Results

YAR BARIKI book 2 page 17

Kayanta ta shiga sanyawa, english wears ne,riga da wando. Hum! Ba'a magana, na bar maku alkalam, ku hasko tasleem mai kyawun diri cikin shiga ta kananun kaya maroon colour.

Jikinta kuwa kamar anyi ruwan turare sai mutum ya rasa kalar turaren data fesa, game da makaman aiki kuma, tun safiyar ranar tayi aiki da kayanta. Murmushi ta sakarwa kanta kafin ta dauki wayarta tayi hotuna. Bataso ya dawo bai sameta a saman ba wannan yasa ta yin azamar daukar wayarta da jakar data riga ta had'a, domin daga yau tasa a ranta matukar ta hau wajen mijinta toh ba abunda zai kara sauko da ita sai wata safiyar. Saida akayi sallah yazo!
Itama ta idar da salla harta maida doguwar abayar salla da hijab daki, jin ana kwankwasa kofar yasa tayi saurin mikewa ta bude mishi. Lokaci daya suka sakarwa juna tattausan murmushi kafin ta amshi jakar hannunsa, rik'ota yayi gaba d'aya, ya janyota zuwa jikinsa, a hankali ya tura kofar dakin da k'afarsa. Salo ya soma chanjawa, har ya zamana tsayuwa tana neman gagararsu, tasleem ce ta soma ankara da sautin takalmi dake nufowa saman, hakan yasa tayi azamar janyewa tana mai daukar jakarsa zuwa daki, cikin kasalallan duba yake binta da ido yanajin takaici yanda a katse hanzarinsa. Jin ana shirin turo kofar, ya gyara mab'allin

rigarsa, kafin ya amsa sallamar yana mai sa hannu ya gyara sumar kansa. Zahra ce ta shigo, sukayi murmushi, kafin tayi mishi sannu da zuwa. A karshe ta sauka. Wannan ya bashi damar kutsa kai cikin d'akin, batanan ya jiyo motsin ruwa, ganin bata rufe kofar bane ya sanyashi shiga ciki. Ruwa yaga tana had'amai, ta juyo da murmushi kafin ta hau b'alle mishi botilan riga har lokacin bata yarda koda wasa ta dauke kwayar idanunta daga cikin nasa ba. "Ya dace ayi wanka haka ko my king?" Baida niyyar amsawa don baiji wannan kuzarin ba, hakan yasa kawai ya hau bata amsa ta musamman! Dakyar ta goce ta fita tana dariya.


Ajiyar zuciya yayi, wani zugin kauna yana k'ara k'arfi cikin ransa.
Madallah da wannan dare mai wuyar fassara yanayi da jin dadin masoyan nan! Godiya da yabo sun cancanta ga Sarkin sammai da k'assai wanda Ya halattawa namiji da mace aure, Ya kuma sanya so da kauna marar yankewa tsakaninsu! Kwarai Allah mai iko da baiwa ne! Mak'agin kowa da komai!


Zukata biyu ne da basu gajiya da begen juna, burin kowace zuciya bai wuce ta kyautatawa yar uwarta ba, ta nuna mata tsantsar kauna da tsananin begen da take kwana da yini a ciki. Babu wacce ke fatan rabuwarsu, karshe ma sai zuciyoyin suka raunana bisa tunawa da baya!

Har dai baiwar Allahn ta kasa dannewa kawai ta d'ora kanta saman kirjinsa ta fashe da kuka mai tsanani wanda hawayen ke zuba kamar famfo a saman kirjin nasa. Cikin tashin hankali yasa hannu ya d'ago kanta kafin cikin muryar rad'a yace "Queen, nayi wani laifin gareki ne? Please ki sanar dani, kukanki yana tayarmin da hankali, banason damuwarki. Tab'a kiji yanda kirjina ke bugu tamkar zuciyata zata fito, gayamin me Haris yayimaki, na rantse da Allah zan hukuntashi".

Ta dago kwayar idanunta tana dubansa, tuni idanunsa sun kad'a da alama dai hawaye ke shirin fita daga cikinsu. Ta riko hannunsa "Na tsani kaina ne!" A gigice ya tallafo fuskarta "No please, kibar cewa kin tsaneni, domin wallahi duk wanda zai tsaneki shakka babu ni ya tsana, kuma nima banajin zan k'ara ganinsa da k'ima, amma ke menene ya zafi zaki tsaneni, ko ban gamsheki ba?" Kwayar idanunsa kadai zai baka tabbacin cewar dukkan abunda yake fad'i tsantsar gaskiyarsa ce. Bakinta yayi nauyi, dakyar ta sunkuyar da kanta tasamu kwarin gwuiwar yin ma gana.

"Ka gafarceni my king, ai kai d'in namiji ne cikakke wanda babu macen da bazata yabawa bajintarka ba, saidai inajin nauyi bisa yanda ka riskeni, da...". "Ke mene haka wai? Bana son shirme!"

Ya fada cikin fusata, kafin ya cigaba da magana "An fadamaki wannan kadai shine so? Ko an fadamaki Kauna ce? No tasleem, son da nakeyi gareki so ne na gaskiya wanda babu algus cikinsa. Ina yi maki so wanda baki bazai iya misaltawa ba, na soma sonki tun sadda naji labarinki, tun lokacin nake kwana da wuni cikin tunaninki.

 And you know what? Tun kafin faruwar wani lamari, inada niyyar aurenki. Son da nakeyi maki bai danganci wannan hanyar ba, duk da kwarai nasan wannan ne mutunci da alfaharin diya mace, don wallahi ba don kauna ta gaskiya ba, bazan taba neman auren YAR BARIKI ba! Inada kyankyami, banson kazanta fa. Ya fada kamar yanda zahiran fuskarsa ta nuna hakan kafin ya dafa cinyoyinta,

numfashinsu na gauraya "But you are special to me, ban taba son wata ba yanda na soki, i mean to say, you are my firstlove. Ni musulmi ne, nasan menene KADDARA kuma nasan ladan dake cikin imani da ita. Allah ne kadai zai bani ladan aurenki my queen. Kada ki kara damun kanki, ni sai na jiki ma kamar wata sabuwa, gayamin menene sirrin?" Tana murmushi cikin sanyin murya tace "You want to know?" Gira kawai ya d'aga mata, nan take ta shiga labarta mishi darussan cikin gwanancewa, ganin abun yafi karfina da yan uwana, muka rufe kofar muka barsu.

Wannan daren, dare ne na alheri agaresu, yayinda alk'awurwura da dama suka wanzu tsakaninsu. A safiyar kuwa basu samu farkawa ba sai wajen tara na safe bayan sunyi sallah kenan suka koma. Shine ya soma tashi, ji yakeyi kamar kada yaje ofis, hakanan dai ya fad'a toilet. Rufe kofarsa ne ya farkar da ita, ganin lokaci ya sanyata mikewa da azama. Saifa lokacin ta tuna da saukarta k'asa ya zama dole saboda had'o kayan karin kumallo. Taja tsaki ba don taso ba, ta fiddo wa mijinta kaya ta feshe da turaruka kafin ta zura doguwar rigarta da hijab ta sauka.

Saida ta hada komai sannan ta komo saman, daman breakfast yanzu kowacce nata takeyi. Bai riga da ya fito falon ba, tayi mamaki, tun kafin ta karasa ta fidda hijab dinta, daga ita sai doguwar riga. Ta iskeshi yana zura riga, sukayi murmushi batace komai ba ta fara shiga ta wanko bakinta, kafin ta durkusa ta gaisheshi ya amsa mata yana mai d'agota ya hada da jikinsa. "

Ya daren jiya?" Babu wani abu wai kunya daya rage tsakaninsu, ta dora hannuwanta bisa kafadunsa cikin narkakkiyar murya tace "Bazan iya misalta zumar dake cikinsa ba". Yayi murmushi mai bayyana hakora "Dagaske?" Tana mai basarwa tace "Ba laifi". Sukayi dariya Koda sukayi zaman karyawa, bayan ta kammala had'a mishi ta zauna sannan ta dubi bangon da har dubansa ya zame mata jiki duk da ba hoton.

Juyowar da zatayi sukayi ido hudu, yana murmushi yace "Kina yawan kallon frame dinnan, koda dai tun kafin na sanyashi ne, why?" Ta tsuke baki "Tunda ka fadi haka ai kasan meyasa nake kallo hakanan ka rabani dashi". Ya harareta da wasa "Meyasa kika k'i gayamin? Wacce ta fiki so ai kinga ita tayi magana". Ta daga kafadu nuna rashin damuwa, "Ai kun kyauta, nima sai a wankomin irinsa inaso". "

Haris kikeso kenan?" Wani murmushin tayi da gefen kumatu daya tana mai tsuke baki bata tanka ba. Ya numfasa cikin jin wani sanyi a ruhinsa, ya hakikance komai na Tasleem daban ne dana sauran mata. Kb! Shine wanda ya fad'o mishi a rai. Ya godewa Allah daya zamana shine mai nasarar samunta.

Har kasa ta rakoshi, ta wuce kofar dakin Zahra tayi gaba har baranda ta tsaya, saida ya kwankwasawa Zahra sukayi sallama kafin yabi bayan tasleem. Ta mika mishi jakarsa, ya hada da yatsunta "Take care".

Zai tafi tayi azamar riko hannunsa "Af nayi mantuwa". Yayi mata duban alamar tambaya ta sumbaci kuncinsa kafin tace "Mazan ne ko matan??" Daga haka tayi dariya tana daga mishi hannu tayi ciki abinta.

Ya murza hanci yana mai tabe baki "Jimin queen da wata tambaya? Maza ne koyaushe da higher marks, right?" Ya dubi hagu da dama babu mai bashi amsa, kawai ya murmusa ya fice.

Haka rayuwar gidan Haris ta cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da lumana. Ga surukansu kuwa, sai sambarka. Ba ga mamin ba, ba kuma ga mahaifiyar haris ba, wato Umma, dukkansu suna nuna kulawa garesu hakanan basu nuna bambanci wai zahra ce ta jikinsu sosai. Gwara gwara ma Umma takanji nauyinsu.

Tuni Zahra ta soma zuwa makaranta, hakan yakan sosa ran Tasleem taji inama ta samu wannan damar. Har dai tayi karfin halin tambaya rannan.

Zaune suke a barandar shan iska dake daga can gefe idan an bude wata kofa a falon haris. Yammaci ne mai dadi, iska ke kad'awa mai nuna alamun lokacin sanyi ya soma shigowa. Kwance yake akan restingchair dake wajen, fuska dauke da murmushi yayinda idanunsa ke a lumshe sanadin dadin da yakeji na tausar da takeyi mishi. Ya gama shantakewa kawai yaji taja yatsan yayi k'as, da sauri ya bude ido ya mike zaune gami da sakin karamin ihu. Tayi dariya ya girgiza kai kawai ya koma ya kwanta "Yarinyarnan zan soma zaneki kenan, K'iriniyarki tayi yawa". Tayi dariya yana tayata, damar nan take jira daman, ta sameshi ciki nishadi
"My king".

Ta furta a shagwab'ance, ya dubeta duban da tafi muradi akan kowanne salon kallo da zaiyi. Fuskarsa da murmushi saidai bai amsa ba, ta numfasa kafin tace "Inada wata bukata awajenka". Jin hakan ne yasa shi mik'ewa zaune, sai lokacin yayi magana

"Game dame fa?" Ta hadiyi miyau cike da fargaba, kafin tace "Kayimin iznin komawa ga karatu..". Sauyin data gani a fuskarsa ne, ya sanya bata k'arasa ba, tayi gum. Fuskar nan tamkar bai tab'a dariya ba, cikin kausashshan murya ya soma magana "Nayi zaton shiruna ya isa ya fahimtar dake ashe baki fahimceni ba, ki gafarceni, amma ko kusa bazan tab'a samun nutsuwar hakan ba.

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 17"

Post a comment