Results

YAR BARIKI book 2 page 19

Hibbah tayi dariya "A'a toh, nima a baya ba don fa kin hanani ba da tuni nayi auren wata ukun nan, kice nima da kusan hakan ne zai kasance dani?" Dalal tayi wata yar iskar dariya "Ai ke kam da sauki, kinga yaron da kika jajub'o akwai naira, kuma yana ji da yarinta bazaiyi wuyar juyawa ba."

Hibba tayi kwafa tana murmushi "Hum! Lallai Dalal kin raina HAYAT, nan da kike ganinsa yasan abunda yake. Da fari fa da naje mishi da maganar auren wani kallon zargi yayimin, wai meyasa nake sha'awar muyi aure bayan a baya na tabbatar mishi ni d'in 'yar sharholiya ce? Ke ba don dai ni d'inma tsohuwar hannu ce a bariki ba da alokacin ya tutseni, sai ga shegen harda zuwa a sanarwa iyayensa. Inda baki haneni ba ai da tuni na tsufa gidansa."

Sukayi dariya, Dalal tace
"Shegiyar gari kawai, yanzu meye abun dadi a aure? Haka kawai wani k'aton gardi(wa'iyazubillah) ya ajiyeka a gida da sunan karkashin ikonsa kake, yayita juya ka kamar waina? Never, bazan tab'a yin aure ba wallahi."

Hibba tayi murmushi
"Mutum d'aya nakeji ko gobe zan iya watsar da komai na aureshi matukar zai amince da sharad' ina."

Cike da mamaki Dalal ta dubeta "Wa kenan?"
"Garba". Dalal ta yamutse fuska "Menene wani Garba? Kicemin Abubakar malama. Toh shi kuma wane tsamin ne? A ina kika jajib'o shi?"
Hibba tayi dariya daidai lokacin da take kokarin shiga harabar hotel d'in

"Tsohon saurayina ne, adalilin babana ya hanani aurensa ya sanya na shigo duniya, Baraka yar uwarsa ce yar kanwar mamansa, kuma aminiyata a baya wacce take karatunta anan B.U.K kamar yanda kika sani, ta hanyarta nake aikawa mamana sak'o. Ke kwana biyun nan ma na daina aminta mu had'u da ita, tun sadda tace min umma ta matsa akan saita kawota wajena. Garba kuma yana da mata da d'iyarsa yanzu, shi kadai ne muddin zai saki matarsa zan aureshi na watsar da komai don babu laifi yayi kud'i."

Dalal ta tab'e baki kafin ta soma magana tana kokarin bude mota. "Kuna da matsala wallahi, aure aure dai kamar wani tsiyar ne cikinsa? Dallah ki bud'emin k'ofar".

Hibba tana dariya ta cire mata key ta wajenta kafin ta fice daga motar. "Dalal ko bala'i?" Ta fada a fili kafin ta kashe komai ta rufe kofar tabi bayanta.
*******

Kamar yanda suka tsara d'in, wajen biyu saura suka isa gidan Momi. Tuni daman Dalal ta yiwa Samuel magana akan su had'u gidan. Ya rigasu isa ma. Samuel mutumin kudu ne, amma idan kaji yana Hausa saika rantse haifaffen arewa ne. Nan suka tsara komai, Samuel ya amince zaiyi. Bayan an kammala komai ne, Momi ta k'ara duban Samuel "Sam, ka tabbata baza'a sami matsala ba?" Yayi dariya, kafin yayi magana Dalal ta  rigashi

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 19"

Post a comment