Results

CIKIN WAYE page 11 to 20

CIKIN WAYE?🤰


    ❤❤❤❤
         ❤❤
            ❤      Story
             and
                   Written

By
  Fateemah Sunusi Rabee'u
Ummu Affan

🅿1⃣1⃣-1⃣2⃣🌿Koma dai menene addu'a ta kullum ita ce Allah ya shiryata,

A kwana atashi ba wuya a gurin Allah,mun kammala jarabawarmu lfy har Allah ya kawomu gobe sallah ranar wuni nayi aiki kamar me na gaji sosai,

Washe gari sallah da wuri na tashi nashirya cikin wata atamfa riga da siket sosai ta amsheni kamar dama ajikina aka tsarata nayi make-up d'ina simple sosai nayi kyau Yayah Ameen ne ya aiko mana da kayan sallah kala biyar biyar masu kyau da tsada,k'awata Zainab na biya mawa muka wuce salar idi,sai yabani take wai nayi kyau,bayan an idar muka dawo,

Abba da Yah Ameen suka shugo sun dawo sallar idi ne,Yah Ameen yana cikin wata d'anyar shadda da akayiwa d'inkin da samari ke yayi,gaskiya yayi kyau ainun,

Tunda ya shugo idanunsa na kan k'anwar tasa da yake matukar kauna a zuciyarsa,kusa da ita ya samu ya zauna,sannan ya rad'a mata a kunne,"gaskiya kinyi kyau kanwata sosai,murmushi tayi har sai da dimple d'inta suka lotsa,ita ma ahankali yadda shi daya kawai zaiji tace"ai Yayah ka fini kyau ka ga yadda ka had'u kuwa,ido ya d'an kura mata na wani lokaci sannan yace"ke kanki kinsan ba zaki had'a ni dake ba ke me k'ira irin ta indiawa,dariya tayi sosai har Abba nacewa "yau kuma me yasami Naanahr Abba ta ke irin wannan dariyar,tace"Abba kamanta yau take sallah dole inyi farin ciki,yace"haka ne,sannan ya maida hankalinsa gurin abinda ya ke yi,

Ta k'ara cewa a hankali"Yah Ameen ai gwamma kai kasan da Abba kake kama su Aunty Rahma kuma da Umma ni kuwa da wa nake kama,ta fad'i hakan cikin damuwa,ya d'anyi shuru na wani lokaci sannan yace"ai kema da Abba kike kama ko baki ta6a jin wanda yace muna kama ba,

Tasan wasa yake mata sai kawai tayi murmushi ba tare da tace komai ba,Ashe duk abun da suke Umma na kallonsu abinda suke cewa ne kawai ba taji,tace"waiku k'wusk'wus d'in me kuke,Yah Ameen yace"Umma ba komai,sai kuma batace komai ba,

Bayan sun fita ne Umma ta kamamin kunne taja sosai,zafin da naji yasa na saki 'yar k'ara tace"wallahi kinji ni inhar baki fita idona na rufe ba sai na sa6a miki sau nawa ina gargad'inki da ki dena shigewa yaron nan meyasa bakiji halinki ya ke irin na mayu ne iye to ina sanar dake wannan yaron yafi k'arfinki kurwarmu kurrr da ke me bak'in hali,

Nace"don Allah Umma kiyi hakuri bazan k'ara ba,ta k'ara jan kunnen tare da sakinsa kuka na saka saboda zafin da naji yana min,ta buga min tsawa,"tashi ki fita cen waje kiyi kukanki ba zakiyi mana shi anan ba,tashi nayi na d'auko mayafina nayi waje kai tsaye gidansu Zainab na nufa,

Ina shiga harabar gidan naga motoci da yawa,duk da cewa in nazo gidan ina ganin motoci a ajiye amma na yau sunfi yawa,sai nayi tunanin ko don sallah ne kila 'yan uwana sukazo gaishe su,Ina shiga farlour cike yake da 'yan uwa,gaishe su nayi suka amsa cikin fara'a da sakin fuska,Zainab ta taso ta kama hannuna tana cewa"Naanah zo ki gaishe da Yayana Marwan ya dawo daga karatunsa,da yake tana bani labarin yayanta Marwan dake karatun likita a kasar Egypt,sai faman jana take har gabansa sannan ta ajeni kusa dashi ita ma ta zauna,tace"Yah Marwan ga Naanah wacce nake baka labarinta a waya aminiyata,d'ago kansa yayi daidai da d'ago nawa kan muka kalli juna lokaci guda,take naji gabana ya buga kamar yadda naga alamar shima abinda naji yaji,gaishesa nayi ya amsa a hankali,ganin yayimin banza na juya gurin Hajiya nace"Hajiya ina wuni anyi sallah lafiya,ta amsa min tana me fara'a,da ya ke haka yaranta ke kiranta da Hajiya nima hakan nake kiranta,

Na zauna kusa da Zainab anata hira kamar nima daman 'yar gidan ce,na lura da kallon da Yah Marwan ke min hakan yasa na kasa sakewa,na d'ago ido kenan sai kawai muka had'a ido dashi na kallesa sosai,bak'i ne shi duk da a zaune yake zaka iya ga ne yana da tsayi ba laifi kyakkyawa ne,fatar jikinsa daga gani kasan akwai hutu,sanye yake cikin k'ananun kaya jeanse da t-shirt,

Ganin ba zan iya jure kallonsa ba yasa nayi kasa da kaina ina wasa da ya tsun hannayena,...

    Fateenku

        Ummu Affan
🤰CIKIN WAYE?🤰   ❤❤❤❤
        ❤❤
          ❤
 

   Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
Ummu Affan


🅿1⃣3⃣-1⃣4⃣

Bismillahir rahmanir rahim


🌿Ganin nayi shuru sai Zainab tace"Naanah na lura yau baki son magana ko anyi miki wani abu ne,Hajiya tace daman cen Naanah ba maison Surutu bace irinki,Zainab tace"uhmm Hajiya ke dai bari don batare kuke da ita ba ne a haka ne kike mata kallon shuru shuru amma idan kika zauna da ita surutu sai ya isheki hakan ta ke kamar Aku,

Na kalleta na d'an harareta sannan nace"Zainab ban son sharri fah,

Hajiya tace"rabu da ita kawai nasan sharri ta ke miki,haka mu kai ta hirar mu har na mance abinda Umma ta min,

Wayata naji tayi Ringing ina dubawa lambar Yah Ameen ce 6aro-6aro,hakanne ya tuna min da gargad'in da Umma ta min,na d'au kiran tare da sallama,

KO amsa sallamar beyi ba yace"kina ina ne!,nace "Ina gidan su Zainab,yace"maza kizo ina son ganinki,"toh,na amsa masa,na mik'e Zainab tace"sai ina kuma,nace"Yah Ameen ne ke kirana,

"Tace"shi kenan kinsan halin Umma da nazo munje mun amshi barka da sallah gurin Yah Ameen,nace"kedai idan zaki taso muje!,ta mik'e muka fita zamu shiga gidanmu kenan ta juyo ta kalleni tace"inhar Umma ta ko ro ni ke kika jamin,nace"haba dai Zainab ba ma zata koroki ba,da ya ke da Zainab tana yawan zuwa guri na Umma tayi ta mata habaici daga baya ta dunga korarta data shugo,shine Hajiya tace"ta dena zuwa,

Yana ta safah da marwah a farlour shi kansa bai san me yasa yadamu da Naanah da yawa haka ba,ya da mu da lamarinta yana matuk'ar jinta a jini da tsokar jikinsa,

Da sallama suka shugo ganinsu da yayi tare da Zainab sai yaji hankalinsa ya kwanta tare da sakin sanyaryar ajiyar zuciya,

Zainab ta gaishesa ya amsa fuska sake,tace"Yah Ameen munzo amsar barka da sallah,murmushinsa mai kyau yayi,yace"Zainab kinyi sauri a binda zan baku yanzun na fasa,Naanah cikin shagwa6a tace"kai Yayah yanzun sai ka fasa ba mu,

Yace"k'warai kuwa tunda kun tambaye ni,Zainab tace"Yayah a mana afuwa,yace"shi kenan nayi amma sai gobe zan baku don akwai inda zaku rakani goben saiki tambayi Hajiya,tace"shi kenan ba damuwa Allah ya kaimu,ya amsa da "Ameen,

***************

Ai kuwa washe garin munsha yawo,Yah Ameen ya kaimu gidajen abokansa da 'yan uwan Umma na nan cikin gari,gaskiya mun samo kyautuka da yawa,gab da magrib muka dawo ya so ya kaimu gidan Daddynsa saidai ganin magrib tayi yace muyi hakuri sai wataran,

Gidan su Zainab muka wuce Hajiya muka bawa kudin da muka samo ajiya,da kayan,sannan na wuce gida,

Ina shiga Umma ta hauni da fad'a,tace"daga ina kike,Anty Sakina tace"ina zata idan ba yawon iskancinta ba,Umma tace"shegiya tana abu kamar me gaskiya nan kuwa iskanci ne cike da ciki figigi da ke kamar a hureki ki fad'i mutum kullum yana cin abinci amma yana yadda ya ke,

Anty Rahma ta kwashe da dariyar mugunta tace"ai wannan yarinyar inaga kome zata ci bazata ta6a k'iba ba,ni kuwa na kada baki nace"wallahi Anty Rahma da nayi irin k'ibarki gara na zauna a haka na,

Da ya ke Rahma a kwai jiki ga ta gajeruwa gab da k'asa ga bud'ad'd'an hanci sai k'aton baki,gara Sakina ta fi Rahma komai don ita da tsayinta irin na Abba,ba dai wani kyawun aje agani gareta ba don duk Umma suka kwaso,

Naanah kuwa fara ce doguwa mai yalwal gashin kai bak'i wuluk,tana da manyan idanuwa masu haske da kyau,hancinta d'an dogo ya bud'e kadan daga k'asa,la66anta sirara masu kyau kalar pink bakinta k'arami mai kyau zubin hakoranta kwanin ban sha'awa,

Bata cika k'iba ba gaskiya siririya ce amma fa bacen ba don akwai cikar diri da mazaunai ga hifs,shine suke mata gorin sirinta wacce ba k'aramin kyau ta mata ba har kishi suke da irin kyawun da Allah ya bata,

Gaba d'ayansu sukayo kanta harda Umma jin irin maganar da ta fad'awa Rahma nan suka rufar mata da duka,saida sukai mata ligiligi duk sun ji mata ciwo...

Muje zuwa Fateenku ce😂👇

  Ummu Affan
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


    ❤❤❤❤
         ❤❤
            ❤


*Story and written by*
 *Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*_*🌿Duk sunji mata ciwo ko motsi ta kasa,amma hakan baisa sunji tausayinta sun rabu da ita ba saima ci gaba da sukayi da bugunta,*_

_Bismillahir rahmanir rahim_


🅿1⃣5⃣_1⃣6⃣

"Abba da Yah Ameen suka shugo ganin irin ta Asar da suke yasa suka k'arasa da sauri Yah Ameen ya ture Rahma da Sakina suka fad'i Abba ya d'aga Umma da ke zaune kan Naanah tana bugu,Yah Ameen ya rufe su da bugu suma saida ya bigesu sosai Umma cewa take"karabu da su Ameenu ko so kake ka kashemin yaran naea,hargagin da ta ke baisa ya rabu dasu ba suma saida ya musu dukan tsiya,

Kin kimar Naanah yayi ya fita da gudu,cikin mota yasa sannan Abba ya shiga wanda ya gama zage Umma tas,sannan suka wuce asibiti,lokacin da suka isa Naanah ta gama fita haiyacinta ko numfashinta sama-sama ya ke futa,nan likitoci suka yi kanta don ceton rayuwarta,

Yah Ameen ya kasa zama yayi nan yayi nan a bakin d'akin da aka shiga da ita Abba kuwa xama yai ya buga uban tagumi sosai ya ke tausawa rayuwar Naanah ya rasa me yarinyar ta tarewa Karimatu take mata irin wannan k'iyayyar,

Bayan likita ya fito ya tabbatar musu numfashinta ya daidaita yanzu ta sami barci ne sun d'aura mata k'arin ruwa,

Shiga suka yi d'akin Yah Ameen ya zuba mata ido idanuwansa sunyi jawul saboda tsabar 6acin rai,ji ya ke kamar ya me ransa duk ajagule yake,

Saida aka kira sallah sannan suka fita,masallacin asibitin sukayi sallah suna dawowa suka iske na tashi,ba abinda nake sai kuka,da sauri suka k'araso,Yah Ameen ya tallabo ni jikinsa ya na bubbuga bayana cikin sigar rarrashi yace"Please Naanah kiyi hakuri kukan nan ba abunda zai k'ara miki sai ciwo,

Na d'ago fuskata cikin kuka nace"Yah Ameen me na musu suka tsane ni nima fa jininsu ce meyasa sukemin hakan Umma bata sona bata k'aunata Yah Ameen me yasa please na lura kai da Abba kamar kuna 6oyemin wani abu don Allah ku fadamin idan ba Umma ce ta haifeni ba ku futo kusanar da ni don Allah!👏,

Ta k'arashe maganar da sakin wani gigitaccen kuka,gaba d'aya sai suka rud'e,cikin inda inda Abba yace"uhmm Naa..nah ki kwantar da hankalinki Ummarku ita ta haifeku dukanku,girgiza kai ta fara"uhm uhm Abba ina kokonto don ba uwar da zata dingawa 'yar cikinta haka,

Yah Ameen yace"haba Naanah ki kwantar da hankalinki maganar da Abba ya fad'a miki gaskiya ne,sadda kaina k'asa nayi ina matsar hawaye,Yah Ameen ya d'ago fuskata yana sharemin hawaye,

Da yamma aka sallame mu bayan ruwan da aka samin ya k'are,da sunce kwana zamuyi Yah Ameen ne ya matsa aka bamu sallama aranar,

Saida ya biya da mu wani babban Super Market ya min sayayya mai yawa,sannan muka biya gurin masu sayarda kayan marmari yasaya min muka wuce gida,

Da sallama na shiga farlourn amma ba wanda ya d'ago ya kalleni balle ya amsamin,kaina k'asa na wuce d'akina,inajin lokacin da Umma taja wani dogon tsaki mtsuww,nidai na shige da saurina,kan katifa na fad'a na saki wani sabon kukan ko sai yaushe hawaye zaibar zuba a fuskata Allahu a'a lamu,

Washe gari kuwa tun asubar fari Umma ta tadani,saijin ana maka min bugu nayi a furgice na farko tace"munafuka algunguma shegiya saiki tashi kin wani rashe rashe kina barci kamar kin sami gidan ub...sai kuma tayi shuru,a furgice na d'ago ina kallonta,hawaye ya k'wace min,cikin kuka nace"Umma me kika ce?,

Tace"to munafuka bance komai ba bare ki kaini gaba cewa nayi ki tashi kiyi aiki tunda ba bayi kika bari agidan ba,sannan ta fita fuuuu!sai da naci kukana mai isata sannan na tashi,na fita na fara aikin,wanke-wanke tun najiya da banyi ba ina asibiti sune tule ba wacce tayi duk sun bushe haka na zauna nayi sannan na share gidan na d'aura abinci,

Da rana 'yan uwan Umma wasu duk sunzo murnar sallah haka naci aikin girka musu abinci,ba godi bare na gode,

   Fateenku ce

  Ummu Affan✍🏽
🤰CIKIN WAYE?🤰


   ❤❤❤❤
        ❤❤
           ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)


AREWA WRITERS ASSOCIATION
____________________________

💦(Arewa ginshikin al'ummah)💦

____________________________


Bismillahir rahmanir rahim🅿1⃣7⃣-1⃣8⃣


🌿Ba godi bare na gode,har suka tafi,

'Da yamma muna zaune tare da Zainab a gidansu nace"Zainab abinda Umma ke min yana matuk'ar da muna,zuciyata na yawan bani cewa ba ita ce ta haifeni ba,Zainab ta share min hawayena tace"nima kaina wannan abu na d'aure min kai kuma ina zargin ke ba 'yar gidan bace,domin ba uwar da zata haifi d'a ta nuna masa tsana yadda Umma ke miki,

Na kalli Hajiya da ke zaune kusa da mu,kanta na k'asa saboda tausayin da takewa Naanah gaskiya ita kanta abun yana d'aure mata kai,nace"Hajiya daman mutum yana haihuwar d'a ya nuna bai k'aunarsa kamar yadda Umma ke min,

Ta kalleni cikin tausayawa tace"Naanah ba wanda zai haifi yaro yace bai sonsa kodai akwai abinda kike mata ne?,girgiza kai na fara ina hawaye,nace"Hajiya ba'abinda na ke mata a kullum burina in faranta mata ko na samu ta soni amma duk abinda na ke a banza bata gani yanzun ya zanyi da raina Hajiya,na k'arashe maganar ina kuka wiwi😭

Hajiya Tace"kin ta6a tambayar Abbanku kuwa?,nace"duk lokacin da abun ya da meni ina tambayarsa kullum maganarsa guda ce ita ta haifeni,Hajiya taja numfashi sannan ta dafa Naanah tace"kici gaba da hakuri Naanah watarana sai labari,share min hawaye kawai Zainab keyi tana kara bani hakuri,

****************

Zaune ya ke shi d'aya a farlour,yana tunanin Naanah matuk'a ya ke jin tausayinta gashi Umma ta musu shamaki tace yadena kula Naanah yarasa ya zaiyi,kimanin wata guda kenan rabunsa da gidan zuciyarsa ta gaza hakuri da rashin ganinta shiyasa yau yazo ya ganta ko zuciyarsa ta masa sanyi,

Da sallama na shugo farlourn sanye nake da uniform na islamiyya,ai kuwa karaf muka had'a idanuwa,muka k'urawa juna ido,ganin bazan iya jure kallonsa ba yasa na sadda kaina k'asa Yah Ameen yana da kwarjini sosai hakan yasa tunda na tsaya ko k'afata na kasa d'agawa daga inda na ke,gaskiya Yah Ameen ya had'u,yana da wata irin baiwa wacce inhar mace zata kallesa dole taji wani abu a jikinta,

Da k'yar na samu na d'anyi tafiya da niyyar in shige d'aki,har na kusan shiga sai naji yace"Naanah tsaya ina son magana da ke,tsayawa nayi chakk!,ni ban juyo ba kuma ban tafi ba,ya k'araso kusa da ni idonsa na kaina,yace"Naanah nasan yanzu kin girma kinsan abinda kikeyi,ina so ki tsaida hankalinki waje d'aya ban son gayyace-gayyacen samarin banza domin ba da kinyi (SSCE)za'amiki aure ba,ina son kici gaba da karatunki,ya d'anyi shuru tare da wani guntun murmushi sannan ya d'aure fuska yace"kinji na rantse miki wallahi na ganki da wani saurayi ko naji labarin kina kula wani sai ranki ya 6aci kina JINA!ya k'arashe maganar da tsoratarwa,

Da sauri nayi baya ina kallonsa,shi kuwa yana gama fad'a yayi juyawarsa ya fuce,na dad'e a tsaye cike da mamakin jin kalaman Yah Ameen na shiga jujjuya kalaman a raina,"toh me ya ke nufi wa yagayar mai ina kula wasu samari,ni banma kaina kallon wata budurwa tunda kwanan nan muka shiga (SS1)d'aga kafad'a nayi alamar ko ajikina,ni daman me son karatu ce ina da burin ganin nayi ilmi mai zurfi,

Washe gari ina zaune a farlour sai ga Abba ya shugo hannayensa d'auke da manyan ledoji,ya zauna kusa da ni yana murmushi,nace "Abba sannu da zuwa,"yauwa 'yar albarka,Umma ta kaida kai tare da ta6e baki tace"sauran ka kira su da 'yan tsiya tunda kai ke bada albarkar,ba wanda ya kulata cikin mu Abba ya mik'omin ledar da yashugo da ita yace......Fateenku ce👇

          Ummu Affan
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


  ❤❤❤❤
       ❤❤
          ❤


*Story and written by*
 *Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim

🅿1⃣9⃣-2⃣0⃣

🌿Abba ya mik'o min ledar da ya shugo da ita,yace"ga d'inkin nan da kayan saukar na amso miki,na kar6a ina dariya nace"kai Abba da kanka me makon tunda Yah Ameen ya sanar da ni gurin d'inki da ka barni na amso,

Yace"naga na biyo ta wajen ne shine da yace ya gama na kar6o miki,nace"nagode Abba ina k'okarin bud'e ledar,d'inki yayi kyau sosai daman kala uku ne Atamfa sai Shadda da Leshi kuma anyi min d'inkuna masu kyau,nace"gaskiya Abba sunyi kyau Allah ya saka da alkhairi,ya amsa da "Ameen,

Umma ta mik'e tsaye tare da buga wani uban tsaki mtssuuw!!,"Ayi dai mugani idan tusa zata hura wuta kuma ai k'arshen alewa k'asa,ta galla min harara tayi gaba,Abba yace"karki damu da wannan abun da tayi kinji,nace"ni Abba na rigama na saba da halin Umma,yace"kici gaba da hakuri har Allah ya kaimu lokacin da zata gano gaskiya,nace"toh,Abba Allah ya ganar da ita,ya amsa da "Ameen,

Na kwashe kayan na nufi gidansu Zainab don in nuna mata,ina shiga na iske ita ma murnar take an amso mata nata d'unkunan,nan na zube mata nawa,tana dubawa tace"kai Naanah kinga naki har sunfi nawa kyau,Yah Marwan yace"toh ya son ranki ita fa 'yar gatan Abba ce ke kuma 'yar gatan waye?,jikin Hajiya ta fad'a cikin shagwa6a tace"Hajiya kinga Yah Marwan ko!daman na lura yafi son Naanah a kaina,Hajiya tace"rabu da shi zanyi maganinsa,gaba d'aya muka kwashe da dariya,nace"amma ke Zainab d'innan 'yar shagwa6a ce,Yah Marwan yace"rabu da ita kawai Naanah ta girma ita bata san ta girma ba ai kuna gama secondry zamu mata aure,

Zainab sai kawai ta saki kukan shagwa6a,tace"ni wallahi ba wanda zai aurar da ni sai na zama cikakkiyar lauya don burina kenan,nace"da gaskiyarki Zainab ina goyan bayanki,Yah Marwan yace"Ok ni zaku had'awa kai,to ke Naanah me kike so ki zama,nace"ni yah Marwan burina in zama (Pediatric)likitar yara,yace"da kyau gaskiya kun burgeni Allah ya cika muku burunku,muka amsa "Ameen,

*** *** *** ***

Daman masu salon iya magana sunce Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya,yau makarantar tasu cike ta ke da manyan mutane,sakamakon gayyatar da a kayi ta yaye d'aliban makarantar,manyan malamai da attajirai 'yan kasuwa da 'yan siyasa duk sun cika wajen ga dandazon d'alibai,

Tuni aka fara gabatar da duk abinda ya dace,inda aka fara kiran 'yan sharar fage,daga bisani 'yan sauka suka fara,lokacin da a kazo kan Naanah zo kuji k'ira'a tana ba ko wanne harafi hakkinsa cikin karatunda sai kai tunanin muryar wata Balarabiyyar ce saboda tsak'in murya,

Bayan an kammala karatun ne sai a ka kira Naanah Firdausi Isma'il a matsayin wacce zata bada tarihin makarantar cikin harshen larabci,"uhmmm humm humm zo kuji murya,turk'ashi ai kowa gurin shuru yayi sai zazzak'ar muryarta da ke tashi,kowa zuciyarsa tayi sanyi sai sauraronta suke,

Wanda bai san Naanah sai ya d'auka ko Balarabiya ce,kai zo kuga kyaututtuka da Naanah ta samu domin ita ce tazo ta d'aya cikin jerin wad'anda sukayi saukar,Yah Ameen wani irin kallo yake mata wanda ita kanta ta kasa fassara irin wannan kallo,

Sun sha hotuna da 'yan uwa da abokan arziki da malamai abin dai gwanin ban sha'awa,sannan suka tafi da k'awayensu gidansu Zainab a nan zasuyi walimarsu,

An dai yi taro cikin jin dad'i da walwala sai fatan alkhairi

*****

Zaune ya ke a katafaran farlour wanda ke d'auke da kujeru na alfarma,wanda ke d'auke da kayan alatu na zamani,idan ka ga gidan sai ka d'auka wani shugaba ne ko me babban muk'ami a Nigeria,yana zaune ne d'aya daga cikin jerin kujerun falon wanda set biyu ne,zuciyarsa ji ya ke kamar zata buga,kwarai da gaske mahaifiyarsa ta kafa masa abinda ya ke ganin zuciyarsa ba zata iya d'auka ba,shi kansa yarasa wanne irin so ya kewa Naanah kuma son aure ya ke mata,yasan inhar hakan ta kasance yana da babban rikici nan gaba,kuma yad'au burin ko wanne irin rikici ne zai dauke sa indai a kan Naanah ne,

Domin rasa Naanah tamkar barazana ne da rayuwarsa


Tofah,shin wanene wannan ma da ya ke wannan maganar😂

Kudaici gaba da biyoni har yanzu bamu tsunduma ciki ba,

Fateenku ce👇
   

          Ummu Affan

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 11 to 20"

Post a comment