Results

CIKIN WAYE page 41 to 50


CIKIN WAYE?🤰


❤❤❤❤
❤❤Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿4⃣1⃣-4⃣2⃣

Tace"aikin banza kai bari gaji ba kuka ba ko gajijiyar mutuwa kake kabar ganin Naanah,kai bari kaji yau Naanah zata bar mana gida ba sai gobe ba,

Kuka sosai yasaka kai kace ba wannan Ameen d'inba mai taurin zuciya tsayayyen namiji yau shine ke kuka kamar wani k'aramin yaro,yace"Umma inhar kika kori Naanah to daidai yake da kirasani gaba d'aya,ina son kisani Umma Naanah ita ce farin cikin d'anki rasata daidai yake da rasa rayuwar d'anki,

Hannu tasa aka🙆tace"yau na shiga uku ni Karimatu Al-ameenu ni kake gayawa magana haka,sai takama kukan k'arya tana cewa"amma ba komai duk Malam kaine silah da baka goyawa Ameenu bayan barin yarinyarnan Naanah a gidaba da hakan bai faruba,

Daddy da Momy kallonta suke cike da mamaki Momy tayi k'arfin halincewa"wai Naanahr nan wacece ne haba Karimatu kina abu sai kace wata k'aramar yarinya,Abba yayi saurin cewa "gara dai kimata fad'a Hajiya k'ila idan taga kece kika mata ta d'auka,

Daddy yace"duk ba wannan maganarba yanzu mu bari Ameen yaji sauk'i sai muji komai,hakan yasa kowa yayi shuru,amma zuciyar Ameen cike take da farga ba tunani kala-kala yayi su akan cikin jikin Naanah,

"""""""
Da yamma Umma da suka koma gida ta iske Naanah kwance a k'asa tsakar gida tana barci,wani wawan duka ta buga mata"shegiya 'yar kaza-kazancen ta danno ashar,taci gaba dacewa"saboda tsabar jin dad'i zaki kashe Ameenu har wani barcin dad'i kike ko kenan ko ajikinki ko tunda kinaso ki nakasa masa zuciya ko,A furgice Naanah ta farka sai hawaye ta duk'a gaban Umma tace"wallahi Umma bansan barci ya kwasheni ba kiyi hakuri ya jikin yah Ameen,"ai dole barci ya kwasheki tunda kina cikin farin ciki,

K'asa tayi da kanta tana hawaye ita a ganinta ai tafi kowa damuwa da irin halin da yah Ameen yake ciki,Umma ta tureta ji kake gumm!ta kifa k'asa,cikin d'aure fuska Umma tace"ki tashi ki had'a yanaki naki kibar gidan nan tunda baki da gadonsa,da sauri Naanah ta d'ago kai"Umma ban gane ba?ta tambayeta,tsuww Umman taja tsaki tace"da sannu zaki gane yarinya tunda har kin fara lashewa Ameen kurwa to gara kibar gidan dangin mayu kawai,

Tuni kuka ya 6allewa Naanah,cikin kuka tace"to Umma idan nabar nan ina zani sai ki fad'amin dangina koda mayunne sai naje gurunsu tunda naka nakane kuma hannunka bai ta6a ri6ewa ka yankesa kajefar,wani wawan mari da Umma ta kifawa Naanah saida ta wuntsila ta kifa ta saki wani gigitaccen kuka,Umma ta nunata da yatsa"don ubanki ni zaki gayawa bak'ar magana,to karin maganar naki baiyi daidai ba a yau naka bai zana nakaba tunda inda naka nakane dayau kina cikin ahalinki,idan da kuwa hannunka bai ri6ewa ka yankesa ka jefar da iyayenki basu yankeki sun jefarba ubanmawa yasani ko shegiyace ke saboda kunyar duniya ba atsoron na lahira akayarda ke to wallahi yau sai kinbar gidan nan ba zamuci gaba da zama dakeba anyi cikinki a titi kema kinyi na titi Allah dai wadaran naka ya lalace,

Ai gaba d'aya kukanma nemansa Naanah tayi ta rasa,kallon Umma kawai take,rok'o take Allah yasa mafarki take ba ido biyu ba,Innalillahi wa'inna'ilaihir raju'un kawai take nanatawa a zuciyarta,biyu biyu kawai take kallon Umma da Anty Rahma dake hankad'ata waje,

Daidai tsayawar Abba ya sauka a keke napep,haka nan yaji tunda Umma suka taho yaji zuciyarsa bata amintaba yasan halin Umma sarai zata iyawa Naanah komai tunda bata k'aunarta,cike da tsoro yake kallon Naanah wacce kwata-kwata ma kamar bata cikin haiyacinta k'arasowa yayi da sauri ya tallabeta,Ganin Abban take ya kasu mata wajen biyar cikin rawar murya tace"Ab...Abb...Abba.da..daman baku kuka haifeni ba Umma tace bakune iyayena ba tace ni Tsintacciyace ni shegiyace iyayena suka yarda,

Cikin wani irin fushi dabansan Abba dashiba naga ya d'ago yana kallon Umma kuma daman kunsan ance mai hakuri bai iya fushi ba,Wani kyakkyawan mari ya zubawa Umma a gigice ta d'ago ta kallesa cikin fushi yace"daman Karimatu na fad'a miki duk ranar da kika sanarwa Naanah cewa ita ba 'yar gidan nan bace a bakin auranki,to kije na sakeki saki d'aya,

Ai wani uban kururuwa Umma tasaka"Wallahi bazan sakuba kuma babu inda zani tsofai-tsofai dani sai inje ince an wani sakeni to ba inda zani,yace"idan gidanki ne sai ingani,

Wata k'ara da Naanah ta saka yasa ya ruga da gudu girinta kafin yakai ta zube gurin a sume......


Fateenku ce👇Ummu Affan✍🏽


Share and Comments
🤰CIKIN WAYE?🤰


❤❤❤❤
❤❤Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿4⃣3⃣-4⃣4⃣D'agata yayi yana kiran sunanta,amma ina ko motsi batayi,Umma ko ajikinta wai antsikari kakkausa cewa mata ke"dama zata mutu ai da an rage mugun iri,Abba baibi takanta ruwa ya d'auko me sanyi ya zuba mata,dogon numfashi taja,sai kuma ta tashi a furgice,

Cikin kuka tace"don Allah Abba kace mafarki nake da gaske bakune iyayena,rungumeta yayi yana buga bayanta"Naanah ki natsu ki cire komai aranki k'addara ta riga fata,shiyasa nake yawan ce miki Allah ya jarabce ki da jarobobi masu yawa amma idan kikayi hakuri da ta wakkali sai kiga kin sami kyakkyawan rabo,

Kuka na saki tare da k'amk'ame Abba nace"shi kenan na tabbata shegiya me yasa iyayena suka kasa rik'eni suka jefar,"saboda ke shegiyace abar a guda,Umma ta fad'a,Abba ya mik'e cike da zafin rai,yace"Karimatu zo ki fitar min a gida,

Hannun Rahma taja zasu fice,Rahmar ta kwace hannunta"A'a Umma ba inda zani kedai ki tafi,harara ta bankamata"to nima ba inda zani asibiti zan koma don wallahi bazan bar gidan nan ba,ta fita fuuu!

Girgiza kai Abba yayi cike dajin takaicin Umma wannan wacce irin annobar matace,an sakekima bazaki bar gidan ba,lallai shima Allah ya jarabcesa ta hanyar auran Umma da yayi,

Haka yayi ta lalla6a Naanah akan tayi shuru tayi hakuri amma takasa ranar haka ta kwana kuka,kai tun tanayi da hawaye harma hawayen ya gaza fitowa sai na zuci,

Safiya nayi bayan Abba da Rahma sun tafi asibiti,Naanah ta shiga gidan su Zainab anan take sanar da Hajiya da Zainab komai,Salati Hajiya ta d'auka tace"ni na dad'e ajikina inajin ke ba 'yarta bace amms kiyi hakuri komai tayi kanta tamawa akwai Allah zakiga danginki nan kusa insha Allahu,jikin Hajiya na kwanta ina kukan zuci don idona tuni ya gama bushewa nace"Hajiya taya zanga dangina?aini kuma nasan a haka rayuwata zata k'are,Zainab tace"ki dena fad'ar hakan Naanah insha Allahu zaki gansu,

Nan suka dunga rarrashina da fad'amin da d'ad'an kalamai amma ina ni kad'ai nasan kunci da bak'in cikin da nake ciki,

Zan fito a harabar gidan mukaci karo da Marwan da sauri nayi k'asa da kaina zan wuce,tare gabana yayi yace"ina zakije munafuka,da sauri na d'ago na kallesa cike da mamakin jin kalamansa,d'aure fuska yayi tare da rungume hannayensa a k'irj yana min wani kallo wanda daga ganinsa na tsana ne yace"da kyau Naanah amma kin bani kunya kinsa naji na tsaneki kuma wallahi yadda kika bak'an tamin kema saina bak'anta miki,

Idanuwana na zubar hawaye na d'ago na kallesa"Yah Marwan idan kace haka bakamin adalci ba,kafi kowa sanin halina me yasa zakamin haka me yasa kakasa fahimta ta me yasa......da sauri ya katseta ta hanyar d'aga mata hannu✋"ya isa haka karki tarwatsani da wad'an nan kalaman naki da zasu cikamin kunne👂akan me zan yarda dake bayan kin bari samari sun gama yaudararki har sun k'umsa miki wannan k'umshasshiyar🤰wallahi tundaga ranar da naji abinda kika aikata naji na tsaneki Naanah kuma sai na rama abinda kikamin,

Zuwa wannan lokacin Naanah ta gama tsurewa da Marwan,kallonsa take tana kuka tarasama da wacce kalma zata fahimtar dashi batasan CIKIN WAYE?ba,muryar Hajiya suka jiyo kamar daga sama tana cewa"Marwan sai yau na yarda damancen ba kaunaR Naanah kake ba duk masoyi na hak'ik'a ba ya gudun masoyinsa a ko wanne irin hali d'aya daga cikinsu ya shiga,ka bani kunya ina ma ace ba kai kad'aine d'ana namiji ba yau da naba d'ayan Naanah amma ba komai ni nasan Naanah bazata tagaiyara ba akwai masoyi na hak'ik'a da gaskiya da zai sameta kai kuwa kayi asarar mace kamila da ko wanne namiji ki muradin samu,wannan cikin na jikinta wata kaddara ce da Allah ya rubuto mata kuma ko wanne bawa bai wuce kaddararsa,

Kama hannuna tayi muka koma ciki sai kuka nake muka barsa nan tsaye kamar ginki,shima part d'insa ya wuce yana shiga bedroom d'insa ya fad'a kan bed tare da rik'e kansa,duk abinda yake fad'a k'arfin hali kawai yake amma soyayya Naanah ba inda taje tanan zaune daram a zuciyarsa amma idan ya tuno ciki gareta sai zuciyarsa tayi k'una yajisa cikin bakin ciki,shifa bai yarda batasan CIKIN WAYE?ba,gashi shi kansa yarasa gane CIKIN WAYE?zaice tunda shidai tunda yake da Naanah bai ta6a ganinta da wani saurayi ba bayanshi,

Alh Mukhtar Salisu Sada da matarsa Hajiya Rabi'atu sai yaransu Fareeda Sayyeed da Fahat ne ke shiri don zuwa asibiti gaishe da Ameen,Fareeda tace"Didi don Allah kuyi ku fito nifa tuni nashirya,Mamee tace"kiyi gaba idan kin gaji bazakizo ba fa kitakura mana ki bimu a sannu,Didi yace"haba Mameen yara garadai kiyi sauri kinga don ita zamu surukinmu ba lafiya,Mamee tace"a'a wallahi ni badan ita zani ba,Sayyeed yace"bare ni kawai don zamu gaishe da Yah Ameen Didi saikace saboda ita,to ita a suwa,tuni Fareeda ta fara cika daman taji haushin maganar Mamme sai kuma ga abinda Sayyeed yace ta zun6uro baki gaba nan ta fara hawaye,Didi ya jawota cikinsa yace"rabu dasu Fareeda dani suke zancen duk bak'in cikinsu saikin auri Ameen,ta rungume Didiy kamar ba itace mai kuka ba tahau dariya"yauwa Didiyna shiyasa nake sonka,Fahat ya ta6e baki "son maso wani dai k'oshin wahala 'yan mata,Mamee tace"maganarka hakkun Babana,

Fareeda tayi kan Fahat zata daka,nan yayi ta wahalar da ita suna kewaye farlour,kan kujera ta fad'a tana kuka,Sayyeed yasa dariya"Anty Fareeda ba k'arfi sai tonon fad'a,kamar jira take ta sake sakin kuka shima tayi kansa,amma shima wanata yayi suna ta mata dariya jikin Didiy ta zube tana kuka,yace"Rabu dasu kai Sayyeed na fasa siya maka motar da kace kanaso kai kuma Fahat karatun da kace k'asar Misira zaka na masa kaika sai in gani,ai tuni suka dawo k'asan Fareeda suna bata hakuri,ita kuwa ta saki dariyar mugunta tace"yauwa Didiyna haka nakeso,

Sayyeed yace"haba dai my Antynmu kinsan bamu haka dake,Fahat yace"Anty Fareedarmu kiyi hakuri bamu sakewa,Mamee me zatayi ba dariya ba tace"kai Didiy gaskiya a ma yarana afuwa,kalon Fareeda yayi tace"tunda Mamee tasa baki to a musu,

Gaba daya suka rungume juna tare da addu'ar Allah ya nuna musu 'yar uwarsu,sannan suka shiga mota,Sayyeed yajasu sai hosbital.......Fateenku ce👇


Ummu Affan ✍🏽


Please Share and comments
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


❤❤❤❤
❤❤*Story and written by*
*Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_Bismillahir rahmanir rahim_


🅿4⃣5⃣-4⃣6⃣


Suna isa suka iske Abba,Daddy,Momy,Umma sai Rahma,sosai suka tarbesu cikin fara'a da girmama juna,da gudu Fareeda ta k'arasa gadon da Ameen yake kwance,an jingins masa filow a bayansa,ya rame sosai sai haske da ya k'ara,

"Sannu yah Ameen ya jikin naka,"da sauk'i,ya fad'a a hankali donshi yanzu ko magana baisonyi burinsa bai wuce yayi ido biyu da Naanahrsa,Su Didiy suka masa ya jiki,Sayyeed ya zauna kusa dashi yana gaishesa,shima Fahat haka,

Didiy yace"me ke damunsa ne,naga lokaci guda ya zube haka,Daddy yace"kadai bari yasawa zuciyarsa tunani gashi har ta kamu da ciwo,subuhanallah suka k'walalo ido gaba daya😯Mamee tace"ciwon zuciya kai kuwa Ameen wanne irin tunani ne wannan,Umma tace"haka kawai yasawa zuciyarsa tunanin yarinyar da bazai ta6a samunta ba,kallonta sukai yayin da Fareeda da sauri ta k'araso gabanta,tace"wacce yarinya don Allah karkice bani bace taya Ameen ya fad'a ciwon son wata ni yabarni😭kuka sosai Fareeda take,

Duka gurin suka bita da kallon Mamaki,Umma kuwa ta saki baki da hanci tana kallon Fareeda aranta tana fad'in wannan kyakkyawar yarinyar badai son Ameenu take ba amma indai ko haka ne duk yadda zanyi sai nayi ya aureta yaro arziki na binsa yanason kwaso tsiya,d'aga Fareeda tayi daga durk'usan da tatyi tace"kwantar da hankalinki 'yan mata kina son Ameenu ne,da sauri Fareeda ta d'aga kanta alamar eh,Umma tayi wani murmushi mai manufofi da dama,tasa hannu tana sharewa Fareeda hawaye tace"kisa aranki tamkar kin auri Ameenu share hawayenki 'yata,(Su Umma ba'a abu don Allah),

Gaba d'aya kowa kallonta yake cike da mamaki shi kuwa Abba murmushin takaici yayi don tuni ya gama gano manufarta nayin hakan,Didiy da Mamee sai sukaji dad'in abinda Umma tawa Fareeda kunsan mai d'a wawa,

Ameen kuwa aransa yasa har abada bazai iya auran Fareeda ba bawai don bata kaiba a'a shikawai Naanahrsa yake so kuma bayajin zai iya had'ata da wata,kai shifa a zuciyarsa babu sauran gurin da wata ma zata samu muhalli,

Sunci sa'a a ranar aka basa sallama badan yaji sauk'i ba sai takurar likitan da Ameen yayi akan ya sallamesa koshi ya sallami kansa,sosai Umma ta fara fad'a amma Daddy tace karta damu tunda baisan asibitin su koma gidan akwai likitan da zai dunga dubasa,

Koda suka kama hanya ya d'auka gidansu za'a kaisa amma sai yaga sun nufi gidan Daddy kamar yayi magana sai kuma yayi shuru ganin k'ok'arin da suke tayi kansa idan yace wani abu sai yake ganin kamar bai musu adalci ba,

Nan gidan Fareeda ta tare sosai take kula da Ameen,duk da Momy ke masa komai amma ita ma tana bakin k'ok'arin ganin ta faran ta masa,

Yana zaune a bedroom shi d'aya tunani kawai yake CIKIN WAYE?jikin Naanah wasu hawaye suka zubo masa yasa gefen hannu ya goge,

Wayarsa ya jawo ya nemo numberta ya danna kira,akashe take buturiyar nan ta cikin waya ta sanar masa,lumshe idanuwansa yayi tare da sakin wayar kan bed,Fareeda da ta dad'e da shugowa ta k'araso zaunawa tayi kusa dashi tare da sakin a jiyar zuciya,"Ameen"ta kira sunansa cikin sanyi murya,a hankali ya bud'e idanuwansa ya kalleta baice mata komaiba,ta kallesa ido cikin ido,tsigar jikinta taji na tashi tayi saurin kallon gefe,ta6e baki yayi,yasake lumtse idanuwansa kamar maijin barci,

Tace"Ameen me yasa baka sona?,bai tankamata ba taci gaba dacewa"nidai nasan nakai macen da kowa zaiso tu meye narasa,mud'e ido yayi yana kallonta,ta mik'e tana jujjuya baya tace"kalleni sama na k'asa nasan ko agasar kyau idan banzo ta d'aya ba to dole nazo ta biyu,mutane da yawa suna sona 'yayan manya da manyan attajirai amma nak'i bawa kowa dama saikai haba Ameen me yasa kake wulak'antani koni bankai macen da zaka kalla bane,

Cikin tsawa yace"ke!,sosai ta furgita,yace"baki kaiba kuma har abada bazaki kai macen danake soba,gara tun wuri kiba maneman naki dama su fito kafin damarki ta ku6uce,yana gama fad'ar haka ya juya mata baya,kuka ta saka me ciwo tafita da gudu,tsaki yaja tare da sake lumshe idanuwansa,wani abucen da ya faru wani lokaci yake tunowa,bai fad'a a filiba balle ni 'yar rahoto na ruwaito muku shi😄,

********************

Umma na gani bakin k'ofar gida tana ta surfa bala'i,"Malam kazo ka bud'emin k'ofa,banza yayi da ita yayin da ni da Rahma mukayi shuru musamman ni da nayi zuru-zuru,bugun k'ofar take sosai,

Na kalli Abba cikin fuskar ban tausai na had'e hannayena waje d'aya na d'aga a lamar ban hak'uri👏nace"Please Abba don Allah ka bud'ewa Umma k'ofa kayi hakuri ta koma gidan nan,kallonta yayi"yace"rabu da ita Naanah sai kace bata da dangi wannan masifar har ina,

Nace"kayi hakuri Abba Umma addu'a take nema,Rahma tace"Abba in bud'e mata don Allah kayi hakuri,bai magana ba,nasake rok'onsa "shike nan Naanah taci albarka cinki ki bud'e mata,cike da murna na bud'e mata k'ofar ko ba komai yah Ameen idan yaji Abba yasaki Umma bazaiji dad'i ba shiyasa tun kafin yaji gara ta kome,me zai faru?ai ina bud'ewa Umma k'ofa ta wani ban gajeni saida na bige da bango na wuntsila,harara ta bankamin tace"sanadinki Malam ya kwance igiya d'aya ta auranmu abinda tun muna yara bai minba to zaki gane kuranki wallahi,tayi ciki fuuuw!!,kakka6e jikina nayi tare dabin bayanta don zuwa yanzu yaci ace nasaba da halin Umma,

Zaune nake ina wanke-wanke,sai na dungajin motsi acikina sosai na tsorata na mik'e zunbur nasha wani abunne,ganin banga komai ba nasake zaunawa,wani motsin na sakeji wanda yafi na d'azun sake mik'ewa nayi na d'aga rigata,sainaga cikina ne ke motsi har wani harbawa yake,nan take hawaye suka gangaromin,Allahu akhbar duk wahalar nan danakesha ashe cikin nan shi lafiya ma yake k'arawa,ganin cikin bai girma sai na d'auka ko ya fucene saboda wahala ashe yanan,watansa biyarfa kenan,zaman da 6aro nayi ak'asa ina kuka ina bugun cikin,

Umma ta fito bina tayi da kallo kafin taja tsaki,sa6ar mayafinta tayi sai gidan k'awarta Asabe da tace ta samo mata wani magani mai k'arfi na zubar da ciki tace mata saidai Naanah bata shaba amma tanasha zai fita fittt!,

Cike da farin ciki na isa gidan bayan sun gaisa tace"Asabe naganar maganin nan nazo,tace"ai ina ganinki nasan da hakan,d'aki ta shiga ta fito da wani k'ullin magani tace"gashi saidai dubu biyar ne,saida Umma ta amshi maganin ta k'ulle a ha6ar zani tace"a'a Asabe bazamuyi haka dake ba dubu biyu zan baki,Asabe tace"wallahi bazan yarda ba kinsan atar da nasha kafin nasamo miki maganin na kibada hud'u da d'aribiyar,

Dubu uku Umma ta zaro tace"iya kud'ina kenan idan zaki amma sa to,Asabe ta amsa tana fad'in "k'aro d'aya,harara Umma ta ban ka mata tayi gaba tana cewa"idan basu miki ba saiki dawomin da kud'ina,har ta fita ta dawo"Asabe dame ake shan maganin,tace"jik'a mata zakiyi ta shanye ruwan,"to,tace tare da ficewa tayi gida cike da farin ciki a yau tasan cikin Naanah zai fice,

Tana shiga tasami langa ta juye maganin tass ta zuba ruwa ta rufe tana jiran ya jik'a.........Fateenku ce👇Ummu Affan✍🏽✍🏽Please Share and Comments.
*🤰CIKIN WAYE?🤰*


❤❤❤❤
❤❤*Story and written by*
*Fateemah Sunusi Rabee'u*
*(Ummu Affan)*

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Bismillahir rahmanir rahim


🅿4⃣7⃣-4⃣8⃣


Da yamma bayan na gama aikina,na idar da sallar la'asarr kenan Umma ta kirani,addu'a na shafa sannan na fito gabanta na duk'a "Umma gani,kallon banza tamin tace"Rahma mik'omin maganincen,Rahma ta kawo,mik'omin tayi tace"kafa kai ki shanye ki bani langar,

Kallon maganin nayi da yayi duhu sosai,runtse idona nayi don ni banson magani ko kad'an,balle wannan dana gansa wani iri sai naji zuciyata na tashi,kafa kai nayi idanuwana a kulle kur6a d'aya nayi na bud'e ido cike da tashin hankali saboda d'acin maganin,sam babu dad'i kamar mad'aci,

Nan na fara hawaye nace"Umma kiyi hakuri maganin d'aci,rik'e baki tayi"ehye ke harkina da za6in maganin da kike so kisha don zan temakeki na rabaki da alak'ak'ai to wallahi saikin shasa ko namiki d'ure,

Runtse ido na sake akaro na ba adadi na sake kaiwa baki,amma ina warin maganin ba kad'ai ya isheka,kuka na fashewa Umma nace"don Allah kiyi hakuri,

Mik'ewa Umma tayi cike da 6acin rai tace"Rahma kamamin yarinyar nan batasan halina ba har yanzu,cike da mugunta Rahma ta murk'ushe Naanah abinku da ban da ita ba kad'an ba sai Naanah ta kasa tashi,

Nan suka had'u suka murk'usheta suna mata d'uren magani,wani ya shiga wani yafita kuka kawai Naanah take tana neman matemaki,

Sakina tun daga waje takejin ihun Naanah da sauri ta shugo gidan,"Subuhanallah Umma, Rahma meye haka,nan tasamu ta ture Rahma taja hannun Umma wacce ta gama juyewa Naanah maganin nan tasss!,

Sakina tayi kan Naanah ta d'agaa"sannu Naanah,take fad'a,wani amai ne yazo mata ai dagudu tayi waje,suma duka suka bita,Umma fad'a take wallahi kika kuskura kikayi amai saikin biyani kud'in magani na bazakisa nayi a sarar banza ba,

Ina ai tuni Naanah ta dunga kwarara amai kamar zata amayar da kayan cikinta,Sakina ce kawai ke mata sannu,ta zuba mata ruwa ta wanke bakinta da jikinta,sannan Sakina ta gyara gurin,

Umma tacika tayi fammm!ta kalli Sakina tace"wallahi iska na wahalar dame kayan kara,ita dai Sakina bata kulata ba,ta kalli Naanah tace "ke kuma idan cikin nan bai zube ba saikin biyani kud'ina mayya kawai,Rahma ta dungureta tace"me halin mayu kindaiji kunya Naanah wai cikin shege,

Kuka Naanah ta saka don taji dungurin,bayan sun wuce Sakina ta zauna kusa da Naanah tace"Naanah kici gaba da hakuri don Allah wata rana sai labari,cikin kuka tace"maganar kenan kullum wata rana sai labari to yaushe labarin zaizo ni na k'osa inga yadda labarin zaizo,ta sake fashewa da kuka,Sakina ta rungumeta tana rarrashi,

******************

Kimanin wata biyu kenan da ciwon Ameen Alhamdulillahi jiki yayi sauk'i sosai saidai abinda ba arasa ba,kallon Momy yayi dake 6are masa lemu yace"Momyna yau ina son zuwa gida,kallonsa tayi''kai Ameen kusan kullum sai kace zaka gida ina hanaka don Allah ka bari jikinka ya k'ara sauk'i mana,yace"nifa Momy naji sauk'i sosai ba abinda ke damuna,girgiza kai tayi"bayan har yanzu my son ba kadena tunani ba,

Murmushi kad'an yayi"kai momy nifa na dena please ki barni naje gida yau badan niba👏ya had'a hannayensa guri d'aya alamar rok'o,murmushi tayi shikenan my son,amma ka bari Daddynka ya dawo,

Ba haka yasoba don ya k'osa yaje yaga Naanah da iyayensa akwai wani muhimmin abu da yakeson sanar musu,yace"shikenan Allah ya dawo dashi,ta amsa amin,

Yah Marwan ne zaune a farlournsa wayarsa ya ciro ya kira lambar Naanah yaci sa'a a kunne take,itamma kunna wayarta kenan wai tayi game ko ya d'ebe mata kewa ganin Umma sun fita bakowa gidan sai ita,kiransa ya shugo,gabanta taji ya buga,ta amma ta kara a kunne kasa magana tayi"Hallo Naanah,taji muryar Marwan,a hankali tace"Na'am ina kwana,yace"lafiya lau,sai kuma dukansu sukayi shuru,

Zuwa cen yace"Naanah kiyi hakuri da abinda nayi miki nakasa iya hakuri ne akan abinda kikayi amma nayarda ba laifinki bane,wani sanyi naji ya ratsa jikina jin yayarda dani nace"nagode yah Marwan da ka fahimceni,"ba komai yace,sannan yace"Naanah inason zamuyi wata magana dake mai muhimmanci,gabana naji ya buga da k'arfi nace"to,yanzu ko yaushe,

Yace"yanzu zan fita office amma idan na dawo zan kiraki sai ki futo mu had'u a waje,nace"tom shikenan,yace"nagode Naanah inaso kisa a zuciyarki Marwan yana sonki har yanzun i luv u,kawai naji ya kashe wayar,bin wayar nayi da kallo gabana na dukan uku-uku,

Wani ringing ta sakeyi,da sauri na d'ago YAH AMEEN ya fito 6aro6aro a fuskar wayar gabana yaci gaba da bugu,kamar kar in d'auka har takusan yankewa sai kuma na danna,

"Naanah"ya fad'a cikin muryarsa me dad'a lumshe ido nayi don yadda naji kiran sunan nawa dayayi yana ratsa jikina,cikin sanyi nace"na'am yah Ameen,yace"nagode da bakizo gaisheni ba Naanah meyasa baki damudani ba ko koda mutuwa nayi ko ajikinki ko,Tuni hawaye suka wanke fuskata cikin,muryar kuka nace"ya kakeso nayi yah Ameen nayi duk bakin k'ok'arina na ganin nazo amma Umma ta hana,"ya isa kinsan banson kukanki ko,don kukan nata har cikin zuciyarsa yake jinta,da sauri tayi shuru,tace"yah Ameen yaushe zakazo,

Shuru yayi zuciyarsa na harbawa yace"yau naso nazo amma Daddy har yanzu bai dawo ba ina ganin gobe inan zuwa sannan akwai wata magana mai muhimmanci da nakeson muyi dake a goben,gabanta ya buga da k'arfi,maganar Marwan ta tuna wacce sak babu banbanci data yah Ameen"kona jina kuwa,tace"ina jinka yayanah Allah ya kaimu lafiya"Ameen ya amsa sannan sukayi sallama,

Wayar take kallo bayan ya kashe yanzun gabanta tara tara yake bugu,tace Allah yasa duk alkhairi zasu sanar dani,haka ta wuni duk jikinta yayi sanyi,ta kira Zainab ta sanar mata tace"to Allah yasa duk alkhairi ne,ta amsa da ameen,sannan ta kashe wayar tana ta tunani ta k'osa goben tayi taji me zasu fad'a mata.......


TOFAH Fans nima saidai mu had'e goben donjin abinda Ameen da Marwan zasuwa da Naanah amma ku atunaninku me dukansu suke son sanar mata?

Uhmmm nidai ko......

To idan abinda nake tunani ne ko kuke tunani a cikinsu CIKIN WAYE?

Yah Ameen ko Marwan
Muje zuwa
Fateenku ce👇


Ummu Affan
🤰CIKIN WAYE?🤰


❤❤❤❤
❤❤Story and written by
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

Gaskiya masoya ina yinku oba jiya kawai da ba kuji littafin nan ba jiya wasu harta pc suna tambaya ko lafiya wasu harda kira,gaskiya nad'i dole ma yau namuku typing ko banso ana tare🤝I luv u masoyan Ummu Affan❤Ina sonku a duk inda kuke💞.Bismillahir rahmanir rahim


🅿4⃣9⃣-5⃣0⃣Haka ta kwana jiki duk a sanyaye sai takejin kamar wani abu ne zai sameta,tun asuba ta tashi kamar ko da yaushe aiyukanta tayi bayan ta idar da sallah,wajajen takwas na safe ta kammala komai,

Lokaci-lokaci tana duba wayarta ko Marwan ya kira,haka kuma tana yawan kallon K'ofa ko yah Ameen zai shugo,shikansa Abba yaga duk jikinta yau a sanyaye ta tashi yace"Naanah lafiya daiko idan kinajin wani yanayi kisanar fa,murmushin yak'e tayi wanda yafi kuka ciwo tace"Abba ba komai kawai yau na tashi naji ni haka gani nake kamar wani abu zai sameni yau,

Shafa kanta yayi yace"Naanah kiyi ta addu'a insha Allahu alkhairi ne kinji Naanahta,murmushi ta sake "to Abba,sannan ta kallesa"Abba ina so inje gidansu Zainab yanzu,yace"shi kenan saikin dawo,

Hijab na zura dogo har k'asa,daman tunda cikina ya fito dogayen hijabai nake sawa,gidansu Zainab na wuce,ina shiga ta rungumeni har muka kusan fad'uwa,Hajiya tace"waiku yaushe zaku girma Zainab baki ganin cike ne jikints idan kika kadata fa,kan kujera muka zube Zainab nace"ni wallahi mancewa nike da wani ciki,nace"murnar me kike haka,tace"yanzun nake niyar kiranki a waya sai gaki daman zan sanar miki na sami Addmision ne a Poly,hawaye suka zubomin ba wai na bak'in cikiba natayata murna nace"na miki murna Zainab ni kuwa da yin wata makaranta ai saidai ko alahira idan anayi,Zainab ma sai hawaye tace"wallahi naso ace tare zamu fara karatun nan amma ba komai karkicire rai da zarar kin haihu sai ki fara,nace"uhmm kedai bari kawai wanne karatu zanyi ni kuma bayan wannan abun kunyar ni wallahi ko k'ofar gida bansan fitowa tunda Umma ta gama yad'ani a unguwar nan,

Gaba d'ayansu sai kuka suka rungume juna,ita kanta Hajiya sai taji hawaye na gangaro mata,


***************

Ameen ne ke tashiri cikin wata bugaggiyar shadda marun ya feshe jikinsa da turarukansa masu dad'in k'amshi ya taje sumar kansa wacce sai shinning take saboda gyara da take samu,

Wow zo kugansa gaskiya yah Ameen ya had'u ajin farko ne kyakkyawa ne na k'arshe ga kyau ga cikar kamala haiba da annuri ga uwa uba kwarjininsa,


Farlour ya fito ya iske su Momy a dinning table suna breakfast,shima zaunawa yayi Momy ta zuba masa arish falantai sai wainar kwai da bread ta had'a masa tea,sauri-sauri ya ke karyawa,

Daddy yayi murmushi yace"Ameen duk saurin ne haka lallai ka k'osa kaje gida,murmushi yayi yana sosa k'eya,zaiyi magana saiga Didiy Mamee da Fareeda sunyi sallama gabad'aya suka juyo,Daddy ya tashi ya tashi ya taro d'an uwansa suka rungume juna"Mukhtar kaine kuke tafe,Didiy yace"ai kuwa,Momy tace"ku k'araso ku karya,ta fad'a cikin fara'a,Mamee ta k'arasa"kamar kinsan bamu karya ba wannan fitinanniyar ta sakomu gaba,ta fad'a tana nuna Fareeda wacce gaba d'aya hankalinta ke kan Ameen ya gama tafiya da imaninta,

Bayan sun gama karyawa Ameen ya mik'e yace"Daddy ni zan wuce,Kafin Daddy yayi magana Didiy yace"ina zaka,Daddy yace"gida zashi,Didiy yace"yauwa abin yazo gidan sauk'i muma daman gidan nasu mukeson zuwa,

K'walalo ido Ameen yayi😯aransa yana tambayar me zasuyi,don kar ace yayi rashin kunya ya kasa tambaya,Daddy yaji nacewa"ina fatan dai lafiya ko?,Didiy yace"Fareeda ta ishemu da ita Ameen take so jiyafa suma ta dungayi kuma duk akan Ameen shine yau da safen nan tasamu gaba wai saimunzo wajen Ameen,du kansu kowa yayi shuru Ameen ya zauna ja6al har ga Allah badan yana son Naanah ba da ya auri Fareeda kodan darajar iyayentas musamman ma Daddy saidai baijin zai iya,Daddy ya kalli Ameen yace"to kai ya kagani ni ina taya d'an uwana neman alfarman ka auri Fareeda,a gigice Ameen ya d'ago dukansu shi suke kallon ya saukar da kansa k'asa yace"Daddy bazan 6oye makaba wallahi akwai wacce nake so yanzun ma gurinta nakeson zuwa,yace"amma kace mana gida zaka,yace"eh gidanmu take k'anwata ce,shuru sukayi nawani lokaci kafin Didiy yace"kai namiji ne mijin mace hud'u inhar ka amince sai ka had'asu biyu,numfashi yaja dukansu yanajin kunyarsu,Daddy yace"idan Abbanka kakeji ku tashi dukanmu muje munemi alfarma,yace"a'a ba komai Daddy bama saikunje ba na amince,Didiy yace"mun gode karkaji komai daman munyi niyya zamuje musami Abbanka,numfashi yaja yace"tom shikenan,

Gaba d'aya suka d'unguma zuwa gidan Abba,Ameen ne kejan motar cike yake da tunani iri-iri ya yain da Fareeda ke kusa dashi cikin murna da farin ciki,

Suna isa yayi parking suka shiga gidan da sallama,Umma tana ganinsu ta hau washe baki"sannunku da zuwa sannunku maraba marhabin,suma cikin fara'a suke amsa mata,anan farlour suka zube ana gaishe-gaishe,Abba yace"sannunku,Rahma da Sakina da tazo itama tsohon ciki gareta suka gaishesu,nan aka kawo musu lemuka da ruwa,

Ameen ganin baiga Naanah ba wayarsa ya ciro yatura mata sak'o kamar haka


Naanah kina ina gani na k'araso baki gida,

Yana gamawa ya tura,lokacin suna zaune ne da Zainab Hajiya ta shiga ciki,sak'on ya shugo tana dubawa ta mik'e yayin da taji k'irjinta ya buga da k'arfi,innalillahi kawai take nanatawa,tace"Zainab zo muje yah Ameen yazo,mik'ewa tayi itama tasaka hijabinta mukayi waje,karo mukaci da yah Marwan yace"yauwa Naanah daman yanzun zan kiraki,tace"ohkey ina zuwa yanzun,yace"tom,ciki ya shige mu kuma muka fice,gabana bai dena bugawa ba haka muka shiga cikin gidan,

Mutanen dana gani a farlour nike bi da kallo suma ni suke kallo kafin wani mutumi daga cikinsu ya mik'e yana nuna Naanah da hannu👉🧕.......
My WhatsAPP no 08104335144

Muje zuwa Fateenku ce😂👇


Ummu Affan✍🏽✍🏽✍🏽

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "CIKIN WAYE page 41 to 50"

Post a comment