Results

NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part D

Namijin gaske 1
Part 1D
(c)shuraih Usman
@shuraih 99%
NAMIJIN GASKE
Littafina daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih Usman
Tel. 08133209890
Part D
.
Doka, banyarda wani yayi copy ko ya sarrafa wannan labari ta
ko wace hanya batare da izni na ba. Dafatan za'a kiyaye
Copyright
Shuraih Usman
.
Koda Takobin tazo daidai saitin wuyan kallabu
Sai wata iriyar guguwa mai karfin tsiya ta bayyana
cikin kankanin lokaci guguwar ta zuke kallabu da
kamsas.
.
Koda ganin haka sai ran sarki hinzur yai matukar baci
nan da nan ya auka wa sauran yanfashin da suka
rage,
Cikin kankanin lokaci aka karkashe dukkan yan
fashinnan,
A sannan ne sarki hinzur ya dubi sarkin yaki zabbagu
yace da shi
"Ya kai sarkin yaki birnin tehran shin ta ina wayannan
runduna suka bi har suka shigo cikin wannan fadan"
.
Sarkin yaki yace " ranka shi dade ina kwance bisa
shimfidata naji sautin busa toh a sannan ne nasan an
kawo mana harine ,"
Wani badakare dake gefe yazo ya durkusa agaban
sarki hinzur yace"ya shugabana muna cikin aikinmu
na bada tsaro , kwatsam sai gani mukayi sun bayyana
rike da makamai a hannuwansu"
.
Koda sarki yaji haka sai ya bada umarnin a kwashe
gawarwakinsu a tafi a kona, nan ya wuce zuwa
turakarsa ,
Washe gari kuwa afada sarki hinzur ya nuna tamkar
bai damu da al'amarin daya faru jiya da dare ba
.
Amma a boye ya saka wani bokansa mai suna

KAMSUSULJANI yayi masa bincike
.
Kwanaki suka ringa ja harzuwa watanni biyu acikin
watanni biyunnan abubuwa da yawa sun faru ciki
kuwa har da aurena da sarki hinzur,
Al'amarin ya kasance ne wata rana sarki hinzur na
zazzagaya gari yana duba yanda talakawansa suke
kamar yadda ya saba aduk karshen shekara
.
Ni kuma alokacin banfi shekaru goma sha tara ba ,
nazo kasuwa zan siya kallabi, kawai sai ganin
cincirindon jama-a nayi a waje guda dana tambaya
kome ke faruwa sai aka sanar dani cewa sarki hinzur
ya kawo ziyara , kawai sai na tsinci kaina ina mai
karissawa. Wajen,
Don nasha jin labarinsa da kuma irin yabonsa da
jama'a keyi, amma ban taba ganinsa ba
.
Ashe dai kyaututtuka yake rabawa wa jama'a ,
Dogon layi akayi a yayin da shi kuma sarki hinzur
yake gaban wata rumfa dankarere ,agabansa wani
makeken teburine akan teburin kuwa kyaututtukane
kala kala ,
Banyi kasa a guiwa ba nima nabi layi , har layi yazo
kaina ,
Kaina na sunkuye ina dago kaina nai arba da
kyakkyawar fuskarsa ma'abociyar murmushi , nan
take naji zuciyata ta buga,
Maimakon sarki hinzur ya miko mani kyautar dake
hannunsa sai ya kura mini ido kaman yana nzarin
wani abu a tattare dani ,koda naga haka sai na
sunkuyar da kaina kasa,
Ina sunkuyar da kaina kas ne idanuwa suka ci karo da
abin da ya tayarmin da hankali
Bakomai bane illa wata zabgegiyar macijiya baka
kirin, jelar macijiyar da sauran jikinta yana kasan
teburin a yayin da kan macijiyar ya leko ta saman
teburin daidai saitin hannun sarki hinzur,
Nan take macijiyar ta fiddo da harshenta , ai koda
naga haka sai nayi wuf cikin zafin nama na bangaje
hannun sarki hinzur ,da hannuna kafin na kauce da
hannuna sai wannan macijiyar ta dankara mani cizo a
hannu, nana na kwala ihu daga nan ban san meya
faru gareni ba.
.
$ai farkawa nayi na ganni acikin wata kimtsastsiyar
turaka bisa wata luntsumemiyan katifa na alfarma
wannan turaka ta isa daular duniya don kayan dake
cikinta yayi hannun jarin wani attajirin.
.na mike zaune
Kofan dakinne ya bude sannan wata kuyanga ta shigo
, koda wannan kuyanga taga na farka sai ta washe

baki sannan tamin sannu na amsa mata cikin boye
murya ,
Fitan kuyangan keda wuya sai naji takun sahun
mutun yana nufo dakin , ya bude kofa ya shigo ya
kariso har inda nake zaune bisa katifa ,
Bakowa bane face sarki hinzur , yai mani sannu da
jiki sannan ya fice,
Ficewarsa keda wuya
Sai wasu kuyangi suka shigo nan suka tasar dani sannan suka shiga bayi sukai mani wanka bayan
mun fito daga bayine suka zaunar dani bisa wata kujera,
.
Anan sukai mani kwalliya sannan suka sanya mani wani tufafi na yadin alharini. Sannan suka ce
dani naje sarki naso yayi magana dani.
.
Acikin wata turaka na sameshi kai alokacin in ka ganni kace sarauniyar duniyace , doguwar rigace
sanye a jikina rigar an yimata ado da duwatsun lu'u lu'u sannan na yafa wata mayafi wadda akayi
mata cin baki da zubar jadi, wannan mayafi ya rufe mani ilahirin fuskata
.
Bayan na zaune a daya daga cikin kujerun dake cikin turakar sai na yaye mayafin dana rufe. Fuskata
da shi , koda sarki hinzur yai arba da fuskata sai ya mike tsaye yana mai cewa " tsarki ya tabbata ga
wanda ya kagi wannan kyakkyawan halittar"
.
Koda naji sai na sun kuyar da kaina kasa cikin jin kunya
Sarki hinzur yacigaba da cewa " ya ke wannan sarauniyar kyawawan duniya kiyisani a lokacin dana
dora idanuwana akanki tunanina,hankalina,dakuma natsuwata duk sun guje daga gareni,
Banki nayi shekaru ina kallon wannan kyakkyawan fuskar taki ba,
Kiyi sani yake wannan kyakkyawa wannan sarki yazo da kogon barar sa gareki da jin cewa zaki
amshi tayin soyayyarsa"
.
Koda naji yayi shiru sai na dago kai na dubeshi nace
"Yakai wannan sarki ma'aboci a dalci, kayisani cewa babu wata ya mace da zatayi arba da kai sonka
bai shigeta ba,
Kasani tun alokacin dana fara ganin ka naji ina matukar kaunarka,"nayi shiru cikin kunya
Anan dai mukai ta hira cikin nishadi
In ka ganmu sai ka rantse munfi shekaru muna tare
.
Aranar sarki bai fita fada ba
Bayan kwana uku aka daura aurena da sarki hinzur sai da aka kwashe kwanaki goma ana ta
shagulgulan bikinmu
Abun babu kama hannun yaro
.******* **
Al'amarin waziri humaiz kuwa tun dayaga shirin daya shirya na halaka dan'uwansa baiyi tasiri ba
sai ya shiga kulle-kulle ya kulla wannan ya kwance wannan har dai daga karshe wata dabara ta fado
masa.
****** **
Al'amarin boka kamsusulajani kuwa bayan yayi bincike a hallaran tsafinsa sai ya gano cewa waziri
humaiz ne keson kashe sarki hinzur
Sai yaki fada ma sarki gaskiyan Al'amarin
.
****** **
Sarki hinzur kuwa yayi tacin amarcinsa ya kasance baya zuwa fada sosai kuma kullum cikin
farinciki yake

Wata rana a fada ana cikin fadanci sai ga wani badakare yazo gaban sarki ya tsuguna yace
"Ranka shidade wani bakone akofa yace wai daga birnin KuFA yake kuma yazo ya isar da sakone,
Nan sarki yace abarshi ya kariso
Koda zuwan wannan manzo sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa wajen sarki sannan ya fidda wata
takarda ya mika ma wani badakare,
Take maga takarda ya karbi takardan yafara karantawa kamar haka
.
Sako daga sarki hurshad bin harush mai mulkin birnin kufa zuwa ga aminina sarki hinzur bin
humas, dafatan kuna cikin koshin lafiya kai da al'ummarka kayi sani cewa ban rubuta wannan
wasikar don komai ba face don na sanar da kai cewa, matata kuma abar begena ta haifa mani
santalelen yaro ayanzu haka dai na zama baba, sannan ina gaiyatarka walimar radin suna , dagamai
mulkin birnin kufa sarki hurshad bin harush,
.
Koda magatakarda ya idda karatunsa sai sarki ya dubi dan sakon cikin murmushi yace "kagayawa
 aminina ina nan tafe nan da kwanaki biyar
.
Marubuci:- Shuraih Usman
Hakkin mallaka (m) Shuraih Usman
Company:- Shuraih 99%
(c) shuraih Usman 2017
Typing:- shuraih 99%

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "NAMIJIN GASKE littafi na daya 1 part D"

Post a comment