Results

CIKIN WAYE page 21 to 30

CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)


Didicated to Hussaini 80k


Kina raina Anty Hauwa,I luv u wujiga-wujiga_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿2⃣1⃣-2⃣2⃣


🌿Domin rasa Naanah tamkar barazana ne a rayuwarsa

Wata farar mace wacce baza ta wuce shekaru hamsin a duniya ba,ta sakko daga kan matattakalar benen da ke farlour,har tazo kusa da shi bai sani ba,ganinsa cikin irin wannan halin sai taji hankalinta ya tashi,

A hankali ta zauna kusa da shi tare da dafa kafad'arsa,yayi firgigit ya kalleta,d'an guntun murmushi yai yace"Momy kin fito,cikin a lamun damuwa tace"me ke damunka Al-ameem ka kasa sanar da ni?,yace"ba komai Momy kawai ina d'anyin wani tunani ne,kallonsa tayi cike da rashin gamsuwa amma ganin ya saki ransa sai tace"to banson kana irin wannan dogon tunanin,yace"nadena Momyna bazan sake ba,duka sukayi murmushi,

Al-haji ne ya sakko cikin shadda da a kawa d'inkin babbar riga,ya kalli Ameen yace"My Son ya ka kwana,yace"lafiya k'alau Daddy,yace"yanzu zan fita zamuyi wani meeting ne idan mun gama kasame ni Office,cikin ladabi yace"sai ka dawo,sannan ya wuce,Su kuma sukaci gaba da hira,

*******

Muna zaune ni da Yah Marwan a kan wasu kujerun roba da ke harabar gidansu,ya kirani ne wai yanason magana da ni,gaba d'aya munyi shuru saida baya ya kalleni sosai yace"Naanah nasan baki da saurayi,ko ince duk wanda yazo gurinki baki sauraronsa balle kuyi wata maganar soyayya,hakan da kike yi yana matuk'ar burgeni,amma ni na kasa daurewa saboda gaskiya Naanah tun kafin kikai haka nake k'aunarki tun ranar da na dawo karatuna naganki sai naji kin kwanta min,ina sonki kuma ina burin ki zama uwar yarana,

Kunya naji duk ta kamani,sai na duk'ar da kaina k'asa ina murmushi,ganin haka sai ya d'ago da fuskata muna kallon juna,yace"me kika ce?,

Na k'wace fuskata sannan na mik'e na ruga cikin gida,ikon Allah yace,sai kuma yayi murmushi,

Tun daga ranar sai na dunga wasan 6uya da Yah Marwan,ba wai don bansonsa ba kawai kunya na keji nace masa "na amince,kunsan abunku da saurayin fari shiga rai,

Duk ranar da kuwa yaci sa'a muka had'u,sai ya da meni da tambayar in basa amsarsa,ganin ba zan iya ba sai na tura masa test message,kamar haka,

   Aslm Yah Marwan ykk?,bawai bansonka ba ne a'a ina sonka amma ina so kayi hakuri domin Yayana yayi min gargad'i da kar in kula samari domin karatu zanyi,in har zaka iya jirana toh,bye daga Naanah Firdausi,

Tana gamawa ta tura masa,sai da ta tabbatar ya shiga sannan ta kashe wayar don karr ya kirata,shima da ya gama karantawa yaji dad'in sak'onta domin shi kansa mutum ne maison ilmi,ya d'aga wayar ya kirata yaji a kashe yasan kashewa tayi don kar ya ne meta,murmushi yayi yana bala'in son mace mai kunya,gashi Allah ya had'a shi da Naanah yarinya kyakkyawa ga hankali da nutsuwa uwa uba kunya da hakuri,Naanah duk ta had'a wannan a bubuwan,shiyasa yake bala'in sonta,

Zaune suke da Zainab a skul bayan sun futo Break fast,Zainab tace"waini Naanah meya tsakaninku da Yah Marwan sai naga kamar akwai wani abu,murmushi na d'anyi nace"uhm ke dai bari na mance ban sanar da ke ba,wai Yah Marwan sona ya ke,dariya tayi sosai tace"aini naga alama irin wannan zumud'in da yake akanki abun yayi yawa nasan da wata a k'asa,kallonta nayi"to ke yanzu ya kika gani,tace"wallahi nayi murna Allah yasa ayi damu,nace"Amin to,ta kaimin dukan wasa,tace"ashe dai ana so,nace"ke kanki kinsan Yah Marwan ya kai a so shi,tace"kin fasa karatun kenan sai aure,nace"a'a zanyi karatuna mana,gaba d'aya mukasa dariya,

Wata irin soyayya da shak'uwa ce tsakanina da Yah Marwan yanzu,sun shak'u sosai cikin k'ank'anin lokaci,saidai a kullum Naanah tana tsoran kar Yah Ameen yazo ya ganta da Marwan,ita kanta Hajiyarsu Marwan da taji abin ya mata dad'i don tana matuk'ar k'aunar Naanah da tausayin halin da take ciki a gidansu,

Marwan yana k'aunar Naanah bilhakki da gaskiya,yanzu haka ma suna tare,sak'on soyayya kawai suke aikawa zuna don ita ma Naanah yanzu ta cire kunya tana furta masa kalamon so don tana sonsa,sun shagala sosai suna hirarsu cikin nishad'i da begen juna,a haka motar yah Ameen tazo gurin basu sani ba,

Shi kuwa da ke cikin motar yana hangensu,ji yayi zuciyarsa na barazanar bugawa,wani irin abu yaji yana kaiwa da komowa a zuciyarsa,idanuwansa nan take sukayi wani jawur zuface kawai ke kwarara a fuskarsa......


Muje zuwa dai😂

  Karku manta Fateenku ce👇                      Ummu Affan✍🏽
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Masoya nima ina yunku,kamar yadda kuke yi da wannan littafin,ina sonku fiye da yadda kuke son CIKIN WAYE?,Fatana kuci gaba da suburbud'omin Comments d'inku yana k'aramin k'warin gwiwa,Ina yinku sosai,One luv💋
Bismillahir rahmanir rahim


🅿2⃣3⃣-2⃣4⃣


🌿Zuface kawai ke kwarara a fuskarsa,

Aransa yace"lallai nayi mugun sake amma...bai k'arasa ba ya fita a fusace,ya doshi inda suke zaune,basu ga taho warsa ba,saiji tayi an funcukota,kyakkyawar marin da taji Afuskarta yasa ta gigita jinta da ganinta suka d'auke na wucin gadi,wasu fararan taurari take gani saboda tsabar shigarta da marin yayi,cikin 6acin rai yace"Naanah yaushe kika koyi rashin ji,kenan maganar da na fad'a miki ta shiga ta kunnen dama ne sannan ta fita ta hagu,aijin muryar Yah Ameen yasa ta mik'e da sauri tayi ciki a gigice,

Ya kalli Marwan cikin izgili tare da ta6e baki yace"kai kuma a suwa don Allah ko kunya bakaji ba kazo k'ofar gidan mutane wai da sunan hira duka ya Naanah ta ke da zaka zo wai hira,to bari kaji daga rana irin ta yau banson sake ganinka da Naanah,Marwan ransa yayi mugun 6aci yace"Al-ameen kai baka isa ka rabani da Naanah ba don tana sona,nima kuma ina k'aunarta,kallon raini ya masa miskilanci ya 6otsa,k'ala bece masa ba yayi gaba abinsa,har zai shiga gida sai kima ya juyo cikin muryarsa ta isa yace"Ok muzuba mugani ni dakai,yana gama fad'a yayi shigewarsa,

Marwan ransa ya 6aci aransa ya fara shakku anya Al-ameen da Naanah ciki d'aya suka fito,don a maganganunsa tsantsar kishne ke tashi,d'an guntun tsaki yaja mtsuuww!ya wuce,

Ita kuwa Naanah a rud'e ta shiga cikin gidan tana zuwa ta fad'a jikin Abba tana kuka,Umma ta daka mata tsawa"ke da uban waye zaki shugo mana kina kuka,kan ta bata amsa sai ga Yah Ameen ya shugo rai a 6ace,yayo kanta zai duketa da gudu ta ruga bayan Abba tana ba shi hakuri,

"Don Allah Yah Ameen kayi hakuri bazan sake kulashi ba,ya dank'ota yace"idan kika sake kulashi fa,da sauri tace"ka kasheni kawai,tsaki yaja"ba zan kasheki ba amma sai jikinki ya gaya miki,cikin kuka tace"nayarda,nayarda wallahi nayarda,kunsan Naanah da shegen tsoron bugu,


Sakinta yayi tare da cewa "zabuwa kawai sai shegen tsoro,zaunawa yayi tare da gaishe da iyayensa,Umma aranta sai dad'i ta ke ji wai yau Al-ameen ne da bugun Naanah shi da baison a daketa ko k'uda inda da hali baiso ya ta6ata,,Abba yace"yau me ya had'aka da mutuniyar taka ne,yace"Abba rabu da ita kawai yanzu Naanah ta koyi rashin jin magana,Abba yace"Naanah har yanzu yarinya k'arama ce sai ana binta a hankali,Umma tace"haba dai ai Naanah ta wuce yarinya k'arama wacce ke SS2 aji biyar a secondry ai ta wuce a kirata yarinya,don da tasami miji aurar da ita za'ayi mu huta,

Da sauri ya kalli Umma yace"a'a Umma tunda Naanah tana son karatu to zamu bata wannan damar Rahma da Sakina sune zasu fiddo mazaje tunda sunk'i karatun kulum shekarunsu k'aruwa suke,yanzu Rahma shekarunta 26 Sakina ce me 23 ita kuwa Naanah sai wannan shekarar ta cika 17,

Harararsa tayi tace"to uban iya mace ake kira uwar iya amma kaima yau kazama uban iya kai ka haifarmin 'ya'yan to nida na haifi a bina ban gaji da ganinsu ba,Sakina tace"nidai Yah Ameen a kwai wani saurayina da yacemin zai turo,yace"to masha Allahu,ke kuma Rahma fa?,kai ta fara sosawa,kafin tace"babu,Umma tace"nifa karka takuramin yara kabarsu idan ta samu namaka magana,ke kuma basai kin takura kanki ba idan wanda kike so yazo saiki magana,tace"toh,

Abba tashi yayi yana girgiza kai cike da takaicin irin wannan hali na Umma,ya nufi d'akinsa,Umma ta kama Rahma suka wuce ciki,Ita ma Sakina tabi bayansu,

Daga ni saishi a farlour,ya maida kallonsa gareni,k'asa nayi da kaina na kasa had'a ido da shi,hakan yasa ya sami damar k'aremin kallo,Naanah kyakkyawa ce ajin farko balle yanzu da ta zama budurwa tana da cikar zati ko a cikin mata samun kamarta sai an tona,dole duk namiji mai hankali yaso ace ya sami kamar Naanah don ta tara komai da akeso,

A hankali ya tashi daga inda ya ke ya dawo kujerar da take zaune,ya ruk'o hannayenta suka had'a ido,tare suka saki a jiyar zuciya,yace"Naanah me yasa kika mance gargad'in da na miki,tace"don Allah kayi hakuri Yah Ameen bazan sake ba,kallonta yayi yace"Naanah kina sona kuwa?,da sauri ta kallesa jin abinda ya fad'a tace"me kace Yah Ameen,yayi saurin dawowa duniyar da ya fad'a tare da gyara furucinsa yace"cewa nayi kina son karatun nan kuwa?,ajiyar zuciya tayi,tare da gyad'a kanta alamar"eh,yace"to kar in sake ganinki da Marwan idan ba haka ba kuma sai mu aurar dake yadda Umma tace,yana gama fad'ar haka ya mik'e ya fita,

D'akina na shiga na fad'a kan katifa ina numfashi,wayata ce naji ta fara k'ara na jawo wayar,lambar Marwan ce kamar karta d'aga,sai kuma ta d'aga asanyaye,"hallo yace,a hankali tace"ina jinka Yah Marwan,yace"Naanah abinda kika yi kin kyauta kenan,tace"kayi hakuri yah Marwan kasan dama na sanar dakai tun farko Yah Ameen ya hanani kula kowa,kuma kaga dai yadda ransa ya 6aci gaskiya ni bana son ransa ya 6aci,yace"ok ni kike so raina ya 6aci kenan,"a'a ba haka na ke nufiba,"to me kike nifi Naanah amma ba komai,kawai ya kashe wayar,d'aga kafad'a tayi sannan ta gyara kwanciyarta nan take kuwa barci ya kwasheta.


      Fateenku ce👇


                  Ummu Affan
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿2⃣5⃣-2⃣6⃣


🌿Nan take kuwa barci ya kwasheta,

Ansaka bikin Sakina wata hud'u masu zuwa,Alh Babale matarsa daya da yara hudu shi zata aura yana sonta da tana masa wani gani-gani burinta ta sami saurayi amma ganin cikin samarin duk wanda tawa magana daga ranar bata sake ganinsa dole ta hakura,ba laifi yana da arziki don d'an kasuwa ne,

Yanzun mun shiga SS3 aji na k'arshen secondry zuwa lokacin Naanah ta wani ciko sosai ta zama cikakkiyar budurwa samari sosai suke kawo mata hari amma bata kulasu don tana son cika burin Yayanta,

Marwan kawai ta ke kulawa wanda ya gama fushinsa da kansa ya sauko ganin ita Naanah ko ajikinta shi kuwa yana mata son da bazai iya rabuwa da ita ba,sosai suke soyayyarsu amma a 6oye don bata son Yah Ameen ya sake ganinta da shi so take idan tagama saita fitar da Marwan a matsayin mijin da zata aura tuni suka yi alk'awarin hakan,

*** *** *** ***

Allah ya kawo mu bikin Anty Sakina wanda yazo daidai rana d'aya da na Anty Rashida yayar Zainab,sosai suka sha biki har taro yatashi lafiya,inda aka kai Anty Sakina Badarawa,gida d'aya suke da kishiyarta saida kowa da part d'insa,ita kuwa Anty Rashida kinkinau aka kaita sai addu'ar Allah ya ba ma'aurata zama lafiya Ameen,

Kwance ta ke a d'akinta tun wajen goma na safe ta ke barci sai wajen uku na yamma ta farka,wannan wanne irin barci ne ita kanta abin ya bata mamaki don bata ta6a irin wannan barcin ba,

Abinda kawai zata iya tunawa yau wajen k'arfe tara na safe Anty Rahma ta bata wani Fresh milk tasha tun daga lokacin bata sake sanin inda kanta ya ke ba,yink'urawa tayi da niyyar tashi amma sai taji ta kasa tashi,wani irin zugi ta keji ta k'asanta bata san lokacin da ta fashe da kuka ba,da k'yar ta rarrafa ta sa ruwa a hita don daman bata iya wanka da ruwan sanyi,

Ta dad'e tana gasa jikinta sannan taji dama-dama,ta d'auro alwala tazo ta gabatar da sallah tana istigifari ganin lokacin sallah har ya shige bata yi,jin ana kiran la'asar yasa ta tashi tayi,ta dad'e zaune a gurin jikinta takeji wani iri duk saitaji kamar ta wani abu yasameta,ganin tunani zai dameta ta tashi ta koma kitchin ta daura abincin dare daman su Umma sun fita gidan suna k'anwarta ce ta haihu,

Tun daga wannan rana sai Naanah ta dunga jinta wani iri,da haka harta samu suka kammala jarabawarsu wa Waeci da Neco,kamar ana jira sukama sai yawan kasala da amai ga tofe-tofen miyau,da barcin ba gairi babu dalili,

Yauma suna zaune a farlour Abba da Umma sai Anty Rahma,kwance nake kaina bisa cinyar Abba muna hira,ina hammar barci,Rahma ta zubo abinci tanaci,k'amshin abincincin da naji yasani tashi da gudu nayi waje bakin fanfo na fara a mai kamar zan k'arar da yayan cikina,

Da gudu suka biyo bayana,Abba ya rik'eni yana"subuhanallah meke damunki ne Naanah,saida na wanke bakina sannan nace ina haki"Abba banda lafiya bansan abinda ke damuna ba,Umma ta matso kusa da ni tace"ni nasan wannan farin da Naanah keyi a kwai wata a k'asa,ta kamo hannayena ta bud'e tafin hannuna,ta bud'emin ido tare da le6an bakina,

Ta sakeni da sauri tana tafa hannu tace"yau na shiga uku ni Karimatu Naanah badai ciki ne da keba,basu Abba kad'ai ba hatta ni abinda ta fad'a ya furgita ni,Abba yace"Karimatu ki iya bakinki sharrin naki har yakai kice Naanah ciki ne gareta to aniyarki ta biki,tace"zanyima k'arya ne to wallahi baza a haifar mana shege a gida ba,Abba yace"ranki zai 6aci aniyarki saidai ta koma miki,ya kama hannu na muka koma ciki ba abunda nake sai kuka,bayan mun zauna Abba ya kamamin hannaye cikin damuwa yace"Naanah ki fad'amin gaskiya shin maganar Ummanku gaskiya ce ko yaya?,Nan na sake fashewa da kuka nace"wayyo na shiga uku Abba wallahi ni bana da ciki,ya saremin hawaye yace "nayarda da ke Naanah nasan sharri take miki sako hijabinki inkaiki asibiti a dubaki ko shawara ce gareki,da sauri na sako muka wuce,Umma sai surfamin ashariya take,

Gwajin likita na farko ya tabbatar cewa ina d'auke da ciki na wata d'aya da sati d'aya,wata k'ara na saki na zube a gurin ina kuka da birgima,Abba kuwa ko motsi ya kasa numfashinsa nayin sama-sama,yana k'okarin d'aukewa,da sauri ni da likitan mukayi kansa nan ya fara masa temakon gaggawa,

Abba na kwance gadon asibiti yayin da Umma da Rahma suna tsaye ni kuwa zaune nake da6as a k'asa ina kuka,tun jiya da mukazo asibiti sai yau Abba ya farfad'o,kwatance nawa likitan yaje ya kira su Umma don yana da kyirki sosai,Abba ya bud'e idanuwansa,yana zubar hawaye yace"Naanah kin 6ata wayonki kin cuci rayuwarki wallahi kin bani kunya,banta 6a tunanin zakiyi hakan ba,


Umma tace"aini yarinyar nan duk naga take-takenta kuma wallahi kinji na gaya miki bazaki haifar mana shege a gida ba,kuka na fashe dashi na kasa cewa komai don tun jiya da likita yace cikine gareni nazama kurmar k'arfi da yaji ni sonake ms in tuna taya hakan ta faru,

Kwanan Abba biyu aka sallamesa muka koma gida,

A falo muka zube,Idan banda aikin harara ba abinda nake samu daga gurin Umma,dole na sadda kaina k'asa ina kuka,Abba ya kalleni yace"Naanah ina so ki fad'amin tsakaninki da Allah CIKIN WAYE?A jikinki,kuka ya sartsemin harda majina nace"Abba ina so ka fahimceni domin kai mai fahimta ne wallahi bansan ko CIKIN WAYE?A tare dani ba,

Umma tace"kuji munafukar yarinya kije ayi miki cikin kice bakisan ko CIKIN WAYE?ba to k'aryarki tasha k'arya yarinya wallahi ki fad'a mana ko yanzun nan in yanka ki.....  Uhmm,hmmm,hmmmm
Kudai cigaba da biyono


Fateenku ce👇

                Ummu Affan✍🏽
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿2⃣7⃣-2⃣8⃣🌿Wallahi ki fad'a mana gaskiya ko yanzun nan in yankaki,

A gigice na d'ago runannun idanuna na zuba mata,tace"kina ganin wasa nake ko mayya da shegun idanunta kamar na aljanu,da sauri na mayar dasu k'asa ina hawaye,

Umma tace"Rahma mik'omin wuk'ar nan a kitchin yau idan bata fad'i CIKIN WAYE?ba kasheta zanyi,Rahma ta nufi kitchin a gigice na tashi zan gudu ta rik'eni gam,Abba yace"Karimatu wannan wanne irin haukane,harara ta banka masa"ai gara ta fad'a musan ko waye tajecen gurinsa ta k'arata don ba za'a haifar mana shege a gida ba,ance duk gidan da aka haifi shege gidan ba a ruwan sama kuma mala'ikun rahma basa shiga gidan,

Abba yace"a'uzubillahi wannan wanne jahilin malamin ya fad'a miki hakan wallahi Karimatu kiwa kanki fad'a,cikin fad'a tace"na lura kai bakasan laifinta amma kana ganin abin kunyar da tayi so kake a dunga nuna mu a layi ko me?,yace"ba haka na ke nufi ba amma sai mu bita a hankali yadda zata sanar da mu ko,tsaki taja me k'ara tsuuuwwwwwww!!!,tace"kanka kuma a keji don wallahi bazan yarda a haifar mana shegeba,nan ta fara kimata kuka nake ina mata rantsuwa bansan CIKIN WAYE?ba,amma tak'i saurarata,

Ta sauta wuk'ar da Rahma ta kawo mata a wuyana cikin masifa tace"zaki fad'i CIKIN WAYE?Ko sai na kasheki,aini tunda naga wuk'ar nan a wuyana na tsure saboda tsabar tsoro,fitsari kuwa tuni ya fara juba ajikina,

Kuka nake kamar raina zai fita ina bata hakuri"wallahi Umma bansan CIKIN WAYE ba a jikina kimin rai kiyi hakuri,Abba ne ya taso ya ture Umma wuk'ar ta fad'i yace"kee!wacce irin mahaukaciya ce,ita ma a fusace ta tashi ta sake yowa kaina"ai gara in kasheta kowa ya huta taya zamu had'a shegu har biyu a gida,muna so murabu da k'aya za'a k'aro mana wani to bazai yuwuba,

Ganin ta tun karoni,nayi gurin Abba da gudu ina kuka na k'amk'amesa,jana yayi bayansa yace"Karimatu karki kuskura ki ta6ata,kallonsa tayi a wulak'ance ta juya ciki a matuk'ar fusace,

Zaunar da ni Abba yayi gefe dare da dafe kansa,duk'awa nayi gabansa cikin matsanan cin kuka nace"Abba ka yarda dani wallahi tallahi bazan CIKIN WAYE ba,bansan yadda akayi na sami wannan cikin ba,yau ni na shiga uku ya zanyi da rayuwata ya Allah ina rok'onka ka d'auki rayuwa ko na huta da wannan kuncin na duniya,

Da sauri Abba ya rufemin baki yana girgiza kai"Ki dena fad'in haka Naanah na yarda da k'addara nasan ke bazakiyi hakan ba Allah shine mafi sanin abinda ya faru da ke,ke kuma taki k'addarar kenan,

Wani matsanan cin kuka na saki tare da zubewa jikin Abba nace"nagode Abba da ka fahimce ni daman nasan kai mai fahimta ne

****************

Tun daga wannan rana rayuwata ta sake jagulewa,ina matuk'ar jin tasko gurin Umma da Anty Rahma,magungunan gargajiya kala-kala Umma ke d'uramin don cikin ya zube amma kamar ana k'ara masa ban ruwa fon beda alamar zubewa,

Gaba d'aya wankin gidan ni ke yinsa haka wanke-wanke,shara goga kai da duk wani aikin wahala har ruwa Umma ke aikena d'auka duk da yah Ameen ya mana bohol,amma Umma tace saidai inje waje in dauko,duk da k'udirinta na cikin ya zube amma ya k'i,

Yau kimanin watanni biyu kenan da faruwar hakan zuwa lokacin tuni nayi wata irin muguwar rama,k'ashin wuya ya fito sosai nayi duhu duk haskena amma na koma bak'a,saboda aikin wahala ga bugu ko ishasshen abinci ban samu a fad'ar Umma idan ina cin abinci da yawa cikon dole zaik'i fita,ko wayata ban takanta tun ranar da naji cewa wai ina da ciki wanda bansan CIKIN WAYE ba,na kashe wayar daman Yah Ameen yayi tafiya England a kan harkar kasuwancinsu,tun kan wannan abun ya sameta,

Tana kwance a d'aki bayan ta gama cin uban wankin da Umma ta sata,sai numfashi take yunwa takeji kamar zata mutu amma Umma tace yau sai na dare zata bata tun safe ba abinda taci,kuka take tana bugun cikinta da k'arfi,cikin kukan take cewa"ciki don Allah kafita yau na shiga uku ya zanyi da rayuwata shikenan burina na karatu bazai cikaba shi kenan nasan na rasa Marwan dan nasan bazai auri wacce tayi ciki ba shi kenan nasan Yah Ameen ya dawo kasheni kawai zaiyi,yau nashiga uku me yasa rayuwa kikazo min da haka meyasa hakan ya faru dani bayan ban ta6a aikata zina ba meyasa rayuwa ta take a haka ni bansan wani farin cikiba tunda na ke sai akasin hakan,me yasa...me yasa...Wayyo Allah kad'au raina kawai na huta da wannan mummunar rayuwar,ta kife taci gaba da kuka mai cin rai,

Sakina da tun d'azu tazo d'akin,sai jin hawaye tayi na tsiyayar mata,tunda tayi aure tayi hankali balle da ta had'u da muguwar kishiya me gasata son ranta,sai ta dawo tausayin Naanah da tausayawa rayuwarta sosai yanzu take jin Naanah cikin ranta,

k'arasawa tayi tare da dafata Naanah na juyowa ta rungume Sakina tace cikin kuka"don Allah Anty Sakina ki kaini inda za'a kasheni na huta wallahi na gaji da wannan rayuwar,da sauri Sakina ta rufe mata baki tace"A'a Naanah kar bak'in cikin da kike ciki yasa kiyi sa6o ki zamu me ta wakkali a duk kan halin da kika sami kanki Umma ta sanarmin ko mai Naanah na tausaya miki nasan halinki bazaki aikata hakan ba,amma ina mamakin taya hakan ya faru da ke,cikin kuka fuskarta har ta kumbura saboda kuka tace"bansani ba wallahi bansan taya hakan ya faru dani ba bansan CIKIN WAYE ba,

Sakina ta jinjina kai cike da tausayin Naanah tace"to ya isa kidena kukan haka,komai daran dad'ewa gaskiya zatayi halinta,nan taci gaba da sharemin hawaye......Wasa farin girki,muje dai zuwa fans,plsss sharhi nike buk'ata ba wani tnx ba,da fatan angane😎Lol ana tare,kar ku mance,

Fateenku ce👇              Ummu Affan✍🏽
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Fans I luv u,wujiga-wujiga,Farin ciki kune masu baiwa Fateemah,bak'in ciki in nai kusakani dariya,da na ganeku sai inji nazam sarauniya👸comments d'inku na jiya yasani farinki,
Wow jiya nayi tsalle da murna kunsani farin ciki da ina karanta Comments d'inku,aci gaba da gashi ina yunku irin sosai d'in nan❤💋 nagode🙏
Bismillahir rahmanir rahim


🅿2⃣9⃣-3⃣0⃣

🌿Sakina tana sharemin hawaye,sai ganin Umma muka yi ta fad'o d'akin kamar an turota,

Cikin fad'a ta kalli Sakina tace"Ehye yamiki kyau in zauna in sanar da ke abinda shegiyar yarinyar nan tayi shine kika zo kina rarrashinta kamar wata k'aramar yarinya,

Sakina ta kalli Umma tace"haba Umma ki kalli yadda Naanah ta koma ai abin a tausaya mata ne,cikin rage murya taci gaba da cewa"Umma ina rok'onki da Allah ki tausayawa halin da Naanah take ciki kiyi tunanin inda mune muke cikin wannan halin ya zakiji ki duba wulak'anci da cin kashin da abokiyar xamana take min nasan bakijin dad'i kuma...,

"Ya isa haka Umma ta katse Anty Sakina cikin tsawa da fad'a,tace cikin masifarta"ke kika so kuma ke kika k'yale kishiyarki da baki maganinta wallahi masifa da bala'i kawai idan kika rufar mata sai ki kori kafirar amma kin zama wata shashasha sakarya tunda kikayi aure sai kace kanki farau,Sakina ta kalli Umma cike da takaici wai uwarta ce ke fad'a mata sbinda ko k'awayenta bazata so su gayamata ba Umma ta gama cutarsu,

Tace"haba Umma don Allah kiwa kanki fad'a wallahi abinda kikeyi sam bai dacewa,wata ashariya da Umma ta saki ni kaina saida na toshe kunnuwana tace"to dan ubanki saiki zo ke kimin kujimin ja'irar yarinya ni kike gayawa magana Sakina saboda kinyi aure,tace"Umma don Allah kiyi hakuri ni wallahi yanzun na tuba duk wani abu mara kyau na dena na dama danayi ina roko Allah ya yafemin,ta kalli Naanah tace"kema ki yafeni Naanah ko na sami sassauci don yanzu nasan mugunta bata dad'i fitsarin fako ce,Umma taja tsaki"ke yadama ni babu ruwana,ta fita tana masifa,na jawo Anty Sakina nace"kiyi shuru ni ban ta6a ruk'arki a rainaba Allah ya yafemana baki d'aya,haka suka rungume juna suna kuka sosai,


Marwan ne sai safa da marwa yake a farlour,danna waya yake yana karawa a kunne alamar kira yakeso yayi yayi hakan yafi sau goma da alama wayarce bata shiga,sai guntun tsaki yakeja,Zainab ce ta sakko matattakalar bene,itamma cike take da damuwa,zaunawa tayi kan kujera tace"yah Marwan lafiya kuwa,mtsuuww yaja tsaki"wai Zainab lafiya naga ban ganin Naanah wallahi duk hankalina atashe yake gashi sai gwada kiran wayarta nake tak'i shiga,

cike da damuwa Zainab tace"nima ina cikin damuwar rashin Naanah kusan wata uku rabona da ita kasan halin Ummarsu kwanaki na shiga muka had'u a zaure wallahi idan kaga cin mutumcin da tamin sai kayi mamaki tace karna k'ara shugo musu gida,

Marwan yace"jikina na bani Naanahta babu lafiya ya zanyi Zainab wallahi inason in ganta,

Zainab tace"nima inason ganinta bansan yadda zamuyi ba lambarta bata shiga kullum sai nakirata fiye da sau ashirin,Hajiya ta k'araso wacce duk taji hirar da suke ta zauna sannan tace"Allah yasa dai tana lafiya fonni kaina abin na damuna Naanah bata ta6a kwana uku bata shugo gidan nan ba,bare wata uku,ta jinjina kai "uhmmm ni abin wallahi har tsoro yake bani Allah dai yasa lafiya,dukkansu suka amsa da amin cike da juyayi da tashin hankali,


Yah Ameen na hango zaune cikin wata luntsume miyar kujera ya k'ara wani haske da kyau na musamman sai shek'i ya ke idan ka kallesa baza kace wani abu na damunsa ba amma cike yake da damuwar son yaje gida,Naanahrsa na yawan fad'o masa sai yaji gabansa ya fad'i sosai,lumshe kyawawan idanuwansa yayi tare da shafa kyakkyawar sumar dake kansa,6are ledar chocolute yayi ya wurga bakinsa ya fara tsotsa,ya d'au remote yana cenza tasha,gabansa ne yaji ya buga da k'arfi lumtse idanuwansa yasakeyi tare da jawo wayarsa lambar Naanah ya nemo ya danna kira,amma abinda yaji baturiyar cikin wayar na sanar dashi wayar ya kashe take yasa shi k'walalo manyan idanunsa akan wayar,sake gwadawa yayi nan ma akaashen take,siririn tsaki yaja tare da cillar da wayar,ya zame kad'an ya mayar da hankalinsa ga TV,amma sai yaji ya kasa fahimtar komai,sake d'auko wayar yayi yasake jaraba kira bata shigaba,gashi k'irjinsa ya kasa dena bugawa,"Naanah"ya kira sunanta ciki Sweet voice d'inshi,ya duba wristwatch d'insa karfe tara ne na dare acen k'asar,da Daddy yaso ya kira ya fad'a masa gobe zai dawo amma ganin dare yayi sai ya fasa,yaci gaba da kallonsa da bai fahimtar komai sai tunanin Naanah da yacika masa zuciyarsa,

*******

Umma ce zaune a kan ruwan cikin Naanah tana bugu da kai naushi,cewa take "yau sai cikin nan ya zube na gaji wallahi bazan yarda ki haifar mana shege a gidaba kisa talauci ya mana sallama don duk gidan da aka haifi shege talauci ke musu katutu ga ruwan sama da ba'a musu,

Anty Rahma tace"nusheta da kyau  Umma shegiyar ko kunya bataji ba wai itace hardayo cikin shege a fuska musa a zuciya fir'auna,nishi nake sama-sama donko kuka nakasa numfashina da k'yar yake fita,saboda shak'ar da Umma ta min kakarin mutuwa kawai nake,ganin yanayin da nake ciki baisa Umma ta tausayamin ba.....


  Fateenku ce😂


                 Ummu Affan✍🏽

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 21 to 30"

Post a comment