Results

YAR BARIKI book 2 page 20

"Haba Momi, kiyi masa fatan alheri kawai mana. Ita kuma waccan tsinanniyar da zarar komai ya kammalu ki koreta". Sukayi na'am da hakan.
********
TASHIN HANKALI!!!!

Dalal tana kwance saman gado tayi rigingine tana chatting, wayarta tayi k'ara, ganin sunan Momi ne, yasa ta mik'e zaune tana murmushin sanin kanun zancen bai wuce su Samuel sun cika aiki ba.

Saidai tana dauka ta jiyo hayaniya, cikin fusata Momi ke cewa "Dalal gashi komai ya b'aci, an samu matsala, Sam da wasu cikin yaransa suna hannun yan sanda!" Dalal batasan sadda tayi wata wawuyar mikewa ba, cikinta ya bada wani irin sauti saboda tsananin rud'un da ta shiga. Saidai sanin halin momin tasu da barkwanci yasa kuma ta karyata a farko, bayan ta numfasa tace

"Momi yau ma wasan ne?" "Wane wasa anan inayi maki zancen gaskiya? Ni yanzu dole nabar garin nan domin ko inspector yakubu dana buga masa cemin yayi babu ta yanda zai iya sanya baki domin kuwa hannun wanda su Samuel suka fad'a baisan wani maganar cin hanci ba ballantana muyi tunanin bayarwa. Kuma ga maganar kashe Alhaji Kwangila ta bazu don akwai wadanda suka bada shaidar ganin fitarsu Samuel daga gidan, ke bazan iya dogon bayanin nan ba yanzu, nasan kowane lokaci zamu iya ganin dirar yan sanda a gidannan."

Daga haka Momi ta katse kiran, cikin tsananin tashin hankali Dalal ta jefa wayarta kan gado kafin ta janyo akwatinta ta hau jefa kayan sawarta a ciki, ai idan asiri ya tonu zata fi Momi matsala tunda da shawararta ne aka aikata kisan. Daidai lokacin hibba ta fito daga bandaki cikin tashin hankali saboda tana sauraron wayar da Dalal tayi da Momi, wuyanta duk kumfa ta dubeta "Me naji kuna fad'a keda Momi?" Dalal cikin rud'ewa ta sanar da ita komai, ta k'ara da cewa "Ina! bazan k'ara kwana garin nan ba, dole mubar garinnan."

 Sai lokacin ma Hibba ta lura da akwatin da take lodawa kaya,ita kanta ta rud'e, toh me zata zauna tayi itama bayan da tasan an jima ana son cafkesu yanzu kuwa da dama ta samu mezai hani hakan yiwuwa? Ai itama batayi wata wata ba ta soma shiri.
******

Gudu takeyi kamar zata tashi sama, kallo daya zai tabbatar maka ba cikin hayyacinta take ba.

 Hibba wacce zafi biyu ya had'e mata, na tunanin makomarsu dana tashin hankali da tsoron irin gudun da Dalal keyi wanda ya tabbatar mata saida Dalal ta hadiyi kwayoyin data saba kafin ta kama sitiyarin. Ganin da wannan gudun nata dakyar ya kaisu Abuja lafiya yasa ta dubeta "Dalal ki tsayar da motar ki bani na tuk'amu, wannan gudun naki na ganganci ne yayi over." Dalal ta kundumo ashariya ta k'ara da cewa "Yar tasha tsinanniya, idan bazaki bini ba ki sauka daga motar nan banson iskanci."

Wani kuuu da Hibba taji ne yasa ta yin k'ara gami da toshe kunnuwanta, wai ashe babbar mota ce suka kusan gogar juna Dalal ta goce. Ai da k'arfi tace "Tsaya!! Ki tsaya!!! Wallahi zan sauka, idan banyi kwanan cell ba zanyi na kabari indai da irin wannan tuk'in zamu cigaba da tafi.." Kafin ma ta k'arasa Dalal taja burki ta tsaya, hibba tasa hannu saman kujerar baya ta janyo akwatinta sannan ta dauki jakar hannunta ta bude kofar ta fita bayan ta dubi Dalal tace "Allah Ya tsare toh."

Daga haka ta sauka don ma inda Allah Ya taimaketa sun kusa Zaria. Dakyar ta samu motar hawa, nan dinma sai a gidan gaba kusa da wani matashi ta zauna. Suna tafiya saidai tana lura da mayen kallon da yakeyi mata, hakan kuma yana da alak'a da dan iskan shigar dake jikinta wanda a garin sauri ko bireziya bata saka ba ga wasu English wears da suka d'ame jikinta abun dai abun tirr!
Har wani gwauron numfashi yaja.

 "Idan har ka aikata abunda muka sanyaka, lallai zaka samu abunda kakeso komin girmansa a duniyar nan." Wadannan kalaman shugaban kungiyar nasu ne na mafia. Ya k'ara satar kallon Hibba, ransa yayi mugun kwadaituwa da ita bayan haka kuma ga tsananin buk'atarsa na ganin cikar burinsa na son zama hamshak'in mai kud'i.

"Ka kawo dukiyar fulanin mace guda d'aya tak na b'arin hagu kuma bana matacciya ba, babu abunda bazaka samu ba idan ka cika umarnin kungiya."

Ya k'ara tunano wasu cikin zantukan shugabansu. Hakan yasa shi samun karfin gwuiwa musamman da aka taki sa'a ya lura cikin yanayin firgici take. "Sannu ko?"
Ya fada yana dubanta, ta dubeshi, kallo daya zaka yiwa fuskarta kasan cewa tabbas bata cikin nutsuwarta. Dauke kanta tayi bata amsa mishi ba. Baiyi zuciya ba yayita gwada sa'a cikin dabarunsa na kwararren dan iska kuma tsohon hannu har saida ta sanar dashi cewar tana tattare da damuwa ne. Ya nuna tausayinta ya tambayi wajen wanda zataje a Kd, tace bata da kowa, niyyarta daga can tayi Abuja ta kama d'aki a hotel. Ya girgiza kai "Idan babu damuwa mezai hana ki tsaya anan kd, tunda ni inada gida kinga you will be safe akan dai kije wani wurin."

Ta dubeshi ya sakar mata murmushi, ta sauke ajiyar zuciya ta maida kanta ga titi "Shikenan, nagode." Yayi wani mugun murmushi yana mai hamdala a ransa.
Hakan kuwa akayi, suna isa Kaduna ya biya kudin motarta kafin ya samar musu abin hawa har zuwa dan flathouse din da yake zaman haya.
Hibba na tsaye tana k'arewa karamin falon kallo ya shigo, ta dubeshi sukayi murmushi

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 20"

Post a comment