Results

YAR BARIKI book 2 page 16

koyaushe. Ya kanyi iyakar k'ok'arinsa wajen ganin ya b'oye damuwa da azalzalar da zuciyarsa keyimishi akan Tasleem. Muryar Zahra ta katse tunaninsa inda take dariyar film. Ya daki

bayanta "Cry cry baby, kinbar mijinki da
yunwa". Kunya ta kamata, ta mike da sauri! Ta rigaya tasan me yake nufi, cikin shagwaba murya tace "Gaskiya nidai nagayama banaso". Ya kwaikwayi muryarta "Ni kuma inaso". Ta turo baki, sukayi dariya yakai hannu da nufin rik'ota, a guje ta bar wajen tana fad'in "Taso ka cika
cikinka".

Misalin goma na dare, Zahra ta sauko sashenta
da niyyar shirin bacci, shi kuwa yana kwance saman gado yana browsing, wayarsa tayi k'aran shigowar sak'o. Murmushi yayi ganin daga inda
yazo. Ga abunda take cewa "Zuciya ta kasa daina

tunaninka, hakanan na kasa samun sukuni. Kai kadai ka zamto abun muradina, inama inama mu kasance tare kullu yaum! Sweetdreams my king! *hugs nd kisses*. Oh God! Ya lura tanason kasheshi, ya karanta yafi a k'irga kafin daga bisani ya yanke hukuncin maida martani, saidai jin motsin dawowar Zahra ya sanyashi fasawa gami da jona wayar chaji. Daren sun kasance masu faranta ran juna kamar jiya, hakanan so da shak'uwa suka k'ara wanzuwa a zukatansu.!

RAN A TA UKU

AIKI SAI MAISHI!!
Kamar koyaushe, ya gama shirinsa cikin nishadi da walwala, yana yi suna hira da matarsa kafin su fito yayi breakfast sannan ta rakoshi zuwa k'asa. Ya kwankwasawa Tasleem, suna hada ido suka sakarwa juna tattausan murmushi, hakanan kwayoyin idanuwansu suna aikawa juna sak'onni na musamman.

Kasancewar ba gaba daya ta bude kofar ba, hakan yasa Zahra bata gane wainar da suke toyawa ba. Sai lokaci Tasleem tayi jarumtar bud'e k'ofar, tana mai russunawa ta gaisheshi, ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Zahra ta gaisheta, ta amsa ta tambayeta lafiyarta. Kafin Haris yace "Zan wuce, saina dawo".

Har lokacin murmushi bai gushe ba saman fuskarta "Toh a dawo lafiya my king, Allah Ya bada sa'a". Ya amsa kafin ya nufi hanyar fita, Zahra tayi mai rakiya batare data sab'a iyakar da yayi musu ba. Ya rungumeta ya sumbaci kuncinta kafin kuma ya daga mata hannu "Gudbye my baby, Kularmin da kanki".

Ba tare da gajiyawa ba, Tasleem wajejan sha biyu ta k'ara tura mishi text mai nuni da tsananin kauna da bege. Kafin kuma ta cigaba da girkinta. Fankaso da miya sai

romon kayan ciki da tayi kafin kuma ta had'a lemun citta da fosterclarks na pineapple guda biyu, karshe ta had'a komai takai sama ta jera, lemun kuwa ta sanyashi a firij kafin ta sauko, saida ta kimtsa kicin d'in, harda wanke wanken data tsana a rayuwa tayi, don yafi kowanne aiki wahalar da ita. Ta fad'a wanka, kwalliya sosai

tayiwa fuskarta, ta murza lebb'anta har saida taga jan janbakin data sanya ya zauna d'abas ya daidaitu, kafin ta mike don saka kaya. Riga da siket ne na atamfa skyblue da fari, ta zura rigar dakyar, kafin taja zip. Daga daidai gaban rigar, an bud'e da shape na circle har kana iya hango halittar wajen. Hakanan siket d'in shima ya kamata kwarai, ya kuma zauna d'as a jikinta. Ta sharce gashinta wanda tuni ta tsefe kitson, tayi murmushi, tunawa da gashin dokin da a baya take sakawa duk da daidai gwargwado tana da gashinta.

Ta murza daurin dankwali duk da bata gwanance sosai a d'aura d'ankwali ba saboda bata fiye shigar manyan kaya ba. Saidai koyaya ta murza sai kaga ya amsheta kamar daman can ita d'in ta saba. Tana fesa turare taji hon na motarsa.

Ta kammala, saida ta bawa minti goma baya kafin ta zura takalminta mai tudu bak'i da kwalliya ruwan toka, wanda ya k'arawa k'afarta kyawu da haske, sannan ta bude ta fito. K'amshinta ya karad'e corridor d'in, tana tafiya cikin salo na nutsuwa, a hankali take taka steps din har ta isa ga k'ofar, tana murd'awa ya bud'u alamun daman can a bud'e yake. Sallamarta ta doki kunnuwansu, fitowarsu kenan daga d'aki, da alama cikin nishad'i suke saboda rike yake da hannun Zahra suna dariya.

Tsayar da idanunsa yayi cak ga abunda yafi muradi a rayuwarsa, ganin idon Zahra yasa shi basarwa ya taka zuwa dinning chair ya zauna. Idanunsa sun gaza daina satar kallonta, yayinda ita kuwa take takunta mai fisgar hankali, tana murmushi ta duk'a saitin kujerarsa "My king barka da rana".

Ta fada tana watsamishi salon kallonta da murmushi saman fuskarta. Ajiyar zuciya ya saki, bazai iya magana ba, har lokacin idanunsa sun gaza daukewa daga kanta, gyada mata kai kawai yayi yana murmushi. Cikin dauriya ba kad'an ba, ya kauda idanunsa daga muradinsa yana maida dubansa ga Zahra wacce tuni kishi ya tafaso zuciyarta. Ido ya kashe mata "My baby a zubamin abincin mana".

Jin sunan daya kirata dashi ya sanyayata. Shi kuwa sai kallon tasleem yake awajen firij.
Bud'ewa tayi ta dauko lemu da ruwa duka ta ajiye, kafin ta zauna ta janyo filet itama. A sannu suke cin abincin bayan kowannensu yayi bismillah. A hankali kamar kuma da wasa taji kafar mutum saman nata yana shafawa. Wannan yasa ta dubansa, akayi sa'a ya kallota, saidai fa kallon ya bambanta dana koyaushe, ta nuna masa Zahra (da kanta ke kasa tana kai fankaso baki) da ido, ya harareta kadan kafin ya murmusa, mintsilinta yayi da yatsu biyu, ta yamutse fuska don zafi, kafin ta sanya takalminta ta d'an takeshi. "Aush!" Ya fada da karfi, ganin Zahra ta kalloshi ya wayance da firfita bakinsa "Abincin zafi fa".

 Zahra ta hau sannu kafin ta mike tana fadin "Bari na k'ara fanka, please yayana kaci sannu". "Sannu".Cewar Tasleem, idan ka dubi fuskarta saika rantse batasan abunda ta aikata ba, harararta yayi kafin cikin rad'a yace "Kinci bashi". Murmushi mai bayyana hak'ora tayi batare da tace uffan ba.

Misalin biyar na yamma, Tasleem ta kammala girki har ta zubawa Zahra nata ta mik'a mata, kafin ta hau saman ta ajiye nasu da maigidan nata daga bisani ta sauko ta fada wanka.

Zama na musamman tayi bayan ta goge jiki ta shafeshi da cream dinta mai kamshi sosai. Tayi kwalliya mai fiddo kyawu kwarai kafin ta  mike.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 16"

Post a comment