Results

YAR BARIKI book 2 page 14


RANA TA FARKO!!!

Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, da alama ya sha'afa da batun ofis, a hankali yaji ruwa yana fallasa a saman fuskarsa, wannan tasa dolensa ya bude ido fuska daure. Karon da idanunsa yayi da kyakkyawar fuskarta ya sanyaya ran nasa "Amincin Allah da rahmarSa su tabbata gareka my king, ka tashi ko yau baka zuwa ofis?" Tayi maganar ne cikin kwantar da murya, yayinda shi kuwa ya zuba mata ido, daga ita sai tawul ko cinyoyinta basu gama rufuwa ba ga dukkan alamu fitowarta kenan daga wanka don fuskarta ma da jikin akwai digo digon ruwa, nan ya tuno farkon ganinsa
da ita. Duk wannan tunane tunanen yana yi ne yana bibiyarta da kallo, tuni ta juya tana shiri!

Bata yarda data dubeshi ba ta madubin, har ta kammala goge jikinta, tana cikin shafe jikinta da cream dinta mai kamshi ne kuma yayi dauriya wajen mik'ewa ya cire jallabiyarsa dagashi sai gajeran wando ya fada toilet. Tabi bayanshi da kallo kafin tayi murmushi. Kadan ma ya gani. Kafin ya fito ta hade cikin leshi kalar darkbrown, mai b/curve. Riga da siket ne, siket din ma ya kamata, kamar yanda rigar ma saida ta dauke numfashi ta zurata. Daurin ma ya zauna d'abas, tuni ta gama da fannin kayan karin kumallo. Ta fente fuskarta ta feshe ko'inanta da turare kamar koyaushe. Ta maida komai jakarta, sannan ta fiddowa Haris manyan kaya duk da tasan lokuta da dama yafi kaunar zuwa ofis da kananun, saidai yau zab'inta tafison Haris dashi. Milk colour shadda ta zab'o mishi, wanda ya hau sosai da leshinta kasancewar katuwar fulawar da aka sanyamata a gefe milkcolour ce da kuma sauran kwalliyar da leshin yazo dashi. Daidai da hula saida ta ajiyemishi, tana kokarin gyara gadon ne ya fito, takowa yakeyi saidai ya gaza dauke kansa daga dubanta!

Yana tunkaro cikin dakin amma idanunsa yana kanta har yana buge kafa da gado, yayi sauri ja baya. Cikin nuna halin ko'in kula ya nufi wajen dressingmirrow. Ba zato yaga ta janyo man ta lakato a hannu, ya dubi hannun sannan ya dubeta. Fuskarta har lokacin yana dauke da murmushi mai burgewa. Ai saiji yayi an jawo hannunsa, yana ji yana gani ta gama shafa mishi man, sannan tayimai farr da ido "My king, kafin ka kammala bari na had'a maka tea ko? Naga kamar zaka makara". 

Ta sumbaci kuncinsa sannan ta nufi hanyar fita tana tafiyarnan dai nata. Saida yaji bugun kofar ya dawo hayyacinsa, yana son yarinyarnan, wai kuwa tasan da haka? Kodai nema takeyi ya bada kai da wuri? No bazaiyi hakan ba, toh amma har tsawon wane lokaci da kwanaki zai d'iba cikin juriyar k'arya. Ya dafe saitin zuciyarsa, tanan yakejin wata kibiya tana sukarsa, tanan kuma yake jin zafi da radadin so da matsanancin kauna yana kara shigarsa. Dakyar ya tattaro nutsuwarshi ya cigaba da shiri, kayan data fiddo mishi ya saka kafin ya dora agogo ya dauki jaka da wayoyinsa..!

Fitowa yayi ya sameta tuni ta hadamasa. Zama yayi sai ya ankara babu Zahra. Hakan yasa shi tambaya "Ina Zahra?" Ta murguda baki gefe kadan tana murmushi "Bata tashi ba." Ya gyada kai ya soma karyawa "Daman inada wata shawara, please inaso ya zamana girkin rana ne kadai za'a dunga haduwa tare ana ci, na safe da dare akaiwa mara girki sashenta." Kallonta yayi da wannan dara daran idanunsa masu lumewa acikin na mata harma su janyowa zuciyarsu matowa akan Haris "Akan wane dalilin" Tak'i janye idanunta daga nasa, ta kara k'aimi wajen kwantar da kwayar idanunta "Inaso 

kowaccenmu ta dunga samun enough time dakai. My king ka duba zancena". Tasleem batasan wani abu ba, my king da take fadi birkita lissafinsa yakeyi shi kadai yasan me yakeji, ya kawar da kansa daga dubanta ya maida ga filet din gabansa "Bani da matsala, kiyi shawara da kanwarki". Murmushi ta saki kafin tayi godiya. A ganinta hakan yafi, babu wata alama da wata zata fuskanta harma ta fahimci yanda alak'arta da mijin ke tafiya. Koda sukayi magana da Zahra, ta fita jindadi 

Itama tayi na'am da shawarar nan, murmushi baby tayi kawai.

Zaune yake a ofis ya kasa katab'us, kansa yana jingine jikin kujera idanunsa a lumshe, a hankali yake juyi da kujerar yana tunani. Shifa ba dutse bane, yau duniyar tunaninsa akan mata ya fada, ya kasa daina hasko tasleem, hannu yakai ya shafi kuncinsa kafin ya murmusa, yes! Yana sonta, hakanan yana tsananin bukatar keb'ewa da ita.
Buga tebur dinsa da akayine ya maidoshi hayyacinsa, ya bude idanunsa wadanda tuni sun kad'a ya zubawa mai shi ido, kafin yaja guntun tsaki ya mike ya shiga toilet, can sai gashi ya fito da tawul a hannu yana goge fuska.

"Ka daina shigomin babu sallama malam." Sayyid abokin aikinsa, sun saba har sun zama tamkar abokai yayi dariya yana duban Haris dake korawa mak'oshinsa ruwa "Ta yaya zakaji sallamata harma ka amsata alhalin kayi nisa cikin tunanin matanka? Ka gode Allah, a farko darakta da kanshi yayi niyyar zuwa amma sai akaci sa'a ya hakura ya aikoni, ka manta da meeting na 1pm. "Da sauri ya zari laptop da hularsa, shaf ya mance.

 Suka fita!
Ya dawo da rana cike da d'oki da son ganinta. Numfashinsa ya kusan daukewa sakamakon kyau da shiga doguwar riga ta atamfar tayi mata. Zahra itama taci adonta tayi kyau, shi dai Haris ya k'ara godewa Allah bisa sa'ar daya ci na dace da samun zuk'a zuk'an yan matan nan. Wannan karon ma itace ta zubamishi yaci, tamkar kada ya koma ofis haka yaji, can dai ya daure ya fice.

 Mintuna uku da barinsa daga gidan, taslim kwance a gadon dakinsa ta jawo wayarta ta soma tsara mishi kalamai "The king of my heart, har na soma kewarka. Please and please idan ka taso ka taimaka kayo gida kai tsaye, tun kafin rashinka yayimin yawan da zan kasa jurewa na b'alle da ruwan hawaye. Tasleem, yours forever!"

Murmushi yayi yayin daya kammala karantawa, lokacin yana tsaye a junction, kibiyar so na kara sukar k'ahon zuciyarsa. Ba k'arya, tasleem tana kara rura wutar kauna a zuciyarsa! Ya kara muryar wakar da cikin sa'a aka sanyo a tashar Wazobia, wato Fall in love na dbanj kamar ansan yanayin da yake ciki, ransa yayi fari. A gefen Tasleem kuwa, bata damu da rashin maido martanin sak'onta da Haris baiyiba, tana da yak'inin tarkonta yana matukar kokarin kama kurciya.Ta kirayi hasinat suka sha hira abinsu kafin ta kirayi hindu, anan kuma ta nemi data aikomata lambar Hamida saboda zumunci. Mammanta da Abbanta kuwa, kai harma da waziri takan nemesu su gaisa.
Bayan magrib ya shigo gidan cike da buri da d'okin son yin tozali da ita, saidai kuma kash! Zahra ya tarar zaune a tsakar falon nasa tana kallo, ta cancara kwalliyarta kamar mai zuwa wajen wata liyafa. Da murna ta tarbeshi, a ladabce ta mishi sannu da zuwa sannan ta karb'i jakar hannunsa. Ya amsa yana murmushi, saida yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, kafin ya fito zuwa falon. Ya dubi Zahra yana murmushi kafin ya shafi gefen fuskarta "Myn bari naje masallaci lokacin sallah yayi". 

Wani sanyi ya ziyarci zuciyarta. "Myn?" Wancan karon ya kirata da tawan a gaban tasleem, yau kuma myn? Wow ta yarda kwarai yana matukar kaunarta. Shi kuwa gogan yana dawowa daga masallaci, ya kwankwasawa bby.
Ta budemishi kafin ta bude baki "Lah, daman ka dawo? Shine banji ma shigowarka ba ballantana nazo yin sannu da zuwa gareka? I'm sorry".

 Tuni ya karasa shigowa ciki, farar shirt bodyhug ne ajikinta, sai wani wando pencil jeans wanda daf yake da karasawa gwuiwarta, kanta babu ko dankwali. Numfasawa yayi kafin ya juya ya dubi tv,Arabica tv take kallo, muryar nancy yana tashi cikin d'ayan wak'okinta. Ya juyo "Wa kika yiwa wannan kwalliyar? Please ki dunga suturta jikin if you are alone. Nasha gayamaki banason kishiya, koda aljanu ne!" Jin haka yasa ta hau mutsitstsika ido, kafin ta kauda hannuwanta sai ga hawaye sun zubo, yayi mata kuri da ido kafin a tausashe yace "Me akayi toh?" 

Ta juya da gudu ta fada kan kujera tana kuka, kamar ya shareta ya fice saidai bazai iyaba, da sauri ya karasa ya durkusa gefenta, numfasawa yayi kafin yakai hannu ya dago hab'arta "Hey,menene kuma?" Ta share fuskarta, ta tsuramai ido "Kai na yiwa kwalliya baka yaba ba". Yanda tayi maganar yaji har kwanyarsa, ya share mata fuskar "Ok, i'm sorry kinji" Ta gyada kai.

Ta sanya hannuwanta ta kama yatsunsa kafin ta saukesu daga saman fuskarta, still dai tana rike dasu tace "Kabar kanwata cikin kadaici".

 Tab! Ai abunda Tasleem bata sani ba shine, bawai kanwartata ba, daidai da duniyar gaba daya ya manta da mutanen cikinta. Ya kara kama hannuwanta sosai "Kinmin iznin tafiya?" Tasan da ace da dama zata sakashi yin fiye da haka, murmushi tayi tana wani lumshe ido kafin taja hannuwansu ta sumbaci nasa sannan ta tsaida idanunta kansa, har lokacin murmushin nan takeyi "Muje na rakaka". Suka mike. "Oh ni rufaida yau naga ikon Allah, kuga yanda jaruman maza ya zama solob'iyo gaban mace?" Na fada ina duban iyalan Hannu da yawa writers dake facebook, na lura mazan sun daure fuska, don gasa mukeyi tsakani aga wandanda zasu ciri tuta, can na hango matan suna shewa da tafi, idan an cire sayyada muhd k'awar Zahra! Muka maido hankulanmu ga ma'abota nunawa juna tsantsar soyayya. Har sun kawo kofar dakinta, takai hannu da niyyar budewa, taji runguma, sunkai 2mins kafin ya sumbaci kuncinta "Ki chanja shiga, gud nyt". 

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 14"

Post a comment