Results

YAR BARIKI book 2 page 23


Ta hau kukan kissa,da azama ya riko fuskarta yana kasheta da wadannan mayataccen so na musamman kuma nata ita d'aya
"Menene abin kukan? Kinaso ne na rasa kwanciyar hankalina? Toh wai ma menene zaki sayo?"

Nan take ta saki fuska,saidai bata da niyyar sanar dashi sakamakon surprise da take shirin yi mishi. Ta muskuta tana kallonsa ta gefen ido kafin ta rausaya kanta ta mak'ala kafad'a d'aya
"Um um,bazakaji ba,idan na siyo na kawo zaka gani ai."

Ya daga kafad'a kadan gami sannan dai ya tab'e baki kamar yanda ya zamto masa jiki
"Ok,saikin dawo kenan,kuma ban baki iznin zuwa ko'ina ba daga can,gida straight."

Ya k'arashe yana kokarin mikewa,ta saki ihu tana mai mak'alo wuyansa tana dariya
"Woo!! That is my king! Love you so much." Mintsili ya kaiwa fatar cikinta,karamin ihu ta sanya babu shiri ta sakeshi tana mai sosa wajen. Yana shafa wuyansa ya dubeta
"Kijimin mace zata karyamin wuya?"
Ya dauki hularsa da agogonsa yayi gaba

"A fito a bani breakfast."
Ta mike tana mai turo baki har lokacin bata bar susar wajen ba,ita kam wani sa'in har mamakin Haris takeyi,idan yaso akwai matsanancin iya sarrafa mace da kula da ita,idan kuwa dan kananun muguntar tasa suka motsa toh fa sai a hankali.

Har ya kammala tayo mishi rakiya bata sakarmishi fuska ba. Bayan yayi sallama da Zahra,ya samu Tasleem na kokarin ajiye jakarsa a k'asa ta shige ciki abinta.
Da azama ya rik'ota yana janyota
"Wai fushin na menene?" Tayi shiru,saida yayi gyaran murya ya dubeta
"Zan maki wak'a fa?"

Dariya ta sub'uce mata tunanowa da tayi da wak'ar d'azu wanda tasan ba haka akayita ba. Murmushin shima yayi
"King ya akayi ka iya wak'a har haka? Alhalin naga kallo bai dameka ba."
Harara ya jefo mata
"Aka fadamaki bansan me duniya ke ciki ba? Bar ganina haka fa,nima a baya ko? Hum um,saina dawo."

Dariya sosai takeyi har ta juya zuwa ciki,Haris badai iya bada dariya ba,ita kam bata tab'a kwana da fushinsa ba. Ya iya tarairayar matansa kwarai.
*******

Misalin uku da rabi na rana ta fice sanin da tayi ranar alhamis ce maigidan yana azumi kuma shi da dawowa sai magrib kuma ba aikinta bane.

Shoprite ta nufa kai tsaye anan kan titin Zoo road. Tayi fakin ta fito cikin shigarta ta kamala,wato riga doguwa ta abaya da karamin hijabi iyaka kirji. Babu ko hoda a fuskarta hakanan ta sanya safar k'afa.
Ta rufe motar ta shiga, bayan ta kammala ta fito da zummar nufar motarta. Kamar daga sama taji ana kiran tsohon sunanta
"Baby! Baby!!"

Sanin da tayi ba ita kadai aka tab'ayi mai sunan ba yasa bata juya ba saidai gabanta yana bugawa da sauri ba tare da tasan dalilin ba. Taji ansha gabanta,ta dago kanta a fusace,saidai ta sassauta kadan ganin wanda ta sani ne,fuska a daure ta bude baki zatayi magana,saidai kafin takai ga cewa komai ya tareta
"Assalamu alaikum."

Dole ta amsa mishi,ya numfasa da murmushi dauke saman fuskarsa
"Baby aure babu ki gayyata? Ai ki gode Allah domin kuwa yanzu yan kungiyarki sun tarwatse. Ke kam Allah Ya kwaceki. Momi da yaranta su na kaso."

Tunda ya soma maganar bata saki fuska ba saima kokari da takeyi ta bude motarta, jin abunda yace yasa taji faduwar gaba, ta dubeshu babu shiri
"Menene ya faru haka dasu? Ina Hibba da Dalal? Manal fa?"

Ya matso yana mai jingina bayansa jikin motarta idanunsa suna kanta,yayi 'yar dariyar da batasan manufarta ba. Nan ya labarta mata komai,ya kara da cewa
"A yanzu haka an samu Dalal,bayan da tayi hatsari a babban titin Abuja,ita kuwa Hibba,bani da labarin inda take. Manal itama tayi aure abinta."

Hawaye suka kwaranyowa Tasleem,banda innalillahi babu abunda takeyi,ta dubi BAABA(idan kun mantashi,ku duba yar bariki part1,tsakanin 1-10).
"Kana da lambar Manal?"
Ya gyara tsayuwa
"Wallahi babu,saidai ta Hibba."
Ta girgiza kanta tana share ruwan hawaye
"Barshi kawai,nagode,sai  anjima."

Daga haka ta shige motar bayan data jefa ledojin kayan siyayyarta a back seat. Ya bata wuri,taja motarta tana tafe tana hawaye ainun. Kaico rayuwa,me kenan haka? Nadama da tsantsar imani ya k'ara shigarta. Yanzu menene amfanin Bariki? Wace riba take kawowa masu yinta?
****

A can kuwa bayan tabar mall din,wani ya iso wajen Baaba,ya nunamishi camera ta wayar hannunsa,hotunan sunyi kyau sun fito yanda sukeso. Baaba yayi dariya ya shafi kumatunsa
"Mari?!!" Ya fada kafin ya girgiza kai.
"Ni yarinyar nan ta tab'a saka hannu ta mara ko? Lallai yau rana ce ta Daukar Fansa!" Ya karashe cikin daure fuska tamau yana mai tunano sadda ta daga hannu ta mareshi agaban gayu.
"Tura mishi,idan ka aika kayi blocking dinsa sannan ka cire simcard din ka karyashi."
Daga haka ya debo kudade masu dama ya bawa saurayin
"Gashi,zan ciko maka ragowar kudinka dubuhm hamisin gobe.."
Daga haka suka rabu.... !!
BAYAN  SATI BIYU


Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 23"

Post a comment