Results

CIKIN WAYE page 1 to 10

CIKIN WAYE?🤰
   
        ❤ ❤❤❤
              ❤❤
                 ❤       story
               and
                       written
by

  * Fateemah Sunusi Rabee'u *
ummu affan

🅿1⃣-2⃣

Bismillahir rahmanir rahim

wannan labarin qirqirar ran labarine da na qirqiresa domin fad'akarwa ilmantarwa jan hankali tare da nishad'antarwa da fatan xai amfanar da jama'a,banyisa don wani ko wata ba da fatan xa'a gwuji xargi,A sha karatu lafiya.

🌿 Ina xaune takure ajikin qofar farlournmu A qalla nakai wajen awa d'aya ko fiye da hakan,hawaye ne wasu kebin wasu kan kumatuna wani sabon kukan na fashe dashi,

Wnn rayuwar ta isheni baqin ciki yayi yawa agareni,wacce irin mummunar rayuwa nakeyi a ckn gdnmu Ace mutum da uwarsa da ubansa amma yake cikin mawuyacin hali,anya umma itace ta haifeni,nashawa kaina wnn tambayar domin ko makaho yashafa yasan da walakin goro amiya,ma'ana duk wanda yakalli yanayin xamana a gdn xai iya fahimtar ba itace ta haifeniba,

xuciyata tayi rauni yaushene xa'asanar dani sirrin dake bibiyar rayuwata,

Wata tsawa danaji itace tadawo dani daga duniyar tunanina,Aunty Rahma ce nagani tsaye akaina sai wani jijjiga take ta kalleni a wulaqance,tc"makira munafuka mai halin mayu maitarce taki ta motso,duk da nasabajin irin wnn kalaman amma a kullum najisu sai naji ba dad'i,

nc"kiyi hqr Aunty Rahma,fuxgoni tayi ta had'a da garu ta fara kima,cewa take,"uban me kika xaunayi anan munafuka salon baqi suxo suce cutarki ake,muryar umma mukaji wacce tafito daga farlour tc"ai munafuncinta ya wuce da haka Rahma so take ubanku yadawo yace na mata wani mugun abun,itama tajawoni "yar kaxakaxan ubancen ayi mace sai shegen fi'ili kamar 'yar gdn wani hamshaqin sai anyi mata abu taxo tana Allah Annabi kamar wata ta k'warai,

kuka nake ina bata hqr"don Allah umma kiyi hqr baxan sake ba,tsaki taja mtsuuww tasakeni na xube a gurin ta kalleni,"wllh kika shugomin farlour saina karyaki shegiya kawai,

Takama hannun Rahma sukayi ciki Rahma hardasa qafa tasake tureni,sosai nake kuka ina tausayawa kaina da rayuwata,nayi qasa da kaina ina matse k'walla daidai shugowar Abba,

da sauri na share hawayena na miqe cike da murna da niyyar 6oye damuwata,amma na makaro kallo d'aya Abba yaimin yasan ina ckn damuwa daman dagashi sai yah Al-amin suke gane halin danake ciki saiko qawata aminiyata Zainab,

Kallona yayi yc"Naanah mikikeyi anan har yanxu baki ganin dare ya fara bana hanaki xama waje idan dare yayiba ko ba komaima wnn sanyin da ake sai yashiga jikinki mura bata da dad'i mamana,

d'an murmushin yaqe nayi tare da kamo hannunsa nc"Abba kai fa nakejira kadawo nasan xakayomin tsarabata shiyasa ko abinci banciba sai kadawo,shima mrmshn yayi yc"Naanah manya kesai ankawo miki tsaraba snn xakici abinciko?,

Turo baki gaba nayi cike da shagwa6a nc"Abba bakai kasabarminba,kumatuna yaja yana dry snn muka shiga ciki,

su umma suna farlourn muna shugowa tabimu da harara tare da ta6e baki,xaunawa mukayi ina liqe ckn Abba kaina qasa ko d'agowa nakasa don banson mu had'a ido dasu,soyayyar doya da k'wai Abba ya miqomin cike da murna na amsa don rabona da abinci tun safe,bud'ewa nayi nahauci Abba da kallo ya bini yc‘’Naanah kinci abinci kuwa,d'ago kaina nayi aiko muka had'a ido da umma kallon da tamin yasa da sauri na gyad'a kaina"eh Abba naci,na fad'a tare da d'aukar doyar nayi d'akina da kallo yabini cike da tausayi,

kallon umma yayi yc"karimatu nadawo babu sannu balle insamu matsayin ko ruwane a bani nasha,wani mugun kallo ta masa ckn rashin d'a'a tc"sai yanxu ka ganni tunda ta tashi ko,girgixa kai yayi yc"kiji tsoran Allah karimatu Naanah fa 'yarkice meyasa kike nuna mata banbanci da sauran yaranki baki tunanin jefa rayuwarta ckn garari,mtsuuww taja tsaki mai qarfi"a inda ba 'ya kenan ni kadena had'ani da waccen shegiyar yrnyr,"Karimatu!,Abba ya fad'a cikin tsawa da sauri tayi shuru tana wani yi masa kallon tara saura kwata,

miqewa yayi ya kalli Rahma yc"ina Sakina,kame kame ta fara don har yanxu Sakinar bata dawo gida ba,girgixa kai yayi tare da fad'in Allah yashiryaku,ya wuce,

da sand'a Sakina tashugo gdn don tadade da dawowa ganin Abba a falon yasa bata shugoba,sai da taji ya shiga ciki,umma tc"meye na wani sand'a,tc"uhmm umma Abba mana kinsan halin tsohon nan yanxu ya cikama mutane kunne da wani wa'axinsa,

Guri tasamu ta xauna umma tc"me akasamo mana yau Allah yasa akwai kud'i masu auki kinsan xankai kud'in adashi danake tarawa idan bikinku yaxo(A'uxubillah uwace waike fad'in hakan Allah kashiryamu kashirya mana xuriya),

Sakina ta turo baki gaba "wllh ke umman nan kin cika son banxa ni dashan wuya keda kwace kud'i kinsanma menayi nasamesu,umma tc"don kaxakaxanki bansonji idan ban barki kin fitanba xaki samesu sai in had'aki da tsohon naku ince gaki kin dawo daman yanxu ya gama tambayarki,sakina tc"ke umman nan kin cika kwafsi daga wasa nifa wasa nake miki,nan ta bud'e xaka ta kwaso kud'i taba umma nan haqora suka washe tc"da kyau 'yar albarka kinga da bikinki xaki kwashi kaya,banda su Naanah da ba abinda aka iya sai xaman gida da xuwa makaranta hali sak irin na tsoho gaba d'aya sukasa dariya harda tafawa,

girgixa kai nayi daga ckn d'aki nayi juyi a kan ya mutsattsiyar katifata hawaye na tsiya.


       ummu affan


please share
and comments
🤰 CIKIN WAYE? 🤰

   
        ❤❤❤❤
              ❤❤
                 ❤

          story
                  and
                          written
       by

*Fateemah Sunusi Rabee'u
ummu affan


🅿3⃣-4⃣

   Bismillahir rahmanir rahim


🌿Hawaye na tsiyaya,sai yaushe umma zata gane gaskiya ta kula da tarbiyyar yaranta Allah kashiryasu na fad'a tare da goge hawayena nayi addu'ar barci,nan kuwa barcin ya kwasheni,

Washe gari da wuri na tashi kamar kullum alwala na d'auro na gabatar da sllar,salatul fujur na fara sannan nayi sallar asubah,na dad'e ina addu'o'i sannan na shafa,

Kasancewar ranar asabarce babu boko,sai na koma na kwanta baikai ga yin barcinba naji ana kwalamin kira,tashi nayi ina tafiya cikin sanyina duqawa nayi saitin umma wacce itace tayi kirana,

Nace''umma gani,cikin masifa tace'"wllh duk munafurcinki saidai ki tsaya iyakar uban naku da yayanku amma ni bazakimin shiba,Aunty Sakina tace"shegiya wata simimi kasau da ita saikace mutiniyar arziki,

Nidai bance musu komaiba sai hawaye dake bin fuskataAunty Rahma tace"duk kukanki na banza ne yau ko bazakije wannan makarantarba aiki zakiyi,umma ta amshe maganar dacewa"Abu dole ai ko bakiso saikinyi tunda bazakije ki wani kwantaba sai aini kici,

Bance musu komai ba na nufi kitchin d'in ni kaina inason yin aikin girki don nak'ara k'warewa saidai Abba ne ya hana tasani ganinsa ga manyan 'yan mata nan gabanta bata sakasu saini,

Sauri-sauri nayi aikin don k'arfe takwas da rabi muke zuwa Islamiyya kuma malaminmu yayi gargad'i akan duk wanda baizo ba bulala goma don hadda ya bada,kuma zai iya don malam sani bashi da mutumci,ni kuwa a duniya idan akwai abinda natsana to bulalace,

Kusan takwas saura na gaba girkin na jera komai a k'aramin dinning table d'inmu snn nazo na gyara kitchin d'in na wuce d'akina,toilet na fad'a wanka nayi sannan nazo na shirya cikin uniform d'ina purple colour nasaka safa na d'auki lik'af d'ina a hannu farlour na dawo harsun gama breakfast d'insu gurin kacha-kacha,

Tsintsiya na d'auko na tattara gurin sannan na karya,na d'au na wankewa na kwanke sannan na fito na d'aura nik'af d'ina,har lokacin Abba bai fito ba daman idan yadawo masallaci yana dad'ewa kan ya fito,d'akinsa nashiga yana zaune kan prayer mat yana lazumi ganina yasa yayi addu'a,duk'awa nayi kusa dashi na gaishesa ya amsa cikin sakin fuska da nuna kulawa,

Yace"Naanah har anshirya kenan,nace"eh Abba zan wuce sai nadawo,shafa kaina yayi yace"Allah yayi miki Albarka ya kareki aduk inda kika shiga,cikin farin ciki na amsa da "Ameen Abbana,gaba d'aya mukayi dariya sannan namasa sallama na wuce,

Kasancewar makarantar tamu ba wani nisa gareta ba anan k'asan layinmu ne da k'afata na k'arasa,ina zuwa kuwa malamin da zai amshi haddar na gani cikin ajinmu,nashiga cikin ajin da sallama,

Ya kalleni sama da k'asa sannan yace"Naanah Firdausi Isma'il zonan,dawowa nayi na tsugunna daga k'asansa nace"gani malam,yace"inaga agwogwon gidanku bai tafiya daidai ko?,k'asa nayi da kaina cike da rud'ani nikaina nasan na makara domin tara daidai nafito gida,

Ahankali nace"don Allah malam kayi hakuri wani aiki nayi,yace"wanda yasaki aikin baisan lokacin makarantane ba,yana fad'ar hakan yana zaro bulalarsa,cikin sauri na mik'e a razane nayi cikin ajin,kallona yayi yana zaremin ido sannan yace"ke Naanah na lura duk cikin ajin nan kinfi kowa rainani ko,nace"don Allah donsonka da Annabi muhammad S A W kayi hakuri bazan sake makara ba,

Ajiye bulalar yayi yana kallona sosai yace"shi kenan na rabu dake amma idan baki iya haddar dana baku jiya ba kinsan sauran,nace"na yarda,sannan na tsugunna na fara yi mishi karatuna cikin natsuwa daba ko wanne harafi hakkinsa,bayan nagama akayi kabbara,sannan naje na zauna inda nasaba zama kusa da k'awata Zainab Ibrahim....


 
           Ummu Affan

Please Share
and comment
🤰CIKIN WAYE?🤰       ❤❤❤❤
            ❤❤
               ❤


      Story
              and
                     Written

By

 Fateemah Sunusi Rabee'u
Ummu Affan


🅿5⃣-6⃣

  Bismillahir rahmanir rahim


*Na sadaukar da wannan page ga Hussaini 80k Nagode kwarai da gaske Allah yabar zuminci Ameen*🌿Zainab ta kalli Naanah tayi mgn cen kasa,"gaskiya Naanah kin ya bawa aya zaki da yau kinsha bulala,murmushi kawai tayi don Malam Sani sam bashi da kyirki yana kyale Naanah ne saboda tana da kokari duk ajinsu ita ce ta farko sannan Zainab,shiyasa kosun makara wataran ba a bugunsu don makarantar na alfahari da su,

Zainab Ibrahim nan kusa da gidan su Naanah take tun suna yara suka taso tare,makarantar boko da islamiyya duk daya suke kuma aji guda,


mahaifin Zainab yana da kudi sosai babban dan kasuwa ne,yara uku suka haifa shida matarsa Hajiya Rabi wacce suke kira Hajiya Marwan shine babban dan su wanda yake qasar waje karatun likita sai Rashida sannan Zainab,

Iyayensu suna matukar ji dasu sun taso cikin gata da kulawa ga Ingantacciyar tarbiyya,Hajiya da farko bata son kawancen Zainab da Naanah saboda atunaninta halinsu daya da sauran 'yan gidansu sai daga baya da taga ne halin Naanah ya banbanta da nasu takejin sonta har cikin ranta take kaunar kawancen nasu tana matukar tausayawa halin da Naanahr take ciki,

An tasosu suna kan hanyar dawowarsu gida Zainab tace"wai yau Naanah me yasaki makara kuma kinsan sarai malam Sani zai amshi haddarsa yau,

Nace"kedai bari Zainab kinsan halin Umma ita ce tasani aiki bayan nayi sauri ma da bazan samu zuwa ba,tace"Allah ya kyauta,na amsa da ameen,

Daidai nan tazo kofar gate dinsu tace"ni zan wuce gida sai gobe mun hadu a skul,nace"shi kenan sai goben,

Wata dan kareriyar moto na gani kofar gidanmu,ba ka ganin wanda ke ciki a tunani na samarin su Aunty Sakina ne don haka na shige ciki,saidai ina shiga na jiyo hira sama-sama da sauri na shiga ciki,

"Yayah Ameen,na fada cikin murna da fara'a,shima fuska sake ya kalleni tare da sakarmin tsadajjen murmushinsa,da sauri na karasa na fada jikinsa ina murnar ganinsa,"oyoyo Yayanmu,shima cikin muryarsa mai sanyi yace"oyoyo autarmu, daga makaranta ake,Nace"eh yayah Ameen saukar yaushe,yace"ban dade da zuwa ba,

Ganin ba'a kawo mishi komai ba sai na wuce dakina na cire uniform na wuce kitchin ruwa da abinci na d'oro akan tire na aje gabansa,na zauna kusa dashi,

Abba yace"kinfi wadan nan sakarkarun anyi bako basusan sutarbesa dako ruwa ba,murmushi kawai nayi yayin da su kuma sukaci gaba da jefata da mugayen harararsu,

Saida yaci ya koshi sannan aka fara hira,Umma tace"ke me kama da bakar mayya saiki tashi ki bani guri ingana da d'ana,...
🤰CIKIN WAYE?🤰


     ❤❤❤❤
          ❤❤
             ❤       Story
                and
                       Written

By
 Fateemah Sunusi Rabee'u
Ummu Affan


🅿7⃣-8⃣

Bismillahir rahmanir rahim
🌿Zan tashi Yah Ameen ya riqe hannuwa na,ya kalli Umma yace"Haba Umma har yanzu baki dena wannan abun ba,tace"to uban 'yan shisshigi da kai nake magana ko da ita,yace"amma me yasa baki kori su Rahma ba sai ita,cikin fushi tace"Al-ameen ka fita idona in rufe kai kanka kasan da kyai banbaci atsakanin su kuma wllh ka dena samin baki a cikin magana ta da wannan shegiyar yarinyar,

Girgiza kai kawai ya ke zuwa cen yace"Allah yabaki hakuri ya huci zuciyarki,tsaki taja mtsuwww sannan ta juyo kaina "ke bada ke nayi magana ba,

Tashi nayi jikina asanyaye ina zubar hawaye,ko da zuwana dakin kan katifa na fada ina kukan bakin ciki,waini mai nayiwa Umma ta fiddani daban cikin 'yaranta,ina 'yar cikinta tana nunamin banbanci da sauran 'yan uwana,sosai nake kuka na tusa kaina cikin fulo,

Banji shugowarsa ba sai ji nayi ya dagoni zaune,yana sharemin hawayena yace"Naanah ke me hakuri ce da juriya ga hankali please kar maganar Umma ta d'aga miki hankali,kallonsa nayi ido cikin ido nace"Yah Ameen abin da Umma ke min ya fara isa ta hakan yasa nike jin shakkar anya Umma ta aifeni?,da saurin yarufemin baki yace"kul karki sake fad'ar haka Umma ita ce ta aifeki ko da wasa kar in sake jin kinyi wannan maganar,da haka yayi ta rarrashi na har na sakko muna hira yana bani labari ina dariya,

Yasa hannu aljihu waya ya ciro k'arama ce kirar TECNO ya bani,mai kyau ce da tsada,yace"ga waya na saya miki,nayi sauri na amsa da akwaini da son waya ko don game don idan na dau wayar Zainab game kawai nake,nace"kai amma tana da kyau,"tayi miki kenan,yace,nace"sosai kuwa nagode Yayah saidai ina tunanin Umma bazata barni da waya ba,yayi murmushi yace"karki da mu saida na nuna mata saboda hakan har Rahma da Sakina na sayawa,

Nace"kai Yayah amma naji dad'i Allah ya kara rufa asiri yasa kafi haka,yace"ameen,yana jin dadin yadda idan yayi mata kyauta take nuna jin dad'inta tare da masa kyawawan addu'o'i,sa6anin su Rahma wani lokacin ma idan yayi musu kyauta cewa suke baiyi musu kyau ba,amma ita ko da bata son abun zata amsa kuma ta masa godiya da addu'a,shiyasa ako da yaushe yake kara sonta,

To tunda yazo gidan su Rahma aka natsu domin inhar yazo to dole ne su natsu ba wacce ke fita daga makaranta sai gida,su daman ba wani da muwa suka yi da makaranta ba,to in fa yazo dole aje shiyasa basu kaunar yazo mugun tsoransa suke don bai wasa da yara,

Yah Ameen cikakken mutum ne mai haiba da kamala matashin saurayi me jini ajika shekarunsa talatin da biyu yanzu fari ne dogo cikakke mai cikar kamala kirarsa ta kar fafan maza ce bai cika fara'a idan kaga yayi ko murmushi to tare yake da iyayensa saiko Naanah da yake tausayawa halin da Umma ta ke mata,

Malam Isma'il wanda aka fisani da malam Sama'ila shine mahaifinsu bafullatanin Adamawa wanda neman halaliya yadawo dashi Kaduna ba wani mai kudi bane saidai rufin asiri sana'ar saida takalma yake a shagon da yakama haya kasuwar barci,ba laifi yana samu don har Lagos yake zuwa sari,Anan kasuwar su ka hadu da Karimatu wato Umma har Allah ya hada auransu ita haifarfar nan ce,

Karimatu tun farko ba dad'in zama da ita yake ba saidai hakuri don yana da hakuri sosai d'ansu na farko Al-ameen wanda ake cewa Ameen sannan Rahma sai Sakina da Karamarsu Naanah Firdausi wadda nike tantamar anya ita ta aifeta(uhmm mudai je zuwa),

Ameen yayi karatun primary har zuwa matakin secondry da ga baya kuma ya shiga jami'ar Ahmadu Ballo da ke Zaria ya karanci Business,duk da temakon Babansa da shi kansa da ke buga bugarsa har Allah ya temake sa yakai matakin digiri,wajen neman aiki ne Allah ya hadasa da Alhaji Salisu Sada babban d'an kasuwa da sunansa ya shahara babban mai arziki ne wanda yatara dukiya mai tarin yawa,kallo daya yawa Ameen yaji yaron ya kwanta masa sosai yaja shi jiki ya nuna masa harkar kasuwarsa,in takaice muku mutane da yawa basusan Ameen ba d'an Alhaji Salisu Sada ba ne,yanda Alhajin ke jin Ameen a ransa ko dan da ya aifa arbarka daman kuma Allah bai basa aihuwa ba duk tarin dukiyar da yatara,

Hajiya Asma'u matar Alhaji Salisu Sada d'a ta dauki Ameen haka shima Alhajin komai yana iya zartarwa kuma yazartu agidan Alhaji Salisu har d'aki garesa a gidan...


    Muje zuwa har yanzu ba mu shugo cikin gundarin labarin ba taku Fateenku 

      Ummu Affan
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


         Story
                 and
                       Written
By
 Fateemah Sunusi Rabee'u
Ummu Affan

🅿9⃣-1⃣0⃣

 Bismillahir rahmanir rahim

Duk kan 'yan uwan alhaji Salisu Sada da na Hajiya Asma'u sun san da zaman Ameen kuma dukansu suna kaunarsa,

Idan yazo gida ba wani dad'ewa yake ba kasancewar aikinsa don har kasashen waje Daddy yake turasa akan har kokin kasuwancinsa,

Wannan karon ma satinsa guda ya koma cike da tausayin Naanah,

Mun fara jarabawarmu ta kammala k'aramar secondry wato (JSCE)cikin azumi ne amma Umma bata tausaya min duk kan aikin azumi nice keyi dana dawo skul banda wani lkc,

Ina duk'e ina wankin waken da zan soya kosai anjima Abba ya shugo,dawowarsa sallar la'asar,"Sannu da zuwa Abba,yace"yauwa Naanah,gefen tabarma ya zauna daga gefen inda nake,yace"Naanah yaushe ne zaku kammala jarabawar,nace"Abba sauran kwana biyar ana sauran kwana uku sallah,yace"to Naanah Allah ya nuna mana,na amsa da ameen,

Zuwa cen nace"Abba kana dai sane da saukarmu bayan sallah ko,murmushi yayi yace"kai Naanah kinsa saukar nan aranki Yayanku ma ya turo kud'in shahadar na biya miki,nace"yawwo Abba Allah yasaka sai kuma d'ayar maganar,"ta me?,ya tambaye,turo baki gaba nayi cikin shagwa6a "kai Abba ba dai kamance da maganar ankonmu ba,dariya yasa yace"Naanah iyayen rikici kinsan Yayanku yace zai komai ni ya hutar dani,zum6uro baki nayi,"kai Abba kasan Yah Ameen da mantuwa,"ehye baya saya miki waya ba saiki dunga tuna masa,cike da yarinta nace"eh fa haka ne Abba,gaba daya mukasa ka dariya,

Umma ce ta fito daga farlour,taja tsaki mtsuuww,ta gallamin harara take na dawo hayyacina,tace"aikin banza harara a duhu ayi dai mugani idan tusa zata hura wuta,

Abba ya kalleta ganin yadda tayi masa k'erere a kai,yace"lafiyarki,"qlau ta basa amsa a tsiwace,kafin ta juyo kaina "KE tace min daman mafi akasari tafi kirana da ke,juyowa nayi ina kallonta,tace"mayya da shegen manyan idanuwan ki kamar na aljanu kurwata kurr da ke,

Da sauri na sadda kaina kasa"kiyi hakuri,nace cikin sanyi,"yar kaza kazan nan ai daman haka kike da anyi magana kice ayi hakuri kamar kinfi kowa sanin Allah a fuska musa a zuciya fir auna,

Sake sadda kaina kasa nayi,tace"zan fita ne kan indawo ki tabbatar kin kammala komai na bud'a baki sauran kiyi abinci da yawa ko kiyi kad'an yazo bai isa ba sakarya shashasha,ture ni tayi tai gaba ko tambayar Abba babu daman duk in zata fita bata tambayarsa,

Tashi nayi ina kakka6e jikina Abba ya kalleni ckn raunin murya yace"Naanah kici gaba da hakuri wata rana sai labari nima dai kina kallo hakuri na ke da ita,ajiyar zuciya kawai naja naci ga ba da aikina,

Araina ina tunanin irin wannan hali na Umma,Abba yana matukar bani tausayi wani lokacin saidai ina tunani da mamakin mai yasa bai taka mata burki idan tayi wani abun ko da yake gsky yana bakin kokarinsa ina ga gajiya yayi yanzu...


     Ummu Affan

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 1 to 10"

Post a comment