Main menu

Pages

★ABOKAI★
littafi na daya 1
Marubuci
Shuraih Usman
Typing by Shuraih Usman
Post by Shuraih 99%
© shuraih 99% 2019
Part 09
.
***
Karamin wajene mai dauke da manyan bishiyu guda hudu bishiyoyin sune suka taimaka sosai wajen yiwa wurin rumfa da rassansu, na daga cikin abun dake kara wa wajen ni’ima shine daddadan iskan dake futowa ta cikin bishiyoyin da suke wurin
.
Tsirarun mutane ne a wajen suke kasuwancinsu yawancinsu matane masu saida Abunci da kayan kwalama, daga gaban wajen da dalibai suke kira da beneu market dogon bencine a girke saman kututturin itace a gaban bencin da kadan wani teburin katako ne mai dauke da manyan kuloli na abinci sai Robobin zuba abinci dake gefe cikin karamin roban penti
.
Tana zaune akan dogon bencin tayi tagumi, lokaci lokaci takan mike tsaye tayi waige waige da alama dai wani abun take nema,
Kamar ko wani lokaci yanzuma ta mike tsaye ta kai dubanta hanyar dakin kwanan dalibai tana waige waige ko idanunta zasu ci karo da Abunda take nema
!!
Wasu yan mata biyu wayanda kallo daya zakai masu ka gane ba Musulmai bane suna zaune a gefenta sun kula sosai da yanayinta hakan yasa suka dan matso kusa da ita,
“Zara, me kike lekawa ne haka tun dazu kin kasa samun sukuni sai leke leke kike”
Daga cikin matan daya ta fadi cikin gurbatacciyar hausa,
Zara tayi ajiyar zuciya ta juyo da kyakkyawar fuskarta ta dubi yan matan wayanda suke sanye da kananan riguna da fingilallun Siket tace
“Ba komai Janet”
Bakar budurwan da aka kira da jenet tace “ko dai Aliyu kike lekene”
“A’a aliyu kuma me zai sa na riga lekensa”
Zara ta fadi
“So mana,” janet ta bata amsa tana duban budurwar dake gefenta
Cikin halin ko’in kula zara tace “So kuma haba waya fada maki cewa ni ina sonsa,”
Dayar budurwar tayi murmushi tace “zara kenan kina so kina kaiwa kasuwa, in bakiyi sauri kin amshi soyayyarsa ba kina ji kina gani wata zatai maki kwace”
.
Zara tayi shiru taki cewa komai ta sadda kanta kas tana Tunani a hakikanin gaskiya tana matukar Son Aliyu to amma tana jin kunyar fadamasa,
.
Tun Aliyu yana SS2 zangon karshe ya hadu da zara a benue market,
Wata rana suna dawowa daga Aji zasu wuce zuwa hostel ,
Suna tafiya suna hira cikin wasa da dariya Aliyu sai dariya yake kyakyatawa, kamar ance ya kai dubansa benue market, ya na kai dubansa benue marker yayi arba da ita tana kokarin, zuba shinkafa a roba,
yana ganinta yaji zuciyarsa ta harba, cikin kankanin lokaci wani kifiya mai dauke da dafin sonta ya soke shi a zuci,
.
Lokaci daya ya tsayar da dariyar da yake, ya tsaya cak yana kallonta,
Tana da matsakaicin tsayi gami da matsakaicin Jiki,farace amma ba sosai ba ta mallaki doguwar fuska mai dauke da kananun idanuwa hade da dogon karan hanci gami da tsukakken baki mai siraran labba wayanda ta rinesu da jan baki,
.
Tana sanye cikin doguwar riga har kasa, ta suturce jikinta da shudin hijabi har kasa,
Zuciyar Aliyu ta tafi ga zara, ya saki baki galala yana kallonta, tun da yake a rayuwarsa babu macen daya taba gani yaji kwatankwacin abun daya ji akan zara kanta, yasha arba da kyawawan mata wayanda suka dare zara kyawu kira da komai amma ko kadan basu taba burgesa ba bare har takai ga yaji yana sonsu,
Lokaci na fari da ya fara jin wani abu akan mata, lokaci na farko daya fada cikin Kogin Soyayya,
Babu abun da ya kara rikitashi sai da lebbanta suka fara motsawa, lokacin datake kokarin mikawa wani yaro canjinsa,
.
Kai tsaye ya nufi wurinta fuskarsa na kallonta idanuwansa kafe a kanta,
“Sarki ina zaka je”
Haidar ya tambaya yana kokarin bin bayansa
Aliyu wanda hankalinsa yayi gaba bai ji abunda haidar ya fada ba ya cigaba da tafiyarsa,
Da gudu haidar ya karisa wurinsa tun kafin ya isa benue market ya kama kafadarsa yace “haba Aliyu na yi maka magana yafi baki uku amma kayi biris dani”
“Yi hakuri aboki wallahi hankalina ne yayi gaba” aliyu ya fadi yana duban haidar
,
Mansir,jibrin da hasan suka kariso wajensu
“Haba malamai muna cikin tafiya kun zo kun tsaya anan alhalin kun san halin da nake ciki”
Mansir ya fada yana kallon Aliyu
Hasan ya kara da fadin “kun fa san dukkanmu yunwa ce ke hajijiya damu, kai aliyu ba dazu kai ta kukan ba’a tashi daga aji wuri ba, to gashi an tashin kuma kunzo kun tsayar damu”
Jibrin kam shiru yayi, fuskarsa babu yabo ba fallasa , ya dafe cikinsa da hannunsa na dama
Haidar ne ya yace da su “kuyi hakuri abokai Aliyu ne yayi kamu shine ya biyo kamun ni kuma na rakosa”
Jibrin yadan yamutsa fuska yace “wani irin kamu kuma”
Haidar yayi murmushi yace “Suruka ya samo mana”
Dukkansu suka zazzare idanuwa suka hada baki wajen cewa “da gaske, wacece”
Shi kansa Aliyu bai san yadda akayi har haidar ya gano sa ba to amma abun da bai sani ba shine alokacin da ya saki baki yake kallonta, haidar na kula da shi, har sanda ya nufi benue market shi yasa haidar ya bishi a baya,
.
Cikin zumudi da rawar jiki jibrin ya matso kusa da Aliyu kai kace ba shi bane dazu yayi lamo dafe da ciki, yace “aboki wace ce ne”
Aliyu yayi murmushi yana mai kallon inda zara’u take Zaune,
Dukkansu suka juya da dubansu izuwa kanta,
“Kai tubarkallah” mansir ya fadi
“Amma kayi dace Aboki” jibrin ya dora
“Shin ka sanar da ita kuwa” Hasan ya fadi
“Ya kamata muje yanzu ka sanar da ita” haidar ya fadi yana kokarin janyo Aliyu, a hankali aliyu ya zame hannunsa daga na haidar yace da su “daga ganinta bakuwa ce don ni ban taba ganin ta a nan ba to amma hakan ba shi zaisa na gagara sanar da ita Ina Son ta ba, amma ba yanzu ba ku bari sai mun zauna mun yi shiri”
.
Tun daga wannan Rana sai ya kasance a kullum Abokan biyar sai sun kaiwa benue market ziyara kuma kai tsaye wajen Zara’u suke tafiya, Aliyu yayi ta cikata da surutai, tun yanayi bata kulashi har dai ta fara Kulashi, tun bata damuwa da shi har takai ta fara damuwa da shi, ganin cewa ta saki jiki sosai da shi sai suka hadu shi da abokansa suka fada mata kudurinsa, sai dai har yau shiru kakeji , babu amsa amma Aliyu ya riga yasan cewa tana sonsa , kunya ne ya hanata furta masa
.
Aranar yau ne Zara’u ta kudurce a ranta zata sanar da Aliyu Amsar tambayarsa, ta kudurce zata kauda kunya ta fadamasa cewa ita ma tana sonsa, a iya saninta duk lokacin da aka tashi daga Aji abokan basa taba wucewa zuwa hostel har sai sun yada zango a beneu market, sun dubata
.
To amma yau sabanin kowanne rana Awa biyu kenan da tashi daga Aji amma bataji duriyan abokan ba, hakan yasa sa’I sa’I take  mikewa tsaye tana leke ko zata hangosu don tana da tabbacin zuwansu
,,

Comments

table of contents title