Main menu

Pages

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 07
.
Motar yan sanda ce ta faka a gaban tangamemen Hotel din, wanda a saman sa a ka rubuta da manyan haruffa CITY HOTEL,
Daidai kun mutanen dake zazzaune a harabar gaban hotel din da masu sai da kayayyaki duk hankulansu ya koma ga motar yan sandan
.
A.C.P kamalu ya fara fitowa daga motar yana sanye da bakar riga big kwala da damammen wandon jersey . Bindigarsa kirar pistol tana soke a kugunsa cikin kubenta,
.
Yana fitowa wasu kattin yan sanda su biyar suka firfito daga cikin motar sanye da bakaken kaya, sai zazzare idanu suke tamkar za su ci babu
.
A.c.p kamalu yayi mika gami da hamma yayi hamdala kai tsaye ya nufi cikin Hotel din
Daddaikun Mutanen da suka mai da hankali wajen kallon yan sandan sai suka cigaba da sha’aninsu don inda sabo sun saba da ganin yan sanda a hotel din, sai de abin da ya daure masu kai shine ganin mataimakin kwamishina na yan sandan Garin Kano da kansa, wanda kusan kowa a garin kano ya sansa saboda yana yin aikinsa cikin Gaskiya,amana da adalci,
.
*********
Tsattsaikan daki ne mai matsakaicin tsayi gami da fadi, dakin a kawace yake da kayan kawa,
Jibga-jibgan karti ne su biyar a cikin dakin ko wannensu na rike da karar Sigari a hannunsa
.
Daya daga cikin kartin ya kai sigarin cikin bakinsa ya zuka sannan ya cire ya buso hayaki ta baki da hanci,
Yace da sauran “dafatan dukkaninku kuna cikin shiri akan aikinmu na gaba”
,
“Kada ka damu Oga Sidi dukkan mu a shirye muke “
Wani kato dake can zaune akan Gado ya fada yana mai zazzare idanuwa
Katon da aka kira da oga Sidi wanda da gani shine shugabansu yana sanye da jibgegiyar shudin rigar sanyi gami da bakar wando fela, ya sake zukar sigarin a karo na biyu ya buso hayaki ya jijjiga kai yace “abin dana ke so da ku shine kai AUDU ” ya dubi katon dake zaune kan gado
“Zaka je BENUE ka taho da yaran mu na can, kai kuma JAGWA” ya karkatar da dubansa izuwa kan wani kato mai sanye da hula hana salla ya na zaune akan dan karamin firji,
“Zaka je IKEJA ka taho da yaran mu na can, sai kai BALBALI” ya karkato da dubansa izuwa kan wani garjejen kato dake tsaye jikin bangon dakin ya tokare kafarsa daya da bangon dakin yayin da dayan kafar tasa ke damfare a kas
“Zaka nufi TUNGA cikin jihar Nasarawa dakwai wani yarona mai suna TAKU ku taho tare da shi daga nan sai dukkanmu mu hadu a maboyarmu ta Kaduna, don harinmu na gaba shine babban Bankin Nigeria dake Abuja wato CENTRAL BANK OF NIGERIA, “
Ya dakata ya zuki sigari ya fesar da hayaki sannan yaci gaba,
“ABA YAWO “
“Na’am Oga Sidi” wani kato dake kusa da Oga Sidi ya fadi cikin garjejiyar muryarsa
“Kai zaka tsaya tare dani don zamu kai wa Malam ziyara , saboda neman sa’a, kasaan cewa babban aikine a gaban mu dole muna bukatar a nema mana Sa’a “
.
“Hakan yake Oga kuma sai munyi nasara a wannan aiki namu”
Balbali ya fadi lokacin daya fesar da hayaki daga bakinsa
*********
A.c.p kamalu ya shigo cikin hotel din kai tsaye ya nufi wani ma’aikacin hotel din mai kula da Dakunan Baki,
“a.c.p kamalu ma’aikacin dan sanda ” yafada yana nuna wa ma’aikacin hotel din I.D card na sa,
“Yalla bai, me za mu taimaka da” ma’aikacin hotel din ya bukata cikin tsoro
“Nasan cewa kana da labarin wasu yan ta’adda wayanda suka fitini Al’ummar Nigeriya”
Mataimakin kwamishina kamalu ya fadi yana wasa da yan yatsunsa
.
Lokaci daya fuskar ma’aikacin hotel din ta sake birkicewa cikin in ina yace “yallabai badai yan ta’addan nan da suka kashe Gwamnan jihar Nasarawa ba, yan ta’addan da sukayi garkuwa da shugaban yan kwadagon Nigeriya”
.
“Eh sune” A.c.p kamalu ya bashi amsa cikin yanayi na ko’in kula
“Inna lillahi wa’inna ilaihirra ji’uun, wallahi yallabai ban san su ba bani da gami da su yallabai”
Ma’aikacin hotel din wanda ya gama birkicewa ya fadi cikin wata irin murya
.
“Ai ba cewa nayi ka sansu ba ko kana da gami da su, na samu rahoton cewa wasu daga cikinsu suna fake a cikin hotel din nan hakan yasa na debo jami’an tsaro don na kamasu”
.
“Alhamdulillah yallabai har naji sanyi cikin raina”
.
“Amma duk da haka dakwai aiki daya da zaka yi mun”
.
“Wani aiki kenan yallabai ” matsoracin mutumin ya fadi yana duban a.c.p kamalu
************
“Oga Sidi bamu tabayin aiki mai kwari wanda ya laso kudade ba kamar na kashe gwamnan jihar Nasarawa har miliyan,Dari fa yallabai ya biya mu”
.
Jagwa ya fadi yana duban aba yawo
Oga sidi yayi wani abu wadda a zatonsa murmushi yayi “kada ku damu yara, kudaden da zzamu samu a aikinmu na gaba sai ya ninka wanda muka samu a kisan gwamnan jihar Nasarawa sau Goma”
.
Balbali ya dubi Oga sidi yace “kace babbar bankin Najeriya zamu kai wa hari shin ya zamuyi da jami’an tsaron dake ciki da waje na bankin”
.
Koda oga sidi yaji haka sai ya bushe da dariya mara dadin sauraro yadau sakanni ashirin yana dariyar kafin daga baya ya tsuke bakinsa sannan ya daure fuskarsa tamau tamkar ba dazu ya gama tikar dariya ba
“Balbali da halama har yanzu dakwai sauranka cikin wannan aiki namu, shin tsoro kake ji ko me, Jami’an tsaro me akayi akai jami’an tsaro da har zasu sanya mu fasa aikin da muka sa agaba, ya akayi har muka kashe gwamnan jihar Nasarawa Alhaji sagir mai duka, cikin jami’an sa muka kashe shi, shugaban yan kwadagon najeriya shima cikin jami’an tsaron muka sace shi kuma muka karbi kudin fansa har milyan saba’in a kansa, yaron ministan kudi na najeriya cikin makarantan Sojoji N D A muka saceshi.
Shine har iyau kake fadamani wasu jami’an tsaro,
Ni SIDI kashe babba kashe yaro, bana tsoron jami’an tsaro kuma a gabanka ganin idanunka zamuje har bankin , na kashe jami’an tsaron mu debe kudade mu yi tafiyarmu”
.
“Hakan take Oga sidi wannan Gaskiya ce”
Balbali yafadi yana feso hayaki
.
Suna cikin hirar ne sukaji ana kwankwasa masu kofa cikin sauri dukkansu suka zare bindigoginsu daga kugunsu suka daga bindigogin sama lokaci daya duk suka dawo jikin bangon da kofar dakin ke manne a jiki suka tsatstsaya cikin shirin kota kwana.
.
Oga sidi ya dubi abokan ta’addancinsa yace da su cikin kankanuwar murya “cool down Gayu bazan duba ko waye”
.
Suka gyada kawunansu
“Waye wannan” oga sidi ya bukata
“Yallabai ma’aikacin hotel din ne”
Matsoracin mutumin ya fadi jikinsa na kyarma
Ya dubi bayansa inda tarin jami’an tsaro suka zagayeshi , abin ya daure masa kai ainun ganin har da masu goge-goge a hotel din da masu kula da fulawowi da masu kai abinci cikin jami’an tsaron suma kuma suna rike da bindiga kirar pistol a hannunsu sun saita bakin bindigar yana kallon kofar dakin,
Jira kawai suke mai tsatstsauyi ya bude kofar
.
“Me ya faru “
Oga sidi ya fadi yana saukar da bindigarsa kas
“Kwanu kan da kuka ci abincine na zo kwashewa”
“Ok ” oga sidi ya fadi lokaci daya ya na kokarin bude kofar dakin,,,,,,
Shakka babu da dan ta’adda SIDI KASHE BABBA KASHE YARO yasan abun da zai biyo bayan bude kofar , da bai yadda yayi gangancin bude  wa
.
Gaba dayan yan ta’addan suka sauke bindigoginsu suka soke a gefen kugunsu,
**=**

Comments

table of contents title