Results

YAR BARIKI book 2 page 18

Bazan iya barinki ba Queen, wanda kikayi ma Allah Ya amfana, saidai keda karatu kuma?" Ya girgiza kai kawai kafin ya mike ya shige daki, ta tsurawa jug mai dauke da orange juice dake saman tebur ido, a sannu taji hawaye sun zubo mata tana tariyo maganganunsa.

Kai jama'a, tirr da abunda zai zamto silar da mijinka zai soma zirginka. Ina amfanin Ranar Nadama haka? Yau gashinan ta yiwa kanta, da ace duk haka bata kasance ba da babu wani abu da zai janyo mata wannan matsala. Yau gata ga babbar dama ta cigaban karatunta amma Haris yace sam! Dana sanin barikanci ya k'ara mamaye zuciyarta, taji tsanar Momi. Wai tana ina ma??!

Ta tambayi kanta, ya manal tayi da auren Alhaji Ubale? Dalal fa? Ta bar wannan hanyar ko kuwa dai ta cigaba? Hibba tana ina yanzu? Babu amsa, wannan yasa tayi fatan shiriya garesu kafin kuma ta jiyo muryarsa yana kwala mata kira, ta mike tabi bayansa.

Daga kasa a farfajiyar, ni da jama'ata muna zaune a saman kujeru muna hangensu, anan na numfasa na dubesu, zanyi magana ummu faruk ta rigani da cewa "Kwarai, ya kamata mu bincikowa taslim amsoshinta". "Ni kaina abunda na matsu naji kenan". Cewar asiya rafin dadi, kafin zainab sirajo ta mike "Idan kunyarda zanje na dubo". Mukayi na'am ta mike, ga bayanin da muka samu akansu.

Rayuwa tana tafiya ba yanda ake so ba ga Hajiya Hannatu, Momi. Harkoki sun soma dagule mata sakamakon wani mugun dan kasuwa daya sakota a gaba akan sai ya dauki fansar mugunta da tayi mishi na hadashi da yarinya mai dauke da cutar kanjamau wanda sanadin hakan shima ya kamu da ita. Sanin kowa ne, Alhaji Sa'ad Kwangila shahararran dan kasuwa ne mai ji da tarin dukiya.

Saidai duk da dukiyarnan, bai taba koda wasa ya fidda zakkah ba, asalima mutumin ya kasance mai auri saki wanda wasu da sukasan mutuncin kansu, basu amince su bashi auren yaransu ba, masu kwadayin abun duniya kuwa, su bayar.

Dukiya bata wasa ba yake cika iyayen yarinya dashi wanda yakan makantar da idanunsu su dauki 'yarsu ko tanaso ko bataso su bashi, idan yayi watannin biyar dake toh alal hakika kin taki sa'a.

Da zara kin samu ciki zai soma wulakantaki.
Bayan haka kuma ya kasance manemin mata na gani a fada, baya damuwa da dukkan zagin da mutane kanyi masa, kodayake dai ga wadanda sukasan asalinsa basu fiye mamakin wadannan halayya tasa ba, yo mutumin daya haik'e dukiyar marayun Allah, ya hanasu tayaya zai ga haske a rayuwa? Shine fa wanda uwarsa ta fito bainar jama'a tana kai masa duka tana tsine masa fa, ai sai fatan shiriya!.

A wannan rayuwa ta bariki, ya hadu da Momi, sakamakon jan da wani abokin shiriritarsa, Alhaji Fa'iz Hamdala, yayi masa zuwa gidanta. Anan ya nemi shima ta bashi ta rage dare cikin zuk'a zuk'an yanmatan dake gidan, wadanda a haife ya haifesu, basu fi sha takwas zuwa ashirin ba, hakanan suka sanya kansu awannan gurb'atacciyar harkar. Ba musu momi ta kiraye su, suna wani kwarkwasa har dai da kansa ya zab'i Jiddah Yola, sai gashi sakamako baiyi kyau ba. Toh wannan dalilin ne ya harzuka Alhaji kwangila har yaci alwashin daukar fansa akan Hajiya Hannatu da Jiddah  Yola.

Tun sadda Momi ta samu wannan bak'in labarin ta rude!
Ya zamana ta soma kokarin ganin ta sanya an kawar da Alhaji kwangila kafin shi d'in ya dauki matakin daya shirya a kanta. Ta dubi jidda yola rai b'ace, "Na rasa yanda akayi nayi sakaci wajen auna lafiyarki kamar yanda ya zamemin farillah.

Kowace yarinya dake gidannan bana bari ta soma harka da customers dina har sai na kirayi doctor lurwan ya d'ebi jininta ya kawomin cikakkiyar shaida akan ingancin lafiyarta, yau gashi a garin wannan karamin kuskuren kin janyomin matsalar da take neman fin karfina! Yanzu menene mafita?!" Cewar momi cikin daga murya,

tana duban mutanen dakin wadanda dukkansu suka amsa gayyatarta!
Daman sunyi mamakin kiran gaggawar data sanar a group nasu na whatsapp ashe matsalar takai har haka? Lallai uwar barikin tasu tana cikin mugun tashin hankali. "Ai wannan ba na ganin wani abu ne na tada hankali, ita dai wacce ta janyo matsalar, ita kadai zata iya maganceta". Cewar Dalal, cikin muryarta wacce zuwa yanzu koda bata cikin maye, saika rantse a buge take. Duk suka dubeta, momy ta zauna tana duban Dalal, "Yi mana gwari gwari yanda zamu fahimta".

Dalal tayi dariya kafin ta fesar da hayakin sigari, "Itace zata koma ta aikashi lahira, nasan yanzu kun fahimceni?" Jiddah Yola ta dubeta a razane "Ta yaya zan kasheshi?
Harararta Dalal tayi, kafin tayi magana, Hibba ta rigata "Don ubanki ta yaya kika ci kudinsa?" Jiddah taja tsaki "Wannan kuma inaga ko sabon shiga a bariki, banajin zaiyi mata wuya, amma wannan ana magana ne na kashe rai, idan hukuma ta sani fa?" Momi itama ta jinjina kai, "Gaskiyarki jiddah, bama fatan hakan shiyasa muke kaffa kaffa don yanzu tsaro ya samu sosai,

kuna sane cewa gwamnan Kano na yanzu, Dr Ahmad Bichi (a cewata,lol) baya wasa da aikinsa, anan ansha aikomin da wasika akan gwamnati na sane da abunda muke shukawa, ta bani lokaci na sallami yaran mutane, ba don akwai masu amsar cin hanci ba, da tuni mun watse..!

Momi ta k'ara dubansu "Don haka, bana tsammanin kyakkyawar shawara ce wannan kuka bayar, a dai nemo wata mafitar". Wata dattijuwa wacce takai shekaru arba'in kuma tsohuwar kilaki ce, don kuwa har shege ta tab'a haifa ta jefar a bola, Hajiya Zeenat kenan.

Ta tari numfashin Momi da cewa, "Haba hajiya, yau muka saba karawa da hukuma? A ganina shawarar da Dalal ta kawo shine mafita kawai, barin wannan hatsabibin mutumin a doron k'asa babbar barazana ce, sau nawa muna sanyawa a kashe rai ko a lahantar? Kin tab'a ganin tonuwar asirinmu ne? Ai duk wata hukuma tasan wacece mace! Ba dole jidda zatayi ba.

Dalal ta girgiza kai, "Aa momi zeenat, babu wacce zata iya wannan aikin cikin sauki sai jidda, akwai wata dabara da zamu shirya, na tabbatar maku cewa baza'a sami matsala ba". Duk suka zuba mata ido, kafin Momi tace "Fad'i muji".

Ta kalli matan dake falon, kafin ta danyi shiru cikin chanza shawara "Amma kuma momi kina da gaskiya, kisa bai zamo mafita garemu ba a wannan lokacin, ya dace dai a bawa kowa dama yaje yayi tunani nan zuwa safiyar gobe". Sukayi na'am da hakan, bayan sun jima anan ne sun tafi harkokinsu, dalal ta yiwa momi waya cewar zata zo misalin daya na dare suyi magana, ta sanar da ita abunda ta yanke. Jin haka, hibba tayi dariya kafin ta dubeta kadan "Kinsan risk din da kike shirin jefa kanki ciki kuwa? Wannan sam ba mafita mai kyau bace madam, domin wannan aikin nasu Samuel ne, sune yafi kyautuwa suyi".

Dalal ta danyi shiru kafin ta dubeta "Kina ganin Samuel da yaransa ba zasu kawo cikas...". "Haba dalal, wai yau ne muka saba wannan aikin ne? Kodai kin manta ne cewar Samuel sune sukayi aikin kawar da hamshakin mai kudin nan kuma mai neman takarar gwamnan garin minna? Toh waye kwangila kuma?" Dalal ta jinjina kai cikin gaskata maganar hibba, karshe tayi na am da shawararta "Shegiya tawan, ba

dai hangen nesa ba. Hibba tayi murmushi "What are friends for? Ni yanzu chanjin Manal ke damuna, anya bazata juyawa kungiya baya ba kamar yanda baby tayi?" Dalal cikin neman karin bayani ta dubeta "Me kika gani?" Hibba ta girgiza kai, "Jiya kafin na baro Abuja na biya gidanta, hakikanin gaskiya na tsorata da ganin yanda take rawar jiki akan Alhaji Ubale. Abunda ya ban mamaki, wallahi nakai minta sha biyar ina zaman jiran

dawowarta sai gasu sun fito suna dariya, yana ganina ya daure fuska, kadahan kadahan muka gaisa yayi awon gaba, nan ma ta tafi rakashi sun jima kafin ta dawo. Hum, wai ce mata yayi nabar zuwa gidan, ko a waya mu dunga gaisawa! Nayi mamaki kwarai, ke nidai na sare da lamarin Manal tamkar ba itace mai zafin nan ba mara daukar raini wacce bata tankwaruwa".

Dalal ta saki ashariya tana jijjiga jiki kamar zata tashi sama "Wai dagaske kikeyi? Haba no wonder idan na kirata bata fiye dauka ba ashe mu zata rainawa hankali? Lallai tayi kuskure babba, da ace ta san wahalar dake a rayuwar aure da bata biyewa Baby ba. Nikam idan har jaki zaiyi k'aho to ki tabbatar da cewa zan fita daga bariki. Ai kina gani dai ko arba'in na gwaggo (gwaggon dalal, idan baku manta part 1 ba!) ban bari anyi ba na dawo ruwa, yo inace itace ta dorani kan turbar?" Taja tsaki.!


"Babu wacce ta bani mamaki kamar Baby, dubi fa yarinyar nan tana kan ganiyar holewarta da tashen naira amma tayi watsi da komai ta kama wani shirme wai aure? Toh ai shikenan suje suyi tayi, shegiya Manal, bari mu rufe wannan case din, takanas zanje har gidan nata sai naga tsohon najadun da zai yimin iyaka da k'awata. Ai cin amana ne kawai bayan sunyi aure su watsar damu, ko babu komai ai a baya sunyi abunda mukeyi har suka fimu kwar ewa".

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 18"

Post a comment