Results

NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part C

Namijin gaske 1
Part 1C
(c)Shuraih Usman
@shuraih 99%
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part C
.
A cikin farfajiyar gidan sarki hinzur dakaru sai kai kawo suke
duk da yake cikin darene amma farfajiyar gidan a haskake take
yadda ko Allurace ta fadi sai anganta,
.
Ba zato ba tsammani sai gani akayi wata iriyar guguwa ta
bayyana
Gaba daya dakarun gidan suka mai da hankalinsu ga wannan
guguwa, cikin kankanin lokaci guguwan ya lafa , koda bacewan
guguwan sai su kallabu suka bayyana suna masu rike hannuwan
junansu.
Dakarun sarki hinzur na ganin bayyanarsu sannan sukaga
dukkansu suna dauke da muggan makamai,
Take sukayi kukan kura sannan suka zare makamansu daga
cikin kufe,
Sannan suka afka ma su kallabu,
Su kuwa su kallabu koda ganin haka sai suma sukai kukan kura
sannan suka falfala da gudu don su tarbi dakarun sarki hinzur,
Nan aka rincabe da azababben yaki
Farfajiyar gidan bakajin komai sai karafkiyar takubba da
karajin Dakaru, jini sai malala yake tamkar an yanka wani
babban dabba,
Aikoda aka fara wannan yaki sai dakarun sarki hinzur suka
raina kansu , domin yan fashin wani irin salon yaki suke ,sannan
gasu da juriya dacin rai da naci, don sai kaga badakare ya zabga
masu sara a jikinsu jini yayi fallatsi, amma sabida tsabar naci
haka zasu cigaba da yakin
.
A yayin da dakarun sarki suka fahimci muddin akaci gaba da
wannan gumurzu toh yan fashin na iya karar da su gaba daya,
hakan tasa wani badakare mai matukar girman jiki ya falfala da
gudu izuwa wani bangare na gidan,
Koda ya je wajenda yake son zuwa . Wata irin dogon ginice mai
tsayi wacce a samarta akayi mata rumfa,
Irin wannan ginin ana amfani da sune ta hanyar ganin wanda
yake wajen gidan sarki ko ta hanyar sada wani sako, ajikin
ginin da kwaita iriyar matattakala ta katako, da isan wannan
badakare sai ya kama wannan matattakala ta katako, ya fara
hayewa izuwa saman birnin ko da yakai ga karshen ginin sai, ya
dauki wata makekiyar mabushi, yana dauka ya kafata abakinsa
sannan ya ringa busawa har tsawon wasu dakiku sannan ya
saurara.
.

A yayin da ake tsaka da gumurzu lokacinda su kallabu suka fara
cin karfin dakarun sarki hinzur
Suna kara kusantar asalin babban kofan da zata sada mutum
izuwa cikin falon gidan sarautar,
,
Alokacinne suka ji wata irin busa na tashi,koda kallabu ya
saurari wannan busa sai zuciyarsa ta bashi lallai ba lafiya ba,
hakan tasa ya ayyana aransa ya kamata suyi sauri su aikata
abinda zasu aikata su wuce abinsu,
Rashin sani tafi dare duhu, lallai da yanfashinnan sun san abin
da zai biyo baya toh da sun gaggauta barin wannan gidan
sarautar don ceton rayukansu,
.
Wannan busar bana komai bani illa busan Yaki, kuma sanar da
mutane cewa gari babu lafiya.
.
Kwance yake bisa shimfidarsa daga shi sai gajeran wando, duba
daya zakai mai kagane cewa yana jin dadin wannan baccin da
yake
Gabjejen katone baki amma bakinsa bawai irin baki kirin nan
bane,
,
Ba kyakkyawa bane amma kuma ba a kirashi da mummuna ba,
Yana da tarin damatsa, jikinsa a cure take a waje daya ,
Kamar acikin mafarki sai yaji wannan busa , zumbur ya mike
sannan ya natsu don kara sauraron busar tabbas wannan busace
dake tabbatarda cewa birnin nan na cikin tashin hankali, nan da
nan ya sanya kaya ajinkinsa, sannan ya sanya sulken yakinsa,
Ya daoki takobin sa ya rataya , sannan ya fito farfajiyar gidan
Nan da nan ya nufi turkin dawakansa da zuwa ya haye kan wata
bakar doki
Take dokin tai rimi sannan ta fice daga cikin gidan.
Wannan gabjejen mayaki ba kowa bane face sarkin yakin
birnin Tehran mai suna ZABBAGI bin SHARMIL
.
Abin da su kallabu basu sani ba shine A lokacinda suka isa
gidan sarki hinzur Dakarun da suke fada dasu dakarune masu
kare lafiyan sarki su dubu daya,
.
Su wayannan dakaru basa rabuwa da wannan gidan sarautar sai
sati yadda za'a canja da wasu su wayannan suje su huta
.
Acikin gari kuwa koda Mayaka da dakaru suka ji wannan busa ,
Nan da nan duk wani mayaki kuma dakare na wannan birni yayi
shirin yaki sannan aka tasamma gidan sarki,
Sabida karan busar daga cikin gidan take fitowa,
Sarki hinzur na turakansa sai sharbar barci yake kwatsam sai
yaji karar wannan busar acikin kunnuwansa
Nan take ya mike daga kwancen daya ke ,
Koda ya fahimci busar na fitowa daga cikin gidansa ne sai ransa
ya baci,
Cikin kankanin lokaci gagarumin shigar yaki irin ta sarakai, ya

dora takobin sa akan kafadarsa
Cikin hasala da zafin rai ya bangaje kofan turakanshi take
kofan ta fadi kasa shirim,
Kofar na faduwa ya fito ya fara tafiya cikin izza koda yaga yayi
tafiya mai dan tsayi amma bai hadu da dakarunsa ba, sabanin
da, sai ya kara fusata nan da nan ya falfala da azabaBben gudu
Cikin kankanin lokaci ya iso bakin babban kofan da zata
sadashi da farfajiyar gidan,
Cikin kunan rai ya daki kofan da kafansa take kofan ta fadi
rikica ,
Kofan na budewa sarki hinzur yai arba da wayannan yan fashin
sai ratattakan dakarunsa suke.
Nan take ya kwala wata irin kara wacce tasa gabadaya mayakan
suka tsaida yakin sannan sukai dubi izuwa wajen da yake tsaye
.
Yanfashin naganin haka sai suka falfalo da gudun tsiya don su
afka ma sarki hinzur
Sarki hinzur na ganin haka sai shima ya ruga da gudu don ya
tarbesu,
Koda ya rage baifi saura taku kadan ba tsakaninsa da yanfashin
sai ya daka tsalle yai sama , a saman ne cikin zafin nama ya
shafttare,
Makogwaron yanfashinnan da sukai kansa su biyar.
.
Nan fa sarki hinzur ya cigaba da sara da suka baji ba gani duk
inda ya nufa sai de kaga sassan jikin mutun na yawo bisa
sararin samaniya, yadda kasan ana sassabe a gona, tabbas
masifa ba' a samata rana lallai da mutum yana wajen yana ganin
irin yanda sarki hinzur ke yiwa wayannan yanfashi kisan gilla
toh daya tabbata lallai sarki hinzur ya cika NAMIJIN GASKE
duk girman kato sai dai kaga yayi tsalle ya saka takobinsa ya
farke masa ciki take zakaga jini yayi tsartuwa, cikin kankanin
lokaci sarki hinzur ya kashe kasu biyu cikin kaso uku na
yanfashin
.
Koda yan fashin suka fuskanci muddin aka cigaba da wannan
yakin a haka toh tabbas nan da wasu yan dakiku za'a karar da su
Ai nan take yanfashinnan suka fara neman hanyar tsira, cikin
masifaffen gudu suka tasamma kofan fita daga gidan da nufin
su fice daga gidan sarautar,
Bazato sai gani sukai kofan gidan ta bude da kanta
Budewar kofan keda wuya sai ga sarkin yaki zabbagu ibn
sharmil da mayaka abayansa kimanin milyan daya ,
Nan fa sarkin yaki ya cigaba da fille kawunan yanfashinnan shi
kallabu koda ganin haka sai ya hankalinsa yayi matukar
dugunzuma take ya sadakar cewa ya rigaya ya mutu,
Tsulum sai ganin Kamsas yayi ya bayyana agabansa yana
baiyana ya kama hannun kallabu yana shirin furta kalmomin
dazu kenan kawai sai gani sukai sarki hinzur ya baiyana a
gabansu
Cikin matukar hassala sarki hinzur ya daga takobinsa sama da
nufin ya fille kan shugaban yan fashi kallabu  da kuma kamsas ,

Koda Takobin tazo daidai saitin wuyan kallabu
Sai........
.
SAI ME
SHIN AGANINKU KALLABU ZAI TSIRA DAGA KAIFIN
TAKOBIN SARKI HINZUR KUWA
.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part C"

Post a comment