Results

NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part B

NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part B
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Kimanin shekaru ashirin da suka gabata a birnin tehran , birnin
tehran babban birnine wanda mutanen cikinsa yawancin
sana'arsu itace Noman kayan Abinci iri iri,
Kasuwar garin nacine a duk mako. Kuma daga wasu garuruwan
sukan ziyarci wannan kasuwa a duk makon da zaici,
.
Al'umman birnin tehran ma'abota son zaman lafiya ne, A yayin
da adalin sarkinsu hinzur bin humas, ya tsaya tsayin daka wajen
yada zaman lafiya a duk sassan birnin
.
Sarki hinzur babban sadaulkine wanda duk ilahirin nahiyar
babu sadauki kamarsa.
Ya kasance yana da wani dan uwa mai Suna Humaiz bin Humas
.
Shi Humaiz yan uba suke da hinzur wannnan tasa ya kullaci
hinzur sosai a cikin zuciyarsa,
Wacce har takai ta komo So yake yaga bayan sarki hinzur
sannan ya kwaci mulkinsa. Duk da kuwa alokacin matsayin
wazirin tehran yake.
Duk wani bakin ciki da hassada gami da kyashi da yake wa
sarki hinzur bai taba Nuna wa a gabansa ba, hasalima irin
biyayya da so da kauna da yake nuna wa hinzur kai kace tamkar
da gaskece amma na ciki na ciki
.
Waziri humaiz yasan bazai iya tarar sarki hinzur gaba da gaba

ba, don kuwa linzami tafi karfin bakin kaza.
Hakan tasa yaje ya samu wasu yanfashi a wajen gari cikin wani
kungurmin daji , nan take ya zayyane masu bukatarsa na son su
taimakeshi su hada karfi da karfe, don su kawar da sarki hinzur
a ban kasa.
.
Shugaban yan fashin mai suna kallabu ya dubi waziri humaiz
bayan sun gama sauraron bayaninsa yace da shi ,
"Yakai wazirin birnin tehran hakika kazo mana da abinda muka
dade muna jira tsawon wasu watanni, lallai kasani wannan
taimako daka nema daga wajenmu tamkar mune muka nemi
taimako daga gareka"
Waziri najin haka sai ya cika da tsananin mamaki sannan ya
dubi kallabu yace "shin kai kuwa wannan shugaba ta yanfashi
meye dalilin ka na fadin hakan"
Nan take Kallabu ya bushe da dariya saida yayi mai isarsa
sannan ya dubi
Waziri humaiz yace da shi "yakai humaiz kai sani cewa mun
dade muna son ganin bayan sarki hinzur bisa takura mana da
yayi, lallai zamu taimakeke ba tareda mun karbi ko kwandalarka
ba, Abin dana ke jimana shakka iyace ta yaya zamu ratsa har
mu shiga gidan sarki hinzur .
Humaiz najin wannan tambayar sai yayi murmushi sannan
yace" indai maganan shiga gidan sarkine toh lallai ina tabbatar
maku shan ruwa ma ya fishi sauki a wajena, domin kuwa akwai
wani hadimina da zansa ya jagoranceku har zuwa turakar sarki"
."
Koda yamma tayi sai shugaban yanfashi da yaransa kimanin su
dari biyar, sukayi shiri irin ta fatake sannan suka tasamma
birnin tehran
.
Koda suka iso bakin kofan birnin tehran sai masu tsaron kofa
suka tsaida su,
Wani badakare wanda da alamu shine babba acikin dakaru masu
tsaron kofan garin ya kusanto gaban wayannan yanfashi
wayanda suka yi shirin fatake ya tambayesu
"Yaku wayannan ayari su waye ku , sannan Me ke tafe da ku
izuwa wannan kasa tamu mai tarin daraja"
.
Koda jin haka sai kallabu wanda yabadda kamanninsa ta hanyar
nade wata katuwar rawani a kansa ya dubi wannan dakare yace
"Yakai wannan mai tsaron kofan kasani mu fatakene sannan
bada niyyar komai muka iso wannan birnin ba face don
kasuwanci"
Shugaban masu tsaron kofan yace
"Wacce irin haja kuka dauko"
Kallabu yai nuni da hannunsa ga bayansa wasu rakumane a
kalla sunkai hamsin dauke da manyan sundukai a bayansu,
Sarkin kofa ya iso gaban rakumi daya sannan ya bude sunduki
daya daga cikin sundukannan ,
Babu komai aciki face kayan masarufi kama daga dangin zinare
har zuwa kan su murjani da yakutu.

Nan take shugaban masu tsaron kofa ya bada umarni da a bude
musu kofa su wuce
.
Koda suka shigo birnin tehran basu zame ko ina ba sai cikin
kasuwan garin , inda suna isa suka tarar da wani hadimin waziri
humaiz .
Wannan hadimi yai masu jagora izuwa wata babban gida ta sirri
wacce ta kasance mallakin waziri humaiz ne.
**** *****
Can cikin talaitainin dare kuwa dukkan wayannan yan fashin
sunyi mugun shirin yaki. Kai kace yakin duniya zasuje
Gama kimtsawarsu keda wuya sai hadimin waziri humaiz daya
jagoranci su kallabu izuwa wannan gida ta sirri ya shigo garesu
.
Sunan hadimin KAMSAS kuma shine amintaccen hadimin
waziri humaiz
Kamsas ba karamin hatsabibi ba ne don kuwa duk cikin
hadiman waziri babu wanda yake matukar ji dashi tamkar
kamsas
.
Nan kamsas ya dubi kallabu yace " ya shugabana Muna iya
tafiya yanzu"
.
Ta bayan gari suka bi gudun kar wani yaji takun sawaye ya
yawaita ya farka daga barci.
Ba a dadeba suka fara hango kofan gidan sarki, masu gadi na
nan sai zagaye suke ta ko ina
Koda kallabu yaga haka sai ya dubi kamsas
"Shin ta ya ya kake ganin zamu ratsa wayannan da karu masu
tsananin yawa wayanda na tabbata ko munyi nasarar gamawa da
toh sai nayi asarar dakaru masu yawan gaske .daga karshe kuma
in muka shiga gidan sarki ragowan sauran dakarunsa su
karisamu.
Kamsas na jin haka sai yayi murmushi sannan yace "ya
shugabana kai dai ka tsaya zakaga ta yadda zamu samu nasarar
shiga gidan kuma batare da mun raunata badakare ko guda daya
ba"
.
Kamsas na gama fadin haka sai ya rike hannun shugaban
yafashi kallabu sannan yace mai yai ma yaransa umarni da
kowa ya rike hannun juna,
Cikin dan kankanin lokaci sai gaba daya yan fashinnan suka
rirrike hannuwan yan uwansu.
Nan take kamsas ya fara fadin wasu kalmomi daga cikin yaren
girkawa,
Take sai wata guguwa bayyana , koda bayyanar guguwar saita
nufosu tana zuwa wajenda suke sai ta suresu tai sama da su
****** *****
Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017

Typing:- shuraih 99%

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part B"

Post a comment