Results

YAR BARIKI book 2 page 31

"Sisna marar ce ko? Tun safiyar yau kike complain a kanta amma kink'i muje asibiti."
Zahra tayi murmushi cikin dauriya
"Kai anti,bafa wani abune ba,zai warware,d'an rikewa kawai yakeyi."

Haris dake sauraronsu ya mike zaune
"A'a,wane d'an? Tashi dole muje asibiti."
Haka suka matsa mata,babu yanda ta iya dolenta ta mike. Tasleem ce ta janyo akwatin da tuni sun had'ashi,Haris kuwa ya tafi tayarda mota,suka dunguma asibiti. A mota ciwo ya k'ara k'arfi,hankalin Tasleem ya tashi,ta hau sannu babu iyaka hakanan Haris shi dinma kasancewar bai taba kai mai nakuda asibiti ba hankalinsa bai jikinsa sosai har suka isa asibitin da take awo. Sun amsheta da gaggawa,Tasle ta gaza nutsuwa,musamman yanda ta jiyo wasu matan suna ihu da kuka da kiran sunan Allah. Wadanda ba musulman ba sai ambaton Jesus sukeyi.

Kawai taji kuka ya kwace mata ta fito wajen da Haris yake,yana tsaye ya rungume hannuwansa a saman kirji yana safa da marwa,ganinta cikin wannan halin yasa hankalinshi tashi,ga kuma idon mutane dake gun babu damar ya rungumeta saidai duk da hakan yayi kokarin dafa kafadarta da riki hannunta cikin tashin hankali

"Meke faruwa? Ina Zahra?"
Tayi kokarin tsaida kukanta
"Tana ciki,da saura bata haihu ba."
Zai watso mata tambaya na dalilin kukanta sai kuma ya fasa sakamakon nurse din data fito tana tambaya

"Ina wadanda suka kawo Zahra'u Yusuf?"
Da sauri suka nufeta
"Gamunan." Tayi murmushi
"Toh Alhamdulillah,ta sauka lafiya,an samu baby boy."

Farin ciki gun Tasleem da Haris ba'a magana kafin kuma tace su d'an jira a kammala shiryasu. Haris daman tuni ya yiwa su Mami waya,sai gasunan hardasu Daddy saidai Umma batazo ba saboda alkunya. Sai wajen isha'i aka sallami Zahra,suka dunguma gida. Saidai fa Mami ta kafe lallai wajenta zata tafi,Tasleem da Haris suka hau roko Allah da annabi s.a.w,Daddy ya tsawatar mata akan cewar ta barsu su wuce gida,hakanan ta hakura,tana komawa ta tura dattijuwa mai tayata aikace aikacen gida(Delu) ta zauna da Zahra. Gida fa yayi dadi.

Washegari da safe,Tasleem tun saukowarta bayan ta ajiyewa Haris kayan kari,saita shashance a wajen Zahra da baby. Yaron ya shiga ranta ainun,tana mai jin kunyar abunda ta aikata a baya na zubar da cikin da tayi da saninta. Fitowar Zahra daga wankan jego ta zaro ido
"Lala lala,antina har yanzu yayanmu bai tashi bane?"
Tasleem ta mike da sauri,shaf ta sha'afa
"Na shiga tara,nasan ma tuni ya shirya abinsa."

Ta fita tare da baby cikin sauri,delu da Zahra suna dariya.

Zaune ta sameshi yana kurbar ruwan tea babu ko madara,ido kawai ya zuba mata fuska ba walwala. Saidai can kasan zuciyarsa ta burgeshi ainun tayi kyau da baby. Ta karaso ganin bai taba komai ba,ta kama kofin da yake shan ruwan tea ta kurb'a,ko sugar bai sanya ciki ba. Langab'ar da kanta tayi gefe tana mai kashe murya
"My king, I am sorry please."
Yasa hannu ya karb'i yaron,ya dan kama hancinsa yana murmushi
"Zuwanka yasa matata ta mance da duty dinta,ina kuma ya kasance yau itama ta samu bebinta,hum?"

Ya karashe yana harararta,murmushi tayi ta dafa kan bebin
"Ka fadawa daddy,mominka bazata tab'a mancewa dashi ba koda ta haifo kanwarka don yanzu haka ma she's pregnant."
Ta karashe tana duban idanun Haris. Yayi azamar jefomata tambaya
"Are you serious?"

Tayi murmushi
"Hum, lallaima my king,yaushe rabon da kaji nace maka ina period? Count it."

Yayi tsam,kwarai an kusa wata uku rabonsa da yaji hakan.
"Itama baka tausayinta ne? Bazata iyaba,nauyin zaiyi mata yawa,zan dai turo Delu."

Ya tunano kalaman Mami,hamdala yayi don murna kafin ya rungumeta cike da tsantsar so da kauna.
Ranar suna yaro yaci sunan Abba,wato Hussein suke kiransa da Daddy.
Sai ya zamana,Tasleem tana kula da Daddy,Haris yana kulawa da ita. Alokacin da cikinta yake wata na biyar aka sanya ranar auren Hindatu,hakanan suna da biki na yanmatan Kazaure saidai fafur Haris yace bazataje ba. Tayi fushin tayi koke koken amma a banza. Mamma tace ta hakura,tana kallo su Yasmeen dama sauran yan uwa suka wuce,ita kuwa Hasina bata samu zuwa ba sakamakon bikin yayanta Hayat da akeyi da matarsa Samira wacce itama dole akayi ya aureta sakamakon abin kunyar da yayimata kuma gata cousin dinsa.

Ranar daurin aure, Tasleem k'in daukar wayar kowa tayi don haushin bataje ba. Tana zaune a falonta tana chanje chanjen tasha taji ana kwankwasa mata kofa. Baba maigadi ne ya sanarmata tanada bak'uwa. Tace ya shigo da ita,tayi matukar mamakin ganin fuskar da batayi zato ba.. "MANAL?" Ta ambata a fili.

Ta k'ara k'iba tayi kumatu,bak'ar fatarta sai shek'i takeyi idan ka cire kurajen daya fito ya b'ata gefe da gefen fuskarta kadan. Tana murmushi mai bayyana hakora,yayinda kwalla suka cika idonta tace
"Baby Tasleem tamu,nice dai Manal."
Tasleem ta rungumeta cikin tsananin farincikin ganinta. Taso zuwa wajenta saidai rashin sanin hanyar had'uwar ne babu. Ta jata sukayi ciki. Nan hira ta b'arke,inda Manal take bata labarin irin kaunar da mijinta keyi mata,ba don ma ita d'in tana tsoron Allah ba da zai iya tarewa awajenta ya manta da uwargidansa. Saidai kuma yanzun suna nan Abujan tare suna zaune yau da dadi gobe babu dadi. Manal ta dubi Tasleem cikin zubar hawaye
"Mu godewa Allah da Ya kwatomu daga rayuwar bariki,mu cigaba da nemawa yan uwanmu gafararSa. Naso kwarai na kaiwa Dalal ziyara saidai ya tabbatarmin muddin naje toh a bakin aurena.

Hibba kuwa naje da kaina na sanarwa iyayenta rasuwarta,wallahi babanta har suma yayi a karshe yace ya yafemata zunubanta. Don kuwa yasan wacece Hibba a baya,babu ruwanta kuma tana kare martabar addininta a ko'ina saidai idan Allah Ya kaddarowa bawa abu babu wanda ya isa ya chanjashi."

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 31"

Post a comment