Results

YAR BARIKI book 2 page 22

Ya gyara kai, kafin ya bud'e sak'onnin ya mik'a mata wayar
"Dukkan wani tabbaci mun samesu akan lallai kinsan wanene Samuel kamar kuma yanda kike da hannu a kisan Alhaji Kwangila. Don haka babu wani b'oye b'oye, ki bani labarin yanda akayi kuka kashe Alhaji Kwangila, da kuma dalilinku."
Ganin da tayi fuskarsa a daure, yasa ta nutsuwar da babu shiri, tiryan tiryan ta labarta mishi komai, sai lokacin sauran matan kungiyar suka san komai domin kuwa basu da labarin hakan, banda Allah Ya isa babu abunda sukeyi. Ya dakatar dasu ta hanyar tsawatarwa, ya maida dubansa ga Momi
"Yanzu ina ita Jidda Yolar? Ina kuma wacce kika ambata da Dalal?"
Ta hau rarraba ido cikin matan wajen, kafin ta nuno Jidda wacce ke rusa ihun kuka, ya jinjina kai  yace


"Dalal fa?"
Momi ya girgiza kanta
"Tun bayan da mukayi waya na sanar da ita halin da ake ciki ban k'ara ganinta ba."
Inspector Bashir ya mike bayan ya bada umarnin a maidasu cell a rufe har zuwa lokacin da zasu mik'a case kotu, kafin ya bawa yaransa umarnin nemo Dalal aduk inda take. Daga haka ya dauki sanda da hularsa yayi ofis dinsa bayan ya tafi da wayoyin Samuel da Momi... .!

Acan kuwa, Hibba ce, tuni ta kammala kimtsawa ta zauna tana mai kunna TV saboda rashin ganin wannan matashin, saidai ba kallon takeyi ba. Tana zaune shiru tana tunanin abunda zai biyo baya, yanzu ko ina Dalal take? Allah Sarki, yanzu Momi tana wane halin? Taji tanason sanin halin da Dalal ke ciki, hakan ya sanyata mikewa da zummar shiga d'aki ta dauko wayarta taji an turo kofar an shigo. Ido suka hada ta sakarmai murmushi. Ya maida mata martani, hannunsa rike da leda irinta take away. Ya karasa shigowa yaja kofar ya rufe
"Sannu fa, kinjini shiru ko? Na samo maki abinci ne naga kamar kina tare da yunwa."

Taji dadi kwarai domin kuwa lokacin da suka baro otel, karfe sha daya na safe, kuma babu wanda yayi kari cikinsu.
"Nagode fa."

Nan ya ajiye ya shiga kicin ya wanko musu faranti da cokula biyu ya kawo musu kafin kuma ya juye musu suyi zaman dirshan su soma ci. Anan ne yake shaida mata sunansa, Zakari (saidai fa asalin sunansa, Na'im). Ya sanar da ita karatu yakeyi anan jami'at kd, iyayensa suna Kano ne.

Bata kawo komai ba itama ta sanar mishi sunanta. Haka dai suna hira da dariya har dai ya bijiro mata da bukatarsa, baiyi mamakin yanda ta soma bayar da kai ba bori ya hau. Nan dai lamura suka gudana, abin tirr har ya b'aci don yawaitar da yayi. A karshe ya zauna saman gadon yana mai tuntsirewa da dariya na rashin imani. Hibba tun tana murmushi har dai ta tsaya cak tana dubansa

"Wai lafiyarka kuwa Zakari? Ina fatan dai kwalliya ta biya kudin sabulu?"
Ta fada tana murmushi hadi da k'ara gyara zaman bargon dake rufe da kirjinta tana dubansa. Sai lokacin ya tsagaita da dariyarsa ya dubeta
"Kwarai ma kuwa, ina zuwa."

Ya mike ya zura suturarsa kafin ya fice daga d'akin. Ta muskuta tana sakin hamma, lokacin Magriba ta kawo kai, abun kunya babu azhar balle ayi batun la'asar koda dai asubahin ma bata samu shiga ba. Lumshe ido ta d'anyi, taji shigowarsa saidai bata bud'esu ba, bata ankara ba taji mutum ya danneta. Tana dariya ta dago idanunta, saidai ta tsorata ainun ganin yanayin fuskar tasa babu digon imani, ga wani sharb'eb'iyar wuk'a a hannunsa, ya d'ora wani jan abu a goshinsa. Hannunsa daya dake dunk'ule ya bud'e, zatayi magana tana zillo, amma tuni ya watsa mata wannan abun mai kama da hoda a fuska, nan take ta sume.
******

TASLEEM FA???
Tsaye yake gaban madubi yana afkin gyara zaman hularsa,lokacin karfe goma na safe yayi shirin fita zuwa wajen aikinsa. Satar kallonta yayi ganin yanda take kumbure kumbure tana wani mustsika ido kamar mai kuka. Murmushi ya saki gami da soma rera wak'a


"Iye yaraye a,a iye yaraye muyi soyayya,bari kijini tasleem,ayau dake nakeyi,soyayya,don yau fa ke nakeso...muje Abuja,can can muje Abuja muyi soyayya."
Batasan sadda ta kyalkyale da dariya ba shima yana tayata,ya ajiye kwalbar turaren dake hannunsa ya juyo,yana mai nufota. Ta harareshi cikin wasa tana mai marairaice fuska,bai fasa rik'ota ba. Har saida ya dangana goshinsu wuri guda
"Hey Queen,fushin na menene haka?"
Ta janye fuskarta ta zauna gefen gadon cikin shagwab'abb'iyar murya tana wani bubbuga kafafunta tace
"To ba kaine ka k'i yarda naje shopping ba,shikenan ni nidai koyaushe ina k'ulle a gida,kullum kaida kanwata ku tafi ku kyaleni,nida i...."


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 22"

Post a comment