Main menu

Pages

ARANAR SALLAH complet hausa novels littafin soyayya

 ARANAR SALLAH
Marubuci:- Shuraih Usman
2017
Publish:-shuraih 99%
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 1
.
$
Tsaye nake a kofar bayin gidanmu, na daura tawul a
jikina , yadda wannan tawul din ya samu nasarar rufe
mani daga cibiyata izuwa guiwowin kafafuna .
A gefena kuwa bokiti ce cike da ruwa , hannun
damata na rike da kwandon soso, a yayin da dayan
hannun wato hannun haguna na dunkulata sannan
sa’I sa’I nakan naushi gini bayin da dunkulallen
hannuna cikin bacin rai.
.
Ba komai yake sa nake naushin ginin ba illa batamin
rai da yayana yayi.
.
Shi yayana mai suna Abdul, ya kasance A duk lokacin
daya shiga bayi yin wanka ,ko fitsari ko kuwa bayan
gida
Toh fa akalla yana shafe rabin awa bai fito ba
Sai ka rasa me yake yi acikin bayin.
.
Kamar kullum ma .yau gashu yana neman ya zaftare
awa daya (1h).
Kamar daga sama sai naji karar budewan kofa ainan
take cikin zumudi na mike na dauki bokitin ruwana
ina jiran ya fiti in sa kai.
Can sai ya leko da kansa yace dani
“Yauwa shuraih ,dama sabulun wankana ne ya kare
dan Allah dan taimakeni da taka “
.
Wani kullun kululun bacin raine ya takale min a
magogoro na yamautsa fuska tamkar zanyi kuka nace
“Yaya Abdul dama baka idar da wankan ba”
“Eh wallahi ina kanyi ke nan sai sabulun ya kare dama
guntune sabulun” yabani amsa
Mika mai sabulun nayi batare da gardama ba
A kalla dai sai daya shafe kusan Awa daya da rabi
sannan ya fito.
.
A gurguje nayi wankana na fito , ina fita ban zame
ko’ina ba sai dakina
Ina kan shafa maine wayata kirar blackberry ta dau
ringing ina dauka sai naji muryar mujahid(mijin biza)
Anan yake sanar dani nayi sauri gashinan tahowa
,agurguje na kammala shafa mai, sannan na dauko
wata rigata zariya fara sol, daidai guiwa na buga, na
sanya wandonta sannan na dauko babbar riga wacce
ta kasance na dinkin ne itama,
.
Ko karyawa ban tsaya yi ba a sakamakon saurin dana
ke da kuma farin cikin daya Addabi zuciyata ,
.
A ranar yau Babbar ranace ga duk wani musulmi
dake doron kasa baki daya , don babbar ranace
wacce A shekara sau daya tak take fita wato
A RANAR SALLAH
Eid el kabir/ma’ana babban Salla,
.
Toh ya zata kasance a wannan rana shin wata iriyar
ce zata afku .MAI KARATU KA BIYO Shuraih 99% a
labarin
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 2
.
,
Na fito bakin titi na tsaya a yayin da mutane ke ta rafka sauri don su isa masallacin eidi.
.
Wasu kuwa a babura suke wucewa yayin da wasu a motoci suke wucewa.
.
I na tsaye a bakin titin ne , A lokacin dana fara gajiya da tsayuwar.
Ji nai an kwala min kira “shuraih”
Duk da muryar a shake take amma na gane wanda ya kirani ,
.
Ina juyowa kuwa mukayi kicibus dashi, bawani bane illa mujahid , yana sanye da farar shadda dinkin babban gare
.
Yana karisowa wajena na mika mai hannu mu kai musabiha, can sai nace masa
“Sai yanzu kaga daman zuwa”
“No na tsaya goge ma hajiyata kayantane” yafada
Na dubeshi da kyau ina nazarin maganarsa don na riga na sanshi da Bula (karya)
.
“Toh mutafi koh” nace da shi
Ya dubeni cikin rashin fahimta yace
“Ina zamuje”
“Masallaci man, ko bazaka je bane”
“Me zai hanani tafiya ” yafada a lokacin daya ke kokarin tare dan acaba
.
Akalla ya tare yan acaba kusan biyar kenan amma duk cikinsu babu wanda suka daidaita,
A sakamakon shi mujahid shi mujahid bazai iya cire Naira dari #100 ya biya kudin acaba ba.
.
Daga wajen da muke zuwa masallacin iedi tafiya ce ta kusan kilomita daya
Sukuwa yan acaba muddin tafiya ta kusan kai mil daya toh fa kudin da zaka biyasu bazaiyi kasa da #150 ba
.
Dan acaban farko daya tare wani dan sililine baki, yana sanye da jaket da kuma hula hana salla,
Dan acaba:- yauwa mallam tafiya ne
Mujahid:- (ya dan gyara tsayuwa) eh masallaci zaka kaimu
Dan acaba:- Na wa zaku bada
Mujahid:- Naira talatin 30
Dan acaba:- (ya burga wutan mashin ) mallam dan Allah kar ku bata mani lokaci. Ina da aikinyi, in zaka biya naira dari 100 toh in kuma bazaka biya ba inyi tafiyata
Mujahid:- maganar gaskiya mallam naira hamsin 50 garemu in zaka taimaka ka agaza ka kaimu a haka toh
Dan acaba:- (ya murda totur) yi hakuri yan samari ba taimako na fito yi ba, wai ace duk wannan wankan da kuka dauka kuce bakwada sisi inba hamsin ba ,mtssssssss( yayi tafiyarsa)
.
Mun tare yan acaba hudu kenan mujahid nace dasu naira hamsin gareshi, wani ma har kusan kaDan ya rage ya zabga mai mari, a yayin da wani kuma kadan ya rage ya damuko wuyan rigarsa.
.
Ni kuwa ina gefe ina kallon wannan diramar
Nasan mai karatu zaiyi tunanin mai yasa ni banje munyi ciniki da yan acaban ba
Toh hakan ya samo nasaba ne da rashin danshi danshi a aljihuna,
.
Maganar gaskiya ban tashi da sisi ba balle kobo
Toh tayaya mutumin da baya da sisi zaije suyi ciniki da dan acaba alhalin bani zan biya ba .
.
Amma maganar gaskiya nasan ba hamsin ce kadai ajikin mujahid ba , a zahirin gaskiya duk nisan tafiya mujahid ya fison yayita a kafa , maimakon ya cire kudi ya biya acaba yakaishi,
.
Kuma koda ma zai hau acaba toh kudin da zai biya baya wuce Naira 40
.
TO SHIN MAI KARATU
Da wani suna kenan zaka kira mujahid
Ni ma KUMA Shuraih DA wani Suna zaka kirani
.
Part 3
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 3
.
,
Muna tsaye a bakin titin ne duk na kosa na gammu a masallacin eidi don ji nake tamkar da na rufe idanuwana na bude na zan ganni a masallaci ne
Na duba agogon dake hannuna naga ya nuna karfe tara da mintuna arbain da uku 9:43am
.
Sannan kuma shi wannan masallaci karfe goma daidai suke fara sallan eidi.
Nan da nan wata dabara ta fado mani na dubi mujahid nace mai
” Duk dan acaban daka sake tarewa kar ku tsaya ciniki, mu hau kawai kaga da mun isa masallaci sai mu mikamasa Naira hamsin din sannan mu bashi hakuri muce mai cikon hamsin dince ta fadi a hanya”
“Lallai ka kawo shawara mai kyau abokina shi yasa kake burgeni” yafada alokacin da ya ke bubbuga kafafuwansa a kasa.
.
Cikin sa’a kuwa sai ga wani dan acaba nan ya sulalo, in ka gansa zai tuna ma da irin kartin bosawan film din INDIA nan
,
Garjejen katone wanda na tabbata zai iya yin gammo ya daga babur din daya ke kai ya azata bisa kansa,
.
Sanye yake da farar jaket , bakine irin baki mai daukar idanu(shining) a saman kansa babu ko silin gashi a sakamakon wata kwalkwal daya sha(skin cut)
Kana kallon wannan kaga jan wuya , nan take na tsaida shi,
Koda na tsaidashi sai mujahid yazo dab dani yace
“Kai shuraih wannan katon basamuden katare, gaskiya ina jin tsoro, domin idan wannan ya fara hajijiya da ni toh Allah kadai yasan abinda zai biyo baya izan ya sakeni”
Duk da wannan zancen da mujahid yayi yaban dariya amma sai na matse nace mai
“Kar ka damu ai dabara zamuyi masa daga baya kuma saimu lallabashi mu bashi hakuri kaga shikenan ” gyada kawai yayi alamar ya fahimta
Dan acaban na tsayawa nace mai “malam masallaci zaka kaimu”
Batare dana tsaya na saurari amsar da zai bani ba ,kawai sai na haye bayan m
ashin din,
Koda mujahid yaga na hawa shima sai ya haye.
.
Dan acaban dayaga mun zazzauna abayan mashin din sai ya tasheta ,murda totur yayi sannan yafara tafiya,
Acikin zuciyata kuwa sai tunanin irin badakalar da zata faru nake , don nasan wannan dan acaban bazai amshi naira hamsin ba , sannan kuma bazai tolerating wani cuku-cuku ba,
Nidai nasan duk rintsi duk wuya dan acabannan bazai amshi naira hamsin ba, hakanan duk rintsi duk wuya mujahid bazai iya biyan kudin acaba sama da naira hamsin ba don shi aganinsa ma a hakan ba karamin kwaransa dan acaban yayi ba
.

Ina cikin zancen zuci kenan sai mujahid ya ce dani lokacin daya miko mani wata yamitsatstsiyar naira hamsin
“Rike mani kudinnan bazan gyara zama”
Na karbi kudin a lokacin mun iso gangaran tudu
Kadab ya rage mu isa masallacin, dan acaba kuwa ko juyowa ba yayi bare ma yasan abin da ke faruwa.
.
Acikin raina na riga dana aiyana da naga mujahid da dan acaba sun fara hayaniya zan sabe na sulale nayi tafiyata .
Kaga na barshi da rikici kenan , don nasan muddin nayi gangancin tsayawa to kuwa wannan rana ta salla ba zata kasance RANAR SALLAH A gareni ba sai dai RANAR JINYA,
.
Burkin da dan acaban ya takane ya katse mani zancen zucin da nake na dan saurara wai ina jiran mujahid ya sauka , sannan nima na sauka , amma sai naji shiru har kusan second 20 ashirin
Hakan tasa na juya don nace mai ya sauka mana,
.
Kadan ya rage na saki fitsari asakamakon abun da idanuwata suka gane mani, Abin mamaki sannan kuma abin Al’ajabi
BABU MUJaHID BABU DALILINSA
In kadubi bayana yadda nabar wadataccen space sai ka rantse da Allah babu wanda ya taba zama a wajen.
.
Koda na sauko daga kan mashin din fuskata a tsorace ina tunanin ta yaya wannan basamuden dan acaban zai karbi naira hamsin,
Ni danake tunanin zanbar mujahid acikin cukuma ashe dai nine zan tatsiye a cikin cukuma
“Ya kai mallam sallameni mana. Nayi tafiyata “
Murgujejen muryansa mai kama da kukan jaki ya katse mani tunanina,
Na dubeshi da kyau ba karamin kato bane sannan A buguwa bazan iya dukansa ba , hakanan ko guduwa nace zanyi toh wannan sai ya karemani gudu ya kamoni daganan kuma basai na fada maku abin da zai biyo baya ba
.
.
TOH YA FRIENDS
INA MAFITA
.
www.Shuraih99.nextwapblog.com
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 5
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
Ba kowa nayi arba da shi ba illa mujahid .
Yana ganina ya fashe da dariya har yana buga kafa.
.
Sai da yayi mai isarsa sannan yayi shiru don kansa,
Tabe baki nayi sannan na jinjina kai nace mai
“Lallai ma mujahid wato ni za kaiwa haka”
.
“Yakake son nayi shuraih , ai tun farko na fada maka wannan mutum daka tare ba irinsa ake wa haka ba
.
“Yanzu dai mubar wannan zancen , ya’akayi har ka zame ka sauko daga mashin din ban sani ba” na tambayeshi
.
Yasake fashewa da dariya akaro na biyu,sannan ya dubeni cikin yanayi na shegantaka yace
“Adaidai wajen go slow(bumbs) na yan rake na sauka”
“Shine ko ka ankarar da ni”
.
“Ai dana ankarar da kai toh daka bata mani shiri, da yanzu muna hannun wancan basamuden dan acaban”
.
“Bamagujene, wallahi daya kamaka daka fada wa aya zakinta”
.
Cikin razana ya dubeni “wai kana nufin dan acaban can bamagujene”
“Kwarai kuwa don Da bakinsa ya fadi mani”
.
“Allah yasa dai bai rike fuskokinmu ba “
Yafada cikin kaduwa,
.
Wata harara na dalla masa sannan na dan hambareshi nace “kace dai Allah yasa bai rike fuskana ba, domin kuwa izan muka sake haduwa na tabbata wannan bamagujen ba imani ne gareshi ba, Allah kadai yasan abin da zai aikata agareni
.
“Wai ma ya kuka karike da shine” mujahid ya fada yayin daya dafa wata bishiya
.
Nan take na zayyane masa duk yadda mu kayi da shi, aikoda ya gama jin zancen sai ya tube babbar garensa sannan ya gyara tsayuwa ,
Dubana yai a tsanake sannan yace “lallai ko ba muga ta zama ba a waje daya”
.
“Maganarka dutse , don na tabbata izan yaji shiru -shiru dole ya shiga cikin lungunnan
Kaga kenan zai bulla adaidai bakin kofar masallacinnan kenan daya shigo kuwa toh anan zai cimmana “
Ina rufe baki kenan al’amarin ya afku, al’amarin daya tarwatsa dukkan wani bakin cikin dake tattare da ni
Sannan ya kore dukkan wani zullumi da tsoro daga zuciyata,
.
Wata kyakkyawar furece na hango farace ,amma ba fara tas ba, mai matsakaicin tsayi da matsakaicin jiki, ta mallaki kewayayyiyar fuska mai dauke da dara-daran haskakkun idanu,gami da yalwataccen gashi gira a samansu,
Dogon hancinta dake makale a saman madaidaicin bakinta ,shi ya taka muhimmiyar rawa wajen bayyana cikar kyawun surarta,
Tana da duk wasu halitta da ake bukata domin cikar halittar mace hakan yasa zuciyata ta rada mata suna kyakkyawar fure.
.
Dana kai dubana ga gefen da mujahid yake tsaye sai na tsinci kaina ina maijin wata wutar tarzomar haushin mujahid na ruruwa a kasan zuciyata,
Sakamakon yadda ya bude baki sai kallonta yake ayayin da ita kuma kyakkyar furen ta nufo wajen da muke tsaye.
.
Har ta kariso wajen idandunanmu akanta suke
Sallama ta rangada da zazzakar muryarta mai kam da sautin sarewa
.
A tare muka amsa sallamar
.
Toh a sannan ne nayi Gaba-gaba wato na kara kusanci da ita
Dubanta nai sannan nai karawa na gyara murya nace da ita
“Yake wannan kyakkyawar furen ma’abociyar haske mai kore dukkan wani duhu, shin wani abune ya faru “
.
Murmushi kawai tayi wanda ya kara fidda tsagwaron kyawunta tace dani
“Sunana ba kyakkyawar fure bace,sannan kuma ni ba wajenka Na zo ba wajen dan Uwanka na Nazo”ai tana gama fadin hakan tayi wuce warta izuwa wajenda mujahid yake tsaye
.
KAI KO MUJAHID
WAI FREINDS KU BANI SHAWARA
MAI YAKAMATA NA MAI NE DON
HUCE FUSHINA
Ammafa karku manta abokina ne banda shawarar da zata cutar da shi
Lolz
$
Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 6
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
Shi kuma mujahid koda yaji tace wajensa tazo sai ya gyara tsayuwa .tana isowa ta dubeshi fuskarta ba yabo ba fallasa tace
“Don Allah malam karfe nawa ne agogonka ya nuna.”
“Goma saura minti shida”mujahid ya fada cikin wata irin salon karya murya .
Sai ayanzu ne na gane dalilin daya sanya wannan kyakkyawar furen tace ba wajena ta zo ba.
.A sabida bana da agogo
Yamutsa fuska tayi sannan tace “kenan saura mintuna shida a fara sallah”
.
“Kwairai kuwa gimbiya “mujahid ya fadi dauke da wta guntun murmushi akan fuskarsa,
“Suna na ba gimbiya bace sannan ni ba jinin sarauta bace” tafadi tana kallon cikin kwayan idanuwan mujahid yadda tayi maganar sai ka zanta cikin hassala ne.
“Duk da kin kasance ke ba jinin sarauta bace amma sunan yayi matukar dacewa Dake”
Na fadi yayin dana ke takowa izuwa wajen da suke .
Gani nayi muddin naja baki nayi shiru toh tabbas mujahid zai iya tsara kyakkyawan yarinyarnan. Hakan yasa nace INA.
.
Gaba dayansu suka juyo da dubansu izuwa kaina daga nan ne kyakkyawar yarinyar tayi murmushi sannan tace “toh naji sauri nake , nabarku lafiya “
.
“Amma yakamata gimbiyar ta sanar da mu sunanta ko don gaba “
Nafada alokacin danaga ta fara ja da baya zata tafi
Koda taji kalamina sai ta tsaya cak awajen da take
“Suna na kursiyya ” ta fadi
btare data juyo ta dubemu ba ,kafin na budi baki nace da ita wani abu tuni har tayi nisa
Tafiyarta keda wuya nazo wajen Aminina mujahid nace mai “kagani mujahid kaima kasan bama haka “
“Kamar yaya bama haka “yafada cikin nuna alamun rashin fahimtar maganata
“Ina nufin wannan yarinya kursiyya ni nafara ganinta kuma naga alamun kana so kayi mani halin ojibebe”
Nafada cikin marainiyar murya wai don yadan ji tausayina , dariya yayi yace” maganar kai ka fara ganinta duk bai taso b , kokari zakai ka samu soyayyata kafin…”
“Kana nufin ka janye ka bar mani”
Na katseshi da fadin haka
“Amma baka cikin hayyacinka bane ko, wannan santaleliyar yarinya, kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa kake cewa na barma ka tabdi jan
.
Toh in bakasan wani abu ba bazan fadama, ni da kursiyya mutu ka raba takalmin kaza,” ya fadi cikin daddaga murya amma ba yadda kowa zaiji ba
.
“Da kyau ,hakama wato kace toh shikenan ,zamuyi wata gasa da kai”
Na fada cikin nuna alamun karfin guiwa
ya dubeni fuskarsa ba yabo ba fallatsa
.
Yace”wata gasa kenan”
.
“Gasar itace: Ni da kai duk wanda kursiyya ta furta mai tana sonsa , bawai shi ya furta mata cewa yana sonta ba, toh shine ya mallaki kursiyya”
Nafadi ina murmushi
.
“Ban gane zancen kannan ba”
“Ina nufin duk wanda kursiyya ta furta mai tana sonsa , bawai shi ya furta mata ba toh shine yayi nasarar mallakar kursiyya a matsayin budurwarsa, izan har ya kasance kursiyya ta furta cewa ni take so toh dolenka ka hakura da ita, izan kuma ya kasance kai ta furtawa kalmar so ma’ana tace tana sonka , toh anan take zan janye na hakura”
.
Koda mujahid ya gama sauraran bayanina sai yayi murmushin mugunta sannan yace”na amince da wannan gasar.
“Amma fa….”
“Amma me” ya katseni
“Da kwai sharadi guda a cikin wannan gasar”
Na fada da kakkausar murya
“Menene sharadin” yafada cikin zullumi
.
“Sharadin itace lallai wannan gasar ba zata wuce yau ba , ina nufin baza ta wuce wannan ranar ba”
“Kamar yaya bazata wuce yau ba” ya tabya
“Lallai dole kursiyya ta furta tana son wani acikin mu kafin safiyar gobe” na bashi amsa
.
“Toh amma idan kuma har gobe yayi ,bata zabi daya daga cikin mu bafa” yasake tambaya akaro na biyu
.
Naja dogon numfashi sannan na bashi amsa”in har gobe yayi kursiyya bata furta ma daya daga cikinmu cewa tana sonsa ba, toh hakan na nufin mun fadi,Loosers) Shikenan sai dukkanmu mu hakura da ita”
.
“Toh amma meyasa kace kafin safiyar gobe, ya tambaya wannan karon da dan guntun Damuwa akan fuskarsa
.
Wannan cakwakiyar soyayyar awannan rana ta RANAR SALLAH ta fara don haka A RANAR SALLAH zamu kawo karshenta
.
Toh FREINDS
.
Shuraih 99% ko Mujahid(mijin biza)
Comment with your actor
.
Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

.
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 7
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
.
Zaune nake a daya daga cikin kujerun da suke makure a cikin falon , centre table a gabana , dauke a samansa kular abincine , yayin da a gefe kuma talabijin ce ke ta faman aiki
.
Gabaya Daya hankalina baya tare Dani,
A wowi na hudu kenan da dawowa gida
acikin wayannan Awannin A bubuwa dayawa sun faru ciki kuwa harda sake gamuwarmu da kursiyya.
.
Al’amarin ya farune a masallacin iedi bayan an idar da sallah kowa ya fara kama gabansa , a lokacinne Ni kuma na fara Tunanin hanyar da zanyi na hadu da ita
Kwatsam kamar daga sama ganinta nai zata wuce ta gefena , nai mata sallama ta kuma amsa toh anan ne take sanar dani cewa ta hadu da dan’uwana wato mujahid sannan kuma harta bashi lambar wayarta da adireshinta.
.
Anan ne na fada mata sunana sannan ta sanar dani unguwar da take sannan ta bani lambarta a gaban idanun ta shiga mota sukai tafiyarsu.
.
Yanzu haka zaman danake a wannan falo babu tunanin da nake face tunanin yadda zan tsara wannan yarinya ta furta cewa tana sona ;
Nadai daure na bude kular dake gabana ,shinkafane dafa duka sai kifin da’aka marmasa akanshi.
Nan take na take wannan abincin ragowar daya rage baifi cikin cokali ba
.
Firji na bude na dauki ruwa mai sanyi nasha toh
Sai asannan ne na dawo hayyacina na duba agogo karfe ukune da minti ashirin 3:20
.
Ta shi nayi naje gidan su mujahid ban sameshi ba
Don haka sai nazaro wayata na matsa namba mai dauke da sunan MY LOVE TO BE
.
Ringing daya tayi aka daga wayar “assala’mu’alaikum wane ne” daga can bangaren aka bukata
“Wa’alaikissalam” na fadi
“Dan Allah dawa nake magana “ta sake fadi a karo na biyu
“Ai bai kamata ace kin manta wannan muryar ba”
“Hmm ko dai Shuraih ne ”
Nayi dariya wanda nasan sai taji sautinsa sannan nace
“SHAKKA-BABU”
“Tuntuni nake tsumayar kiranka naji shiru , nace ko lafiya kake”tamkar yadda kike ” na bata amsa
.
“Kai kasan yadda nake ne a yanzu”
.
“Tabbas kina cikin koshin lafiya ” ta danyi wanda inso samune banki in kwana ina sauraron sautin dariyartarnan ba
.
“Yauwa ka shirya ina jiranka a Emir palace”
“Me kuma zamuyi a Emir palace”na tambaya na kara jan hirar tamu tai tsawo
.
Babu abin da zamuyi a wajen , da shike kasan ni bakuwace a garin naku, kuma naji labarin wai da salla akwai wuraren da suke wasan salla toh shi yasa nake son kadan zagaya dani wuraren don na kashe kwarkwartar idanuwa na”
.
“Kice yawon bude idanuwa zamu”
“Duk sunan daka kirashi da shi , sannan karka manta kazo da wuri don Allah,
.
“Karki damu in don ta nine ki bani minti goma kacal”
Nan na kashe wayar, cikin sauri ma fada bayi na wanke jikina ina fitowa na dau wata bakar zariyata na sanya sannan na dauki wata hula zannan bukar na buga na feshe ilahirin jikina da turare
.
Fita nayi bakin titi ,don tsare dan acaba toh a sannan ne na tuna ai bani da sisi bare kwabo acikin aljihuna.
.
Nan take gabana yabada ras ras ras matsalar gayu kenan NAIRA DA KWABO
.
Da gudu na shigo gida na zo wajen ummana nace mata ta bani rancen dubu biyu , ba musu ta bani.
.
Da fitowata bakin titi sai ji nai wayata ta dau ringing, alamar messages sun shigi, har zan share sai kuma wata zuciyar tace kafin ka share ya kamata ka duba ka gani
.
Ina bude wannan message din sai naci karo da abinda ya sanyani…….
.
YA SANYANI ME??
FARIN CIKI KO
BAKIN CIKI
Choose one
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 8
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.

Ina bude wannan messega din sai naci karo da abinda ya sanya ni farin ciki
Bansan lokacin da na. Kurma wata dariyar farin ciki ba .
Alhamdulillah ,alhamdulillah, alhamdulillah na fada har sau uku
.
Ba komai bane ya sanya ni farin ciki ba face ganin alert cewa mahaifina ya turo mani naira dubu goma sha biyar #15,000.
.
Ai atake awajen na shiga gida na mayar ma mahaifiyata da dubu biyun ta .
A gurguje naje unity bank na ciro kudaden duka sannan na dauki hanyar EMIR PALACE
.
Tana zaune bisa wata kujerar roba sanye da wata tsadaddiyar atamfa dinkin riga da siket ta yafa wani mayafi wanda launinsa yazo daidai da launin takalminta, shi ko jakanta launinsa ya zo daidai da launin kayan dake sanye ajikinta
.
Irin zunzurutun kyaun datayi bazan iya misalta shi acikin wannan gajeren labarin ba ,
Koda na iso gareta sai nai mata sallama take ta amsa da muryatta ma
i dadin sauraro
Sai na saki wata murmushi mai dauke da sakonni kala kala sannan nace da ita “maganar gaskiya itace a kowani lokaci kara kyau kike gimbiya kursiyya”
.
“Lallaima wato abin ya zama yar zolayace ko” tafadi
Nan take nasa hannu na jawo wani kujera sannan na zauna ina mai fuskartarta
Hira mukai da ita sosai,amma ko kadan babu wata kalma ta so ko kauna dana bari ta subuce daga bakina
Bayan mun idar da hirar ne muka tashi muka nufi bakin titi don tsaid abin hawa
Toh anan ne nace da ita”kinga ma na manta ban tambayeki ,inda zamu fara zuwa ba”
Tayi mani fari da idanuwa tace ” ai kafini sanin garin don haka kai zan tambaya ina muka dosa”
.
“Ok tunda haka kikace sai ki saka io,sannan kija bakinki kiyi gum, ga duk wajenda na kaiki”
.
Napep na tare sannan dukkan mu ,wato ni da ita muka dunguma izuwa ciki, na dan matsa gaban direban na rada mai akunne wajenda zai kaimu
**** ****** *****
Kayataccen wajene wanda iya tsaruwa ya tsaru, tamkar gidan gona haka yake ,
Kujerune makare a wajen an masu wani irin salo
Salon kuwa shine kujerune guda biyar ake ajiyesu yadda zasu fuskanci juna (cycle) a tsakiyar kujerun kuwa wani dankareren teburne na gilashi.
.
Zaune take a daya daga cikin kujerun a yayin da ni kuma nake fuskantarta yayinda wata dankareriyar teburi ta gilashi ta raba tsakaninmu
.
A makare a saman teburin kayan makulashe ne da tande tande sai lemuka iri iri
Duk kuwa ni nai ordansu wa kursiyya duk da kuwa wasu daga cikin kayan makulashen ban taba ganin suba sai yau ARANAR SALLA.
.
A tunanina na riga na gama sace zuciyan kursiyya tun da gashi ta kirani izuwa yawon bude ido,
Ta danci kayan tande tanden kadan sannan ta kora lemo sai ta dubeni tace itafa so take taje gida, dariya nayi sannan nace “keda kika fito yawon bude ido , tun ba’aje ko’inaba har kin fara sarewa “
.
“Ba sarewa nayi ba yanayin garinne bai min ba “
Anan dai na shiga lallabata har na ci nasara na shawo kanta ta amince zamu karisa yawon bude idanuwanmu
.
Wani ma’aikacin wajen ne ya kawo mani bill na dauki bill din da hannun hagu alokacin da na dau lemo zan kora da hannun damana
.
Ai koda na kalli bill din bansan lokacin da kofin gilashin dake hannuna ya fadi akasa ba
Sakamakon ganin irin makuden kudaden dana kashe yanzu yanzu
.

.
Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
https://facebook.com/Shuraih-99-296485144050085
.
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 9
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
Naira na gugar naira har naira Dubu biyar #5000
Ni dana ke tunanin duk wannan lodi danayi baifi na dubu daya #1000 ba amma ashe hadin manyan mutane nayi ,
“Dubu biyar ” na fadi acikin raina
“Wainine nan na kashe dubu biyar cikin mintuna kalilan akan wani abin banza wanda bama zamu’iya cinyewa duka ba.
Ai da badin muna tare da kursiyya ba da babu abin da zai hanani kwashe duk wannan kayan tande tande na zuba su acikin leda,nayi gida
.
“Ina ganin ya kamata mu wuce”
Muryar kursiyya naji kwatsam acikin raina
Tashi nayi naje na biya su kudinsu ba tare da son raina ba haka ina kallo muka tafi muka bar damin abinci da lemo bisa tebur.
Godewa Allah na sake yi daya sa mahaifina ya turo mani da kudi. In badan haka ba da yanzu haka ban san irin ukubar dana ke ciki ba
**** ****** ******
Kishingide nake acikin daki na bisa katifa nayi daidai da kafafuwa kai kace dan kaciya ne ,
.
Babu abin da na ke tunani sai abinda ya wakana tsakanina da kursiyya
A wanni biyu da suka wuce lokacin da muka bar wannan restaurant din bamu zame ko ina ba sai wani wajen chasun Salla anan ma muka dan shafe wasu mintuna sannan aka tatsi lalitata har naira dubu biyu #2000
Kai in takai ce maku wannan labarin, saida muka ziyarci wurare akalla sunkai biyar, akowani waje kuwa sai an tatsi lalitata.
.
Bazan mance lokacin dana sauke kursiyya a kofar gidansu ba, alokacin ne ta fito daga cikin kafi babur din da muke zaune dukkanmu, fitowa nima nayi daga cikin kafi babur din, sannan na sallami mai kafi babur din yai tafiyarsa
.
Kursiyya ta matso dab dani yadda zamu iya shakan numfashin junanmu ,tace dani
“Shuraih” yadda ta kira sunan sai naji tamkar ita ce ta rada mani sunan sannan taci gaba da cewa
“Agaskiya na godema abisa wannan halaccin daka nuna a gareni”
“Ai nine da godiya bake ba gimbiya kursiyya”
Nace da ita yayin dana dan ja da baya
“Toh ni zan shiga gida. Shuraih”. Tafadi mani lokacin data nufi hanyar da zata sada ta da kofar gidansu
“Bakiji ba” nafada
“Baka fadi ba” ta bani amsa
“Gimbiya kursiyya yanzu a wani matsayi kika ajiyeni acikin zuciyarki”
Tayi murmushi sannnan tayi mani wani kallo wanda ke nuna ta dago jirgina
“Shuraih lallai zan baka amsar wannan tambayar taka amma ba yanzu ba,
“Sai yaushe “na tambaya cikin kaguwa
“Zan kiraka a waya da karfe 9:00pm na dare. Sannan sai in sanar dakai inda zamu hadu” tanagama fadin hakan sai tai tafiyarta
.
Sa’o’i biyu kenan da faruwar wannan al’amarin
Yanzu dana ke kwance bisa katifa acikin dakina, babu abin dana ke jira face karfe tara na dare tayi, duk kusan minti daya sai na duba a gogo haryanzu dai karfe 8:30pm ne
.
Sautin budewar kofa naji daga gefena hakan yasa na maida dubana bakin kofa, mujahid ne ya shigo. Yana zuwa daidai wajena sai yace” baba kafara shirin cin kasa fa”
Na dubeshi cikin mamaki nace mai name kuwa
Yayi murmushi sannan yace
“Ai dazu da muka dawo masallaci, na kira kursiyya awaya mukai ta hira , nace mata zanzo gidansu, nan take ta bani adreshin gidan
Ina zuwa kuwa na dauketa ,muka je sabon gari gidan su Anas daganan kuwa muka zarce zuwa karofi na kaita gidan hajiya suka gaisa, kai in takaice maka labarin har cewa tayi zata kirani yau misalin karfe taran dare izuwa wani shagali”
BADAKALA KEnAN
Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 10
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
Take na tashi daga kwancen danake sannan cikin alamun mamakin maganar mujahid. Nace mai
“Yaushe kenan duk wannan al’amari ta kasance tsakaninka da kursiyya alhalin yau throught out muna tare da ita ne”
Nan na zayyane ma mujahid dukkan wani al’amarin daya faru tsakanina da ita.
Koda mujahid ya gama sauraren labarina sai ya kama habar bakinsa sannan yace
“To yanzu wannan yarinya me take nufine damu”
“Ni ba wannan ne yafi damuna ba ,shin me yasa ta ce zata kiramu da karfe tara” na fada
Girgiza kai mujahid yayi sannan yace”ni ma abin dana ke tunani kenan”
.
“Kodai zata kiramune don ta zabi wanda take so a cikin mu” nafada
“Tabbas maganarka hakan take kiranmu zatayi don ta nuna wanda ta keso atsakaninmu” mujahid ya fadi
“To amma…” Karar ringing din wayar mujahid ce ta katse mani zancena “
Ciro wayar yayi daga aljihunsa sannan yai sallama , tsayawa yayi da wayan akan kunnensa har tsawon wasu dakiku ,sannan yace “toh ganinan zuwa”
.
Yana sauke wayar daga kunnensa ne nima tawa wayar ta fara ringing ,ina dubawa naga nomban kursiyya ne
Na da
ga tare da doka sallama, ta amsa sannan tace
“Shuraih ka saurareni da kyau yanzu haka ina (U.CENTRE) , Bikin salla ake don haka ina jiranka a wajen yanzu, dan Allah kar ka wuce mintuna biyar ” tana gama fadin hakan ta kashe wayar.
.
Na dubi mujahid nace “kursiyya ce ta kirani tace dani wai na sameta a..”
“U.centre ko” ya katseni da fadin haka
“Toh amma kai ya akayi kasani” na tambayeshi
“Kiran da akai mani yanzu itace ta kirani take sanar dani wai na sameta a U.centre” ya bani amsa
***** ******
A tsaye muke abakin titin muna neman acaba , can sai ga wani dan acaba nan ya sulalo, tsayar da shi mukai, sannan muka hawa muka cemai U.centre zai kaimu
.
Gudu acaban keta shararawa,
Babu tunanin danake illa irin cakwakiyar da zata faru izan har kursiyya ta zabeni a matsayin masoyinta, hakanan wani irin cakwakiya za’a diba izan har ta zabi mujahid ,
Can sai ji nai dan acaban ya taka burki, take babur din ta tsaya cak a gefen titi
Na duba gefen dama na , sannan na duba gefen haguna banga wani mai mota yana ko masu babur suna giftawa titin ba.
Duk da kuwa a cikin duhu ne amma hakan bai hanani gane A DOKAR DAJI muke ba.
.
Mujahid ne ya fara saukowa sannan yace “ya malam mun ce maka ka kaimu U.centre ne bawai DOKAR DAJI ba “
Juyowa dan acaban yayi sannan ya dubemu, duk da acikin duhu muke amma hakan baisa kwakkwal din dake kanshi ta daina kashe idanu ba, haka kuma hakan bai sa na kasa gane wannan bakar fuskar tasa ba
Kamar dazu dai fuskar nanan babu walwala bare annuri a tattare da ita ,
Koda nai arba da fuskar nan tashi sai naji gaba daya gabban jikina sunyi lakwas, alamun razana suka bayyana akan fuskata ,
.
Na juyo dabi mujahi na ce mai “kasan ko wanene wannan dan acaban din”
Girgiza mun kai yayi alamar bai ganeshi ba
.
“BA WANI BANE FACE BAMAGUJEN DAN ACABAN DA MUKA CUTA DA SAFE”
Na fadi mashi
.
Hausa wa suka ce inkere na yawo zabo na yawo wataran sai an hade
.

Warnin:- Ina fadi ina sake fadi, da kwai wasu da suke Editin mani post suna cire sunana sannan su saka nasu, wato ina nufin SATAR FASAHA
Ban hana copy ba amma ban yarda a canja mani tsarin labari ba
.
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%
https://facebook.com/Shuraih-99-296485144050085
.
ARANAR SALLAH
Kagaggen Labari
Shuraih 99% & mijin biza
NA
Shuraih Usman
Part 11
.
Doka:- ban hana copy ba , Amma duk wanda yacanja mani tsarin labari ko ya cire sunana ya saka nasa toh Allah ya isa.
.
.
Koda dan acaban ya fuskanci mun ganeshi sai ya fashe da dariya marar dadin sauraro sannan ya fuskance mu yace
” Mu maguzawa ,ba a cutarmu sakamakon wanda ya cucemu kuwa itace mutuwa”
.
Ai yana gama fadin hakan sai ya zaro wata narkekiyar wuka daga kugunsa ,kafin ya yunkuro ya juyo
Tuni har mujahid yayi tsalle daga kan babur din , take nima na mara masa baya,
Bamu tsaya duban gabanmu ba sai kawai muka ari na kare
.
Wannan bamagujen kuwa sai ya buga wutan babur dinsa sannan ya cigaba da binmu.
.
Fadawa mukai cikin daji sai gudu muke
A yayin da mujahid yake gabana ni kuma nake bayansa
.
A duk lokacin dana waiga bayana sai naga wannan bamagujen ya kusa cimmini hakan ce tasa na dage sai gudu nake
.
Muna cikin wannan gudun ne muka shigo wani gona wanda kunyen doya ne birjik a ko’ina ,ban ankara ba sai ji nayi wani kututturen itace ya tsarge mini kafa,
.
Take na fadi shirim bisa kunyen doya ,
Na yunkura kenan zan mike in cigaba da gudu , kawai sai ji nai an ciccibeni an buga da kasa , sannan aka hawa ruwan cikina aka danne ni
.
Ashe dai bamagujen nan ne ya cimmini, wukar dake hannunsa ya daga sama sannan yace
“Kai yaro babban kuskuren da kuka aikata agareni itace karya da kukai mani, a rayuwata na tsani karya , kaine mutum na goma sha uku da zan kashe ata dalilin karya”
Yana rufe bakinsa sai yadaga wukan sama da nufin ya caka mani, kawai sai ji nai ya kwarara ihu, sai hannunsa mai rike da wukar ta fara yo kasa tana kusan toni,
Nan take bamagujen ya bingire kasa sumamme
.
Abin daya bani mamaki kenan , sai dana mike tsaye sannan na lura da mutum agabana .
Mujahid ne rike da wata zabgegiyar katako a hannunsa,
Sai yanzu nagano abin dayasa bamagujen nan ya bingire akasa sumamme .
.
Nan take muka dauki babur dinsa muka hau mujahid yajamu.
.
**** ******
Saukarmu kenan abakin dankareren hotel din wanda a samansa anyi rubutu da wata na’ura mai haske rubutun cikin manyan haruffa suke(U.CENTRE)
.
Nan take muka kutsa kai ciki, bamu sha wahala ba wajen ganin kursiyya ,
Azaune bisa kujera kursiyya ce
Sannan wani saurayi kyakkyawa yana fuskantar ta koda muka kariso sai muka gaisa da shi sannan muka nemi kujeru muka zazzauna
.
Tun lokacin dana hada ido da wannan saurayin naji gabana ya fadi,
.
Akaron farko kursiyya ta dubemu tace “shuraih ,mujahid, wannan shine saurayina ANAS, kuma mijin da zan aura “
.
Ai bansan lokacin da kaina yafara juyiba ,kunnuwana suka kurumce ,
Nidai naga kursiyya na motsi da baki amma bansan me take fadi ba ,take na tashi naje na nemo ruwa nasha sannan ne hankalina ya dawo jikina
Kursiyya ta dubi waNnan saurayin tace “Anas wayannan Abokaina ne kuma yan’uwana “
Nan dai muka sake gaisawa da anas
A sannan ne take sanar damu cewa bikinsu saura sati biyu kuma zata aikomana da katin gayyata .
******
Nida mujahid muka fito daga cikin hotel din rai a bace ,
Dukkanmu da abinda muke tunani acikin zuciyarmu,
.
“Sannunku dan Allah tambaya nake “
Wata zazzakar murya ce ta katse mu,
Waigowar da zamuyine mukai arba da ita,
Farace tas,mai matsakaicin tsayi hade da faffadan fuska, dauke da haskakkun idanuwa , dan siririn karan hancinta shi yataka muhimmiyar rawa wajen bayyana kyawunta.
.
Koda mukai arba da wannan kyakkyawar budurwa sai muka rugo izuwa kanta
Da saurina na matso gefenta na dama shi ko mujahid ya matsa gefenta na hagu,
.
Rike mata hannu nayi sannan nace wa mujahid
“A’a fa mujahid kar mui haka dakai kasan ni nafara ganinta”
Shima ya rike mata hannun hagu gam yace dani
“Karya kake ni nafara ganinta”
Nan dai muka cigaba da jayayya da shi, izan naja hannun damanta sai kaga shima mujahid ya janyo hannun hagunta, yadda kasan zamu ballata
Ita ko inbanda ihu da karaji babu abinda take
.
Wani mai shayi dake dan nisa damu, yana kallon duk wannan badakalar,
.
Sai ya wangame katoton bakinsa sannan yace”jama’a ina kuke ga wasu yan banzan yara can suna neman su lalata yarinyar mutane” cikin bude murya ya fadi hakan
.
Ai koda mutane suka ji haka sai suka nufo inda muke
Daga mai katako 2 by 2 sai mai icce da gora
Kai hardama masu Adduna da fafale
Suko yara kankana na sai suka debi duwatsu.
.
Koda muka hangosu sai muka saki wannan yarinyar sannan mukace kafa mai naci ban baki ba
.
Muna cikin gudun ne kawai sai naji saukan wani katon abi a goshina , nan na kwarara ihu, ina taba goshin naji danshi danshi a goshina wannan shi ya tabbatar mani da an fasa mani goshi
.
ADUK LOKACIN DANA KALLI TABON DAKE GOSHINA A MADUBI SAI IN TUNA
DA RANAR SALLAH
.
TABBAS BAZAN TABA MANTAWA DA IRIN CHAKWAKIYA DA BADAKALAR DATA FARU DANI ARANAR SALLAH BA IYA TSAWON RAYUWATA
.
Tammat alhamdulillah
Kagaggen labari daga Shuraih Usman
Na godewa Allah daya bani ikon kammala wannan labari
Duk wani kuskure dana tafka acikin wannan labari Allah ya gafartamani
Sannan ina mika gaisuwata ga dukkan masoyana da masu bani shawarwarin alkhairi
Allah yabar zumunci
Daga karshe nake cewa sai kunjini a cikin wani sabon littafina mai suna TUHUMA
.
ARANAR SALLAH
Shekarar rubutawa:- 2017
Hakkin mallama (m) Shuraih Usman
Company:-Shuraih 99%
Tel.08133209890
Tel.09086261484
.
Warning. | Gargadi
Ban hana copy ba, Amma duk wanda ya canja mani tsarin labari , ko ya cire sunana yasa nasa toh Allah ya isa
.
LITTATAFAN MARUBUCIN
1.TAKOBIN JINI 1-2-3
2.LABARINA
3.NAMIJIN GASKE 1
4.ARANAR SALLAH
LITTATAFAI MASU FITOWA
1.TAKOBIN JINI 4-5
2.NAMIJIN GASKE 2-3
3.TUHUMA
4.SADAUKI UBAN SADAUKAI
Coming soon…….
.
Sadaukarwa ga
Mal.Usman
Haj.Maryam
Mujahid hamza
Zainab Usman
AAmina Usman
Abdul’aziz Usman
BAN MANTA DA KUBA
Dahiri Usman diffusion(D.U.D)
Anas Aliyu katuka(bin maleek)
Suleiman ishaq(big army)
Abdullah(B.O.C)
Dafatan kuna cikin koshin lafiya

Comments

table of contents title