Results

CIKIN WAYE page 31 to 40

CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Sorry Fan's jiya baku jini ba,karku damu ana tare,kuci gaba da biyoni,wasu cikinku suna tacewa suna son jin CIKIN WAYE?saurin me kuke kubini a sannu k'ila da kanku ma zaku gano,amma dai muje zuwa,akwai sauran tafiya ,ina jin dad'in comments dinku musamman masuyimin sharhi,inayi daku sosai,❤
Bismillahir rahmanir rahim

3⃣1⃣-3⃣2⃣


🌿Ganin halin da nake baisa ta tausayin ba,saima k'ara nusar cikin da take,cewa take "Wllh ni na gaji da wahala tsintacciyar mage ai bata mage,

Jin abinda Umma ta fad'a yasa na d'ago fuskata a waharce kukanma ya kasa zuwa sai na zuciya,d'agani tayi tanaci gaba da masifarta,na tattare guri guda kamar kayan wanki na cusa kaina tsakankanin cunyoyina,ji nake kamar girjina zai fito waje saboda bugun da yake,"tsintacciyar mage bata mage,na sake na nata kalaman Umma"to me take nufi?,na tambayi kaina amsar da nakasa ganowa,

Jan k'afata nayi zuwa d'aki ina tafe iska na d'aukata saboda tsabar ramar da nayi daman abu ga bamai jikiba,ga wani irin jiri da ke kwasata saboda rashin isasshen abinci,ina zuwa na zube a d'aki ina haki numfashina na sauka da k'arfi,

Wayata na jawo na kunna,kamar ana jira sak'onni suka dunga shugowa,na mutum uku ne Yah Ameen,Yah Marwan,sai Zainab,nata na fara bud'ewa ga abinda tace,

  "Naanah lafiya kwana2 baki ba dalilinki please sister don Allah kizo naganki,duk kin sani a damuwa karki manta shak'uwarmu tum muna yara Allah ne ya had'a soyayyarmu wallhi jinki nake tamkar ciki d'aya muka fito,gashi nazo harso ba adadi Umma na korana ke kuma kin kashe waya idan wani abu na miki kiyi hakuri sis.

Ina gama karantawa hawaye ya fara zubarmin "Allah sarki Zainab babu abinda kikayimin rayuwace ta cenzamin bansan yadda zaki d'auki k'addarar da ta fad'omin ba,Nima kina raina 'yar uwata,

Na Yah Ameen na bud'e,shi kuwa cewa yayi"Naanah meke faruwa kika kashe wayarki,ina fatan kina lafiya,I miss u ina kewar ganinki sosai ki gaishemin su Umma Abba da Rahma,

Share guntun hawayen da ya zubomin nayi tare da jan ajiyar zuciya"yanzu idan yah Ameen ya dawo yazanyi ni nasan kasheni kawai zaiyi yaji wannan labarin to CIKIN WAYE?zance masa idan ya tambayeni,nan na rushe da wani irin kuka ina bugun cikin wayyoni na shiga uku ya zanyi da rayuwata ko waye yamin cikin nan bazan ta6a yafe masaba,

Jawo wayar na sakeyi na dubo na Marwan shi kuwa cewa yayi"My luv me yasa me nayimiki kinsan halin da nashiga na rashin ganinki kuwa zuciyata tana cikin k'una rayuwata tana cikin jin d'aci ina cikin rashin lafiyar ganinki kuma kece kad'ai maganin wannan ciwon domin kallonki ganinki jinki sune zasu warkar dani,

"Wayyo Marwan d'ina nima kana raina saidai nasan idan kaji abinda nike d'auke da shi nasan rabuwa zakayi dani,na fashe da kuka ina nushin cikina fad'i nake"ciki don Allah ka fita meyasa ka zauna a jikina bayan kasan bai kamata kazo a irin wannan lokacinba,me yasa kayimin haka,me yasa kayi saurin zuwa baka bari saida nayi aure ba,a lokacin da ba wanda zai tambayeni NA WAYE?balle a takura rayuwata a lokacin da kowa zaiso ganinka me yasa kazo a lokacin da aka tsani jinka ko ganinka,(NI KUWA UMMU AFFAN NACE NAANAH TAKI K'ADDARARCE TAZO DA HAKA DOMIN TUN RAN GINI TUN RAN ZANE HAKA ALLAH YA TSARA MIKI),

Ina cikin wannan halin naji sallama a tsakar gida kamar muryar Hajiyarsu Zainab,da sauri na tashi ina layi kamar wata 'yar maye,na nufi tsakar gidan,abinda naji Umma na fad'a yasani dakatawa "munafukai azzalumai me kikazo yi mana a gida bayan kinsa d'anki ya gama lalatama yarinya rayuwa sannan zaki wani lalla6o wai kina nemanta to k'aryarku tasha k'arya kuna ganin ku ga masu kud'i kun isa kuyi komai a gari ba wanda zaice muku donme to kuje ku da Allah,

Hajiya naji tana cewa cikin 6acin rai"Karime kiji tsoron Allah 'ya'yayammu kiwone a wajenmu wallahi sai Allah ya tambayemu duk abinda muka aikata garesu,ke wacce irin uwa ce Karimatu ni wallahi tuni na gama gano bake kika haifi Naanah ba,amma ko bake kika haifeta ai d'a na kowa ne don kaima idan katemaki d'an wani kaima wani zai tai maki naka don bakasan inda zasu fad'a wataranba,

Cike da hargagi da sababin masifa Umma tace"eh d'in ba 'yar tawa bace ke saikizo ki d'auka kitemake tan kuma wallahi bakinki yasari d'anyan kashi kice yaranki zasu fad'a uk'uba wataran ba yarana ba,kuma ki barmin gida kafin inmiki babban wulak'anci magulmaciya kawai,

Hajiya ta kalli Umma cike da takaici kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta juya harta kai"k'ofa ta juyo,tace"wallahi na barki ne saboda nice nazo gidanki,Naanah kuwa da sannu Allah zai ku6utar da ita daga hannun muguwa irinki jahila kawai,

Kururuwa Umma ta saka tana zage-zage don taji zafin jahila da Hajiyar ta kirata,ita kuwa tuni Hajiyar ta fita ta barta tana zage-zagenta,juyowar da zatayi ta ganni tsugunne ina kuka,wani hauri da takaimin saida na kifa nan take goshina ya fashe,tace"munafuka ba ke kika jawomin abinda akazo har gidan mijina akamin ba,wallahi yau sai kinbar gidan nan bazan iyaba na gaji,

Daidai shugowar Abba yace"bazata bar gidan nan ba saidai ke kibarsa Karimatu,harara ta buga masa tace"ai idan kaga nabar gidan nan to saidai idan wani gidan ka sake ko kuma gawata,yace"to itama haka Naanah aure ne kawai zai rabata da gidan nan,ya jawoni yana min sannu,hannuna yarik'e muka shiga ciki,

Muna jin Umma lokacin da take fad'in"to ubanwa zai aureta wanne d'an iskarne zai auri wacce tayi cikin shege idan banda ma ta rainawa mutane wayau har tace batasan CIKIN WAYE?ba yo naga dai cikin nan ba'a ruwa ake shaba balle tace a ruwa tasha,

Ba wanda ya kulata daga ni har Abba,samun guri mukayi muka xauna a farlour,"Abba ya kalleni cike da tausayi yace"Naanah kici gaba da hakuri don Allah na rasa gane kan mahaifiyarnan taku kina gani dai nima ba lagamin tayi ba balle ku yaranta,kuka kawai nake ina dafe goshina,shima Abba ya dafe kai cike da damuwa yace"wannan wacce irin k'addara ce,Naanah Allah ya jarabceki da jarabawa iri da iri amma idan kikayi hakuri kikaci jarabawar da Allah ke miki nan gaba nasan zakiji dad'in rayuwarki kiyi hakuri addu'a itace makamin mumini ki dage muma munataya ki,

Kwantawa nayi jikin Abba ina kuka maganar kanta ta gagareni,addu'a yake min yana tofamin,


Hajiya kuwa bayan ta koma gida tasanar da Zainab da Marwan abinda Umma ta mata ko Naanah bata bari ta ganiba,Zainab ta fashe da kuka yayin da Marwan ya hasala yace"Hajiya wannan wacce irin muguwar matace ki bani dama yanzun na kira hukuma ta shiga cikin wannan lamarin,girgiza kai tayi"Marwan mubi abin nan a hankali ni kaina matarnan na bani mamaki da takaici wallahi da k'yar idan ita ce ta haifi Naanah,kuma inaga idan d'iyar 'yan uwanta ce idan sukaga abinda take mata zasu amshi d'iyarsu k'ila dangin Abbansu ce shiyasa take mata haka,

Cikin kuka Zainab tace"yanzu ko Naanahr bata bari kin gani ba kodai ta kashemin aminiya ne,tace"haba dai duk rashin imaninta ai bata iya kasheta ba,Marwan yace "wannan muguwar matar meye bazata iya ba,kawai ki bari inkira hukuma,Hajiya tace"karka kuskura ka fara duk abinda tayi kanta wata rana sai labari,haka Marwan ya fita cikin 6acin rai,Zainab kuwa ta kwanta jikin Hajiya tana rarrashinta

Yah Ameen ne na hango yana ta harhad'a kayayyakinsa da muhimman takardunsa na aikin da yayi a k'asar,sauri-sauri ya ke komai da alamar ana jiransa ne,rataya jakar yayi ya fito wata Taxi ya fad'a,yana zuwa filin jirgin kuwa yaji ana kiran suna yana jin sunansa ya nufi matattakalar jirgin yashiga,ba a wani d'au lokaciba jirginsu ya cilla sararin samaniya,sukayo kasarsa ta gado wato Nigeria......


Please sharhi nakeso,hakan zaisa na gane kuna gane inda na dosa,

Muje zuwa😂
Fateenku ce👇            Ummu Affan✍🏽
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


*Story and written by*
 *Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


_*MAMAN PHATYMAH ZARAH*_
_*Uhm Umma akwai ranar kin dillanci ai,ki kara hakuri naanah duk*_ _*tsanani sauki na nan zuwa,gaskiyarki Hajiya da danginta ne ai bata haka,amma dai muna*_ _*biye don warware mata zare da abawa mungode MARYAM*_
_*Wow luv u littafin CIKIN WAYE?gaskiya kin samoshi sister sosae,tau kenan naanah kinga takanki nidai ina tunanin ba uwarki bace akwai magana amma ba uwar da ta haifeta bace,tau ga yaya Ameen xuwa ko yaya zata kaya idan yaga Naanah a wanga hali muje zuwa Allah ya kara zakin hannu amin muna godiya,*_
_*FIRDAUSI JANAIDU*_
_*Wayyo Naanah Allah ya baki ikon cinye*_ _*jarabawarki ya kareki daga sharrin Umma da Rahma.*_

_*Gaskiya dad'in sharhin da kukaimin yasa na sakoko cikin page din nan,sannan na sadaukar da shi gareku,ina yinku irin sosai din nan💋*_


Bismillahir rahmanir rahim


🅿3⃣3⃣-3⃣4⃣🌿Misalin karfe biyar na yamma jirginsu yah Ameen ya sauka,Daddy da Momy ne sai direba sukazo tararsa,yana sakkowa ya nufosu sai washe baki yake yana jin dad'in yadda Daddy da Momy suke sonsa ko d'an cikinsu ne shi sai haka,

Jikin Daddy ya fad'a yana murmushi "Daddy na sameku lafiya,yace"lafiya k'alau my son sannu da k'ok'ari,"yauwa,ya amsa ya kalli Momy"Momyna ya kike,"Lfy qlau my son,ta amsa masa cikin nuna kulawa,gaba d'aya suka rugund'uma sai gida,

Abinci kala-kala ya iske Momy ta tanar masa,ya kalleta cike da k'auna irin ta d'a da uwa yace"Momyna sannu da aiki duk ni d'aya,murmushi tayi tare da shafa kansa tace"my son kafi gaban haka,ya rungumeta"ina godiya momyna,gaba daya sukayi dariya,

Bedroom d'insa ya wuce wanka ya fad'a toilet bayan ya fito ya shirya cikin k'ananun kaya jeanse da t-shirt,sosai yayi kyau,fuskarnan tasa sai annuri ke fita,

Farlour ya dawo ya iske su Momy na jiransa,dinning table suka nufa,harda Freeda wacce tazo takanas domin Ameen,d'iyace gurin k'anin Daddy suma nan cikin gari suke Malali GRA,sosai take k'aunar Ameen irin sosai d'innan,budurwace cikakkiya tana kimanin shekaru ashirin da biyar ta mace akansa inda harta kasa 6oye son Ameen dake ranta ta fito fili tasanar da shi haka iyayenta da su Daddy duk sunsan da zance,shi kuwa Ameen ko ajikinsa wai an tsikari kakkausa a salima ya tsani Fareeda saboda rawar kanta yayi yawa,'yar gata ce ta sosai mahaifinta yana da kud'i sosai nakece misali,shi da yayan nasa ma sai karasa gane wanne yafi wani kud'i,Fareeda tana karatunta a jami'ar jahar Kaduna(Kaduna State University)KASU tana karantar fannin jarida MASS COM.su hudu ne gurin mahaifinsu Fareeda ce babba sai Sayyed sannan Fahat sai k'aramarsu Autarsu Firdausi,sun taso cikin gata da soyayyar iyayensu,sun basu ingantacciyar tarbiyya da ilmi saidai Fareeda ta kasance daman ko a gidansu batada mutumci musamman idan kai talakane ta tsani talaka ko 'yan aikin gidansu hakuri suke da ita amma sam bata da kyirki ga wulak'anci da izgilanci,tun ranar da tafara ganin Ameen taji ya kwanta mata irinsa ne namijin da takeson aure ingarma,

Bata da kunya nan take tace"gaskiya Ameen kayimin irin kane mijin da na dad'e ina jira,mamaki maganarta ta basa ya wani mata kallon baki da hankali ko amsa ya kasa bata kunsan abunku da miskili,nan tacikasa da surutu harda tsara musu irin rayuwar da zasuyi idan sunyi aure(INA RUWAN DAGA GANIN SARKIN FAWA SAI MIYA TAYI ZAK'I),

Ganin zata basa ciwon kai ya tashi yabar mata wajen,tun daga ranar ta tsari zuwa gidan bayan ada sai ta shekara batazo ba,saida ya taka mata burki ta rage zuwa gidan ta matukar tsoron yah Ameen don ko kallonta yayi sai tajia jikinta amma tak'i kiyayarsa acewarta batajin zata iya rabuwa da shi,kuma tayi alk'awarin ko ta halin k'ak'a sai ta auresa,

Itace ta zubawa kowa abinda yakeso,kallon Ameen tayi cikin murmushi,"my luv me kake so,yi yai kamar baiji abinda take cewa ba ya kawar da fuska,Momy ce ta tashi ta zuba masa tana hararar Fareeda don Allah ya gani ba k'aunar halayen nan na Fareedar take ba,ita bama ta k'aunar Ameen yace ya auri Fareedar yarinyar da bata da kunya ko kad'an,hakan da Momy tayi ba k'aramin k'onawa Fareeda rai yayi ba,

Bayan sun gama suka dawo kan kujeru,Daddy fita yayi yacewa Ameen anjima yasamesa suyi magana,ba haka yaso ba yaso yanzu suyi maganar don yana son zuwa gida a yau yaga Naanahrsa amma ya ya'iya haka ya daure amma zuciyarsa na masa zafi,MOmy ciki ta shige,Fareeda na ganin haka ta dawo kujerar da Ameen yake,hannunsa ta kamo"Ameen nayi kewarka wallahi bansan ina sonka sosai ba sai da kayi wannan tafiyar gaskiya ka dad'e kusan wata biyar,fincike hannunsa yayi sai kyakkyawan mari da ya kifa mata,

Tadafe kumatunta da sauri tana kallonsa cike da mamaki,gyara zama yayi ya mayar da hankalinsa a TV,miskilancin ya 6otsa"ka mareni,Fareeda ta fad'a tana hawaye,kallonta yayi a wulak'ance yace"duk ranar da kika kwatanta irin haka wanda zan miki sai yafi na yanzu,

Mik'ewa tayi tana kuka ta shiga d'akin Momy,jakarta da mayafinta ta d'auka tayi waje a fusace,Momy na tambayarta"Lafiya?,amma ko juyowa batayi ba balle ta bata amsa,a matuk'ar fusace ta wuce ta6e baki Ameen yayi tare da d'aga jafad'a alamar ke yadama,jin ana kiran salla ya fita zuwa masallaci,

****************

Wani katafaran gida naga Fareeda tayi hune da k'arfi,da sauri me gadi ya bud'e mata sauran kad'an ta taka masa k'afa saboda yadda ta shugo da gudu,tana parking ta fito da gudu tayi cikin gidan,

Da k'arfi take kiran Mamee"Mamee"Mamee,wata farar matace na gani ta sakko matattakalar bene da sauri tana"Fareeda lafiya meke damunki,k'an nanta ma suka fito da sauri,haka Babansu,

Jikin mahaifinsu ta fad'a tana kuka sosai kamar wata k'aramar yarinya duk yabi ya rud'e sai tambayarta"lafiya yake,cikin kuka tace"Didi wallahi Ameen ne na fad'a maka yarda nake k'aunarsa takanas nayije don tarbarsa amma bayan bak'ak'en maganganun da yaimin harda mari,"Mari,Didi ya fad'a da k'arfi,gyad'a kai tayi cikin zubar hawaye,Mamee tsaki taja mtsuwww tace"wallahi nasha wani abunne ya faru ko kuma rasuwa akayi kike irin wannan kukan ai ni yayimin daidai Fareeda dama chasaki yayi tunda kedai baki da zuciya irin ta mata,tayi gaba tana k'orafi don halin nan na Fareeda yana damunta,Sayyed yace"babu mace mafi k'ask'anta a gurina sai wacce ta furtamin tana sona,fahat yace"wallahi kuwa ke Anty da za'azo ace ana sonki a matsayinki na mace saike kike tusa kai wallahi Allah ya k'ara dama bugunki yayi,

Nan tayi kansu da bala'i,aiko suka ruga suna mata gwalo daman sun saba,nan suka dunga kewaye k'aton farlournsu,kuka take haik'an irin na shagwa6a66u,su kuma suna mata dariya daga baya suka barta suka fice,Didi ya rik'eta yana bata hakuri"rabu dasu Fareeda k'annanki ne kuma ai ba haramun bane don kince kina son Ameen ra'ayinsu ne hakan,da haka yashawo kanta ta hakura,

Bayan wucewarta ya share hawayen dasu gangaro masa,Mamee da ke kallonsa ta k'araso ya zauna kusa dashi cike itama da damuwa tace"haba Alh kadena tuno abinda ya faru kasan kana da hawan jini ga ciwon zuciya don Allah kacire da muwa a ranka Allah zai nuna mana ita......


TOFA wakenan suke nema su kuma wad'an nan bayin Allah,ni yadda naga irin gidan da abubuwan dake ciki banyi zaton akwai wani abu da zai dami rayuwarsu,muje zuwa😂


Fateenku ce👇          Ummu Affan✍🏽
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


*Story and written by*
 *Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿3⃣5⃣-3⃣6⃣🌿"Allah zai nuna mana ita,taci gaba da sharemai hawaye itamma ji take kamar ta zubda hawayen,cikin raunin murya yace"sai yaushe?Rabi'atu ki fad'a min sai yaushe?kullum maganarku kenan za'a ganta me yasa haryau ba agantan ba,ni nasan 'yata ta rasu na fawwalawa Allah shekaru goma sha biyar da za'a gantan da tuni anganta,

Mamee ta kallesa kamar zata fashe da kuka tace"ina ji ajikina 'yata tana raye saidai ina yawan mafarkai marasa dad'i akanta ni kullum addu'a nake mata a duk inda tasami kanta Allah ya duba mata al amuranta,Didi yace"to amin,

Nan dai sukayi zaune suna k'ara jajanta abin,harsu Sayyeed suka shugo ganin iyayen nasu a irin wannan halin sunsan abinda ke damunsu,don haka zama suma sukayi cikin damuwa,Fareeda harda kuka don tana matuk'ar k'aunar 'yar uwarta,nan suka yi addu'o'i suka shafa,ko abincin kyirki suka kasaci haka suka kwana ranar cikin damuwa da bak'in ciki,daman duk ranar da suka tuno 'yar uwar tasu haka suke kasancewa,

"""""""""""""

Duk'e na hango Naanah tana wanki,tayi wani iri kamanninta duk sun sauya saboda wuya,Umma sai mgn take ya6o mata,ganin Ummar ta shiga ciki yasa ta jawo hijabinta da sauri ta fice,daman Anty Rahma bata,gidan,

Kai tsaye gidansu Zainab ta shiga bayan ta gaida me gadi ta wuce ciki da sauri,kici6is sukayi da Zainab zata fito,ai ganin Naanah yasa Zainab sakin kuka tare da rungumeta,sosai take kallonta"Naanah baki lafiya ne ramarnan taki tayi yawa wannan wanne irin ciwo ne kike,Naanah ta k'amk'ame Zainab cikin kuka tace"Zainab naga k'angin rayuwa,rayuwa tazomin da wani sabon yanayi ina cikin tasku da uk'uba,Zainab ji nake inama ba a duniyar nan nakeba ina ma zan mutu na huta da wannan rayuwar mara dad'i,wallahi na gaji da wannan duniyar inama zan mut....

Zainab ta rufewa Naanah baki cikin kuka tana girgiza kai"Naanah kar wata wuya ko tsananin da kike ciki yasa kiyi sa6o,Naanah ke musulmace ki yarda da ko wacce k'addara da Allah ya yimiki duk da bansan abinda ke damunki ba amma nasan ba k'aramin abu ne zaisa ki dinga furta irin wad'an nan kalaman ba,Meke faruwa Naanah ki sanar dani,

Wani irin kuka na saki nace"Zainab ciki ne da ni,a tsananin furgice ta kalleni tare da dafe girji,sai kuma ta fara girgiza kai tana cewa"k'arya ne duk wanda ya fad'i hakan k'arya yake miki Naanah tare muka taso dake tun muna yara nasan halinki kinsan nawa duk inda zamu tare muke zuwa boko islamiyya duk d'aya muke zuwa gidan nan kina shugowa indai bamu da makaranta kema naku ina zuwa saida Umma ta hanani shiga na dena zuwa idan harke kina da ciki to nima ina dashi,

Gaba d'aya kuka muke dagani har ita mun k'amk'ame juna,nace"Zainab da gaske nake,nan na kwashe komai na sanar mata har izayar da su Umma kemin,sosai take kuka kamar itace akace da cikin,

Nace"wallahi Zainab kinji na rantse banta6a sanin wani namiji ba bansan yadda akayi hakan ta faru daniba bansan CIKIN WAYE?ba Zainab koda kasheni za'ayi bansan CIKIN WAYE?ba ni kaina tambayar kaina CIKIN WAYE?nake,don Allah karki tambayeni basan nawaye zan ce miki ba,

Kuka muke sosai Zainab ta gyad'a kai"nayarda dake Naanah nasan bazaki ai kata hakanba duk wanda yayi miki haka Allah ya tona asirinsa,da amin na amsa,

Hajiya ta k'araso wacce duk hirar damuke tajimu,ta rungumeni cike da tausayi tace"Naanah na tausaya miki Allah ya saka miki,ni kaina na yarda dake,anyi amfani da wani abu ne aka gosar da tunaninki aka yi miki wannan aika-aikar amma karkiji komai da sannu gaskiya zatayi halinta ai k'arya fure take bata 'ya'ya,

Tuno abinda nake wato wankin da Umma tasani yasa cikin sanyin murya nace musu"zan tafi Umma batasan na fito ba kuma wanki tasani,Zaunar dani Hajiya tayi kitchin ta shiga ta had'omin tea mai kauri aiko jiki na rawa na amsa na fara sha,ta zubomin shinkafa da jar miya da nama zuk'u-zuk'u,sai ruwa a gefe,naci abincin sosai daman yunwar nakeji,sai kallona suke cike da tausayi,bayan nayi dam ni kaina sai naji jikina cikin dad'i rabon danaci abinci irin haka tun kafin wanna cikin daman san CIKIN WAYE?ba ya sameni,

Zainab ta rakani har k'ofar gida barabon mu had'u da Marwan yana Asibiti kunsan abunku ga likita bokan turai,

Naci sa'a har lokacin Umma bata fito ba,na duk'a naci gaba da'aikina,


Yah Ameen ne cikin moto yana tafe yanajin sautin wak'ar M-Shareef,cikin nishad'i yake harbin wak'ar yake"Soyayya idan har bakece ba,babu macen da zanso mi zaunawa tabbasssss,yayi murmushi har kumatunsa suka lotsa yace"Tabbasss Naanah babu macen da zanso muyi zaunawa idan ba kiba,ya dafe saitin zuciyarsa ya d'anyi d'an murmushi da ya tuno wani abu,zuwa cen kuma yayi shuru jikinsa kamar yayi sanyi,sai kuma yace"Ina k'aunarki Naanahta,k'ara sauri yayi don ya k'osa ya isa gidan yaga Naanahrsa,

A k'ofar gidansu yayi parking kamar kullum idan yazo gidan,sannan ya fito cikin takun k'asaitarsa ya nufi cikin gidan.......
Muje zuwa😂
Fateenku ce👇               Ummu Affan
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿3⃣7⃣-3⃣8⃣

Da sallama ya shiga ba kowa tsakar gidan,kai tsaye ya shiga farloun,"Assalamu alaikum,Umma dake zaune ita da Abba suka amsa masa,guri ya samu ya zauna,yana gaishe su,

Umma tace"mutanan waccen kasa meyema sunanta engula take kome,Ameen yasa dariya "kai Umma England ne,tace"to sannu da zuwa,Abba yace"ka dawo lafiya ya kabaro iyayen naka,yace"suna lafiya Abba suna ma gaisheku"tom muna amsawa,

Rahma ce ta shugo"lah yah Ameen sannu da zuwa"yauwa sarakan yawo daga ina haka?,sosa k'eya ta fara"uhmmm uhmmm Umma ce ta aikeni,Umma tace"kin dawo,"eh tace ta gode tana gaisheki,

Uhmmm Abba yaja ajiyar zuciya tare da girgiza kai nan take sun hada k'aramin film kai ka d'auka da gaske aiken nata tayi Allah ya kauta ya fad'a a fili,Umma ta zuba masa harara,

Yah Ameen ya mik'awa Rahma key d'in motarsa yace"ki bud'e but akwai kaya kisami almajirai su shugo dasu,ta amsa sannan ta fita,

Uban kayayyaki ne ake shugo dasu fannin na masarufi,buhun Shinkafa garin semo,katan-katan d'in taliya dana makroni jarkar mai da manja su maguna sai kayan lambu su kayan miya dasu kabeji,d'anyen nama da kaji yankakku,daman duk wata ne yake musu irin wad'an nan siyayyar shiyasa ya hana Abba fita kasuwa,amma duk da hakan yakan fita ya motsa jiki,

Sai kuma tsarabar England da yazo dasu akwatina hudune cike da kayayyaki na sawa dana kwalliya,Ya mik'awa Abba nasa"shaddoji ne d'in kakkaku da yaduka sai turaruka da takalma,yayi godiya yana samasa albarka,Umma kuma atamfofi da shadda itama takalma da hijabai dasu turare,Tayi godiya,ya ware d'aya yace"wannan na Naanah ne ke kuma Rahma kid'au wannan keda Sakina,

Umma ta yatsina fuska tace"ita Naanahr fin su Rahman tayi kome,dazaka bata d'aya su kuma d'aya su biyuh,cikin ladabi yace"Umma ita Sakina batana gidan mijinta ba,ita kuma Rahma naga tafi Naanah kaya,tsaki taja"kaiwai dai kace kafi sonta fiye dasu to wallahi barama kaji idan akwai wani abu a zuciyarka gami da wannan yarinyar gara tun wuri kacireshi aranka don bamai yuwuwa ba ne atoh nama fad'a maka,a gigice ya d'ago ya kalleta,

Abba yashafa kan Ameen yana murmushi yace"kwantar da hankalinka Aminullahi karka biye maganar Umman nan taku da bata da tunani,tace"ko mahaukaciya zaka kirani ka kirani amma ba zan bar d'ana ya auri wacce ta gama gantalinta a titiba ta gama sayar da mutuncinta a banza harda cikin shege munafukar wai batasan CIKIN WAYE?ba,

Ai yadda naga Ameen ya zaro ido😯ya mik'e tsaye da saurin cikin kid'ima yasani gyara zama don ganin abinda zai faru ni 'yar rahoto LOL

Hawaye ne ke zuba a fuskarsa cikin tsananin damuwa da al'ajabi yakecewa"ciki,ciki,ciki kuma Umma badai Naanahta ba don Allah Umma kice bada gaske kikeba,kallon banza Ummar ta masa tana wani hura uban hanci tace"to nayi k'arya don ubanka kujimin yaro ohww wo yanzu nagane inda kadosa kana nufin sonta kake to wallahi idan barci kake gara ka farka tsakaninka da Naanah ba aure,

Dafe kansa yayi dake barazanar tarwatsewa,nan ya fara ganin hazo-hazo,juwa ta kwashesa nan take ya zube k'asa,gaba d'aya sukayi kansa,

Naanah dake cikin d'aki tun zuwan yah Ameen tana la6e a window tana kallon duk abinda ya faru,jin Umma nacewa yah Ameen badai sonta yake ba kuma bazai aureta ba yasa zuciyarta ta fara rawa shin daman ita da yah Ameen ba ciki d'aya suka fitoba,to idanma hakan ne ita dashi waye ba d'an gidanba,sai tambaya takewa kanta bata da amsa,

Ganin tashin hankalin da yah Ameen ya shiga da akace ciki gareta ta sadak'ar yau sai gawarta tasan garin bugunsa dazai mata yau ita sai lahira,amma sai gani tayi ya fad'i ya sume,ai ta riga kowa dura gurinsa,

k'amk'amesa tayi tana wani irin kuka,"yah Ameen don Allah ka tashi karka mutu wayyo na shiga uku yah Ameen d'ina karka mutu kabarni,Wata irin funcika Umma tawa Naanah ta mayar da ita gefe cikin masifa tace"munafuka tunda kin saba chakumar maza dole ki chakume min yaro to rabu dashi tun kafin in kasheki in kashe banza,

Ai Naanah bama tasan abinda Umma kecewa ba tuni takoma jikin yah Ameen ta sake k'amk'ameshi tana kuka,Nan Umma ta hau bala'i,Abba fita yayi yasami wani yaro nan makota ya basa key motar Ameen saida ya kira matasa suka kama Ameen akasa shi moto suka nufi asibiti,Naanah zata shiga Umma tace"wucecen munafuka wallahi d'ana ya mutu ta silarki kema sai na kasheki algunguma kawai,

Agurin Naanah ta duk'e tana kuka mai cin rai,sauran mutanan gurin sai hakuri suke bata amma ta kasa tashi,Yah Marwan ne ya fito daga gida a mota ya hango wata duk'e a kasa tana kuka kamar Naanarsa da sauri yayi parking ya k'araso gurin,duk'awa yayi saitinta,"Naanah ya kira sunanta,da sauri ta d'ago ido hawaye na zuba fuskarta,shima kasa jurewa yayi sai hawaye cikin sanyin murya yace"Naanah lafiya meke faruwa dake?me kike a wannan gurin?,wani sabon kukan ta fashe masa dashi,da sauri ya d'agata daga gurin ya kama hannunta suka nufi gidansu,

Suna shiga ta fad'a jikin Hajiya ta saki kuka,bubbuga bayanta Hajiya ta fara tasa Zainab ta kawo ruwa mai sanyi ta tasha,bayan tasha sai ajiyar zuciya take"Hajiya tace"Naanah komai yayyi zafi maganinsa Allah sannan dukkan tsanani yana tare da sauk'i,kwantar da kanta tayi jikin Hajiya tace"Yah Ameen ne ya dawo Umma na sanar dashi abinda ya faru dani ya fad'i ko numfashi bayayi,ta k'arashe maganar tana hawaye,

Hajiya tace"kiyi hakuri Naanah Allah zai basa sauk'i,Marwan yaji zafin maganarta daman akan Ameen ne ta zauna atiti kamar wata mahaukaciya sabon kamu tana kuka,ha d'aure damuwarsa yace"menene ya faru dake?naga kin rame kinyi duhu kamar bakeba,lafiya kika dena shugowa gidan nan yanzu badan naganki waje na shugo dake ba da bazaki shugoba?,

Da sauri ta tashi zaune daga jikin Hajiya "ba kasan abunda ya sameni ba?,sai ta kalli Hajiya da Zainab duksnsu sukayi shuru,Hajiya cendai tace"Naanah wannan maganar ba abar ayi ta terere da ita bace,hawaye suka xubomin da gudu na fita don banson ina nan ma Marwan yaji abinda ya sameni,

Zai bini Hajiya ta kirasa,nan take sanar dashi komai,ai a gigice ya mik'e "ciki kuma amma Naanah ta cuceni saida ta gama sawa sonta ya shiga cikin zuciyata sannan ta yaudareni amma ba komai kanta ta cuta wallahi sai ta gane ni tawa wannan babban wulak'ancin sai ta d'and'ani zafi da azaba kamar yadda nima tasawa zuciyata........Fateenku ce😂👇           Ummu Affan✍🏽


Yawan comments yawan typing,Muje zuwa.
🤰CIKIN WAYE?🤰


      ❤❤❤❤
           ❤❤
              ❤


Story and written by
 Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)        💞'YAR GATAN AREWA💞


                 🤪🤪🤪


_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com


Alhamdulillah Alakulli halin👏Allah ina k'ara gode maka daka bani ikon kammala littafina me suna UWANIN QAUYE,kamar yadda kasa na gamasa lafiya Allah ka bani ikon kammala wannan lafiya👏Abin alkhairan dake cikinsa Allah yasa a amma fana dashi akasinsa Allah ya tsaremu dashi,wannan page d'in sadaukarwa na ga 'yan UWANIN QAUYE fans NAGODE da sayayyar da kuka nunawa littafin.Bismillahir rahmanir rahim


🅿3⃣9⃣-4⃣0⃣


🌿Da sauri Hajiya da Zainab suka kallesa jin abinda yake cewa,Hajiya tace"kana da hankali kuwa Marwan a tunani na kaine mutum na farko da zaka fara tausayawa Naanah amma Marwan kaban kunya ashe ba sonta kake ba,jin abinda Hajiyarsa ta fad'a yasa jikinsa d'anyin sanyi amma zuciyarsa tak'i aminta cewa Naanah batasan CIKIN WAYE?ba yama za'ayi ya yarda da hankan,

Yace"Hajiya ina kaunar Naanah saidai wannan abinda da tayi ya 6atamin rai har tasa zuciyata na shakku akanta ban yarda bata san CIKIN WAYE?,k'arya take wallahi kuma sai na rama abinda tayimin,yafita a fusace,

Hajiya girgiza kai tayi cike da takaicin kalaman Marwan,harga Allah jin Naanah take kamar 'yarda ta duk'a ta haifa,

""""""""""""

Naanah gida ta shiga ta kasa zama kuka kawai take,cike dajin takaicin hanata shiga mota da Umma tayi,ko wanne hali yah Ameen yake yanzu?ta tambayi kanta,bata da amsa ta zauna taci gaba da kukanta,saida ta gaji don kanta tayi shuru tunda ma me rarrashi,sai ajiyar zuciya take daga bisani barci 6arawo ya kwasheta a gurin,

"""""

Acen asibiti kuwa bayan isarsu nan take likitoci sukayi kan yah Ameen domin ceton rayuwarsa,suna nan sun kasa zama Umma sai masifa take"Wallahi wannan mayyar yarinyar ta kashemin d'ana namiji tilo bazan yarda ba wannan wacce irin rayuwa ce,an kwaso mana abinda zai cucemu,duk wad'anda zasu wuce sai kallonta ake wasu sun d'aukama ko mahaukaciyace sabon kamu😀,

Abba yace"Allah ya shiryeki Karimatu yanzu a cikin asibitinma sai kin nuna halinki,harara ta watsa masa"ai gaskiya na fad'a inhar Al-ameen ya mutu ita sai na kasheta,matsawa yayi cen gefe yace"bari na baki guri kar a d'auka tare muke,tsuwww taja tsaki"aikin banza harara a duhu kai kasani cen ta matse maka,Rahma bata ta6ajin haushin Umman ba irin na yau tace"kai Umma a asibiti fa muke nan ma saikin nuna halin naki,"kinci gidanku Rahma don kaza kazanki nayi ko zaki bugeni ne,

K'unk'unai Rahmar keyi ta koma kusa da Abba tana cewa"kya k'arata ke kad'ai,Umma ta mulmulo mata wata ashar,nan mutane suka hau magana,hakan yasa Umman yin shuru tana na ciki-ciki burinta ta koma gida ta k'are kan Naanah jira take likitocin su fito,

Wayar yah Ameen dake hannun Rahma ta hau ringing,Daddyna haka aka rubuta,ta amsa bayan ta gaishesa yake tambayar me wayar tace"Wallahi munanan asibiti an kawosa babu lafiya ko motsi baiyi,ai salati taji ya dauka ya tambayeta wanne asibiti ta sanar masa ya kashe wayar,

Ba'afi minti sha biyarba sai gasu a rud'e,Momy harda hawaye,nan suka gaggasa dasu Abba da Umma,Rahma ta gaishe su,

Zuwansu Daddy da minti goma likitoci suka fito suna share gumi,nan sukayi kansa gaba d'aya suka had'a baki"likita ya jikin nasa,murmushi yayi"jiki alhamdulillah mun samu ya farfad'o wani abu aka fad'a masa da yatada hankalin ko yagani,shiyasa ya sume amma gaskiya zuciyarsa akwai matsala amma zamu d'aurasa kan magani tun abun ba wani girma yayi ba,sannan da ya farko yana ta kiran ko Naanah yake cewa gaskiya idan tana kusa muna son da ya farko barcin da ya samu ya ganta domin inaga itace yake yawan tunani har yasama zuciyarsa ciwo,

Cikin takaici Umma tace"ai kuwa bazan gantaba idaiko Naanah ce kujimin ta k'adarin yaro au da ya farko bai kirani ko Abbansa ko 'yan uwansaba sai wata shegiya Naanah,da mamakin likitan yake kallonta haka su Momy,

Abba yace''za'ayi k'ok'arin likita rabu da matarnan mun gode,likitan ya wuce aransa yana tunanin anya matar nan bata da ta6in hankali,

Gaba d'aya suka shiga d'akin da aka kwantar da Ameen barci yake sakamakon allurar barcin da aka masa,Momy ta kira waya gida tacewa mai aikinta Lami ta shiryowa abin abinci mai ruwa-ruwa irin na marasa lafiya,

Wajen biyar na yamma Ameen ya fara bud'e idanuwansa ahankali,lokacin su Momy sun idar da sallah tuni suna zaune a tabarma da Lami tazo da ita da kuma abincin da takawo,Daidai kuma shugowarsu Abba sun dawo sallah danma sun dad'e zaune a masallacin suna addu'o'i,

"Naa"Naan"Naanah!!!,ya fad'i na k'arshen da k'arfi gaba d'aya suka mik'e sukayo kansa,suka rurruk'eshi,Bud'e idansa yayi ya zuba musu,sai kuma ya fara waige-waige,dafe saitin zuciyarsa yayi hawaye na zubar masa"ina Naanah,ya fad'a cikin wata irin murya mai sanyi ta marasa lafiya,

Umma cikin 6acin rai tace"kai wai wanne irin yaro ne,yauni na shiga uka ni Karimatu anya yarinyarnan ba shanye maka kurwa tayiba,Momy tace"Haba Karimatu meye hakan da wanne kikesoyaji ciwon da yake fama dashi ko masifarki,shuru tayi don ba kad'an take girmama Momynba saboda tasan akwai masu gidan rana balle yadda suka rik'e mata Ameen abin na mata dad'i,tace"ai Hajiya ne shi ya fiye cika ciki wallahi,

Daddy yace"Wai wacece Naanahr nan ne,Abba yace"K'anwarsa ce,Momy tace"anya k'anwa kad'ai kodai yana sontane,Umma zatayi magana Abba ya rigata fad'in "eh inaga dai yana sonta ne don komu bai ta6a sanar damuba,Momy tace"gaskiya yana sontane akawo ta yaganta Malam kar wani abu ya samesa,Umma tace"Hajiya ki bari kawai ba wani sonta da yake yarinyar da bata da tarbiyya cikin shegefa tayi,

Momy da Daddy suka kwararo ido😯😯tare suka furta"CIKIN SHEGE,Umma tace"k'warai kuwa shiyasa bansonshi da ita shine zaisawa zuciyarsa tunanin banza,sukace"gaskiya kam gara ya hakura ya nemo ta gari,

Ameen yasaki wani rikitaccen kuka yace"ba yarda za'ayi  Naanah taui cikin shege idanko har hakanne to CIKIN WAYE?,Umma tace"ohoo to wa yasani,kuka yaci gaba dayi kamar wani k'aramin yaro yana girgiza kai,su kuwa Daddy da Momy sai rarrashinsa suke amma yak'i shuru,

Wata tsawa da Umma ta buga masa gaba d'aya gurin suka toshe kunne saboda k'ara,harni dake gefe saida na tushe kunne,cikin fad'a tace..........Fateenku ce👇
               Ummu Affan✍🏽

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 31 to 40"

Post a comment