Main menu

Pages

AWA 48 A ZIRIN GAZA complet Hausa Novels littafan gwarama

AWA 48 A ZIRIN GAZA
Ibrahim Ahmad Daurawa
Made:- Shuraih Usman

Domin download na wasu kayatattun hausaebooks namu sai ku ziyarcemu a shafin yanar gizo gizon
mu akan wannan adireshi http://shuraih.waphall.com

Kuna iya ziyartarmu a shafinmu na facebook kuyi like http://fb.com/hausaebooks

AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi daurawa
Littafi na daya 1
Page 1
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
JAFFA
.
Allah daya gari ban ban nace a zuciyata bayan da iska mai zafi ta bugi fuskata a lokacin dana leko
waje. Na tsaya karewa wajen kallo , tutar kasar izra’ila na fara hangowa tana filfilawa akan
husumiyar filin jirgin saman , inda nan ake gudawar da zirga zirgar jiragen sama
.
Jama’a suna kaiwa da komowa a filin sannan na fara tako matakalar sauka daga jirgin , wani abu da
bana mantawa da shi ne duk san da na dubi tutar izra’ila sai naji gabana ya yanke ya fadi ras
.
Da haka jakata a rataye a kafada ta muka yi dan tattaki zuwa falon karbar baki , wasu yan uwan su
ko abokan harkansu sun zo tarar su cikin murna da annushwa .
.
Na kuma lura dda wasu ba taryar kowa suka zo ba babu wata walwala ko fara’a tare da su, idanunsu
na kan kowa, kamar yadda kyanwa ke tare nutstuwa idan taji motsin bera. Ko ban fada ba kasan ko
su waye su JAMI’AN TSARO NE
.
Wajen karban baki nan ne kuma ake duba fasgo da sauran takardun tafiye tafiye , gurin a tsare yake
akwai kayan binciken muhimman takardu na zamani kamarsu inji mai kwalkwalwa da fitilun
siddabaru wanda suke bayyana rubutun boye sirri
.
Kaman misali irin na takardar kudi, na bude baki ina kallon abubuwa har layi yazo kaina wani
bayahude ya kalleni sama da kasa alokacin dana mika masa fasgodina a lokaci guda kuma gabana
yaba da ras. Daga nan ya fara jeho tambayoyi barkatai iri iri kamar ruwa, kai ka cebai karanta
fasgodina ba.
.

Abin dayai ba shi muhimmancin shine “me ya kai ka bosniya Hasgobina har tsahon wata biyar “
don ya lura kan sarkin dayake jikin fasgon da kuma sabon da aka buga akwai tsahon kusan wata
biyar a tsakani.
.
Azuciyar tana ce wannan bai shafe ka ba. Ina tunanin amsar da zan bashi yace “me ya kaika
sayarebo” kai tsaye na bashi amsa “neman labari ya kaini” ya dubeni sosai kamar lokacin ya fara
gani na “me ya zaunar da kai har tsahon wannan lokaci ” ya bude ta ya kuma dubeni sosai ” na so
dawowa amma babu hanya saboda filin jirgin saman sayarebo yasha wata majalisar dinkin duniya
ne ta rufeshi” yayi mini kallon ban gamsu ba
.
Ya gyada kansa cikin dabara hannunsa yanakan tebur ya gusa da shi gefen teburin ya danna wani
dan kulltu wanda aka rufe gefensa da takardu, cikin ya aikata amma na lura da komai, don haka
nasan cewa wani abu zai faru
.
Na kalleshi ido da ido yana shirin sake tambayata a cikin dakin dayake ciki kofa ta bude daga
bayansa wani dogo kakkarfan bayahude ya fito ko’ina jikinsa an rubuce shi da jami’an tsaro ba sai
ka tambaya ba duk da babu wata alama ko ta kayan sarki ,kallo daya kawai zaka yi masa ka tabbata
jami’in tsaro ne ajin farkon babu wata tantama
.
Ya karbi fasgodina ya duba sukayi yaren yahudanci ya danna na’urar mai kwalkwalwa, yayi nazarin
wasu bayanai cikin sauri “daga wacce kasa kazo nan” ya jeho min tambayarsa a lokaci guda kuma
ya kura mini ido “daga Bosniya nake” na maida masa kai tsaye nima na kura masa ido ” kai dan
wacce kasa ce” ya sake tambaya ta
.
“Nijeria” na fada ba tare da na dauke idona daga kansa ba
“Me ya kawo ka nan?”
Nayi tunnani cikin sauri kafin na bashi amsa don na fara fahimta makircin da suke shirin kulla min
kuma na san kasar izra’ila basa maraba da yan jarida kasan wanda yake da abin fada kum yason a
afada bazai taba maraba da dan jarida mai kishin ba, sai dai yan abi yarima asha kida
.
Ni HADI sam ba irinsu bane ni dan jarida ne na hakika mai kishi, ina cikin wannan sake sake ne
yace meye sana’arka na amsa “rubuce rubuce da neman labari” ya matso kusa dani “kana da sheda”
na ciro katina daga aljihun rigata na mika masa ya duba ya kalleni ya sake kallona ya dauki kan
talho yayi magana .
.
Ya ajjiye shi a hankali naga kamar yana tuna wani abu “me kazo yi nan” cikin sauri nace “yawon
bude ido” ya tsira mini ido yasa hannunsa daya a aljihun wando ya kuma nuna ni da hannunsa na
dama “bana son yan jarida a kasarmu sam bana maraba da ungulaye”
.
Yana rufe bakinsa wasu majiya karfi suka nufoni sun fito daga kofar kudu da inda nake ,kai tsaye
suka nufo ni kamar kibiya,cikin sauri suka kewayeni daga nan suka ce na bisu inda suka fito na bisu
ban yi wata gardamaba suka kai ni wani dakin bincike kwkkwara duk kayan jikina ba ain da basu
duba ba hatta dunduniyar takalmina sai da aka kusa ballata bayan an gama bincike da wata yar
na’ura mai kwalkwalwa da ake kira metal detector kwalar rigata ma bata tsira ba, babu inda ba’a
bincike ba na share sama da sa’o’I ana yimin tambayoyi kala kala kamar mutumin daya fado daga
duniyar wata
.
Daga karshe aka shige dani wani ofis inda na iske wani bayahude kato zaune akan kujera mai
juyawa yana da kasumba da saje da gemu da kumatu luhu luhu yan idanunsa sun nutse ciki , akan
teburin akwai talho zai kai biyar daya ajjiye wannan sai ya dauki wannan, ban ga sunan sa ba kamar
yadda ake ajiye sunan mutum akan tebur ajikin dan katako ko roba , yana zaune yana busa tabar
hanavana katuwa ahannunsa kamar yankan rake, muna shiga firgigit ya juyo da kujerar ya zuramin

ido tamkar yana kallon wani dan kwaron da yake neman fada masa cikin shanyinsa ya gummtsi
hayaki ya fesa sama, kumatunsa sukayi sama da kasa sai naji wani dan sauti kamar na kuya
“Vulture are not welcome here and we think you have a hidden mission not tourism, even though
we have nothing to incriminate you”
Ma’ana ba a maraba da da ungulaye ,kuma muna tsammanin kana da wani boyayyen shiri ba yawon
bude ido ka zo ba, ya sake busa sigarinsa na dube shi kawai cikin tsana da bacin rai don duk na
gama galabaita da tambayoyi da bincike na wulakanci ga kallon kaskanci iri iri ya kalleni sosai
“you are to deported back to where you come from” bansa dana yi subul da baka ba nace ” tafi nono
fari” ya dubi jami’an tsaron dake baya. Nan da nan suka bukaci dana fassara abin da na fada ya nace
“shi kenan na gode”

Toh anan zan dakata Tambayata anan shine
MAI NE NE SUNAN MARUBUCIN LITTAFINNAN
.
AWANI SHEKARA YA WALLAFA WANNAN LITTAFI
Bazan ga masu cika bakin cewa wai su suna karanta tsoffin littatafan hausa
Daga naku shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 2
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Lokacin daya juya na naji yayi tsaki yace “we don’t know who give you this pucking visas…..”
Na dan tsaya don naji karashen maganar jami’in tsaron ya rike kafada ya hankadani gaba “you are
not welcome here”
Turanci irin na amurka
.
Hankalina ya tashi gaba daya yayin da muka fito muka shiga dakin da akayi min bin cikie na zauna
ina jiransu su tattaro min kayana .
Raina ya gama baci matuka ainun don ba irin wulakancin da ban gani ba wajen binciken nan
tambaya kamar wanda aka kama da laifin kisan kai
.
Aka garomin fasgo din akan tebur ya fado ka
n cinyata na yunkura na dauki jakata , don haushi ko
budawa banyi ba na saka a ljihu, na figi jakata na saba a kafada nayi waje fuskata a daure rai na
abace
.inajin takun sahun mutun yana biye dan yana kokarin kwantar min da hankali wai ba sun yi min
hakan don wulakanci ko kin bako bane sunyi ne don matakan tsaro
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Ni dai ko sauraransa ban yi ba da haka ya rakoni har tsakiyar filin jirgin saman abin dauya dameni
kawai in rabu da wadannan yan wulakancin in dawo sayarebo wajen kausar ko hankalinta ya
kwanta ni kuma inji sanyi a raina saboda ganin masoyiyata
.
Mutumin yayi min rakia zuwa kofar wani jirgin saman “swiss air” ina kokarin mika “boarding pass”
dina na shige jirgin sai naji an rike min hannu ta baya , na juya a hankali na dube shi tsaf, dogo ne
fatar jikinsa jajaja alamar ya zauna a kasa mai zafi ,
.

Idonsa kanana masu launin toka toka , gashin kansa ruwan gitsawa yana da gashin baki ba gemu
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Ya mika mini hannu nine mr Ros ina son ganinka a ofis dina
Wannan kalaman sun bata mini rai kwarai sai naji kamar ya kwaro min ruwan zafi, cikin sauri na
nuna masa bodin pas “bana bukatar ganawa da kowa ba kun koreni ba na jefa masa maganar cikin
gadara
.
Alokaci guda nayi kokarin shigewa ya rikeni gam ” haryanzu kana cikin kasar izra’ila don haka dole
ka mutunta dokokin karsa, ka biyoni kada kaji komai”
.
Naso nayi gardama koda na lura jami’an tsaro suna yimin muzurai kuma na san cewa ban shiga
cikin jirgin ba dana shiga to nabar izra’ila kenan, ina cikin inuwar swizland” dole subarni ganin haka
dole na rufawa kaina asiri na bishi duk jama’a suna kallona sun kuma san cewa da walakin goro
amiya wannan shima ba karamin wulakanci bane , ace cikin dubbai an tasa ka gaba kamar barawo
kowa na kallonka
.
mintina biyar a tsakanin ya miko min takardar iznin yawon bude ido a izra’ila amma banda wasu
wurare daya kira “security zone” na duba takardun na ga babu iznin zama a telaviv da kewayanta
sannan kuma an rubuta baro baro kada na shige kwana uku a kasar
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Na nutsu sosai wata tambaya tazo min me yasa yanzu aka bani izini bayan angama wulakantani an
galabaitar dani an koreni kuma meyasa aka bani izni bayan da an mini cikakken bincike an gano ni
hatsari ne ga tsaron izra’ila har an koreni don a huta da kaya sannan kuma a kirayoni a bani iznin ba
wani kace na ce , lai lai da sake wai mai kaza ya tashi da kai, don haka nace dole nayi taka tsantsan
da mutanen nan sai maganar shugaban hizbulla a sarayebo ta fado min “zasu iya binka su halaka
ka”
**************************************
Rana ta raba sama gari ya dauki zafi sosai na duba agogona na ga shabiyu da rabi na rana , na shafe
a sama da awa biyar kenan a filin jirgin saman ana yimin tambayoyi da binciken bin kwakwaf
.
Na fito harabar filin jirgin tare da dan rakiyata inda jama’a suke zirga zirga a wajen akwai wajen
ajiye motoci masu zuwa filin jirgin.
Akwai kuma wajen ajiye motocin haya da bas bas na alfarma sunyi layi , sai ka fadi inda zaka kuyi
tsada da direba
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Kai tsaye ko kuma kaje ofis dinsu idan kana da kudi da yawa ka cashe musu kudinsu su baka direna
ya kai ka duk inda kake son zuwa iya tsahon zaman ka a kasar, idan kuma kai sananne ka iya hayar
motar har iya zamanka.
.
Na dauki hayar mota ajin masu kudi duk kuwa da cewa ba matsala bane a guna amma ina da wani
abu araina
.
Muna shige shigen karge na jami’an tsaron filin jirgin sama na faa fahimtar halin kuncin da
falasdinawa suke ciki.
.
Duk ina da naga ana aikin kaskanci ko aikin wahala idan na tambayi direna sai yace falasdinawa ne.
Ina son tambayar dalilin daya sa falasdinawa ne kawai suke aikin kaskanci sai naji gabana ya fadi
Ras. Don haka na kanne nace na bincika da kaina
.
Yayin da yake shigowa yakin cikin birnin telaviv lokacin na kuma ga wani abu daban wato taruwan
jami’an tsaro da sojoji dauke da makamai kamar ana yaki, motocin yan sandan tarzoma suna zirga

zirga ko’ina rike da bindigogi da rediyon walis a kugunsu suna lura da kowa suna muzurai kai kace
jiya jiya ne akaci garin da yaki.
.
Gaba daya yanayin garin ya sauya ya koma irin yanayin filin daga , a gaskiya har yasa tunanin tuzla
ya fado mini arai, naji na kasa jurea har zuciyata ta fara bugawa da karfi, na dubi wanda yake
gefena wanda shine dan rakiyata “tourist guide ” na kalleshi sosai “wannan jami’an tsaron haka
lafiya kuwa?” Na tambayeshi tun daya shigo baice komai ba sai a lokacin
“Sune dakarun zaman lafiya” ya dauke kansa yana kallon waje a daidai lokacin wata mota ta gifta
mu na lura da ita ganin yadda ya kalleta, sabuwa ce mutum biyu ne acikinta daya yana magana ta
rediyon walis dake cikin motar babu fallen rubutun lamba, bayanta kuma wata ta shigemu an rubuta
“first class citizen” dan kasa mai daraja ta daya. Ba a jima ba kuma wata ta shige da lambar “third
class” da fari dai banyi niyyar tambaya ba saboda yadda naga na kusa dani yana kallona amma cikin
dabara sai na jeho tambayar”mai daraja ta daya” meye kuma haka ya dubeni zaiyi magana sai
mukayi burki a shigen jami’an tsaro
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
A gabanu jerin gwanon motoci suna tafiya a hankali zuwa kofar shingen sojoji da yan danda wasu
dauke da bindigogi suna muzurai, wasu kuwa suna rike da na’urorin bincike irinsu na’urar sansanar
bomb data binciken bindiga wasu kuma suna takardun mutane sunayensu da kuma gurin da zaus da
lambar motar da matsayin mai motar wato bako ne ko dan gida ne, shi din ma wacce daraja yake da
ita kuma wanne jinsi ne bayahude ne ko balarabe “kai wadannan mutane da rashin yarda suke”
bansan lokacin da wannan furucin ya fito daga bakina ba sai dai nayi sa’a da harshen hausa nayi shi
.
Mutumin dake kusa dani ya kura mini ido ya kalleni sosai, adai dai lokacin kuma motarmu cikin
sanda ta kai ga kofar shingen wani soja rike da bindigarsa kirar amurka m16 ya iso cikin sauri ya
sunkuya tun kafin yayi magana direban ya bashi takardunsa sukayi magana, ga alama dai sun saba
da shi na lura lokacin daya mika takardunsa sinyi musanyar alama ta cikin dabara cikin na lura da
su ta wutsiyar idona
.
Wani ya karaso dauke da wani dogon karfe mai fadi daga karshen sa kamar shebur ya karasashe a
karkashin motar sannan ya umarcemu mu fito ya kara mana na’urar binciken bindiga, ya bukaci
fasgo dina na mika masa ya buda ya dubeni sama da kasa
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Yayi magana sojoji cikin sauri suka baibayeni kafin kace kwabo har wani ya doramin bindiga a
wuya , sunyi mamaki da suka ga ko gezau banyi ba ni mamaki kawai suke bani ba tsoro ba,
Na dubesu daidai cikin natsuwa “ka keta dokar kasar izra’ila “wata murya ta fada a bayana nayi
kokari na waiwaya don yin tozali da mai maganai suka hanani motsawa “what is the hell with you”
na fada cikin fushi “you are deported” murya ta mayar mini duk jami’an tsaro dake wajen suka juyo
guri na cikin sauri suna jiran cika aiki kamar kare ya hango muzuru
.
Toh anan zan tsaya don na gaji
Sai mun hadu ranar friday
Daga shuraih Usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 3
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]

Cikin hanzari na fisge fasgona daga hannunsa na buda wani shafin na nuna musu inda aka buga
mini iznin shiga kasar kuma na cire “tourist visit permit” na nuna musu a daidai wannan lokacin
wata mota jif patrol ta soja tayi birki a gabanmu akwai eriya doguwa a jikin motar
.
Wani manjo janar din soja ya dirgo kato ne mai katon
ciki kamar tulu da walis a hannunsa fuskarsa
kamar an aiko masa da mala’ikan mutuwa a turbune babu wani annuri
Idanunsa irin na kyanwa kumatunsa kamar an sassaka, mai zagayyar fuska yana da saje da gemu
buyya wanda ya maida shi tamka dattijon biri
.
Kafafunsa shafta shafta kamar dirka, kafarsa daya tafi daya tsawo abinda yasa tilas yake tafiya irin
na kaguwa ya na dinkisawa a birkice
.
A kowane gefensa wasu matasa madaka kare suna biye da shi, kowane da karamar mashigan rike a
hannunsa sun gama shirin tsaf suna shirin bude wuta jiransa kawai suke yace ket su cika aiki.
Duk suna sanye da kayan soja mai rodi rodi , sauran kuma cikin motarsu suke suna masa rakiyta
duk sunyi shirin kota kwana , yana karisowa gurin sauran sojojin a sauran jami’an tsaro suka sara
masa sukayi cirko cirko wani kurtu ya fara masa bayani da yahudanci, ya dubi ne yayi musu
magana da amon sautin jemage
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Nan take suka janye bindigoginsu daga saman sukayi sororo da su suna sauraransa cikin tsoro da
girmamawa kai kace mala’ika neshi .
Wannan girmama ta bani mamaki
.
Ya karen kallo tsaf ya karbi takarduna ya duba su a hankali cikin takama, kasaita da nuna isa ya
gama ya sake kallona yayi magana daga cikin motar sai naga wal hasken fitilar daukan hoto na
tabbata hoto na aka dauka , kawai sai naji sautin jemagen yana furta kalmomin turanci “be careful
don’t do anything wrong like gathering information or tres-passing into security zone or any no go
area” yayi murmushin mugunta ya girgiza kansa “I will teach you a lesson that you will never forget
throughout your life “
Ya kalleni ya nuna ni da dan yatsansa cikin wani sauti mai tsoratarwa yace ” kada ka tara ko ka
rubuta mummunan rahoto akan kasar izra’ila kada ka kuskura ka aika da labarai a ciki ko a wajen
izra’ila idan ka saba wannan ka’idodin yan yatsunka zasu baka amsa”
.
“I will cut this into pieces if you write mischief against us Mr goyim remember I am major dayin
robert” ya kalleni sosai ya kada kai ya juya yana dingisawa ya shige motarsa suka rankaya a guje
suka barni anan ina gumi ina yarfewa, sautin maganarsa yana kararawa acikin kwakkwalwata
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Mun karaso birnin telaviv da la’asar, yunwa da gajiya da zulmin major doyin yasa abun duniya ya
dameni
Na lura lallai nan ba wurrin da yan jarida suke da yanci bane , banayi binciken abubuwan da suke
raina .
Ko’ina jami’an tsaro da sojoji ne birjik kamar wani sansanin yaki, irin shingayen da na gani a hanya
tamkar wani filin daga ne daya fada hannun abokan gaba , irin yadda ake binciken mutane daga
inda suka fito da inda zasu da kuma abin daya fito da su sai ya tuna mini kasar afirka ta kudu
alokacin wariyar launin fata inda bakin mutum bashi da iznin zuwa wani gari sai da takardar izni
idan turawa sun amince da dalilin zuwansa a bashi kayadadden lokaci idan kuma lokaci yayi ya fice
ko ya yabawa aya zakinta
.
Direba ya dauke hanya yaki shiga dani cikin birnin ya zarce dani wani gari a bayan telaviv JAFFA
inda larabawa ne suke zaune a cikinsa
.

Dana nemi dalili yace wai ba bashi iznin kaini cikin birnin tel-aviv ba “doka ta hana shiga da bako
sai da izni na musamman”
.
dana ji haka nace ya kaini otal mai saukin kudi ba wai don babu kudi isassu ne aguna ba , ina da
kudi masu yawa wanda na samu daga wajen kaosar dalar amurka cinkus a jakata kuma duk binciken
da akayimin ba wanda ya damu da kudina ina dauke da “america express card” don gudun sata ko
shiga halin kaka ni kayi naso zama a otal mau saukin kudine don na samu cudanya da talakawa da
sauran mutanen da ake samun labarai barkatai a gunsu
.
Sabo da yar gogayyar dana samu a aikin jarida , na lura mutane masu kudi ko fada aji basu cika
fadar labaran rayuwansu ba, ko abinda jama’a suke da sha’awa akansa na halin zamantakewa ko
halin musgunawa daga hukuma , su kullum suna boye labaransu suna kuma kaffa kaffa da abinda
zasu fada a ko’ina suke, sannan kuma hukuma bata cika musguna musu ba, don haka basa sukarta ,
Bihasali ma ra’ayinsu shine ra’ayin hukuma amma ta zama cikin talakwa kuma larabawa zai kai ni
na samu na kai ga bin da na zo nema ba tare da katsalandan din jami’an tsaro ba
Matsala ta itace wannan dan rakiyar dole nasan yadda nayi na yarda shi cikin dabara
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Tafiyar kamar mil shida daga tel-aviv muka yi kwana zuwa dan gari mai girma da ake kira jaffa,
abubuwan danagani sun bani mamaki kwarai , gidajen larabwa falasdinawa wasu sun rushe wasu
kuwa sun dade da zama kango, wasu kuma ga suna ,rabi a rushe rabo a tsaye , babu wani gyara
kamar wani sansanin bayi ,
Jami’an tsaro da suke safa da marwa sun maida garin kamar garin da aka fafatawani yaki
.
Abinda zaka fara fahimta shien talauci yayiwa mutanen farin kanta na tambayi direba dalilin da
gidajen wasu suke a rushe “basu da iznin gyara gidaje” ya fada mini
.
Wannan amsar ta bani mamaki mutum da gidansa wai sai ya sami iznin gyarasa, zan sake tambayar
naga dan rakiyata yana kallona sai kawai na kanne dana tuna da maganar mr doyin , muna dada
ratsa garin jami’an tsaro suna kara yawa suna tsaida abin hawa suna bincikawa suna buda kaya
sannan su caje mutum tsaf
.
Da kayi wata gardama sai su kama mutum su garkame shi acikin wata shiga ba biya.
Wannan abubuwan din bani mamaki da tsoro da haushi alokaci guda, domin wannan babu wata
maraba da mai mutane fursononi a garinsu ko daurin talala mai kamar sake
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Mun isa babbar kasuwar garin karfe biyu da rabi na yamma munje don nayi saye saye sannan ya
wuce dani gidan saukar baki
Tun kafin na fito daga motar naga matan larabawa suna saye da sayarwa cikin fara’a wasu suna sai
da kayan marmari da yayan itace .
.
Alokacin guda kuma wani abu ya bata mini rai matasa sanye da wandon kaki rin na soja da fara
singileti sanye da wata hula yar karama mai kama da yar madina shudaye mai ratsin fari suna rike
da mashigan suna bi layi layi , rumfa rumfa kamar duba gari kasancewar su agun sun mai da
kasuwar kamar kurkuku
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Can na hango wata katuwar rumfan sai da kayan mar mari iri iri kamar su tuffa lemon tsami dana
zaki kala kala, akwai dabino da inibi kala kala da sauran yayan itatuwa ,yawuna ya guda don haka
na dauko jakata na rataya na doshi rumfar “ina kuma zaka” direban ya tambayeni ” zan sayo kayan
marmari a wancan rumfar” na maida masau
.

Nayi sallama a kofar rumfar wata balarabiya sanye da dogon siket har kasa ta sanya riga mai dogon
hannu ta yafa mayafi kato ya rufe tun daga kanta zuwa kaurinta tana fara’a ta tareni “ahlan
wasahlan” tayi min nuni dana shigo ciki”marhababika ya akhi”
Ta nuna min kujera na zauna ina shiga kanshin yayan itatuwa suka bigi hancina sha’awa ta
motsa ,kanshin ni’ima na kayayyakin marmari ya kaure rumfar
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Cikin fara’a ta tambayeni sunana da kasar dana fito na gaya mata ni dan najeriya ne sai kawai cikin
sauri ta bani ruwan sha ta jinjina min “nayi farin ciki da ganinka saboda dan uwana yana kasuwanci
acan ” ta fada cikin larabci
.
Sannan ta dauko jakar saye syae ta cika mini da kayan marmari ina kokarin ciro kudi na biyata ta
riken hannu tace “kyauta na baka dan uwa na, saboda ina son musulmin Nageriya “
Na gode mata na gaigaisa da sauran mutanen da ke rumfar na fito kofar rumfar ta biyoni “ina ne
masaukinka kwana nawa zaka yi ” na bude baki zan bata amsa kenan sai wata kara mai karfi da
fashewa ta abku, wuta da hayaki a lokaci guda suka watsu cikin sauri na saki ledar da ke hannunsa
na watsar da jakata na rumbace ta muka zube a kasa , nayi haka don gudun kada tararratsi
n bomb ya
same ta
.
TOH FA DAN JARIDA YA FADA HATSARI
Daga shuraih usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 4
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Daga kowacce kusurwar kasuwar sai mutane ne ke runtumawa a guje , daga nan kuma sai harbi da
bindigogi masu sarrafa kansu ya biyo baya abin da yakara yamutsa gun kasuwar ta yamutse ,
.
Hayaki ya turnuke sama kura ta tashi hargowa ta cika ko’ina mutane da gudu suna tsallake
rumfunansu ko rufe su basu yi ba wasu sunyi karfin hali sun tsaya rufe kofofinsu
.
Cikin sauri na samu naja jiki na rakube a jikin gyaren rumfar ita ma tayo ciki, cikin sauri muka rufe
kofar ta matse matsen kofar na samu wata yar kafa data bani daman kallon abun da yake faruwa
acikin kasuwar
.
Matasar dana gani suna kaiwa da komowa a cikin kasuwar rike da bindigogi suna harbin mutane na
tabbata falasdinawa suke harbewa
.
Cikin mintina biyar kasuwar ta yaye ba kowa sai jami’an tsaron yahudu suna zirga zirga wasu a kasa
wasu acikin landorobobi
.
Suka shiga kama wanda aka harbe suna jefawa acikin motocinsu wasu kuma suna bin falasdinawa
da gudu suna kamasu izan sunyi gardama sai su harbesu wasu kuma suna kofofin rumfunansu suna
kamo mutanen da suke ciki wannan yasa na gane dalilin dayasa wasu suke guduwa daga
rumfunansu
.

Matan ta mike ta janye katakon da ake leken waje nan da nan ta rude ganin suna ta jifgar mutanen
da suka kama , na lura da inda motarmu ta tsaya ba komai sai karikiceta dai-dai da direbanmu cikin
jini, hannunsa ya cire idonsa ya fita sai kafarsa ce take dan motsawa ganin wannan ya tayar min da
hankali sosai bansan lokacin dana fara kyarma ba zufa na keto mani , “wai da ban fito sayen lemo
ba da yanzu bani ” nace a raina
.
Motar asibiti tazo tana jiniya tazo ta kwashe gawarwakin mutane ban san kowane bane , akwai
wasu mutum hudu da suka rasa sassan jikinsu motar janwai motocin da bomb yayi kaca kaca da su .
.
Ko mintina goma sha biyar ba ai ba an kwashe gawarwakin an janye mushen motocin an wanke
jinin . Wama ya nuna cewa lallai yahudawa sun shirya da irin wannan ranar sosai kuma basa son
kowa yasan irin barnar da suke
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
.
Ina shirin cewa ta bude kofar ganin kura ta lafa sai naji hayaniya da kawar mutane sai na hango
mutumin da muka shigo mota tare ya shiga motar jami’an tsaro ya tafi da fari nayi mamaki amma
dana tuna akasar yahudawa nake ko ince kasar da su ka kwace da karfin tsiya banyi wani mamaki
ba
.
Alokacin da motar shiga-ba-biya take shirin ficewa daga kasuwar a lokacin hayaniyar jama’a ta
karaso cikin kasuwar wasu matasa a guje suna kabbara suna jifansu da duwatsu suna tunkararsu,
.
Batare da ko bindiga ba kowani kwakkwaran makami ba , ganin haka ban sana lokacin dana
wangame kofar ba na fito don na kashe kwarkwatar idona ba
.
Rannan naga ikon Allah matasan falasdinawa suka taho gadan gadan ba wani tsoro ko fargaba a
guje a daya barin soja da yan sandan izra’ila cikin sauri suka dinga dirgowa daga cikin motocinsu
wsu suka durkusa wasu suka sunkuya wasu kuwa suna harbi suna gudu da haka suka tarbi
falasdinawa masu jefa da duwatsu kamar soja yayi karo da abokin gabarsa soja afilin daga [shuraih
usman inkiya shuraih 99% ke magana]
,
Mamaki da al’ajabi ya kamani ,ina mamakin yaya soja da muggan bindigogi zai harbi farar hula da
bashi da makami, alokaci guda kuma ina al’ajabin yadda akayi mutum ba komai a hannunsa ya
tunkari mai bindiga ,
.
Aka ja daga daya barin karar bindiga daga daya barin kuma kabbara gurin ya kaure
.an shafe sama da mintina ashirin ana dauki ba dadi falasdinawa suyi kora soja da bindiga kaga ya
ruga da gudu har yana fadiwa, in anjima kuma kaga falasdinawa suna gudu abin kamar al’mara ,
.
An harbi falasdinawa da yawa an jikkata wasu wani abu daya bani mamaki shine duk wanda aka
harba yana faduwa na bayansa zai zo da gudu ya daukeshi
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
.
Sannan kuma wani nan take zai maye gurinsa, don haka babu wata gawa ko masu rauni da sojan
yahudawa suka kama
.
Ana cikin haka sai wasu falasdinawa suka hau saman rumfunan suna kabbara , suna jifansu da
duwatsu wasu kuma suka biyo ta bayansu ganin za’a yi musu kofar rago sai suka jefar da wadanda
aka kama suka tsere a guje n nan da nan kasuwar ta rude da kabbara da sowar falasdinawa suka
mamayeta
.

Wannan shine abu na farko daya bani mamaki a saukata a cikin falasdinu . Na kirata falasdinu
saboda shine sunan halal ba izra’ila ba kamar yadda yahudawa yan kaka gida suke kiranta
.[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Tambayar da nake yiwa kaina kuma na rasa amsar ta shine wane abu ne ya ingiza mutum ba
makami ya kori mai bindiga har ya gudu yana faduwa yana barin bindigarsa
.
Me ya baiwa falasdinawa karfin guiwa har suka fuskanci yahudawa rike da bindigogi duk da sun
san cewa harbesu zasuyi ga kuma sheda agansu sunga an kashe da damansu,
.
Sannan kuma wane daliline yasa mutum yana gani an harbe dan uwansa zai tsallake gawarsa ya
shige gaba ya kuma tabbata shima harbeshi za’ayi sannan kuma me yasa suke dauke gawan wanda
aka harbe
.
Wannan tambayoyin da wasu irin kamar son jin dalilin da ko’ina aka saka jami’an tsaro suna gadin
dauka cin garin kamar anci garin da yaki kuma na ajin tsoron kwace shi koda wane lokaci, me yasa
aka tsaurara matakan tsaro bayan kuwa su falasdinawa ba su da makamai da zasu iya yaki da
yahudawa,
.
Kai kona kare kai basu dashi sannan wata kuma me yasa duk matakan tsaron nan ba su hana
falasdinawa yunkuri da yin bore a kasuwa ba ?
.[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Hakika wadannan tambayoyi ne da suke bukaar amsa wanda duk wani dan jarida mai kishin aikinsa
zai so ya gane bakin zaren abin da na kuduri niyya kennan duk kuwa da cewa ba neman labari na zo
ba , na zo ne neman yar uwar NAGIS don na bata sarkar wuyanta to amma yaya za ace ni HADI
dana shiga cikin runtsi a bosniya lokacin da ban san komai ba a dabarun yaki, yaki ta rutsa da ni na
fito lafiya cikin ikon Alla
.
Sannan ga wata dama ta samu ta aikin jarida na hakika na kiyin wani abu sam-sam ba zan iya
hakuri ba idan kuwa na hakura ban bincika na , to ba sunana hadi hantsi leka gidan kowa ba, neman
labari ya zame mini jini da tsoka don haka naji ba zan iya barin wannan damar rubuta halin kunci da
kuntatawa da yan uwana musulmin falasdinu suke ciki ba.
.
Wannan shiya sauya mini makasudin tafiyata, shu’urin aikin jarida ya motsa sai dai kuma na san
cewa nan fa ba a maraba da yan jarida domin yahudawa sun san tasirin yada labarin abun da suke
aikatawa, don haka basa yiwa yan jarida da suke aiki bil hakki da wasa , saboda basa son duniya taji
labarin irin danne hakkin dan adam din da sukeyi .
.
Kawai sai na gabana ya fadi ras dana tuna da gargadin mr. Doyin
.
Har kullum dai nine Shuraih Usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 5
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Na bude kofa zani wajen da aka fafata matar nan ta riken hannu ” kai bako ne kada kaje su kamaka
bari in rufe muje gida in saukeka” ta fada mini sunanta “ismi zulaikha” ta fara hada kayanta cikin

sauri “motar ku aka sawa wa bomb ko” ta tambaya tana kallona na gyada kai sauran mutanen da
suke cikin rumfar kowa yayi ta kansa
.
Ta shige gaba ina bunta muna gudu-gudu sauri sauri ta kurda can ta kurda nan . Da haka muka fice
daga kasuwar jami’an tsaro suna yiwa kasuwar tsinke , tafiya mai dan nisa ta kai
mu wani dan gida
a cikin rukunin wasu jerin gidajen talakawa, duk unguwar larabawa ne acikinta idana kaga
bayahude toh babu shakka jami’an tsaro ne babu ja wai kare ga mutu a saura , sai da cikin unuguwar
babu jami’an tsaro a ciki sosai
.
Tayi sallama ta kwankwasa kodar wani karamin gida bayan yan mintina wata yarinya doguwa
budurwa mai matsakaicin kauri ta bude kofar, gashin kanta har kirjinta tana da fararen idanu kamar
madara a koko ga dogon karan hanci har baka , tana da siraran lebba da yalwar gashin gira
shekarunta zasu kai goma sha bakwai ko sha takwas , muna hada ido ta rufe kanta da mayafi.
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
A hankali ta bude kofar ta karbi kayan zulaikha sannan ta kalleni tayi min barka da zuwa kuma ya
karbi jakata muka shiga dakin saukar baki, shine na farko da cikin gidan daga hannun dama ta bude
kofar tace na shiga na zauna a cikin akwai kujeru guda uku tsofaffi da dan karamin teburin shan
shayi, sai kananan kofuna na shan shayi a gefe guda na wani gadon katako tsoho.
.
Na zauna kenan yarinyar ta shigo da butar shayi ta daureye kofunan dake kan teburin ta zuba min
shayi ta fice tana tafiya cikin nutsuwa, sannan ta shigo da yayan itatuwa irir iri da ruwan sha ta
fita,shayin dana sha ya sana ji karfina ya dawo na kuma wartsake yayan itacen da sha sun gusar min
da yunwa
.
Ni dinne dai Shuraih 99% ke typing
.
Alokacin ne na nutsu sosai na shiga hayyacina na dauke takarda na tsara abubuwan daki daki,
wannan al’adace a gareni duk sanda zanfara wani aiki sai na zauna a tsanake na tsara komai dalla
dalla , saboda kashin bayan cin nasara a kowace irin harka ta duniya kota lahira shine kyakkyawan
tsari, da shiri mai inaganci ,
.
Domin kuwa duk wanda bai tsara al’amarunsa ba to kuwa ya dauki matakin ruda kansa.
.
Abu na farko shine lokacin dana ke da shi kankane ne ,kuma abin da yake gabana yana da yawa, ga
kuma wahala ba kamar yadda ba zata ba, yadda jami’an tsaro suke ta safa da marwa babu wani
yanci walwala, ga tashin hankali iri iri ga harsashi na yawo.
.
Akwai hatsarin na shiga neman yar uwar nagis kai tsaye don ban san matsayinta ba agun jami’an
tsaro ko taba cikin wadanda ake nema ruwa a jallo ,sannan jin cewa ina nemanta kuma na taso tun
daga sarrayebo, wannan zai bada haske ga jami’an tsaro su tasani a gaba don su halakamu gaba
daya,
.
Sannan kuma ban san waye jami’an tsaro waye da leken asiri ba, sannan na tuna da wanda muke
tafiya tare na tabbata dan leken asiri ne , nayi hamdala da Allah ya raba mu cikin sauki
.
Nagode nine dai Shuraih 99%
.
Babban abinda yake damuna nake son kuma sanin bakin zaren shine dalilin da falasdinawa suke
cikin wannan kunci da takura, koma meye harzukasu, suke dauki ba dadi da su haka, Na tsara
komai cikin dabara da yadda zan sami amsoshin wadannan tambayoyi ba tare da wani jami’in tsaro

ya sansano wani abu ba, kuma ba tare da mai bani labarin yasan cewa yana fadamini wani
muhimmin abu labari ba,
.
Zan lullube komai da sunan ni dan yawon bude ido ne da san jin tarihi ne wannan abu ne mai sauki
wajaen kwararren dan jarida musamman idan ya samu kansa cikin hatsari, Amma ba abu ne mai
sauki ba Izra’ila
.
Kuna tare ne dai da Shuraih 99%
.
Zulaikha ta shigo tare da wani saurayi da wannan yarinyar suka zauna”wannan yayana ne ” tace
“sunansa Abduljalil shine wanta ita ana kiranta zakiyya shi yana karatu a jami’ar jaffa , ita daliba ce
a kwalejin yan mata ta jaffa
.
Bayan shirin yan mintuna sai na jeho musu tambaya cikin dabara “ko kun san labarin sarkin
Ramalla na karshe?”
Na zuba musu ido , wannan ne karo na farko dana fara aikin daya kawoni, ya kalleni sosai yasa
hannunsa a aljihun kirjinsa ya fito da kwalin taba ya kasta ashana sai zakiyya ta fice waje “ban san
labarinsa ba” ya gumtsu hayaki ya fesar “wani tsoho abokin babanmu yasan komai na labarin
falasdinu kafin a mamayeta da bayan an mamayeta da irin yake yaken da akayi tun kafin a haifemu,
duk sanda nake da wani aiki daya shafi tarihi shi nake ziyarta ya bayyana mini komai” ya dube ni ya
kalleni mahaifiyarsa ” idan bazaka damu ba dana hada ka da shi mutum ne mai son bakon da yake
son sanin tarihinmu zai gamtsar da kai da duk wani bayani da kake bukata”
.
Shuraih 99% ke cewa
.
Nayi murna da jin haka don haka nace ” muje na ganshi mana yanzu “ya dubeni yayi murmuishi
“Ba a nan garin yake ba sai gobe zan kaika wajensa a nablus ne ” na duba agogona naga lokacin da
nake dashi bashi da yawa “ina son ganinsa yau don sauri nake akwai wani uzuri da nake da shi”
Ya kada kafadarsa ” banda hali zuwa nablus a yau , ina son zuwa jami’an ina da jarabawa kuma
kafin agama dare yayi, kasan nan ba’abari ayi tafiya da daddare daga wani gari zuwa wani garin ,
karfe shida zuwa bakwai na dare dole kowa ya koma garin da yake da zama ko ya fuskanci tuhuma
.
Shigewar zakiyya da farantin abinci ta ajiye a agabana tafice ” zan biyo ka jami’ar nace masa bayan
da yayi mini bismillah
.
Jami’ar jaffa tana daya daga jami’ar da larabawa suka gina suke gudanar da ita da harkokinta, akwai
falasdinawa da yawa suna karatu wasu kuma suna koyarwa,
Haka zalika akwai yahudawa har ma da turawa dalibai da malamai
.
Hukumar yahudawa ce ke lura da tsara tsaren makarantan da manhaja da ake amfani da ita , tana da
shashen karatu mai zurfi akan ilimin kimiyya da aikin likita, tarihin da aikin injiniya
.
Abduljalil yana koyan aikin likita yana da sekara ta biyu muna shiga ya shiga aji bayan ya kaini
dakin karati, ina shiga na dukufa binciken littatafai, da kasidun tarihi daban daban akan kasar
izra’ila amm banga abin da nake son gani ba , labarai ne wanda ko agida najeriya na iya samu, sai
dan abin da ba a rasa ba,
.
Wanda ya karamin haske akan binciken dana ke son yi
Kuna dai tare ne da shuraih 99%
.
Bayan ya gama yazo muka fita zuwa gida a tahowar mu mun shafe kasa da mintuna goma sha
biyar , amma akan hanyar komowa mun shafe sama da mintuna arba’in saboda cunkoson da jerin

gwanon abun hawa “me ya kawo wannan Jerin gwanon” na tambayeshi “abduljalil yace “larabawa
da yawa suna aikin leburanci a da sauran aikin karfi a tel-aviv da saura garuruwa na yahudawa da
suka mamayee in sun kwana a gidajensu da sassafee kuma su sake neman iznin shiga garuruwan
domin neman abun da zasu ci, wannan yasa duk safiyar Allah da kuma La’asar hanyoyi suke cika
makil da abin hawa saboda kowa yana kokarin zuwa gida kar lokacin fara tare mutanee yayi
.
Nayi shiru kawai ina kallon jama’a a cikin dogayen motocin bas da sauran ababan hawa makare da
mutane ,
.
Yauwa anan zan tsaya na dan huta sai mun hadu a page 6
.
Dan Allah ku saka ni acikin Addu’anku
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 6
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[Shuraih 99% nake cewa daku]
.
Toh jama’a sai daikuyi hakuri don kuwa fallayen littafin sun babbale, a saboda hakanne zamu danyi
tsallake ,
.
Amurka da sauran kasashen turai sun tara musu dimbin makaman yaki na zamani wasu ma ba’a taba
jarabasu ba sai a lokacin, yahudawa suna da cikakkiyar masanaiya game da duk wani motsi da
sojojin larabawa sukeyi , domin suna samun bayanan sirri kai tsaye daga ma’aikatar tsaro ta amurka
kada ka manta kuma shugabannin wasu kasashen labarawa munafikaine
.
“Wannan nasarar ta basu daman waftar kasashen larabawa, don haka min sake fafatawa da su
ashekarar 1967, wannan shine yakin kwana shida, kwanan bakin ciki”
Abuja’afar yayi shiru banyi wani kokarin tambayarsa ba don na lura fuskarsa ta sauya idanunsa sun
kada sun yi jawur don haka na lura abin daya ke son fada ne yake masa ciwo matuka zuwa can sai
hawaye ya dinga tsattsafowa daga idanu
nsa yana bin kumatunsa a hankali
.
Ni dinne dai shuraih 99%
.
Cikin murya mai rauni tana rawa cike da sauti mai ban tausayi ya labarta mini labarin yakin kwana
shida ” yakin kwana shida yakine yakine da larabawa ba zasu taba mantawa da shi ba har abada,
domin kuwa mun tozarta acikin kwana shida mun kaskanta mun ga wulakanci , munyi asaran
filayen mu, an kashe mana mata da yaya iyalai masu yawa bazasu sake gaini juna ba.
.
Domin iyalai da yawa an watsasu acikin duniya suna yi gudun hijra cikin kaskanci da yawa sun
halaka matayenmu da yawa sun ga wulakancin da basu taba zata ba domin kuwa an yiwa da
damansu fyade,
.
Yi tunani a ranka cewa matar da bata taba fita waje ba ko kuma wacce wani namiji bai taba ganin
fuskarta ba , balle kirjinta, rana daya ta samu kanta cikin fasikai sui mata tsirara suna lalata da ita a
gaban ya yanta ko danginta , sannan a yasar da ita a filin Allah bako sutura,
.

Tuna yaya zakaji izan matarka ko yarka ko mahaifiyarka ce a kayi wa a gabanka, abubuwa munana
mafi muni kuma awannan yakin ne yahudu ya kwace kudus gaba daya har masallacin al’aksa
.
Kai gaskiya na tausayawa larabawa, ehm Shuraih 99%
.
Amurka ta gina rundunar sojan izra’ila ta kuma sabunta kayan yaki ta da na zamani mafi inganci,
tun a shekaar 1948 duk shekara suna wasu wasu makudan kudade na musamman da suna
“development Aid” da kuma “military Aid” domin gina kasar da rundunar sojanta, suna kuma ba su
kayan yaki wanda basa sayarwa kowacce kasa irinsa
.
Sannan suna ba sojansu horo na musamman ga kuma bayana da rahotanni na sirrin na watan dan
adam
.
“Kwatsam izra’ila ta farwa kasashen larabawa don cimma burinta na kafa izra’ila babba , acikin
kwanaki shida akayi mummunar fafatawa a tsakanin larabawa masu tarin kayan fada marassa
inganci ga sojoji mara kwarewa cikin kankanin lokaci suka yi mana kaca kaca, sojojin mu suka
zubar da kayan yakinsu su suka gudu, suka bar mu da abun fada ana dariya
.
Izra’ila ta mamaye lardin sinai mai tarihi na kasar masar, sun mamaye rabin jodan wanda ya hada da
gabanshin gabar kogin jodan sun wafci wani bangare na kasar siriya bayan anyi kazamin yaki a
tuddan golan
.
Nidinne dai shuraih Usman inkiya shuraih 99%
Sun mamaye ilahirin ZIRI GAZA da sauran gabar kogin jodan (west bank) sun kuma kame
daukacin darussalam (jerusalam) suka kwace masallacin kudus suka keta alfarmar masallacin suka
kashe daukacin mata da yaran da tsofaffin da suka fake a cikinsa jini ya malala cikinsa kamar ruwa,
suka kuma sake kwace wani bangare na kasar larabawa
.
“Acikin kwana shida sun yiwa larabawa wulakancin da ba a taba yi musu ba , tun bayan zuwan
Annabi muhammaduu (SAW) mun ga tasku da wulakanci iri iri a hannun yahudawa har ta kai mun
rasa inda zamu sa kanmu an kashe mata iyaye an yi lalata da yan mata , an kakkaraya mana matasa
an zuba su a rami an rufesu da ransu, matayenmu,yayanmu a gabanmu akayi musu fyade, an
wasashe dukiyarmu an kone an kuma rusa mana gidaje an mayar da mu yan gudun hijra a cikin
kasarmu, Ta gado
Shuraih 99% ne din dai
.
Falasdinawa da yawa sun watsu a duniya da sauran kasashen larabawa suna shan wulakanci iyalai
da yawa sun halaka, iyaye basu sain inda yayansu suke ba , dangi sun warwatse yanzu akwai akwai
faladinawa yan gudun hijra sama da milyan daya a cikin duniya basa ko tunanin dawowa kasarsu ta
gado sai dai a mafarki……
.
Abduljalil ya fashe da kuka yana fadin babana ko yana ia oho..”
Can kuma sai ya dinga fadin wallahi zamu rama sai mun dauko fansa komai dadewa sai mun kwace
kudus ko duk zamu kare”
.
Na lura duk ya sake jikinsa yana tsuma yana karkarwa, bayan ya nutsu abuja’afar yaci gaba
.
“Yakin kwana shida yasa larabawa sun farka sun shiga cikin hankalinsu sosai sun san kuma duniya
ta canja, sun gane cewa ba wani shirin daukan fansa da dawo da martabarsu a idon dunia.
.
Ashekarar 1973″ cikin kukan abujafar muryarsa a karye yadan saurara sannan yaci gaba “kasahen
laraba sun nunawa duniya sun dauki darasin abubuwan da suka fari sannan an kuma samu sabbin

shugabannin masu jini a jika masu kishin larabawa, wadanda sukayi aiki tukuru sukayi shiri na
musamman acikin watan azumin wannan shekarar yakin da ake kira “yakin october” ya faru
.
Yahudawa suna da wata rana da suke kira “yom kippur” a wannan ranar basa aikin komai hatta
jiragen sama basa tashi ko sauka balle wani aiki , muna zaune a unguwanmu dan ba damar shiga
garuruwan yahudawa ranar hutu
.
“Na bude rediyo sai naji anacewa “meat pie” sea wolf and woll stringl wannan kalmomin sojane na
siddabaru ana kiran sojan kota kwana da su dawo bariki cikin sauri”
.
Cikin sauri na katseshi “ya akayi ka gane kiran soja akayi musamman da kace kalmomin siddabaru
“code word” na lura abduljalil bai ji dadi dana katseshi ba “nasan hakane saboda na shiga wata
kungiyar karkashin kasa ta fada da manufofin izra’ila na mamaye palasdinu kuma ina aikawa da
labarin sirri ga wasu kungiyoyin leken asiri don haka na san wannan dama wasu kuma wasu bayan
da za fada maka a gaba na sansu ta irin wannan hanya ina fatan ba zaka tambayeni hanyoyin dana bi
na sani ba,
.
Da kuma hanyar dana kebi na sanar da nawa bayanan asiran” nayi shiru bance masa komai ba.
.
“Bayan wannan sai muka ga motocin sojoji cike da sojoji da kayan yaki sun doshi bakin iyakokin
da suka shatawa kansu, misalin goma na safe manyan rundunonin sojan izra’ila ssu dinga motsawa
bakin daga cikin sauri,
.
Jirafe saman yakinsu suka dinga shawagi kasa kasa a cikin gari ko’ina daga nan kuma sai muka ji
muryan firmiyan lokacin “golda meir” a redio tana cewa “bama wata tantama game da nasararmu,
an yiwa abokan gaba mummunar barna” daga nan kuma muryar dan ta’adda moshe dayan yana
cewa “larabawa ba zasu ci moriyar wannan yakin ba kafin a tsagaita wuta, kuma mutane birnin telaviv zasu samu suyi barci sosai”
.
Rugogin jiragen saman yaki yasa mutane gudu cikin gidajensu abin daya sabawa al’adar “yom
kippur” ranar hutu da zaman jagwab, ta koma ranar yaki zazzafa,
.
Ranar da yahudu ba zai manta da ita ba domin a wannan rana sun dandana kudarsu, tunanin da suke
nacin nasara cikin sauki ya koma kokarin kwatar kai ta kowane hali.
.
Yauwa hakann na keso shuraih 99% ke magana
.
“Ayakin ramadan ko yom kippur ko black october”
Kamar yadda yahudawa suke kiransa an gwabza shi sosai anyi gumurzu kuma kazamin yaki mafi
muni a taihi yakin zamani tun yakin duniya na biyu anyi kazamin gumurzu a guraree guda biyu da
yakin sinai da daya kewaye na tudda golan
.
“Kasar masar sanadiyar kwace mata sinai tayi shiri sosai sai a kewayen sinai, ta sawo kayan yaki
sabbi daga kasar rasha, wanda ya hada makamai masu linzami samfari sam 6, sam 3 da sam 2 da
rokoki da bindigogi kakkabo jiragen sama na zamani,
.
Sun hada da garkuwan sararin samaniyar mai sarkakiyar a yakin sa sinan , sun tara tankoki masu
inganci da saukin sarrafawa a cikin hamada da sauran bindigogin atilare na zamani masu amfani da
na’urar mai kwakwalwa.
.
Wanda kwamandojin kasan rasha suka hada masu

.
.
HMM LALLAI ZA’AFAFATA KAZAMIN YAKI
.
Kafin nan dai nine Shuraih Usman
Inkiya shuraih 99%
Nake cewa daku muhadu a page 7
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 7
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
Cikin dare wasu kwale kwale dauke da masu nutsu suka haura gabar ta suwiz (suez canal) suka dasa
nakiyoyi a bangaren izra’ila ,cikin sauri a lokacin da sojan izra’ila suka motsa nakiyoyin suka tashi
suka watse ramikan karkashin kasa na boyar soja
.
Hayaki ya turnuke kura tayi sama,kafin kura ta lafa sojojin tanka sun haura da tankoki sama da uku
ta kwalekwa
len katakon da suka hada su saki wuta armuka ginin karkashin kasan maboyar soja da
kayan yakinsu , gurin ya hautsine wuta ta kama , gine-gine da sauran tantunan sojoji suka kone
kurmus
.
Sojojin da suka taso don hana sojan misira haurawa cikin kankanin lokaci aka gama da suwajen
guda dari sukayi saranda, sauran aka kashe su, daga nan larabawa suka yiwo kora, suka kame
sansanin mai girma a yankin.
.[Kada ku sha’afa ni dinne dai Shuraih 99%]
Ta amfani da gurnati da yollar wutar aka kone yahudawa da kayan yakinsu. Kafin yammar wannan
ranar jiragen yaki masu saukar ungulu suka yi ta jigilar sojoji da kayan yakinsu.
.
Sojan kasa dauke da makaman atilare suka mamaye yankin sinar sun keta sinar ta wajeje biyar
sukayi kaca kaca da sojan izra’ila suka lalata barakokinsu da kauyukan yahudawa , sun kama da
yawa a masayin fursunoni, wajejen da suka fi barna mai yawa shine bakin gabar fu’ad da ismailliya
an yiwa izra’ila barna mai yawa a Qatara
.
Sojan misira sunyi kokarin haurawa da jiragen saukar ungulu a Ras da sudr, sunyi asarar jirage
goma kuma kowanne yana dauke da mutum 30 zuwa 40, kwamandoji sun yi kokarin katse hanyar
samun kayan sojan izra’ila amma basuyi nasara ba sun harbo jiragen izra’ila sama da arba’in 40 sun
yi asara nasu sama da goma,
.
Yahudawa sun lugudan wuta Shuraih Usman inkiya shuraih 99% mai tsanani ta sama da tankoki,
Amma bai yi tasiri ba
.
Rundunar sojan izra’ila tayi kokarin karya sojan misira Amma duk shirinsu ya zama a abanza
jiragen yakinsu , abin da suke mana zarra, sun gamu da garkuwar makamai masu linzami wadanda
ake harba su daga kasa “surface to air missile” duk jirgin daya shigo cikin yakin sinai sai yayi karo
da mizal ko Roka ya kone,
.
Ko bindigogin harbo jiragen sama ,jiragen amurka kirar phantom da hawk da sauran jiragen masu
saukar ungulu sun sha lugudan wuta da ruwan mizayal da rokoki, ko ina ka duba a sama sai kaga

jirage na faduwa kasa suna ci da wuta , wasu kuwa a sama zasuyi bindiga su watse hayaki ya cika
sama kaman gajimare mizayal sam 6 yana harbo duk jirgin daya tashi sama sosai kamar kafa 40,000
a sama wanda yayi kasa kasa domin yin bomb akan tankoki zai ci karo da sam 3 ko sam 2 wanda
aka saita su don harbo jiragen da yake kasa kasa
Shuraih usman 99%
.
Tarun ayarin tankokin yakin da izra’ila ta turo a yakin sinai sun sha wuta sun yi dai dai suka watse a
cikin hamada suna cin wuta, saboda sun gamu da sabon makamin kone tanka, don haka tarun
tankoki sama da dari hudu basuyi komai ba
.
Illa zama kaskon suya yahudawa, tilas sojan suka fita daga tankokinsu suna jifa da makamansu da
hulunan kwanansu suna zubawa aguje suna ihu
Wasu sun bace a hamada wasu sun haukace wasu sun kurmance ko’ina takalma da hulunan da belt
da bindigogi kirar amurka zaka gani birjik
.
Sojan kasar siriya sun kai farmaki daga barin gabas takan tudun golan sun share sojojin izra’ila
acikin AWA 48 suka danna har wasu kauyuka sun kone gevel kibbuts da heamek.
.
Wayewar gari jiragen izra’ila sun kai hari kan garuruwan fararan hula sun kone gidaje da asibitoci
da makarantu sama da mutum 1000 sun mutu a rummaneh.
.
“Mummunan yakin atilare da tankokin yaki ya fara da misalin karfe biyu na yamma bayan da suka
sha kashi a shuraih Usman inkiya 99%
Hannun siriya, tankoki samfurin cneturions da patton suka dirkako zuwa tuddun golan nan suka yi
karo da tankokin siriya aka gwabza yakin tanka mafi muni da tsanani a tarihi
.
Hayaki da wuta ko’ina ga rugugin bom da manyan harsasai da inji tanka kawai zaisa kunnen mutum
ya kurmance, anyi kare jini biri jini ko’ina karekican konannun tankoki da gawarwakine suke yashe
kamar kasa
.
Can kuma jiragen saman amurka na phantom suka dinga ruwan boma bamai kamar ruwan sama
akan tankokin siriya sun yi lugudan wuta mai tsanani na lokaci mai tsawo,anyi daga sosai mutum da
kansa zai bude tankarsa ya fito ya ruga da gudu, sama wuta kasa wuta tsakiya masifar zafi
.
Kashe gari da taimakon jiragen yakin amurka da bayanan sirri na watan dan adam daga amurka,
izra’ila sunyi raga raga da tankokin siriya sun kuma lalata garkuwar makamai masu linzami da suka
hada jiragen izra’ila suka karya Shuraih Usman inkiya 99% rundunar sojan siriya suka sake kama
tuddan golan an sake fafatawa sosai akan golan sama da tankoki 1500 suka gwabza aka yi kazamin
yakin tanka a tarihi
.
Hakazalika wayewar gari a lardin suwiz sojan izra’ila sunyi nasarar karya sojan misira da suka
hauro cikin hamadar sinai, saboda sun kai tankoki masu yawa , sun kumayi nasarar lalata cibiyar
makamai masu linzami da suka hana jiragensu haurawa.
.
Wannan ya baiwa yahudawa damar raunaa ragowar tankokin da suke hamadar sinai ba tare da wata
kiryar mizayal ba , rashin sabbin tankoki da zasu ci gaba musu da raunatesu.
.
Rundunar sojan izra’ila sun keta garkuwan jiragen saman yaki ta yankin sinai sun lalata rumbunan
rokoki da mizayal da taimakon amurka da kayan yakinta da bayanan sirri na watan dan adaam, sun
lalata cibiyar bada umarni ta makamai masu linzami sam 6 sam 3. Amma haka bai faru ba sai da
amurka ta shiga kai tsaye
.

AMma dai kafin wuta a tsagaita larabawa sun kwato Shuraih Usman inkiya Shuraih 99%. Da dama
daga filayensu da izra’ila ta mamaye a yakin kwana shida 1967. Martabarmu ta dawo a idon duniya,
mu larabawa ba abin da muka tsana face ayi galaba da mu kuma a din ga kallonmu a mutanen
banza,
.
Abin dayasa muka samu nasara bai wuce cewa sojanmu sun samu kyakkyawan horo da ingattattun
kayan yaki na zamani irin wanda izra’ila take tinkaho da shi ba, kuma sojojinmu sun shiga fagen
daga da niyyar ko cin nasara ko su mutu, Amma ba su gudu kamar yadda sukayi a yakin kwana
shida ba, mun nuna wa izra’ila cewa mu ba kanwar lasa bane”
.
Matarsa ta shigo tare da wani mutum suka gaisa ni da abduljalil muka yi sallama da shi bayan nayi
masa godiya mai “nine zan gode maka da ka taho tundaga wata kasa don binciken yadda
rayuwarmu take da halin da muke ciki, ka nunan kana kaunarmu kwarai”
.
Ya saki hannuna nayi masa alkawarin zan dawo muci gaba da shira akan halin da aka jefa
falasdinawa a ciki
.
Har na juya zan tafi sai na tuna da maganar neman gidansu Nagiz nayi masa maganar sarkin ramalla
yace ” sai na dawo ma ci gaba “tayaya zanje gidan ” na tambayeshi
.
“An rushe gidan tuntuni don mu daina tunawa da shi, ba komai yanzu sai fili kawai, amma yana da
‘ya’ya ya mike tsaye ya dauki Shuraih Usman 99% kwagirinsa ya rakoni kofar ya sunkuya kamar zai
sumbace ni ” yana da diya sunan ta Nagis taana da kanwa Ikram dukkaninsu suna cikin kungiyar
hamas, bansan inda nagis take ba yanzu kada kaje nemansu
.
Ba mamaki jami’an tsaro su halakaka don kowacce ana nemanta ruwa ajallo”
Ya dafa ni kamar yana bani shawara sai ya fadi wasu kalmomi da sunan wani layi a cikin ramalla
yace na tambayi wani mutum na fada masa abin daya fada mini “zai taimaka maka kaga daya daga
cikinsu na gaya maka ne don na amince da kai maga alamar kai mujahidi ne”
.
Muka fito da abduljalil ya shiga mota zuwa gida ni na tafi cikin Ramalla
.
.
Anan zan tsaya sai mun hadu bayan kwana biyu
Nine naku akoda yaushe Shuraih Usman
Inkiya 99%
.
Abun dayasa kukaga bana post kullum kuma banayi da yawa shine
Nafi ga ne nayi post kadan mai amfani
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 8
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
ZIRIN GAZA
——————–Na shiga garin ramalla a wa daya bayan rabuwar mu da abduljalil kai tsaye na shige masallaci nayi
sallar azahar bayan sallama limamin masallacin ya mike yayiwa masallata wa’azi yana fadakar da su
abin da yake gabansu na fafatawa da yahudawa

.
“Dole
ne mu sauke nauyin daya hau kanmu dole mu kwato kanmu daga kan gin bautar ‘yan kaka
gida , falasdinu ta falasdinawa ce kuma masallacin kudus na musulmi ne”
.
Kabbara mai karfi tama sallata ta katse shi da aka lafa yaci gaba “duk musulmin duniya ya
haukansu suyi yaki don yantar da masallacin daga hadarin da yake ciki,
.
To amma mune makwabtan masallacin don haka mune zamu fara nuna kin yardarmu , da
bijirewarmu sannan muyi tawaye , mu yi fito na fito mu fafata, mu hautsina da yahudawa don mu
nuna wa sauran musulmin hanya”
.
Aka sake kabbara mai karfi har sau uku, da haka yayi bayani na zaburar da matasan dake cikin
masallacin ya kuma kare da “Allah ya tsinewa masu danne hakkin mutane, ALLAH YA TSINE
WA ‘YAN TA’ADDA” masallacin ya kaure da kabbara yayin da ya ce “ALLAH YA TSINE WA
IZRA’ILA, ALLAH YA TSINEWA AMURKA”
(Nima shuraih 99% nace Allah ya tsinewa yahudu, jama’a kuyi comment da Allah ya tsine masu)
.
Cikin dabara wasu matasa suka sashi a tsakiyarsu suka fice da shi daga masallacin suna kabbara
suna daga hannuwa, wannan lamarin ya farkar dani samun wani kuzari a ruhina, duk da labarin
yakin da abuja’afar ya bani wanda yasa jikina yayi sanyi bakin ciki kuma ya rufeni wannan bayanan
da kuma kumaji da kuzarin da ruhin gwargwarmayar dana gani tare da matasan Ramalla ya bani
kwarin guiwa da farin ciki a raina, domin naga alamun daukan fansa a tare da matasan
.
Kai tsaye na tafi inda akayi min kwatance bayan na gama nazarin gurin a taswirar matafiyata dana
saya na nablus, na sauka daga bus na yi tattaki mai dan nisa , kwatsam sai (shuraih usman inkiya
99% bazan taba daina fadin Allah ya tsinewa Izra’ila ba ) jikina ya bani kamar ana bina cikin
hanzari na waiwaya naga wani mutum dogo dan tsattsama yana sauri yasa bakaken kaya da hula
hana sallah.
.
Ina ganin sa gabana ya fadi na sassauta tafiyata na saurara ya cimmini ya dan bangajeni ya shige
.
Ganin haka sai na koma baya ina isa bakin hanya wata motar limousine mai kofa shida , gilashin
motar bakine yana daukar ido ta tsaya a gabana a hankali, ganin ta tare hanya sai na kauce zan gifta
sai naji wata murya kamar na taba jinta amma na manta inda na taba jinta , nayi kamar ban jiba sai
na sake ji ” may I give you a lift “
.
Muryar mace matashiya mai taushi lokacin na tabbata na taba jin muryar, don haka na waiwaya
sosai na sunkuya don inga mai maganar, ban iya ganin ta ba, sai gabana ya fadi ras, don haka ban
amince na shiga ba naci gaba da tafiyata
.(Shuraih Usman inkiya 99%
Na fara tafiya amma ban san inda zan nufa ba ganin ina kokarin ciro taswira daga aljihuna sai motar
tayo gaba ta cimmin “can I help you” har zance a’a sai kofar motar ta bude wata yarinya ta fito
sanye da siket iya cinya da tabarau baki a idonta tasa takalmi mai tsini rigarta shara shara wacce ta
bayyana dukkan surinta kusan mamanta a waje suke, hannun ta akwai agogon gwal
.
Ta tsaya a gabana tana kanshin turare kana ganinta kaga ba Amurkiya, hakika na san cewa akwai
inda na taba ganinta amma saboda halin da nake ciki na kasa gane ta
“Kai bakone anan ko” tace dani na dubeta
“Ni dan yawon bude idone ” ina gama fada mata nayi kokarin tafiya tayi murmushi
“Ina kake son zuwa ne in kaika “ta duben tayi dariya “kana jin tsorone” jin haka na gaya mata inda
zani
.

Ta girgiza kanta “bana shiga nan akwai hatsari garemu”
Tai mun kwatance na kama hanyar shiga motar tayi gaba har da dago min hannu
.
Na shiga unguwar datai mani kwatance, nayi ta shiga lunguna har nakai ga fadar sarkin ramalla ba
komai sai fili kato an kewayeshi wayar mai kugiya sojoji suna Shuraih Usman inkiya 99% gadin
filin suna dauke da bindigogi masu sarrafa kansu, a gefe daya akwai wata yar rumfar soja an
kewaye filin
.
Ban aune ba sai naga wani soja a gabana rike da wani jifgegen kare mummuna yana haushi sun
tsaya a gabana “no tresspassing mister”
Sojan ya fada cikin fusata na rufawa kaina asiri nayi gaba
.
Na isa masalacin ramalla don nayi sallar la’asar ina sallama ba shida nisa da filin , shine masallacin
sarkin ramalla , baban nagis ne ya gina kafin yahudawa su kasheshi, bayan na idar da salla na
tambaye wani dattijo ko yana da labarin filin can da sojoji suke gadinsa,
.
“Wani yace maka wani abune game dashi” nayi shiru zuwa can nace masa “ni dan yawon bude
idone , ina dai son jinko yana da wani tarihi”
.
Yadubeni sosai “daga wacce kasa kake” cikin sauri nace masa “nazo daga Nijeriya” ya nade
carbinsa “zo na kai ka wajen wanda zai baka labarinsa”
.
Yana gaba ina binsa a baya cikin ladabi muka shiga wani dan karamin gida a cikin wani lungu a
tsakiyar unguwar, muka shiga can kuryar gidan, muka iske wani mutum yana zaune akan wata
darduma mai alfarma irin ta da matasa majiya karfi sun kewayeshi, muka Shuraih Usman inkiya
99%. Gaisa bayan dattijon ya gabatar dani na gaya masa labarina
.
“Ni ina daga cikin ‘yan gidan sarautar Ramalla sunansa abdullahi ya fada mini kai tsaye,
“Wacce sheda za ka nuna mini” na tambayeshi yayi murmushi “wannan sune shaiduna” dattijon
daya kawoni ya katse mu shi dan jinin sarautar gaba na baya”
.
Wannan yasa nayi farin ciki gani ban sha wahalar da na zata zan sha wajen neman kanwar Nagis
don haka cikin zakuwa nace “ina son ganin ‘ya’yan sarkin Ramalla yanzu”
.
Wani matashi a gefe yacee “ba shi da ‘ya’ya” na kalleshi “yana da su mana “na mayar masa . Wani
abu kake da shi muhimmi haka da kake sin ganinsu”
,
Dan gidan sarautar ya fada yana kallona “kwarai kuwa ina son ganin Nagis binta Taziz da
kanwarta” sai nayi kallamar da abuja’afar ya fada mini gaba dayensu suka kura mini ido, can yace
bani da labarin Nagis Shuraih Usman inkiya 99% yanzu na samu labarinta jiya amma ban tabbatar
ba ance dan aike zai zo yayi min bayani
.
Amma kanwarta tana cikin zirin gaza, suna kiranta da sunan bintul jihad a gaya mini layi har da
gidan da zan same ta .
.
Cikin murna da farin ciki na barsu, kamar cewa aka yi gata nan, ashe dala dashi da shiga biirni
bane, nayi sallama ko labarin dalilin girke sojoji a filin ban tambaya ba
.
*** *** ***
Gaza birni ne mai girma yana da fadin kilomita mirrabba’in 350 yana kuma da fadin kilomita 40km,
birni ya fada hannun sojan izra’ila a lokacin yakin kwana shida a shekarar 1967 ,kafin lokacin yana
hannun misra tun daga yakin shekara 1948 har zuwa 1967,

.
noma da kasuwanci shine sana’ar mazauna birnin, akwai mutane wajen miliyan daya mazauna
birnin , sannan akwai unguwannin yahudawa ‘yan kama guri zauna da suka yi kaka gida aduk gurin
da yake da wata ni’ima an yi musu barkoki sojoji suna gadinsu dare da rana cikin shigar yaki
.
Gaza duk sauran garuruwan Shuraih Usman 99% nake da tarin sojoji cikin kayan fada sabodaa
cibiya ce ta tashin hankali
.
Doguwar bas din dana ke cike tayi birki a gaban wani katon shingen binciken shigi da ficen sojoji
da karnuka masu sansanar bom,
.
Da na’urorin sansanar bom sun bin cika gurun akwai matsanancin tsaro agun sosai zaiyi wahala
mutum ya shige da ko allura batare dako na’ura ko karnuka sun ganoshi ba, haka dai muka shige
.
Muna isa cikin garin na fara ganin kayan abinci iri iri da yayan itatuwa baja baja a ko’ina an baza
sana saidawa kamar yadda zakaga shagunan sai da kayan tireda idan ka shigo birnin kano
.
Mutane birjik suna harkokinsu na yauda kullum , sai dai kuma dole mutum ya tsorata idan bakone
kamar ni irin yadda sojan izra’ila da yan sanda da sauran jami’an tsaro suke kaiwa da komowa layi
layi,
.
Matasa kuma suna cikin halin harzuka da shirin fito na fito da jami’an tsaro kamar an yi musu
allurar yaki, kafin na shiga cikin garin Gaza na sha bin cike da caje caje barkatai da tambayoyin
yaya kazo duniya……..
.
Yo ana zan tsaya
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Mamallakin shafin hausaebooks da
Keffians News Teller nake cewa
ALLAH YA TSINE WA IZRA’ILA
Kai/ke ma ku tsine masu
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi daurawa
Littafi na daya 1
Page 9
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
Karfe biyar da rabi na yamma daidai na shiga cikin garin gaza, jami’ar tashin hankali makarantar
koyon gwagwarmaya da daki ba dadi , fagen daga kwami filin yada kanin wani
.
Na duba agogona naji kausar ta fado min arai na yanzu saura sa’o’I goma sha biyu alkawarin da na
yiwa kausar na komawa ya su cika, kuma shine yayi daidai da sauran sa’o’I araba’in da takwas na
lokacin da aka diba mani na zama kasar izra’ila ya kare gashi ban ga kanwar nagis ba
.
Amma nasa araina nan da sa’o’I biyu ko uku komai dare na gama abin da ya kawoni. Gobe na kai
ziyara masallacin kudus na kammala komai na koma sarayebo wajen kausar kafin mako guda na
koma gida najeriya Shuraih Usman inkiya 99% ina tawa Allah na tasa kuma ta Allah ce mai
tabbatar ko ina so ko bana so
.

Alokacin da muka ratso ta bazar din gaza na ga shaguna duk a rufe na za ci har sun rufesu ne haka
da wuri, na tambayi abokin zamana cewa da wuri ake rufe kasuwa ne?”
.
Ya dubeni “kai bakone ko” na amsa masa maimakon yayi wani bayani sai yayi shiru kawai zuwa
can wani agefe yace ” intifada ta shigo kasuwa kenan” sai yayi kabbara munzo daidai da wasu yan
sanda, wani matashi a kujerar gaba,
.
Yana sanye da suwaita fara mai tmabarin pLO da wando baki yasa tabarao shima baki ya yafa
makawuya mai rodi rodi fari da baki , kakkarfa dashi ya mike ya leko ta taga yace ” al mautu lil
izra’ila” ya fada da karfi cikin motar suka amsa masa
.
Kafin kace kwabo sun durkusa kasa suka dinga yo mana harbi gadan gadan gilas din baya na motar
ya zube shar kamar ruwa na gaba yayi caba caba da hudojin Shuraih Usman inkiya 99% arsahshi
.
Direba ya take kwano, cikin motar maimakon ya rude da kara da hargowa kamar yadda zai abku
inda ace a sarayebo ne cikin sauri sai kowa ya kwanta cikin motar wasu akarkashin kujera wasu a
karfen motar suna kabbara suna AL MAUTU LIL IZRA’ILA
.
Ni kadai na rage a zaune ina son ganin kwakwaf na dauka abin wasa ne , wata mata mace agefena
tana yi mini ishara na kwanta naki, koda gilas din gefena ya zube ya tarwatse , tartsatsinsa ya same
ni a fuska cikin rabin dakika daya nai tsalle nabi lafiyar kwano
.
A guje muka ratsa bazar din , muna gab da fita wasu sojan izra’ila suka ja daga suka durkusa
kowanne ya dana bindigarsa ya saito mu, abin dana iya gani kenan na sake bin lafiyar karfen motar,
.
Dakikoki biyu ko uku a tsakani sai gilas din gaba ya zube, direban yayi kara ya saki matukin motar
ya fadi a gefe jini yana zuba ta kansa, motar tayi sartu damu a guje ta tunkuyi wasu jerin rumfunan
kayan marmari ta shige ciki tayi karo da bango gao!
.
Shuraih Usman inkiya 99% tana tsayawa na nemi inda kofa take na laluba gun da nasa jakata na
jawo ina tsima nayi waje na taka mutane cikin jini na bazama da gudu ban san inda nake ba
.
Nabi ta bayan rumfunan na bullo ta wani kwararo dogo ina kaiwa tsakiyarsa, sai na hango yan
sandan izra’ila guda biyu da bindigogi a gabana suna muzurai suna jiran na karasa, cikin sauri na
waiwaya baya na hango soja da bindiga ya biyoni da gudu, nayi tunani cikin kankanin lokaci na
rasa mafita gaba kura baya siyaki nace araina
.
Halt halt, sojan ya kwalan tsawa na tsaya cak. “Am a tourist don’t shoot me please”na fada cikin
kaduwa kafin na rufe bakina har yayi harbin iska guda biyu, na tsaya na kama salati a cikin zuciyata
.
Yan sandan suka kariso “hands up” suka ce dani na daga hannuwa sama gabana yana faduwa ,
lungun shiru ba motsin komai, mari mai karfi cikin sauri ya sauka a fuskata har sai danaga walkiya
ta gifta,
.
Dan sandan ya kufuteni a baki dayan kuma ya hada mani Shuraih Usman inkiya 99% naushi da
mangari, daga nan sai mari, naushi da kutifo da managari ta ko’ina ya dinga sauka ajikina
.
“Ku saurareni kuji matsayina mana” na dinga fada ina rokonsu, amma kememe suka ki saurerena
sai duka suke min kamar Allah ya aikosu,
.
Sojan yana karisowa ya tabe iya karfinsa yakai min duka da gindin bindigarsa bai fi taki daya ba
bindigar ta sauka akaina na lura cikin sauri da hanzari na ban mamaki na kauce cikin dabara na

hankada dan sandan dake gabana nayi tsalle gefe guda, bindigar na sauka akansa yayi kara kafin ya
fadi idonsa ya juya yif ya fadi kasa kamar itace
.
Ganin haka daya dan sandan yaja da baya ya fito da bindigarsa daga kugunsa a cikin rigarsa, kamar
na rumbacceshi ta irin salon da aka koya mini yadda ake kwace bindiga in an rutsa mutum,
.
Amma ganin bayana akwai soja da bidiga, naji gabobina sun tsaya cak kamar an zaren min laka,
sanyin karfen bindiga akeyata shi ya karyan lago Shuraih Usman inkiya 99%
.
“You are under arrest” sojan ya fada da kakkausar muryarsa, na daga hannuna sama “kayi amfani da
karfi akan jami’an tsaro” na bude baki zanyi magana sai naji kakat yana shirin harbi don haka na
tsaya kam bana ko motsi
.
A hankai suka bincike jakata suka dauken american express card dina da kudina sam dala dubu
ashirin dina na takardar dala dari dari acikin sin kinsu, suka dauki fasgo dina suka bincike kasar
jakar suka dauko sarkar wuya ta nagis, suka duba sosai “ancient atiquity” dan sandan ya mikawa
sojan, yadaga sosai precious jewellery of the middle age ” ya saka a aljihunsa yasa dariya
.
Naji kamar an cire mani zuciyana koda nayi kokarin magana sai “zamu kashe ka yanzun nan” suka
sa dariya cikin kankanin lokaci nayi tunanin sarkarnan ita ta kawoni nan , sannan ga alkawarin dana
yi wa Nagis gashi nazo garinsu mintuna kadan ya rage na kaiga mai sarakar,
.
can na tana ai jiya ba yau bane ,yanzu ina da Shuraih Usman inkiya 99% horon soja na kuma kware
a fagen dabarun yaki naga kuma yaki nayi shi na shiga hatsari daban daban , don haka dole na
kwace sarkar nan ko da zan mutu kuwa, wannan shine abin da zanyiwa Nagis bayan ranta
.
Na saki jikina nakama rokonsu na marairaice har da hawayen karya, mai bindigar yana dan
waiwaya don duba wanda ya suma cikin hanzari na shammaceshi ni kai na nayi nayi mamakin irin
saurin danayi nasa hannuna na bige bindigar da karfi
.
Kafin dan sandan dayake gabana ya danna kuna man bindigarsa ne na dauke shi da kafata tayi sama
cikin sauri da azama na sunkuya kasa, yayin da sojan ya kawo harbi harsashi ya sami dan sandan
aka yayi tsalle ya fadi kasa tum
.
Nakai kasa Shuraih Usman inkiya 99%cikin sauri nayi kwabo na kwashe kafafunsa ya saki bindigar
ya zube da baya cikin sauri da azama nayi tsalle na hau ruwan cikinsa , muka kaure da kokawa
naiya kokawa don ni gwanin kokawane tun ina yaro
.
Ganin nayi biji biji da shi kuma bazai iya galaba da ni ba, ya zaro wuka a kugunsa ya kai min suka
nayi tsalle na goce gefe, ya sake kai mun wani wawan suka Allah ya kiyaye na sake gocewa
.
Ganin na daga shi sai ya tashi idonsa a rufe ya nufi bindigarsa ina share kafafunsa , ganin zaici da
baka dole ya saki wukar don ya ceci hakoransa daga zubewa ban san ya akayi ba sai naji ya kurma
ihu, wukarsa ta nutse a cikinsa jini na zuba hanji waje
.
Cikin sauri na kwashe kudina da sarkar da katuna na na harhada kayana cikin hanzari na rataye
jakata, ina ratayawa motar yan sanda ta gifta kwararon tana jiniya ban san lokacin dana daka wani
wawan tsalle ba na hau katangar rumfar kasuwar nayi sulu a bangon gini, Na dire waje na rarimi
jakata na kama cin gudu
.

Matsanancin gudu kamar raina zai fita ya kaini cikin wani lungu inda palasdinawa suke karfina ya
kare na yanke jiki na fadi, cikin murya mai taushi akayo mini sallama wasu hannuwa suka
ci cira ni
zaune na bude ido na duhu ya fara yi “ina ne wajen saukar baki”
.
Na fada ina haki, wani ya karbi jakata yabani dabino, wani kuma ya kuma ya mika mani jaka cike
da tuffa da inibi da lemon zaki
.
YOH KAGA MUSULMAN DUNIYA KENAN
.
Anan zan tsaya maci gaba a page 10
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99% mamallakin shafin hausaebooks da
Keffians News Teller ke cewa
ALMAU’TU LIL IZRA’ILA
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi daurawa
Littafi na daya 1
Page 10
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
Mun isa wani gida wasu matasa rike da bindigogi masu sarrafa kansu suka kewayeni, sun rufe fuska
da makayuwa idonsu kawai ake gani, a kusurwar gidan akwai wasu dauke da “rocket propelled
launcher”
.
Kowanne yana rike da madubin kawo nisa kusa ,muna isa daya ya dirgo yasa sauko yana bani
mamaki, kuma ya tuna min da yadda yan hamas suke dirga yabani hannu muka gaisa
.
“Na hango yadda kayi da la’annun can ka birgeni ko ka taba yaki ne” ya saki hannuna na bashi
labarin zuwana da kuma gaskiyar cewa ni dan jarida ne”
Muka shiga wani dan ofis a kuryar gidan ya saka aka kawo min ruwan sha “nine aba yusuf
mataimakin shugaban Hamas reshem zirin gaza da kewayenta, jin haka murna ta rufeni sosai , don
wannan shine mutumin da Abuja’afar yace na nema a zirin gaza Shuraih Usman inkiya 99%
.
Naji kamar nazo gida , nayiwaa Allah godiya daya saukaka min abubuwana haka , amma duk da
haka ban saki jiki da suba don gani nake kamar basu bane
.
Wayewar gari da sanyin safiya unguwar jeninta cike da matasa birjik , na fita daga layinmu na ktsa
cikin jami’an tsaro cikin tsoro, na isa wani dan banki da ake canjin kudi na dade ina bin layi,
.
Ina gaf da zuwa kanta suka samu umarnin tsaida harkokin banki kai tsaye,dana nemi dalili matar da
take kanta tace “sabon tashin hankali ya barke a zirin gaza yanzu ba shiga ba fita an rufe ko’ina”
.
Gabana ya fadi Allah yasa dai ba abin da ya sameni a sarayebo bane za’a maimaita ba nace araina
“waya bada umarnin ” na tambayeta
“Peoples committee” tace dani sai na gane kwamitin jama’a na palasdinawa na ya bada wannan
umarnin ba gwamnatin izra’ila bace
.
Kamar yaddaa na fara fashintar abubuwan tun daga jiya a wajen Abu yusuf Shuraih Usman inkiya
shuraih 99% ke typing

.
Jama’ar cikin gari suka harzuka suka hau kan titi suna zangar zangar lumana na fice daga harabar
bankin ina tafiya ina waige waige, na shiga wani shagon sai da shayi don na karya, kuma naji
tsegumi
.
Na fara shan shayin kenan sai naji kabbara ta kaure akan titi, motocin yan sanda suna kawa da
jiniya daban daban cikin sauri na kurbe shayin na fito na tsaya a bakin titi don na kashe kwarkwatar
idona
.
Matasa mata da maza , yara da manya dauke da kwalaye an rubuta tsinuwa da la’anta ga mamayar
yahudawa, wasu anyi rubutun ayoyin jihad, wasu kalmar shahada aka rubuta
.
Suna tafe suna kabbara suna tsinuwa yahudawa da gwamnatinsu, sahun gaba ya kunshi matasa
majiya karfi da kuma wasu yara kanana cikin jan kaya, matasan suna sanye da bakaken kaya dun
suna rawa irin ta soja na gabansu ya rike wata jar tuta an rubuta INTIFADA,
Shuraih Usman inkiya 99%
.
Gefensa matasa suna zarya suyi gaba suyi baya cikin azama da kumari a bayansu wasu suna dauke
da tutar palasdinu da kwalayen da suke kira ayi tawaye, wasu an yi kalmomin masu daraja da ayoyi
masu tsarki
.
Suna tafiya cikin jin karfi suna buga takalmansu a kasa da karfi kasa tana rawa bayansu wasu
matasa sunyi shiga mai ban sha’awa suna jan tutar izra’ila a kasa wani na dauke da kwali a bayansu
an rubuta death to izra’ila
.
Haka suka ringa shigewa kungiya kungiya sahu sahu cikin tsari gwanin ban sha’awa, nan da nan jiki
na ya dau tsima kamar an yimini allurar karfin jiki
.
Kawai ina tsaye sai naji kafata tana tsima kamar an kada mini gangi, koda wani ayarin cike da
matasa majiya karfi yan bana bakwai wanda suke sanye da bakin wando da farar riga da jajayen
kyalle a goshinsu , suna waka suna rawar soja suna zarya suyi gaba da gudu su dawo baya Shuraih
Usman inkiya 99% suna fadin;
.
Shahada maganin mutuwa
Allah bamu shahada
Allah a gaza mana
Allah karya yahudu
Allah karya amurka!!!
.
Wannan wakar na sha jin yan hizbullah suna rera ta alokacin dana ke bosniya, ban san lokacin dana
amsa musu ba, ban yi aune ba sai na tsinci kai na a tsakiyar yan zanga zanga cikin yan mintuna sai
na ganni a sahun gaba
.
Ina rawa ina waka ina juyi ina buga kafata a titi, kamar ba ni ba duk hatsarin da nake ciki na manta
cewa bafa a kasarmu nake ba, na mance kasar izra’ila nake, na manta a bin daya faru jiya atsakanina
da jami’an tsaronsu, bana shakka kuma ana nemana, dadin dadawa kuma lokacin da aka kayade min
saura kadan kuma yana cika akan dole na fice ko su shiga farautata,
.
Amma gaskiya duk wanda ya saba shiga rawar sojoji ko zanga zanga ta fito na fito yasan cewa duk
wani hatsari ko tsoro bacewa suke yayin da kaga ayarin masu zanga zanga na ficewa tya gabanka,
komai mantawa zakayi dashi har sai ka shiga sannan hankalinka zai kwanta,
.

Tun ina jami’a Shuraih Usman inkiya 99% na sha karanta babin zanga zanga da ake kira Mob
Action amma ban fahimci ainashin sa ba sai dana samu kaina a gaban sahun matasar zanga zangar
INTIFADA
.
Can mun zo tsakiyar wani fili ban yi aune ba kawai sai ga motocin sojoji dana yan sandar kwantar
da tarzoma cikin mugun shiri, sunyi sahu sun shirya sosai mu suke jira mu karaso
.
Bayansu motocin daukar gawa sun layi kai kace yaki za’ayi tsakanin rundunoni, masu karfi kuma
karfinsu yazo daya, ban taba zaton za’ayiwa farar hula masu zanga zangar lumana wannan
mummunan tanadin ba , ganin yadda suka zo da motocin daukar gawa ya nuna cewa sun zo da
nufin halaka mu gaba daya
.
Ina tsaye ina kallon wannan shirin kisan gilla sai wani matashi ya tabani “kafita daga sahunnan, kai
bako ne, sa kuma sheda ka, kuma kai baka zo ne saboda gumurzu ba ka Shuraih Usman inkiya 99%
barmu mune muka gaji fafatawa da yayan da Allah ya tsinewa
.
Naki matsawa ko’ina, wani na yazo ya gaya mini haka, toh don na sami daman kallon komai ba don
naji tsoro ba, don har wannan lokacin jikina tsima yake , sai na koma gefe na tsaya ina kallon yadda
mara bindiga zai fafata da mai cikakkun kayan wuta, wanda ya tanadi duk wani makami na kisa ko
tsoratarwa da gallazawa dan adam
.
Akayi cirko cirko sojojin sun shirya tsaf sun saka hulunan gwano maganin iskar tiya gas, sun sanya
wasu rigunan roba suna rike da garkuwar karfe, motocin asibiti na jiniya shiga baya sunyi layi,
palasdinawa Shuraih Usman inkiya shuraih 99% masu zanga zanga suna kabbara sun a hailala suna
rokon Allah yabasu juriya da nasara
.
“Wata doguwar mota na tabbata tankar ruwar zafi ce tayi birki, daga baya a daidai lokacin da wasu
matasa dauke da bindigogi suka karasa cikin masu zanga zanga, kamar a film wani kyaftin din sojan
izra’ila ya karaso fili a cikin wata mota mai sulke, ya fito da kasan daga cikin motar yayi magana ta
lasifika daaga nan ya daga hannunsa alamar umarni sojoji suka karba, karar bindiga da kabbara a
lokacin guda suka abku, wani abu kamar abu kamar ruwa kamar hayaki yayi tsiri sama daga dogon
bututn dake gaban tankar ruwan zafin……………….”
.
Anan muka kawo karshen littafi na daya
Marubucin yace zai cigaba a AWA 48 A ZIRIN GAZA na biyu
Ibrahim akhatibi daurawa nagode , wassalam
.
Ammafa jama’a sai dai kuyi hakuri don bani da littafi na biyun Shurarih Usman inkiya 99%
.
DIRAR MIKIYA
Yakin basasa yayi kaca kaca da kasar somaliya ,
Yunwa na kashe mutane yan tawaye da sauran yan ta’adda suna cin karensu ba babbaka , gefe daya
sojojin Amurka sun
a kokarin mamaye kasar gaba daya , sun shiga fasadi da mata da yada
gurbatattun Al’adunsu
.
Daga ibrahim akhatibi daurawa
SANARWA
Wannan labarin kago shi akayi, amma akwai abubuwa da yawa a cikinsa wanda suka faru a tairhi
ka bincika sosai zaka karu
.
Alura sosai ba fim bane, an rubutashi sakamakon bincike mai zurfi na lokaci mai tsaho
Ba’a yarda a juya shi ta kowacce irin hanya ba, sai da rubutaccen iznin marubucin

.
DAGA IBRAHIM AHMAD DAURAWA
Sarayebo.
1,2,&3
Dirar Mikiya
Baradan Chechen
Kundunbala
Hadirin Kasa
Kowane Allazi. 1&2
Tarnaki
Gidan Rina
Awa 48 A Zirin Gaza 2
.
P.O. Box 5055, kano
Anfara bugawa a 2000
INAD Publisher Al-khatibi, 2000
.
Kada ku manta zaku iya downloading wannan littafi zuwa kan wayoyinku ta hanyar ziyartar
shafinmu na yanar gizo gizo Hausaebooks
.
Ko kuma kuyi searching nashi a google ku downloading
.
Daga Naku Shuraih Usman
Inkiya 99%
Littafinmu na gaba shine
TARAR ARADU
Littafina Uku 3

Comments

table of contents title