Results

YAR BARIKI book 2 page 21

"Sannu fa, nasan kin gaji ya dace ki d'anyi wanka ko?" Ta girgiza mishi kai "No bani da damuwa, saidai zan kama ruwa, ina toilet din?" Ya dauki akwatin kayanta yana murmushi
"Biyoni."
Ba musu tabi bayansa batare da fargabar komai ba.
*******

INA LABARIN SU MOMI???
Ance rana dubu ta b'arawo, rana d'aya ta mai kaya. Kwarai na yarda da wannan zancen domin kuwa wannan karon lamura sun kwab'ewa Momi da kungiyarta fiye da tsammanin mutum. Duk yanda taso ta b'ullowa al'amarin ta kasa a karshe suna shirin tattara yanasu yanasu sukaji dirin motoci. Hanjin cikinsu ya kad'a, babu hanyar tserewa domin kuwa yan sandan nan zagaye gidan sukayi, hakanan aka titsa k'eyarsa da duka da mari aka wurwurgasu cikin mota sai police station.

Haka aka titsa Momi da tambayoyi bayan an nuna mata Samuel, Inspector Bashir ya dubeta

"Kinsan wannan?"
Cikin rawar jiki ta dubi Samuel wanda duk fuskarsa ta chanja da ga jini ga kuma kumburi. "Kinmin shiru!!" Ya fada cikin tsawa yana buga tebur wanda saida duka sauran matan barikin suka tsorata. "Oga tasann..." "Shut up!!" Ya katse Samuel daya tsoma bakinsa, da sauri Samuel yayi tsit babu shiri. Inspector Bashir ya k'ara cewa "Idan ka k'ara sanyamin baki a aikina sai na fasa bakinka." "Sorry Sir."

Ya maida dubansa ga Momi dake kuka cike da tsoro
"Hannatu ki bamu hadin kai, idan kuwa kikace zakiyi mana wasa da lokacinmu lallai ki sani zamuyi wasa dake kema. Domin jina jina zamuyi maki. Ki bani amsoshina sai komai yazo da sauki."
Ya gyara zama kafin ya cigaba
"Ki bani amsar tambayata ta farko, kinsan wannan mutumin?"

Momi wacce kukanta ya tsagaitu, ta dubi Samuel tana muzurai kafin ta girgiza kanta ta dubi inspector
"Ni bansanshi ba, yau na soma ganinsa ma."

Samuel ya bude baki zaiyi magana, Inspector Bashir ya dagamishi hannu, ya dubi Momi yayi murmushi kafin ya dubi sajan isa "Kana iya mik'omin wayoyin nan."
Sajan ya sarawa ogansa sannan ya juya ya nufi 'yar kwabarsu ta ajiye evidence. Wayar Momi ya dauko data Samuel ya kawowa Inspector.

Inspector ya kunnasu kafin ya mik'awa Momi nata
"Fiddamin password din." Hannunta yana rawa, ta karb'a, wani irin gumi ke tsatstsafo mata, ga wani fitsari da takeji. Ayau tana mai dana sanin rashin goge sak'onni da logs da batayi. Aikam asirinta ya gama tonuwa. Dakyar ta bude sakamakon tsoron shan kulkin da takeyi. Ta mik'a masa. B'angaren sak'onni ya soma shiga, domin son ganin ko itace Samuel ya aika sak'o yake shaida mata ya cika aiki. Ai kuwa shine sak'o na biyun k'arshe daya shigo wayarta, na karshen kuma shaida mata yakeyi an samu matsala. Sai kuma b'angaren kira daya iske lambobi uku da tayi waya dasu tsakanin lokacin da abun ya faru da yanzu. Daya da ma'aikacin da ya bashi mamaki ne, inspector yakubu? Menene had'insa da wannan kilakin? Dayan kuma wata ce wai ita Dalal sai lambar k'arshe na Samuel wanda sune suka sanyashi yayi kira don ya bugar musu cikinta don son sanin inda take, sai akaci sa'a ma bata bar gidannata ba.

Tabe bak'i yayi, kafin yayi mugun murmushi ya dubi Momi
"Ummmm! I see, ashe akwai masu daure maki gindi ki aikata son rai a garin  nan?"

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 21"

Post a comment