Results

YAR BARIKI book 2 page 24

Kwance take tayi rigingine saman resting chair dake nan barandar shan iskarta na kofar kicin ta waje. Ta lula cikin tunani mai tsananin gaske,har batasan hawayenta suna zuba ba. Gaba daya ta rame,fuskar nan ta jeme babu ko kwalli,rabonta da kwalliyar ma ta mance. Kallo daya zakayi mata ka fahimci lallai tana cikin damuwa matsananci. Abinci kuwa bata wani cin kirki. Gaba daya Tasleem ta hargitse kai bakace wannan yarinyar bace sarkin gayu da kwalliya. Wasu hawayen suka k'ara kwaranyo mata
"Kin cuceni! Ashe zaki iya cin amanar aure har haka?! Ashe daman bazaki tab'a shiryuwa ba?! Ki gayamin da wa da wa kika kula bayan shi?!! Dame na rageki ne Tasleem! Menene banayi maki? Menene bana baki? Ki gayamin!!"

Cikin tsawa ya k'arashe maganar,hakan yasa taji kamar lokacin yakeyi mata zancen,har saida ta razana. Muskutawa tayi akan kujerar gami da kurawa jemagun dake shawagi a sararin samaniya ido,Baaba ya cuceta,ya wargaza mata farincikinta har na tsawon kwanaki goma sha hud'u. Wai itace Haris baison had'a shimfid'a da ita? Itace yake guduwa falo ya barta a daki? Tun Zahra bata fahimci komai ba har tazo gashi ta fahimta. Saidai koda taso yin maganar Haris ya tsawatar mata da cewar ta kula da nata igiyar babu abunda ya shafeta da fad'ansu. Tun daga ranar ta kama bakinta saidai ko kusa batajin dadin yanayin da antin nata ke ciki. Har ma akwai sadda ta isketa tana kuka itama ta fashe da kukan tace zata sanarwa Umma domin ta tsawatar mishi tunda ita dai batasan laifin da Tasleem din ta aikata ba,Tasleem ta haneta,tace idan ta fadawa wani bata yafe mata ba,kawai dai ta taimaka mata da addu'a kuma tabar damun kanta akan matsalar da ba ita ya shafa ba taji da lafiyar yaron cikinta.(Kasancewar ciki ne da Zahrar)

Saidai har zuwa yanzun ta daina samun sukuni da walwalar zuciyarta,ta riga ta saba da Haris,suyi wasa da dariya abinsu,ya sanyata kuka ta sanyashi fushi su shirya kansu,saidai na yanzu ya tsananta,ko girki idan tayi a banza,bazai ko kalleshi ba. Hakanan da rana in har ita zatayi abinci bazai dawo bama ballantana yaci,ganin hakan ne yasa ta cewa Zahra kowa ya dunga cin na ranar ma da mijin. A zatonta hakan zaisa ya sauko yace bai amince da tsarin raba kwano da rana ba amma saima ta lura ko ajikinsa. Ta gaji fa! Sati biyu ba kwana biyu bane! Wannan wane kalar zargi ne? Daga ganin hotuna a wayarsa shikenan sai yayi musu mummunan zargi? Bata mancewa ta fita tayo mishi siyayyar ban mamaki domin ranar birthday dinsa ne,hakanan data dawo taci kwalliyarta tsaf,tana jin tsayuwar motarsa ta kuma san zai leko su gaisa kafin ya haye sama,da azama ta kashe fitilunta,ta bude kofar ta b'uya,saidai me? Yana shigowa taji cikin tsawa tsawa yana kiranta. Da azama ta kunna fitila cikin firgici,saida ya karewa shigarta kallo na kananun kaya kafin ya dubeta da jajayen idanunsa ya dago mata wayarsa. Anan ne akayi rikitatar har takai ga ya kwad'a mata mari,yayi gaba bayan ya furta mata tsauraran kalamai. Tun daga ranar komai ya chanja.
*****

Tasleem ta ja majina kafin ta mike zaune duk jikinta ya dauki zafi,ga matsanancin ciwon kai wanda koyaushe dashi take kwana take tashi. Dakyar ta daure ta mike tana dafe bango sakamakon jirin dake kwasarta domin zuwa duba girkinta,saidai kuma tana zuwa cikin kicin din wani mugun jiri ya kwasheta,idanunta sukayita ganin komai biyu biyu,kafin duhu ya mamayesu ta zube ta gaba,goshinta ya bugu da teburin kicin kafin ta k'arasa kaiwa k'asa....!

Takai mintuna goma cikin wannan halin,girkinta ya k'one k'urmus har hayaki ya cika kicin din yana fita,yayi daidai da dawowar Haris. Kasancewar rumfar da yake parking motarsa, tana nan koda mutum ya fito daga kicin din Tasleem za'a iya hangoshi matukar anzo daidai wajen. Ga mamakinsa yaga hayaki yana fitowa,gabansa yaji ya fadi.
"Me takeyi haka?"

Ya tambayi kansa,jikinsa ya bashi babu lafiya,hakan yasa ya fito da sauri,gudu gudu zuwa kicin din,gabansa yayi mugun faduwa ganin ba'a hangen komai.

Abdulaziz direba,da baba maigadi wadanda ya zame musu al'ada,matukar ogansu ya dawo sai sun biyoshi sun mishi sannu da zuwa. Ganin hayaki yasa suka gane babu lafiya. Haris ya hau salati,yayita lalube har ya gano inda matsalar take,saidai yana sanya hannu wani azabar zafi ya ziyarceshi. Yayi kara,tuni baba maigadi ya taho da tsumma saidai bai iya murdewa ba,Abdulaziz ya amsa,bayan da Harris zaiyi ne,yayi tuntub'e da mutum. Yana tari ainun haka ya duk'a yana lalube,dakyar idanunsa suka hango masa ita.

"Tasleem!!!" Yayi maganar cikin karfi,tuni ya sunkuceta,a guje yayo waje, abdulaziz da baba maigadi suka biyoshi a baya. Masu gadin makwafta har sun shigo gano hayakin da sukayi ta waje suna tambayar lafiya? Abdulaziz ne ya koma da azama ya murde gas cylinder din. Tuni Haris ya sanyata a mota ya shiga,cikin tsabar kidima ya kasa sanya key dinma. Dole mutane sukace yayi hakuri Abdulaziz ya jasu,ya fito ya koma wajen matarsa yana mai rike hannuwanta gam,a haka har suka fice zuwa asi bitin...!

Da taimakon Allah ta farfado. Tayi mamaki kwarai na ganinta a asibiti. Babu kowa a dakin,dakyar ta d'aga nauyayyun idanunta ta dubi drip din da aka d'ora mata. Ta sauke idanunta yayin data tunano iyakar abunda ta sani. Hawayenta suka zubo,turo kofar da akayi yasa ta dubi mai shigowar. Kallo daya tayi mishi ta kauda kanta gefe. Ya daure ya karaso ya zauna gefenta,hannu yasa ya tab'a goshinta. Lumshe ido tayi hawayenta suka zubo,rabon da jikinsu ya gogu da juna tun kafin faruwar lamarin,shi kansa saida yaji wani shock wanda kuma ya tabbatar mishi lallai yayi kewarta bata wasa ba. Yayi azamar janye hannunsa,yayi hamdala a ransa jin da yayi zazzab'in ya sauka.
"Sannu,bari na kira Doctor."
Ya mike ya juya, takai hannu da zummar tsayar dashi,saidai kuma ta fasa.

Hawayenta suka k'aru,ina Haris zai fahimci shine matsalarta? Inama zai gane shine warakarta? Bata da wani fata da burin daya wuce na su dawo daidai,su cigaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da soyayya. Haris meyasa ya kasa gane cewar bazasu iya rayuwa babu juna ba? Meyasa yake kokarin k'irk'iro musu wani sabon yanayi wanda zukatansu da gangar jikinsu bazasu jura ba? Wai ta yaya za'ayi ma su iya wannan rayuwar?

Shigowarsu ta katse tunaninta,ta share hawayen fuskarta ta kauda kai. Ya lura da ita, ji yakeyi tamkar yaje ya rungumeta ya rarrasheta,saidai kuma da zarar ya tunano hotunan nan sai komai ya kauce.(Mtsw,sai kace wanda ya ga wani banzan abun a hoton.)

Likita ya tabbatar da samun saukinta saidai kuma yace dole a dinga bari tana hutawa don yawan damuwar da take ciki yasa jininta ya hau,kamar kuma yanda doctor yace yanajin ba wannan ne karo na farko data kamu da ciwon ba result ya nunamusu daman tana dashi. Ya kara duban Haris bayan sun fito yace
"Madam dinka tana da damuwa kwarai,gaskiya ya dace ka kula da lafiyarta kasan menene damuwarta kayi kokarin magance mata."
Haris yayi godiya.

Zahra daga makaranta nan ta zarto tare da Hibba. Sun samu tana bacci,suna zuwa Haris ya tafi gida. Jimawa kadan sai gasu Mami da Umma harma da Daddy da Abba.
Sun dan jima,har suna ta'ajibin irin ramar da tayi,duk ta k'are. Alhaji Aliyu wanda Hankalinsa ya gaza kwanciya ya dubi Haris wanda tuni ya dawo harda guzurin kayan ciye ciye da sha,yace
"Wai daman ta jima tana  ciwo ne?"

Related Posts

Subscribe Our Newsletter

0 Comments to "YAR BARIKI book 2 page 24"

Post a comment