★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 08
.
Karar fitar harsashi daga bakin bindiga gami da ihun da Oga sadi ya saki shine abun daya Razana sauran yan ta’addan,
.
Cikin zafin nama yan ta’addan suka zare bindigoginsu suka fara yiwa yan sandan dake waje ruwan harsashai,
.
Jami’an yan sandan suka cigaba da sakin wuta ya zamana cewa suna musayar harsashi tsakaninsu da yan ta’addan
.
Shakka babu yan ta’addan sunyi mamaki kan yadda akayi har aka gano suna boye cikin hotel din, cikin bacin ran an harbi shugabansu a kafa, yan ta’addan suka ta sakin wuta ba sararawa
.
A cikin musayar wutar da ake ne wani jibgegen dan sanda ya kwalla ihu ya fadi kasa kafadarsa na hagu na bulbulo da jini
.
Da wuri yan sanda biyu suka kinkimi katon dan sandan da aka harba a gefen kafada su kai waje da shi
Da yan Ta’addan suka tabbatar cewa muddin aka cigaba da wannan gumurzu to nan bada dadewa ba Alburusan bindigoginsu zasu kare a samu nasarar kamasu sabida haka sai jagwa ya zo gindin tagar dakin ya doketa da hannu take gilashin da ke jikin tagar ya tarwatse
.
Ya juya yawa Balbali inkiya da hannu kan cewa su zo su fara fita shi zai ji da yan sandan
Batare da bata lokaci ba Balbali ya nufi tagan dakin wanda ke can kuryar dakin , jagwa ya dawo bakin kofa ya cigaba da sakin harsashai daya harba harsashi daya sai ya dakata yaji ko harsashin tayi nasarar aikata abun da ake bukata
.
Sabanin yaji ihun jami’an tsaron sai de ya sake jin wata karar fitar harsashi ta durfafo dakin hakan tasa yake boyewa a jikin bangon dakin
,
Jagwa,aba yawo da Audu suka durfafi tagar dakin bakin bindigunsu na fuskantar kofar dakin da yake a bude , jira kawai suke wani mai kararrar kwana ya leko,
Kimanin dakiku talatin kenan da lafawar musayar wutar, bakajin karar komai cikin dakin in ka dauke nishin da oga sadi yake,
Yana kwance a kasa ya rakube da jigin bango hannunsa na rike da bindigarsa ya saita bindigar a daidai saitin kofar dakin, kafarsa ta hagu kuwa sai bulbulo da jini take tamkar an yanka Kaza
.
Cikin kankanin lokaci jagwa da Aba yawo suka fice daga dakin ta taga, Audu yai wa balbali inkiya da hannu kan cewar su dau Oga sidi su tafi da shi
.
Audu da balbali suka ciccibi oga sidi sukai sama da shi suka dumfari tagar dakin da zummar su fice da shi toh a lokacinne Al’amarin ya faru, Al’amarin daya yi matukar fusata dan ta’adda Audu, Al’amarin da ya kusan Zauta dan ta’adda Audu,
.
Mataimakin kwamishina kamalu ya jinjina bindigarsa da yadubi wasu yan sanda biyu dake gefen hagunsa yai masu inkiya da hannu
.
Lokaci daya yayi Gungure ya wuce ta gaban kofar dakin fuskarsa da bakin bindigarsa na kallon cikin dakin
.
Abun daya ga yan ta’addan na kokarin yi shi ya sanya cikin sauri ya harba harsashin bindigarsa
,
Audu na na wajen dakin ta taga Balbali yana ta ciki yana kokarin daga Oga sidi Sama ya tsallake tagar , Audu kuma kokari yake ya tallabo kafafuwan Oga sidi ta yadda da zarar ya haure tagar to a hannunsa zai fado
Balbali ya baiwa kofan dakin baya bindigarsa na ajjiye a gefen Tagar , kokarinsa shine oga Sidi ya far ficewa,
,
Karar da Balbali ya kwala gami da karar fitar harsashi shine abun da yayi matukar Razana Audu, balbali ya fadi a kasa Rikica kai kace giwa ce ta fadi, ko shurawa bai yi ba yace ga garin ku nan
.
Audu da oga Sidi sun yi matukar Razana da harbin Balbali da akayi nan take audu ya fara kokarin janyo oga sidi daga cikin dakin
.
Jami’an Yan sandan gaba daya suka kunno kai cikin dakin suna masu sakin wuta,
.
Ganin jami’an tsaro sun kunno kai cikin dakin kuma ya tabbata in har suka shigo dakin zasu iya hallaka sa
“Audu ka sakko mu tafi”
.
“Me kake jirane Audu ka sakko mu tafi”
“Kassako man audu”
“Zasu iya kashe ka muddin sukai arba da kai”
“Ka sakko mu tafi”
Audu ya tsinkayi muryan yan ‘uwansa Jagwa,Aba yawo da Taku,
Ya kai dubansa izuwa kasan hotel din ta inda yake jiwo sautin muryoyinsu
.
Ya hango su akan Rufin wani gida, kasan Hotel din kuwa mutane masu yawa suka mamaye suna kallon abun da ke faruwa
.
Bakin bindigar wani dan sanda ne ya leko cikin dakin, ganin haka sai audu ya daga bindigarsa yana kokarin sakin wuta amma sai bindigar tayi Turjiya , ta na kukan rashin Alburusai,
.
Audu yai harbi da bindigar ta bakin kofar dakin lokaci guda yayi tsalle ya rabu da jikin Hotel din yana mai kallon oga Sidi wanda ya tabbata ba makawa zai jami’an tsaro sun kamashi
.
…..
Babban kurskuren da yan sandan suka yi shine da suka dunguma baki dayansu suka afka ma yan ta’addan , izan da sun bar wasu a wajen harabar hotel din da babu makawa sai sun yi Nasarar Kame yan ta’addan
.
Koda Dan ta’adda Audu ya dirgo saman Rufin wani Gida, bai tsaya wata wata ba ya Ruga da gudu ta wani sashe mai karancin mutane
.
********
Hasan,Aliyu,Mansir,Jibrin da haidar suna sanye cikin riga riga mai launin ja da fari dogon hannu da Jar doguwar wando
.
Tafe suke cikin Annashwa da farin ciki
“Sarkin dariya yanzu dai sai ayi kokari a kame dariyar ko” mansir yafadi cikin murmushi yana kallon Aliyu
.
Aliyu wanda ya natsu sosai yadda kasan frofesa za shi wajen wani muhimmin taro yayi murmushi gami da gyara kwalan rigarsa ya sake tsuke zanzaron da yayi sannan yace “in Allah ya yarda”
.
Dukansu suka kyalkyale da dariya,
Kai tsaye suka nufi Kasuwar makarantan wurin da ake saida Abinci da sauran Abubuwan kwalama, dalibai suna kiran wurin da BENUE MARKET,
Kasancewar kasuwar yana kusa da BENUE HOUSE shi yasa aka lakaba masa wannan suna
.
“Aboki kafa yi dacen budurwa sai de…”
Haidar ya fadi yana murmushin tsokana
Mansir ya ce “sai de mai”
Jibrin yayi murmushi yace “sai de ita zahra’un batayi dacen saurayi ba, haba mutun kullin baki a bude wannan wata rana ai sai ka cije ta” ya karisa maganar yana dariya
,
Dukkansu suka dara in ka dauke Aliyu daya sha kunu ya bata rai, hasan ya matso kusa da Aliyu ya dora hannunsa akan kafadar Aliyu yace “Aboki ka rabu da zancensu na soki burutsu nasan ita kanta Zahra’u tana sonka domin kaidin ba karamin kyakkyawa bane, gaka da haiba da cika Ido, “
Aliyu yayi murmushi yace “nagode aboki kai kadaine ke goya ma soyayyata baya kuma da yardan Allah nan da yan lokaci kalilan zata sanar dani cewa tana sona a gabanku yan kushe”
Yafadi yana kallon su haidar
Dariya sosai jibrin yayi kafin yace “tab kace ma kai kake kidinka kuma ka ke rawar ka “
.
“Ai ya sanar da ita sai de har yau shiru kake ji babu amsa” mansir ya fadi yana duban jibrin
“Toh Allah yasa dai ba son maso wani kake ba wanda hausawa suka ce koshin Wahala”
Haidar ya fada
.
Haidar,jibrin da Mansir sukai shewa sai dai ganin Abokan nasu biyu sun bata rai
Yasa jibrin ya dan matso kusa da hasan yace “haba aboki sarkin dariya kada kayi Fushi ni nasan yarinyar tana matukar sonka, kawai dai tsiyace muke maka”
Haidar ya kara da fadin “shin kai baka lura da irin kallon data ke maka bane aduk lokacin daka je Benue market,izan da wata rana zaka lura da irin kallon to tabbas da ka tsinkayi zuzzurfan So na gaskiya Makare a cikin kwayar idanunta”
.
“Irin murmushinn data ke yi ma ya isa hujja domin murmushine dake dauke da sakon Zuciya,aboki muna tare dakai yau sai ta sanar damu matsayinka a Zuciyarta”
Mansir ya fada yana kokarin tallafo habar aliyu wanda y
a saki fuska , har zuciya Aliyu yaji dadin maganganun Abokan nasa,
.
Lokaci guda yaji wani kwarin gwiwa ya shigeshi cikin dakewa y ace “maganarku Gaskiya abokai ayau ya kamata nasan matsayina a wurin ta don haka mu je mu same ta”
Comments
Post a Comment