juya ya dubi tsamurarren dan sandan dake gabansa wanda ko tantama babu ba wata abun kirki yake tsinanawa ba cikin aikin yan sandan
.
Kai tsaye bakin mutumin yakai hannunsa ga gaban rigar tsamurarren dan sandan inda sunan shi ke rubuce ,
“Kwastabul sabi’u,”
Bakin mutumin ya fada da garjejiyar muryarsa mai kama da sautin bajimin sa yana kallon tsamurarren dan sandan dake gabansa sannan yaci gaba
“Sunan kenan”
“Eh yallabai”
“Kamar naji ka kirani dazu” bakin mutumin ya tambaya cikin kokonto yana jujjuya dan yatsansa atsakiyar kansa
.
“Eh yallabai dama kwamishina ne yace da zarar kazo na fada maka yana neman ka a ofishinsa” kwastabul sabi’u ya fada yana kokarin gyara zaman wularsa dake barazanar subucewa ta fadi kasa daga kan katuwar kansa
.
“Ok ” bakin mutumin yafadi lokaci daya ya juya ya nufi wani sashi na ofishin
*******
“Haba A.C.P Kamalu kada ka bamu kunya ba mana, kasan cewa ta’addancin mutanen nan yayi yawa ya kamata ace an dakatar da su, yanzu na gama waya da shugaban kasa ya bamu umarnin duk sadda muka gano maboyarsu, to muyi kokari mu sanar wa da rundunan sojoji don su kamasu, amma ni sam bana bukatar sojoji su shigo cikin kes din shi yasa kaga na kiraka domin kusan yadda zakuyi gobe ku kamo mutanen nan”
Dan guntun mutumin ya dasa aya yana mai duban bakin mutumin dake gabansa
.
Guntun mutumin wanda bazai wuce shekaru hamsin ba 50 yana zaune a kan kujera sanye da shudin uniform na yan sanda,
.
Yana da wadataccen hasken fata , fuskarsa a kewaye take yana da dakwa-dakwan idanu, ya mallaki dogon wawakeken hancin mai kama da kofan gari gami da madaidaicin baki,
Mulmulallen kansa dake dauke da daidaikun fararen gashi shine ya bayyana asirin Saikon da ya kusan zaftare rabin kan, guntun mutumin mai tarin gashin Kasumba da gemu yana zaune akan kujera ga Tangamemen Teburin katako a gabansa , takaddu ne da files burjik a saman teburin katakon, sai wani karamin Allon katako mai dauke da sunan guntun mutumin, cikin manya da kananun haruffa aka rubuta Abdullahi makeri dorayi COMMISSIONER OF POLICE Allon katakon yana fuskantar gefen kujeran da bakin mutumi mai sanye da koren riga da shudin jeans ke zaune
.
Bakin mutumin da aka kira da kamalu yace “yallabai da yardar Allah gobe tamkar yan ta’addan nan sun shigo hannu ne saboda dakwai yan leken asiri dana tura suka gano mani maboyarsu , jira kawai nake Allah ya kaimu gobe rai da lafiya mu shigan masu”
.
Kwamishina abdullahi yayi murmushi wacce duk da ya dan tsufa amma sai da ta fidda kyawun fuskarsa yace “yauwa kamalu, shi yasa nake jin dadinka don kai baka wasa da aiki kuma duk aikinka sai an samu nasara, shima wannan muna fatan asamu nasarar din”
“Ameen Yallabai” kamalu yafadi
“Ma’aikata nawa zaka diba yayin aiwatar da sumamen” kwamishina Abdullahi ya bukata
“Ina ganin ma’aikata 20 sun yi”
Mataimakin kwamishina kamal u yafadi yayin daya ke kallon kasa
“Ok”
***********
Comments
Post a Comment