Results

MAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part A

NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part A
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Saurayi ne kyakkyawa ma'aboci kyawun
fuska, wacce duk ya
macen da yai arba da ita sai kware masa.
Babu komai ajikinsa face wata falmara ta
fatan zaki, falmarar
ba'a rufe madannin ta ba, hakan tasa dukkan
ilahirin kirjinsa a
bayyane yake a fili,
Gaba daya kirjinsa waje yake, hakan ce ta
bayyana surar kirar
jikinsa, ko ina ajikinsa a murmurde suke, a
yayin da wasu
guruna suka bayyana bisa tumbinsa kai kace
baya cin abinci ne.
A kasansa kuwa wata gajeriyar wando ce iya
guiwa , ya sanya

,rike yake da gabjejiyar itace a hannunsa .
Yana tafe yana waige waige koda zaici karo
da abinda ya fito
nema, kai da gani kasan wannan kyakkyawan
saurayin farauta
ya fito yi,
.
Yana tafiya yana gunaguni a cikin zuciyarsa
kuwa tunani yake
"wai yayane anya wannan karon da sa'a
kuwa, Ni dana ke fitowa
farauta na kamo manyan namun daji masu
ababen al'ajabi,
Kuma cikin kwanaki biyu rak nake kamosu
sannan na tasamma
gida,amma wannan karon gashi har na
tasamma kwanaki hudu
amma ko tsuntsu banyi arba da shi,
Maganar tasa ta katse a dalilin wani gurnani
daya ji,
Ai koda yaji wannan gurnanin sai ya cika da
farin ciki ainun
bisa ganin wahalarsa tazo karshe,
.
Gurnanin yaci gaba da kusanto shi, ta cikin
wata duhuwar
sarkakiya ne gurnanin ke fitowa.
Nan ya tasamma wannan sarkakiyar, koda ya
rage baifi saura
kadan ya karisa ba, kawai gani yayi wata
murgujejiyar damisa
ta fito daga cikin sarkakiyar ta bayyana a
gabansa,
.
Ya dubi wannan damisar sai ya ganta
lafceciya, sai yayi
murmushi sannan a fili yace da alamu dai
yau zan koma izuwa
gida da karamin nama.
Itako damisar sai dalalar da yawu take bisa
kasa,
Yau kwanakinta kusan goma kenan bata
dandani Nama ba ,
kullum sai ciyayi take ci
Toh yau ga tsuntsu daga sama gasasshe,
.
Mayunwaciyar Damisar tayi ruri sannan ta
fada kan jarumin
saurayin ,
Nan suka zube kasa gaba dayansu
Damisar tana bisansa sai kokarin farke
wuyansa take da

hakoranta, a yayin da shi kuma saurayin ya
rike habarta da
hannunsa, sannan yasa kafa ya taka ta , take
damisar tayi sama
yadda kasan an dauketa da majaujawa , koda
damisar ta fado
bisa kasa sai tayi wata irin kara sakamakon
jin zafin takun da
saurayin yamata .
.
Saurayin ya mike tsaye sannan yayi wata irin
tsayuwa irin na
Mazan kwarai,
.
Damisar na ganin haka sai ta kara dumfaro
shi da nufin tai tsalle
ta diram mai a wuya,
Koda tai tsallen da nufin ta fada akan
wuyansa sai kyakkyawar
saurayin ya sanya hannunsa guda . Ya rike
mata makoshi, sai
gashi murgujejiya kuma lafceciyar damisar
na wutsil wutsil a
hannunsa kai kace, masunci ne ya kama kifi.
.
Take saurayin ya daga damisar sama sannan
yai jifa da ita ,
koda yai jifa da ita sai taje ta gwaru da wani
babban bishiya ,
take bishiyan ya fadi rikica,
Wannan damisar ko shurawa batai ba,
Kyakkyawan saurayin yazo gaban gawar
damisar , ya tsugunna
da nufin ya sabata a kafadarsa yayi gida,
.
Ba zato babu tsammani kawai sai ya fara jin
Dirdir gowan wasu
abubuwa a bayansa,
Koda ya juya don yaga mene wannan.
Anan ne yayi arba da su,
Wasu gabza gabzan Arnan daji ne,
Su wayannan arnan dajin suna sanyene
warki na fatun
mesa,dukkanninsu kamanninsu da fasalin
surar jikinsu dayane ,
Lafta lafta ne ma'abota tarin damatsa babu
kaya a jikinsu face
wannan warkin na fatan mesa,
.
Daya daga cikinsu yazo gab da wannan
kyakkyawan saurayin
yace " yakai wannan kyakkyawan saurayin

kayi sani cewa ka
aikata babban kuskure a garemu wanda
hukuncinka shine kisa
mafi muni"
.
Cikin gadara saurayin ya dubi arnan dajin
nan wayanda
adadinsu yakai dari yace
"Ku sani ni bansan mai na aikata a gareku ba
da har zaku yanke
wannan hukuncin akaina "
.
Shugaban arnan dajin ya daka masa tsawa
sannan yai nuni da
dan yatsansa izuwa ga gawar damisar nan
yace "shi wannan
damisar daka hallaka , shine mafi kusanci ga
abin bautarmu,
duk wata bukata da muke da ita ga abin
bautarmu muddin muka
kama kafa da wannan damisar toh take abin
bautarmu yake biya
mana buka tunmu.
.
Kasani yakai wannan gafallallen saurayi, ako
wacce rana mun
kasance muna farauto ma wannan damisar
mutun daya don tayi
kalaci da shi,
Haka muka kasance muna yi har tsawon
wasu shekaru,
Kwatsam sai gashi an wayi gari mun fita
nemo wa damisar abin
kalacinta, har muka debi tsawon lokaci bamu
dawo ba,
Hakan yasa yunwa ya addebeta ta fito neman
wanda tsautsayi
ya kasa dashi, sai gashi ka kashe mana ita,
Abisa wannan mummunan zunubin daka
aikata mana ne
shugabanmu Boka Abulzulmu ya turo mu
damu yimaka kisa irin
ta wulakanci ,
Don haka ina umartarka daka bani kanka
cikin maslaha nai
maka kisan sauki, "
Koda jin haka sai kyakkyawan sauyarin ya
tuntsire da dariya,
sai da yayi mai isarsa sannan yace "Ashe ma
mugun iri na rage
A doron kasa kunga yanzu babu wata rai
dazata kara salwanta a

dalilin wannan Damisar"
Yana rufe bakinsa sai shugaban arnan dajin
yayi kukan kura
sannan nufo kan saurayin, hannunsa rike da
sharbebiyar takobi,
Koda yazo daf da saurayin sai ya kai mai sara
da nufin ya cisge
mai kai, cikin zafin nama saurayin ya sunkuya
saran tabi iska,
.
Kafin shugaban arnan dajin ya sake kaimai
wani saran . Sai
kyakkyawan saurayin yayi wuf cikin zafin
nama ya kirba ma
shugaban arnan dajin dundu a baya,
Nan take shugaban arnan dajin ya kwalla
kara sannan yayi taga
taga tamkar zai fadi amma sai ya tirje, take
ya furzar da jini
daga bakinsa.
Saurayin baiyi kasa a guiwa ba ya kama kan
shugaban arnan
dajin ya murde, karan karyewan kashi ta
bayyana, duk wata
gaba ta daina motsi ajikin shugaban arnan
dajin,
.
Kyakkyawan saurayin yai jifa da gawar izuwa
ga sansanin da
arnan dajin ke tsaitsaiye,
.
Wasu arnan daji biyu suka cafe gawan amma
sabida karfin jifan
da saurayin yayi da gawan sai da suka zube
kasa gaba dayansu.
.
Koda arnan dajin suka ga abinda saurayin ya
aikata ga
shugabansu sai dukkaninsu suka yi kururuwa
sannan suka zare
makamansu, nan suka rugo da gudu da nufin
su isa wajen da
saurayin yake su gididdibashi gida gida.
Shi ko saurayin koda yaga sun nufoshi sai
yayi murmushi
sannnan ya gyara tsayuwansa.
Koda arnan dajin suka kariso wajenda
saurayin yake sai sukai
mai rubdugu.
Shi ko saurayin koda yaga haka sai ya sanya
dukkan karfinsa ya
tarwatsasu, hohoho!!

Da mutum yana wajen yanaganin yanda
mutun daya ya gagari
daruruwan mutane lallai daya tabbatar da
cewa wannan
kyakkyawan saurayin ya cika NAMIJIN GASKE
mai tarwatsa
maza.
.
Arnan dajin sai kai masa sara da suka suke ,
shi ko ya wanzu
yana mai zullewa da gociya,
Babu abin da zaibaka mamaki da saurayin
face ganin ko
makami babu a hannunsa.
A duk lokacin daya samu arnen daji ya kirba
mai naushi ko
dundu. Nan take zakaga mutun ya fadi
wanwar akasa ko
shurawa bazai yiba
.
Sai da aka dauki tsawon lokaci ana wannan
fafatawan inda
saurayin yai ta ragargazar arnan dajin ,
Har ya samu nasarar karkashesu gaba daya.
Sannan ya dauki gawan damisar ya azata
bisa kafadansa, yayi
tafiyarsa
.
Tafiya yake har ya kawo bakin wata bukka ,
sannan yayarda
gawar damisar a kasa,
.
Ya nufi wani turki ya zauna ,
Zamansa keda wuya sai waya kyakkyawan
mace ta fito daga
cikin wannan bukkan
.
Wannan matar zata kai shekaru hamsin da
doriya amma in
kaganta kace yar shekara talatin da wani
abune.
Matar ta dubi saurayin tace dashi
"MUHAISIN sai yau kadawo"
Jarumin saurayin da aka kira da muhaisin ya
dubi wannan matar
yace
"Ummi na kenan kisani dadewar danayi ta
samo asaline daga
rashin samun dabbar danake nema"
.
Wannan matar sunan ta hamasiya sun
kasance suna rayuwa

acikin wannan kungurmin dajin shekara da
shekaru ita da danta
muhaisin
Tun muhaisin bai mallaki hankalin kansa ba
Ya taso ya tsinci kansa acikin wannan daji,
Tun baifi shekaru tara a duniya ba
mahaifiyanshi hamasiya take
ganin ababen al'ajabi a tattare da shi.
Don alokacin baifi shekara tara a duniya ba
amma sai taga ya
fita da nufin zai je farauta, in ya fita kuwa
baya da wowa sai
bayan kwanaki biyu
.
Nan zai dawo da manyan namun daji
wayanda ko rikakken
mafarauci ma sai yayi da gaske kafin ya kama
irinsu
.
Tun hamasiya tana al'ajabi har tazo ta daina
,bangaren jarumta
kuwa duk yawan abokan gaba tarwatsasu
yake, kuma shi baya
fada da makami don ko dabbobi ma wuyanzu
yake murdewa.
Tun da yake a rayuwarsa bai taba yin yaki ko
fada da makami
ba da zallan karfin damtse yake yakan ayari
guda na yan fashi,
da kuma gungun yan harin sumame.
Haryanzu da kwai wasu yanfashi dake
tarkonsa
Su yan fashin sun riga da sunsan yafi
karfinsu shi yasa da sun
hadu sai kaga yan fashin sun ruga a guje .
Ace warsu wai lokacin haduwarsu baiyiba
tukun idan lokaci
yayi su da kansu zasu nemeshi,
.
Alokacin da muhaisin ya mallaki hankalin
kansa sai ya fara
tambayar hamasiya mahaifinshi
Hamasiya takance da shi mahaifinsa ya rasu.
.
Alokacin da hamasiya tazo gaban muhaisin
don taga alamun
gajiya ajikinsa sai taga gefen damtsensa na
zubar da jini , nan
da nan hankalinta ya tashi ta yagi wani kyalle
dake rataye bisa
wannan turkin , sannan ta kama hannun
muhaisin tana daure

mai wannan raunin
.
Nan ta tambayeshi meya ji mai wannan
rauni,
Bai boye mata komai ba , ya labarta mata
artabonsa da arnan
daji
.
Koda hamasiya ta saurari labarinsa sai nan
da nan kwalla ya
cika mata idanu, koda muhaisin ya lura da
yanayin da
mahaifiyarsa ta shiga sai ya ce" yake ummina
shin ina dalilin
zubar da hawayenkinnan , "
Hamasiya tayi sauri ta share kwallan tace"
yakai dana kayisani
bako maine ya sanya ni zubda hawaye ba
face tuno da
mahaifinka da nayi, Lallai ka gaji mahaifinka
dana."
.
Muhaisin najin haka sai ya durkusa bisa
guiwowinsa yace" Na
rokeki ummina daki sanar dani labarin
mahaifina da kuma
dalilin dayasa muke rayuwa a cikin wannan
kungurmin dajin"
.
Koda jin wannan tambayan sai Hamasiya ta
mike tsaye sannan
ta nufi wannan bukkar koda tazo gab da
bukkan sai ta tsaya ta
dafa bukkan da hannu daya sannan ta juyo ta
dubi muhaisin
tace " yakai dana hakika yau kayi mani
babban tambaya ,
hakika bawai banason sanar dakai labarin
mahaifinka bane sai
dai, bana son tuna baya, bana son tuna
babban masoyina abin
kauna na" koda tazo nan a zancenta sai wasu
kwalla na bakin
ciki suka gangaro bisa kuncinta.
.
Muhaisin ya kariso wajenda take sannan
yace
"Ya ummina hakika kece kadai nake gani
nakejin farin ciki a
cikin  zuciyana, bana son ganin zubowan
kwallanki, bana son
jin labarin muddin hakan zai tsaida zuban

kwallanki"
.
Hamasiya najin haka sai ta tausaya ma
muhaisin ainun ta sanya
hannu ta tallafo habarsa tace
"Yakai dana kasani Mahaifinka Gawurtaaccen
Sarki ne Adali
mai jinkan talakawa,
Mahaifinka shike mulkin birnin Tehran .
Kamanninka dana mahaifinka sak babu
banbamci, Sunansa
Sarki HINZUR IBN HUMAS"

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "MAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part A"

Post a comment