Results

YAR BARIKI book 2 page 15


Daga haka yayi ficewarsa, ta kulle kofar kafin ta jingina da kofar tana dariya, kai musamman ma idan ta tuno wani jiji dakai, da shan kamshin haris gareta a baya sai abun ya k'ara bata dariya, ta wuce daki ta chanja shigarta tunda dai kwalliya ta biya kudin sabulu, a yau ta d'ana mishi babban tarkon da bazai iya ganin mace ya kyale ba. 

 Sai kuma ta zauna d'abas saman gadon, a fili tace "Ba mu'amalata da Haris kadai nake gyarawa ba Zahra, ke kanki da mijina inaso naga komai ya daidaita". Duk da cewar tasleem tana da kishi matuka, don har wasu lokutan takanji haushin Haris daya auri mata biyu batare daya bari sun more rayuwa ba, amma saidai hakan bai zame mata dalilin da a zuciyarta taji muguntar son ta kori Zahra daga gidan ko kuma miji ya juyamata baya ba. Kowa yayi takunsa kawai!

Acan kuwa zuciyace ta shiga cikin wani yanayi, ta kasa daina tunani, ta kasa yakice dukkan sak'onnin da aka aika zuwa gareta. Kasancewar gangar jikin, bai taba kuskuren hada kansa da haramun dinsa ba a rayuwa, sai halaliyarsa, ji yake inama su dauwama haka. Saidai da komai ya nisanceshi, dole ya rungumi abunda ke kan idanunsa. Baiyi k'asa a gwuiwa ba wajen yakice wannan tashin hankalin akan daya halal din tasa! A bangarenta itama ta cika da mamaki tsantsa, saidai ta gurzu matuka da har a karshe ta fashe da kuka wanda dole bayan kwarnafi ya kwanta, ya mike tsam ya hada ruwan dumi a toilet kafin ya bata kyakkyawan agaji, da kansa ya sanyamata kayan barci ya shiryata, kafin kuma ya bata paracetamol ta sha.

 Saida ya kimtsa tsaf ya dubeta yana neman iznin tazo suci abinci, cike da tsananin kunyarsa ta tura kai bargo "Na koshi". Yayi yayi amma tak'i tasowa dolensa ya fito falon bayan ya kashe mata fitilu. Bude fuskarta tayi tana mai murmusawa, Haris daban ne! Ta yarda da wannan, a karshe ta hau mamakin yanda yana shigowa falon ya kawo mata runguma bata wasa ba. Kalamai na so da kauna kam tasha su har saida ta tsorata da rawar k'afarsa.

A gefen Haris kuwa, kwarai ta burgeshi matsayinta na budurwa data iya kokarin tsare mutuncinta har gashi ya bata wata daraja mai girma a ransa!!

Kasancewar baisanta ba, ya sanya koda suka shigo falon da kallo kawai ya bita kafin ya maida dubansa ga Tasleem dake nuni da tambayace. Tana murmushi, ita kuwa Hamida zubewa tayi tana gaisheshi, gaba daya yayi mata wani mugun kwarjini, daman haka Haris din yake? Namiji ne wanda yakeji da kudi da kuruciya, uwa uba kuma kyakkyawa ne na gani na kwatance. Kwarai Tasleem tayi mugun sa'a a rayuwarta, wannan miji haka? Inama inama hum! Ta ayyana a ranta tuni ta koma kalar tausayi.

Ya amsa gaisuwarta duk da dai fara'ar dake saman fuskarsa ragagga ce na rashin sanin kowacece. Ya dubi Tasleem. Murmushi ta k'ara sakar mishi "Hamida ce kanwata, d'iya ga Marigayiya Raliya". Ya k'ara kallon Hamida da murmushi saman fuskarsa, ikon Allah kenan, wato dai Hamidar data tab'a bashi labarinta ce kenan? Shi kam baiga wani abu da take dashi ba da har yasa ta nunawa Tasleem k'iyayya

 "Sannu fa kanwarmu, ya maigidan naki?" Hamida ta amsa "Lafiya kalau yake." "Toh madallah, a gaisheshi ko?" Ya fada yayinda yake zura hannu cikin aljihun wandonsa, ita kuwa hamida tuni ta amsa da toh gami da mikewa, ya mik'awa Tasleem dubu biyar "Ki bata." Hamida ta amsa cikin rawar jiki ta koma durkushe tana godiya, yace bakomai.
Zahra dake kokarin zuba abinci ta dubi Hamida "Hamidah kinci abincin ko?" 

Tasleem ta bata amsa da cewa "Taci." Daga haka sukayi sallama da Zahra kafin tasleem ta fice domin yi mata rakiya, saida suka isa farfajiyar gidan sannan ta mik'awa Hamida ledar da tun shigarta falon Haris take a hannunta, kayan kwalliya ne, sai sabbin dinkunanta kala hudu da bata tab'a sakawa ba sannan kudi har dubu goma cikin wadanda take dasu bata kashewa, hamida ta soma hawaye da godiya, Tasleem ta dafa kafad'arta "Menene haka? Na gayamaki banaso kina damuwa, kefa yar uwata ce". Daga haka sukayi sallama, sai sukaji muryar Haris, ashe yazo. "Ba'a mota take bane?" Jin haka duk suka kai dubansu garesa. Tasleem ta amsa "Eh." Ya dubi Tasleem cike da takaicin yanda ta fito, don daga ita sai yalolon mayafi wanda bai gama rufeta ba "Ok, ki koma ciki zansa a kaita." Tasleem ganin yanda yayi kicin kicin ne yasa ta komawa ciki. Shi kuwa Abdulaziz direba ya kwalawa kira kafin ya bashi mukullin mota "Ka mik'ata gidanta". Daga nan suka k'ara sallama da juna, hamida tayita godiya bisa karamcin da Haris yayi mata daga haka yayi ciki.

 Tasleem ta fito daga sashenta zata hau sama don yin lunch sukayi arba. Harara ya wurga mata ya wuceta zuwa sama. "Toh menene kuma?" Ta tambayi kanta kafin ta tab'e baki ta bi bayanshi. Tuni ya zauna saman kujerar dinning, tana k'arasowa ta zauna, Zahra har ta kammala zubamishi itama ta zauna. "Na sanya muku doka, duk wacce tayi bak'i ban yarda ta wuce daga baranda ba, ta tsaya anan suyi sallama koma da wacece. 

Daga yanzu ku kula, ke kuma". Ya dubi Zahra, "Admission naku ya samu, ranar monday mai zuwa zaku soma halartar karatu. Ki kiyayemin darajarki, banaso kina zuwa daukar darasi da sutura marar dacewa, ko kuma kice zakiyi kwalliya, duk wannan ban amince masa ba, sannan kisan irin wadanda zakiyi mu'amala dasu, 

banason k'awaye sune masu lalata tarbiya, don haka ki kula, ki gane kuma ki fahimta, kada ko kusa ki bari naga wani chanji daga kulawa ko kuma biyayyar da kikemin, hakan ga tarbiyyar da kika taso cikinta. Nidai babu wacce ta isa ta juyani cikinku, kamar yanda ya zamto dole agareku kuyimin biyayya, nayi alk'awari zan k'ok'arta wajen kulawa daku da sauke hakk'ok'inku da suke akaina. Aurenku nayi bisa kauna da soyayya ta don Allah, don haka kuji tsoron Allah ku kiyaye hakkin aure!" Yana magana cikin damuwa matsananciya wanda daga Tasleem d'in har Zahra basusan abunda ya jaza damuwar tasa ba. Sun dai amsa da toh kafin kuma ya tsakuri abincin ya koma ofis!.
Bayan tafiyarsa, tasleem tana kwance saman 

doguwar kujerar falonta, kwayar idanunta yana ga
fankar dake juyawa, tunani takeyi game da makomar karatunta, tasan ta riga ta yiwa kanta, bata zaton koda wasa Haris zai amince
mata ta cigaba. Musamman tunawa da maganganun daya gama fad'a yanzun, ji takeyi inama ace itace da wannan opportunity da Zahra ta samu, ai karatu har saita dangana da masters, da ace ta maida hankali a baya da tuni ta zama cikakkiyar lauya, ta muskuta tana mai numfasawa, ko giyar wake tasha tasan Haris
bazai barta ta cigaba, hakanan dai zata hakura.
Bayan magrib tana jin shigowarsa ta nufi saman.

Lokacin tayi wankanta tsaf, ta chanja shiga zuwa riga doguwa marar nauyi, mai fad'ad'd'an hannu daga k'asa. Ta yafa karamin mayafi tayi talha, babu kwalliyar komai saman fuskarta. Ta shiga da sallama, lokacin hira suke harda dariya, yana sanye da jallabiya bak'a marar nauyi kuma shara shara. Suka amsa mata sallamarta, wani sassanyan kallo yake jifanta dashi yana sakin murmushi. Ta maida mishi martani kafin ta dan russuna tayimai sannu da zuwa. Ya amsa yana kokarin ganin kwayar idanunsu ya had'u da nata saidai kokusa bata dubeshi ba, ta mike, tana kaiwa kofa ta juyo akayi sa'a yana kallonta. Murmushi mai burgewa ta sakarmai kafin ta kashe masa ido d'aya, daga haka ta fice. 

Ajiyar
zuciya ya saki, a hankali kuma ya shafi sumarsa
yana mai lumshe ido. Ko kusa Zahra bata kula
ba, hankalinta yana ga tv ganin ansoma series din
da take matukar so da kaunar gani, Laali. Shi kadai yasan yanayin da zuciyarsa ke shiga akanta, baik'i su kwana su wuni tare ba 

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 15"

Post a comment