Results

ADALILIN YAYATA Complet Hausa NovelsA DALILIN YAYATA
Na Nabila Rabi'u Zango
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA...._*馃崄馃崄
                   馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*馃挕
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS_
   1 to 2
   _*Assalamu Alaikum ...na canza wannan littafin daga A
DALILINSU ...to ...A DALILIN YAYATA....Saboda naga sister
jannah tayi littafin mai irin Sunan.......馃崄*_
    Duk da bana da wayau amma nasan duk lokacin da
wannan mai bakaken kayan yazo dole sae mamana tayi
kuka ranar ....baya da maganar da ta wuce ta babanmu
duk da yayi shekara daya da rasuwa...Mugun haushinsa
ya turnukeni ...ji nake da ina da karfi babu abunda zai
hana ban mashi jajjagen kasa ba abaki...
    ..Kai maman tamu bata nan kuma ba yanzu zata dawo
ba.....na saka hannu na tare bakin kofar ina mazurai ...
     Yaushe zata dawo ...ya fada fuskar a murtake kamar
yarda yake kullun ...
  Ohon maka ....kullun kai kazo sae ka saka mamanmu
kuka kai kana so kaga maman taka tana kuka  ....na fada
tare da rike kugu...
  Yayata dake cikin gida tana wanke waken da zatayi
awara ta kwala man kira ....
  Na kalleshi duk na bata rai ina fadin ...matsa zan rufe
gidan saboda barayi.. ....ban jira komae ba na turo gidan
da karfi  ...ina jin lokacin da ya sake tsaki mai karfi ....nayi
saurin dawowa na bude kofar  ...lokacin har ya bude
motarshi zaya shiga ....
   Da karfi na kwala mashi kira kamar yarda naji mamana
na kiranshi .....Lauya ...
   Ya juyo yana kallona ....Maman tawa ta dawo Ashe ban
sani ba....na sake  dariyar shakiyyanci ...
  Karamin tsaki ya dan ja sannan ya dawo cike da bacin
rai ....na bashi hanya ya shiga ni kuma na koma kusa da
motarshi na tsaya ....
  Ina ganin ya fito na tattare siket dina na kwasa a guje
...don nasan mamar tawa batta nan ...tsakin da ya man
ne ya bani haushi ...
  Ban dawo lungun ba sae da na tabbatar ya bar unguwar
sannan naje kiran da yayata keman ...
  markade ta bani na kai mata sannan ta tace awarar ta
daura saman wuta ...
  Mamana ta dawo rike da ledar gari yayi zafi ....nayi
saurin karba ina dariya ....sae da ta dauko tabarma ta
shinfida sannan ta fito da kayan dake ciki .....
  Irin kayan kwancen nan ne da ake bata inda take aiki
....ta miko man dae dae nawa sannan ta mikawa yayata
wanda zasu mata ...nan na dinga murna tare da godiya
.....
  鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
  Tunda na fito daga gida yaron dake zagaye da kaskon
tuyar awarar yayata suka fara watsewa .....bana dagawa
kowa cikinsu ....don duk yawancinsu masu cima yayata
zalun ne ...basa bata kudinta idan sun dauka ita kuma ba
mai yawan magana bace ...sae dae ta kyalesu ....amma
idan ina gurin ko karkashin gadon uwarka ka boye sae
na bika na karbo kudina .....bana jin komae idan ka
daukar wa yayata awarar naira goma na je har gidanku
na kwanto akuyarku idan ma baku da ita zan iya dauko
tukunyar ku na taho da ita ..kuma idan duk duniya zata
hadu baran ce ga inda na kaita ba har sae anbiyani kudin
sannan zan bayar ...don bana ajeta gidanmu gudun kar
mamana tace na bayar ...
   Shafi'u dan makwabtan mu na gani sae dauka yake
yana ci ba tare da ya kirga ba ....na kafe shi da ido har na
zauna bai san da zuwana ba ....sae da ya koshi sannan ya
mike yana kakkabe riga ya fito da naira goma ya aje bisa
kwandon yana fadin ...Saa ga kudinki nan kin biyoni sha
biyar ...
 Kam ubancan ...Ashirin da biyar fa ...na fada tare da rike
kugu..
  Yayi saurin kalloni yana washe baki kafin yace ...Haba
Hudata ina nufin saura naira Sha biyar aljihuna yanzu
zan fito mata da ita sae ta biyoni Hamsin ...
  Nace ...owo ai na dauka ta ashirin da biyar kaci ...
  Ya washe baki ...aa ina ni ....ai ina lissafi ...ya lalubi aljihu
ya fito dasu ya mika mata ...ya tafi yana kakkabe hannu
tareda  kalloni ....
  Gurin na koma na zauna ....Yayata ta Bini da kallo tana
so tace na tashi amma tana shakkata ...tasan in har na
zauna ba ciniki zatayi ba sossae ....Mutane na son zuwa
amma Ni suke tsoro ...
  Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA..._*馃崄馃崄
                   馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*馃挕
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
3 to 4
          Barister Shehu abunda kake niyar aikatawa sam bai
dace ba ...wannan zaluncine tare da yaudara  ...matar
data amince da kai ta baka amanar dukiyar mijinta
yanzu kuma ta fito kana so ka zalumcesu ...idan har kai
baka taimakesu ba to bai kamata ka zaluncesu ba ....
  Ya kife wayar tare da juyowa a firgice yana kallon
Mahmud daya kafeshi da ido harde da hannayensa a
kirji ...
   Cikin borin kunya yace ...so what dan naci amanarta
kanwar babata ce ...kai Mahmud zan iya komae akan
kudi ...
  Ni kuma Barister Mahmud nace indae har ina raye bara
ka taba wannan cin amanar ba ....
  Wae me ya shafeka ne da rayuwata ....kaga ka fita
wannan maganar ...meyasaka tunda mijin nata ya rasu
baka je ka taimakesu ba sae yanzu zaka zo kana man
wani waazi ...
  Sabida ta yarda da mutumin da bai kamata ta yarda
dashi ba....yana gama fadar haka ya matso kusa da table
din shi ya dauki takardun da zai dauka tare da briefcast
dinshi ya fita ...
  Tsaki Barister shehu ya sake kafin shima ya tattara nashi
nashi ya bar office din ....daga nan gidansu Huda ya nufa
kai tsaye ...
  Cikin lungun ya hango ana dambe da huda ...ta haye
ruwan cikinshi sae jibgarshi take yara sae kara zugata
suke ....yayi kwafa ...yana tunanin da itace ake duka haka
to babu abunda zai kaishi rabasu ...yafi kaunar a kasheta
kowa ya huta don da alamun yarinyar tana neman
shigar mashi hanci ....da wannan tunanin ne ya isa gurin
...tare da fincikota ya dagata daga yaron da karfi sannan
ya dauketa mari .......
  Marin ya shigeta sossae  ta dago tare da zuba mashi ido
kafin ta dauki katon dutse ta jefawa glass din motarshi ta
gama ......nan take glass din ya fashe ...ya juyo da azama
amma kamar walkiya ta bace .....yayi kwafa tare da sake
murmushin mugunta yayi sallama gidan ...da yake baida
katanga da gidan ya fada ciki ba tare da shamaki ba  ....
   Bayan sun gaisa yake fadawa mamanta cewa ....kudin
sallamar aikin  babansu Huda malan Ibrahim sun fito
...yanzu haka gobe yake shirye shiryen fito dasu banki
sae ya kawo masu zuwa jibi ...
  Tace  ...ka barsu hannunka lauya ...idan ka kawo mana
ina zamu ajesu   ...na tabbata bara ka cucemu ba ...don
haka ka barsu hannunka ..sae dae ka dan bamu abunda
zamu kara jari dashi dan Allah ..
  Murmushi yayi yace ...aa hajiya zan kawo maki su ki
gani bayan kwana biyu sae nazo na karba ...don yanzu
haka ina shirye shiryen saya maku da gida wanda zaa
zuba yan haya a ciki duk shekara sae su dunga baku
kudin ...idan na kawo kudin jibi to wanshekare zanzo da
mutanen da zaku sayi gidan gurinsu sae a karbi kudin a
basu ....
  To Amma ina tunanin inda zamu aje su Lauya ...
  Murmushi yayi yana fadin ...Allah zai karesu Umma
....ya mike yana fadin zan tafi idan huda ta dawo a ja
mata kunne bata jin,magana yanzu daga rabasu fada ta
fasa man glass din mota ...
  Ta  hau sallallami tana bashi hakuri tare da fadin idan
kudin sun fito dan Allah ya sayi glass din dasu ...
  Yace mata to ...tunda dama haka yakeso .....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
 Barister Mahmud indae kana bukatar wani abu cikin
kudin ka fada man bawae ka dinga man wani waazi ba
na daban ....
  Wani kalan murmushi ya sake yana fadin ...nawa ne
kudin nasu ...
  Yauwa dan gari ...10m ...ne ...zan baka 1m .....shikenan
ko ...
 Dariya ya sake mai cike da maanuni daban sannan yace
  ...zan baka 10m ka bar masu nasu please
  Barister Shehu ya sake dariya yana fadin ....Am not a kid
Barister baran taba cin kudinka na zauna lafiya ba
....nasanka sossae ...don haka kabar wannan uwar watsin
...
  Suma wannan sae ka basu kayansu ...
 Dariya yayi yana fadin gobe karfe biyar na marece zan
kiraka na basu agabanka barister ....ya juya ya shige
motarshi ...
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
  Karfe biyar dae dae ya kira Mahmud ya mashi
kwatancen gidansu Huda sossae yace yazo lungun gidan
ya iskesu ...ko minti talatin bai cika ba ya shigo lungun ....
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_*
                   馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*
Na Feedohm馃挒
_*DEDICATED TO*_
_EXCLUSIVE WRITERS.._
5 to 6
     Motar Barister shehu da ya gani ya tabbatar mashi da
yana gurin ...ya fito ya jingina da motarshi tare da harde
hannaye ....kafin ya ciro wayarsa ...ya hango Huda janye
da tunkiya da gudu ....yana gani ta shiga wani lungu
sannan ta fito babu tunkiyar ta cire dan kwalinta ta
daure a kugu .....
  Wata tsohuwa ta shigo lungun da sauri janye da
hannun wani karamin yaro ....
  Ke diyarnan yanzu akan naira shabiyar zaki kwanto
man tunkiyar dubu sha biyar dan rashin
mutunci.....tsohuwar ta fada tare nuna huda da Hannu ..
  Me ya saka da nace ki biyani kudina baki bayar ba
....idan kina son tunkiyarki wallahi sae kin bani kudina
...idan ba haka naje na sayar da ita na baki canjinki ....ta
fada cike da tsiwa ...
  Tsohuwar ta kwantar da murya ...Haba Hudalliya ....na
rantse maki da Allah da fatse ta dawo daga talla zan
bashi ya kawo maki kudinki ..dan Allah karki sayar man
da tunkiya ..
  Ta juya baya tare da dage kitsonta tana fito keya ...Nifa
Innarsu Fatse dan karki ga na maki rashin kirki amma
gaskia sae kin biyani kudina tukun na bada ...
   a ranta tace ...rashin mutunci kuma har nawa
Hudalliya.....amma a fili cewa tayi ...iyakar mutunci kin
man shi Hudalliya yanzu dae alfarma nake nema yar
albarka ...
  Barister Mahmud dake kallonsu yana dariya har da rike
ciki ya matso ya kama hannun Huda yana fadin ...nawa
ne kudin naki ..
  Sarkin neman suna zaka biya mata ne ...ta bashi amsa
tare da mashi kuri da ido .....sannan tace ...hala ba nan
unguwar kake ba don ban taba ganinka waccen
majalisar ba ta sa ido ....
  Naira Ashirin ya fito ya mika mata yana fadin ...karba ki
sakar mata tunkiya ...
  Tsohuwar ta kalla tace ...Allah ya soki da na maki rashin
mutunci ..
  Da dae taga an biya kudin sae cewa tayi
.....rashin mutunci har na wana shegiyarnan ......
  Oho dae ...huda ta fada tare da shigewa lungun ta janyo
mata tunkiyarta ta koma ....
  Barister Shehu ya kira ya fito daga cikin gidan suka
shiga tare ....gabanshi ya mikawa Mamansu Huda duka
dukiyarsu a cikin jikka sannan ya mika mata makullen
suka tafi akan gobe zai dawo da masu gidan da zaa saya
..
  da Suka fitone Mahmud ya mika mashi hannu cikin jin
dadi da bai ci amanarsu ba sannan suka rabu .....
  Wajen karfe goma na dare Wayar Barister mahmud ta
fara kara ...lokacin suna zaune da family  dinsu suna
dinner ...ganin number barister Shehu ce ya saka ya
dauka tare da sallama ....
  Barister Shehu yace ...Please ka sameni gurin gidansu
wannan yarinyar akwae matsalane yanzu please ....
  okey ...ya fada tare da daukar keys ya fita da sauri
....yana isa lungun gidan yaga ba motar Shehu ya kira
wayarshi ringing daya ya dauka sannan yace gashi nan
....da yake lokacin sanyine mutane duk sun shige
gidajensu ....kofar gidan su Huda ya matsa ya zauna
saman dakalin dake wajen ....
  Kaya yaga an watso mashi a jiki ....yayi saurin mikewa
tare da daga tsumman da aka jeho mashi ....bindiga ya
gani a ciki nannade ...da saurin ya daga cikin rashin
fahimta ....ba dae wani abu akawa wadannan mutanen
ba ..
ya fada da karfi tare da kara daga bingidar .....
  Flashlight din da ta dinga haskashi tare da karar daukar
hoto ya sakashi sakin bindigar kasa .....
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 _*A DALILIN YAYATA..馃崄馃崄*_
                馃崄
*_HASKEN WRITERS ASSOCIATION馃挕_*
Na Feedohm馃挒
_*DEDICATED TO*_
_EXCLUSIVE WRITERS..._
7 to 8
        Weldon Barister ...ba dae kace zaka hanani aikata
abunda nake so ba ....good gashi yanzu zaayi komae da
kai ...
Barister Shehu ya fada lokacin da yake takowa kusa
dashi ...
  Bai san lokacin da ya sauke mashi mari ba tare da
shakarar wuyan rigashi ...
wadanda suke tare sukayi saurin banbareshi tare da
maida hannunshi baya suka rike ...
  Shehu ya sake dariyar mugunta yace ..
Kayi abunda kake so Barister ....zaka bimu gidan mu
karbi abunda nake bukata sannan ka tafi ....ko kuma na
watsa wadannan pictures din a duniya na rubuta bayan
na kaiwa Marayu Hakkinsu ...baristern duniya yaje da
yan fashi sun karbe asirinsu ya tonu ...kayi tunanin
makomar baristoci sannan kayi tunanin mutuncin
mahaifinka sannan da son da yake maka ....na tabbata
daga rannar da ubanka ya sami wannan labarin bara ya
kara motsi ba ...kana sane da yana da hawan jini
....amma rufe wannan zancan shi zaya saka na goge
wannan pictures din bayan wasu shekaru ....na lura kana
so ka tuna man asiri ...
don haka zabi ya rage naka ...
  Idanuwanshi suka ciko da kwallah ....tabbas indae har
mahaifinshi yaga wannan labarin ya tabbata bakinciki zai
zama ajalinsa .....ba tare da yace komae ba ya nuna kofar
gidan da hannu ...alamun su tafi ...
   Mask suka saka sannan Barister Shehu ya sakawa
Mahmud suka shiga .....kauren an turoshi da alamun
haka suke rufeshi dan an kangeshi da dutse ta ciki ......
  Baka jin motsin komae sae kukan kaji dake tashi cikin
....suka kutsa kai suka shiga ciki ...kamar rakumi da akala
haka Barister Mahmud ke binsu .....
  Barister shehu ne ya saka kafa ya naushi mamar dake
bacci ....tayi firgigi ta mike tana tasbihi ....
  Nan da nan ya canza murya yace ina kudin da aka kawo
masu ....
  Bamu da kudi Wallahi dan Allah kuyi hakuri ....ta fada
tana hawaye  .
  Karyane shegiya ....wani ya fada da karfi ..
  Kaine dae Shegen munafuki ....Huda dake bacci ta farka
tare da bashi amsa ....ya kai mata uban duka da yake
dama ba kaunarta yake ba ....
  Ta sake uban kara tana fadin ....Allah ya isa shege
mugu  ....ka bugi Uwarka na kashi .......
  Bata rufe baki ba ya kara daga hannu da niyar dukanta
....Saa ta rungumeta tana kuka tare da bashi hakuri ....
  Mahmud dake tsaye kamar gunki ..yace ...No.........kayi
abunda ya kawoka amma banda duka ....ya karashe
maganar da karfi ...
  Gurin Uwar ya dawo yace....kina son ranki Hajiya ....ki
fito man da kudin da aka kawo maki yau naira million
goma da marece ko kuma na kasheki anan ...
  Wallahi hakkin marayune kuyi hakuri dan Allah ....ku
barmu hakkinsu ...ta fada cikin kuka ...
  Duka ya kai hannu zai mata saa ta rarrafo tare da rike
mashi hannu tana kuka ...Dan Allah karku dakar mana
Umma wallahi inda kudine zan fito maku dashi ...ku
barmu dan San Allah .....
  Karkashin gado ta leka ta janyo jikkar bakko....ta fitar
da tsumman dake ciki sannan ta janyo masu jikkar ta aje
gabansu tana kuka ....
  Huda tayi tsalle tare da dira saman jikkar ta cire
kallabinta ta daure a kugu tana kuka tana fadin ....Wallahi
ko uwayenku zasu zo nan bara ku fita da jikkar nan ba ....
  Barister Shehu ya hankadata gefe guda ta fada jikin
mahmud ....rikeshi tayi gam tana fadin ....karku tafi da ita
Dan Allah ...da itane Mamana zata sakani Js One ....ku bar
mana don Allah ....
  Lumshe ido yayi ya banbareta daga jikinshi ya fita daga
dakin da sauri ..
  Motarsa ya fada ya cire Mask din dake fuskarshi ya jefar
sannan ya data motar ya fita da ita daga lungun da gudu
....ko da ya koma gida Dad dinshi na zaune baki gate
yana jiranshi ...yana ganshi ya taso tare da rungumoshi
yana fadin ....
  Lafiya dae ko .....
 Dauriya ya saka a ranshi ya sakar mashi murmushi yana
fadin ....Alhmd dad ....me kake anan har yanzu ..
  hannunshi ya kama yana fadin ...taya hankali zai kwanta
banga ka kwanta ba har 12 .....
  Baice komae ba sae dae ya bishi da kallo suka shige ciki
...sae da Dad din ya rakashi har part dinshi sannan ya
dawo ya kwanta ....
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA...馃崄馃崄_*
                      馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*
Na Feedohm馃挒
_*DEDICATED TO*_
_EXCLUSIVE WRITERS..._
 9 to 10
      Tunda suka tafi mutanen gidan suka hade guri guda
suna kuka ...mamarce ke karfin halin lallashinsu amma
sam Huda taki shiru sae ma abunda yaci gaba .....bawae
yawan kudin takewa kuka ba ...wae Mamarta ta mata
alkwarin idan har aka samu kudi ta kaita Js one zata
dinga bata naira Hamsin na break  to shi takewa kuka ....
  Saa kadae ta fahimci abunda Huda kewa kuka ...don sae
da mama ta fita sallar asuba sannan ta rarrafa tare da
kwanciya saman cinyar Saa tana fadin ....Yanzu Shikenan
Yaya Saa tunda an dauke kudin mama bara ta dinga bani
naira hamsin din da tace ba ta tara .....ta saka bayan
hannu tare da share hawayen tana fadin ...Allah ya isa
ban yafe ba ...kullun naira hamsin in kashe ashiri na saka
talatin asusu ..don Allah nawa zan tara yaya Saa ...
  Saa tayi shiru tana jinjina rashin wayau na Huda
...bawae kudin suka dameta ba ...aa hamsin din da zaa
bata takewa wannan ihun dama ....share mata hawayen
tayi tana fadin ...Allah zai kawo wasu Huda kinji ..
  Karfe 9:30 na safe barister shehu yazo gidan karbar
kudin wae zaa kaiwa wadanda zaa sayi gidan gurinsu ....
   tunda ya fara magana ...maman huda ke kuka har sae
da ya dasa aya .....sannan ta fada mashi duk abunda ya
faru .....
  Salati ya fara yana dafe kai .....har da hawaye ..yana
nuna yama fisu damuwa da dauke kudin da akayi .....don
cewa yayi daga gidan police station ya nufa zai kai report
dole a nemo wadanda suka sace kudin ......
  Tace .. kawae ya barsu police babu abunda zasu iya yi a
kae ...su sun barsu da Allah ko su waye ...
  Cemata yayi zaya je ya dawo in Allah ya yarda yanzu
...sannan ya mike ya tafi .....cikin kudin da ya sace ya
dauko dubu dari biyar ya kawo mata ....yace tayi jari da
su ......
  Godiya ta dinga mashi har da kukanta ......Huda ta shigo
dakin tayi saurin dukawa gurin mamarta ta ...
  Mamana me aka maki ....dan Allah kiyi shiru idan ma
naira hamsin da zaki dinga bani kikewa kuka ...wallahi na
yafe ki dinga bani arba'in idan kin samu ......ta karashe
maganar kamar zatayi kuka ...
  Huda Lauya ya bamu taimako ...banda bakin gode
mashi ....ku tayani godiya ....ta share hawayenta ...
  Mamana dama ya kawo ya sace.. kuma ya sake kawowa
zai kuma sacewa ne .....ta fada tana kallonshi....
  zumbur ya mike yana fadin ....Huda waye ....nan da nan
zuba ta fara keto mashi ....
    Da hannu ta nunashi tana fadin ...eh mana banda kai
waye yasan muna da kudi ....
  Mamanta tayi saurin buge mata baki tare da korata ta
fice waje tana kwalla ...
tana fita gurin motarshi ta nufa ....ta samu kwalba duk ta
bula tayoyin gaban motar sannan ta bar unguwar ...
  Maman tata ta dinga ba barister shehun hakuri tana
fadin ...Huda yarinyarce karda maganar ta bata mashi rai
....sun gode sossae Allah ya basu abunda zasu saka mashi
dashi .....Yaya Saa ta shigo har kasa ta gaidashi ....ya amsa
cikin faraa da yake ita yana shiri da ita ...ta mike ta fita
...yabi bayanta da kallo yana wani irin murmushi .......
  Sun dan taba hira da mamar sannan ya tashi ya tafi
.....da yake weekend ne gurin mutanen da sukayi aiki tare
ya nufa ...su hudu ya basu 1m suka raba ....sannan ya tafi
da saurin yana ganin yarda akawa tayar motarshi ya
tabbatar da huda CE ..don ta bar mashi sheda a gurin  na
dankwalinta da ta yarda ...kwafa yayi ya bar motar gurin
...sannan ya turo mai gyara yazo ya dauka shi kuma ya
haye okada......Da yake yana business din zinari ...sannan
duk kasuwar kano babu mai katon shagon zinari irin
nashi ...sae ya kaiwa wanda ke sayo mashi zinarin india
kudin duka ....yace cikin satin yaje ya sawo a kara jari
akan wanda suke dashi ....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
  Bayanshi Abba ya dafa ..meke damunka mahmod ....
  Da juyo da sauri tare da goge hawayen da suka wanke
mashi fuska ....
Subhanallah ...wae meke faruwa Mahmud ....ya fada tare
da zama kusa dashi ...
  Bakomae Abbah ....ina so na aje aikine ....ya goge
hawayen da suka zubo mashi a fuska ....
  Kul Mahmud kar na sake jin wannan zancen a bakinka
...shekaranka nawa kana karatun ? ....ka bar iyayenka
tsawon takwas baka kasar ...sannan yanzu ka cika man
gurina kace zaka aje akan me .....
  Ban cancanta ba Abba ......Wallahi ban dace da zama
barister ba ...a matsayina na mai kare hakkin mutane
amma nayi falling akan rayuwar marayu ....
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA...馃崄馃崄_*
                         馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
11 to 12
         Abba yace ...Allah ne bai baka saar karesu bane
Mahmud ...karka damu kayi ta addua wata rana zaka
zama jigon marayu ......tashi muje kayi breakfast kaji ko
.....
       Bayan sun gama breakfast din ya fita unguwarsu
Huda ya je ....ya aje motarshi cikin inuwa ya haye saman
motar yana kallon mutanen dake zirga zirga .....
         Yaya Saa tazo wucewa janye da hannun Huda
....ganin yana kallonsu ya sakasu tsayawa ta gaisheshi
sannan suka wuce ....shigarsu gida da yan mintuna
kadan yaga Huda fito dauke da markade ....
     Mekake kallo tun dazu .....ta katse mashi tunani tare
da kura mashi ido ...
    Murmushin yake ya sakar mata yana fadin ...zo nan
ina zaki ...
       Harara ta watsa mashi ...inda ka aikeni .....
  Zo dan Allah Hudallah ....kinji ko ...wani abu zan
tambayeki ....ya mika mata hannu
   Kaini yanzu an bar hadani da Allah na yarda ....nima
jiya ina ta hada wasu da Allah amma sukaki bar mana
kudinmu ....kaje kayiwa Mamana jaje kuwa ....ko baka
sani ba ....
    Yaya Saa ta leko tana nemanta ....tayi sauri boyewa
bayan motarshi tana fadin ....Dan Allah kace mata ka
ganni nayi nan da gudu tun dazu ....
  Dan murmushi yayi sannan yace ....ki fito ta koma
....sae da ta dan leko sannan ta fito .....da gudu ta tafi
....kafin ta bar layin bokitin markaden ya kife kasa ......
   Da Sauri ya isa gurin ya dagota yana kakkabe mata jiki
tare da sannu ....sannan ya tsince mata wanda bai taba
kasa ba sossae yace ta koma gida a wanke mata....
  Ido ta waro tana fadin ...ka dauka banda hankali ...so
kake mamana ta daman dukan tsiya....baka gani tun
dazu na fito ka tsayar dani da surutu ...
   Ta dauke bokitin ta sake kwasawa da gudu ....gidan
markaden aka wanke mata sannan aka markada .....
  鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
 Malan Ibrahim Headmaster ne na primary ta gwamnati
...mutun ne da yake da kyakyawar dangantaka da
mutanen da yake muaamula dasu ....tun yana yaro bai
cika kwarabniya ba ....su biyu ne gurin mahaifiyarsu sae
daga shi sae Yayarshi hanne ...yana da yan uwa wadanda
suke uba daya su shidda hudu mata sae biyu maza ....tun
da suka taso basa kaunarsu Ibrahim har suka girma suka
zama ware ...wadancan kuma suka hada kansu tare
....Hanne nada ya'ya biyu ciwon daji ya kamata ....bata
dade tana jinya ba Allah ya dauki ranta ....ta bar Malan
ibrahim shi kadae cikinsu ...yaso yaga sun hada kansu
amma sam suka nuna basa kaunar dangantaka da su
...daga karshe ma suka ce sun yanke zumunci da shi
gaba daya  ....haka ya barsu ba dan yaso ba ....ya dawo
cikin garin katsina da zama unguwar kofar marusa inda
yake aiki a matsayin headmaster tare da matarshi guda
daya ...Fatima da ya yansu biyu ...Saadatu sae Huda ......
       Suna zaune cikin rufin asirin Allah ...duk da Huda
bata jin magana hakan bai dameshi ba kullun addu ar da
yake Allah ya shiryata .....Yaya Saadatu kuwa bata cika
magana ba ...sannan ba ruwanta da kowa bata da abokin
fada duk unguwar shi yasa mutane ke mugun ganin
girmanta ....Sae ta dauki son duniya ta daurawa Huda
...bata kaunar taga koda digon hawaye a idon Huda
.....don lokacin da Hudar ke karama ....kullun tana
makale da yaya saa duk abunda ta samu to zata bawa
huda shi ...idan kudib tara aka bata naira biyar to bara ta
kashe ko naira ba sae dae tayowa Huda tsaraba da su
....tana dawowa zakaga Hudar tana tsalle ko hannun wa
take tare da washe baki tana mikawa Yaya Saar hannu
....to har dare bara ta kara yarda da kowa ba sae yaya
Saar ......idan kaga Yaya saa na kuka ta Huda ce take kuka
...sannan idan har tana dariya ta Huda ce ke dariya....Har
mamakin Soyayyarsu ake ...zaa iya cewa Yaya Saa tafi
son Huda Akan iyayenta ....
  Lokacin da suka fara girma ...aka saka Huda makaranta
....idan suka makara to yaya saa zata tara hannu ayi mata
dukanta dana Hudar sannan ta raka hudar Aji itama ta
tashiga nata ...da yake Lokacin Huda na Aji Daya ...ita
kuma yaya Saa na aji shiddah ......
   Barister Shehu makwabtan gidansu Malan Ibrahim ne
...ya yarda dashi matuka ..duk wani abunda ya shafi
gidan Malan ibrahim Barister Shehu yake fada mawa
...da yake ya daukeshi kamar kaninshi tunda baya da
wasu yan uwa da zaya nuna yace nashine ...
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_*
                    馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*馃挕
Na Feedohm馃挒
_*DEDICATED TO*_
_EXCLUSIVE WRITERS.._
13 to 14
             Huda na aji Uku Malan Ibrahim sunje wani taro
da suke na oldboys daura mai adu'a...sukayi hadari
motar ta kama da wuta ...su shidda cikin motar babu
wanda ya fita cikinsu ....a ranar sunga tashin hankali
unguwar don ba karamin rashi sukayi ba ......Sam Huda
bata san me ake ba ...ana zaman gaisuwa ita kuma ta
tara yara suna carafke .....kowa kallonta yake ...
  Bayan kwana goma ne da taga ta rabu da ganin babanta
sae ta fara tambayar Yaya Saa ...ina babanmu
  Sae dae tace mata ...Huda bayana nan ...zaya dawo kinji
ko ...
  Daga bayane ta fahimta sosaae ....shima batayi kuka ba
sossae ...ta danyi yan hawaye da akace mata bara ya
dawo ba ...daga baya kuma ta share hawayen tacigaba
da wasanta ....
  Barister Shehu sae ya koma shi ke kula da duk dan
abinda malan Ibrahim ya bar masu ...mutane sun dan
tara masu taimako...sannan duk abunda ta samu sae ta
sanarwa da Barister Shehun ...Daga baya sae komae ya
tsaya masu abincin da zasuci ma sae ya fara gagarar su
daga baya ma Sae mamarsu Huda ta koma tana zuwa ta
dan taya mamarsu Barister Shehun aiki duk wata ta dan
bata abunda zasuci abinci ...Da yake masu kudine ...
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
    Wae lafiya barister two weeks baka zo office ba .....
  Dariya ya sake da rafu kuka ciwo sannan yace
....Normal Shehu kawae har yanzu ban sake da lamarin
munafikin mutun kamarka bane ....ya karashe maganar
yana dafa kafadarshi .....
   Munafukan mutane dae guda biyu ....ya bashi amsa
tare da fashewa da dariya .....
   Meye Ribarka ciki Shehu ka cutar da marayu wadanda
kae ya dace ka taimaka masu .karamar yarinya tana
rokonku amma ka kasa tausaya mata....Ya tambayeshi a
sanyaye ...
 *_DALILIN YAYARTA_* nake komae shi yasa na tsani
yarinyar don na lura duk abunda bata so to yayarta ma
bata so ....saboda yarinyar yayarta take kina duk da bata
fada man ba .....Barister Mahmoud ina tsananin son Saa
...amma Huda bata sona .saboda hakan Saar ma bata
kaunata ...har gida naje na kaiwa saadatu kudi ta bar
awarar amma taki karba tace suna da abunda zasu
rufawa kansu asiri ....idan suka talauce ba ...ita da kanta
zata zo ta rokeni ni kuma lokacin zanyi amfani da
damata .......
  Ba tare da ya bashi amsa ba ya bar office din don baya
bukatar zama tare dashi .........
    Gidansu Huda ya nufa cikin saa ya ganta ta fito tana
cin goriba ......kwala mata kira yayi ....
  Daga bakin kofar gidansu ta tsaya tana watsa mashi
harara tare da fadin....wallahi yaro ka mayyar garinnan
ta yayeka bara ka ci goribar nan ba .....
   Lumshe ido yayi ya matsa kusa da ita yana fadin ...baci
zanyi ba Huda ....ki shiga kicewa Mamanki ina son
magana da ita kinji ko ...
   Lah bata nan ....tana gidansu lauya tana aiki sae da
marece zata dawo ....ta bashi amsa tana kallonshi ...
  five thousand ya ciro ya mika mata yana fadin ...ki
kaiwa Yayarki ...kice tayi maku cefane kinji ko ...
  Tsaye tayi tana kallonshi kafin ta juya ta shige gida ba
tare da ta karbi kudin ba ....ya dade tsaye yana tunanin
ko zata sake fitowa amma sam babu dalilinta ......
  Ko da ta shiga cikin gida ta iske yaya saa tana wanki ...da
yake yanzu ita kewa yan gidansu barister shehu wanki
suna biyansu ....
  Yaya Saa kawo na dauraye maki ....ta janyo bucket din
da kayan wankin ke ciki ta fara daurayewadaurayewa
   Da sauri ta rike hannunta tana dariya ...barshi Huda
karki jika jikinki ....
  Baran jika ba Yaya Saa ki bari na tayaki ....ke kullun
mutun zaya maki abun kirki sae kice bakya so ....ta
karashe maganar kamar zatayi kuka .....
  Bana so ki wahala ne Huda kinji ko ....zan maki komae a
rayuwarki in Allah ya yarda ba zaki wahala kamar ni ba
....karba ....ta fito da naira goma dake daure a zaninta ta
mika mata ....
  Jiya kince kina so ki sayi dankalin gidan Lado ko ....ga
kudin na samu kije ki sayo sae kici kinji ko ....karki toni
kuwa saman hanya ba ruwanki da kowa ....kinji ko ...
  Kallonta tayi tare da kura mata ido ba tare da ta amshi
kudin ba ...ita tama manta ta tayi maganar jiya ...amma
yaya saa tana rike da abun bata manta ba .....
  Karba kanwata ...ta katse mata tunani tare da janyo
hannunta ta aza mata kudin ta turata waje tana
murmushi .....
  Har lokacin Motar mahmoud na kofar gidan .....ta
kalleshi da idanuwanta da suka ciko da kwallah sannan
ta kauda kai taci gaba da tafiyarta .....
Feedohm馃挒
   鈥⑩€⒙奥�
馃挧馃挧 *_A DALILIN YAYATA馃崄馃崄_*
                       馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
   *_Gaisuwa mai yawa ga haske writers Allah ya kara
basira da daukaka.._*
15 to 16
         Saadatu bakya wankewa su hajiya kaya suna fitane
sossae ....Mama ta fada lokacin da ta kai lomar tuwo a
bakinta ...
  Da Sauri Yaya saa tace ...wallahi mama ina wankewa
sossae ...cewa sukeyi basa fitane
 Aa cewa sukayi wae sae dae kije can ki dinga wankewa
zasu fi fita acan .....amma gaskia ni bana son wannan
yawon Saadatu ...ni ina fita aikatau kema ace kina
wankau ...Sae dae suyi hakuri
   Aa mama zanje ....don Allah ki bari naje ....idan har na
bar wankinnan ban san inda zaa sami kudin da zaa kai
huda secondary ba ...dan Allah karki hanani ...bana so
Huda ta wahala kamarni ..ina son ta samu ilmin mai
yawa ...dan Allah ki bari na nemawa Huda kudin
makaranta da karfina ...dan Allah mama .....hawayen
dake cike da idonta suka samu damar gangarowa saman
kumatunta .....
   Huda ta matso kusa da ita saka hannu tana goge mata
....Dan Allah yaya saa kar kiyi kuka kinji ...ta tabe baki
hawaye na sauka saman fuskarta ...
  Nan da nan yaya Saa ta maida hawayenta tana lallashin
Huda ...Mama na zaune ta zuba masu ido .....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
  Table din dake gaban Barister Mahmoud ya buga da
karfi yana fadin ....Meye dalinlinka na bincikar shaguna
na
  Idan table din ya amsa to barister mahmoud ya amsa
masa ....
  Wallahi Mahmoud ka kuskura maganar nan ta fasu na
rantse maka da girman Allah sae na watsa ka a duniya
...sai na saka ubanka da kake takama dashi ya tsaneka da
ka shi zai koreka ka fitar mashi da gida ...Don wallahi
bani kadae zan dauki laifinka har da kai ...sannan ka sani
inda kyakykyawar hujjar da kai akayi fashin .......
   Then   So what  idan ka fadawa duniya har dani akayi
fashin ....kai duniya ta dama amma ina tabbatar maka
wallahi asirinka yana gab da tonuwa..
掳掳鈥⑩€⒙奥�
  Dady wani abokin aikinmu ne ke cikin matsala wallahi ..
  Dady ya kalleshi tare da fadin ..
Subhannallah meke faruwa dashi ....
  Lumshe ido yayi sannan yace ...Wae wasu sukayi
forcing dinshi yayi fashi a wani gida ....
  Ya so ne Mahmoud ....sam bai kyautawa aikinshi ba da
iyayenshi ...
  Dady dole ba aka mashi ....
  Mahmoud na san idan kaine ko zaa daura maka bindiga
bara kayi ba ....kabar wannan maganar ....Allah ya kyauta
..
  Ameen amma dady ...
  hannu ya daga mashi     ....akul Mahmoud ....gobe ka
shirya zamu je kauye akwae diyar Kawu Nalado da yace
ya baka ka aura  ....
  Aure dady ....ya fada a firgice ....
 Nima umarni aka bada Mahmoud Allah yasa Alkhairi ce
.....
 Ba tare da yace komae ba ya sadda kai ...kirjinsa ke
dakan uku uku ....addua yake karantuwa har ya samu
natsuwa sannan ya mike ya fice  falon....
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
Kamar yarda Yaya saa ta fadawa mama haka take zuwa
kullun gidansu barister shehu tana wanki sannan ta
dawo ta baro mama gidan .....A lokacinne Huda tayi
jarabawar fita daga primary school .....bayan jarabawar
ta fito ta samu Government day dake kusa dasu .....
  Yaya saa tace bara tayi government ta tara kudin da
zata kaita makarantar kudi ....ita da kanta ta kaita
makarantar ta mata registration da kudin da take
tarawa......
  Ranar da ta kaita makarantar ta juya zata tafi taga
discipline  dinsu ya daga bulala zaya daki Huda ....tayi
saurin dawowa ta rungumeta tana rokanshi kar ya
daketa sabuwar zuwa ce .....
  Huda kuwa girgije girgije take tana fadin ...yaya saa
barshi ya tabani bai san Hudalliya bace ...yaro kaje
unguwarmu ka tambayi yarda nake kada katti kasa ina
duka ...
  Yaya Saa tacewa malamin ...dan girman Allah kayi
hakuri ka barta tana da matsalar aljanu ne shiyasa bata
ji..
  Ido ta waro tana karkade kunne ....zuki ....Kai yaya saa
dan dae kece da sae ince ...Mamanki ta saka man su
....amma kiyi hakuri kinji ko ...
  Bata ce mata komae ba taci gaba da bawa malamin
hakuri wanda yace ...idan duk duniyace gatanta sae ya
daketa tunda bata da kunya.....
  Ganin yaya saa na kuka ya saka malamin kyale Hudar ....
Feedohm馃挒
馃挧馃挧 _*A DALILIN YAYATA馃崄馃崄*_
                         馃崄
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION馃挕_*
Na Feedohm馃挒
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
       _*Thank you so much sweet HAJJA....YAS鉂�..komae
naki daban yake da na saura .....!..I Hhp am the first to
wish you Happy birthday ASMY馃憚 ....WULLNP.....!..Best
wishes UMMI A'YSHA..Kdeey ..Ayusher..Kubrieh CIE...billy
galadanchi..Maman Khadija ...Asy darling ...khadeeja
chafe ...Khadija candy ...jeedah Aliyu ..Billy BB...Nafee
Anker.. Amnoor ... Queen Mermue ...IRSY馃槝*_
*17 to 18*
      Zaman Yaya saa gidansu barister Shehu ...Sae ya fara
kawo mata salo daban daban ..
   Idan tana zaune inda take wanki sae barister shehu ya
dinga zuwar mata da zancen banza ....tun bata kula shi
har ta fara jin tsoronshi ...don tana zaune sae taji mutun
ya shafa bayanta ......
  bata taba fadawa kowa ba sae dae tayi ta kuka ....don
kwata kwata bata jin dadin aikin yanzu ...Sae tana zaune
sae Shehu ya dinga kokarin taba mata kirji ....Sae tayi
niyar Barin aikin sae ta tuna da Huda dake makaranta ....
  Yau ma  bayan ta gama wankin  tana tsaye tana shanya
kayan ...Shehu yazo ta bayanta ya rungumeta ....ta fara
kokarin kwace kanta tana kuka ...yaki sakinta sae ma
kokarin sakamata hannu yayi a cikin riga ....hajiyarshi ta
leko tana fadin ...
  "Shehu wane irin shashanci ne wannan"...!
   ya juyo a firgice yana kallonta ....Yaya saa kuwa wani
sanyi taji a ranta ta saka bayan hannunta zata goge
hawayen ....cak ! ta tsaya lokacin da hajiyar ke fadin ...!
    "Idan sha'awarta kake bara ka jata daki ba sae ka tsaya
waje salan uwarta ta fito ta ganka kuma ka ja mana
tsegumi ".....!
    Bai jira komae ba ya fizgeta da karfi ya shiga da ita
dakin dake kusa dashi ...wani ihu ta saki tana turje turje
tare da hadashi da Allah ya barta amma sam yaki barinta
...sae da ya rabata da darajarta ta ya mace ....sannan ya
janyota kamar kayan wanki ya wurgota waje inda take
wankin ya koma daki.....
  Hajiyarshi kuwa tana shiga ta iske mamarsu Huda na
goge goge ....tace mata.." ta tafi gida zata fita unguwa".....
  Mama tace mata ...."To bara na kira Saadatu tana baya
tana wanki "....
  Hajiya tace ..."aa ki barta na aiketa nan makwabta ta
karbo man sako" ...
  Mama tace ..."to Na tafi hajiya Allah ya kiyaye ".....!
  Yaya Saa lokacin da hankalinta ya dawo ta hade kai da
guiwa tana kuka kamar ranta zai fita ....ga uban radadin
da ke damunta ....haka ta ja jikinta ta fice daga gidan
tana kuka ......
  Zata shiga gida ta ga Huda ta dawo daga makaranta
rataye da jikka .....baya ta koma ta lafe jikin bango gudun
kada Hudar ta ganta tana kuka hankalinta ya tashi ...har
sae da hudar ta shige gida sannan itama ta share
hawayenta ta shiga gidan ...
     Bata bari Mama ta gane halin da take ciki ba ...sae dae
Huda da ta kamata tana kuka bayan ta gama sallah isha'i
...!
 " Yaya Saa me aka maki ."...ta tabe baki ...nan da nan
idonta ya kawo ruwa ...
  Jikin Hudar ta fada tare da sakin kuka ....Hudar ke
girgizata tana kuka ...."Yaya Saa dan Allah kiyu shiru ...me
aka maki dan Allah ....waya tabaki Yaya ...Yaya Saa dan
Allah ki fada man ".
  Girgiza mata kai take tana kokarin tsaida kukan amma
sam ta kasa ....ita da Hudar ke kuka kamar ransu zai fita
....Yaya Saa ta kasa fadawa Hudar asalin damuwarta
....tama rasa bakin da zata mata magana ...bata so Hudar
taji abunda ya faru da ita saboda tasan Huda sarae zata
iya rike abun a ranta har abada ...
    Mama ta shigo ta iskesu haka ...tambayarsu take meke
faruwa amma babu wanda ya bata amsa ...da taga abun
bana karewa bane ta zauna ta zagesu tsaf tace su mata
shiru ko su fitar mata daga daki ...idan bara su fada mata
damuwarsu ba ......Yaya Saa ta fara shiru sannan ta
lallashi Huda da kyar ta samu tayi shiru ...
鈥⑩€⒙奥扳€⑩€�
    Karfe 3 na rana su Barister Mahmoud suka isa kauyen
....Kawu ya masu tarba mai kyau aka kawo masu
madarar shanu da dambu ....Mahmoud kasa ci yayi sae
dae yasha madarar kadae ...
  shi kuwa dady zama yayi yaci ya koshi. ...Inno ta shigo
suka gaisa sannan ta fita
..Kawu yace "a kira Hanne "...
*_Feedohm馃挒_*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                🍁
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS_
   *_Nagode sossae da addu'o'in Ku Allah ya saka da
Khairan💞_*
 *19 to 20*
           Kaninta ya fita da gudu ya kirata dandali.....Ko
minti 10 baayi ba sae gata da tawwagar Yara sunzo ga
nin mijin da zata aura daga birni ....
  Gaban Mahmoud  din ta zube tare da kura mashi ido
tana dariya ..
    sannan ta juya gurin kawayen tana fadin ....Kun ganshi
nan irin mutumin nan na jikin Rigar dan mai gari
....!!..Wohoho no Hanne Duk kauyen nan albarka !!
   Hanne diyar kawu nalado ...irin mutanan nan ne masu
shegiyar karya da iyayi .....bata cin abincin gidansu ta
gwammace ta sayi malak'i ....saboda inno bata sanya
masu kayan miya kamar yarda gidan maigari suke nasu
girkin .!!...Irin yaran nan ne masu hange hange ..baka da
gashin wacce kace sae kayi kitson wance ....!!
    Doguwace Jawur tana da kugu sossae da tsawon gashi
...amma kirjinta ba wani cikakke bane ....tun lokacin da
kawu nalado ya fadawa Hanne cewa zata auri Mahmoud
take ta murna don bata kaunar rayuwar kauye duk da
acikinta ta tashi .....!!
   Sae ma ta daina hudd'a da yaran da take hudd'a dasu
ya'yan talakawa kalarta... ta koma sae Ya'yan gidan
Maigari da masu kudin kauyen take hudda ...!!
  Su Mahmoud basu tafi kauyen ba sae da aka daura
aurenshi da Hanne .!!...duk da dama ba da shirin aure
suka zo ba ...amma kawu Nalado yace ba abunda zasu
jira ayi komae a gama su tafi da ita ....nan take suka bada
sadaki aka daura ....su hanne sae murna ake ....Bangaran
Mahmous kuwa tunda ya sadda kai bai kuma dagowa ba
...zufa ke biyo mashi ta ko 'ina ..."Innalillahi wa inna
illaihir raji'un" kawae yake ..."Allahumma Ajir ni fi
musibati "...kuwa ya furta ta tafi dari.!! ...
  wannan wace irin masifa ce ..!!!.abunda yake fada a
ranshi kenan .....har aka gama daurin auren ....!!
   Ko a mota bai iya furta koda kalma daya ba ...sae
Hanne dake ta karadi Abbah na biye mata ....!!
  Gidansu Mahmoud din ta zauna kafin ya ida gyara nashi
....Momy ba ta iya cewa komae ba sae fatan alkhairi data
mashi ....
••°°••
  Tunda Shehu ya ma Yaya Saa fyad'e bata kuma zuwa
gidan ba ...haka mamanta kuma bata takura mata...sae
dae tayi tambayar duniyar nan ta fada mata me ke
damunta  .....!
    Bayan wata daya ne Yaya Saa ta fahimci tana da ciki
...domin har lokacin menstruation din yazo bata ganshi
ba ...sannan ga wani canji da take ji a jikinta ....
  Hankalinta yayi bala'in tashi sam bata da sukuni duk ta
bi ta rame kullun cikin kuka take ...ga bala'in tashin
zuciya da take ...abun kadan zaya sakata amai ...
  Tana tsugunne a kewaye tana amai gidan ba kowa
....Taji an dafa mata baya ...ta juyo a firgice tana kallonta
...ganin Huda ce ya saka ta sake a jiyar zuciya tare da
janyo buta ta wanke bakinta ta mike ...
  Daki suka shiga Huda na rike da hannunta ta zauna
saman gado tare da kara janyo Hannunta tana fadin ..!
   "Me ya sameki Yaya Saa ...sannu kinji" ...cikinki ya
kumbura ?....ta fada tare da kura mata ido...
  Hawayen dake fuskar yaya saa suka samu damar
gangarowa ....tana girgixa kai ...
  "Kiyi Shiru mana Yaya Saa ...me kika ci ya kumbura
maki ciki...bara naje gidansu Fatse na karbo maki
maganin kumburin cikin kinji ko ...sannu" .....ta mike da
niyar fita ...!
  Yaya Saa tayi saurin kamo hannunta tana fadin
..."Hudallah ! ...
 " Na'am Yaya saa" ...menene ko tafasar jiya ta bata maki
ciki ...?.
  Girgiza mata kai tayi tace ..."Huda maganin da kike
kokarin karbowa bara ya iya man magani ba !!...
  Dariya tayi ..."haka zaki ce Yaya saa bawae ki rikeni
ba ! .."to bara na kira mama gidansu lauya sae mu kaiko
asibiti su baki magani ...sae su rubuta sunana idan na
gama makaranta na fara aiki sae na biyasu ko? ....ta mike
da sauri ...
  "Tsaya Hudallah "....ta fada a hankali ..."karki fadawa
Mama hankalinta zai tashi kinji ko ...ki barshi tsakaninmu
karki fadawa kowa ina amai" ..
  "Sirri Yaya Saa ..!!....ta fada tare da dafe baki tana waro
ido ...!
  "Sirri Hudallah!! ...ta bata amsa..
""Sirrin Amai !!!...ta kara tambaya cike da mamaki ...!
  "Bara ki iya rike sirrin yayarki ba Huda ?...
  "Zan iya mana Yaya Saa ...ko mama baran fada mawa
ba ..sae ma nacewa mutane Yaya Yar baiwa ce bata amai
....Sannu kinji Yaya saa ..Allah ya baki lafiya ...Allah ya
isarmu mai tafasar nan da ta sayar mana ...muguwa shi
yasa naga tana kallona ...kila ma ni taso cikin nawa ya
kumbura."..!!
  Bata ce mata komae ba ta mike ...surfen da aka kawo
mata ne ...ta dauka tayi ...sannan ta bawa Huda kudin ta
saka Jikkarta ta makaranta gobe tayi kudin Tara...!!
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAAYATA🍁🍁_*
                   🍁
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_21 to 22_*
            Hanne!!!...irin matannanne masu shegen kilbibi da
karya ....watanta biyu gidansu Mahmoud ta waye ta goge
kamar ba ita ba ...kafin kace me tayi kawa makobtan
gidan ....mai suna Saly ...haduwarta da Saly sae idonta ya
sake budewa ...don kullun saly na gidansu Mahmoud
tana kara budewa Hanne Ido ...kadan kadan sae ta fara
zabgawa Maman Mahmoud Rashin kunya ....sannan idan
an dafa abinci bai mata ba sae ta saka a sake dafa wani a
zubar da wancan ...
  Abun ya fara damun Momy gashi bata son ta fara kai
karar Hanne gurin Abba ...sae yaga kamar bata son zama
da ita ....
  Momy na zaune ta rabka uban Tagumi ...Abba ya shigo
tare da Mahmoud suna fira kadan kadan ....Hanne ta
sauko daga upstair ta tsuke da riga da wando three
quarter .....tana ganin Mahmoud ta sake fuska tare da
tahowa tana murmushi
..
  Babu kunya tayi niyar fadawa jikinshi ...wani kallon ya
sake mata babu shiri ta sulale kasa tana gaida Abba ....
  Abba yace " Hanne ki shirya zamuje kauye an kirani
babanki baya jin dadi .."
  Ta hade Fuska tana Fadin "ni gaskia Abba baran je
...idan kunje ku gaidashi .."
  Akan me? ...Abba ya tambaya cike da Mamaki ...
  Gaskia Abba yanzu lokacin damina ne ...nasan gidan
duk ya kazance da kashin goat da cow da chickenks
...kuma inno ba iya gyarawa zatayi ba ...ni kuma baran je
wari ya isheni ba ...
  daga Momy har Mahmoud sakin baki sukayi suna
kallonta ...Abba kuwa dariya ta bashi ..wae Goat da cow
da chickenks .
..
    Hanne Manya...!! ...ya fada lokacin da yake kallonta ...
   Mahmoud yace " Abba da yaushe zaa tafi ?...fuska
daure
  Gobe Mahmoud ....ya bashi amsa ...
 Ke !! ...ki shirya gobe da safe zamuje kauyenku!!!,...ya
mike ba tare da ha sauri kowa ba ya shige daki ...
  Momy kuwa cewa tayi ." Allah ya kyauta .." ..sannan ta
mike ta fada kitchen itama ...
••°°••
  Maman Huda na tsaye tana goge goge .. Barister Shehu
ya fito daga daki fuska daure ....ya zauna bisa kujeran da
take kallonta ...
  Malama ...daga yau karki kuma zuwa aiki nan gidan an
sallameki !!!!...ya fada tare da daukar remote yana
latsawa ..
  Maman Huda tayi sararo tana kallonshi cike da mamaki
kafin ta danyi murmushi tace .,." Lauya wani abu ya faru
kuma ?...
  Lokacin da nace kizo ki dinga taimakawa Hajiya kin
tambayeni dalili? ...ya bata amsa yana kallonta ...
        "To ....Me yayi zafi Haka lauya ? ..."bara na samu
Hajiyar idan wani abu nayi mata sae na bata Hakuri "...
  Ba sai kinzo ba ...!!..gani nan fitowa ....hajiya ta fada
lokacin da take fitowa da part dinta ...
  Sannan ta ci gaba ..." Da kike son zuwa gurina ...dama ni
daukeki aikin ? ...ina jin Shehu ne .. kuma yace ya
sallameki to meye na sauran magana ? ...
  Maman Huda tayi tsaye rike da tsumma tana kallonsu
...a iya saninta babu wani abun da ta aikata ba dae dae
ba  ...ta ko don Saadatu ta daina zuwa ne? ...ta tambayi
kanta arai...
  Tace "Kuyi Hakuri Hajiya idan dan saadatu ne wallahi
har ga Allah bani na hanata zuwa ba ..!! ...
  Wake maganar sakaran yarinyarki yar iska...!!! ...Hajiya
ta katseta tare da zabga mata uwar harara ...
  Yar iska ....?...ta fada lokacin da idonta ya ciko da kwalla
...
  Eh Yar 'iska matsiyata ...barister Shehu ya bata amsa ...
  Wallahi diyata ba yar'iska bace sae dae kaine dan iska
...arziki da talauci duk na Allah ne ...!!!ta basu amsa a
fusace ...
  Bata rufe baki ba Hajiya ta dauketa da Mari tana fadin
.."Allah ya mana katanga da talauci ...fice mana daga gida
tun kafin na saka a futa dake  ...bara kizo har gida ba kina
kiran dana dan'iska na zuba maki ido ba ....kama hanyar
akurkunki tun kafin na sakashi ya maki shegen duka
gurinnan...
  Allah ya baku Hakuri ...Abunda ta fada kenan tare da
fitowa daga gidan ....ko gabanta bata gani sossae har ta
isa gida ...
  Ganin yanayinta ya saka Yaya Saa tayi saurin kamota
tana tambayarta lafiya..
  Lafiya mama ...me ya faru ?..me suka maki..?...ta
tambaya a rude ...
  bata boye mata komae ba ta fada mata duk irin
wulakancin da Barister Shehu da hajiyarshi suka mata
...daga saa har Maman kuka suke kamar ransu zai fita ..
  Huda dake tsaye jikin kofa tana jinsu ....ta fita da gudu ..
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                        🍁
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_23 to 24_*
            Ta fitaa da gudu daga gidan ... ..bata tsaya ko'ina
ba sae kofar gidansu Barister Shehu ...Wai dadi taji ganin
ba maigadi a kofar gate din.. ...ta kutsa kai ta shige cikin
har tsakiyar  falon ...babu kowa a cikin ...katuwar Plasma
dake falonsu ita ta nufa ta fito da duwatsun dake cikin
jikkarta ta makaranta ...ta dinga bugawa da karfi ...kafin
me plasmar duk ta farfashe ...sannan duk wani abunda
tasan na glass ne sae da ta fasa shi..harta windows din
dake cikin falon sae da ta fasa...!
     Jin karar Glass yasa Hajiyar fitowa da sauri daga sink
din wanka. ..ta daura towel  ...don duk tunaninta daga
waje karar ke fitowa sae da taji tabbas daga falon take
fitowa Sannan ta fito daga toilet ....tana fadin  ..
    "Waye anan ? ..."nace wane shegene ya shigo yake
mana barna...? ...cak ta tsaya ganin karamar yarinya rike
da duwatsu duk ta farfasha masu kayan dake falon ...!!
    Nice nan Hudalliya ....ta fada tare da runtumawa da
gudu ta fita daga falon ...hajiya ta bita da gudu tana fadin
..
       Bala rike man wannan shegiyar yarinyar karka bari
ta fita ...!!!...ganin babu maigadi ya saka Huda sake
juyowa tare da jifar Hajiya da wani dutsin sannan ta fice
da gudu ...!!
  Da sauri hajiyar ta dafe gefen idonta da dutsin ya
sameta ..kafin zafin ya saketa Huda ta bace mata da
tunani ...!!
     "Wace Shegiyar yarinya ce wannan ? ..take tambayar
Kanta ..yar gidan wane shege ce ? ...me muka mata dan
ubanta ?..."Hurul ..aa Hudiya...mts ...aa ba haka tace
sunan ba" ...ta fada tare da dafe kanta tana son tuno
sunan ...Da yake bata san Huda ba ...don duk da suke
zuwa Huda bata taba biyo Yaya Saa ko Mama ba ...
  Barister Shehu ya shigo rike da friut din da Hajiyar ta
aikeshi sawowa tun bayan fitar Maman Huda ....turus
yayi yana kallon hajiyar da ta zabga uban tagumi zaune
tsakiyar falon ...
    "Yan Fashine suka zo Hajiya? ...ya tambaya a rude  ...
    "Yan fashi ko shegiyar yarinya Shehu ?...ta bashi amsa
tare da mikewa tsaye..." wallahi wata shedaniyar yarinya
ce ta shigo duk ta mana wannan barna ...ban san ko yar
gidan uban wa cece ba ...amma tace ko Hurus ...wallahi
sunan ya shige man ...amma zan saka a nemo man ita
cikin unguwar nan ..."
  da Sauri yace ..."ko Hudallah? ...
       "Ba Hudallah ba Shehu ...na manta sunan ...amma
wallahi duk randa na kamo ta taja wa ubanta bala'i dan
baran kyaleta ba ...har da ni fa tayiwa ruwan duwatsu
Shehu ji binan Yar da idona ya kumbura"..to meye
hadinmu da ita ..?..
    "Hajiya kinga yi man kwatancen yarda yarinyar  take
...na tabbata Huda ce wallahi "...
    "To wacece ita Huda? ..."na fada maka ba haka sunan
yake ba" ..."itama da Hu din sunanta ya fara amma nata
sunan ban taba jinshi ba ."..
   "Huda diyar mamansu Saadatu ce wadda aka kora yau
...kuma nasan yarinyar sarai bata da mutunci ...bara
yanzu zanje idan ma itace ta sake jawa uwarta bala'i ....!!!
  Ya fita da sauri ...ko mota bai dauka ba ya taka kasa
....baiyi Sallama ba ya fada gidan a fusace ...Mama na
tsugunne ta rafka uban tagumi ...Yaya Saa tana wanke
kwanukan da suka ci abincin safe dasu ...
  Su duka suka mike tsaye ganinshi ...
     ya Nuna Mama da hannu yana fadin ..."Ina
shedaniyar diyarki ? ....
  Ran mama idan yayi dubu ya baci ta kalleshi a fusace
zata yi magana yaya saa ta rigata ...
      "Bamu da Shedaniya a gidannan ....amma akwaita a
gidanku mai dattin da kwali sabon shigan arziki ...banza
maciya amana jahilai ...!!! ...ta fada tare da rushewa da
kuka ...
  "Rufe man baki Shedaniya ...akwae shedan irinki mai
bin maza ....shegiya karuwa..!!!
  Mama ta daukeshi da mari ..."Karya kake Shehu har
yanzu ban haifi Karuwa ba Wallahi kuma baran taba
haihuwarta ba " ..!!
    Ni kika mara ? ...ko da yake ba komae bane tunda har
na kwanta da diyarki !!..zafin ba wani bane da zai dameni
....don ko kadan bai kai zafin da zakiji ba alokacin da kika
fahimci diyarki karuwar Shehu ce ..!! ..don bana tunanin
ban bar maku yaron da zaku raina ba na Shehu ..ko a
tunaninku mutuncin da nake maku sonku nake ..? mtsee
Jahilai ...to Sha'awar diyarki nake kuma fine ta kawon
budurcinta har gadona ....!! ...ba wani shegen da iyasa ya
tsaya maku ..matsiyatan banza!!
  Wani wawan mari yaya saa ta dauke shi dashi ..tare da
sakin kuka ...bata sauke hannunta ba ..Mama ta dauketa
da mari itama tana kallonta cike da tuhuma ....!!
  Sulalewa Yaya Saar tayi bisa guiwarta tana fitar da wani
irin gujin kuka ....!!
  Dariya Barister shehu yayi tare da fita daga gidan ya
barsu cirko cirko ...yaya Saa na tsugunne Mama na tsaye
tana hawaye ...
  A zaure yazo fita sukayi karo da Huda ...wani mugun
kallo ya aika mata ....itama ta sake mashi nata ...sannan
tayi cikin gidan da gudu jin kukan yaya Saa ....
  Yaya Sa 'a ....dukanki ki ya kuma ?....ta fada tare da
dukawa kusa da ita ...
  Mama ta saka hannu a fusace ta janye Hudar Gefe guda
tare da dauke yaya Saa da mari ta janyo kwalar rigarta ta
dago kanta ....!
       "Fada man Sa'adatu' ...fadan man gaskia abunda
Lauya ya fada hakane ?..ko karya ya maki Sa'adatu?..ta
fada tana kuka ...
   "Wallahi karya ya mata Mama!! ...Huda ta fada ba tare
da tasan abunda ake magana akai ba kawae ta tsinci
maganar ne...
  "Yi man shiru Huda dan Ubanki ...!!!..mama ta kwasa
mata tsawa ....firgitar da tayi ya sakata fadawa jikin yaya
Saa tare da sakin kuka ..."Fada man Saadatu "...shin na
haifi karuwar Shehu kamar yarda ya fada?.. koko sharri
ne .!!...
  Cikin Kuka Yaya Saa tace  .."wallahi Mama baki Haifi
karuwa ..ba laifina bane  Fyad'e yayi man mama ...!!
   Wani uban duka ta kai mata tana kuka da karfi ....Huda
ta rike mata hannu tana kuka ...
    "Wallahi Mama Hard'e yayi mata ".....ta leka fuskar
yaya Saa tana tambayarta ...Yaya Saa Hard'e kika ce
ko? ...
  Fizge Huda tayi daga jikinta tana dukanta ba tare da
tasan inda take duka ba ...su duka ukun kuka suke kamar
ransu zai fita...
  "Dan Allah Mama ki kyaleta na rantse maki da Allah
Hard'e yayi mata ..!! .mama wallahi agabana yayi mata
...har cewa nayi karka yi mata Hard'e amma yaki
saurarena !!! ...kuma wallahi Yayata bata Amai kullun!!!.
....Mamarmu dan Allah ki bar dukanta ..bana so ..!!.....ta
karashe maganar tare da rike hannun mamar  tana
kuka...
  Wani Uban Mari Mamar ta bata ' ..kafin ta hankadata
gefe guda ta cigaba da dukan yaya sa'a ...amma Huda
dawowa tayi jikin  yaya Sa'ar mama ta ci gaba da
dukansu a tare ...
  Jikin Mama har ky'arma yake ...jin zata fadi kasa ya
sakata jingina da bango tana kuka ....sannan taja jikinta
ta shige daki ta barsu tsakar gida !!
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                     🍁
*_HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITER'S..._
*_25 to 26_*
    Da marece Mahmoud yazo kofar gidansu Huda ya aje
motarshi ...jingina yayi yana jiran ko Huda zata fito
...don so yake yau yayi magana da mamanta ....
  Cikin saa ta fito idanunta jawur tayi kuka har ta gaji
....bisa dakalin gidan ta zauna tare da hade kanta da
guiwa ....
  A hankali ya tako ya iso gurin ya zauna gefenta ..yana
kallonta..
   " Hudallah"....
 dagowa tayi tana kallonshi kafin ta kalli motarshi ta sake
maida kanta gurinshi ba tare da ta amsa ba ...
 a hankali yace "Me aka maki Huda? ....wani abu kike
so ? ..
  Kai ta girgiza mashi a hankali tana goge idonta ....
  "To fada man mana ' ...ko mamanki ta dukeki? ...
  nan ma kan ta girgiza mashi tare da kura mashi ido ...
    "To Yaya sa'arki aka batawa rai? ...yauwa Hudallah
goge hawayen kinji ki fada man ...oya Yaya Sa'a ce? ..ya
fada cikin sigar lallashi ..
  Daga kai tayi tana fadin ..." Ba lauya bane ya cuci Yaya
Sa'a yayi mata hard'e ...kuma sae da nace kar yayi mata
...amma yaki jina!!  ..gashi yanzu ya saka mamanmu sae
dukanta take ...tana kuka ..."
  Hard'e ? ...mene haka Huda?....!
 Harara ta balla mashi tana fadin " karka maidani yarinya
mana ...kato da kai baka san Hard'e ba ....wanda idan
akayiwa mutanen gidansu suyita kuka??? ..ko baa taba
maka bane?..
  Shiru yayi yana tunanin me take nufi ...zuwa can yayi
saurin kallonta yana fadin ko dae Raping kike nufi ?
  Ba tare da tace mashi komae ba ta mike zata shige gida
...yayi saurin riko hannunta yana fadin ..." Tsaya man
Huda kinji ....please idan kin shiga gidan kice ina son
magana da mama ...!!
   " amma kai mugune ...!! ..baka ga irin marin da ta man
ba yau" kake aikeni na mata magana ...so kake ta sake
marina kenan. ?
  kamar yana tsoronta yace " Please Huda ki taimaka
kinji ko "...
  "Idan ta dakeni ' kanka zan rama wallahi "
 Da sauri yace " Na yarda Hudallah "
  Shiga tayi ciki zuwa can ta fito tace mashi Idon mamar
a rufe yake ....ta mata ...magana taki budewa .....ce mata
yayi taje tacewa Yaya Sa'a dan Allah yana son magana da
ita ..
  Kafin ta bashi amsa yaya sa'a ta fito daga gidan da gudu
tana kuka ...tare suka shiga gidan har da Mahmoud din...
   Mama na kwance bata motsi daukarta yayi da sauri ya
sakata mota sannan yaya saa da huda suka shiga ciki
suna kuka sannan yaja da gudu suka fita daga lungun ...
   Direct asibiti ya nufa da ita ...cikin gaggawa aka
amsheta ....bayan an dubata ne aka tabbatar masu da
tana raye ..hawan jini yayi attacking dinta sossae ... Bp
dinta 210 ...
  Daga Hudar har Yaha Saa kuka suke ...Barister
Mahmoud kuwa tsaye yayi yana kallonsu ..shi ya biya
kudin komae ...aka hada mata magunguna ..
  Har isha'i yana asibitin ...sae da ta daeo normal sannan
likita yace zaa sallameta su tafi gida .....
 Barister Mahmoud ya dauko su ya kawo su gida ...da
zaya tafine ya fitk da 20k ya bawa mama yace su sayi
abinci kafin ya dawo ..
  Sam Mama taki karba ...tace wanda ya mata bata sani
ba ta gode amma wannan bara ta karba ba don yanzu
bata bukatar taimakon duk wani mutun Taimakon Allah
kawae take so ...Babu irin rantsuwar da bai mata ba
...amma taki karba ...
  Ganin yafi damuwa da Huda ne ya saka Yaya Sa'a saurin
janyo huda jikinta tana hawaye ...don bata kaunar wani
namiji ya kula Huda yanzu .....a iya saninta zata iya kashe
duk wanda yayi kokarin batawa Huda rayuwa ...
  ganin kamar basu bukatar shi ya sakashi tashi ya tafi
...zuciyarshi cike da tunanin maganar huda ..."wae
Hard'e"...what does she means? ...haka yayi ta sake sake
har ya isa gida ...
  Yana Shiga Mama tace ya dauki matarshi ya tafi da ita
...don wallahi ta gaji da Hanne ....!!!...
  Ba dan yaso ba ya shiga dakin Hanne tana kwance sae
barcinta take hankali kwance ....pillown da ta daura
kanta ya dan buga kadan
   ta mike ba salati tana fadin ..."wane banzane mutun na
bacci yake tadashi ?
   Ba tare da yace mata komae ba ya juya zai fita ..."sam
hanne ba da'a" ...abunda ya fada kenan a ranshi ...
 hannunshi ta riko "Ohhhh ...Yaya ne  ....Yi hakuri bansan
kai bane yasin" ....ta fada tana dariya
   ba tare da ya juyo ba yace " ki iskeni falo zamu tafi
gidan yau" ...
      Ihun dadi ta sake tana fadin " Haba yanzu  naji
magana amma an kunshe mutun cikin gidan sirikai ba
damar ya sake sae shegen sa ido "...
   Ko nuna alamun yaji me take fada baiyi ba ...ya fice
daga dakin ...kafin ya zauna har ta fito janye da uwar
jikkar ...
  Mamanshi yayi wa bankwana tare da Abba ...sannan
suka tafi ..da yake bai ci komae ba ..ya tsaya wani
karamun restaurant zai sayi abinci ...
  Hanne tace " haba yaya me zaka saya a wannan
karamin gurin dan Allah? wallahi ba girmanka bane ...!!
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                      🍁
*_HASKE WRITER'S ASSOCIATION💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITER'S..._
*_27 to 28_*
           Dan juyo yayi kadan yana kallonta cike da mamaki
kafin yace " banda wani girma Hanne ..sae dae ke nake
tunanin girmanki yakai diyar sarki a babban kauyenku !!!
  tasan magana ya fada mata sae ta kulle bakinta tayi
gum ....har suka isa gida bata kara magana ba ..bareshi
da ba kowa yake kulawa ba ...
   Gidan ya dan nunnuna mata sannan ya shige dakinshi
ya barta hangame da baki ...
••°°••
  Da kyar Yaya Sa'a tayiwa Mama bayani ta yarda ...ranar
tace su tashi suje gidansu Barister Shehu ta fada ubanshi
wata kila shi ya sauresu a bi masu Hakkinsu ....
   Da Mama da Yaya Sa'a sae Huda suka tafi ...cikin saa a
harabar gidan suka iske su duka ukun tsaye da alama
wani guri zasu ....sae sojojin dake tsaye cirko cirko
   Hajiyar na ganinsu ta daure fuska tare da kallon Shehu
....Mama ta iso ta gaida Alhajin ...tun yarda ya amsa mata
gaisuwar jikinta yayi sanyi ...
  Tace " Alhaji nazo na sanar dakai abunda ya faru ." ..
  A wulakance yace "ina saurarenki"  .
  tace " Alhaji mu talakawa bamu da komae sae Allah ...ni
da diyata muna zuwa aiki anan gidan ...sae Shehu ya
haye mata har ya mata fyad'e ...shine nazo na fada maka
ko akwae matakin da zaka sauka "
   "Bullshit kauyawan banza da wofi!! ....matsayita!! sae
uban me dan yayi Raping dinta ....kanta aka fara raping
koko kanta aka kare ....? ..Kai Shehu ko yanzu kake
bukatar Yarinyar nan ...na yarje maka kayi abunda kake
so da ita ....gidan ubanka suka shigo .,
..basu isa su wulakanta me ba har gida...!!!
      "Dat my dady "....ya fada yana aika masu wani irin
matsiyacin kallo ...!!
  Dad din yace ..".Guard !!....ku fitar man da wadannan
matsiyatan ku bar waccen ...!!! ya nuna yaya Sa'a ...
  Da saurin Mama ta rugumeta tare da janta da gudu
zasu fita daga gidan ...amma kafin su fita wani daga
cikinsu ya fizge yaya Saa tare da tura mama da karfi waje
....haka ya dauki Hudar ya wurgota waje tana ihu tare da
turje turje .....
  Mama kuwa kwanciya tayi kasa tana birgima lokaci
guda numfashinta ya fara sarke mata ....sam Huda bata
lura da halin da mama take ciki ba ...tana jikin Gate din
tana kuka tare da buga kanta jikin karfen kamar ranta zai
fita ...
    Yaya Saa kuwa ba shehu kadae ba harda guard din
dake sae da yace duk mai bukata idan shehu ya gama
...ya bashi dama ....kadan daga cikinsu ne basu taba yaya
Saa ba .....numfashinta har daukewa yake don azaba ...
  sae da suka gama wulakanta ta sannan aka bude gate
din aka jeho da ita kamar kayan wanki ....Huda tayi kanta
ganin jikinta duk jini ..tana kuka tare da jijjigata ......
  ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Huda ....fuskarta
kamas babu alamun hawaye sae dae kurawa Huda ido
da take tana kuka .....Inda mama take yashe ta kalla
....kafin ta ja jikinta ta isa gurin tana kallon fuskarta  ...
   Ba tare da tace komae ba ta koma ta zauna kar ba
mutun ba ....
 Huda ta cakumo Yaya Saa tana fadin .." Yaya saa me
suka maki ? ....me suka yanka jikinki duk jini?....Me yasa
bakya kuka ? ...
  Ba tare da tace mata komae ta nuna mata mama dake
kwance a kasa ......gurinta ta nufa tana kiran sunanta ...
  Mama !!!...ga Yaya Sa'ar sun maido mana. ...ki tashi ki
ganta mama duk jini jikinta ban San me suka yanka ba a
jikinta......ki tashi dan Allah ta dawo fa Mama ....!!! girgiza
take tana kuka ...amma mama ko motsi bata yi ...
  Liman din unguwar yazo wucewa ta gurin ya gansu
haka ....yace " Subhanallah Huda Me ya sami mamar
kwance a kasa ..."
  "ban sani ba ...taki tashine ...kazo ka mata magana
...yaya saa ki taso don Allah ...!!!
  Da sauri ya iso gurin ...ya leka fuskarta tare da ja da
baya ....."inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un "...yake
nanatawa ...sannan ya tafi da sauri...
   Jimawa kadan sae gashi da mutane ....ina suka dauki
Mamar suna fadin wae ta rasu ....duk abunnan da ake
Yaya Sa'a na zaune idonta na kallonsu ...har sae da aka
dauki mamar sannan Huda ta jata tana kuka suka tafi ...
  Kafin me ...gidan ya cika tab da yan gaisuwa ....huda ke
ta uban ihu amma yaya saa kukan ma yaki fitowa ....ita
kanta so take tayi kukan amma ba dama
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                     🍁
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION💡_*
( _Home of Expert and perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
               *_Main mera dil aurtum ho yana phir kyun ho
palken ..👌🏻..jhuka yein wahan ..😘 Haske writers ..Ummy
Aisha ..Hajja ..Asmy ..Ayusher ..Fatee ..Khaleesalat hydar
..Billy ..Nana diso  ..Asy ..HOENPW😘_*
*_29  to 30_*
          Bayan sati daya ne barister Mahmoud yazo ganin
jikin mamar ....Yana zuwa yaga ana addu'ar bakwae
kofar gidan .. ...tambaya yayi me akeyi ...wani ya ce
mashi Maman su Huda ce Allah yayiwa rasuwa sati daya
kenan...
  turus yayi ya kasa koda daga Kafa da k'yar ya samu ya
dafa bango ya zauna a dakalin tare da tallabe kanshi da
hannu biyu...
Yaya Saa kuwa ta bar magana da kowa ....Sannan duk
wani namiji da yazo masu gaisuwa bata karba ...sae ma
ta janyo Huda jikinta ta hanata koda motsawa ....!!
  ••°°•••
  Barister Mahmoud yana kokarin kawo masu taimako
amma sam yaya Saa bata karba ....da taga yana kallon
Huda zata fara kuka tare da rokanshi ya fitar masu daga
gida dan Allah ...!!!
    Cikin dan lokaci abunda zasu ci ma ya fara gagaransu
....ganin basu da madafa yasa yaya saa fara wanki da
guga da kuma dakau idan ta samu ...duk kokarinta na
nemawa Huda kudin makaranta da abinci ...zata iya
kwana biyu bata ci abinci ba ...amma bata barin Huda da
yunwa ko ta mintu Biyu....duk wani aikin wahala da
zatayi bata kashe ko sisi a jikinta sae dae ta kashewa
Huda .....duk wani gurinta na duniya  yana ga
Huda !!.....ta dauki son duniya ta kara daura mata ...
  Lokacin da cikinta ya fara girma sae ta fara fuskantar
wulakanci gurin yaran Unguwa ..da Huda ta fita sae
yaran su dinga tsokanarta wae yayarya tayi cikin shege
...!!
  Haka itama yaya saa da ta fita an dinga zind'enta ana
gulmarta ....sae ma ta daina fita kwata kwata ....duk tayi
bak'i ta rame ...don Ma Huda ba kanwar lasa bace ...duk
wanda ya taba yaya saa bata kyaleshi sae ta bishi har
bayan uwarshi ta duka  ...idan matar aurece bata kyaleta
.. kan yaranta kanana take fanshewa don da sun fito
waje zata kamasu ta doka ..yaran basu kara sukuni har
sae matar ta zo har gida ta bawa yaya Sa'a hakuri.....
   Ranar da Huda akayi masu hutu ta dawo daga
makaranta ta iske yaya saa kwance bata lafiya ...
  " Yaya Sa 'a ki tashi muje asibiti kinji ko ...sannu ..ki ta
masu Allah ya isa har su mutu ....!!!
  Ganin ciwon ya dameta ne ya sakata tashi ta shirya suka
tafi asibiti ...
  Bayan sunje ne aka mata aune aune sannan aka ce su
jira result ...suna zaune sae uban surutu Huda keyi
..nurse ta fito da result din tare da kiran yaya Saa office
din ...
  banda "Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un" babu abunda
yaya Saa ke furtawa ...wae HIV ni Sa'a .... ....Juyar da
kanta take ta rasa inda zata sakashi ...
  tun likitan na kokarin mata bayani har ya fuskanci sam
bata cikin hayyacinta ...Huda ta fado office din da gudu
...tana fadin ..
  "Yaya Sa'a ki fito mu tafi mana ....kin zauna sae surutu
suke maki wae Har da fadin kina da HIV ..dan Allah ba
sae ki godewa Allah ba ...ni da ko ABC ban dashi ya to
zanyi ...ki tashi mutafi ...dan Allah" ..
   Zuba mata ido doctor din yayi tare da fadin "Sister
baraka ...ki fita da wannan yarinyar mu karasa maganar
tukun"...
  Yaya Sa'a tace " kubarta ...itace rayuwa duk abunda ya
sameni tare muke bakinciki ...na sani ko batayi yanzu ba
gaba sae tayi bakincikin da yafi wanda nayi yanzu...ku
kyale ta ...ku kyale man Hudata ...!! ...idonta ya ciko da
kwallah ..
      Da sauri Huda ta kalli doctor din tare da zabga mashi
harara tana fadin .." ku mazan nan mugayene ..me
yayata ta maku da duk lokacin da ta ganku sae tayi kuka
...ba ku sonta ne? ....tashi muje Yaya sa'a ki bar kuka kinji
ko .. Ni kadae ke sonki yayata kuma duk wanda ya cuceki
baran taba kyaleshi idan na girma ...!!! ..hannu ta saka ta
share mata hawayen tana kallon likitan ...
    Hannu Yaya Sa'a ta fizga da karfi suka bar office din
...yarda take jan Yaya Sa'a sae ka dauka itace yayarta ....
  Yaya Sa'a in tsaida mana Okoda mu hau ?...
  Cikin Kuka tace ..Huda banda kudi okoda.. ....kin gaji da
tafiyar ne ? ...
  Daga kafarta tayi tare da nunawa Yaya sa'a tana fadin..
   " lokacin da kika shiga gurin likita na taka kwalba ...ban
iya tafiya Sossae Yaya Sa'ata ...
  kanta ta dafa tana fadin ..."Sannu kinji Huda ....".
    kafin Huda ta amsa Yaya Sa'a ta sab'eta ...duk da uban
nauyin Huda ga kuma ciki sannan bata lafiya haka ta
kaita gida ...sannan ta shinfideta saman katifarsu ...
  Nan da nan ta hada wuta ta zuba ruwan zafi  ta dafa...ta
gasawa Huda Kafa ....Duk irin rakin Huda Shiru tayi ganin
Hankalin Yaya Sa'a ya tashi sossae .....
  Tunda akace Yaya Sa'a nada HIV sauran farincikinta da
ya rage mata  ya tafi ....bata da aiki sae kuka ....sannan
bata gaza ba gurin neman kudin da zata biyawa Huda
Makaranta ba ....
  Barister Mahmoud kuwa kullun kokarinshi na yarda zai
taimaka masu amma duk a banza ...don da Yaya saa ta
ganshi zata tura Huda daki ta rufo ta dawo tana hadashi
da Allah ya tafi ya barsu ....bama shi kadae ba duk wani
namiji bata kaunar taga ko kallon Huda yanayi ...
••°°••
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
     *_Assalamu Alaikum ...wadanda suka man magana da
dadewa akan na bude masu GRP nace masu banda
ra'ayin haka ...to Alhmd na bude maku saboda wasu
dalilai ...idan har yanzu you're interested sae Ku sake
man magana👌🏻👌🏻_*
     *_Jaane kahan Keene pehesr zyada ..QUEEN
MERMUE..NAFEE ANKER ...AMNOOR ...FEEDOH
CLASSIC...AUNTY SIS ..MUM FATEEY ..SALAMATUN INNA
...AOH😘_*
*_31 to 32_*     Huda ..!!! Ya Kwala mata kira dae dae lokacin da yayi
parking a bakin gidansu ...
  Ta juyo tana kallonshi kafin ta koma da gudu ta janyo
kofar gidansu ta saka dankwalinta ta kulle kofar ta dawo
gurinshi tana hararanshi ..
  "Wae kai ina zuciyarka take ?
 Kirjinshi ya dafa yana murmushi ..."Tana nan Huda !!
  baki ta tabe tana fadin .."ni na dauka baka da ita
...banda k'wak'wa kullun yaya Saa na fada maka ka daina
zuwa gidanmu amma sae ka janyo wata motarka kazo
kana washe baki ..."
   Murmushi yayi ba tare da yace mata komae ba ...
  "bara kayi magana ba ...to Na rantse maka da Allah duk
ranar da ka kara zuwa ka saka Yayata kuka sae naje har
gidanku na saka Yayarka kuka itama ....
  Zagayowa tayi tare da bude Marfin motar tana
fadin..."Zo ka shige ka tafi ko na maka rashin mutunci
....!!
  zuwa yayi kamar zaya shiga sae kuma ya hade
hannayenta guri guda ya dagata ya daurata saman
motar tare da dungure mata kai yana fadin ...
 "Bakya da kunya ko Huda ..? ..ni zakiwa rashin
mutunci ? ...ya hade fuska
  Daga kasan kafafuwanshi ta fara kallo har zuwa kanshi
..saman ta hadiyi miyau da kyar tana kallonshi ...ganin
tsoro ya bayyana a fuskarta ya sashi sake daure fuska
yana kallonta ...
   "Ni zaki wa rashin mutunci nace maki ?
  "Allahu" ...ta juyar da kai kamar saliha ...dariya taso
bashi yarda take zare idanu ga fuskar bayin Allah da ta
koma ..amma ya dake yana kallonta
.
    "Oya ...yiman rashin Mutuncin nace !!
   "To dan Allah idan nace kayi Hakuri fa ? ...ba sae ka
saukeni ba na tafi gida ...sannan kullun kazo ni kuma na
dinga gaidaka ....saukeni ka gani yarda zan dinga maka
..."
  Sake mata hannu Yaya tare da ja da baya ...tsalle tayi ta
dira kasa tana washe baki ...sannan ta hade hannayenta
guri guda ..
  "Kafana ma k'aikayi take man ....bara na sosa kaji ? ...ta
fada tana kalloshi tare da murmushi ..
  Dukawa tayi tana sosa kafar tata ...ta dago a hankali ta
kalleshi taga hannusa a harde kamar ba ita yake kallo ba
...da sauri ta rarumi kafarshi da niyar ta kadashi kasa
...amma sae ji tayi kamar icce ko alamun yasan abunda
take baiyi ba ....
  Ta dago tana hararenshi suna hada ido ta washe baki
tana kakkabe hannu ."Har ga Allah ni bama niyar kadaka
nayi ba " ...
   kafin ya bata amsa ta ...ta bar gurin da gudu ....dariya
yayi ya bude boot din motarshi ya fito da kayan abincin
da ya zo dasu ...sannan yayi waya ...wasu mutane guda
Uku sukazo mata...ya basu kayan abincin sannan ya
shiga motarshi ya tafi ...
  Matan suka saka yara tare da daukar masu kayan
abincin suka kai cikin Gidansu Huda ...yaya Saa na zaune
tsakar gida taga yaran suna ta shigowa da buhunna
...bude baki tayi tana mamaki ...kafin tayi magana taji
Huda na fadin ..
  "Wallahi yaya Sa'a ko kayan waye wannan bara mu
bashi ba ...tashi mu kaisu Daki mu boye tun kafin maisu
ya shigo nema ...Dan Allah Yaya Sa'a tunda muma an
taba yi mana fashi ba sae mu rama ba mu dauke kayan
....
  Kafin ta rufe baki Matan sun shigo ..tsalle daya Huda
tayi tare da tara hannu tana kange kayan tana fadin ..
  "ba Wanda ya isa ya daukesu tunda bamu mukace a
shigo mana dasu gida ba ..."
  Wata daga cikinsu tayi murmushi tana fadin ...dama ai
naku ne Diyata ...daga gidan marayu muke aka baku
Taimakon da ake yiwa Marayu ...
  Murna kamar me gurin Yaya Sa'a ...godiya ta dinga
masu har da kuka ...bayan sun tafine Huda ke cewa ...
  "Yaya Sa'a mu dafashi duka idan mun ci sai mu aje
sauran ...yarda ko wadannan barayin sun zo bara su iya
dauka ba ...kinji .."
  Yaya Sa'a  tace ...Huda ba yarda za'ai mu dafa shi duk
kinji ko ...idan ma sun zo sun dauka Allah da ya bamu
wannan zai sake bamu wani !!!!
   ••°°••
  Huda na JS2 ..cikin Yaya Sa'a ya cika wata tara ...ranar
kasa bacci sukayi ...Tun cikin dare take nakuda ..Huda ke
ta mata fita tare da Sannu ....ana kiran asuba ta fita da
gudu ta kira liman tace yayanta bata lafiya ...
  Tare suka dawo cikin gidan ..lokacin  Yata Sa'a ta wahala
sossae ko Bude ido bata yi ....Banda Kuka babu abunda
Huda ke yi ...har aka dauketa aka tafi da ita asibiti ...
   Basu isa asibitin ba Yaya Sa'a ta rasu saboda deep
labour din da tayi sannan jininta duk ya fita sossae ...
 Tana ganin an juyo zaa dawo ta rike hannun liman din
tana fadin
  "Dan Allah karmu koma ...bata lafiya sossae ko magana
bata iya man ...duba liman  yayata idonta ya rufe ...dan
Allah mu tafi asibiti ...ina sonta ...karmu koma liman
..wallahi da munje asibiti zan fita nayi bara na samo
kudin sae na bayar da kudin ...ni bana so tasha wahala
.!!!...ta fada jikin yaya saa tare da fashewa da kuka ...
  Duk wanda ke motar sae da yayi mata kuka ...ko da
suka isa zaa fitar da yaya saa daga mota kin sauka tayi
daga jikinta sae dae aka daukesu tare ...
  Bayan an aje ta ne Zaa Mata wanka liman ya rugumota
jikinsa ...ya ma rasa me zai ce mata ...ya tabbata duk
wanda ya hana Huda kuka ya cuceta !!!
   Tana jin wani na fadin Ta Rasu ne ...tayi sauri fizge
kanta daga jikin liman tana fadin ...Ta rasu kamar
Mamata????..Barata dawo ba?.
    Da Sauri Liman din yace ...bata rasu ba Huda !!! ..
  Hannushi ta kama tare da daurawa jikin Yaya Saa tana
fadin ...
  "Yauwa Liman ...to tadata ...kace mata Hudanta na
kuka..bata son kukana fa ...nasan zata tashi .liman ka
tadata Dan Alllah !!...yaya Sa'a tace fa ...kace ta tashi' ko
kukan ta ma naji zanji dadi ...Dan Allah ki tashi ...!!
   Da kyar liman din ya fita da ita daga dakin yana
kuka  .....babban tashin Hankalinsu yarda zasu fitar da
gawar daga gidan ba tare da Huda ta gani ba ...!!! ...
   NO WAY OUT ...Haka suka dauko gawar Yaya sa'a
..lokacin  Huda na jikin Liman a waje tana kuka...kowa ya
tabbata da tayi rashi ...RASHI BABBA !! ...wanda babu
wani mahalukin da zai maye mata gurbin Yaya Sa'arta !!!!
  Ganin tana kokarin tashi ya saka liman din riketa gam a
jikinshi ....
   Kamar mai bacci take fadin..  "kace kar su tafi man da
yayata!!...ina sonta ita kadae gareni ...Liman kaga ko
Lauya shine ya ma Yaya Sa'ata Hard'e! ...mukaje gurinsu
suka kara yankar naman jikinta ...sannan suka wullota
...Mamana ta rasu saboda Hard'e ...yaya Sa'ata ma ta
rasu  sabodashi ...Liman nima din ina so in masu Hard'e
...da lauya da babanshi da hajiyarshi ..zaka rakani ?
  Ganin ba cikin Hankalinta take ba ...sannan idonta a
rufe yake  ! ya sashi ..cewa "Zan rakaki kinji
Huda !! .."Yaushe zamuje ..?
  Yanzu !!!...ta bashi amsa tare da rufe idonta ..bai kara ce
mata komae ba sae addu'a da ya dinga tofa mata...
    *_JUST THE BEGINNING....😘_*
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                   🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO ...💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
_*33 to 34*_
          Tun daga lokacin Huda bata kuma magana ba
...kukan da takeyi ma ya tsaya cak ...sae ajiyar zuciya da
take saki lokaci zuwa lokaci ...da marece Liman ya tafi da
ita gidansu bayan kowa ya watse ....
  Bata iya bacci ba .. ta riga ta saba a jikin yaya Sa'a take
bacci kulun amma yau ita kadae bisa katifa ...juyi ta
dinga yi ...da ta rufe idonta barister Shehu take gani yana
kallonta ...sae ta kai hannu zata kamashi sae ya sille mata
...
  Ranar ta Hudu ce bayan an dawo daga masallacin
juma'a aka tsaya za'ayi addu'ar bakwae ...
 Lokacin Barister Mahmoud shima daga masallacin ya
biyo ta gidansu Huda yaga yarda suke ....mutane sun
taro sae addu'a ake ..
  Huda kuwa na zaune gefe guda ta daura kanta saman
guiwarta ...yana gama parking ko fitowa baiyi ba ya kura
mata ido tare da kiran sunanta ..
  Hudallah!!!!!
 Hankalinta baya duniyar gaba daya bata man san da
zuwanshi ba bare ta san yana kiranta .....ganin bata da
niyar kallonshi yada shi fitowa daga motar . ..
  Har yazo gabanta ya tsugunna bata sani ba ...sae da ya
tallabo kanta sannan takalleshi da idanuwanta da sukayi
jawur ...
    " Hudah ....menene ? ..idonki ke ciwo?...ya tambayeta a
hankali ..
  Kamar jira take ta fada jikinshi tare da sakin kuka ....duk
ya rude yana tambayarta ...
  Lafiya Huda? ...menene? fada man kinji ?...wani abu ya
sami yayarki ?...Shiii yi shiru mana ki man magana please
..!!..ya fada a rude ...
    Ba tare da ta bashi amsa ba tacigaba da kukanta
....shafa bayanta yake a hankali ..yana so ta mashi
magana amma ta kasa ..sae uban kukan da take ...
  Liman ya taso ya dafa bayanshi tare da yi mashi
bayanin komae ...
   A tsorace ya kalleta da idanuwanshi da sukayi jawur
...kafin ya sakw rungumeta sossae yana bubbuga
bayanta  ....
   Suna nan tsugunne har aka gama addu'ar sannan aka
fara shawarar wanda zai tafi da Huda gidanshi ...don
babu wanda yasan dangin babanta bare a kai masu ita...
  Liman yace "Har ga Allah ina son daukar Hudallah
amma ina tsoron uwar dakina ? ...sam bata kaunar taga
wani ya rabeni sae ta dinga azabtar dashi ...kuma rikon
Huda ba zai yiyo haka ba ...domin ita marainiya ce ta sha
banban da sauran yaran da ake rikewa kara zube ....dole
wanda zai dauketa .. ya guji kukanta da bacin ranta
...sannan kuma bazai saketa hakanan ba ....Saboda
marainiya Mutun na iya shiga wuta !! ...Na tabbata uwar
dakina bazata taimaka man ba mu riketa tsakani da Allah
ba tare da cuta ba ..."..Amma dan Allah cikin ku idan
akwae wanda ya tabbata zata iya zama gidanshi cikin
farinciki ...wallahi nayi alkwarin duk wata zan bashi
buhun shinkafa da taliya da jarkar mai da kudun cefane
...dan Allah wani ya taimaka !!!
    Mahmoud dake tsugunne yana jin duk abunda suka
fada ....ya dago Huda daga jikinshi tare da share mata
hawayen da suka wanke mata fuska ..
  "In je na dawo ko Huda ? ...zauna kinji ...!!! ..ya zaunar
da ita sossae sannan ya tashi ya matsa gurin
  Yace "Malan za'a iya bani Hudallah ....na maka alkwarin
riketa kamar uwa da diyarta ...sannan in Sha Allah barata
taba kuka ba ta sanadiyata ....Dan Allah ku bani ita .."
   Liman ya dade yana kallonshi kafin yace "Wane
unguwa kake Yaro ? ...kuma dama kasan su ne ? ..
  Cikin Sauri yace ..."na sansu wallahi ba tun yau ba
....nan take ya fadawa liman din address din gidansu ..
  Liman Yace "Alhamdulillah Mahmoud ai nasan
mahaifinka ...duk wata yana kawo mana taimako ...na
tabbata zata ji dadi gurinku !!!
     Godiya sossae yayi kafin ya koma gurin da Huda ke
zaune ....
  "Zaki bini ko Huda ..zan baki rayuwa mai cike da jin
dadi ..zan maye maki gurbin Yaya Sa'anki ...Muje ko?  ..ya
fada a hankali tare da tsugunnawa kusa da ita
   dagowa tayi a hankali tana kallonshi ...bakinta ya motsa
ahankali sae dae bai ji abunda take fada ba ....gurin da su
liman yake tsaye  ta nuna mashi da hannu.....
  Tare da fadin ... .."Lauya"
Feedohm💞
💧💧 _*A DALILIN YAYATA🍁🍁*_
                      🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS....._
_*35 to 36*_
      A hankali ya juya yana kallonsu ...Barister Shehu ya
gani rike da wata takadda yana nunawa liman din rai a
bace ...
   Da sauri ya mike ta rike mashi hannu tare da binshi
suka isa gurin ...
   Cikin fada barister Shehu yake fadin "Dakata malan me
ka sani dangane da wannan gida ...in jin nine lauyan
ubansu tun kafin ya rasu ....to wannan gidan da kake
wani hakilo akan basu sayar dashi ba ....to tun kafin
uwarsu ta rasu ta sayar man dashi kuma ga shaidata
nan"...ya mikawa Liman Takardar gida
   Barister Mahmoud ya karbi takardar ba tare da ya
kalleshi ba ...ya budeta yana karantawa ...tabbas takardar
gidan ce amma ya tabbata karya yake ba sayar mashi da
ita akai ba !!
     Dan Murmushi ya saki kafin ya kamo hannun Barister
Shehu ya damka mashi takardar yana fadin  ..
  "Malan ku bar mashi ya tafi ....Barister har kayan dake
cikin gidan ya kamata ka yi takarda don babu abunda
zatayi da su ....A juri zuwa rafi ".....
  Ya juya tare da jan hannun Huda suka tafi ba tare da ya
juyo ba ...Huda kuma tafiya take amma Barister Shehu
take kallo ta kasa dauke idonta akanshi har suka isa
bakin kofar ....
  Gaba ya bude mata ya sakata sannan ya koma ya shiga
suka tafi !!!
    Falo suka iske hakima Hanne kwance saman kujera
tana kallo ... Suna shiga ta mike da sauri tana dariya
..ganin Huda ya sakata matsawa da sauri tana fadin ...
    "Tsaya  tsaya ...karki shigo ....yaya ina ka samo wannan
yarinyar duk datti ...!!!...karki shigo bara na miko maki
towel kiyi wanka a wancan tap din sannan ki shigo ...yaya
yar aiki ce? ..
   Bai saurareta ba ya janyo Huda Har tsakiyar falon
...tare da dagata sama yana dariya ya zaunar da ita
saman hannun kujera ....
   Juyowa yayi gurin Hanne yana fadin "Hudallah ..
_Daugter ta ...Best friend dita .... Little sister ta ....Heart
cherry ... My Queen _ ......Kin fahimta ? ..
   Ta gurin Mamanka kuka hadu ? ...ta tambaya a dakile
   Huda ya kalla yana fadin ... Hudah ta ina muka
hadu ? ...ta nan ko ? ...ya taba kirjinshi yana mata
murmushi ..
   Bakinta ta gumtse kafin ta fara kyafta idanu tana
kallonshi .....
  Oh Sorry ...Taso muje kiyi wanka kici abinci...mu dawo
na baki labarin Abunda Yaya Sa'armu tace na gaya maki
...
   Da gaske ? ...ta fada tare da fito da idanu ..
  Kai ya daga mata yana fadin ..."Yes ...muje "...... Ya mika
mata hannu ta sauko ..
   Hanne dake tsaye tana kallon ikon Allah tace .."Wae
Wacece wannan ? ...
  Kallonta yayi a fizge yana fadin .
".Hanne bara nayi wanka zamuyi magana kinji ko ..."
  Binshi tayi da kallon har suka shige part dinshi ....
      " Kutmar Uba...ban taba shiga  part dinshi ba amma
ya shiga da wancan ... " ..ta dafe kai tare da fadin ..."to ko
dae kanwar uwarshi ce "
  Dae dae zai fito ya baro Huda tana wanka yaji tana
fadin Kanwar uwarshi ....
  Shigowa yayi Falon yana fadin .."No Hanne ba kanwar
Uwata bace ...Marainiya ce ta wuce duk yarda kike
tunanin"
   Wani Uban tsalle tayi tare da mikewa .."Kuma dan
Iskanci anan gidan ?
  A fizge ya kalleta yana murmushi yace " Ki rushe in da
kika gina man !!!
    "Wallahi bata yiyuwa Yaya ...bamu gidan marayu " ...ta
fada tare da zama kusa dashi
   Look Hanne !! ..kina son zama dani ? ..
  Gyad'a kai tayi tana kallonshi ...
  "Good ...to ki so wancan yarinyar ...."
  "kwana nawa zatayi ?...ta tambaya a hankali ...
    "Abadan da'iman".....shima ya fada a hankali ..
  "Amma ai nan da shekara 8 idan tayi aure shikenan ko
yaya ? ..
  Kallon da ya sake mata ne ya sata yin lakwas ...tashi yayi
ya shiga dakin ...Hudana Zaune bisa kujera da alama
lokacin ta fito daga wanka ...
   "Come on ...kin yi alwala ?  ....ya fada tare da fito da t
shirt daga drawer shi ...red mai dogon hannu ya mika
mata ...
   "Tashi ki saka kafin anjima mu je Super market a sayo
maki naki ko ?....
  Karba tayi ta sanya ...tazo mata iya guiwa ta mata kyau
sossae ...ya kalleta yana murmushi ..
  "Ayehhh Hudata ..kinga yarda kikayi kyau ...come on
...na maki photo ? ...
   Uhm Uhm ...ka fada man abunda Yaya Sa'an tace
....tayi rau rau da idanu ...
    Hannunta ya kama ...tare da dukar da kanshi saitin
fuskarta yana fadin ..."Sae kinci abinci sannan "...yaja
hannunta suka fito falon ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                    🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS...._
_*37 to 38*_
         Still Hanne na zaune inda ya barta ....
   " Me kika hada mana lunch ?...ya fada tare da kallon
Hanne ...
   "Lah Yaya bana fada maka ba tun shekaran jiya kaina
ke ciwo .".
..
   "Good"...ya fada tare da fadawa kitchen ...yana janye
da hannun Huda ..
   Zaunar da ita yayi bisa table din dake cikin
din.....sannan ya kunna gas ....
   "Me kike so ki ci "...ya fada dauke da murmushi tare da
kura mata ido ...
   Lumshe idonta tayi ba tare da tace komae ba ....Tabbas
yasan Har yanzu Yaya Sa'a na ranta ....hannunta ya kamo
...
  "Hudallah ...zaki ci Indomie ? ...
  Girgiza mashi kai tayi alamar aa .....
  "To me kike so ? ... Cous cous ..?
  nan ma girgiza kanta tayi ...
  Dago kanta yayi yana kallonta ..."Su kadae na iya Huda
...ya fada a hankali ...ko na soya maki Dankali? ...
   Bude idonta tayi da ya ciko da kwalla tana kallonshi
...Ganin zatayi kuka ne ya sakashi juya mata baya tare da
kurawa Tagar kitchen din ido ...wanda a zahiri
hankalinshi na kan yarinyar ...!!
  Da sauri ya juyi yana fadin ...Yaya Sa'a tace idan har
Hudallah na kuka to barata taba samun sauki ba a ranta
....
   Share hawayen tayi da sauri tana fadin .." To idan na
daina fa ? ..
   Idonshi ya lumshe ...."Allah zai sakata aljanna taji dadi
sossae ",..
     "To na daina kaji ...kace mata na daina kukan ...taji
dadi sossae dan Allah ...kuma kaji kace har yanzu ina
sonta ....!!! Idonta ya ciko da kwalla tayi saurin maidasu
tana kakaro murmushin dole ...
    Rungumeta yayi tare da mata peck a goshi ...sannan ya
daura tukunya ya zuba ruwan zafi tare da kayan miyan
leda ya bata albasa ta yanka mashi ....cikin mintin kadan
ya dafa masu indo mie da kwae ...ya juye masu a plate...
     Hanne ya kalla yace ..."Come and enjoy your lunch
...ya aika mata wani mugun kallo ...
   Tana son taci amma babu fuska duk da an mata tayin
....!!!
••°°••
  Satin Huda Biyu gidan ta fara warwarewa ...Sae dae
matsalan idan ya fita hanne ta sakata a gaba ...da zagi ...
  Tana zaune a falo ita kadae sae game take abunta tana
dariya ....Hanne ta shigo tare da fizge game din ta wurga
saman kujera ...
   Kunnenta ta murde ta zauna kusa da ita tana hararanta
...
  Da sauri Huda ta dafe kunnen tana ihu ....
  Bakin hanne ta buge tana fadin "wae ke dan ubanki
idan Yaya ya shiga dake daki me kike ce mashi da kuke
dadewa a ciki kuna dariya"
  Cikin jin zafi Huda tace ..."Fada mashi nake ke muguwa
ce kullun idan kina zaune kiyi ta man tusa ..sannan bakya
wanka !!!
   Wani uban rankwashi ta kai mata akae ...ihu ta sake da
karfi ..
  Dae dae lokacin Mahmoud ya shigo falon ...jin Ihun
Huda ya hanashi karasa sallamar ya shigo da gudu yana
fadin...
   Hudah ...lafiya ....tsaye yayi yana kallon Hanne dake
shafa kan Huda tana murmushi tare da fadin "Kai baby
don na maki ci uku shine zaki man wannan ihu "..
   Kallonshi Huda tayi kafin ta sake murmushi ta ruga da
gudu ta fada jikinshi ...dagota yayi yana fadin..
  "Hudah Game kuke ? ..
  Hanne ta kalla sannan tace "Eh Uncle Game muke irin
na aunty muguwa ...Dan Allah Uncle' banda mugunta
irin ta Aunty Hanne sae ta murde man kunne da karfi ?
  Hanne ya kalla duk tayi fiki fiki ...kafin ya maida idonshi
kan Huda ...
   "Me kika mata? ..
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                 🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO_*💡
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_39 to 40_*
           Hanne tayi karaf tace .."Amma Hudah ke
munafuka ce ...daga wasa ? ...
   Murmushi yayi kasa kasa ....sannan ya mikawa Huda
ledar da ya shigo da ita ..."Jeki dauko littafin da na kawo
maki jiya ..."
  Babu musu ta karba ta shige dakinshi da gudu ...
    Bai cema Hannen Komae ba ya koma ya zauna tare da
lumshe ido ...ita da kanta tazo tana bashi hakuri ...sae
dae yayi murmushi ba tare da ya bude idonshi ba ...
  Fad'uwar Hudah jikinshi ya sakashi bude idonshi yana
murmushi ...Sossae ta zauna jikinshi ..ya karbi novel din
yana karantawa ....
••°°••
  Barister Shehu na zaune gida kusa da Hajiyarshi ..phone
din shi ta dauki kara ....
  Kamar bara ya dauka ba ...ganin babban yaronshi dake
kular mashi da kasuwar zinaranshi ce ya sashi dauka
wayar ..
  "Hello ...Bello ya akai ",..ya fada tare da saka wayar
handsfree ya daura saman hannun kujeran ...
  daga dayan bangaren akace "Oga wallahi wata mata ce
tazo ta sayar mana da gold dinta na 2.6m ...bayan ta
tafine muka gane gold din jabu ne ...kuma mun rasa
inda ta shiga a kasuwar...!!
   What ? ....Uban wa cikinku ya auna zinarin lokacin da
zaku saya ? ...ya fada a firgice ...
  "Wallahi oga mu duka muna tsaye Bala ya auna
....Amma...
  "Shuttt up ...banzaye taya mace zata sayar maku da
jabun zinari ku kirani kuna fada man bayan baku
kamota ba ....wallahi bazanyi asara ba ...kune zaku
dauketa wawaye.!!!
   Kashe wayar yayi yana kallon hajiya sae gumi ke keto
mashi ....
  "Zancen banza ne shehu ...ba yarda za'ae mu dauki
asara su zasu dauketa wallahi ..
barsu karka kara kiransu ...!!
  Amma Hajiya...
  "Karka ce komae ...gobe zan tura Auwalu gurin ...zasu
fito da su ne "
   Tashi yayi zai shiga daki ...tayi saurin tsaidashi tana
fadin ...
  "Wae Shehu ya maganar yarinyar nan ta gidan Alhaji
Tukur ...Kun dai daita ?
  Sosa kanshi yayi yana fadin .."Adama wae Hajiya" ..
  "Ita mana "...
  "Nifa dama ba aurenta zanyi ba hajiya ..kawae mum
hutane ...Yarinyar duk da tana diyar mai kudi sae shegen
roko ..!!..So nake Allah ya bani ta kirki sae na aura
..!..Yauwa Hajiya naga wata yarinya gidan liman ko ita
za'a neman man ...tana da bala'in kamun kai ga addini
...kuma suma ba talakawa bane !!
   Hajiya ta saki dariya tana fadin ...Wae Maryam ...nima
kaina yarinyar ta kwanya man ..akwae natsuwa gata yar
mutunci..bara idan dad dinka ya dawo sae in masa
magana !!!...
*_MARYAM..._* Diyar liman ce wanda yace bara ya dauki
Huda ba amma asali bashine ya haifeta ba agolace a
gidan ....saboda Mugun Halin Matarshi ya hanashi daukar
Huda !!....Hajiya zubaida itace uwar maryam ...su biyune
ya'yanta ...daga Maryam sae Abdallah kaninta ....Shi
liman Allah bai taba bashi haihuwa ba har yanzu ...kuma
bai taba damuwa ba !!,..Kullun tana sanye cikin
zunbuleliyar hijab ...a fuskarta kamar sahila amma
azuciya sam babu tsoron Allah ...idan ta saka hijab a
unguwarsu tana fita daga unguwar zata kira saurayinta
yaxo ya dauketa ....duk wani club dake garin babu wanda
Maryam bata zuwa ....yar' bariki ce ta k'in k'ari ....
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                       🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_41 to 42_*
         Duk unguwar kowa zai shedeta mutuniyar kirki ce
....mamanta kadae ta san irin rayuwar da take ...shima
don tana kawo mata tsabar kudine ....ko da rana Daya
liman bai taba fahimtar abunda ke faruwa ba a gidan ...!!
  Bayan da ubanshi ya dawo hajiya ta mashi magana aka
fara nemawa Barister shehu auren Maryam ...
  Wata Biyar aka saka bikin ...ko da yaje gidansu
Maryama bai samu matsala da Ita ba ...ta amsheshi
hannu bibiyu ...
    Lokaci na zuwa aka daura auren ...an kashe kudi
sossae ...don ko lefenta set biyar ne ..Gidansu Huda
Barister Shehu ya saka a rushe suka hade da nasu ...aka
dibarwa Amarya nata part din !!! ...
•• •°°•• •
    "Huda kira man Auntynki "...ya fada tare fa sauketa
daga jikinshi ...
  Uncle ...
  Hannunshi ya saka saman lebenta tare da nuna mata
kofa ...
  Ta lumshe ido kamar yarda yayi sannan ta tafi da gudu
...Hanne na kwance tana waya tana fadin ...
  "Wallahi kawata na gaji da wannan shegiyar yarinya
...Ni kawae zance ya sawake man na tafi gidan iyayenshi
idan ta tafi ya maidoni"
   tayi shiru tana saurarenta ..
kafin tayi dariya tana fadin ..."Haba kawata ya za'ai yanzu
na iya zama kauye ...ai sae dae gidan iyayenshi " ...don ni
da kauye hai hata hai hata ....Ke nifa tunda nazo ba
abunda ya shiga tsakanin mu .....abun har ya fara
damuna kawata "
   "Aunty idan kin gama wayar Uncle na kiranki ...amma
dan Allah kicewa shegiyar kawarki ina da baba ...itane
shegiya bani ba ..!! ..idan kuma ke kika ce man shegiya to
...Allah ya isana !!!
   Bata jira amsarta ba ta kwasa da gudu ....
  Tarota yayi yana fadin "Bara ki bar gudu ba ko
Huda ? ...baran sake goyaki ba !!...
   "Sorry Uncle na rantse maka da Allah na daina ..kaji
...!!!tayi rau rau da ido ..
   Hannunsa ta kamo ...Uncle wae idan Aunty Hanne ta
tafi kauye tana da tsayayyene? ...
     Dariya yayi kasa kasa ..." Ban gane ba Huda !!!
   "Yauwa ...Ina nufin tana da wanda zai aureta ...?..
   zaunar da ita yayi saman hannun kujeran .."Me ya faru
Hudah ?..
     "Kawae Uncle ka saketa mu zauna mu kadae
,,!! ..Kaji ? ...ta fada tare da langwabe kai ..
    Murmushi yayi kasa kasa ...kafin ya dago fuskarta yace
.."Idan na saketa ke zaki aureni "..?
   "Eh mana ...ko yanzu ma ai ina aurenka Uncle ...tunda
ni da aunty muke tsare maka gida ...kai kuma idan ka
dawo ka dafa man abinci ko ..?
   Hanne ta shigo tana fadin
   "Wallahi munafuncin wannan Huda kullun k'ara yawa
yake ...banda muguwar fata ni kike fadar a saka ?...Idan
an sakeni Uwarki zaa aura?,..
    Look Hanne !! ...ya daka mata tsawa ...wallahi kar na
kuma jin kin zagi wannan yarinyar ..."
  Bata ce komae ba ta zauna tana hararan Huda ....
  "Ki shirya gobe ..ko kinki ko kinso ..da safe zamuje
kauye a gano kawu ..!!
  " To dan Allah yaya ka sawo man wanan safar ta leda
mai kama da takalmi ... "
    Cikin Mamaki yace "me zakiyi da ita ?
  Dan dukar da kai tayi tana fadin.."Wallahi yaya baran
iya taka dattin gidan mu ba  yanzu ...bana son kazanta
...!!!
   Dariya sossae yayi ...ba tare da yace mata komae ba
yaja hannun Huda ...Kin tafiya tayi ta tsaya gurin ..
   Muje mana !!
 " Uncle ba kace zaka goyani ba ?...ta fada a hankali ...
   Murmushi yayi ...ai ba yanzu nace ba ko? ...ya dage gira
....
  Kafada ta make .."Yanzu mana " ..
   "To naji ...zoki hau muje ..." ..duk abunki iyakarki toilet
zan direki !!!
    Shegiya ...hanne ta fada a hankali ...
  Gwalo ta mata tana hura hanci ..tare da zaro ido ...
  a harzuke Hanne tace .."Zanci Ubanki Hudah "...
  Mahmoud ya juyo tare zabga mata harara ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                   🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
Na Feedohm💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
   *_Yaseen mutane ma sun maidani yarinya ...to wallahi
am not a kid ..kyas nake kallonki ...wae na bata un edited
copy taza duba man ..yo Fathern ki ya man typing😂😂😂😂😂_*
*_43 to 44_*
       Karfe biyun rana suka isa kauyen ..lokacin anata
haramar shiga masallaci ....Mahmoud alwala yayi ya
shige masallaci ya barsu Hanne zasu shiga cikin gidan ..
  Hanne ta tattare Zaninta sama tana yatsina fuska ...ta
shiga gidan ...da gudu kaninta ya taho yana fadin ...
   "Ga Hanne Ga Hanne ....."
    Da sauri taja baya tana fadin ..."tsaya tsaya boy
...dontu touchi mai wallahi _dont touch me_ "
   Sakin baki yayi yana kallonta tare da tsayawa jiki a
sanye ....Hudah ta kura mata ido tana dariya kasa kasa
....Hanne na lura da Hudah ta zabga mata harara tare da
jan karamin tsoki ....
   Inno ta fito tana washe baki tare da lale marhabun ...a
dakile hanne ta amsa sannan ta isa tabarmar da inno ta
shinfida ...dank'walin kanta ta cire ta shinfida saman
tabarmar sannan ta zauna....ko da inno ta kawo masu
ruwa a kwano ...cewa tayi Hudah ta tashi ta dauko mata
swan water a mota don bara ta iya shan ruwan randa
ba!!....
    Hudah bata amsa mata ba haka kuma bata tashi daga
inda take ba ..!!
   Basu dade ba Hanne ta azalzalesu suka fito ...a mota
banda Dariya ba abunda Hudah ke yi ...Hanne kuwa ta
gama k'uluwa don sae Hudah ta kalleta ta madubi
sannan ta tuntsire da dariya ....Shi kanshi Mahmoud ya
fara gajiya da dariyar Huda  ...ta madubi ya kalleta yace ..
   "Dariyan me kike Haka ne ?
  "Ba komae Uncle " ...ta fada tana toshe bakinta ...
       ganin ba daina dariyar zatayi ba ya sakashi daure
fuska tare da juyowa ya dan kalleta ...
    "ko ki daina dariyan nan ko na bata maki rai Hudah!!!
   Sorry Uncle na daina kaji .!!..Benen gidansu aunty na
gani yake ban dariya don yana bukatar Faci ...gudun
zuwan kawayenta !! ...Uncle Na rantse maka da Allah
aunty ba karamar makaryaciya bace ...kasan me take
fadawa kawayenta !!
.
    "Bana son ji Hudah " ...ya fada tare da daure fuska
   "To uncle baran fada ba ...amma kasan ko ..? Cewa
kawayenta  take idan sunzo wae babanta mai kudine
kuma gidansu ya ma fi naka kyau ...kuma kasan?
   Kallon da ya mata ne ya sakata natsuwa ....Hanne kuwa
rufe ido tayi kamar mai bacci !!
•••°°••
  Rayuwa kenan  ..Barister Mahmoud na zaune da
Amarya maryam lafiya kalau ...sae dae kwata kwata
maryam bata ma hajiya magana ...ko gaisuwa bata
hadasu ...kullum tana part dinta ...Idan hajiya ma ta aika
maryam din tazo ...sae dae tace "aje a fada mata ba
zamanta take ba ...don haka bara tazo ba .!!....
  Barister Shehu na zuwa zata fada mashi ..
sae dae yace mata. " ai laifin ki ne hajiya ...ta yaya
yarinya na zaune dakinta zaki aika ta zo? ...
  Sae dae hajiya ta yi shiru don bata da abun cewa .....
       Shekaransu daya dae dae suka haifi diya mace
kyakykyawar gaske mai suna safina....daga barister
shehu har maryam suka dauki son duniya suka daurawa
yarinyar ..haka hajiya ma da dad duka suna kaunar
yarinyar sossae....kullun sae Hajiya ta aiki yaron dake
mata hidima ya dauki Safina ya kai mata  ....Tun maryam
na badawa har ta fara fadan bara ta dinga bada
yarinyarta ba ana zuwa a wahalar da ita .....
   Ranar hajiya har part dinsu ta shiga tana fada ...ta iske
Maryam zaune bisa cinyar Shehu ...maimakon ta tashi
daga jikinshi sae ma kara shige mashin da tayi ...
   Nan Hajiyar ta dinga balai...idan kujeran dake falon ya
amsa to Maryam ta amsawa hajiya ....
  Barister Shehu yace "haba hajiya taya zaki zo ki sa
yarinyar mutane gaba kina zagi ....bayan ita ta haifi
yarinyar nan ...gaskia bana son abunda zai bata wa
Honey rai ...don haka kawae ki fita ...ni zan mata magana
duk sati sae a dinga zuwa ana daukar maki ita ...!!!
   A fusace ta fita daga part din ...Haka rayuwa taci gaba
duk sati zaa dinga kai safina Part din Hajiya ta wuni a
dawo da ita ..wani sa'in ma hajyar daki take shigewa ta
barwa yaronta yana mata wasa ....
  Yarinya bata cika shekara Daya ba cikinta ya fara
kumbura ....tun suna daukar abun da sauki har suka lura
kullun kara hawa cikin yake ...gashi duk abunda diyar
taci sae ta amayar dashi ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                     🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_Na Feedohm_*💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_45 to 46_*
     Asibiti suka kaita ...duk wani abu daya kamata amata
ana mata ...daga karshe doctor din ya gane cewa ruwan
sperm _maniyi_ ne ya taru a cikinta ....
   Daga Maryam har Barister shehu sae da hankalinsu ya
tashi ...
  Taya zaa ce ruwan sperm sun taro a cikin yarinyar da
bata kai 1yr ba ...haba doctor bara ta yiyu ba ...ka dae
sake dubawa ...!! barister shehu ya fada a firgice ..
   Doctor yace ..."abunda muka gani kenan ..
amma idan baku yarda ba kuna iya sake wani asibitin
sir"..
   Kusan asibiti uku suna zuwa amma abunda aka fada
bai canza ba ....kansu ya shiga duhu ...to ina safina ta
samu ruwan sperm ? ...tambayar da kuke ta wa kansu
kenan ...!!
    Gida suka dawo a firgice ...part din hajiya suka nufa
...a iya saninsu babu inda ake kai safina sae gurin hajiya
...Barister shehu yayi wa Hajiya bayani ...itama cewa tayi
bata yarda ba , ba yarda za'ace yarinya karama sperm ya
taru a cikinta. ..to ina ta samesu? ...amma a kira yaron da
ke dauko safina din ...don wata sa'in gurinshi take
barinta idan bacci ya dauketa ....
     Yaron aka kira ....tambayarshi suka fara yi ...yarda ya
rude ya saka suka gane baida gaskia ...da yaga barister
Shehu ya dauko wuka yace zai kasheshi idan bai fadi
gaskia ba  ..
  Sae cewa yayi wae ..Stick dinshi yake saka mata a baki
tana tsotsar mashi !!! ...
  Kukan kura barister shehu yayi ya makari yaron ..yana
duka tare da fadin Allah ya isa lalata mashi d'iya ...sae ya
kasheta ...da dae yaron ya samu ya kwace daga
hannunshi sae ya ruga da gudu ...dama ba garin yake ba
...zuwa yayi almajiranta hajiyar ta daukeshi ya dinga
mata hidima ....
  Babu irin neman da barister shehu bai mashi ba amma
duk a banza ...ko wanda ya sanshi bai gani ....Sae dae aka
cigaba da bata magunguna har Allah yasa cikin ya koma
dae dae ...
••°°••
   "Hudah bara ki canza ba "...
  " Uncle zan canza wallahi ...kaga nama canza ai .."...
   Hanne ta fito zata raka bakuwarta ...Huda ta fara kukan
akuya ...take jikin hanne ya fara kyarma ...don dama
Hudah ta saba mata wannan tozarcin gaban kawayenta
...
  Allah Allah take kar Mahmoud yama Hudah magana
...abunda taji yana fada ne ya sa cikinta murdawa ...
   Hudah meye Haka ? ..
  Sae dae Hudah ta kalli Hanne sannan tace " Uncle kukan
akuyar gidansu Aunty hanne nake tunawa.. wannan
wadda aka daure kusa da bangon toilet dinsu? da
katangar ta kusa ruftawa ? ...ka tuna Uncle? ...
  Dariya yayi kasa kasa ba tare da yace komae ba ya
cigaba da karanta newspapper dake hannunshi ..
  Kawar ta kalli Hanne tare da tabe baki ...sannan tayi
gaba abunta .....
    "Allah Ya Isa Hudah "...ta fada kamar zatayi kuka ...
  Mahmoud na dariya ya riko hannun Hanne yana fadin
..."Waya sakaki masu karya?
    Hudah ta juyo tana dariya tare da dubarsu ...lokaci
guda ta daina dariyar tana watsawa Mahmoud din
harara dashi kanshi ya rasa ko ta mecece ....
   Juyawa tayi ta shige dakinshi ta barsu yanawa Hanne
dariyar Hudah ta karyata Maganin Mai karya kenan
....Zama hanne tayi suka dan taba fira ....dakin ya shiga
zai watsa ruwa ya fita...
  Hudah ya gani zaune ta kurawa Window ido ...Duk
tunaninshi bacci ta shigo zata yi ...bai ce mata komae ba
ya shiga toilet yayi wanka sannan ya fito yana goge
kanshi da towel ...
  "Hudah !!! ya kira sunanta tare da zaunawa  bisa
kujeran dake kallon gadon ..
  Bata amsa ba haka bata juyo ba ...kanta ya tallabo yana
fadin "Menene "...?
    Da sauri ta buge hannunshi dake saman fuskarta tana
hararanshi ...
    "Me naki Hudahta ...fada man kinji ko ..? ...ya fada
cikin lallashi ..
     "Kaine ka rikewa Aunty Hanne Hannu mana !! ...tayi
rau rau da ido ..
   Ido ya fito cike da mamaki yana kallonta ...kafin yace ..
    "Hudah Dan na rike hannun Auntynki shine kike fushi
..matata face ?..
    "Nima din ai matarka ce !!! ...ta bashi amsa tare da
kura mashi ido ..
  Murmushi yayi kasa kasa ..."Huda ke ba matata ce ...ke
rayuwata ce kinji ko!!..
    "Ba wani ! ...ni din matarkace ...tunda tare da aunty
hanne muke tsare maka gida idan ka fita" ....ta fada tana
hararanshi..
Feedohm💞.
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                     🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_Na Feedohm💞_*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_47 to 48_*
     To wayace maki tsare gida shine aure!!
 Bata ce mashi komae ba ta mike ta fita daga dakin
....kitchen ta nufa ..insa yake aje mata dabino da biscuit
tare da sweet ...ta debo sannan ta dawo lokacin yana
shafawa kanshi mai ..
  " Karba kaci Uncle "...ta fada a hankali tare da mika
mashi dabino daya ..
    Babu musu ya karba ya cinye ..sannan ta bare sweet ta
mika mashi ..itama karba yayi ya shanye yana kallonta
...sae da ta bashi biscuit sannan ta duba aljihun rigarshi
ta fito sa naira dubu ta hankade pillownshi ta aje
...sannan ta dawo kusa dashi tana dariya ...
  "Hudallah na me..
  Hannunta ta daura saman bakinshi ...
   "Yi shiru Uncle ..dama nasan dan ban baka dabino da
sweet ba shi yasa kace ni ba matarka bace ...to yanzu na
baka ..har kudin da ake bawa amare kaga na dauko ko
...To dan Allah Uncle yanzu ban zama cikakkiyar matar
Uncle dina ba ? ...ta langwabe kai tana kyafta idanu ...ita
ala dole fari zata mashi yarda taga hanne nayi idan suna
zaune a falo ..
    Dariya sossae yakeyi  ...har sae da yaga ta fara bata rai
sannan ya dan rage dariyar  ..rasa abunda zai ce mata
yayi ...
    Ya juya ya shiga distrnt dinshi ya canza kaya ...still
yana dariyar ...fesa turare yayi sannan ya fesa mata tare
da jan hannunta suka fita...
    Ko hanne bai ma bankwana ba ya fita da ita .
     Wani katon Moll suka je ya saya mata kaya sossae
sannan suka fito yana janye da hannunta...sae da ya
bude mata motar ya rufe sannan ya zagaya zaya shiga ...
    Har ta zauna sossae ..kafin ya kai ga shiga, ta fito da
sauri tana fadin ...
  "Uncle yaya Sa'ata !!!..idanuwanta suka ciko da kwallah
..
   Barister Shehu ya gani dauke da safina zasu shiga moll
din sae dariya yake yana gaisawa da wasu  ...
   Da sauri yaja hannunta ya suka shiga motar tare
...gurin driver suka zauna su duka biyun ...tana lafe
jikinshi tana hawaye ....baiyi kokarin tursasata tabar
kukan ba ...sae dae hannunshi dake jikinta yana
bubbugata a hankali ...
    ••°°••
  Hanne me kike so maki dan Allah ? ...ya fada a fusace  ...
    Haba yaya...me yasaka baka kulani ne ...ko hugging
dinka nayi ka fara ja da baya kenan ...3yrs da aurenmu
amma ko so daya baka taba sauke hakkin dake kanka
ba !!
  Murmushin takaici ya sake kafin yace  ." Me zan maki
bayan halittar dake jikina ita ke tattare dake ..?
  Amma Yaya duk da nake maza mata ai akwae abunda
ya dace kaman naji dadi nima "
   "Mace ya kamata ki nema ! ...ya bata amsa tare da
barin daki ...!!
  °°••°°
  Shekaru nata tafiya ...sam Huda bata da matsala gidan
Mahmoud ...idan tafiyar nesa ta kamashi zai dauketa ya
kaiWa mamanshi har sae ya dawo sannan ya daukota
...wani sa'in ma cewa take gurin maman zata zauna don
tafi jin dadin zama nan ...amma baya iya barinta ko
kadan bai kaunar yin nesa da ita ko na second biyu ...ji
yake kamar yayi loosing Something very important a
jikinshi .....haka zaita lallabata har ya samu ta biyoshi ...
  Cikin ikon Allah Huda ta gama secondary school dinta
...lokacin duk wanda ya ganta bara ya taba tunanin
Hudalliyar da bace ...Fatarta tayi fresh da ita ...cikar yan
mata tayi ...kamar ita tayi kanta ...a lokacin shi kanshi
Mahmoud tsoron zama da ita yake su biyu ....yayi baya
sossae da ita ...haka itama ta shiga taitayinta ...!!
••°°••
    "Uncle please dan Allah ,yanzu zan dawo wallahi
...please ka ji ? ...ta fada cike da shagwaba ...
    Kallonta yayi tun daga sama har kasa ...tana sanye da
gown black ...sannan ta yane kanta da black gyale ...kaf
jikinta ba inda ake gani ...kamar wata balarabiya
...kafarta sanye da plat shoes black ...sae yar jikkar dake
hannuta black itama ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                   🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_49 to 50_*
         Ganin ya tsaya yana kalllonta ya sakata hade
hannuwata guri guda tare da dan dukawa kadan
     "please uncle " ...na tafi ?,...
    Da kai ya bata amsa tare da lumshe ido ...wani tsalle ta
daka. tana dariya sannan ta fice da gudu ....ya bita da
kallo..
   Gidansu kawarta Lubna dake makwabtansu ta shiga
....ganin ba kowa a falon ya sakata shigewa part din su
lubna ...lubna na kwance tana karanta wani book na
Ummy A'isha *_WANI HASKE_* ...Awayanta ...taji
kamshin turaren Hudah baki kofa...
  Da sauri ta juyo tana dariya ..."Zuwa ba alert "...ta fada
cike da zolaya
    "Duba phone dinki daga CBN na turo maki shi tun
daxu ..."
     Uhm ...ta Uncle Mahmoud ina zuwa wannan irin
kwalliya nasan dai hakanan bara ki man irin wannan
kyaun ba ...
   Baki Huda ta tabe tana kokarin cire gown din dake
jikinta ...tare da jefawa saman gadon ...
   Lubna ta bude baki tana kalllonta kafin tace ...
      "amma wallahi Damsel kin cuci Uncle ...don
munafunci shine kika sanyo wata gown a saman wannan
shedanun kayan .." ina zaki ?
   Riga da wandone matsatstsu ...rigar iya karta guiwa
mai gajeran hannu pink ...sae wando pencil black ....
  Tabe baki tayi tana fadin ... "dallah ban san gulma ni ki
taso ki rakani ..".
   XIna ? ..lubna ta tambayi Hudah cike da mamakinta  ..
     "Bana son wulakanci ..zan sayar dakene? ...ki taso
mana ...bawae dan kina da mota ba ki tsaya ja man aji
...nasan mama batta nan har mun dawo bata dawo ba
...taso please ..!!! ...ta karashe maganar tare da yin gaba
abunta ...
     Da hannu ta dingawa Lubna kwatance har suka isa
tsohuwar unguwarsu ...ta gaban gidansu suka wuce ...sae
da gabanta ya fadi ...inda yaya sa'a ke zama tana awara
ta kalla ...yara zaune gurin sae wasa suke ...take idonta ya
ciko da kwalla tayi saurin juyawa ta goge ba tare da
lubna ta lura ba ..
   Gidansu ta kalla an rusheshe an hade da gidansu
barister Shehu ..baki ta tabe ta kauda kai tana kallon
waje ..
   Nesa da gidansu barister Shehu tace suyi
parking  ...sannan ta duba agogon dake makale a
hannunta tare da fita da sauri tana fadin ..
  Excuse me please lubna !!!...
  Gidan ta fada cikin sauri ...direct part din hajiyar ta
nufa ...sae da tayi gyaran murya sannan ta shiga ...hajiya
na zaune bisa doguwar kujera..tana amsa waya ..
   Sallama tayi a hankali ta harde hannayenta a kirji tana
kallon hajiyar ...
   Katse wayar tayi tare da amsa sallamar tana murmushi
...hajiya dama irin mutannan ne masu son mutun mai
kyau ...
    "Bak'owa shigo mana "...ta fada dauke da faraa don ta
tabbata da ganin Huda ba diyar karamin mutun bace ..
   Dan murmushi ta sake mai burgewa tare da dukawa
kusa da hajiyar tana fadin ...
  "Mummy ina wuni " ...ta fada kamar tana rada ..
    "Lafiya lau ..yarinya ...Tubarakallah ..daga ina
haka ?,zauna sossae mana".hajiya ta fada tare da fadada
fara'arta ..
     Hudah ta dan dukar da kai tana fadin.."Ayyah
Mummyn mu baki sanni ba ..ai kawar Zahra ce ...tana
ma nan kuwa ?
      Zahra. ...?...hajiya ta tambaya tana murmushi .."ae ko
nan gidan ba zahra kila dae baa baki adress din dae dae
ba ...
  Barister Shehu ya shigo tare da sallama...sallamar ta
katse mashine  ya tsaya cak tare da kurawa Hudah ido
yana murmushi ...
   Ta gefen ido ta kalleshi ..sannan ta saka hannunta
tsakiyar cinyoyinta tare da matsetsu tana bubbuga
kafanta a hankali .."Oh Mummy ..wallahi na wahala
sossae ,tun dazu fa nake neman gidan duk inda na shiga
ba nan bane ..gashi phone dinta a rufe....OMG ..what
should i do ? ..ta dan wurga idonta tana bata fuska
kamar mai shirin kuka....   Barister Shehu yayi saurin shigowa falon tare da zama
kujeran dake kallon ta Hudah yana fadin .."Mom bakuwa
mukayine ?
  Murmushi Hajiyar tayi tare da fadin .."Wallahi kuwa
Shehu gashi sae wahala suke bata har yanzu bata samu
gidan ba !!
   Mikewa Hudah tayi tare da dage kafada tana fadin
"anyway!! ..nagode mummy bara na tafi tunda banan
bane .."
   Hajiya tace "Ki tsaya ko ruwa na kawo maki mana "
  Dan juyowa tayi tana kallonsu tare da lumshe ido
..."thanks ...." ta fada tare da juyawa ta fita da dan gudu
gudunta ...
   Har tuntube Barister Shehu keyi gurin binta ...gabanta
yasha yana fadin.."
    "Excuse please"
   Tsayawa tayi tare da kura mashi fararen idanuwanta ..
   "Please wa kika ce ma kike nema "
  Murmushi ta sake mashi tana fadin "Zahra Abdullahi "..
     "To ko zaki bani phone numberki idan na nemo maki
ita nan unguwar din sae na tura maki housenumber
dinsu please !!...ya karashe maganar cikin ky'arma ...
   Kura mashi ido tayi ...ba laifi ya dan manyanta ra fada
a ranshi ..."thanks ...ka barsa" ...ta fada tare da cigaba da
tafiya ...
   "Please na rokeki da girman Allah .." ya fada kamar
zaiyi kuka ...
    Cak ta tsaya tare da sakin murmushi ...takowa yayi har
inda take ..ya mika mata phone dinshi ..hannunta da
yasha jan lalle ta saka ta karbi wayar ta sa mashi
numberta ...
   "Thank you so much beauty" ...ya fada cike da murna
....
   gaba tayi abunda ..da karfi yace .."please me zan sa " ..
   *_DAMSEL SA'ADAH.._*  Ta bashi amsa kai tsaye tana
tafiyarta ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                           🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_51 to 52_*
        Sanin ta dade ne ya sakata bude kofar falon a
hankali ...Tana sanda ....Mahmoud din ta gani zaune bisa
doguwar kujera idonshi a lumshe ...san sadawa tayi a
hankali zata shigr daki ...
   "Hudah ....ya kira sunan can kasan makoshi ...
   Juyowa tayi tana murmushin rashin gaskia tare da
fadan ..."Uncle Allah mamansu lubna ta tsayar dani ..."
     "Su waye suka fita a motar lubna yanzu ? ...ya jeho
mata tambaya..
   "Uncle aikenmu tayi central market muka sawo mata
salad...Allah kuwa" ...
    Bai kuma ce mata komae ba ...ya maida idonshi ya
rufe ...ta dade a tsaye kafin ta shige dakinta ta canza kaya
sannan ta fito ta wuce dakin Hanne ...isketa tayi tana
gyaran gado ...
   "Aunty Hanne na dawo "....
  "Ina kika je ne " ....
  Sae da ta kalli kofa sannan ta matsa kusa da ita tare da
rada mata a kunne !!
   Dariya hanne tayi sannan ta daga mata hannu alamun
jinjina tana fadin ..."Ki dae kular mana da kanki " ..
    Hararan wasa Hudah ta mata kafin tace .."Me zaa dafa
yanzu ",..
   "Ki dafa komae ...bara na ida gyaran dakin sae na fito
nima "...
    Kitchen ta shiga ....ta bude fridge ta fito da kaza ta aje
..sannan ta dauko markadaddun kaya miya da sukayi
kankara ta aje gefe guda ....electric gas ta kunna tare da a
daura tukunya ta zuba man gyada tare da albasa sannan
ta juye kayan miyan ...garlic ta bare ta saka tare da
dakakkiyar citta da kanunfari .....ta rufe tukunyar ...
   Wata tukunyar ta daura ta saka kazan ciki da dan ruwa
kadan tare da albasa da citta da spices ta rufe ....cabbage
ta dauko ta yanka da carrot ....tukunyar da kayan miyan
suke ta koma ...lokacin ruwan cikin kayan miyan sun
tsane ..ta kara mai kadan tare da spices ...bata zuba
gishiri ba don yana da site effect bare ma na buhu
...bayan mintina kadan kitchen din ya dauki kamshi ....stv
fish ta dauko ta gyara sannan ta zuba cikin miyar tare da
cabbage da carrot din da ta yanka...ta rage wutan ta
koma gurin kazanta ...tana zuwa taga ta dahu sossae ...da
yake kazan yana da mai ...ta zuba kuli kulinta a kai tana
motsawa a hankali tare da albasa ...sae da kuli kulin ya bi
kazar sossae sanna ta sauke ta juye a foodflask ....ruwa ta
zuba ta dafa spaghetti tare da peas zallah ....komawa
gurin miyar tayi ta sauketa tare da juyewa a flask ...
      Carrots ta wanke sossae tare da gurje bayanshi
..sannan ta yankashi kanana ta zuba a blender ta
markadata ta tace sannan ta zuba sugar kadan tare da
madara peak ta ruwa ...ta zuba vanilla ginger ...ta hada
...ta saka a fridge ta rufe ...
   Daki ta koma still Hanne na wanka ....Itama wankan ta
yi ta shirya cikin pakistan riga da wando red ta fito ...
Ganin Uncle Mahmoud baya falon ya sakata jera komae
a dining sannan ta shiga ta ma hanne magana suka fito ...
   Hannen ta shiga dakin Mahmoud din ta iske ya fito
daga wanka yana shiryawa ...
  "Looking good yaya"...ta fada tana murmushi ...
   Shima murmushin yayi kafin su fito falon tare
...lokacin Huda na zaune tana jiransu ...kujeran kusa sa
Huda yaja ya zauna ba tare da ya kalleta ba ....
   Serving Huda ta masu sannan suka fara ci ....shi kanshi
so yake ya kalleta amma baya so ta fahimci wani abu
...ga kamshin turarenta ya gama cika mashi hanci
....Kadan kadan Hanne da Hudah suke taba fira ...
   Abinci yaci sossae kafin ya mike ya barsu gurin ...site
din da Hudah take ya juya lokacin da yake kokarin tashi
....itama shi take kallo ....Murmushi suka saki lokaci guda
kafin tayi saurin dauke idonta a kanshi ....kadan ya dan
taka kafarta ..sannan ya juya yacigaba da tafiyar ...
••°°••
  twenty missed call ....ta fada tare da waro ido ...
    New Number ne ...ko baa fada mata ba tasan me ita
...tana kokarin aje wayan aka sake kira ....
   Sae da ta kusa katsewa sannan ta dauka tare da
langwashe murya tayi sallama ...
  Tana jin lokacin da ya sake ajiyar zuciya sannan yace
.."Haba damsel kin san yarda Hankalina yayi masifar
tashi tun dazu nake kira bakya dauka ...dan Darajar Allah
ki taimaka man ki bani lokacinki ...wallahi tun bayan
tafiyarki na kasa samun natsuwa ..harta matata wallahi
kallonta nake maki " ...
   "Ayya bana kusa da wayan ne.. sorry baby " ...ta fada
cikin Husky voice dinta....
  "Ya zanyi Damsel ? .. .lokaci guda kin tafi da tunani
...gaskia ke me sa'a ce *_SA'ADAH_*...Lokaci guda kin tafi
da zuciyar barister shehu ...baki sanni bane da kin
tabbata da you're luckiest person a duniyar nan ..
   Murmushi tayi ..a ranta tace "na sanka shehu sanin da
kai kanka wawan baka yiwa kanka ba " ..
  Amma azahiri shiru ta masa ..cigaba yayi da amayo
mata *_Sirrin zuci_* ...yake ba tare da wani shamaki ba
...Sun kusa 1hour suna wayar har sae da tace zata
kwanta ..sannan ya mata sallama ba don yaso ba !! ...
   Tun da uwar asubaha ya kirata ....dan karamin tsoki ta
ja kafin ta dauki Awayar ...
  "Good morning my damsel ",...ya fada ahankali ...
     "Babyna ka tashi lafiya " ...ta fada kamar mai rada ...
     "Ina fa lafiya na kasa bacci Sa'adah!! ..please ki
taimaka man ki bani address din gidanku na zo yanzu na
ganki dan Allah " ....
   Maryam taji tana bala'in wae ya raina mata hankali
suna kwance yana waya da wata banza ...
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                  🍁
*HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_53 to 54_*
        Tana jin lokacin da ya wanka mata mari tare da
fadin uwarta ce banza ...
  Cikin Shagwaba Hudah tace .."Wae baby hayaniyar me
nake ji haka ...bye ...anjima munyi magana bana son
hayaniya please " ..
  "Yi hakuri Sa'adah .. .bara na bar gurin ...kinga wallahi
nama tashi ...karki katse wayar dan Allah ...."  ya fada
cikin sauri ....
   Duk da sanyin da ake ...can cikin garden ya je ga
rakube gurin flowers yana k'yarman sanyi gudun kar
wani ma yazo ya masa magana ta kashe wayan ....
   ••°°••
    A rana barister Shehu sae ya kirata yafi sau 50 ...duk ta
gama rikita mashi kwakwala ...kullun nacin ta bashi
address din gidansu yake amma sam taki yarda ta bashi
...duk da itama tana so su hadun ...don akwae plan din
da ta
     Tana Zaune barister shehu ya kirata ..sae uwar waya
take tana dariya ....Uncle Mahmoud dake tsaye kusan
30mints ya saurarenta bata sani ba ....
     Yar dariya ta sake mai daukar hankalu tare da fadin
"Everything nawa naka ne babyna ...just fell free wit me
...ni kaina yanzu ji nake kamar ace muna da aure ...da
sae kace baka taba aure ba a rayuwarka ...zan jiyar da kai
soyayyar da matarka bata baka ba before ...
   Shiru tayi kafin ta saki dariya tana fadin ...
     "just ka sa time ...zan turo maka address dina babyna
...you know how much i love you kuwa ???...
    "Jikina da duk wani abunda na mallaka is for you baby
...i reall...
   Ji tayi an fizge wayar da karfi tare da jefar da ita kasa
...a firgice ta juyo tana kallonshi ...hatta jijiyar dake
kanshi ta fito sossae ...
   "  Uncle "...ta fada a firgice ..
  Tsawa ya daka mata "Da uban wa kike waya " ..
   Dukar da kanta tayi kasa ..bara ta iya jin zata fada
mashi gaskia ba yanzu koda zaya daketa ne kuwa ...
   Wani uban mari ya bata yana fadi "For how long kika
mallaka mishi komae naki ...Uban wa yace ke ta shi ke ..?
   "Uncle ...!!
   "Shut up !!! ...ashe abunda yasa kike nacin ki ci gaba da
karatu kenan ...soyayya Hudah as your age 18 years fa
.!!....girgiza kanshi yayi idanunshi suka ciko da kwallah
...first time kenan da ya taba kai hannunshi jikin
hmHudah ba da niyar ya lallasheta ba sae don duka
...juyawa yayi da sauri zaya shige dakinshi...
  Hannunsa ta riko tare da dukawa saman guiwarta
  Cikin kuka tace .."Na tuba uncle ..baran sake ba wallahi
...i promise baran yi soyayyar gaskia da kowa ba wallahi
..please Uncle for morethan 6 years kana tare dani ba
...baka taba sakani kuka ba ...sae ni uncle ?sae nice
Hudah zan saka fitar hawaye a idon mutumin da yafi
kaunata a duniya ...please uncle ka yafe man dan Allah
..!!!
 ...
    Juyowa yayi a hankali yana kallonta kafin ya saka
hannu ya dagota tare da share mata hawayen da suka
bata mata fuska ...sannan ya hade ta da jikinshi ....
  "Bana so Hudah it really hurts ...."...ya fada a hankali
  Daga mashi kai tayi...tare da lafewa jikinshi ...
  ••°°••
  Barister Shehu na zaune maryam ta fito rike da keys din
mota .. ta matse cikin riga da wando ...binta yayi da kallo
...ta gabanshi ta wuce zata fita ...
  "ina zaki haka ? ...bakya da hankaline baki ga yarda kike
ba ? ...ya tambayeta tare da mikewa tsaye  ...
  Wani kallon ta watsa mashi ..."In da nafi wayau zan
koma ..don na lura angulu ma ta koma gidanta na
gaskia !!!
   " Me kike nufi?...kina nufin a haka zaki fita wae ?  .
   "Kana mamakine? ...Shehu kenan ...to zan fita sana 'ane
...oh na manta baka san me nake ba kafin ka aureni ko
...?
   Kallon mamaki ya jefa mata !!
      "Haba meye na wannan kallon ...karfa ka manta akan
karuwarka ka mareni da safe ....nima kuma naga nawa
karuwan suka can suna jirana ..shine naga ya kamata na
kai masu ziyara ....!!!
   Ficewa tayi ta barsa tsaye sake da baki ...ga uwar
sha'awarta da ta taso mashi ....safina ta fito daga daki da
gudu tana kiran ...
     "Mah!!  ..Mah ....zan bi ki "....itama fita tayi waje ta
barshi ..... ganin ta saba fitane ta shiga part din hajiya ya
sashi kyaleta tare da komawa daki ya hade kai da guiwa ..
Feedohm💞
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                 🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
 *_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_55 to 56_*
         Maganganun Maryam suka fara mashi yawo ....wae
karuwanta ...tabbas ba tun yau ya kamata ya gane
maryam yar iska bace ...tunawa yayi da first night dinsu
....ba cikakkiyar mace ya sameta ba ...amma salon da ta
dinga mashi shi ya hanashi mata magana ....sae yanzu
yake tuno wasu abubuwa wanda bariki irinta maryam ta
hanashi gane komae ...
   Wayar Hudah ya fara nema ....Switch off ...yayi kira yafi
dari a take amma bata shiga ...kanshi ya fara mashi ciwo
ya rasa inda zai saka kanshi yaji dadi ...bama maryam
tafi damunshi ba yanxu ...aa Damsel dinshi ...gashi bata
turo mashi address din ta ba bare ya je gidansu
  Zazzabi yake neman rufeshi ...amma sae kokarin kiran
Hudah yake ya kasa samunta ...jin ihun hajiya ne ya sashi
tashi ya fita yana dafa bango .....ko iya bude idonshi baya
yi ...
   A bakin gate ya ga Safina a hannun dad ..hajiya kuwa
sae ihu take kamar tababba ...a hankali ya matsa gurin
  "Lafiya hajiya me ke...."Chak ya tsaya ganin jini a jikin
Safinar ...
  Saurin karbarta yayi a hannun dad din a firgice "Dad
me ya faru ...me ya sami safinar ..ku fada man meke
faruwa ya naga jini a jikinta ..?...take idonshi ya ciko da
kwallah jikinshi sae k'yarma yake ..
   Dad yace "Fyad'e aka mata Shehu ....an cucemu Allah
ya Isa!!!...ya dafe kanshi tare da tokare hannunshi da
bango ...
    Zaman dirshan shehu yayi tare da sakin kuka ...ji yake
da zaiga wanda ya lalata mashi diya ba abunda zai hana
ya kasheshi ....
••°°••
   Hudah na zaune Uncle Mahmoud ya shigo rike da leda
....
    "Uncle sannu da zuwa" ...ta fada a hankali ..
  Dan kallonta yayi tare da sakin murmushi sannan ya
mika mata ledar ...sabuwar wayace Iphone6 ...tare da
mtn sim da recharge card din 5k ...
   Wanni uban tsalle ta saki tare da rungumeshi tana sake
mashi kiss ba tare da ta sani ba ....tureta yayi da karfi ya
shige daki yana mayar da numfashi .....Jingina yayi da
kofar tare da lumshe ido ...
   Huda kuwa Dakin Aunty Hanne ta nufa da gudu ta
nuna mata .....
  "Aunty Uncle ".....ta fada tare da rungumeta ....
   "Uncle na sonki Hudah!!!! ...hanne ta fada da ma'ana
biyu  ....
    Ba tare da ta fahimce ta ba tace ..."Na sani Aunty
Hanne ....Ban san dame zan saka mashi ba ...?
   "Da kanki Hudah 'Zuciyarki ya dace ki bashi Hudah...!!
Hanne ta fada tare da iko Hannun Hudah ..
    Da sauri ta kalli Hannen ..."Aunty amma da wasa kike
ko ? ...ta tambaya a hankali
   "Ba wasa nake ba Hudah ....!!!..ta bata amsa kai tsaya
     " Aunty ki daina wannan maganar please ...Uncle bara
ya iya sona ba ..kawae yana tausayina "...ta mike tare da
fita daga daki ...
    Tana komawa dakinta ...ta hada wayar ...Number
barister shehu tayi dialing ...har ta kusa yankewa sannan
ya dauka ...yana jin maganarta duk ya rude yana
tambayarta lafiya ....Ce mashi tayi bata garin ne taje
maiguri grandynta bata lafiya .....
     Bai yarda ta kashe wayar ba sae da ta bashi full adress
dinta sannan .....ce mata yayi da marece zaya shigo yau
...
   Tun wajen karfe 3 ta fara nacin uncle Mahmoud ya
barta taje gidansu lubna ....hanata yayi daga farko ..sae
da ta fara mashi kuka sannan ya barta ta fita da
zunbuleliyar Hijab dinta .....
   Karfe 4 ya kirata yace yazo kofar gidan ...suna zaune da
lubna alokacin ...ta dan kalleta kafin tace .."ya jira zata
aiko yaro ya shigo dashi ...".
     "  Lubna yazo !! ...ta fada hade da sauke ajiyar zuciya..
   Fahad Lubna ta kwalawa kira tace "yaje ya shigo da
bako yana bakin gate ...sannan ya kaishi falon baki
"....yaron ya amsa da "to" ya fita da sauri
   Mintina kadan yaron ya dawo yace ya kaishi ...Huda
tayi  murmushi sannan ta ciro 1k tace yaje ya sawo
chocolate ...kin karba yayi ya koma ciki da gudu
  Lubna ta sake mata harara ..."Damsel karki fita da
wadannan kayan daukar Alhakin zaiyi yawa ...ko fa rana
baa sa maku ba !!
   "Da waye ...? ..Hudah ta fada tana kallon cikin idonta
   "Barister mana ...sae ki rikitashi wallahi ..."
   Yar dariya ta sake mai sauti tace "Kina tunanin
aurenshi zanyi ke !!!
   Da sauri Lubna ta  kalleta ...
  Amma kafin ta bata amsa ta fice daga dakin da sauri ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                  🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & Perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_57 to 58_*
Cikin takun jan hankali ta shiga falon dauke da
murmushi a kyakykyawar fuskarta  ....duka jikinta
juyawa yake ...da yake riga da siket ne na atampha
holland kuma dinki ya amsheta sossae da yake atamphar
ash ce da orange a jiki...
  Zumbur Barister Shehu ya mike ...ji yake kamar ya je ya
rungumeta amma sam ba da shashanci yake son
Sa'adah ba ...so yake ya aureta ya adanata gidanshi ...don
yanzu sam shida maryam sae kallo gashi ya kasa tabuka
abun kirki a kanta ....
   Katse mashi tunani tayi ta hanyar hure mashi ido
...kamshin mint din bakinta ya sashi lumshe ido ..ya
koma ya zauna kamar wani sakarai...
  "Damsel" ...ya kira sunanta tare da zuba mata ido ...
    "Why ? ...me yasa kike wahalar dani ...2weeks bama
waya wallahi kamar nayi hauka ....bak'ya tausayina
Sa'adah....!!
.
   Kallonshi tayi ...a zahiri ya rame ...amma wannan ba
shine matsalarta ba
    "Ayyah sorry baby ..na fada maka naje maiduguri
gurin grandy ta da bata lafiya ..amma ai yanzu gani na
dawo kuma ina gabanka ..meye na bata rai ...kaga bani
phone dinka dear na tura maka pic dina kaima na tura
naka yarda ko bama kusa da ka gansu zaka ji dadi ko
.....ta karashe maganar tare da langwabe kai ...
  Cikin sauri ya bata wayar yana murmushi tare da fada
mata pin din.. ...
  Janshi ta dinga yi da fira ba tare da ya lura da abunda
take ba ...har sae da ta dauki abunda take so sannan ta
tura mashi pic dinta guda biyu ....
.
   Suna firan tana duba agogo  .....
••°°••
  Ihun da ta saki ne yasa daga Hanne har Uncle
Mahmoud din shiga kitchen da sauri ....
  Tana rike da hannu sae hawaye ke zuba a idonta ....da
sauri ya rike hannun yana kallonta ....yar yankar da tayi
karamace amma duk ta cika gidan da ihu..
   Dan karamin tsoki Hanne tayi ta juya tana fadin "Kin
daiji kunya wallahi ..kamar ba mace ba ".... _Su hanne
mata!!!_
   Uncle Mahmoud din ta kalla da idonta da har yanzu ke
fitar da hawaye ...shima ita yake kallo ...sun fi minti 10
suna kallon juna wanda ke cike da sako kala kala ....ganin
baya da niyar daina kalllonta ga jinin da ke kara tada
mata hankali ya sata fara bugun kirjin shi a hankali
alamun ya mata wani abu ...
.
  "Uncle please do som...!!!.bata karasa ba ya saka
hannun a bakinshi yana tsotse hannun ido a lumshe ....
   Bude ido tayi tana kallon kyakykyawar fuskarshi ...zata
iya rantsuwar tun da take bata taba ganin mutun mai
kyau kamar Uncle dinta ba ....
   A hankali ta janye hannunta a bakinshi ba tare da ta
daina kallonshi ba .......
   Idonshi na lumshe ya janyota jikinshi tare da zagayeta
da hannu ...!!
   Idan har hakan zai saka uncle dinta jin dadi zata iya
tsayuwa a hakan har Allah ya karbi Rayuwarta.....ta fada
aranta bata san ya fito fili ba...
  Ji ta yi ya sake da sauri tare da girgiza kai ...." Bana fatan
Allah ya karbi rayuwarki a haka ba Hudah In Sha Allahu
.....!!
   Binshi tayi da kallo har ya bar kitchen din..sannan ta
jingina da drawers din tare da lumshe ido  ...
••°°••
  Sae da ta kwanta sannan ta bude wayarta ...text din
Barister Shehu ta gani kusa 6 ...ko daya bata bude ba sae
ma tabe baki da tayi sannan ta bude Imo dinta ....
   Hannunta da dungule tare da dagashi sama cikin jin
dadi ...
  Number da tayi saving da Kwad'o tayi dialing thrgh
video call...
*Feedohm💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
               🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITER'S..._
*_59 to 60_*       Cikin Saa yana online ya dauka ...Rufe idonta tayi
tana fadin
  "Uncle nayi fushi kuma baran bude idona ba sae kace
man sorry ...na canza phone da kyar na yi recalling
numberka amma kai ko ka tuna dani haba uncle na
.....oya kace man sorry sannan na kalleka ."..
    Ta fada cikin wata irin murya tare da murmushi a
fuskarta ...wanda ya dada fitowa da ainahin kyawunta ...
   " double sorry pretty"..
    Ya fada cikin sanyin murya ..duk da yana tunanin
mistaken number tayi ba shi bane ...amma da yake ido
ga mata sae yaga bara ya iya barin wannan pretty din ba
ta wuceshi ...
  Ta bude idon da sauri tare da waro ido _wanda ta
tabbata ko uncle tayi wa irinshi sae yafi minti talatin
kafin yabude idonshi ya kura mata ido ..barewa wannan
karen ...wanda take tunanin ko jakka aka daurawa zani
sae ya bita !!!!_
  Haka kuwa ya faru ..don baisan lokacin da ya rungume
wayar ba ..sae alamun zanen shaddah da ta gani ...
  Dariya tayi mara sauti sannan ta datse kiran tare da aje
wayar gefe guda ...
   Kasa hakura yayi ya kirata ..Tana jin alamun ana
kiranta amma ta share wayar ...sae da yayi mata missed
call kusa 5 bata dauka ba ...
    Imo din ta koma ta tura mashi text
   _"am sorry mistake din number nayi..a digit din karshe
instead nasa 6 sae nasa 9 "_
   kafin ta fira har ya fara typing ...
" _Nasan prety ...amma babu ta inda Allah baya hada
mutane_ !!!
   "Ashe kunsa Allah ? ...ta fada a fili sannan ta maida
mashi da "
  " _Ok"..._
   Kiranta yayi a video call ...har sae da ta kusa tsinkewa
sannan ta dauka
   ba kunya ya tasa karamar yarinyar cikinshi gaba yana
mata sabbatu  .   ....
  Kallonshi kawae take tana murmushi kafin tace ..
   "kayi hakuri na fada mata mistaken number nayi
please...!!
   At long last ma cewa yayi ta bashi adress din garin da
take da gidansu ...
   " ba bukata "...ta fada a hankali .."domin gaskia kai
saan ubana ne kaga bara ya yiyu nayi soyayya da kai
ba !!!
   "So baya tsufa pretty" ....ya fada cikin sauri ...
.
   Datse wayarta tayi gaba daya sannan ta kashe .....
  Dad din shehu kuwa cigaba yayi da kiranta amma yaji
ta rufe ...daran ranar kasa bacci yayi ...bai taba haduwa
da yarinyar da ta tafi da imanin shi ba irin yau ....
   tana bude wayarta kamar rige kiran dad din Shehu na
shigowa ..yana katsewa na shehun na shigowa ...bata
dauki ko daya ba ta shige tayo wanka ...dama tun da
daddare mama ta ce da safe Mahmoud ya kawota zata
tayata zama saboda Abba zaiyi tafiya ....
    Bayan ta shirya suka shiga mota ita da Uncle
Mahmoud ..
  Sun dauki hanya sossae ba wanda ya tankawa wani
tsakani ...sae dae lokaci lokaci suna kallon juna ...shiru ya
mata yawa gani take kamar baya lafiyane ...tana so ta
tambayeshi meke damunshi amma ta kasa ...da ky'ar ta
bude baki tace ..
  "Uncle baka lafiyane ? ...tana kallonshi ...
   juyowa yayi a wahale yana kallonta   ..wani murmushi
ta sake mashi da ya sashi ta taka birki da sauri ya kauce
hanya ...
  tsoranta da tayi yasa ta fada jikinshi tare da zagaye
hannunta jikinshi ...sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya
zagaya da hannunshi bayanshi ya riko hannuwanta tare
da zameta jikinshi yana kallon idonta ...
   Bata fuska yayi .."Kin san me kikayi kuwa? ..
*Feedohm💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                  🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_61 to 62_*
        "Uncle me nayi "...ta fada hade da fito ido waje
....yarda tayi tunani haka ta faru ..domin lumshe ido yayi
na tsawon mintina ...
  "Da kin kashemu da kin huta",....ya fada still idonshi a
rufe ...
  Rufe bakinta tayi tana fadin ."Uncle daga murmushi ...
   Harara ya sake mata ...ta kwashe da dariya ...ita kanta
yarda take dariyan so yake ya zame mashi matsala ...
    Tada motar yayi yana fadin "please Hudallah"..
...sauran maganar ya makale a makoshi ....
   Dariyan ta cigaba dayi cikin salo tana kallonshi tare da
fadin  ..."Uncle ...!!! Tare da Jan sunan
   Motar ya kashe ba tare da ya kalleta ba ya fita ...napep
ya tsayar ya zagayo ya bude mata kofar ...
  1k ya daura mata saman cinyarta yana fadin ..."zo ki
wuce Hudah mun hadu acan please " ...
   "Uncle .."..ta fada a shagwabe ...
    "Please Hudah .!!..ya hade hannayenshi guri guda yana
Nuna mata napep
  Ba haushi ya bata ba ...sae dariyar da ta masa ta hau
napep din tana waigeshi ...sae da sukayi nisa sannan ya
tada motar ya tafi gidan shima
  Sae da ya rigasu zuwa gidansu...yana zaune falo ta shigo
tana kwalawa Maman kira ...
  Harara ta sake mashi sannan ta zauna still tana kwalawa
mamanshi kira ...
  mama ta fito tana fadin. ""Wannan kira haka Huda sae
ko fasawa mutun kunne "
  "Mama na gajine mai napep din da ya kawoni zagaye
yayi Dani" ..ta fada tana kallon Uncle din Wanda shima
tunda ta zauna ita yake kallo ..
   "Yo garin ya ? ...ba tare dakuka taho dashi ba ...!!
  "Mama tambayarshi dae... har fa mun taho daga na
mashi dariya shine ya saukeni ya tare man napep yace
na taho ...!!
  Mikewa yayi ya shige ciki ba tare da yace komae ba
...mama kuwa dariya ta masu ..sannan Hudah ta mike
suka shige ciki ...
      ••°°••
 Kwanaki na kara ja....soyayya sossae ake tsakanin Hudah
da Shehu da kuma dad dinshi ...
   duk sun dauki son duniya sun daura mata ...Dad
address din gidansu wata kawarta ta bashi ...duk lokacin
da yace zaya to sae ta shirya ta tafi ....
  Lokaci guda ta gama rikitasu ....Barister Shehu yace
mata yana so suyi aure a wannan shekaran ...
  Ce mashi tayi  "bara ta iya auren mai mata ba Wallahi
sae dae idan zai saki matanshi sannan zata yarda ta
aureshi ..!!.
  Kamar ta mashi asiri yace ya yarda zai saki maryam din
yau ....Ita dae bata ce mashi komae ba sae murmushin
da ta mashi ...
    Ranar da ya saki maryam din ranar yazo gidansu
lubna gurinta ....
   Da kyar dama uncle Mahmoud ya barta ....bayan sun
gama firansu ne ta rakoshi ....ko a wajen janta yake da
fira sam idan yana tare da Sa'adah baya so ya rabu da ita
....murmushi kawae take mai cike da ma'anoni daban
daban ....Karar motar Uncle Mahmoud taji ta juya da
sauri tana kallonshi ...Ji tayi numfashinta na Neman
barin jikinta ..da kyar ta tsaida natsuwarta guri guda.....
  Kallon kallo suke su duka ukun ....wanda barister shehu
yafi maida hankalinshi ga Barister Mahmoud ...Hudah
kuwa dukar da kai tayi kasa
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                     🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm*💞
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_63 to 64_*
Ba tare da yace komae ba ya figi motar ya koma cikin
gida kamar zaya tashi sama
  Barister shehu ya saki ajiyar zuciya yana fadin ...
  "Kin san wancan ne Sa'adah ? ...
  Girgiza mashi kai tayi tana murmushin yake ..  "
   "kai ka sanshi ne ? ...ta tambaya tare da kura mashi ido
    " Yeah ...da gurin aikin mu daya ..Don shine ma
babban mu ..but yanzu ya bar gurin aikin for morethan
5years ban san inda ya koma ba ...amma naga yana maki
wani kallo ...ko ya kyasa ne ...?
  Murmushi tayi ba tare da tace komae ba ...
   " Kwalelenshi ...Sa'adah sae Shehu,! ...Ya fada yana
murmushi ...
   "Jiya munyi magana da dad ...yace zaa turo gidanku ...!!
  Ba tare da tace mashi komae ba sae juyawa da tayi tana
daga mashi hannu ....
  Dakin Lubna ta fada tare da fashewa da kuka ...
  "Damsel menene ? ...wani abu ya maki ...ko cewa yayi
baya sonki ....please kiyi magana mana !!!  ..ta fada a rude
tare da rike kafadarta ...
   "Uncle Lubna ...Uncle ya ganni da mutumin da ya fi
tsana a duniya ....!!! ..ta fada cikin kuka ...
    " Ina ya sanshi Damsel ? ...ya akai kika san baya
kaunarshi ...? ..shin uncle din ya maki magana ne ? ...
    "I know everything a tsakaninsu lubna ...wanda shi
kanshi uncle din bai san na sani ba ...!!!
    "Kinga damsel kije kiyi magana da Uncle din mana
...may be ma shi bai dauka da wata manufa ba ....!!
   Ba tare da tace komae ba ta dauki zunbulelen Hijab
dinta ta saka sannan ta fita cikin sanyin jiki ...yarda taga
yayi parking din motar sae da gabanta ya fadi ....
   Tana shiga falon ta iskeni tsaye hanne na tsugunne sae
uban bala'i yake mata .....fuskarnan tashi jawur kamar
an saka mashi ruwan zafi .  ...
  bai bari ta shigo sossae ba ya shakareta tare da wurga
ta saman kujera ...kafarshi yasa ya take mata ciki  ...Uban
ihu ta sake tana hawaye ...
   "Kinsan Uban waye kike tare dashi !!! ...ya fada cikin
tsawa ...
     ihu ta sake ta kasa magana saboda wuyanta da ya
shake ...hanne ta taho tana rikeshi tare da kuka  ..
  "Dan Allah ka barta " ...kar ka kashe masu yarinya
" ...haba ya....Wani uban mari ya sake mata tare da
hankadata gefe guda ...!!
   "Bansan baki da hankali ba sae Yau Hudah  ...kin san da
uban wakike tare ...fada man tun yaushe kike soyayya da
wannan banzan ....!!
   Batace komae ba sae uban kukan ta take mashi
.....dukanta ya fara yi yana tambayarta ...amma bata
masa magana ba ...
   Ganin kamar kara haukacewa yake yana sabbatu ya
sata kokarin kwatar kanka ....fa kyar ta mike daga inda
take ....da gudu ta ruga zata shige daki ...kafa ya saka ya
tadiyeta ta fadi kasa da karfi ...bakinta ya fara fitar da jini
...still fizgarta yayi da karfi ta mike tsaye ya hadeta da
karfi ...Hanne kuwa Kuka take iya ranta ...gani take kamar
yazauce ....
   "Wane irin so kake mata Yaya ...wanda yasa zaka iya
kasheta don ta tsaya da wani namiji ? ...Hanne ta fada
tare da rike mashi hannu tana kuka ...
  ita da Hudah ya hade guri Guda ....Kamar garwashi haka
Hudah ke ji a ranta ...barata iya daukar wannan dukan
ba anymore ....bata san tana da karfi ba sae yau
....Hannun Uncle Mahmoud din ta rike tana kallonshi
tare da angazashi baya da karfi ...
   "ka daina Uncle !!! ....ta fada cikin tsawa ...tuni idonta ya
bar zubar da kwalla ya bushe tare da sauya kala ...
 Yarda tayi tsawar ya sakashi kallonta shima  ...
   "Ka dauka ban san Waye Barister Shehu ba ? ...to na
sanshi ...sanin da shi kanshi wawan bai wa kanshi ba ...ko
ka dauka soyayya nake dashi ...!!! ...ta kareshe maganar
cikin tsawa ...
     Daga Uncle Mahmoud din har Hanne tsayawa sukayi
suna kallonta ...
   "Mutumin da yayi sanadiyar rabani da Mahaifiyata ya
rabani da yaya sa'ata ...a tunaninka shi zan so
uncle ? ...Juyar da kanta tayi ga barin kallonshi . ..."ya ma
yayata Fyad'e ..mukaje gidan Ubanshi yace ya sake mata
idan yaso....a gaba suka wulakanta ta ...Anan Mamarmu
ta rasu tsakar titi Uncle ...yaya Sa'a ta samu cutar
HIV..shin kasan wacece yaya sa'atah? ..sannan kake
tunanin  ya ci bulus Kenan ? ..  *_A DALILIN YAYATA_* na
ke tare dashi ...hakan yasa na rasa Mamata ...Uncle shine
ya kawo mana dukiyarmu ta gado sannan ya biyo dare
da yan fashi suka sace *Harda kai ciki Uncle*!! .....ta fada
tare da nunoshi da karfi....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                    🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_65 to 66_*
         Baya yayi tare da fadawa saman kujera yana
kallonta  ...
    "Hudah ...!!... ya fada a firgice ..
  "Quite Uncle !!! .....ko zan manta idon kowa baran mata
idon mutumin da na fada jikinshi ba lokacin da Shehu ke
kokarin dauki jikkar kudin ... .Da zoben dake hannunka
na kara tabbatarwa lokacin da kazo gidanmu da safe
Uncle ..idan har zaka lura har zoben na taba lokacin da
ka daura hannunka saman jikina..!!! ...
   Har inda yake ta tako tare da dukawa kasan kujeran
hannunta saka ta dago hannunshi ta zare zoben dake
jikinshi tare da sakawa cikin dusbin ....sannan ta dago
fuskarshi ...
  "Uncle aka pictures kadae ? ...ka shiga gidan
marayu? ...haba Uncle ...na sani kana son Abbanka
amma Uncle bai kamata kaso naka ka tarwatsa wasu ba
...kowa Uncle idan shi aka ma haka na tabbata hakan zai
aikata ..Uncle na goge pictures din duka....!! ..Nagode
sossae Uncle har yanzu baka canza ba a raina !!!
  "Hudallah" ....ya fada ahankali ...
  Hannunta ta daura saman lips dinshi tare da mikewa
taja Hannun Hanne da tayi mutuwar tsaye tana kallonsu
....
••°°••
  Soyayya kuma da mutanen bata fasa ba ...sae dae bata
kara yarda wani yazo gurinta ba cikinsu ....
  Kusan kwana uku bata ganshi ba .. .. tana so taje taga ko
lafiya amma tana kunyarshi. . yarda ta dinga mashi
tsawa ranar da abun ya faru sae take ganin kamar bata
mashi halacci ba ...
   A hankali ta dan kalli Hanne dake cin abincinta hankali
kwance.....
   "Aunty Hanne wae Uncle baya garin ne ko baya
lafiya ? ...ta fada tare da dan goge hawayen da suka zubo
mata da bayan hannu...
   Ta dade tana kallonta kafin ta girgiza kai tace ..
    "amma dae Hudah baki da zuciya mutumin da ya
dakeki kamar jaka shine kike tambayarshi ...cab wallahi
ni ko magana bana mashi ..."
  Aunty baki san waye Uncle ba ko?.. ...ta tambayeta tana
kallonta ..."Dan Allah ki yafe mashi kinji!!!
  "Ke ai kin sanshi.. sakara mara zuciya anan falon ya
gama cin ubanmu amma dan kina banza shine zakice na
yafe mashi..." ...ta mike tare da shigewa daki abunta ...
   Ita kam bara ta iya fushi da Uncle dinta ba..kwana
biyun nan ma da bata ganshi ba Allah kadae yasan yarda
take ji ...Uncle dinta ya riga ya zama wani sirri azuciyarta
wanda ba kowa ne zai fahimta ba .. ...
    mikewa tayi ta nufi dakinshi tare da turawa a hankali
dauke da sallama.....
  Zaune yake ya hade kai da guiwa ...kneeldown tayi kusa
dashi tare da dafa kafarshi da hannunta ...
   Ko bai dago ba kamshinta ya sanar dashi wacece ...
   "Uncle "...ta kira sunanshi a hankali ..
   Dagowa yayi yana kallonta ....da alama kuka yayi yarda
idanuwanshi suka canza kala ...itama kukan ke niyar
kwace mata ...
   "Uncle me ke damunka ? ..ta fada a hankali ..
   "Am sorry Hudah ...dan Allah ki yafe m"...
    saurin toshe mashi baki tayi da hannunta tana girgiza
mashi kai ....
   "Dan Allah ka bar fadin haka uncle..wallahi baka da
wani bashin yafiya da kake bani ..ni ce nake dauke da
bashin alkhairinka a tare dani ...!!!
     "Tashi muje Uncle ..please kawae ka biyoni Uncle am
assure baka ci komae ba Uncle..!! ...hannunshi taja ba
tare da ta jira abunda zai ce ba ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                   🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
*_67 to 68_*
    Kitchen ta ja tana fadin "uncle zaune..!!
   "Me zan dafa maka uncle ?
Shiru ya mata yana kallonta ..."Zakaci indomie ko, Na
dafa maka irish da sauce? ...
  Shiru ya mata ...juya idanunta tayi tana turo
baki  .."Uncle su kadae na iya fa !!
      Dan murmushi ya mata ba tare da yace komae ba ...
  Attarugu da Albasa ta mika mashi tace yayi mata
grinding dinsu ....irish ta dafa sannan ta hada mashi
sauce da taji albasa da kifi busasshe sae kwai ....
  Lallabashi take tana so ya saki jiki da ita kamar da
...bayan ya gama ci ta hada mashi ruwan wanka sannan
ta fita ta barshi ...
   ••°°••
  Tana ganin ya tafi office ta cewa Hanne zata je ta dawo
....general hospital ta nufa ...direct dakin da masu karbar
maganin HIV ta nufa ...duk da baa barin marasa cutar su
shiga da yake sirri ce ...sae da ta ba masu tsoron gurin
20k suka barta ta shiga ta zauna tana kallon yan matan
dake zuwa karbar maganin ...
     Da sauri ta bi bayan wata yar kyakykyawa bayan ta
fita daga gurin ..sallama ta mata ta amsa tare da juyowa
sukayi musayar murmushi ...
  "Mu dan samu guri mu zauna please muyi wata
magana !!! ...huda ta fada dauke da fara'a..
    Cikin asibitin suka koma suka samu wani guri safe da
babu koma suka zauna bisa fararen kujeru ...
   "Wani aiki nake so kiyi man sister please" ...huda ta
fada tare da kamo hannunta ...
   "Wane irin aiki yar'uwa? ...itama ta fada dauke da
murmushi ...
    " Ina so kiyi sex da wani mutumi ...please !!...ta fada a
hankali ..
   Da sauri budurwa ta kalleta ...zatayi magana hudah
tace "please zan biyaki ko nawa ne " ..
   Idanuwan budurwa suka kawo ruwa ...tace "me yasa
Yar'uwa .. kema sun tabaki ne ? ...
   Hudah tace "Sun man babban tabone"....idanuwanta
suka ciko da kwalllah  ..
   Sauke ajiyar zuciya tayi ..."Zan maki ko ba kudi sister
...kin ganni nan wallahi yanzu banki ace duka lalatattun
maza suna dauke da cutar da nake tare da ita ba ..kadan
cikinsu ne na kirki ...Ina da saurayi har an sa mana rana
dashi  ..ana gab da bikinmu don har sadaki yakawo
..yace na rakashi unguwa ...wani gida ya kaini yace ai
yanzu na riga na zama matarshi tunda har an bada
sadaki ...ya yaudareni sossae har yayi amfani dani
...wallahi tundaga lokacin bai kuma zuwa gidanmu ba
...ashe yana dauke da cutar ..shine asalin lika man ita"..
   Murmushi Huda tayi tare da fito da wayarta ta fara
kiran number dad din shehu ...rejecting yayi ya kirata ...
    "Please kana ina ..?
 "Ina nan Guest House dina lafiya Prety? ...
  "Zamuyi discussing wani serious issue ne yanzu ..."
    "To bara bazo gida na sameki yanzu ..just ki bani
5mints ganinan zuwa Pretty" ....ya fada cikin sauri
  "No bani adress din nima na fito ina hanya man .."..
  "Ok pretty ...Sardauna estate No 6 dandume road ....'"
   katse wayar tayi tana kallon budurwar ...
   "Hudallah Ibrahim" ..ke fa ?
    " Shafa'atu kabir" ....ta fada dauke da fara'a ...
   "Please kinsan maganin da zaiyi raising  fellings din
mutun lokaci guda ?
  Shafa'atun ta bude jikarta ta fito da wani abu ta mika
mata  .."Kinga wani nan nima banishi akayi na kaiwa
hajiyarmu ..gashi " ...ta mikawa Hudahn ..
   Dae dae kofar gidan suka tsaya ta kirashi tare da fadin
Sun iso ...
  Fitowa yayi da babbar riga da alamun ko dogon wando
babu ciki ...
  Suna Shiga suka zazzauna ya bude fridge tare da fito
masu da fresh milk ya zuba masu a cup ya mika masu ..
  "Prety wannan special visit haka ? ...bakuwa barka da
zuwa . .!!.
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                     🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_69 to 70_*
    Lumshe ido Huda tayi ..."sweetheart bakuwata bata
shan fresh milk a bata coke   ..'" ..j
   Mikewa yayi yana fadin.."to to pretty " ...da sauri ta
zuba abun cikin cup din dake hannunta tare da girgizawa
ahankali ...har ya narke ...
   Yana zama ta koma bisa hannun kujeranshi tare da
kanga mashi cup din a baki tana murmushi ...yana
kallonta har ya gama kwankwadewa sannan ta koma
kusa da Shafa tana kallonshi ...
   Mika yayi ...yana kallonsu ...kadan kadan take dan
janshi da fira ...tun yana bata amsa har ya fara gyada kai
yana mika ....cire babban rigar yayi ..da sauri ta kauda
kai gefe ...ganin pant ne a jikinshi ...ga stick dinshi ta
mike ...
   K'yarma ta fara ganin ya nufo gurinta ....nannade siket
dinta tayi ta kwasa da gudu tana fadin ..."Shafa'atu
please kiji dashi ..!!..
  A bakin kofar gidan ta zauna har lokacin gabanta bai
bar faduwa ba ....
  Kusan minti talatin tana jiranta sae uban tsaki take
zabgawa bata ga abun dadewa a ciki ba ...
   Cikin gidan ta koma ga mamakinta sae taga Shafa'atu
tana soka mashi allura a hannun .da jini a ciki ...
  Ido ta waro "Ke shafa'atu ya haka karfa ki kashe mutun
gaskia" ...
   Dan juyowa tayi tare da jefa mashi rigarshi saman
jikinshi sannan ta dauki gyalenta ...suka barshi sae uban
nishi yake taja hannun Hudah suka fita ...
   Hudah ta kasa hakuri ..."Alluran me kika mashi wae ? ...
   "Jinina ne na zuba mashi a ciki ...ko bata shigeshi da
sex ba ta shigeshi yanzu ...sai nan da six month zata yi
mugun kamashi ...karki damu ..dama muna haka  .mafi
yawancin abunda zaki saya gurin masu cutar suna zuba
jininsu aciki wallahi ...!!!
   ••°°••
   Suna zaune da Hanne tace ..."Hudah Yaya na nemanki
...!!
   Ji tayi gabanta ya fadi ...bata san dalili ba ...ta mike ta
zata tafi ji tayi hanne na mata dariya tare da fadin
..."bara ki shafa powder ba da lip gloss .?..
   bata san dalili ba sae ta sami kanta da hararan Hannen
....
  Har zata shiga dakin sae kuma ta shige dakinta ...samun
kanta tayi da shafa powder har da janbaki sannan ta fito
...
   Bata shiga can cikin master din ba sae tsayawa tayi
daga dan falon inda kujeru suke tana fadin ...
  "Uncle gani....!!!
  Bai ce komae ba har sae da yaga ma sa shaddarshi light
blue da akawa aiki da zare baki ....ya daura agogo sannan
ya fito ...
  Suna hada ido ta sakar mashi murmushi don ba
karamin kyau kayan suka mashi ba ...
  "Eyeh Uncle daurin aure zaka je ne" ...ta fada tana
murmushi ...
   Shima murmushin yayi tare da zama kujeran dake
kallon tata ....
  "Hudallah ."...Ya kira sunanta ...
   " Na'am Uncle kayi kyau sossae kamar a saceka ..."....ta
langwabe kai ..
 "Ko"
"Huh ,baka duba mirrow bane ?...ta fada yana murmushi
..
    " Sanin nayi kyau dinne yasa na kiraki na tambayeki ..
Zaki auri Uncle din kin? ...ya tambayeta kai tsaye ..ba tare
da tunanin komae ba ...
  Da sauri ta rufe idonta da hannayenta tare da mikewa
zata gudu ...carab ya cafke hannuta guda .. tsaye tayi ba
tare da ta juyo ba ...mikewa yayi shima ya rike kafadunta
ya juyo da ita ....
   A kunnenta ya rada mata ..."Answer me please
"....tsigar jikinta ta tashi tayi saurin matse jikinta gam
tana kallon kafafuwanshi...
   "Please uncle ka sakeni ..." ...ta fada a hankali ...
  "Sae kin amsa man.. .this time biscuit din da kaina zan
sawo maki yarda zaki ji dadin zama cikakkiyar matar
Uncle dinki ..."...ya karashe maganar cikin zolaya ...
    Fizge hannunta tayi ta ruga da gudu tana rufe bakinta
.....
   Daki ta shiga tare da fadawa saman gado tana mirgina
......pillow ta janyo tare da kankamewa ...murmushi ya
sake yana kallonta ...farincikin da ya gani a idon Hudah
shiya tabbatar mashi da tsantsar soyayyar da take mashi
...
   "Ki daina Hugging pillow haka mana ' dani kika yi
hugging may be da kinfi jin dadin sossae" ....ya fada cike
da zolaya ....
     Pillown ta wurgo mashi tare da lullube fuskarta da
zanin gadon tana dariya ....yafi minti 10 yana kallonta
sannan ya shiga gurin hanne ya mata bankwana tare da
kissing dinta a baki ...for the first time kenan a rayuwarta
....sae yanzu ta gane Hudah haskene ga dukkanin gidan...
  dakin Hudah ta fada tana zolayarta wae "amaryar
Uncle" ...kallon mamaki Ta bita hannen da shi a
tunaninta zatayi kishi sae ma taga kamar tana cikin farin
ciki da abun  .
    Mahmoud kuwa gidan liman ya wuce...da yake duk
wani abun Huda sae ya gaya mashi ....magana suka je
Sukayi .. liman yayi farinciki sossae da jin Mahmoud din
zai auri Hudah ...ce mashi yayi duk lokacin da ya shirya
yazo a saka rana ....
   Duk da bata da kowa ..amma duk wani abun alada sae
da Mahmoud ya kawo aka saka rana wata 8 ...ba yarda
Mahmoud din baiyi ba akan a barshi  wata biyu ...amma
liman yace " So yake yama Hudah duk wani abunda Uba
kewa diyarshi ...nan da wata takwas yake tunanin
kudinshi zata su fito don Haka yayi hakuri ya jira.". ....
   Ba yarda Uncle Mahmoud din ya iya haka aka barshi
...Hanne ya gaya mawa..Sae a gurinta ma Hudah ke ji ...
••°°••
    Barister Shehu na gida aka bugo mashi waya wae
shagonshi na zinarai wuta ta kama ...ba'a samu aka fitar
da komae ba duk sun narke ....
   Sae da ya kwanta asibiti kwana 8 sannan aka
sallamoshi ....Hajiya tayi ta wahala dashi don dad yanzu
hankalinshi yana ga Hudah ....ko ya kirata waya bata
dauka sae ta ga dama ...sannan yayi nacin yazo gidansu
ta hanashi .....
  Bayan an sallamo shi da gardadin a guji abunda zai bata
mashi rai saboda yana da ciwon zuciya ga kuma hawan
jini ...Part din hajiya ya koma ...dama safina na can
tunda ya saki maryam ....
   Da marece ya shirya yaje gurin Hudah ...satar hanya
tayi ta iskeshi gidan su lubna ...
  Yana zaune saman kujera duk ya rame ....ta dan kalleshi
tare da kau da kai ...
  Yana ganinta ya mike har kyarma yake  ..don kwana
biyun nan da baya ganinta sae yaga ta kara wani bala'in
kyau ....
     B'ata fuska tayi kamar zatayi kuka
....Tana gaidashi ....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                    🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
     _Na rigaya na sadaukar da wannan book din ga
exclusive da babu abunda zai hanani sadaukar maki da
wannan page din Sweet Farida ... Amma duk da haka ina
maki fatan alkhairi tare da addu'ar samun zuri'a ta gari
...._😘
 *_70 to 71_*
         "Bakomae ."...ta fada tare da kawar da kai gefe guda
tana matse hawaye ....
   "Ya zaki ce ba komae damsel ....Allah ki fada man meke
faruwa ne ...indae ba so kike nima nayi kukan ba ..!!..
   A hankali tace ..."ina yaron da na aiko farkon zuwanka
nan gidan ya shigo da kai....?
  "Eh na tunashi ..wani abu ya sameshi .?...
  "Eh ..ya samu neotrophy ne _ita kanta bata san abunda
kalmar take nufi ba ..jikin kwalin sabulu taga neotrophy
din_ ...shine muke so mu fitar dashi india a masa aiki
...ga dad baya nan ...bama so mu fada mashi saboda
yana da hawan jini ...to kudin ne sun tsaya cak ...ban san
yarda zaayi ba!! ....ta fada tare da goge kwallah da suka
zubo mata ...
   "Haba damsel akan kudu kike kuka  ...duk da shagona
ya kone bayan na gama zuba dukiyata hakan bara ya
hana na samo maki kudi ba duk inda suke ....nawa ne
kike bukata ? ..
  "ka barsa sweetheart" ...ta fada a hankali ...
   "No dan darajar Allah ki fada man nawa kike bukata
...."
   "Kudin na da yawa fa ...ka barshi kawae nagode!!! ....
   "Aa dan Allah wallahi ko nawa ne zan baki !!....
   "ok 20m "....ta fada tare da kura mashi ido tana
karantarshi ...
    Cikin sauri yace ..."ba matsala damsel insha Allah zan
kawo maki zuwa jibi .....
  "Ina zaka samesu bayan kace shagonka ya kone " ....
   "Takardun gidan da muke ciki yana hannuna ...zan
sayar dashi ba da sanin dad ba ...na tabbata nan da one
year na tara kudin sae na mayar masu da kudinsu na
karbi gidan ....ba tare da kowa ya sani ba !!!!
    tasowa tayi tare da kissing nashi a goshi sannan ta
koma suka cigaba da fira ....
  Bayan ya tafine ta kira dad dinshi tace tana bukatar
20M ...tana so ta sayi mota da dan karamin gida ..saboda
friends dinta sun fara mata gori cikinsu itace batta da
mota da gida ....suna gama wayar ya mata transfer kudin
da yake akwae su ...
  ••°°°••
  So take ta tashi tayi inserting farin pure miskin da lubna
ta bata tun da aka samata rana tace duk one month da
ta dinga inserting...satar kallon Uncle din tayi taga ya
maida hankalinshi ga news yana kallo ....Hanne dama ba
gwanar fira bace ...ya shige daki abunta..
  Mikewa tayi da sauri tare da fadawa daki ta shige toilet
ta dauki cotton kadan ta dangwalo .....wani uban ihu ta
sake tana dire dire ...
   Da sauri ya shigo dakin yana kiranta ...ganin tana toilet
ne ya sashi tsayawa bakin toilet din ..
  "Hudah .....menene ?
  Kokarin kunna heater take ta kasa sae uban ihu take
tana tsalle ...
   "Na shigo Hudah? ....ya fada a hankali ...jin ihun nata
yayi yawa ...
   bata bashi amsa ba ta cigaba da ihunta ....tura toilet din
yayi ya shiga da sauri ....kwalbar miskin ya gani da cotton
din da ta dangwalo ...ita kuma tana gefe sae uban ihu
take  ...
  Ko baa fada mashi ba ya san abunda takewa ihun ....duk
da ta bashi tausayi amma dariya yake mata ....bai ga
wanda ya sakata ba kilbibi ne irin nata .....
   Cikin kuluwa da dariyar da yake mata ta juyo tana
hararanshi tare da watsa mashi ruwan sanyin da ke cikin
bucket ....
  "Ba komae kije da zafinki .....see ..naga wani abu irin
wannan a gurin wata mata idan na fita zan sayo maki sae
ki kara sakawa ..tunda naga kin girma da yawa ....!!! ...ya
fada yana dariya ...
   Da sauri ta juya ta hade kanta da bango cike da kunya
...ga azabar take ji ...Allah ya isa kuwa ta jawa Lubna yafi
cikin kwando .....
  Kamar yarda barister shehu ya fada ...haka ta faru
...gidan da suke ciki ya sayar a tunaninshi nan da shekara
daya idan ya samu ya maida masu gidansu ...da marece
ya kawo mata kudin ....ba tare da sanin kowa ba ta
rabasu uku ...kashi daya ta kai gidan marayu akan Allah
ya kai ladar kabarin Yaya Saa ....sannan gudan ne ta
kaiwa Aunty hanne tace ta boye mata ....sauran gudan
kuwa ...babban masallacin garin ta kai tace a gyara shi
sannan a sayi duk abunda zaa bukata ....ta sadaukarwa
Yaya sa'a da mamanta sae babanta .
..
  ••°°••
  Barister Shehu ne ke fada mata dad dinshi baya lafiya
...45%t fever ...ga diarrhea sossae ......"Allah ya sawake ta
fada ."...!!
  °°••°°
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                    🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS...._
*_72 to 73_*
   Tun daga ranar da uncle ya kamata tana matsi bata
kuma bari suka hada ido ba ...tana kwance tana chat
dinta ...ya shigo tare da tsaya bakin kofar ya zuba mata
ido ...rigar dake jikinta cottonsilk orange ta bi mata jiki
sannan iyakarta guiwa ....cinyoyinta sun fito kamar irin
na turawan nan ..sae gashinta data hade shi ta daure
baya ....
   Bude hanci take tana shakar kamshin uncle a
tunanunta daga dakinshi kamshi ke fitowa ...
   Pictures dinshi ta nuno tare da rungume wayar tana
fadin..." I miss you uncle ...matsalanka ka fiye gano
abunda yafi karfinka ...
    Wa yace yafi karfina ....?
  Da sauri ta juyo tana waro ido kafin ta boye kanta cikin
pillow ....
  dan murmushi yayi kasa kasa yace .."ki tashi ki shirya
zaki rakani unguwa "..
  ba tare da ya jira amsarta ba ya wuce abunshi ....dakin
hanne ya shiga yace ta shirya zasu tafi ....wata uwar
harara ta watsa mashi don tun dukan da ya masu over
6month take rike dashi ....
  "Bana zuwa " ...ta fada tare da gyara kwanciyarta ....
  Ba tare da yace komae ba ya juya ...amma a zahirin
gaskia baya kaunar mutun mai riko ..
wacce yama dukan ma ita da kanta ta nemeshi tare da
ba shi hakuri duk da shi ya dace ya bata din ....
   Dan karamin tsoki ya sake dae dae lokacin da Hudah ta
fito daga dakinta sanye da gown red ....
   a tunaninta da ita yake tayi saurin kallonshi tana fadin
..."Uncle sorry wallahi gyalen na rasa inda yake "...
   Dan murmushi yayi yace "Baki man komae ba Hudah
....kinyi kyau sossae ....amma bara ki fita a haka ba ...."
     komawa yayi dakin ...cikin kayanta ya dauko mata
bakar hijab  mai hannu tare da mika mata ta sanya tana
murmushi ....
  A mota ma duk sec sae sun kalli juna tare da sake
murmushi ...
  "Zaki zauna da Auntyn kine koko kinfi so na ajeki GRA
ke kadae" ...ya fada tare da dan kallonta ...
  Shiru ta masa ba tare da tace komae ba ...juyowa yayi
yana kallonta yaga gaba daya hankalinta ba ga motocin
dake kokarin wucesu ....hannunta ya janyo tare da kura
mata ido ....
  "Bakya jine ".....ya fada dae dae kunnenta ...
  "Me kace Uncle ? ....ta fada tare da zame hannunta daga
nashi ...
   Kafarda ya janyo yana kokarin rungumeta .."may be
idan kina jikina kya fi fahimtar abunda nake fada ...."
   "Wallahi uncle naji ..ka sakeni please !!..
  Hararanta yayi sannan yace .."bana jin kinji abunda na
fada tunda baki bani amsa ba !! ...ya fada tare da kokarin
hade bakinta ...
   cikin sauri tace .." Uncle please ka daena ....da Aunty
hanne zan zauna "...ta fada tana kallonshi da idanuwanta
ta suka koma kalar kuka ...
   Dariya yayi kasa kasa tare da sakinta yana kallonta
...turo baki tayi tana fadin ...
      "Saukeni na tafi a napep ni dae !!
    "A da kenan Hudah lokacin da nake tsoron na tabaki
ba yanzu ba da kika zama tawa ...kina iya yin duk kalar
abunda kika so ..am ready na bi da ke yarda kike so
...duk da dama kin shirya don har ...!!.
  Hannunta ta sa abakinshi tayi rau rau da ido .."
  ".Uncle Dan Allah kabar fada ...wallahi lubna ta bani ....!!
   wani fitinannen kallo ya watsa mata tayi saurin maida
kanta kasa tare da zame hannunta daga bakinshi ...
   Central market ya nufa da ita ...wani katon shago suka
shiga ....Wasu kayane gefe guda ...gurin suka nufa ...
  "Ki duba abun da bai maki ba ...gobe zai koma dubai
din sae ya sako maki wasu ..." ..ya fada yana kokarin
daga mata kayan
   Wani fitinannen kallo ta sake mashi tare da juyawa ta
fita daga shagon ta koma mota ta zauna ....
   Kallonshi tayi cikin natsuwa lokacin da yake kokarin
kunna motar tace
  "Uncle idan zaka hada man lefe har sae kazo dani na
gani ...? ..Uncle zan iya aurenka ko babu lefe kuma na
rayu dakai kamar baiwa..Ka mani komai a rayuwata
uncle bansan dame zan saka maka ba ...!!
   So yake ya kashe maganar yace "Lubna ta cigaba da
baki abunda take baki ke kuma ...!!
  Kuka ta sake da karfi tana kokarin bude motar ta fita
...hannunta ya rike yana dariya ...ita kuma sae neman
kwacewa take ...
  "Sorry Hudallah na daina kinji ko !! ...ya fada dae dae
kunnenta ...
   Kallonshi tayi tana turo baki ...sannan tace
"promise" ...a hankali ...
   Lumshe idonshi yayi tare da daga mata kai ......kafin ya
budesu tar ya zuba mata cikin salon soyayya ...juyar da
kai tayi tana kallon waje dauke da murmushi ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                   🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_74 to 75_*
*_3 month ..._*
  Shirye shiryen biki ake sossae ..hanne ta zage sae gyara
Hudah dun bata mata kallon kishiya sae yar 'uwa duk da
akwae dan kishin kadan a ranta ..amma ta tabbata idan
har ta fiyo dashi to batawa Mahmoud adalci ba ...tun da
har ya jure zama da ita tsawon shekaru ba tare da cin
mutunci ba...
   "Aunty Hanne Dan Allah bara naje na dawo ...Lubna
tashi muje !!!!
   Hanne tace ..".ina zaki Hudah ..so kike mutane su
zargeni ...duka gobe fa daurin aurenki kuma zaki fita ...aa
gaskia !!
   Hudah ta riko da hannunta ..."Please aunty
hanne...wallahi daga yau baran sake irin wannan fitar ba
...dan Allah ....kinji auntyna ...!.
    " To Hudah ...ki kula amma kinji ko !!!
   "Yauwa" ....ta fizgi hannun Lubna suka fice ....Motar
Mahmoud din suka shiga ...
    "Ina za mujene ? ...lubna ta tambayeta ...
  Hararanta tayi ..Gidansu Shehu ...!
   "Amma Damsel baki da imani ..bayan kinki aureshi
kuma har da zuwa gidansu ki masa me ....?
  Bata ce mata komar ba tayi parking kofar gidan ...tare
da fito da wayarta ta kira Shehun ...ta tambayeshi "yana
gida ..".ce mata yayi. " eh yanzu ya dawo shi da dad
asibiti suka karbo magani ..."
   Lubna ta kalli .."fito muje" ...ta fada tare da yin gaba
abunta...
   Ba tare da tayi sallama ba ta hankade labulen falon
....cikin saa su duka ukun na zaune sae safina dake gefe
guda tana wasa ...
   Zumbur Dad da shehu suka mike ....Dad yace
..."Pretty"...kafin ya rufe baki Shehu yace "Sa'adah
",....sannan suka kalli juna tare ....
   Yar dariya ta sake ..kafin tace ..
 "Sa'adah ..damsel Pretty.. ..amma asalin sunan Hudallah
Ibrahim _!!! ...
   "Hudallah .".su duka duka maimata har da hajiya data
mike lokacin ..
  "Kwarae amma ba farat daya karamar kwalwarku zata
fahimta ba ...Soyayya ......da uba da dansa ....!!
   " Damsel ..".barister shehu ya fada tare da matsowa
kusa da ita ..."Ban fahimceki ba ..."
    "Yanzu kam zan maka yarda zaka fahimta dakai da
jakin ubanka har da ma tunkiyar uwarka ...!!
   "Ke mara mutunci ....uban me kike nufi ? ..hajiya ta
matso a fusace ...
   Dad da yayi mutuwar tsaye yace ..".karki kuma zaginta
hajiya ...dan Allah Pretty ki zauna muyi magana ...wallahi
har yanzu ina mutuwar sonki .!!...ya fada cikin kyarma ....
   Shehu yace ..."Dad Sa'adah tawace kabar fadin haka
mana ...ka lallasheta kar tace bata sona dan Allah ...!!
   "Ashe kun san Allah ....? ..Yaushe kuka sanshi ..ku fada
man ...!! ...ta karashe maganar cikik tsawa ...
    " A gaida jakin malamin da ya tsaya fadarwa Shehu da
ubansa fadin suna  Allah a baki don basu sanshi a zuciya
ba ....!!
     " Sa'adah "....shehu ya fada tare da yin kneel down a
gabanta ..."Dan Allah karki man Haka wallahi ina
mutuwar kaunarki ...na tabbata idan ban sameki
mutawa zanyi ...!!
    "Aiko ya kamata uwarka ta tafi neman likafani tun
yanzu ....!!
  Lubna tace ..."haba Hudah karki yi haka ba ...karki zama
mara imani ...komae suka maki bai kamata kiyi haka ba
.....!!
  Cikin tsawa tace ..."Kinsan Wacece Yaya Sa'a ? ....
   Ba Shehu kadae ba Hatta Lubna sae da ta tsorata ....
     "Yaya Sa'a ...tana iya kwana biyu bata ci abinci ba
amma bata taba barin Hudarta da yunwa ko da seconds
2 ....takan kwana tana wahala duk saboda Farincikin
Hudah ....Wadannan munafukan Lubna su sukayi
sanadin barata da duniya ke har da ummana .... _*A
DALILIN YAYATA*_ Nayi komae lubna ba wae don kowa
ba sannan nayi soyayya daku !!...
     "Shehu na tabbata baka manta wacece Ya ya Sa'adatu
ba ...mumina saliha daka tarwatsa mata rayuwarta ....to
Hudah ce kanwarta ...!!
     "Wallahi nasan ban kyauta ba amma dan Allah ki
gafarceni ...ki tsaya muyi magana wallahi na tuba na
gyara duka halina  Hudah ...duk saboda ke ...dan Allah
karki barni ...na tabbata dad zai bar manke ...,!!!
   " Mtsee ....gobe kamar yanzu na zama matar barister
Mahmoud mutumin da kukayi forcing yazo gidanmu
ashe ma haske kuka kawo mana ...!!
  bata rufe baki ba ya fadi kasa yana tari ...dad da hajiyar
sukayi kanshi ...dad ke fadin ...
    "Karkiyi haka Hudah ...na bar masa ke wallahi na
hakura ...!!
  Harara ta watsa mashi ...
   Tana fadin... ..."Sweetheart ayi maza aje gwajin
kanjamau don na tabbata akwaeta a jikinka ...don ina
tunanin har da jakar matarka ma ta kwasa ...a lisaafina
Yau 6month kenan da cutar  ta shiga jikinka
na tabbata tayi kwarin da barata fita ba .....bye!!!  ..ta juya
ta tafi ..
  Juyowa tayi da sauri tana fadin ..
   "Oh na manta ...Shehu ya sayar da wannan gidan akan
Naira million 19..idan ya tashi ku tambayeshi ..wawan
bai sani ba nina sayi gidan  sannan ya maido man da
kudin a matsayin kyauta ...so nan da wata daya a tattara
komatsae a fita!! ......
   Ta fizgi hannun Lubna suka fita ....ita kam lubna binta
take da kallon kamar tv ...gani take kamar ba Hudah da
ta sani bace ..
     Da daddare Uncle Mahmoud ya kaisu ita da Lubna da
Farida kawarsu da tazo.. gidan liman ....
   Bayan su Lubna sun fita daga motar ne ya riketa
....yana shafa kunshin da aka mata na zallah bakin lalle ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                  🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS..._
     _GWS.....SWEERY ...ALLAH YASA ZAKKAR JIKINE
.....PLEASE IDAN AN TARA KANKANA CIKIN KAYAN
DUBIYA KI AKE MAN KIN JI KO .....😘😘_
 *_76 to 78_*
        Kallonsa tayi a shagwabe tana fadin ...Uncle suna
jirana please ...!!
   Glass din gurinshi ya rage tare da kwalawa su lubna
kira da suke gefe suna jiranta ...
   Suka matso Lubna na fadin "Uncle gani " ...
   Lumshe ido yayi yana murza hannjnta ..."Ku shiga ciki
Lubna zamu shigo yanzu ..."
  "Uncle "....ta fada kamar zatayi kuka ...
  Kallon da ya bita dashi ya sata yin shiru tare da maida
kanta kasa ....a hankali take mashi guguni tare da turo
baki tana hararanshi ta kasa ...
  Idonshi na lumshe duk yana jin abunda take fada
...bata tare da ta shirya ba ya rungumota kirjinsa tare da
hade bakinsu guri guda yana tsotsa ...
    kokarin kwace kanta take tana yarfe hannu ...kin
sakinta yayi ya cigaba da bata dpkiss ....sae ya ji ta fara
kuka ne sannan ya saketa a wahale ...
  "Maimaita abunda kikace !!...ya fada kasan makoshi..
   kwallan daya fito ne ta saka bayan hannu tana gogewa
tare da turo baki ta masa banza ....
   A hankali ya bude ido yana kallonta sannan ya saka
hannu da niyar rikota ...tayi saurin ja da baya tana fadin
....
  "Yi hakuri zan fada maka uncle" ...ta fada tare da goge
kwalla ...
  Maida kanshi yayi saman sitiyari yana jiranta ...jin taki
cewa komae yasashi dagowa  .yana kallonta .....tayi
saurin ja da baya ..
   "Cewa nayi kamar baka taba aure ba !!!....ta fada a
hankali ...
   "Umhuh ...ina jinki ..sae kika ce mae...kuma bayan
wannan?
 " Shikenan fa abunda nace ."...ta fada tare da janye
hannuta cikin nashi..
   Dan murmushi yayi tare da rungumota yana niyar
kissing dinta ...
  "Zan fada wallahi ......!!
  sakinta yayi tare da zuba mata ido .....
  A ha kali tace .."sae kuma nace..huh...kayi hakuri Dan
Allah Uncle" ...ta fada tare da kallonshi ..
   "May be dama kina bukatar na cigaba da kissing dinki
shi yasa baki so ki fadi abunda na tambayeki .!!..ya dago
fuskarta da hannunshi na dama ..
  Da sauri tace " aa wallahi uncle ..cewa nayi ka cika
jaraba ....!!..ta karashe maganar tare da sanya kanta cikin
cinyoyinta ...
   Murmushi yayi kasa kasa tare da bude motar ya fita ya
zagaya ya bude mata ...ba tare da ta kalleshi ba ta fito
tare da rugawa cikin gidan da gudu ...
   Binta yayi da kallo tare da lumshe ido ya jingima da
motar tsawon wani lokaci ....
   _Karfe 11:30_
  Dae dae lokacin aka daura auren Barister Mahmoud da
Hudallah Ibrahim ...wanda liman ya daura ...tare da
halattar dunbin mutane daga garuruwa da dama ....
  Duk yarda barister Mahmoud yaso ayi party ...liman
hanawa yayi ...yace ...
  "Indae kuna son aurenku yayi albarka Mahmoud to
dole ku kauracewa duk wata bidi'a ...ban hanaku idan
an kai maka matarka ba ...ku shirya walima cikin gidanku
domin mutane su tayaku da Addu'a ...!!
   Godiya sossae Mahmoud yayi sannan ya tashi suka tafi
....
 Bayan magrib ne ...motocin da zasu dauki amarya suka
iso ...kanwar maman Mahmoud ne ta amso amarya an
nadeta cikin Saree yellow colour tun daga kanta har
kafarta .....
   Rungumota tayi tare da sakata cikin Clinto yellow
colour ..sannan ta rufeta ta koma cikin wata motar.. aka
barta ita kadae ....
   Duk da baa gaban iyayenta take ba ...amma ranar
mutuwarsu ta dawo mata sabowa...ta tabbata da yaya
saa na raye babu abunda zai hanata zama gefenta a
yanzu ...tayi kwadayin taga farincikin da zata gani a idon
yayar tata ... ....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                        🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home pf expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_79 to 80_*
      Wani sabon kuka ya zo mata  ..yayin da ta sa hannu
tana kokarin rufe bakinta gudun kada drivern yaji ta ....
   Ji tayi an janyota tare da kwantar da ita ...kamshin da
tajine ya hanata firgita don har ga Allah bata dauka
akwae wani a cikin motar ba bayan driver ...
   A kan kirjinsa ya kwantar da ita tare da bubbuga
bayanta a hankali alamun lallashi ...ba tare da yace
komae ba ....
   Lafewa tayi tana kuka kasa kasa ....Hannunshi ya kai
tare da lalubar bakinta ya tura yatsunshi a ciki yana wasa
dasu a bakinta ....
   Kukan ya tsaya cak sae dae ajiyar zuciya da take saki
tare da kananan kwallah ......
  Jin zaa bude motar ne ya sata tashi daga jikinshi tana
gyara Saree dita ....
   Bude motar akayi tare da fito ta ...sannan Aunty hanne
ta matso ta kama hannunta ...Uncle Mahmoud dinne ya
zagayo tare da rike gudan hannun nata ....
   Pictures aka dinga dauka kala kala ....ga dandazon
mutanen da sukazo taran amarya ...Ba gidan barister
Mahmoud din bane aka kaita ...gidan iyayenshine
....zuwa gobe idan anyi walima su wuce gida ....
   Tare suka jera su duka ukun har tsakiyar babban falon
Gidan ...sannan aka zaunar da Hudah din a kasan tuntu
...Shima barister Mahmoud din zama yayi gefenta ...har
lokacin fuskarta na nannade da Saree ....
   Falon ya dauki haske ta ko 'ina ....yana zagaye da
dangin Abba da kuma na mamanshi sae su biyu a tsakiya
...
   Yayar Mamanshi ce _Aunty Husy_ ta taso tare da aje
yan kunne da sakar gold wanda ya kai naira million
15 ...kusa da Mahmoud ...na sayan fuskar amarya ...
   Gurin ya dauki tafi ganin Mahmoud din ya tura mata
sarkar yana girgiza kai ...alamun bai sayar da fuskar
Hudah haka ba ...
   Wata kanwar mamanshi _Aunty Zuby_ ta taso tare da
cire tata sarkar da yan kunne ta hada mashi ta tura ...still
tura masu yayi yana girgiza kai ...alamun bai yarda ba ...
  Gurin ya kara daukar tafi lokacin da mamanshi ta taso
ta cire tata sakar da yan kunne ta daura mashi a saman
tasu ...
  Sannan ya saka hannu ya dafa sarkokin tare da fara
bude Fuskar Hudah Ahankali ..har sae ya kusa budewa
sannan ya kalli kanwar mamanshi yana fadin "Gaskia
Aunty Zuby ku karo wani abu tukun ..."
  Aunty Husy ta mashi dakuwa tare da watsa mashi
harara ..
 Sannan ya bude fuskar duka yana murmushi .....
  Kanta na a kasa tana kallon carpet din gurin ....
  "Masha Allah ...tubarakallah ..Alhamdulillah amarya ta
hadu ta ko'ina ....fatan mu Allah ya bada Zaman
lafiya!! ....Babbar yayar mamanshi ta fada tare da daukar
su photo ....kamar an bude gidan photo haka flash light
ke tashi gurin ....
  Sae da aka gama photo sannan gurin ya sake yin shiru
...Mahmoud dinne ya saka hannunshi na dama tare da
dago fuskarta ...sannan ya goga hancinsa a lips dinsa
yana lumshe ido  ....duk uwayen mutanen dake zagaye
da falon..
  "Mahmoud baka da kunya  ni wallahi ban ma san haka
kake ba dae yau .."..kanwar Mamanshi ta fada tare da
jehoshi da pillow ....Hudah kuwa yarda kasan ta nutse
gurin haka take ji ..
..
  Murmushi yayi kasa kasa sannan kama hannun Hudah
..tare da rarrafawa kusa da kafar Mamanshi ...
  "Hudallah ki gaishe da Mama "...ya fada dae dae saitin
fuskarta ...
  Dukawa tayi kusa da kafar maman ba tare da ta iya
cewa komae ba ...bayanta maman ta dafa ..tana fadin ..
  "Allah ya maki Albarka Hudah ....!
  Kowa na falon sae da suka rarrafa ya na rike da
hannunta yana fada mata sunanshi tare da matsayinshi
....ita kuma tana dukar da kanta a hankali ...suna sa mata
albarka sannan suka dawo inda suke zaune ...duk
abunda ake idon hudah na kasa bata dago ta kalli kowa
ba .....
    Bayan sun zauna ne babbar yayar mamanshi  _Aunty
Husy_ ta kama hannunta tare da kaita part din hajiya ta
zaunar da ita saman gado ta fita ....
  kamar jira Mahmoud yake ta fita ya fado dakin tare da
saka key kamar munafuki  _nidae feedohm nace
munafuncinne man_...ya zauna kusa da ita ya janyo ta
jikinshi yana fadin ...
  "Hudah sun man bakinciki wae anan zaki kwana ....dan
kada ace nayi rashi kunya wallahi dana saceki mun koma
gida ko ? ...
   Banza ta mashi tare da sakin kuka ....kanta ya dago
yana lallashinta tayi shiru amma sam taki yin shiru ....sae
da ya fara kokarin cire mata Saree da aka lillibuta  dashi
sannan tayi shiru ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                   🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of Expert & Perfect Writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_81 to 82_*
       "Uncle ka fita dan Allah !!....ta fada tana kokarin
tsayar da kuka ...
  Cikin sauri yace .."Idan na fita zaki bar kukan Hudah ...?
  Daga mashi kai tayi tare da sadda kanta kasa ....dan kiss
ya mata a lips tare da jan hancinta sannan ya fita yana
waigenta .....duk da yayan mamarshi tace anan zata
kwana hakan bai hana Mahmoud ja mata Allah ya isa ba
...
  Allah ya soshi ba wanda ya ganshi lokacin sa yake
fitowa don suna can suns kokarin hada mata abincin da
zata ci wanda zai kara mata lafiya ...
  Su biyu suka shigo da abinci tare da zame malullubinta
...Aunty Husy ce ta bata abincin a baki ...tare da daura
fuska ...don farko cewa tayi bara taci ba ...sae da ta
daure mata fuska sannan ta amsa ...
  Bayan ta gama cin abunci yayar mamanshi ta hada
mata ruwan wanka masu uban kamshi tace ta shiga tayi
...tana fitowa ta bata less red tare da head baki tace ta
sanya ...da katuwar sakar gold ...sannan ta saka mata
takalma hills bakake ...ta rufa mata bakin mayafi a
kai  ..tare da kama hannunta ..suka shiga part din Abbah
...yana zaune sanye fa farin glass suna shigowa ya mike
dauke da fara'a yana fadin ...
    "Marhaban Hudallah" ....hannunta Abbah ya karba
daga hannun Aunty Husy ya zaunar da ita bisa tuntu ....
  Aunty Husy  ta miko mashi plate dauke da
saubatussamina .......kadan ya diba a hannunshi sannan
ya saka mata a baki...ta daukesu photo ....Fita tayi ta ta
barsu su biyu ....
   Wa'azi ya mata mai ratsa jiki wanda ta tattaba ko
mahaifinta na nan iya abunda zai mata kenan ...bata da
abun ce masu shi da liman sae dae fatan Allah ya saka
masu da alkhairi ..
 12:30 ..
  Masu decoration suka iso ....kujeru suka fara fitowa
suna jerawa a harabar gidan ...
.sannan suka fara decorating din da yadi blue da fari
....gurin yayi masifar kyau kamar baa cikin gida ba ....
 Tana zaune Aunty hanne suka shigo ita da Aunty Husy
suka bata Saree blue colour ....kaf jikinta sae da aka
nannade idanuwanta kawai ake iya hanguwa .....
   Fita da ita akayi falo ...acan taji muryar Uncle
Mahmoud yana mayarwa da abokan wasanshi magana
..."wae duk family dinsu babu mai kyaun amaryarshi
......!!
  Gabanta ya fadi lokacin da taji tattausan hannunshi
cikin nata ....babu kunya ya daga Sareen yana kallon
fuskarta tare da fadin ....
   " Gaskia na iya zabe ...Tubarakallah ...Aunty Husy da an
gama walimar zan tafi da matata.. ..ku dan rufe idonku
for some minutes ....!!.
  Aunty Husy ta kai masa duka ..".Gidanku Mahmoud
....ka rike hannunta ku fita bawae ka ma rashi kunya ..!!..
  Dariya yayi tare da kissing dinta a hannu sannan ya jata
suka fita harabar gidan ...
   Sun nuna mata kauna sossae ... _kamar yarda exclusive
suka kaunaci feedohm_ ....sabon lefe suka hada mata
wae kayan karbar amarya ....
   Agaban mutane ango ya ciyar da amaryarshi har ta
koshi ....sannan aka ce itama ta ciyar dashi ...kasawa tayi
..ta nuna alamun zata yi kuka ...
   Auntu Husy ce tace ta sayi hannun amarya naira
million daya cash ta zubesu a table din da suke zaune ...
   Duk da hakan kasa bashi tayi ...hannuta ya kamo ya kai
bakinshi saitin fuskarta ...
  "Ba kya sona Hudah? .....ya fada a hankali ...
  Dagowa tayi da sauri tana kallonshi kafin ta girgiza
mashi kai a hankali ...hannuta ya kama ya debo abincin
sannan ya saka a bakinshi yana lumshe ido ....gurin ya
dauki tafi da ihu ...abokan wasanshi kuwa cewa suke wae
amaryar bata sonshi tunda har ta kasa bashi abinci ...
  A hankali ya dago da fuskarta yana kallon ..."Prove it
Hudah ...ki nuna masu kina sona ...ko bakya sona .?..
   Ba tare da tace komae ba ta kai hannu ta debo
Muhassimba ta kai bakinta ta b'alli kadan sannan ta sa
mashi sauran a baki ....
   Ba karamin burge mutane sukayi ba ...Aunty hanne
kam na can cikin gida bata san wainar da ke toyawa ba
...Yayar Mamanshi ta bata yan shila tace ta gasa masu da
ruwa ruwa idan zasu tafita a tafi da ita..dan haka bata
gani ba.. bare ta kwashi takaici .....
 ••°°••
  Bayan Magrib ne akace a fito da amarya ....sae da
sukaje falon Abbah suka masa bankwna tare da Mama
sannan Uncle Mahmoud din ya jata har harabar gidan
inda aka ajiye motoci ....Daga ita sae Aunty Hanne da
Aunty Husy kadae suka shiga motar ...dan Aunty husy
cewa tayi bara su shiga mota dashi da Amarya ba tunda
baida kunya .....
  Sae da aka fara tafiya sannan ya masu gyaran murya
lokacin Aunty Husy tana karawa Hudah nasiha ..Hudah
kuwa kuka take a hankali ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                 🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_83 to 84_*
       "Aunty Husy dan Allah ki barta hakanan ...kinga zaki
ja ta bata kwalliyar tun kafin na gani ...kuma duk abunda
kike fada mata Allah yau zan fada mata ba tare da tayi
kuka ba " ....ya fada tare da kunna fitilar motar ...
   Sake da baki aunty Husy ke kallonshi "∆mma
Mahmoud baka da mutunci ...ashe dan Ubanka sae da ka
biyomu ....shine ka karbi driving din ko?....ya maka
kyau!! ....
   Dariya yayi kasa kasa tare da kallon Hudah da ta
kwantar da kanta sanan cinyar Aunty Husy  tayi lamo
kamar maijin bacci...
   Hanne ta saka hannu ta kashe filitan ...ba tare da tace
komae ba ...har suka isa gidansu ...sannan aka shigar da
Amarya Part dinta ...amma ba asalin wanda take ciki ba
da ...aa saman bene aka kaita ...dama kuma gurin rufe
yake ...
  Kamar yarda addini ya tsara bayan kowa ya watse ya
tarasu falonshi tare da masu nasiha mai ratsa jiki
...sannan yace kowa ta fadi bukatarta ...
  Aunty Hanne tace ...Idan da hali ya taimaka masu da
jari saboda ita tana so ta dinga fita kasashe tana dauko
kaya ... tasan ko ance ta koma karanta bara tayi abun
kirki ba ....
   Yacce .."kamar nawa suke bukata ?
  Hanne tace " ko nawa yake da hali ..."
  Hudah kam jinsu take  ..don bata da wani guri da ya
wuce tayi karatu domin cika gurin Yaya Sa'arta !!
   Leda da ya shigo dashi yace  Hanne ta je ta dauko
masu plate  ..
  Aa tace ...yafi kyau suje can su ci abunsu kamar yarda
akewa ko wace amarya ...sannan ta mike ta daga Hudah
tare da daukar basket din da ta shigo dasu suka nufi part
din Hudah ....bawae bata jin kishi bane sae don ganin ko
tayi kishin a banza tunda bata da abunda zata iya biya
mashi bukatarshi ..
  Part dinshi ya shiga ...yayi sallah tare da wanka sannan
ya shiga part din hanne ya mata bankwana tare da
hugging dinta yana mata godiya ...don ba karamin
burgeshi tayi ba a hidimar bikin ...bai tafi ba sae da ya
dan bata farinciki ta hanyar romancing dinta sannan ya
fita .... _Ajiyar zuciya ta sake ta bishi da kallon ..wannan
ne karo na farko da ya taba kai hannunshi a jikinta da
niyar faranta mata..kwallah da suka taro idonta suka
gangaro mata ...._
    Hudah kam inda hanne ta barta nan ya isketa ....ko da
ya shigo sae da ya kura mata ido ..duk da tana lullube da
maroon din saree hakan bai hanashi ganin kyauwun da
ta yi ba ....bakin gadon ya zauna tare da yaye mata fuska
yana lumshe ido ...
   " Tubarakallah ...Masha Allah ..Alhamdulillah ya Allah
.."!!!.ya fada tare da dago fuskarta yana kallonta ...kasa
tayi da idonta har sae dae ya kai bakinshi yana gogawa a
dukka fuskarta ....
  "Tashi kiyo Alwala" ...ya fada kasan makoshi ...har
lokacin bakinshi na saman fuskarta idonshi a lumshe ...
   Ganin bata da niyar tashi ya sashi daukarta cak ya dire
ta cikin toilet din tare da zuba mata ruwa har ta gama
alwala sannan ya janyo hannunta ya shinfida masu
darduma ....ya gyara mata zaman saree din a jikinta ta
yarda baka iya ganin komae a jikinta ...sannan ya jasu
sallah ...bayan sun ida ..ya dafa kanta Kamar Yarda Allah
ya umurce mu ...ya dinga kwararo mata aduu'a sanna ya
janyo basket din da hanne ta shigo dashi ...ya fito da
foodflask da waterdesndr ....tare da plate da spoon ...
   Yan shila ne da sukaji kayan yaji ya juye masu  .sannan
ya tsiya mata lemon da aka hada da
kankana,gwanda,dabino da kwakwa ya tsiya a cup ya
kafa mata a baki
.
   Wani bala'in kunyarshi take ji...duk da ba wannan bane
first time da ya bata abinci a baki ....kin karba tayi sae da
ya daure fuska sannan taci kadan tace ta koshi ....
  Ledar ya janyo ya juye mata kazar  dake ciki yana fadin
.."Zauna  kici kinji..bana so ki man irin na meenalle kice
ban kawo maki kaza ba My Hudah!! ....dan hararanshi
tayi sannan ta mike ...
  Shima mikewa yayi ...yana kwance saree dake nannade
jikinta ...rike kafadarta yayi yana juyata har ya gama fitar
da gyalen ya barta daga ita sae siket da wata yar rika
wanda iyakar jibi da karamin hannu ....Sae kwalliyar
stone dake jikin rigar ....
   Wani asirtaccen kamshi ke fitowa daga jikinta ...bai ga
bukatar saka wasu kayan bacci ba ...ya dauketa cak tare
da direta saman gado ...sannan ya koma ya kashe wutar
dakin ...
   Cikin dubara har ya rabata da kayan dake jikinshi
...anan ne ya kusa zaucewa har bai san sadda ya kunne
fitila ba yana kare mata kallon ...da sauri ta rugumeshi
ganin haske ya gauraye dakin tana niyar kuka ...
  Da kyar ya iya kai hannu ya kashe fitilan yana mayar da
numfashi ..cikin kunnenta yace ..
  "Allah ya ma lubna Albarka ...yanzu zan gane idan
abunda take ba dawa yayi amfani..don bana son wannan
rakin ya tafi a banza" ...ya karashe maganar cikin zolaya
....wani uban duka ta kai mashi a kirji tare da ko ma wa
can karshen gado ta kwanta ..
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                    🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_85 to 86_*
      Mirginawa yayi ya hadeta da bangon yana fadin
.."Sorry na daina kinji ko "...Sannan ya janyota jikinshi
yana gentling ko'ina na jikinta
  ••°°••
  Barister shehu kuwa bayan sun kaishi asibiti aka
tabbatar masu da barin jikinshi bara ya taba amfani ba
_paralysis_ ...domin faduwar da yayi ga lokacin jininshi
ya hau ....Hajiya da dad kuka suka sake ...yayin da take
tsinewa Hudah Albarka tare da ja mata alkaba'ai kala
kala ...
  lokacin ne maganganun hudah suka fara mata yawo
...cutar Kanjamau kawae take tunawa ...Dad din ta kallah
taga duk yayi yaushi ga kuraje  da suka fara cika mashi
jiki ....
  Ba tare da tayi shawara dashi ba ta je laboratory tace su
mata gwajin HIV ....jininta suka diba bayan mintuna suka
tambar mata positive ce tana dauke da cutar ....
  Kamar mahaukacya ta koma ...ta shakari wuyan Dad
tana dura mashi ashar ...da kyar ya kwaci kansa ...
  Doctor yace shima a mashi gwajin ...baa dauki lokaci ba
aka tabbatar mashi da shima positive ne ....
  Doctor din ya basu shawara da su rufawa kansu asiri su
zauna tare ba tare da wani ya sani ba ...sannan ya daura
su kan magani ..
  Bayan shehu ya farfado ..ya tabbatar masu da ya sayar
da gidan da suke zaune ...amma ba Hudah ya sayar
mawa ba ...wani makwabcin su Hudah ne amma ba
mamaki ita ta turoshi .. ....
  Dad din yace bai yarda ba wallahi zai shigar da ita kara
...amma sae barister Shehu yace ...babu wata kotu da
zata karbi gidan daga hannun Hudah tun da "ka sayar ya
rabaka da abunka" ..sannan takardun gidan ma na
gurinsu ....Ba karamar nadama barister shehu yayi ba a
ranar ....gashi a kwance rabin jiki a mace ...sannan har
lokacin akwai soyayyar Hudah a ranshi ....wanda ya
tabbata bara ta taba gushewa ba ....
••°°••
  A hankali ya kai fuskarshi tare da kissing lips dinta
...sannan ya sake murmushi ...bai taba tunanin rakin
huda ya kai haka ba ....Ihu ta dinga mashi kamar ita
kadaece macen aure a unguwar ....
   Blanket ya ja mata ya mike ya fada toilet yayo wanka
tare alwala ..
har sae da ya gama sallah  sannan Hudah ta bude
rinannun idonta tare da dallah mashi harara ...
  Murmushi ya sake mata tare da fadin ..."Ni kike
harara" ...
  Kafarta ta sauko zata mike tsaye ta koma da sauri...tana
fadin ..."Allah ya isa wallahi .Lubna..ban yafe ba ..kema
zaki samu wanda zai maki irin hakan ...Shegiya
kawae !!! ..ta saka bayan hannu tare da share kwallah ..
  Dariya sossae ta bashi ...bafa Lubnar ta tsareta ba tace
dole sae tayi amfani da abunda ta bata ...aa itane har da
boyewarta ma dan kar wani ya ganta ....amma kuma zata
zagi yar baiwar Allah tana can gida tana bacci abunta...
  Cikin zolaya yace .."Wae Hudah me lubna ta maki tun
jiya kike mata Allah ya isa ..? ..Gaskia ina neman mata
gafara kinji ...!!
  Harara ta balla masa tana fadin "...Ban sani ba ...ka
shafa kaji ..."..
  Tasowa yayi yana dariya ..
  "Abu mai sauki ..muje toilet idan na hada maki ruwan
wanka sae na shafa da kyau naji ....!!
   Daukarta yayi tana harbe harbe ya direta cikin ruwan
zafi yana mata dariya ....sae sa ya tabbatar ruwan zafin
sun ratsata sannan ya canza mata wasu ruwan zafin yace
"Kiyi wankan tsarkk kinji Hudah ...bara na gyara dakin
kafin ki gama ko!! "...ya barota cikin ruwan tana lumshe
ido..
  Kusan Minti Talatin yana jiran ta fito amma shiru ko
motsinta baya ji ....toilet din ya leka tare da sakin
murmushi ganinta kwance cikin ruwan zafi tana bacci
hankalinta kwance .....
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                   🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_87 to 88_*
       Girgiza kai yayi ..sannan ya dauko katon towel ya
nadeta ciki ya kwantar da ita saman gado tare da shafa
mata cream kadan ....
  Cikin kayanta ya dauko wata doguwar riga mara nauyi
ya saka mata...sannan ya shafa mata powder ...wasa
wasa kwalliya ya mata sosaae tana baccinta don lallabata
yake kamar kwae ....
   Fita yayi ya leka part din hanne   ga mamakin shi ya
tarad da ita kitchen tana hada masu break ....sai da ya
tayata suka hada komae sannan ya koma dakin Hudah
....
  Lokacin ta tashi amma tana kwance idonta na kallon
sama ....Tana jin shigowarshi ta maida idonta ta rufe  ..
    "Hudah ....baki tashi ba har yanzu ....!!ya fada tare da
shafa wuyanta  ...
  Da sauri ya janye hannunshi ...yana kallon fuskarta
...."Subhanallah ...Hudallah...ba dae baki lafiya ba ? ...ya
fada a rude  ...
   Dagota yayi tare da rungumeta yana mata sannu ......
  Sae da taji duk ya rude sannan ta bude ido tana
hararanshi ta kasan ido ...
  "Bakya lafiya ne Hudah .?..sorry fada man kinji ...!! ya
sake tambayarta a rude ..
  Banza ta mashi na tsawon lokaci sannan tace ..."Lafiya
na lau "
  "Amma jikinki zafi Hudah "...ya fada tare da dago
fuskarta ..
  Haka jikina yake fa Uncle ...!
   "Kin tabbata lafiyarki lau ? ...
  daga mashi kai tayi tare da mikewa a hankali ta bar
dakin ...ba tare da yace mata komae ba ya bita da kallo
har ta bar dakin ....
*_4 month_*
    "Uncle wallahi wannan rito ne ...kuma baran  yarda ba
.."..ta fada tare da rike guiwar kafarta  ..
   "Ga Auntynki nan ta mana shari'a ...ai ta  gani tsabar
rigima ne irin naki ...kuma kema kin san ni nayi winning
ba ke ba....."
  Kusa da hanne  ta koma tare da dafa
kafadarta  ..".Aunty hanne dan Allah ba sae da ya'yan
wasana suka shiga ba sannan ya saka nashi? ...
   Cikin dariya Hanne tace .."kinga Hudah ba ruwana da
rigimarki ...kufi kusa...idan kin gama kya sameni kitchen
....
   Gwalo ya mata tare da mayar da kudinshi aljihu ....
   "Wallahi Uncle sai ka bayar dasu ...tun da bani nace ka
sa kudin ba" ...
  Ta fado jikinshi tana kokarin karbar kudin ...fito dasu
yayi tare da yin sama da hannunshi yana mata dariya ....
  Kokowa sossae take sae ta karbi kudin ...hannuwanta
duka biyun ya hade tare da matseta a kirjinshi yana
mata cakul kula ...
   Zuciyar ta ji tana tashi ...ta fara kokarin fita daga
jikinshi saboda bata son kamshin turaren dake jikin
kayanshi ....bai lura da yarda take ba ...ya rike ta gam  ..
   Ganin ta fara kakarin amai ne, ya sashi dagota da sauri
...kafin yayi wani kokari ta wanke mashi jikinshi tsaf da
amai  ...
   Sam Aman bai dameshi ba ..."sorry" kawae yake fada
tare da rike fuskarta da duka hannuwanshi ...
  Sae da Aman ya lafa sannan ya dauketa ya shigar da ita
toilet din dakinshi ya wanke mata jikinta tare da mata
wanka sannan ya fito da ita ya zaunar da ita gefen gado
...ya koma yayi wanka ya canzo kaya ...
  "Sorry Hudah  ....." ya fada a hankali kamar zaiyi kuka
....
  daga mashi kai tayi a hankali ...sam bata kaunar
kamshin turarenshi amma barata iya gwada mashi ba
...rungumeta ya sakeyi sossae ...yana shafa fuskarta ...
   A hankali hawaye suka fara bi mata fuska ...lokacin da
yake kokarin kwantar da ita sossae a jikinshi lokacin
zuciyarta ke kara tashi ....cikin dubara ta zame jikinta
tana mashi murmushin yake ...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
*_89 to 90_*
    Da daddare ta kwashe duka turarukanshi ta boye ....da
ya tambayeta sae cewa tayi  "ta gyara dakin ne ta manta
inda ta ajesu" .....
  da yake ranar ba gurinta zai kwanta ba ...sae tayi
baccinta lafiya .....
  Ranar da ya dawo dakinta kuwa ...kwana tayi tana amai
gashi ta kasa fada mashi shine silar aman nata ...tun da
safe ya kaita asibiti ...
  Doctor ya tabbatar mashi da matarshi tana da ciki wata
2 ...farinciki sossae ya nuna ...shi kanshi doctor din sae
da ya sami kyauta ta musamman ...
   Kasa Hakuri yayi ya wuce da ita gidansu ...acan yake
gayawa Mamanshi wae Ya kusa zama Abbah ...dariya
maman tayi cike da kunya ta barshi ....Haka Hudah kasa
ko da motsi tayi saboda kunya .....
   Tun da suka shiga Mota taki ko da kulashi ..ya sani
sarae fushi take dashi .....Hannunta ya kamo ya rike tare
da kallon Fuskarta ...ganin sam hankalinshi ba ga hanya
yake ba ya sata kwace hannunta tana hararanshi ...
   " Uncle ka kalli gabanka mana "..ta fada tana
hararanshi ..
  "Taya zan kalli gabana bayan kina fushi dani Hudah
.?...to naji nayi laifi kinji ko ...kiyi hakuri, farincikin da
nake cikine bara ya boyi ba ba ...!!
  Turo baki tayi tana kallon taga ba tare da tace komae ba
...hannunta ya sake kamowa ya hade da sitiyarin motar
yana murzawa a hankali ...
  Dan satar kallonshi tayi taga yarda duk ya damu da
fushin nata ....kwantar da kanta tayi saman kafadarshi
tana shafa gefen fuskarshi ...
  "is ok Uncle ..Hudah barata taba fushi da Uncle dinta ba
....!! ...ta fada cikin kunnenshi
    "Are you sure !...ya fada a hankali tare da parking
motar kasan wani icce ...
   Daga mashi kai tayi tare da sake mashi murmushi
...."Me zamuyi nan Uncle?
    "Na gaji ne nake so na kwanta bisa k'ashin matata na
huta for some minutes ...!!
  Turo baki tayi .."Lallae Uncle ni ce k'ashin ? ...wallahi
zaka maimaita ...!! Ta fada tare da girgiza kai..
    " Oho dae ...Lokaci da zaki bukaci na maimata ke kanki
rokona kike na barki .."..ya fada tare da kwantar da
kanshi saman cinyarta ...
  Wani uban ihu ta sake jin kamshin turaren nashi ya cika
mata hanci ..ga har zuciyarta ta fara tashi ....yayi saurin
tashi zaune yana tallabo fuskarta ...
  "Menene Hudah "..,.Ya fada a rude ...
  "Uncle Kaza ...Ji Uncle dan Allah ka sayar man zanyi
kiwo ko guda Daya ce please",..ta fada don bata so ya
fahimci wani abu ... _a tunaninta duk yarda na miji ya kai
ga sonka bara ya ji dadi ba kace baka son wani abu daya
dangance shi_
   "Ohoo Hudah Wae meke damunki ..?..duk wannan
ihun na kaza ne ...?..Allah ya shiryeki !! ....ya fada tare da
bude motar ya fita ...
   Gurin da yaga kejin kaji ya nufa ...ya iske saura kaza
daya da zakara ...kudin ya biya aka saka mashi su cikin
kwali sannan ya sayar masu buhun abincisu daya ....
   Harde Hannayenta tayi tana watsa washi wani
wahalallen kallo ..."He's such a cring person ....!! ..ta fada
a hankali tare da bude mashi motar ya shiga ...suka saki
murmushi lokaci guda ...
  Duk lokacin da Uncle dinta zai kwana dakinta sae ta
sami kerosine ta shafa a wani hanky ta riga sinsinawa ba
tare da ya lura ba ...hakan da take yi ya mata rage yawan
aman da take ...
 ••°°••
  Kamar yarda ta fadawa su barister Shehu ...wanda ya
sayi gidan a hannunsu yaje yace su fitar mashi daga
gida..daga farko dad din yace bai yarda ba  ...sae da
mutumin ya nuna mashi takardun gidan tare da shaida
...sannan ya kalli Shehun cikin bacin rai zaiyi magana...
*FEEDOHM💞*
💧💧 *_A DALILIN YAYATA🍁🍁_*
                    🍁
*_HASKE WRITER'S ASSO💡_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*Na Feedohm💞*
*_DEDICATED TO_*
_EXCLUSIVE WRITERS.._
    *_BONJEN muyitda bueda...Aunty sis , Jeedah
Aliyu,Ummi A'isha, Asy khaleel , Pherty ,Khaleesa ,Afra
,Hajja ce , Queen Mermue ,Nafee Anker, Asmy B, Billy B
,Billy G, Candy, Classic, Aisha Muhammad ,Maman
khadija ,😘😘😘_*
      *END...*
  Sae yayi shiru ganin ba amfanin maganar domin shehu
kamar gawa yake sae tarda akayi dashi ....haka suka
tattara kayansu suka bar gidan ...Allah ma ya soshi guest
house dinshi yana nan ....suka koma can ...
   Cikin Yan watanni kudin magani suka fara cinye duk
wani abu da ya mallaka...ga shehu akwance paralysis ya
gama dashi kullun abun karuwa yake ..sannan shi da
Hajiyar kullun suna neman magani amma abun ba saa
  ••°°••
  Hudah kuwa Uncle Mahmoud soyayya yake nuna mata
kamar ba gobe ..sannan shi da kanshi yace ta bari ta
haihu sae ya maidata makaranta ...
     Suna zaune cikin garden  lokacin ta daina jin warin
turaren da yake sawa  ....lafe take a kirjinshi yana karanta
mata wani novel .. _Tears drop at the sunset_ Zakaran da
ya sayar mata ya biyo kazarta tibi tibi ...suka zo suka
wuce ta shinfidarsu da gudu ...
  Kallonta yayi yana fadin ..."Umhum ...dama barewa
zarayi gudu ne danta yayi rarrafe ..."
  Sam bata fahimci inda zancenasa ya dosa ba ...ta dago
tana kallon kajin tare da fadin .."Uncle sun yi girma ko?
   "Dole suyi girma man ...tun da mamansu ma ta kara
girma ...sae dae ya kazar ya mamanta ...!!
   "   Uncle ban gane ba ?...ta fada tare turo da baki ...don
ta fara gane magana ya fada mata ...
  Huh ...yarda kazar ke gudun zakara haka mamanta ma
ke guduna...kin fahimta sossae ko ?
  Dan duka ta kai nashi a kirji tare da fadin ... "Kai uncle !!
  "  Ba haka bane ? ...ya fada tare da kafeta da ido ...
  Kara shigar da kanta tayi a kirjinsa ... "to yi Hakuri ai
kaga bana lafiya ne ?
  Ko ? ....Ya tambaya tare da saka hannu a yana shafa
jikinta ...
   Bata ce komae ba sae turashi da tayi ya kwanta ta
daura kanta saman cikinshi tare da lumshe ido ...
  ••°°••
   Tun safe ta sakashi gaba tana masa kuka ...tambayar
duniya ba wadda bai mata ba amma taki bashi amsa ...
  wajen sha biyu ya fito daga wanka ya iske  still inda ya
barta tana sharan hawaye ...
  Hannu ya mika yana fadin ..".Haba Hudalliyar Yaya Sa'a
zo nan ki fada man me kike so kinji ko .!!...ya mikar da ita
tare da zagaye kugunta da hannunsa  ...
  Turo baki tayi tana fadin ...
"Uncle ina indomie din da ka dafa man ranar da ka
daukoni daga gidanmu ? ..
  Ido ya waro ..."duk da dai ya manta amma Bai isa yace
bai tuna ba ...sae cewa yayi " Na ma isa na manta ta
Hudah  ..ya akai ?
   " Ita nake so ka sake dafa man yanzu   " ...ta fada tare
da kwantar da kanta a kirjinsa ...
    "   Hudah!! ....ya fada da sauri .."Over 6 years fa
kenan ?
    " Bara ka tuna yarda ka hada ta ba ? ..ta tambaya a
hankali ..
   "  Haba Hudah ..taya zan manta ...bani 30mints yanzu
na kawo maki kinji ko ....? ..ya fada tare da shafa kanta
   Peck ta mashi a kumatu cikin jin dadi....har ga Allah
bawai don ta bashi wahala ba ...aa ta tashine kawae tana
son cin irin indomie din ...duk da itama ta manta koda
kalar taste din bare shi da ya dafa  ...
  Kitchen ya shiga kasancewar Hanne bata ban ...tana
gurin kasuwancinta ...rasa abunda zaiyi yayi ...Hudah ta
riga ta shagwabashi in banda yankan albasa da zuba
maggi a abinci babu abunda ya iya ..hana rantsuwar tana
bashi ya mata taste yaji idan abincin yayi dadi da kuma
zubawa a coler ....
  Lumshe ido yayi a hankali ya bude fridge dauke da
addu'a ...ya fito da fura da youghurt da inibi da kwakwa
ya zuba a blender ya dama mata ...sannan ya saka
kankara kadan ...
  Sae da yayi addu'a sannan ya shiga dakin ...cikin fara'a
ta mika mashi hannu ..tana ganin fura ta bata fuska
zatayi kuka ...
  Dukawa yayi gabanta tare da dafa guiwarta .."
  "sorry Hudah ...wallahi da zan iya tuno yarda na dafa
maki ita babu abunda zai hanani kare rayuwata a
matsayin kukunki ...Kin sani duk wani abunda zai sakaki
farinciki nima shi nake so Hudah ...Kiyi Hakuri kinji ko
..ki sha furar kafin naje kitchen din na dafa har Allah
yasa zanyi wadda zata maki dadi kinji ko ...!!
  Hannunta ta kai ta karbi furan tare da rike hannunshi
da cup din guri guda ...sannan ta saka gudan hannun
tana shafa sumar kanshi ..tare da kissing din goshinshi ...
  "Nagode Uncle .!!....ta fada cikin kunnen  shi tare da
hura mashi iska a hankali ..
   "  Zan sha wannan din ka ji uncle dina ...wallahi
indomie din ma ta fita raina karka damu ...kayi hakuri
idan na bata maka rai ...!!.
  °°••°°.
  Cikinta na cika wata tara ta haihu santaleliyar diyarta
mai kama da Babanta ....Murna gurin family din ba'a
magana  ...kudi  kuwa kamar suke nomansu  ...
  Ranar suna diya taci Sunan Sa'adatu ...ana kiranta da
MUNIFFAH ( _Sabon farinciki.._ ) ...ita kanta Hudah bata
san sunan Mahmoud zaya saka ba ...sae daga baya take ji
gurin wanda suka shigo ....
   Tana zaune tana bawa babyn mama ya shigo cikin
mayan kaya yayi mata masifar kyau ....dagowa tayi ta
zuba mashi ido har ya iso kusa da ita ...tare da dukawa
ya sumbacin babyn sannan ya kai lips dinshi saman na
Hudah yana kallon cikin idonta
   Lumshe ido yayi yana fadinn .."Wannan kallon
fa? ...baki san kin haihu ba ?   ko so kike ki ja man aiki !!!
  Dan murmushi tayi mai sauti kafin ta zame daga kan
gadon ta koma kasa tare da rike kafafuwanshi ...
  "Uncle ...ban da wani bakin da zan iya gode maka ..Illa
iyaka na barwa Allah ya saka maka da mafificin Alkhairi
....Tabbas kai haskene daga lokacin da Allah ya hada ni da
kai na tabbata na cika mai sa'a ga dukkanin rayuwata
....Uncle duk yarda kake tunani ka wuce anan arayuwata
...ka zama wani jigo babba gareni ...ka katangeman duk
wani bataccen lamari a rayuwata ...Tabbas ban da
kamarka Uncle ..sae dae ina tabbata maka da ana
bautawa wani babu abunda zai hana Hudah dawwama
tana bauta maka ...Sae dai Alhamdulillah Allah kadae
muke bautamawa kuma shine zai saka maka da abunda
kaman ...Na maka alkawarin Uncle zan dauwama ina
faranta maka har na koma ga mahaliccina ......
  Dagota yayi a hankali ya rungumesu tare da babyn a
kirjinshi .......
  _Rabbana aamannaa bimaa 'anzalta wat-
taba'nar'rasuula faktubnaa ma'ash shaahidiin....🙏🏻_
 _Bhoti munkje abta neyza pyaza wutebin photah nahi
myezida boti..._
  _Nagode sossae da kaunarku ...08066598868..
*Fiddausi Musa aka Feedohm💞..* Sai mun hadu a littafi
na gaba...👄👄👄👄_
*FEEDOHM💞*
A DALILIN YAYATA
Na Nabila Rabi'u Zango
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "ADALILIN YAYATA Complet Hausa Novels"

Post a comment