Results

NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part E

Namijin gaske 1
Part 1E
(c) shuraih Usman
@shuraih 99%
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part E
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa
wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan
za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Koda magatakarda ya idda karatunsa sai sarki ya dubi dan sakon cikin murmushi yace "kagayawa
aminina ina nan tafe nan da kwanaki biyar
.
A washe garin ranar ne sarki hinzur ya shirya nima ya sanar dani, na shirya muka tasamma birnin
kufa dagani sai sarki hinzur da kuma dakaru goma kacal,
.
A tarihin sarki hinzur baya tafiya da dakaru masu tsaron lafiyashi, don wani sa'in ma shi kadanshi
yake shiri ya tafi rangadi,
Koda yan fashi, ko wasu muggan dabbobi sun tareshi kuwa, take yake tarwatsa su duk yawansu,
Muna tafe bisa dawakai nida mahaifinka a cikin wata daji mai dogayen itatuwa .
Kwatsam ba zato ba tsammani sai gani nayi sarki hinzur ya dakata,
Nima sai na dakata na dubeshi nace
"Yakai mijina kuma abin kaunata shin ina dalilin tsayuwarka acikin wannan dokar daji mai mugun
yanayi" murmushi kawai yayi sannan ya bingiro kasa, yafado daga kan dokinsa,

Toh anan ne naga abin daya tayar mani da hankali, acaccake a bayansa kibau ne har guda biyar,
Koda ganin haka sai na sauko bisa dokina , sannan na karisa wajen dayake kwance bakinsa sai
aman jini yake,
Na tallafo kansa ina mai fashewa da kuka, su ko dakarun da muka fito da su suna zazzaune bisa
dawakansu.
Nan na daka musu tsawa kan cewa su fara binciken wanda yayi wa sarki haka.
Wani daga cikinsu ya bushe da dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya dubemu yace
"Kusani yaku wayannan sarakan yau kam kun gamu da ajalinku"
Sarki hinzur najin haka sai yayi wuf ya mike yayi tsayuwa irin ta manyan sadaukai tamkar babu
abinda ya sameshi, sannan ya zaro takobinsa yace da wayannan dakarun
"Ai NAMIJIN GASKE baya faduwa kasa banza, shin kuna tsammanin wayannan kibau din da kuka
harbeni da su zasu illata nine hakika kunyi babbar kuskure domin kuwa jinake tamkar Allurai kuka
sossaka mini"
Yana gama fadin hakan ya falfala da azababben gudu don ya isa wajen da suke, ai koda ya rage baifi
saura taku biyu ba tsakaninsa da su sai ya daka tsalle sama , ya sanya kafafuwansa ya doki dakaru
biyu dake kan doki , take suka fado kasa daga kan dawakansu.
Cikin zafin nama ya sanya takobinsa ya guntule kawunansu.
.
Koda sauran dakarun suka ga haka sai suka ruga aguje don su tsira da rayuwarsu, duk sun kasance
suna kan doki shi kuwa sarki hinzur bisa kafafuwansa ya falfala aguje don ya cimmusu,
Nan dai aka kasa tsere tsakanin dakarun da kuma sarki hinzur
Cikin kankanin lokaci ya cimmusu, nan take ya daka tsalle sama a samanne tun kafin ya sauko kasa
ya sanya takobinsa ya shaftare makwogaron dakaru uku nan suka fadi matattu.
.
Koda ganin haka sai sauran dakarun suka zage damtse sai gudu suke a yayin da shi kuma sarki
hinzur ke biye da su abaya, koda sarki hinzur yafara jin gajiya , sai ya yar da takobinsa sannan ya
kwala ihu wanda ta haddasa karamar girgizar kasa,
Take tsuntsaye suka ringa canja sheka,
Take dawakan da dakarun suke kai suka firgita ainun da wannan ihu, nan suka tsaya cak suka ki
gaba sannan suka ki baya, a haka sarki hinzur ya kariso ,
Koda zuwansa sai dunkula hannu yaiwa doki daya naushi take dokin ta fadi akas sumammiya
Cikin zafin nama ya cafe wuyan badakaren daya ke kai sannan ya murde
.
Cikin kankanin lokaci duk ya karkashe wayannan dakaru
,
Koda yagama kashe su sai yazo inda nake a durkushe ina kuka
Ya mika mani hannu don na mike tsaye
Kawai sai gani nayi kibau ta hudo ta gadon bayansa ta fasa kirjinsa cikin azama na mike na
tallafeshi ina mai kiran sunansa cikin karaji,
.
Ya lumshe idanuwa sannan yace " yake abar kaunata hakika naji bakin cikin rabuwar da zamuyi na
umarceki daki gudu don ki tsira da rayuwanki"
Cikin sheshshekan kuka nace mai"yakai miijina alfaharin qalbina,kayisani babu abinda zaisa na
rabu dakai a kowanni hali ka tsinci kanka aciki duk rintsi duk wuya ina tare da kai ,
Ko mutuwace ta zo daukarka toh sai dai ta dauke mu gaba daya "
Ina gama fadin hakanne sai muka ji an bushe da dariya a bayanmu, koda muka juya sai mukayi arba
da waziri humaiz shi da dan fashi kallabu sai kyakyata dariya suke,
.
Nan take hawayen bakin ciki ya zubowa sarki hinzur ya dubeni yace
"Na rokeki da ki gudu don ki tsira da rayuwarki..." Maganar tasa ta katse a daidai lokacin da wata
kibau ta cake sa acinya
Nan take ya fadi kasa yana mai aman jini,

Yasake cewa " ki gudu ki tafi ki barni"
Ba don son raina ba haka na falfala da gudu nayi cikin dokar daji, koda kallabu yaga na ruga sai
shima ya biyoni,
Koda ya zo wucewa ta gefen sarki hinzur sai sarki hinzur ya gabza mai wata naushi a yayan
marenansa, take kallabu ya durkusa sannan ya kama wajen da hannayensa bisa jin wata muguwar
zogi,
Damar da sarki hinzur ya samu kenan cikin zafin nama ya zare takobin kallabu a kugunsa,
Sannan ya fille mai kai take dungulmin kan tayi tsalle ta fado a gaban waziri humaiz,
.
A lokacin waziri humaiz na rike da kibau a hannunsa , cikin har zuka ya yarda kibau din gefe,
Sannan ya zaro takobinsa ya fuskanci sarki hinzur,
Nan fa suka rugunzume da azababben yake, nan fa waziri humaiz ya wanzu yana kai ma sarki
hinzur sara da suka, shi kuma sarki hinzur ya wanzu yana mai karewa, sannan kuma yana maida
martani, sai da aka shafe kimanin sa'a biyu ana wannan gwagwarmayar toh a sannan ne waziri
humaiz ya tuna cewa ya riga daya illata sarki hinzur koda gama aiyana hakan aransa sai ya yarda
takobinsa sannan ya yage rigan dake jikinsa,
Lallai shima waziri humaiz ba karamin kato bane don kuwa jikinsa a mummurde suke,
Faruwan keda wuya shima sarki hinzur ya yar da takobinsa ya tsaya atsaye toh sai a wannan lokaci
ne sarki hinzur yafara ganin jiri a sakamakon jininsa dake zuba,
Nan suka afka ma junansu, wannan karon salon fadan ya canja don cikin dakiku kadan suka hada
ma junansu jini da majina,
,
Sarki hinzur ya gaji likis amma saboda tsabar juriya da naci hade da cin rai
Tabbas badun sarki hinzur ya kasance NAMIJIN GASKE ba toh da tuni waziri humaiz ya gama da
shi.
Koda suka ga tsagwaron karfin su yazo daya sai kowa yaja baya ya tsaya, nan sukai cirko cirko
suna kallon juna,
Cikin matukar fushi sarki hinzur yace"shin yakai dan uwana kayi sani daka zo ka sanar dani cewa
kana son mulkina toh tuni na baka, amma tun da ka biyo ta wannan hanyar ne lallai ina tabbatar
maka sai na hallaka ka ayau dinnan"
.
Koda waziri humaiz yaji haka sai ya bushe da mahaukaciyar dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya
dubi sarki hinzur yace mai
"Ni ba dan'uwanka bane kada ka sake ka sake kirana da dan'uwanka'kayi sani tun muna kanana
mahaifinmu yake nuna matukar kauna agareka,
Kulawar dayake baka sam ni baya bani, sannan maimakon ni danake Babba na gaji karagar
mulkinsa amma sai ya nadaka a matsayin sarki alhalin kaine a kasa dani, tun daga wannan lokaci na
fara kulla tarko ina ta kaima ka hare hare amma kana ketarewa, toh yau gashi ka fada a cikin babban
tarkona wadda ina tabbatarma ayau dinnan zan halaka, ka sannan inbi matarka ita ma na hallakata"
Koda gama fadin hakan sai sarki hinzur ya kauma waziri humaiz wata naushi adaidai makogaro da
nufin ya fasa mai makogoro cikin zafin nama humaiz ya goce sannan ya fidda wata yar karamar
wuka a kugunsa cikin shammace ya soka ma sarki hinzur wukan a cikinsa, nan take sarki hinzur ya
kwala kara wacce ta amsa a gaba daya ilahirin dajin
Nan take sarki hinzur ya fadi matacce
.
Koda waziri humaiz yaga ya samu nasarar kashe sarki hinzur sai ya nausa cikin daji nemana,
nikuma alokacin ina saman wata bishiya na rakube sai kuka nake tayi
.
Yadda agaban idanuwana aka kashe mani masoyi,
.
Bayan tafiyarshine na sauko daga kan wannan bishiyar sannan na nausa daji
.

Alokacin ina dauke da cikin ka wata takwas haka na kariso wannan waje a matukar galabaice.
Na hada sanduna,itacuna na sana'anta wannan dan karamin bukkar haka na cigaba da rayuwa acikin
wannan jejin har sa'ar dana haifeka
.
Babu abinda nake ci face yayan itatuwa ,da kuma tsuntsaye sune abincina a haka na raineka ka
girma."
.
Koda hamasiya tazo nan a labarinta sai taa dubi muhaisin tace mai"toh dana kaji labarin mahaifinka
sarki hinzur bin humas na birnin tehran wanda ayanzu ya zama tarihi"
Koda hamasiya ta kawo nan azancenta sai taga fuskar muhaisin ta jike sharkaf da hawaye nan ya
mike tsaye sannan ya rungume mahaifiyarsa yana mai fashewa da matsanancin kuka na bakin ciki.
.
Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part E"

Post a comment